sani ba, isowan mummy sai yayi dai-dai da fitowan Teemah daga d'akin nata arikice sai sukayi karo da mummyn takuwa k'ank'ameta jikinta sai rawa yakeyi takasa cewa komai.
Ko fad'an damuwarta ma ta kasayi illah rintse idanunta da tayi da k'arfin gaske.
mummy duk ta shiga damuwa sai tambayarta take ta faman yi amma ko amsa d'aya bata samu ba daga Teemahn ba..
Abbas na isowa sai ya wuce d'akin nata ya shiga, anan yaga k'adangaren shima anan inda Teemah ta ganshi har yanzu bai motsa ba, sai ya tsaya kallonsa da mamakin ta inda ya shigo d'akin.
Har ya fara rarraba idanunsa a d'akin.
Ai kuwa take ya tuna da ranar dayaga windown ta a6ud'e harya mata magana akan tana rufewa.
Tunowa da yayi da hakan yasa ya d'aga kansa ya kallo 6angaren da windown yake, ga mamakinsa sai kuwa ya gansa a bud'en yauma, hatta net d'in ma ta zuge tabarshi a bud'eko miye fa'idar hakan oho.
Zuwa yayi ya bud'e wurin datake ajiye kayanta da niyar d'auko wani abinda zai kama k'adangaren dashi sai kawai ya d'auko wani farin vest d'inta ya je ya d'au k'adangaren dashi .
Ta windown data bud'e d'in ya jefa k'adangaren tare da vest d'in gaba dokin yasan ya tsaji a aiki , sannan yaja ya rurrufe glass da net d'in sannan ya sake labile.
Koda ya fito su mummy basa inda ya barsun sai kawai ya wuche parlourn mummy, anan yatarar dasu dukkansu Teemah tawani shige jikin mummy kamar me shirin komawa cikinta.
Zama yazo yayi shima agefen su sai mummy tajefo masa tambayar" wai miye ad'akin ne Abbas inata tambayar ta tak'i tabani amsa tun d'azu sai rawar jiki takeyi"
Amsa ta yayi atakaice da fad'in
"K'adangare ne mummy"
Baki mummy ta kama sannan tace ikon Allah nikam garin yaya kuma ya shiga har cikin d'akinta?"
Baiyi magana ba illah d'aga idanunsa dayayi ya kalleta sai yaji ta matuk'ar bashi tausayi, musamman yanda yaga duk tayi laushi, idanunta a lumshe yake hakan yasa ya k'are mata kallon da kyau sai dai daya lura ba kayan kirki bane ajikinta sai ya kauda kansa gefe tare da korar shaid'an azuciyarsa.
Tambayar dayake so yamata ne yasa shi adole badan yaso ba ya sake kallonta ahakan " _Fateemah_ " ya k'ira sunanta asanyaye ta bud'e idanunta batare da ta amsa k'iran daya mata d'inba.
Sanin datayi cewa shine yak'iratan yasa ta sauk'e idanunta akansa.
"Ban ta6a cewa ki rufe windown d'akin kinnan ba? ya tambayeta
K'asa tayi da idanunta dan tasan taurin kantane yasa tak'i rufewa ba komai ba.
"Tambayarki nakeyi fah!
Da kyar ta bud'i baki tace "ehh kafad'a yayah"
" Owk ban isa inyi magana kiji bako "
Yafad'a ad'an harzuk'e.
Jin hakan yasata jijjiga kanta alamar "a'a".
Sai yanzun mummy takar6e maganar da fad'in "ai in juninki taurin kai ne kuwa kina tare da wahala wallahi, ashema dagangan kike barin windown kenan kuma har amiki magana amma bazaki ji ba, yanzu toh wa gari ya waya?!
Ran mummy a6ace yau tketa sababi ta inda take shigaa bata nan take sauk'a ba sai da Abbas ya ga kamar ran mummyn k'ara 6aci yake yi kafin ya fara bata hak'uri musamman daya lura akalar fad'an naso ya canja gaba d'aya.
Dan mummy duk tana masifar ne akan rashin bin maganar Abbas d'in data k'iyi ne bawai dan shigar k'adangaren d'akin ba.
Teemah kuwa tun fara fad'an mummy take zubda ruwan hawaye dan tun d'azun batayi kukan komai ba tun faruwar al'amarin sai yanzu sai hawayen yak'i tsayuwa abin sai ya zame mata biyu.
Sosai jikin Abbas yayi sanyi sai yaji ba dad'i,dan kana ganin hawayen zaka san cewa kukan daga zuciyarta yake fitowa.
Tausayinta yakeji na k'aruwa masa a zuciya sosai da sosai kuma saboda hakanne yasa yayi wa mummyn magana akan tayi hak'uri.
Sai da yaga komai yayi normal ne kafin yace Teemahn tatafi tasa kaya ajikinta aikuwa tak'i taje fir sai ma k'ara shigewa jikin mummy data keyi.
Ganin hakan yasa mummyn cewa "aww bazaki partyn bane ko kin fasa"
Sai kawai ta jijjiga kanta " mekenan?
Mummyn tasake tambayarta dan bata fahimci takamammiyar manufar wannan amsar ba wato jijjiga kai d'in da Teemahn tayi.
Sai Teemahn ta bud'i baki tace "zani ban fasa ba mummy "
murmushi mummyn tayi kafin tace " ai kuwa dai sarkin yawo babu fashi da yake fita unguwa neai, sai Teemahn ta sake 6oye fuskarta a jikin mummyn ita nan wai taji kunya.
"Tashi maza kije ki shirya toh inyaso sai yayankin ya kaiki"
Cewar mummy
Sai da Teemah ta tashi ta zauna kafin ta ce " mummy toh kiraka ni ".
Duk wannan dramar Abbas na zaune yana kallonsu fuskarsa tallafe da hannayensa amma baiyi magana ba.
Mummy ce ta kalleshi wannan karon batare data amsa maganar da Teemah tayi mata ba, sai ta dawo da kallonta ga Abbas tace masa " kayi hak'uri dan Allah ka kaita wai zata je birthday partyn k'awarta ne a _Abbah ibrahim_kuma idan na had'ata da Habibu ba dawowa da wuri zatayi ba kasanta da rashin kunya shiyasa na keso kai ka kaita"
"Ai bakomai mummy taje ta shirya d'in sai tazo kawai mu wuce"
" yauwa d'an albarka ai nasan bazaka k'i ba"
Daga nan ta dawo da kallonta ga Teemah sannan tace "tashi muje toh ki shirya"
Tashi tayi tafar tagiyah sai mummy ta biyo bayanta suka wuce d'akin nata da mummy sai da aka kusan isa d'akin kafin taja ta tsaya mummyn ce ta wuce gaba tare da yin tsaki dan tasan manufar yin hakan domin duk cikin salon tsorone irin na Teemah.
Da d'ari-d'ari ta shirya suka fito daga d'akin, mummy naganin ta sa kaya sai tayi hanyar waje itama sai ta kwaso mayafinta da takalminta tabiyo bayan mummy dagudu sai suka fito atare.
Dariya ne wannan karon yaso kwacewa Abbas ganin yanda Teemah take tafiya tana waiwayen bayanta.
Aparlourn tak'arasa shirinta sannan taje d'akin mummynta ta d'auko kayan make up d'in ta tazo ta yi kwalliyar aparlourn sannan suka fito atare da Abbas d'in bayan sunyi sallama da mummy akan cewa sai sun dawo.
Sosai Teemah tayi kyau acikin shigar datayin sai ta zama tamkar tauraruwa mai haskaka zuciyar............(mamuda)lolz๐
Abbas har satan kallonta yakeyi tsabar yanda yaga tayi shar da ita,sai da suka hau titi taga ya nufi Gashua road sai alokacin tace masa " yayah kawuce fah Abbah ibrahim zamu"
Ko kulata baiyi ba yaci gaba da tuk'insa........
_comment and share_ _pls_
*Salmerhn ku ce* ๐
[10/2, 5:58 PM] Ummiyo: ๐ *CAPTAIN ABBAS* ๐
By
*Salmerh MD*
Luv story๐
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
๐ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
๐ซ
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated_
_2 dukkan masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs.Nagode da_ _irin k'aunar da kuke min da kuma kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai ni da ku mutu ka raba _ ๐
Sister safiyyah Ina tayaki murnar kammala littafinki *(BA JINSUN MU* *BACE*) hak'ik'a wannan littafin ba k'aramar karantar damu yayi ba Allah ubangiji yasaka miki da mafificin Alkhairi ya kuma biyaki....up
up
upโค
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
For those da suke rubuta jamb Allah ubangiji ya baku sa'a yasa daga wannan ba k'ari an wuce kenan.
๐
ฟ *23*
Cikin gari ya wuce da ita shikanshi da farko baisan inda zashiba,sai da yaga ya shigo cikin garin kafin ya yanke shawarar zuwa bayan tasha.
Koda suka isa bayan tashan
guri ya samu yayi parking sannan ya bata umarnin fitowa daga motar.
Kamar bazata fitoba sai kuma taga ya k'ureta da kallo fuskarsa ba alamun walwala sai kawai ta bud'e motar ta fita bakinta kamar zai fad'i k'asa tsabar yanda ta turo shi gaba, dan ita bata san mai yake nufi da hakan ba, inda akace ya kaita daban inda kuma ya kawo ta daban, haushi ne ya sake cikata data tuno irin rok'on data tayi kafin mummy tabarta zuwa birthday party d'in sai gashi kuma wannan mutumin yakama ya yi wani guri da ita.
Tafiya kad'an suka yi sai taga ya shiga cikin wani babban shagon kayan make-up.
Dakansa ya dinga nuna abinda za'a mik'o musu While Teemah na zaune a gefe ko kallo bai isheta ba dan ita gaba d'aya zuciyar ta tatafi ne ga tuanain zai 6ata mata lokaci dan bata son ta makara zuwa birthday d'in da'ake yi na k'awartan hartana zooming d'in yanda k'awayenta zasu fara cashewa ba ita, tasan da tana da waya da yau d'innan k'ira sai ya isheta.
Haka yayi sayayyansa kaca-kaca sannan ya jagorancesu suka fito daga shagon suka kuma shiga mota.
Atunanin Teemah daga nan gurin partyn zasu wuce dan harta fara murna amma sai taga ya d'auki wani hanya daban haka yaita zaga cikin gari kamar me neman wani abu daga k'arshe sai ya nufi hanyar gida.
Teemah tayi ta masa magana yafi sau a k'irga amma ko kallon 6angaren da take ma baiyi ba ballantana ya kulata balle har tasamu amsar maganar da ta masa.
Sai da taga ya d'auki hanyar gidan kafin tasake masa magana akan batun birthday party d'in, duk da bata da tabbacin zai amsata amma sai da tayi dan tasan ko bai bata amsa ba ai dai ya ji ta.
Ga mamakinta kuwa sai taji yanzun ya bata takaitacciyar amsa da " bazaki ba" ya bata amsan ne batare da ko kallon kirki ba.
Ai tanajin haka sai ta fara bori da kuka dan harga ba k'aramin haushin fita da shi d'in nan tayi yau ba, data sani dama adaidaitan ta hau..........
data sani dama Habibu driver ne ya kaita.......
Data sani tayi shi yafi sau ak'irga.
Shikuwa koda yaga tana kukan sai bai kulata ba illah juya kan motar da yayi ya shiga u-turn ya dawo da baya,murna tafara daganin hakan atunaninta zai kai tan ne, dan daman wucewarsu unguwar su Leemah (birthday girl) kenan dataga bayada niyyar shiga shine tamasa magana dajin amasr daya bata kuwa sai tafara wannan iskancin kukan.
Ganin yasake wucewa sai kawai ta yi tagumi dan zuwa yanzun tagama sawa ranta tayi missing birthday d'in kenan har ma tanaji aranta cewar ya wuceta already.
Hanyar Jerusalem ward ya d'auka dake gefen nursing school, sai kuma tafara tunanin toh me suka zo yi anan kuma?
Kar dai wata yarinyar kuma ya kwaso acikin unguwar nan kuma?
Kauda kai tayi gefe tare da jan tsaki aranta ta kuma fad'in mutun sai kwashe-kwashen tsiya har arn......ma bai bari ba.
YETIM care foundation (gidan marayu) taga yayi parking awurin ya fito sai da tayi kalle-kalle kafin ita ma tafito tabiyo bayansa suka shiga ciki.
Sun tarar ma ana wani programme sai basu wani dad'e ba suka fito bayan ya gaiggaisa da mutanen wurin akan sai gobe insha Allahu zai dawo.
Mota suka koma yaja ya nufi hanyar gida.
Yanzun kam da suka fito bata wani tsaya mamaki ba bud'e bakinta tayi ta tambayeshi muryarta wasai tace" yayah yaushe kasan nan wurin?
Sai da ya kalleta kafin yace "Mahmud ne ya kawo ni nima kwanaki"
"Sai ta sake cewa " toh shi yah Mahmud d'in wa ya nuna masa ai naga shima bai san nan garin ba akace"?
"Toh sai ki jira idan yazo ki masa wannan tambayar?
Yayi maganan ne fuskarsa ba yabo ba fallasa sai ta d'an ji dad'in hakan hartaji tasamu k'arfin gwiwar sake yi masa magana, aikuwa ta kuma cewa" yayah toh ni mai yasa kak'i ka kaini inda mummy tace ka kaini d'in?"
" Banyi ra'ayi bane"
ya bata amsa a takaice.
Tura b aki tayi gaba sannan tace " amma yayah k'awata ce fah ita seat mate d'ina kuma"
" Kice mata ni na hana ki zuwa"
Ya bata amsa lokacin dayake k'ok'arin tada mota.
" Dan Allah ni...........
Zata sake yin magana ya dakatar da ita da fad'in
" ya isheni please kimin shiru"
Dan dolenta tayi shiru bawai dan ta gama fad'ar abinda ke ranta ba.
Suna zuwa gida kuwa tafice daga motar da gudu tayi ciki.
Kamar anjeho ta ta fad'awa mummy ajiki tana k'ananun kuka kamar wata yarinya k'arama.
Mummyn ce tace wai nikam ke kullum bakya ganin kin k'ara girma ne Teemah?
Cikin shesh-sheka dajan magana tace..." mummy k'in kaini fah yayi ya dinga yawo dani acikin gari kamar nace masa inaso"
"dai-dai kenan maganin irinku kenan ai"
Mummyn tafad'a tare da murmushi kwance akan fuskarta.
" mummy ke kullum-kullum bazaki bi bayana ba sai shi ko?, Allah in Daddy ya dawo sai na fad'a masa nima "
tana gama fad'in hakan ta tashi tayi d'akinta da sauri amma sai dai me........ tana zuwa harta shiga tafara zuge zif d'in rigarta ai sai ta tuna da k'adangaren d'azun sai kuwa tafito da gudunta ta dawo parlourn dai-dai Abbas ma ya shigo sai ya ganta aguje
"ke lafiyarki kuwa?"
ya jefa mata tambaya da mamakin irin yanda ya gantan kamar an koro ta.
Bata kulashi ba har sai da taga kanta zaune akusa da mummyn ta kafin ta d'anji dama-dama.
Abbas d'inma k'ara sowa yayi ya zauna akan kujera yana ta kallonta so yakr yaji me yakuma korota, yarinya kamar mai ta6in hankali.
Mummyn nata ne tasake tambayarta the same abinda Abbas d'in ya tambaya, sai a sannan tace " mummy k'adangare a d'akin fa kin manta?"
"Hmm"kawai Abbas yace kuma sai a sannan ya ajiye ledojin dake rik'e a hannunsa.
Mummy kuwa masifa tafara yimata inda tace
" banason hauka ni kinga Teemah, kadangaren da aka fitar tun d'azun shine kike wannan uban gudun akansa?"
"Waye ya fitar dashi toh?
Teemah ta sake tambayar mummyn.
Mummyn ma amsa ta sake bata da fad'in " yayanki mana"
Sai ta zaro idonta waje tare da fad'in " yah mahmud ya dawo ne dama"?.
Dank'walinta mummy tayi dan tasan dagangan tayi tambayar sannan tace "bafa nason iskanci ya dawo d'in ne kuma bazaki ganshi ba, koshi kad'ai ne akace yayanki?"
'Kasa tayi da kanta sai ta jiyo muryar Abbas yana fad'in " zo ki kwashe kayan nan anan" yafad'i tare da nuna mata ledojin daya shigo dasu d'azu a hannunsa.
Dayake atsare yayi maganar sai bata wani yi iyayi ba taje ta tsugunna ta kwashe ledojin ta mik'e tsaye sannan ta kalli inda yake d'in sai suka had'a idanu, sai da ta kauda kanta kafin tace "ina zan kai kayan"
Kallonta ya tsaya yi aransa yana mamakin yanda yarinyar nan ta gama raina shi gaba d'aya ya kuma rasa dalili.
Dayake baiyi magana ba sai tayi zaton ko baiji tambayar data masan bane sai ta sake maimaitawa a karo nabiyu.
Baiyi niyar bata amsa ba dan gani yake kamar iskanci ne ke damunta baya ga haka ai tasan dai ita yayiwa siyayyar tunda da ita suka je, darajar mummy dake gurin a zaune ne yasa shi bata amsa da " naki ne "
(nikuwa nace oga Abbas d'in mar-yerm sai a hankali, in ba haka waya san meke cikin zuciyarka da har kake tunanin Teemah tasan cewa siyayyan ta ne kayi).๐
Tana jin haka sai ta fara tafiya batare da ta kuma cewa k'ala ba.
Haushi mummy taji da wautar Teemahn sai kawai ta k'irata amsaw tayi kafin ta dawo da baya " baki da hankali ne Teemah?,bazaki iya bud'an bakinki kiyi godiya ba bayan mutun ya miki kyauta, bakinki ciwo yake yine? ko kuma iskanci da rashin hankalin kinne yayi k'wari"
" Kiyi hak'uri mummy daman inada niyyar yi "
Teeman tafad'a da kwa6a66an fuska
mummy kuwa tsaki kawai taja ta kauda kanta gefe dan halin Teemah gaba d'aya yafara isanta.
Ita kuwa sai ta juya ta kallo inda yake kamar baya wurin kansa na k'asa fuskarsa na kallon wayarsa dake rik'e a hannunsa sai tace " nagode yayah"
Ko ya nuna yasan ma da shi take bai nuna ba balle tasa ran yajita, sai ta k'ara maimaitawa ai kuwa sai taga ya d'aga waya yasa a kunnensa yafara magana cikin natsuwa kamar bashiba, jitayi ya matuk'ar birgeta ashe daman yana magana haka anatse, tsabar yanda ta tsaya kallonsa har abinda ke rik'e da hannun damanta ya fara zamewa, taroshi tayi da wuri ta daidaita rik'on ledan sannan ta d'an juyo ta kalli mummy da k'asan ido gani tayi mummyn na hararar ta.
Sai kawai tace " mummy kinga yak'i ya kulani ko "
"Toh tsoronki yake jine Teemah da godiya ma sai an saki kafin kimasa"
sai Teemahn tace " "toh ai shine mummy"
"Shine me?
Mummyn ta sake tambayarta.
Amma kafin Teemahn tasake magana sai mummyn ta kuma cewa " jeki ajiye kayan sai ki dawo kima sa godiyan kafin nan yagama wayar ma ".
Tanajin haka sai ta juya da farin ciki a zuciyarta har tana ayyana babu wanda zai sake ganin ta ma ayau kam, dan batayi niyyar yiwa mutun godiya ba ita kam tunda bata rok'i kaya agun mutun ba.
Amma sai dai me.........tana fara tafiya sai ta tuno da abinda ke d'akinta.
Sai ta fasa shiga kawai ta nufi hanyar d'akin mummy
" Karki kuskura kishigan min d'aki "
Muryar mummy tajiyo tana fad'in haka.
Kwafa tayi sannan ta karkata kanta gefe " ayyah mummy toh ina zan kai"?
" Baki da d'aki ne ke"?cewar mummyn. Teemah ma sai tasake fad'in
" mummy toh kizo ki rakani d'akin nawa "
" karkije inhar saina rakaki"
Dajin hakan tasan mummy ba rakata zatayi ba tunda tafad'i haka sai kawai ta nufi d'akin nata tsoro fal ranta.
Koda taje bakin d'akin ahankali ta tura k'ofar sai ta mimmik'a kayan hannun nata da sauri sannan ta kuma jan k'ofar ta rufe sai ta wuce kitchen tafita ta k'ofar baya tayi zamanta awaje.
Tana zaune awurin tanata sake-saken missing birthday da tayi kusan 15mins can sai ta ga Abbas ya fita amma ganin yana d'an sauri sai ta gane cewa masallaci zashi.
" Mthceeeeew" taja dogon tsaki tare da banka masa harara dan a duk sanda ta kalli Abbas d'in sake tunowa take da batun birthday d'in daya hanata zuwa "mugu kawai " ta k'ara fad'i afili..
(Ni kuwa nace kanki akeji y'an mata).๐
Bata tashi awurin ba sai da taga gari yad'an fara duhu kafin ta tashi ta zagaya ta shiga ta k'ofar parlour.
D'an zaman da tayi awajen sai ta manta da batun tsoron k'adangaren, dan haka tana shigowa sai ta wuce d'akinta saboda tana sauri taga tayi sallahr maghrib dan lokacin yad'an shige kad'an.
Hartayo alwala tazo tahau sallaya bata tuna ba tana cikin yin ik'ama kafin ta tuno da batun sai kawai ta daure tayi ta a'uzubillah sannn tacigaba da sallahn.
Da ikon Allah kuwa harta idar tsoron bai zo mata ba, sai data idar kafin ta juya ta kakakkali cikin d'akin sai taga babu komai, tunowa tayi da maganar yah Abbas akan window, nan ma sai taje ga windown amma sai ta ganshi arufe dad'i taji har aranta sai taji Abbas d'in ya matuk'ar birgeta.
_Comment and share_ _pls_ ๐ค๐ป
*Salmerhn ku ce* ๐
[10/2, 5:58 PM] Ummiyo: ๐ *CAPTAIN ABBAS* ๐
By
*Salmerh MD*
Luv story๐
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
๐ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
๐ซ
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
๐
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Donโt engage small-minded, petty people unless youโre able to help them. What you say & do will never be good enough for them. Theyโll make your life difficult. Focus on controlling our own actions. We canโt allow ourselves to get sucked into their madness or weโll end up hurt!
๐
ฟ *24*
Dan tasan bazai ta6a barmata k'adangaren a cikin d'akinta ba, tunda har mummy tace ya cire toh ya cire d'in ne.
Dawowa tayi cikin d'akin sai caraf idonta ya sauk'a akan kayan ledan data ajiye d'azu.
Da saurinta taje ta d'auko kayan ta zauna a bakin gadonta ta cicciro su tafara dubawa.
Teemah kam dama badai son kayan make-up ba, d'azun ma da haushin k'in kaita partyn da baiyi bane yasa ta nuna halin ko inkula da kayan kamar irin bata so d'innan ne.
Zazzage su tayi gaba d'aya sai farin ciki ya cika mata zu, dan ganin man da take amfani dashi acikin kayan datayi set d'insa kuma gaba d'aya, ga wani had'ad'd'en tarkacen powder daya tafi da imaninta harda hair removal cream(shavingcream) dasu turare da sauran abubuwan amfani.
Sosai wannan siyayyan ya birgeta, domin a kayan make-up d'in daya dace amatsayinta na 'yan mata tana amfani dashi abubuwa kad'an ne basu zo a siyayyan ba.
Haka tayi ta murna da farin ciki har taso ma ta manta haushin Abbas d'in da ta keji aranta.
Agun kayan ta shantake har aka k'ira isha'i, sai da taji ank'ira isha'i d'in kafin ta fara tattare kayan gaba d'aya.
Kan mirrorn ta taje ta jajjera su sauran kuma da bana kan mirror ba takaisu bayi ta ajiye su suma, haka ta rink'a jin kanta wata so special irin an girma d'innan.
Sai data sallaci sallar isha'i kafin ta fito ad'akin ta koma, parlour tunkan ta zauna ta d'auki remote a hannunta ta fara canja tasha sai da ta samo inda yamata kafin ta zauna ta cigaba da kallo abinta.
Anan mummy tazo ta sameta itama ta zauna suka ci gaba da kallon tare ko kuma nace surutu dan Teemah tun zaman mummy agurin data mata sannu da fitowa shikenan ta hau bata labarin kayan da Yah Abbas ya siya mata sai yaba kayan take tana k'arawa daga kaji yanda take yi d'in zaka san cewa kayan sun matuk'ar birgeta, mummy data gaji da sauraran surutun ne sai tace mata " amma d'azu da kike yangan d'aukan kayan fah?"
Amsa tabawa mummyn da fad'in ai haushi yabani ne d'azun shiyasa"
Ta6e baki kawai mummy tayi tare da fad'in "hmm" ciki-ciki dan bata buk'atan wani bayani akan batun Teemahn saboda tariga da tasan manufar haushin.
Sun kusan ak'alla 40mins zaune awurin kafin Teemah ta karkata kai tace " nifah yunwa nake ji mummy"
"Je k'ira yayanki toh tun d'azu banji motsinsa bama!"mummyn tafad'i tana me daidai ta zamanta akan kujera.
Kuka kawai Teemah ta sanya wa mummyn nata, abin sai ya bawa mummyn mamaki sai kace ba ita keta zuba surutu anan kamar wata parrot ba.
Baki mummyn takama dan abin na Teemah ya fara d'aure mata kai sosai.
Sai bata takura ta ba kawai ta tashi ta koma d'akin ta ta d'auko wayarta ta dawo wajen dinning d'in tazauna sannan tayi dialling numbern sa.
Shikuwa yana can kwance shikansa bai san takamamman me ke damunsa ba har zuciyarsa, sai dai wani lokaci yakanji aduk sanda ya tuno da tafiyarsa (komawarsa wajen aiki) jiyake kamar zaiyi wani abu ne wanda ilahirin gangar jikinsa da zuciyarsa basu son hakan.Amma tunaninsa yagagara tantance masa menene matsalar ko kuma meke damunsa.
Yau d'in ma hakane yana kwance ne shiru yana tunani amma idan da tsare shi za'ayi ace tunanin me yake yi da shikanshi bazai ce ga abinda ke sashi tunanin ba.
Ringing d'in wayarsa ne ya dawo dashi cikin natsuwarsa, dayake wayar na d'an gaba dashi kad'an so baya ganin sunan me k'iran hakan yasa koda yabar tunanin bai wani motsa ba illah ido daya tsurawa wayar kawai batare da yayi yunk'urin d'auka ba.
Haka har k'iran ya yanke wani yasake shigowa amma still bai motsa ba.
K'iran na gab da yankewa ne sannan ya mik'a hannu ya d'auko wayar, ganin sunan da ke kai ne yasa shi mik'ewa zaune da sauri sai dai yana shirin d'auka sai wayar ta kuma yankewa atake yabi bayan k'iran amma cikin rashin sa'a sai yaji ance masa ai katinsa yak'are kaf gashi kuma bata sake k'ira ba, sai kawai ya yanke shawaran zuwa can ya sameta duk dama yasan batun bazai wuce na abinci ba, amma yasan tunda har ta masa 2missed call bai d'auka ba zata iya tunanin ko ba lafiya bane shiyasa ya yanke shawara zuwa d'in.
Tashi yayi ya shiga bayi tukunna amma kuma koda yashiga sai ya manta da batun k'iran da mummyn ke masa, ya d'an 6ata lokaci kad'an abayi, daya fito kuma sai yayi tunanin kawai gara yayi recharging through VTU awayar tasa inyaso sai ya k'irata kawai.
Teemah kuwa wani rigimar ta saka da mummy ta ajiye wayar bayan k'iran nasan datayi, sai ta ce Teemahn ta je ta dubo shi tunda gashi ta k'ira bai d'auka ba.
Toh rigiman da Teemahn ta sanya ne yasa mummyn bata wani takurata akan sai taje dubo shin ba sai ta tsaya kallon Teemahn kawai dake ta bubbuga k'afafu tana fad'in "nikam bazani ba, Allah mummy idan naje mugunta yake min kullum idan naje"
Kuka takeyi da hawaye take fad'in hakan, da mummy taga haka sai cikin hikima ta tambayeta asalin dalilin da yasa bata son zuwa aikan domin kar arashin sani ta cigaba da tura y'arta inda bai dace da rayuwar ta ba.
(wannan haka yakamata iyaye mata su ringa yi domin haka na yawan faruwa azahiri ma, sai kaga yarinya/yaro wani lokaci yakanso yafad'i wa iyayensa damuwarsa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 67