Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta firgita daga jin an ambaci yobe har taso k'ara saka Mahmud cikin tunani amma sai ya waske. "Haba no wonder naganku jigum-jigum ai dole" "Su rasa inda zasu kaika sai wancan garin? Dukkansu kallonta sukeyi yanzu kam,kowa da abinda ke ransa. Abbah so yake yayi maganar 'yar uwarsa Khadija amma azahiri yakasa furtawa,aransa kuwa harhad'a maganar yakeyi tsaf "Yauwa Alhamdulillah fad'uwa tazo dai-dai da zama tunda Khadija nacan ma na tabbata baka da matsala da komai" Maganar dake ran Abbah kenan amma afili ya gagara furtawa,nawi yakejin harshensa yakeyi akullum indai akan Khadija ne. Mahmud kuwa mamaki yakeyi aransa shima naganin ko Anty ma bata kawo batun sauk'in da hakan keda shiba ganin Anty Khadija nacan ko kuma irin yaga ta nuna farin cikinta akan faruwar hakan. Alwashi yaci aransa nasa cewa sai ya tambayi Anty yaji ko me Anty Khadija ta musu suka tsaneta haka,kowa baya son abu agidan indai al'amarin yashafeta ne. Ahakanma gara Anty dan ita idan ya tambayeta abu tana d'an bashi amsa koda kuwa da fad'a-fad'a ne sa6anin Abbansa da ko magana baya masa indai ya had'a da batun Khadija ne toh sai dai kallo da idanu babu magana ko kad'an. Abbansa bai ta6a bashi amsar tambayoyin dayake masa ba akan Anty khadija ko da kuwa sau d'aya. Washe gari kuwa yaje yasamu Anty da tambayar laifin da Anty Khadijan ta musu da har suka d'auki irin zafi haka da ita! Masifa Antyn ta fara masa kamar ta ari baki garin masifar ne ta d'an kuskure ta ce masa "Bana son fitina Mahmud kai komai sai ka bishi da tambaya ne? Meyasa bazaka bar komai ayanda kaganshi ba? Ina zaman zamana kar ka kuskura kaja min fitinar dana kwantar da ita da kyar" "Fitina kuma Anty wace iri? Ya tambayeta da mamaki kwance akan fuskar sa. "Irinta uwarka"πŸ™ˆ Tabashi amsa kai tsaye. "Ah ah naji ne kince kin kwantar da ita da kyar toh kuma ni bansan fitinar ba Anty laifine dan na tambaya? "Katashi kaban wuri ni banason hauka" Ta fad'i da matukar 6acin rai dan zuwa yanzun sosai ranta ya fara 6aci dan ganin Mahmud d'in nason ya k'ureta. Bud'an baki yayi zai sake magana ta mik'e tsaye kamar andannna mata remote hanyar fita ta nuna masa "I said get out from this room now" Da wata uwar tsawa tayi maganar hakan yasa ya mik'e tsaye yana k'ara gyara zaman rigar dake jikinsa har ya fara tafiyah sai kuma ya juyo ya kalleta sannan yace "Hakan da kuke yi ne yake k'ara samin sha'awar tafiya wancan garin dan na san meke faruwa na tabbata zanji koma menene acan d'in ba kamar yanda kuka barni acikin duhu b......... Bai k'arasa ba ta kar6e maganar "Mahmud kar ka ce min da kanka kacika wannan garin dan ka muzanta ni........tak'ara sa maganar tana nuna kanta da yatsanta. Murmushi yayi sannan ya lumshe mata idanu. ga dukkan mai wayo yasan hakan dayai alamar tabbatarwa yayi mata. Haushi sosai taji sai kuwa tace "Za ko kaci ub........πŸ™ˆ Juyawa yayi ya fara tafiyah ahankali yana jijjiga kansa yana fad'in "yau kad'ai Anty kin koyi zagi narasa ma'anar hakan fah" cewa tayi "Eh zaka ce haka mana dake ka maidani sa'ar ka,zanga kuwa ubanda zai barka kaje can d'in ai, idiot" Bai kulata ba yanzun kawai ya cigaba da tafiyarsa har yabar cikin d'akin,yana k'ara jin mamakin Antyn yanda ta wani d'au zafi akan wannan simple abun. Ai dole ma naje kodan na tambayi Anty Khadija abinda ta musu suka tsaneta haka. Kwanaki na k'ara ja lokacin tafiyar Mahmud na sake k'aratowa,kamar yanda hankalin Anty ke k'ara tashi akan batun tafiyar,ita aganinta tasamu ta d'an sake babu batun dangin miji ya zai je ya jaji 6o mata jaraba tana ji tana tana gani. _Kuji fah ikon Allah_ Babu irin k'ok'arin da batayi ba akan tafiyar amma abun yaci tura gani take kamar ma himma take k'arawa Mahmud d'in akan tafiyar. Shikuwa dagangan yake komai akan batun tafiyar duk dama har yau Abbansa baice komai akai ba amma yanda Antyn tayi reacting so yake yaji dalilinta nayin hakan kuma tak'i sanar dashi asalin dalilinta dan haka yake abinsa da gangan dan yata tunzura ta ko zata yi zuciya tafad'a masa dalilin amma shiru. Sai dai tayi ta hantarar sa kamar wani yaro d'an goye ga wani zafin rai data d'auka ta d'orawa kanta da ya rasa manufarsa kwata-kwata. Tafiyar saura baifi sati ba ne Daddyn Teemah yazo Lagos anan Abbansa yake fad'a masa cewa ai mahmud d'in zai zo Yoben Bautar k'asa. Daddy dayaji hakan bak'aramin farin ciki yayi ba musamman kodan matarsa Khadija yasan zatafi kowa farin ciki da wannan batun,amma bai nuna zak'ewarsa ba tunda yaga yanayin Yah yusuf d'in asanda yake maganar shima bawani farin ciki ya nuna da faruwar hakan ba. Sai dai duk da haka sai da yatambayi meyasa kuma sai yanzu Mahmud d'in zaiyi service?...... me yasa baiyi karatun da wuri ba?......... Amsa Abbah ya bashi atakaice. Haka suka rabu da Yah Yusuf d'in Daddy nacewa Allah ya kawo shi lafiya ina nan ina jiran isowarsa. Shima dagangan ya daina sako zancen Khadija a tsakaninsu dan ganin kamar yah yusuf d'in baiso. Dan idan ya matsa masa da tambayar ya sanar dashi laifinta kodan ta nemi yafiyarsa ma sai yaga yatsaya jim kamar an dasa shi wani lokaci har k'walla yake sharewa amma still bazai bada amsa ba. Ana washe gari Mahmud zai tafi ma Antyn kamar ba d'anta ne zaiyi tafiya ba,ita adole fushi takeyi dashi har wani lokaci ji yake kamar yafasa tafiyan amma inah sai yaga bazai iya ba yazama dole ne ma yaje shi d'in. Zuwa yayi ya zauna akusa da ita sai tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da kallon television d'in data keyi. Shima sai ya maida kallonsa zuwa inda take kallan sannan ya fara magana "Yanzu Anty fisabilillahi kin kyauta min? ace zanyi tafiya amma ko kulani ma sai ki dai nayi bayan kinsan dole ina buk'atar sa hannunki ashirin da zanyi? Ni ne fah Anty ki ganni dakyau fah idan na tafi ba dawuri fa zan dawo ba" Amsa shi tayi da "Sai mai toh Mahmud,idan katafi dan Allah karka dawo Har abada kaga ko zan damu" Ido ya zaro waje tare da fad'in "har abada dai Anty" "Uhm,ka gwada mana kagani" ta bashi amsa. "Niii d'in "ya kara tambayarta Harara tabisa dashi kawai "Toh aini Anty bazan iyaba,ina zan iya rayuwa babu ke akusa dani!" "okay sai yanzu kasan amfani na kenan,daka maida ni tamkar abokiyar wasan kan kamanta ko? "Bahaka bane fah Allah,haba Anty kefah uwace ,kar kifiya son kanki dayawa mana,ki tuna abaya dalilin bin umarninki nayi shekaru ina zaman banza agida batare da na k'ara sa makaranta ta ba,alokacin fah dakin bari nayi na tabbata da yanzu na wuce wannan level d'in da jimawa,amma haka na biyeki daga k'arshe kuma bagashi ba ahakan dole nayi batare da burin naki yacika ba. Toh wannan d'in ma haka kike so na kuma yineh? Bayan inada right d'in yin hakan Anty? "bama wannan ba Nidai dan Allah ki daina fushin nan kisamin albarka awannan tafiyar tawa." Kinji". Haka yayi ta lalla6a ta harta sauk'o daga fushin amma dai har yanzu ranta bai d'auki tafiyar ba. Haka dai ta hak'ura tanaji tana gani washe gari ya kama hanya yayi tafiyarsa dolenta tayi masa fatan Alkhairi badon taso ba sai dan son da take masa a matsayinsa na d'anta k'wallin k'wal a duk fad'in duniya. Juyi mahmud yayi zuwa d'ayan gefen sannan yace wannan tambayar ta dawo kanki mummy dole in tambayeki dan so nakeyi in sami amsa ta kafin nabar garin nan. *Serlmern ku ce* 😍 [10/2, 5:55 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DA* *BAZAR MU MUKE* *TUN'KAHO* 😍 In dedication 2 my sistersπŸ‘‡πŸΌ *Ummie* *Maijee* *Zuwairah* *Ameerah* and my lil baby sis *Miemie.* Allah ya barmin ku....(Ameen) Masoya nagode da addu'o'inku I'm safely arrived,nima ina muku fatan alkhairi gaba d'ayanku,duk wacce tamin addu'a Allah ubangiji ya saka mata da mafificin alkhairi,Allah ya kar6i ibadunmu.πŸ‘πŸ» *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Mathematics may not teach us how to add love or how to minus hate. But it gives us every reason to hope that every problem has a solution. πŸ…Ώ *18* _Back to labari_ ........ Sam Mahmud baiyi wani baccin kirki ba adaren,sai kusan 3:00 o'clock kafin baccin ya d'auke sa bayan yayi sallahr nafila sannan yayi baccin. Sallar asubah ma da kyar ya yi ta acikin d'akinsa,saboda baccin dake fisgar idansa,yayin da su Abbas suka wuce masallaci dan sunta mar knock amma bai bud'e k'ofar ba a tunaninsu baccin gajiya ce ta d'ebesa basu san cewa kwanan zaune yayi ba shikam. ***** Washe gari ma Mahmud bai fito ba sai kusan 10:16am kafin suka ganshi. Ad'aki ya samu Abbas yashiga da sallamah abakinsa amma bai tsaya jiran umarnin shiga ba ya shiga abinsa. Abbas na zaune akan cough da system a gabansa sai kawai yaga mutum yashigo,danshi sam baiji sallamar da mahmud d'in yayi ba dan gaba d'aya hankalinsa yatafi ga abinda yake kalla. Juyawa yayi suka had'a ido da Mahmud take sai mahmud d'in ya mik'o masa hannu. Shima hannun ya mik'a suka tafa "Ya ne guy u look bored,meke faruwa ne"? Abbas d'in ya tambayeshi. Tsaki kad'an Mahmud d'in yaja sannan yace "kabari kawai gajiya ce wlh" "Hmm jiya danake koranka kaje kayi baccin ai iskanci kaso yimin sai gashi kuma tun ma ba'ayi nisa ba kana complain" Abbas ne yafad'i hakan yana d'age gira sama. Mahmud baiyi magana ba illah tashi da yayi tsaye sannan ya d'anyi mik'a,Abbas d'in sai ya sake binsa da kallo yana murmushi yace "sai wani abu kake fah kamar mace yanzu akan baccin ne kaketa wannan abin"? "Allah baccin bai isheni ba ne" "Sai ka koma ai ka cigaba dayi tunda bai isheka ba" inji Abbas "Mummy nakeso ingani ne shiyasa in badan haka ba ai ko tasowa ma bazanyi yanzu ba." Abbas d'in ma mik'ewan yayi jin Mahmud ya ambaci mummy. Yace "muje toh nima ban shiga ba har yanzu" Atare suka fito suka isa babban parlour,koda suka isa babu kowa acikin d'akin hakan yasa suka zauna akujera suna d'an hira. Zaman sun baifi da 7minutss ba saiga mummy tafito,murmushi ta sake data gansu,sai kuwa ta nufosu fuskarta cike da annuri. Haka tazo ta zauna suka gaisa ta tambayi Abbas ya yanayin garin yace "Alhamdulillah mummy" "Masha Allah" tace Sannan ta juyo ga Mahmud shima tamai ya gajiyan hanya da kuma bak'unta, cewa yayi "wlh mummy jinayi ma kamar yanzu ne nayi tafiyar tsabar gajiya" "hmm" kawai Abbas yace Mummy kuwa murmushi tayi sannan tace "sai a hankali ai", gacan break fast d'inku a dinning Daddynku ma shikam yafita tun d'azu,bari na k'ira Teemah dan itama bataci ba ni tun safe ma banganta ba" Tana fad'a tamik'e tsaye. Amma sai Abbas yadakatar da ita da fad'in "haba mummy dakanki? yi zamanki bari na mata magana." "Toh shikenan tunda ka hutar dani ai." Tayi maganar tana komawa a inda ta tashin. Abbas kuwa wucewa yayi kamar da gaske,ya nufi d'akin Teemah,daya isa bakin k'ofar sai kuma ya tsaya,sai ya rasa ya zaiyi ma,to k'ira zai kwalla mata ne ko kuma sallama zai mata idan tafito sai ya hankad'a keyarta zuwa parlourn. Rasa wanda zaiyi acikinsu yayi,sai kawai yasa hannu ya tura k'ofar ahankali ya shiga ciki. Gani yayi d'akin bakowa,sai ya hau rarraba idanunsa,yaune farkon shigarsa d'akin nata tunda yazo gidan. D'akin tsab ba wani datti sai dai tabar windown baya a bud'e. Takawa yayi a hankali ya isa wurin windown,labilen ya d'aga sai ya hango yanayin wurin ya matuk'ar k'ayatar dashi. Daga inda yake tsayen yana iya hango cikin lambun dake gidan nasu,sai yaji hakan ya matuk'ar k'ayatar dashi hakan yasa ya 6ata lokaci agun yana kallon wajen har ma baisan lokacin data fito ba. Itama bata lura da shi ba dan yunwa na cinta sosai sauri ta ke ta shirya dan taje ta samu abinda zata ci,kuma kokad'an bata zaci wani zai shigo mata d'akin ta ba. Allah sai ya taimaketa bata cire towel yau ba kamar yanda tasaba. Gaban mirror ta wuce tazauna tana k'ok'ari d'auko man shafawan ta ne ta hango sa tacikin mirrorn,firgita tayi sosai take saita mik'e tsaye daidai shikuma ya juyo. Kallonsa ta tsaya yi kamar yanda shima yake kallonta. Tsawon mintina biyu kafin ya kauda kansa gefe. "Astagfirullah" Yace azuciyar sa sannan ya dawo da kallonsa kan fuskarta. "Ya akayi ne kin wani tsaya kallona" Batayi magana ba still illah k'asa da tayi da idanunta. Ganin hakan yasa ya juya ya koma wurin windown. "Meyasa kike bari abu'de?yajeho mata tambayar. "Mantawa nayi" Itama ta fad'a atakaice. Barin wajen yayi yasake dawowa inda taken "kidinga kulawa idan zaki kwanta kinji" kai ta d'aga masa alamar taji Daga nan sai ya nufi hanyar fita harya kusan isa ga k'ofar kafin yace "kiyi sauri ki shirya ki fito mummy na k'iranki" "Uhmn" ta masa masa dashi daga nan sai ya fice abinsa. Sharp-sharp ta shirya tafito tasame su a palourn. Zuwa tayi gefen mummy ta zauna sannan ta gaisheta daga nan tagaida su Abbas ma. Mummy ce tafara mik'ewa tana fad'in "bismillanku" Teeamh ce tafara biyo bayanta sannan su Abbas ma. Bayan sun isa sun zauna ne mummy tace toh teemah tayi serving d'insu. Tashi tayi ta had'awa kowa nasa sannan tahad'a nata ma daga nana ta zauna. Mahmud ne ya lura da yanda take shan tea d'in yau ba bu yanga sai yace "cin abincin daman zuwa-zuwa ne" Mummy ce takar6e zancen dafad'in "ai in kaga haka toh yunwa ne yaci k'aniyarta" "Ai kuwa naga alama"yana murmushi yayi maganar. Abbas kama bai kulasu ba illah kallonta dayayi sun kuwa had'a idanu sai tayi saurin kawar da kanta gefe. Itace tafara tashi a table d'in ta koma d'akinta. Su kuwa suna gamawa Mahmud yace su fita yawo cikin gari. Haka suka fice yayinda Mahmud kejan motar sikuma Abbas na gefensa azaune. Yobe state university(YSU) suka je dan Mahmud yace akwai wani friend d'insa dake lecturing acan. Basu suka dawo gidan ba har saida suka yi sallar azahar. 15minutes to 2 suka shigo gidan,direct kuwa suka nufo parlour dana tun d'azu Mahmud ke mitan yunwa yakeji kuma yayi-yayi da Abbas akan su tsaya wani wuri su d'an ta6a abu sam Abbas yak'i shi wai sai abincin gida zaici. Zubewa sukayi aparlourn yayinda suna d'an ta6a hira. Muryarsu ne yasa mummy fitowa anan ta samesu sun yi d'ad'd'aya akukera,Abbas sai mita yake yi wai Mahmud bashida dauriya ya fiya ragwanci. "Mahmud kuma yace angaya ma yunwa ta tana yi da wasa ne? "Toh cinye ni mana kafin abincin ya iso"inji Abbas kafin Mahmud yayi magana sai sukaji muryar mummy tanace musu duk su taso abincin ai tun d'azu yake jiransu. Sai alokacin suka lura da fitowarta,gaida ta sukayi ta amsa tana zolayarsu daganan suka mik'e suka wuce kan dinning d'in gaba d'aya. Tun kafin su isa mummy taketa kwalla k'iran Teemah, jin Teeman ta amsa ne yasa mummyn yin shiru suka zazzauna. Mahmud ne yace "wai ita mummy kullun wannan yarinyar sai an gayyatota cin abinci ne kafin takeci" Mummyn amsa masa tayi da fad'in "ai inka barta kace sai ta nema da kanta toh kuwa zaka dade baka ganta ba,shiyasa nake sata ci acikin jama'an wai ko zata saba" Mummy nagama fad'in hakan sai ga Teemah ta 6ullo,binta sukayi da kallo harta k'araso. Abbas aransa yace "masha Allah" dan sai yanzu ya lura da kyaun datayi dukda bawai ta canza kaya bane tun na safen ne data saka ajikinta amma kuma sai yanzu ya lura da kyaun datayi dan d'azun bai kula da hakan ba. Jiyayi yana jin zafin kallon da suke mata d'in gaba d'aya. Zuwa tayi itama ta zauna akusa da mummy sai ya kasance tana tsakanin Mahmud ne da mummyn. Mummy ce tace Teeman ta tashi tayi serving d'insu abincin. Zaro ido Teemah tayi waje tare da fad'in"mummy nikuma? Da "ehh mana Teemah" mummyn ta amsa mata. Sai tace "amma mummy idan na saka kowa sai ya cinye nasa gaba d'aya" "Naji ni dai tashi kisa mana abinci yarana duk yunwa suke ji" Tana jin haka sai ta turo baki gaba sannan tace "wlh mummy kullun wareni kikeyi agidan nan tunda kika gansu,nima indai hakane gidan daddyn Abuja zan koma abuna" Dariya tabasu gaba d'aya,amma sai dai mummy da Mahmud ne suka dara Abbas kam murmushi kawai yayi. mahmud ne yana d'an dariya yace "kai mummy ki barmin lil sis d'ina pls adaina 6ata mata rai" "Hmm ni wlh dariya ma kike bani Teemah toh har ina abin fishin yake anan,kede Allah ya rabaki da mugun halin nan Teemah" "Kauda kanta tayi gefe haushi kamar zatayi kuka. Mahmud kuwa ganin bazata saka musu abincin bane yasa shi fad'in "banace zan kaiki da kaina ba maza tashi kisa mana abinci kinji baby sis rabu da mummy" "Ai cemin tayi mai mugun hali" "Sorry 'yanmata wasa take miki fah" ya fad'a yana kallonta. Zata sake magana yace" haba mana Teemah yunwa fah nakeji" Abbas kam sai rarraba idanu yake akansu ya kalli wannan ya kuma kallon wannan. Dayaji mahmud yace yunwa yake ji ne shima yace "Allah dai ya shiryaka mahmud" "Ehh naji haka kurun ai da gaskiyata ko so kake nayi shiru yunwan ta illatani ne" "Kai kasani ai" Abbas d'in ya fad'a dajin haushi Daganan Teemah ta tashi tana turo bakin ta zuba musu abincin harda na mugunta sannan tasaka nata kad'an ta zauna. "Hmm mummyn tace tana k'ara yin murmushi ahankali tace "Teemah ko rigima in ance mugun hali kuma tace ita ba ita ba,inbanda haka ina zasu kai wannan abincin." Bata kula magananar mummyn ba Zama tayi suka fara cin abincin. Wurin shiru bakajin k'aran komai sai na cokula. Kowa yayi nisa dacin abincinsa yayinda Teemah kwata-kwata spoon d'inta uku sai juya cokalin takeyi a hannunta kamar mai k'rga abincin. Mahmud ne ya lura da ita ganin bata cid'in ne yace "Yadai kici mana keda kika ce kowa sai ya cinye nasa gaba d'aya,ahakn ne zaki cinye?" Sarai tasan da ita yakeyi amma sai tak'i kulasa ko d'aga kai ma takalle sa k'inyi tayi. "Barta mana wai ita sarkin wayo ba" cewar mummy Mahmud kuwa barinta yayi ya sake d'iban wani abincin yakai bakinsa,daganan ya d'ebi wani ya nufo ta dashi. "hun haahh" yace yana kallonta,itama da mamaki tabi abincin da kallo sannan ta kallesa. "Open your mouth mana" Yafad'a da seriuos tune Sai da ta kalli mummy tukun sannan ta kalli Abbas sai ta ga dukkansu babu wanda hankalinsa yake wurinsu. Bud'e bakin tayi yasaka mata abincin. Abbas kuwa duk abinda ya faru yana lure da shi,sai da yaga zata kalleahi ne kafin ya maida kansa k'asa tamkar tun zamansa awurin bai kalleta ba........bata san tun d'azu yake lura dasu ba, jiyayi tamkar ransa zai fita ajikinsa data kar6i abincin,jiyayi ya gagara natsuwa sam,"innalillahi yake ta fad'i azuciyarshi bai san dalili ba amma sai yaji ya tsani wannan scene d'in. Take tunanin baya ya fad'o masa arai,irin yadda yake kula da ita shima yake bata abinci abaki,yau ga wani daban ya fanshe shi.......... Haka yaci gaba da bata abincin ita kuwa kamar jira takeyi daman abata sai kar6a takeyi mummyn kam cewa tayi "aikuwa aiki ya sameka Mahmud indai wannan ce" Maganar tata ce ta dawo da Abbas cikin hayyacinsa sai alokacin ya lura ashe Mahmud cigaba da bata abincin yayi ko kunyarsu bayaji. Shikuwa Mahmud zuciyarsa d'aya yake bata,dan yasan is not a crime tunda sistern shi ce. Spoon kusan biyar takar6a a hannun Mahmud sannan tace ya isheta. Wani uban tsakin da Abbas yaja harni ma na tsorata da ita,sai dai sa'an shi d'aya azuciyarsa yayi shiyasa babu wanda yaji. Cak ya mik'e tsaye ransa amatuk'ar jagule amma babu wanda zai fahimci hakan sai wanda ya sanshi sosai,saboda yanayin yariga yazame masa jiki,shiyasa babu wanda yagane halin dayake ciki. Ummansa kad'ai ke fahimtarsa aduk halin dayake ciki sai ko Daddynsa. D'akinsa yawuce direct yana shiga ya hau fincike riga kamar ita ce tamai laifin. Bayi ya shiga ya watso ruwa ya fito dayake yana ta fad'in "la haula wala kuwwata illah billah"acikin zuciyarsa tunda abin yafaru sai hakan yasa yad'anji sassauci. Kwanciya kawai yayi agadon dake d'akin sa cikin sa'a kuwa sai bacci ya d'auke sa. Yayin da Mahmud yake can zaune da mummy Teemah kuma tashiga dan shirin zuwa islamiya. Fitowa tayi da hijab d'inta ahannu tace "toh mummy na shirya yau wazai kaini"? "Je ki d'auko kud'in adaidai ta ajakata"cewar mummyn. Har Teemah ta juya da nufin zuwa d'akin mummy sai Mahmud yace ta dawo zai kaita. "Dauko wanda zaki dawo dashi toh"mummyn tasake fad'i Mahmud d'in ma sake cewa yayi "bari zan d'auko ta mummy idan sun tashi" "Karfa a takura ka Babana"mummyn tafad'a tana kallon sa "Haba mummy akan d'an wannan d'in" Shima yabata amsar maganar tatta yana murmushi Teemah hijab d'inta tasaka ranta fari k'al dan dama ta tsani hawan adaidaitan dan bata samu ma da wuri gashi ana zabga rana. Koda suka fito kuwa Mahmud sai da ya lek'a d'akin Abbas da niyan sanar masa da fitar tasu amma sai yaga ma yana bacci. Hakan yasa ya fito suka tafi abinsu. Kamar yanda yafad'a d'in kuwa ana tashi yawuce ya dawoda da ita gida. _Comment share and_ _vote pls_ 🀞🏻 *Salmern ku ce* 😍 [10/2, 5:55 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 dukkan masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs.Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Fake friends are like shadows, always near you at your brightest moments but nowhere to be seen at your darkest hours. πŸ…Ώ *19* Mahmud shegen surutu ne dashi, gashi baya da bak'unta sam gashi da iya jan mutun da hira hakan yasa awannan fitar da sukayi da Teemah har sabo ya shiga tsakaninsu na ban mamaki. Tun daga ranar shiyake ajiyeta a school ya kuma d'auko ya dawo da ita gida da yamma ya ajiyeta a islamiya kuma. Tare suke zama suyi hira haka abinci ma bai fasa bata ba kamar yanda ya fara tun farko sai ya mik'e kawai da haka, dan suna zama a kan table zai fara bata sai yaga tace mar tak'oshi kafin yaci shima, wani lokaci har d'akin sa take zuwa dan kawai suyi hira idan taga Mahmud d'in bai zo nemanta ba,idan akayi rashin sa'a kuma ranar yana d'akin Abbas sai fatattako ta tmdawo tana ture-turen baki tana mita,mummy najinta kuwa aja bakin har sai tayi kuka. Koda lokacin shiga CAMP d'in Mahmud yayi ma Abbas ne da Teemah suka rakashi,Teemah harda d'an guntun hawayenta tana ta mar shagwa6an wai zai tafi ya barta shikuwa Mahmud yanata mata dariya. Abbas haushin hakan yaji, sosai abun ya sosa ransa har ya gagara juran ganin abinda Teeman takeyi dan Mahmud zai shiga CAMP ai baisan lokacin daya sa hannu ya finciko ta da k'arfi ba, bai tsaya ko'ina ba sai daya danganta ta da cikin motar ya tura marfin ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima ko takan Mahmud d'in ma bai k'ara bi ba. Idan kagan shi zaka yi zaton ko gajiya yayi da abinda Teeman keyi shiyasa yayi hakan, kamar dai yanda Mahmud ma tunaninsa ya tsaya iya nan.Hakan yasa yabi bayansu da murmushi yana k'ara jinjina hali irin na Abbas d'in sam baisan wargi. Abbas kuwa takaici ne yagama cika mas kwakwalwa, suna shiga cikin motar kuwa ya d'aga hannu ya sake mata wani rankwashii mai azabar zafi dan ya yishi ne a zuciye, amma sai ya waske da fad'in cewa bata da kunya ita kokad'an, wai 'yar k'arama da ita sai fitinan tsiya. Bata fahimci mai yake nufi ba, amma zafin abinda yamatan sai yasata kuka,kukan tafara da d'an sauti dan abin biyu yazame mata ga missing d'in yah Mahmud ga kuma zalinta da akaci abanza. Takuwa k'iyin shiru da gangan ma taketa yin kukan da sauti aranta take cewa aikuwa zaka ga fitina yau d'in nan ganin idonka. Bai k'ara kallon inda takeba balle ya kulata sai da yaga kukan bana k'are bane kafin yayi parking agefen hanya da k'arfinsa sannan ya kalleta yace "Zan 6a66allaki anan wallahi idan bakimin shiru ba idiot" yafad'a yana wani zaro idanu Shiru tayi cak kamar anyi offing switch dayake daman kukan na isaknci shiyasa tayi tsit da wuri dan sosai ta tsorata da yanayinsa na yau d'in acikin ranta tasake fad'in "ashe dai ni zanga fitinar bashi ba." " _Banza jarababbiya_ " Yafad'a lokacin da yake k'ok'arin tada motar aranta ta amsa da "wallahi badai ni ba kam sai dai kai" Tana fad'a tawani kau da kai gefe kamat wata jaruma. Dayake bajinta yayi ba shima sai bai kulata ba. Tuk'in ya cigaba dayi batare da ya d'auki hanyar da zata sada su da gida ba. _Waziri ibrahim_ ya nufa ita kuwa sai ware ido takeyi da mamakin yaushe yasan unguwar kuma mai ya kawo su hanyan nan d'in, kodan ma ai bai san gari ba ba mamaki 6atan kai yayi"duk aranta tayi wannan tunanin. Hakan yasa da gwanintan ta tace "yayah nan fah ba hanyar gida bane" Hannunsa ya d'ago da niyar

Chapter 8 of 67