Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ko 'daya daga cikinsu ba dan haka sai yayi wucewarsa ciki ya nufi 6angaren dayayi niyyan zuwa. πŸ‘ŽπŸ» _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Treat your parents with loving care. You will only know their value when you see their empty chair._ πŸ…Ώ *50* Abu'de yasamu 'kofar dan haka kanshi tsaye ya tura kansa ciki ya shiga, sai de yana shiga ya tsaya daga bakin 'kofar dan ganin mutane biyu ne acikin 'dakin. Dubansa ya kai kan gado domin ya banbancewa idanunsa cikin su biyu amma tunkan tunaninsa yayi nisa yafara jiyo muryar wacce ke kwance akan agadon kunnan ta sa'kale da earpiece tana bin bakin wa'kar Umar m Shareef mai taken ( SAQAR ZUCI) ,hakan yasa yayi saurin fahimtar cewa wannan wata dabance bawacce yasani ba, 'dauke idanunsa yayi yah mayar wajen mirror inda ya hango wata kuma azaune amma kallo 'daya yai mata ya gane ko wacece ita, domin yasanta da san zama gaban dressing mirror, dan haka sai ya 'daga 'kafafunsa cikin nutsuwa ya isa gareta. Zaune take tayi zugum tun 'dazu tana kallon kanta acikin mirror 'din, sai de azahiri ba ganin kan nata take ba, tunani kawai takeyi da bata san inda ya dosa ba. Dukkan su basu lura dashi ba yanzun, dan ita wancen wayar datake sarrafawa ahannunta shiya dauke mata idanu yayin da ita kuma wannan hankalinta yatafi ga tunani, kuma ma a yadda ya shigo 'din ba lallai ne kasani ba koda kuwa kana daidai cikin hankalinka, ne dan tamkar wani marar gaskiya haka ya shigo ballantana su da kowa hankalinsa yana wani wuri ne daban. Da isar sa kusa da itan sai ya tsaya daga bayanta shima yana kallon fuskarta ta cikin madubin gani yayi ta yi kyau sosai fiye da ganinta dayayi na 'karshe, hakama ramarta ta 'dan zarta yanda ya ganta last week. Dubansa yakai ga hannayenta yaga yadda hannayen suka sha kyau cikin zanan flower baki da ja kamar kar su rabu da hannun nata sukasance haka har abada. " is it all because of th...............! " ohh no bahaka bane"! Ya fa'da tare da jijjiga kansa. Be da'de da tsayuwa awurin ba sai ta mi'ke tsaye sanadiyyan tuno maganar Ummah datayi akan ruwan wankan da aka ha'da mata tun 'dazun mai cike da ha'din kayan 'kamshi musamman aka ha'da saboda ita inda Ummahn tace mata karta kuskura ta bari ruwan ya huce batare da tayi wankan ba domin da 'duminsa akeso tayi wanka saboda zaifi kama jikinta yanda akeso idanta gama kuma me shiryata zata zo " tunowa da wannan maganar ne yasata ta mi'ke tsaye da 'dan sauri domin cika umarnin Ummahn. Amma mi'kewanta keda wuya sai ta hango mutun tsaye daga gefenta yana kallon ta, bata waiwaya baya ba sai kawai ta kalli fuskarsa ta cikin madubin tayi murmushi, jikinsa sanye yake cikin kaftan mint green 'dinkin ba 'karamin kar6ar sa yayi ba, rigar tsayinta be wuce gwiwarsa ba, hannun rigar 'daure da links, irin 'dinkin dayafi birgeta kenan acikin 'dinkun maza, yasanya hula wacce ta dace da kalan kayan jikin nasa. Hannu ta 'dago ta nufi madubin dashi daniyar ta'bashi zaton ta idanunta ne ke hasko mata shi domin taganshi ne exactly yanda tayi mafarki dashi adaren jiya, bayyananniyar murmushi tayi aranta tacigaba da fa'din " da wannan daurarriyar fuskar tashi daba ko yaushe ake ganin sakewarta ba sai lokacin da yaga dama sannan kaga murmushinsa sai inko yana tare da Daddy ne wannan kam har zaka gaji da ganin dariyar tasa alokacin" Daf da zata ta6a jikin madubin sai taji an ri'ko hannunta daga baya, hannun ta kalla inda aka ri'ke tan tabi hannun da kallo zaton ta ma Hannah ce sai kuma taga sa6anin hakan domin wannan hannun beyi kala koka'dan dana Hannah ba not even from her friends. A 'dan tsorace ta kuma juyawa takalli cikin madubin sai taga wanda ke bayan tan ne yah ri'ke mata hannun nata, sai alokacin tunaninta yadawo dai-dai sai ta juyo afirgice zuwa inda yake tsaye 'din, gani tayi shi'dinne azahiri ba mafarki ba kamar yadda tasaba ba kuma atunani ba. 'Dayan hannun ta 'dago ta rufe bakinta dashi ta zaro idanu kamar wacce tayi karya tace " _huh_! _Yayaah"!!!_ . Tafa'da ahankali bada bayyanan niyar sauti ba saboda bata manta irin tsawan daka mata ba ranar dayazo last kafin yau, shikuwa be amsa ba duk da yaji me tace saboda tun 'dazun tsayawa yayi yana kallonta sai ma 'kara binta da idanun dayake 'karayi yana wassafa abubuwa acikin ransa ciki harda irin kyan daya ga ta 'karayi, take sai yaji yana kishin duk wanda zai ganta a irin wannan yanayin. Teemah data ga be yimata magana ba kuma be motsa daga tsayuwarshi dayayi ba har yanzun sai tayi tunanin ko irin mafarkan data saba yine, hakan yasa ta 'danji haushi harda turo baki gaba tana 'ko'karin 'kwace hannunta daga nashi sai shi kuma ya 'ki sakinta. Teemah bata tsoron Yayanta na mafarki da tunaninta danshi be ta6a yi mata tsawa ba shiyasa bata wani jin shakkansa, ko yanzun ma dataga ya'ki sakin hannunta sai tace " ka sake min hannuna yayah ni baruwana da kai, kullum idan naganka baka min magana sai de kayi shiru, inaso ma in baka ha'kuri tun ranar da kayi fushi katafi amma bansan yanda zanyi ba, saboda kullum kinmin magana kakeyi idan naganka" Rausayar da kai tayi gefe sai taci gaba da magana " kuma fah ba laifina bane dana 'ki gaya maka, ni bansan me zance bane alokacin koda nace zan fa'da 'din shiyasa ban 'kiraka ba". Sake juyowa tayi ta kalle shi da sanyin murya tace " ka ha'kura yanzu yayaah? Lumshe idanu kawai yayi ya kuma bu'desu akanta duk tana gani, sai de ita hakan be gamsheta ba sosai tagaji da irin hakan daya keyi ita so take ya bu'di baki yayi mata magana kamar yadda suka saba. Data ga bashi da niyyan yin magana sai tace " sake min hannu na toh, Ummah fa'da zata min in tazo taga banyi wankan ba har yanzu " Idanunta akan hannayen nasu tayi maganar. " me yasa? Haka kawai Abbas yace shima yana kallon hannayen nasu inda idanun Teemah yake. " Baka gani ne? yaufa za'a 'daura auren yah Mahmud wai....wai.... danii. Ta'kara fa'da da jan maganar tare da sunkuyae da idanunta zuwa kasa. Duk da tana zaton wannan ma Yah Abbas 'din mafarkin ta ne amma haka kawai take jin nauyin sanar dashi maganar aurenta kai tsaye. Tun ranar daya tafin nan kusan kullum sai tayi mafarkinsa ha kama tunaninsa yasako ta agaba kuma ko amafarkin ma ba magana yake mata ba, wani lokaci sai de tayi ta masa magana shi ya 'ki bu'dan baki yayi magana wani lokaci kuma sai tace tayi fushi itama sai tayi shiru suta kallon juna amafarkin. Abbas da kansa ya gane cewa har nzu bata yadda shi 'din bane dakansa, domin yadda take yadda take yi masa magana ma ka'dai shaida ne. Ga mamakinta sai taji ya mintsine ta ahannun daya ri'ke 'din hakan kuwa yasa ta ta 'dago da sauri ta kalleshi suka hada idanu, rintse idanun tayi da 'karfi ta kuma bu'dewa a 'ko'karinta naganin ta tashi daga baccin da takeyi 'din, amma ko da ta bu'de 'din ma sai ta sake cin karo da fuskarsa agabanta still yana kallonta, baki ta bu'de da niyar yin magana sai ya ja hannun nata da sauri ya janyo ta zuwa jikinsa, ha'da bayanta da jikinsa yayi sai ya juya ga dressing mirror 'din, sai ya zamana dukkansu suna fuskantar madubin, kwantar da kansa yayi agefen kafa'darta yace _"_ _oyah tell me now"!_ Shiru tayi bata yi masa magana ba illah kallonsa data cigaba da yi sai shine yasake fa'din _" bani ha'kurin yanzu inaji"!_ _Comment_ πŸ–Š _Vote_ *⃣ and _Share_ 🀞🏻 pls _My fellow_ _wattpadians jinjinar_ _bangirma I heart u all._ *Salmern ku ce*😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* A moment of patience in a moment of anger saves a thousand moments of regret. πŸ…Ώ *51* 'Kasa Teemah ta maida idanunta batare data yi niyyan yi masa magana ba dan rawar da jikinta keyi ma ka'dai ya isheta ba sai ta 'kara da wata damuwar ba sanadiyyar ganowa datayi cewa Abbas din zahiriyya ne ba mafarki ba, bugu da 'kari ma ita babu wanda ya ta6a ha'da jikinta dashi tunda take hatta da Abbas da Mahmud ada iya kacinta dasu surutu ne na fatar baki, amma sai taga Yah Abbas 'din yau kamar bashi ba tsoro ta keji sosai dan batasan yau kuma da wacce kalar masifar yazo ba, 'kila yau kan zaneta zaiyi tunda ranar ma bata yi magana bama ya daka mata uban tsawa ballantana yau da tayi masa dogon surutu. Agogon hannunsa ya kalla sai yaga lokaci ya 'danja dan haka sai ya raba jikinsa da nata, hannu yasa a aljihu ya ciro wani 'karamin case ya bu'de hannunta ya sanya mata shi ahannun ya kuma rufewa. Sai ya saketa ya juya da sauri ya nufi 'kofah taku 'daya ana biyu sai ya dakata cak ya tsaya amma be juyo ba yana kallon 'kofan yace " _ina miki fatan alkhairi arayuwar auren ki Fateemah"._ Be sake juyowa ya kalleta ba kawai ya sa kai ya fita daga 'dakin ita kuwa tsaye tayi kawai ta bishi da idanu har ya 6acewa ganin ta, kawarta da ke kwance agadon da tun 'dazu ta ke kallon ikon Allah sai ta taso da saurinta ta iso wurin Fatiman," _Fateema wai meke faruwane waye wannan 'din,? shine mijin naki ,? shi zaki aura ?"_ Ta jero mata tambayoyin 'daya bayan 'daya da buri, samun amsarsu daga bakin Teemah. Yayin da ko kallon kirki bata samu daga Teemahn ba ta dai ka'da mata kai alamar kawai alamar _"a'a"._ Kwafah yarinyar tayi yarinyar sannan ta sake fa'din _"meaning"_!!! Shiru Teemah tayi kamar ma bada ita yarinyar keyi ba. Data ga haka itakuwa sai kamo kafa'dar Teemahn da nufin dawo da attention 'din Fateeman zuwa gareta. Teemah dan haushi sai ta dallah mata harara take takuma juya kanta da nufin _kin_ _dameni_ sai taci gaba da kallon 'kofar da ya fita 'din ji take tamkar zata ganshi yasake dawowa. Yarinyar bata damu ba sai ma wasu tambayoyin data sake bin Teemahn da shi. " toh wanene shi naji yana cewa fatan alkhairi ko minene dai namanta, dan Allah ki fa'da min waye shi ? Tafa'da tare da dawowa ta fuskanci Teemah dan ita harga Allah bata san shi ba bata ta6a ganinsa bama ' kawar Fatima ce da suka ha'du lokacin sunje yin wani programme a (Y C A) Yobe Childrens Academy, bata ma san ina yarinyar tasamu labarin bikin ba shine harta wani zo da sassafe ita adole me 'kawa, dan ita Teemah bata gayyaci kowa ba, 'kawayenta na makarantar su ma duk zuwan kansu ne Teemah 'kin yin gayya tayi wai bata son damuwa, mummy tayi-tayi da ita harta gaji gaskiya ba laifi Teemah akwai taurin kai, akan hakan Mummy takan ce mata " mutum fah rahama ne Teemah ko su ka'dan ne ki daure ki kai musu invitation card 'din ai zasuji da'di" Teemah azuciyarta cewa take " sun da'de basuji da'din bai ndai har se naje na gayya toh su ne" dolen mummy ta ha'kura ta 'kyaleta kawai akan ra'ayinta, dama ita Mummyn so takeyi Teemah tasamu masu 'debe mata kewa amma tunda ta'ki sai mummyn ta kyaleta. Haka duk wacce taji labari inta yi ra'ayi sai tazo wacce kuwa taga bazata iya ba sai tayi zamanta. Kafin Teemah tayi magana sai ga Ummah tashigo bayan ta da wasu mata guda biyu mummy kuma na bayansu hannunta ri'ke da kaya da wata jaka. _" kin yi wankan?"_ Abinda Ummah ta fara tambaya kenan data shigo, Teemah sai ta maida idanunta 'kasa dan bata san me zata ce da Ummahn ba ahalin yanzun bayan duk kashedin da ta mata akan ruwan wankan kafin tabar 'dakin 'dazu. Ganin hakan sai Ummah ta fahimci cewa bata samu tayi wankan ba kenan. Hannunta Ummah takawo danta ganta wata iri ma duk ta canja, mummy dake gefe dasu ne ta sake jefo wata tambayar kamar yanda Ummah tayi. 'Kawar Teemahn ce tace " a'a yanzu dama zatayi" Ran mummy 6aci yayi da jin furucin 'kawar Teemahn abin ya bata haushi sai da akace tayi wankan dawuri amma tsabar iskanci ta'kiyi suka tsaya shirme bayan uban ha'din da aka yiwa ruwan mai shegen tsada dan kawai a ga tafita daban. Mummy cewa tayi " tsayuwar me kukeyi toh anan 'din da har yasa ta'kiyin wankan dawuri"Mummy ranta a6ace tayi maganar dan ba 'karamin 'kuluwa tayi ba. 'Kawar Teemahn ce ta bu'di baki zata fara bayani sai Teemah ta 'dago hannunta da sauri ta sau'ke shi akan na Ummah, dukkan su akan idanunsu hakan ya faru dan Teemahn na tsakiyan su ne, dan haka sai yarinyar ta dakata da maganar da tayi niyyan yi 'din dukkansu suka zuba ido dan ganin ko menene manufar hakan da Teemahn tayi. Ummah 'dago hannunta tayi tana jujjuya abin ahannunta, sai take tambayar Teemahn wai " menene wannan 'din kuma ?. Mummy kuma tace " a ina kika samu? dan tuni kwakwalwarta ta canja daga haushi da masifar da ya turni'keta zuwa tambaya tun lokacin da Teemah ta dan'kawa Ummah abin ahannunta. Teemah a hankali ta basu amsa da fa'din. _" Yah Abbas "_ !! " wani Abbas 'din'? Ummah da Mummy suka ha'da baki wahen fa'din haka. _"Yaayah Abbas "_ Tasake maimata musu. Tsaki Mummy tayi dan zuwa yanzun ba'karamin haushi ne ya'kara kamata ba, haushin rashin cikakken bayani daga bakin Teemah. "Tun yaushe yabaki "?mummy tasake tambayarta. _" yanzu"._ "YANZU kuma!! ? Ummah da mummy suka ha'da baki wajen tambaya da mamaki, kai Teemah ta jinjina musu alamar tabbatar wa. Mummy bakin gado tatafi ta zauna ta dafe goshi tare da fa'din " _na shiga uku_ .!!! Ummah tana bu'de case 'din take fa'din " shi da akace bashi da lokacin zuwa ashe kuma zai taho shine harda 'karyar aiki sun masa yawa"? tana murmushi tayi maganar. Yayinda mummy take tunanin yaushe toh har ya zo gidan batare data sani ba. _" WOW!!", "DIAMOND"_!!! Mummy taji yo muryar Ummah na fa'din haka, sai kawai tayi tagumi, sosai take tausayin 'yartata ita, bata ta6a jin 'kin son Abbas ba ko ka'dan arayuwarta amma wannan karan jitayi dama ace be zo ba dan tasan hankalin Teemah zai zama wani irine bayan tasamu ta nutsu ta daina damuwa wata'kila yanzu kuwa sai yanda Allah yayi duk dama tasan Teemahn tana tafiya damuwar ne batare da tasan damuwar tata ba, amma idan ta fiya ha'duwa da Abbas ba mamaki ta iya gano meke damunta shi yasa take tsoron yawan ha'duwarsu dashi, bata son abubuwa suyi wa Teemahn yawa tun tana 'yan 'kananun shekarunta. Da zata iya data mantar da Teemahn nata kowa da komai dan kawai taga ta zauna ta rungumi auran ta hannu biyu tayi facing reality, wata 'kila in hakan yafaru damuwarta zata kasance 'yar ka'dan inyaso sai ta ci gaba da binta da addu'ah Allah ya ha'de kansu da mijinta da kuma Anty yasa Antyn ta 'kaunaci 'yarta 'kauna mafi girma, amma bata da wannan damar sai de ta ha'da dukka tata ro'ka mata ubangiji ya 'kara sassauta mata kamar yanda ya hanata fahimtar takamman abinda zuciyarta ke ciki, bata san me yasa Abbas yake yiwa Teeman haka ba, bata sani ba ko shi'din yariga yagane Teemahn na son shine!!........kai Allah ya kiyaye sam bata fatan hakan ma ya kasance". Kallon Teemahn tayi taga yadda takoma lokaci guda duk da dama yau 'din bata tashi da walwala sosai ba amma gara yanayinta na 'dazu fiye da na yanzun, Ummah ma da ta lura da ita sai tace " hala yau 'din ma sai da kukayi fa'dan kafin yatafi ko dan naganki duk wata iri haka ?....! Dai dai shigowan su Hannah da suka dawo daga kasuwa yanzun, da sallamar su suka shigo Hannah nashigowa ta tsaya turus tace " ya haka kuma dan Allah? wai har yanzu amarya bata shirya ba Ummah meyasa?...... kai !kai !!kai !!! Ummah nawaye wannan gaskiya ya ha'du ta kar6a tana 'ko'karin gwadasu ahannunta ta saka bangles tacire tana 'ko'karin gwada zoben ne tace "dan Allah Ummah nawaye ne? Cikin zumu'di take maganar as if ance mata nata ne. " na amarya ne Yayanta ya kawo mata"? Ummah na murmushi ta bawa Hannah amsar tambayar ta. Sai Hannah tace "wani Yayan kuma Ummah........ kar dai Yah Abbas?" "Shi dai" inji Ummah atakaice. " kut....lalle ma Yayan nan, toh ni ina nawa ?" " kanta Ummah ta dungure tare da fa'din 'kaniyarki. Hannah ance miki na amarya ne toh ke 'din amaryace "? " Ummah toh ainima zanyi kwalliyar naga" "Ki jirashi toh inkin ganshi kwa gama dramar dashi ni kan ki barni na sha iska......... " Yaushe ma yazone Ummah ba ance bazai samu damar m zuwa ba"? " nima jinayi ance yazo amma banganshi ba",.... kinga 'kyaleni in shirya 'yata lokaci nata tafiya har yanzu bata yi dressing ba" Ummah tayi maganar tare da nufar hanyar bayin dake vikin 'dakin Teemah.........tace " Biba yanzu kam sai kin 'kara ha'da mana wani ruwan ko dan inaga wannan yagana yin sanyi." Da " toh" Biban ta amsa tare da ajiye mayafinta itama ta nufi bayin domin ha'da ruwan wankan. Hannah kuwa gurin Mummy ta nufah da set 'din 'dan kunnan tace. " Mummy kinga Yah Abbas abinda yayi ko....... " tunkan ta 'karasa Mummy tace rabu dashi zai zo har gida yasame ni, sai naji dalilin dayasa ya ware ki be siyo miki naki ba ke ma". Daga mummy ta juya gurin Teemah tana kallon ta tace " maza ki hanzarta ki yi shirin wankan toh gashi za'a ha'da wani ruwan. "Gaskiya kam kiyi dawuri danni har na matsu inga anyi angama shirya amarya naga irin kyan da zakiyi da wannan abubuwan". Hannah tayi magaban tasigar zolaya. ***** Babban limamin masallacin Yobe mosque and islamic centre da ke cikin garin damaturu aka gayyato domin 'daurin auren Teemah, guri yacika ma'kil da jama'ah na nesa dana kusa, su daddy suna daga gaba gaba kusa da Limamin, duk hankalinsu yatafi ga sauraron Hu'dubar da akeyi na 'daurin auren yayin da Mahmud ya sunkuyar da kansa 'kasa sam yakasa jin farin ciki da wannan auren yakasa amincewa zuciyarsa kasantuwar Teemah a'kar'kashin ikon sa,yana ji kamar bazai iya ri'keta ba, jiyake kamar nauyin da zau kannashi yafi 'jarfin sa sosai, kamar ya bu'di baki yace adakata da 'daurin auren a 'daura da waninsa, wanda zai iya ri'ke masa amanar Fatima da hannu biyu amma bazai iya ba,bazai iya furta hakan ba gani yake idan yayi hakan tamkar yayi wa mahaifinsa butulci ne da kuma tozarci musamman idan yayi duba da yanda dubban al'ummah suka bar ayyukan dake gabansu suka taho dan kawai su shaida 'daurin auren sai yaji kawai ya saduda ya barwa Allah kawai, fatan shi de Allah ya zama gatansa yaba shi ikon kulawa da amanar dazata hau kansa, Allah yabashi ikon yin ri'ko da ita da gaskiya. Daddyn Abuja ne da kansa ya kar6i wakilcin Fateema saboda rashin zuwan Abbas 'din. Daf da za'a 'daura auren Mahmud yaji mutun ya zauna daga gefensa na hagu da farko ya share dan sanin yawan mutanen dake zaune agurin wata 'kila saboda yawansu ne yasa dole sai sun ha'da jiki, amma sai yaji zuciyar sa takasa ha'kura da sharewan dayake so yayi 'din 'dagowa yayi ya kalli gefen nasa sai kuwa yaga Abbas zaune akusa dashi yana kallonsa. Take yaji wani sanyi azuciyarsa kasancewar Abbas 'din awurin sai yaji wani sabon 'karfin gwiwa ya shige shi, murmushi yayiwa Abbas 'din tare da bashi hannu shima Abbas sai ya mayar masa da martani daga nan sai suka maida hankalinsu wurin da ake hu'dubar. 11:50am awannan ranar dubban jama'a suka shaida 'daurin auren FATEEMAH ZAHRA KABIR da Angonta..................!!!!!🀞🏻 *Keep following me*πŸ‘ŒπŸ» _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmern ku ce* 😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs _ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _People_ *change* , _love *hurts* , friends *leave* , things *go wrong* but just remember that life still_ *goes* *on* . πŸ…Ώ *52* ..............,Abbas lumshe idanu yayi jiyayi da 'ace shi ka'dai ne awurin da babu abinda zai hana hawayen shi zuba a dai-dai wannan lokacin amma yanzu kam daya kasance acikin mutane, mutanen da bazai ta6a iya sanin yawan su ba sai kawai yace _" Allah_ _kaine gatana, Allah_ _ka ji6anci_ _lamura na"_. 'Daurin auren ba 'karamin al'ummar annabi ya tara ba kama daga kan manyan 'yan kasuwa da manyan 'kusoshin gwamnati da sauran jama'ar musulmai baki 'daya. Mahmud da kansa sai da yaji fa'duwar gaba, zuciyarsa tsinkewa tayi da 'karfin gaske _innalillahi wa innah_ _ilaihirraji'un_ dukkansu suke faman ambata azu'katan su. Abbas ne ya daure ya 'ka'kalo murmushi na dole ya azawa fuskarsa sannan ya ciri hannunsa ya mi'ka wa Mahmud suka yi musabiha " _Inai muku fatan Alkhairi 'dan uwa, Allah ubangiji ya baka ikon yin ri'ko da gaskiya da amana ya sanya fahimtar juna a tsakaninku"_ Shima Mahmud murmushin ya 'ka'kalo yayi wanda ta tsaya masa a iya saman la66ansa ko ka'dan ba wannan bane azuciyarsa amma dan kawai ya nuna wa Abbas 'din yabawa da godiyarsa sai ya 'kir'kiri murshima shima sai yace " _Ameen-Ameen Yayan mu godiya marar iyaka"._ Kasa sake hannun Abbas 'din yayi suka tsaya ahakan, Abbas gefe ya maida idanunsa yana jinjina al'amarin ubangiji acikin ransa, in just a month gashi an raba shi da farin cikinsa, wannan aikin kam sai de a'kira da _'kaddara_ saboda shi koda wasa be ta6a tunanin faruwar hakan ba yariga ya barwa zuciyarsa cewa Teemah tashi ce shi yasa be ta6a damuwa ya kauda irin hakan ba, sai gashi rana tsaka ta inda bai ta6a zata ba, aka datse masa mafarkinsa batare da kai ga idda shi ba, sai gashi Teemah ta barshi, bari kuma na har abada. Tunda suka gama maganganun su kowa sai murmushinsa ya kau. Abbas na so ya cire hannunsa daga cikin na Mahmud amma sai Mahmud ya sakin masa hannun, dole tasa ya dawo da kallonsa ga Mahmud 'din gaba 'daya. Idanun Mahmud na cikin na Abbas 'din yace _" Abbas_ _nagode, nagode_ _sosai da irin 'kokarin 'da kai ta faman yi akaina dan ganin na cika BURIN mahaifina_ , _nasani cewa mai sonka shine wanda akullum yake 'ko'karin ganin baka_ _kauce hanya_ _ba, wannan itake tabbatar da son gaskiya da aminci!, Abbas yau gashi BURIN_ _ABBAH NA yacika, amma ni na kasa jin farin ciki azuciyata, inajin tamkar bazan iya ba, inajin tamkar_ _wani gagarumin nawi ne ya hau kaina, Abbas taya kake ganin zan_ _iya ri'ke wannan babbar amanar bayan ban shirya amsar ta ba?"_ Abbas 'din sai yace mishi _" Daure wa zakayi Mahmud, nasani cewa nauyi ne, nauyi ne ya hau kanka Mahmud sai de ba irin wanda kai kake zato ba, kai dai kawai ka mi'kawa Allah komai nasan zai maka jagora"_ Ahankali ya janye hannunsa daga cikin na Mahmud da ya tsaya shiru kamar me tunani dafa kafa'darsa Abbas yayi sai ya 'dago ya kalli Abbas 'din Abbas sai ya daga girarsa sama batare da yayi magana ba, ya kuma 'dan juya jajayen idanunsa yayi wa Mahmud nuni ga mutanen dake gurin. Atare suka mi'ke tsaye ganin yanda guri ya har'de da jama'ah ana faman gaisuwa yayin da dayawa daga cikin mutanen ma tuni sun kama gabansu zuwa gidajensu da masana'antun su saboda an riga an kammala komai, aure yariga ya 'dauru. Kamar jira ake su mi'ke kuwa sai aka fara mi'ko wa ango gaisuwa da fatan zaman lafiya mai 'dorewa. Yanda Abbas

Chapter 25 of 67