Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba illah cigaba datayi da lalla6ata harta hak'ura. mummy kuwa kauda kai tayi sannan tace "rashin aiki dai" "Ai in kika biye ta wannan zaki sha fama" mummyn tafad'a tana mai nuna Teemahr da baki. Murmushi sukayi ummah da Teemah dajin abinda mummy tace, mummyn kuwa ta ta6e baki. Tashi tayi daga kan cinyar ummahn ta zauna sannan tasa hannu ta d'auki d'aya daga cikin abin ta6awan da aka ajiye wa ummahn. "Ummah bari na watsa ruwa in dawo" Da toh ummahn ta amsa mata,ita kuwa tuni ma takusa barin parlourn. Sai da ta cire kaf d'in kayan uniform d'in dake jikinta sannan tafara k'ok'arin neman abinda zata d'aura ajikin nata amma bata samu ba, tana daga tsayen tafara kwalla k'iran Baabah lami mai aikin gidansu na yanzu,bakinta biyu kafin tayi na ukun baabah lami ta amsa mata tare da tahowa d'akin,bata tuna ba kaya ajikin ta ba harse da taji motsin tafiyar Baabah Lami d'in kusa da d'akinta kafin ta tuna,hijab d'in makarantarta ta d'auka tasaka akanta ko gwiwa ma bai rufe mata ba,amma dai yafi babu. Da sallama Baabah Lami ta shigo d'akin Tun kan ma ta gama shigowa Teemah ta jefa mata tambayar "Baabah Lami banga Towel d'ina ko d'aya ba."? "Aw suna baya bakince a wanke miki su ba". "Owk toh anwanke d'in ne ? "Ehh anwanke" Baabah Lami d'in ta amsa mata dashi. Sannan ta k'ara da fad'in barin je inkawo miki.Daga nan tajuya tafita daga d'akin. Dayake fanni tajima dayin aure hakan yasa tabar aiki agidan nasu sai aka samo musu wannan Baabah Lami d'in. Baahbah Lami bawata babba bace don bazata wuce 27/28yrs ba amma dayake bazawara ce,yaranta hud'u kuma sune suke k'iranta da wannan sunan wato Baabah Lami hakan yasa sunan yabita kowa ma haka yake k'iranta da shi yanzu. Koda Baahbah Lami ta kawo towel d'in azaune tasame ta abakin gado tana kallon fuskarta acikin d'an madaidaicin mirrorn dake rik'e a hannunta.Daganin Baaba Lami d'in kuwa ta tashi ta kar6i kayan ta,tsayuwa tayi har sai da taga baabah Lami tafita taja mata k'ofar kafin ta cire hijab d'in kanta ta d'auki towel d'aya ta d'aura ajikinta, sauran kuma ta ajiye su a inda tasaba ajiyewa sannan ta d'auki wani fari k'arami daga ciki ta rik'e ahannunta kafin nan tashiga bayin. Ta 6ata ak'alla kusan 40mins a wanka da yin shirinta kad'ai. Tana fitowa kuwa wajensu daddy tafara zuwa ganin basanan sai ta nufi wajen su mummy,tana shiga da sallamarta tafara tambayar mummy "ina su daddy suka je kuma,? harararta mummy tayi, da me zaki musu? Mummyn ta tambayeta. sai ummah ce ta bawa Teemahn amsa da fad'in "sun tafi masallaci ne zasu sallaci jumma'ah" "Ohh na manta ne ummah ashe fah yau Friday" Daya taga reaction d'in mummy data shigo,mummy da harara tabita kuma tasan ma'anar hararan haka yasa yanzun bata zauna ba ta kuma ficewa daga d'akin,don tasan in bata fitan ba mai zai biyo baya anjima ko gobe,kunnan ta ne zasuji ajikinsu. Mummy bata son wai taringa zama a inda ta ke matuk'ar tana tare da bak'i.Dan yana rushe tsarin tarbiyar yaro.Itama dayake tasan abinta sai kawai tafice can bayan gidan tayi zamanta a inda taga yafi mata da'din zama. Da lokacin sallah yayi ne ta koma ciki dan ta yi sallahr itama. Bayan su daddy sun dawo ne aka had'u agun cin abinci,kowa yana ci amma banda teemah da bai fi spoon biyu taci ba kawai,Daddyn abuja ne ya hankalta da ita hakan yasa ya tambayeta ko bata jin dad'in abincin ne? Murmushi tayi masa batare datayi masa magana ba. Daddynta ne ya bawa daddyn abuja amsa da fad'in "da de kayan itatuwa ne da ba sai ka 6ata bakinka wurin sata ciba ,amma abinci kam ni har na gaji da yi mata magana akai ma" Da kyar ta dage tad'an ci abincin dan yadda taga daddyn abuja yadamu da rashin cin abincin nata, bai san cewa wannan d'in ma daure wa tayi tafara ci ba dan ganin suna nan,amma in su kad'ai ne ita da iyayenta ma ko kula dining d'in batayi musamman in abincin rana neh,su har sun riga da sun saba da wannan halayyar tata. Kwanan su Daddyn Abuja d'aya washegari suka koma Abuja,dayake daman wani abu ne yakawo su garin,shine har suka kwana. Teemah jitayi kamar ta bisu da zasu tafin don ita akwai son mutane sosai. Baifi wata biyu da tafiyarsu ba Daddynta ya shirya wai zasu je passing out d'in Abbas a katsina shida su daddyn Abuja,Allah ya kiyaye kawai Teemah tayi mar tare da fad'in ya gaida mata da su ummah da daddy. Har gun mota suka rakashi "shiga yayi bayan ya amsata driver yaja suka tafi airport. Haka suka je lapiya qalau cikin ikon Allah.acan suka had'u da su daddyn Abujan har sun rigashi isa ma. Abbas yayi murna da zuwan Iyayen nasa,inda suka gama abinda yakawo su cikin sa'a har zasu tafi ma sai kuma Daddn yace su jira Abbas d'in kawai inyaso su taho tare tunda shima washe gari zai tafi. Kud'i sosai su daddy suka kashe kafin Abbas yasamu wannan matsayin,don da farko har daddyn Abuja ma yace wai sai dai Abbas d'in ya hak'ura ya bari ya nemi wani aikin,amma daddyn Teemah yace sam baza'ayi haka ba, don sanin daya yiwa Abbas tun yana k'arami burinsa kenan,Burinsa yazama sojan Nigeria,dan haka ya dage sai da yaga burin Abbas ya cika,don acewarsa rashin bada muhimmanci akan al'amarin yara yana matuk'ar affecting d'in cigaban yaran.don haka ya tsaya tsayin daka ya shiga ya fita har sai da yaga burin abbas d'in ya cika kafin ya samu salama.Dayake daddy yana da manya kuma yabi masa ta sama ne,kuma short service yaje, shima Abbas d'in ya shak'i karatu sosai shiyasa cikin sa'a yafito da babban matsayi, amma kafinnan fa aljihun daddy sai da yayi kuka. A can katsinan aka barshi ba aka kaishi ko'ina ba amma kafinnan sai yayi hutu tukunna zai koma gaba d'aya..... *Salmerh* ๐Ÿ˜ share pls๐Ÿ‘Œ๐Ÿป [10/2, 5:50 PM] Ummiyo: ๐Ÿ’• *CAPTAIN ABBAS* ๐Ÿ’• By *Salmerh md* Luv story๐Ÿ˜ *Wattpad @* *Serlmerh-md* ๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* ๐Ÿ’ซ We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Dedicated 2 _my family_ ๐Ÿ˜ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Why do we often feel like we can speak with authority on someoneโ€™s life? How can we when weโ€™ve not experienced what the other person has; weโ€™ve not walked in their shoes. We have the tendency to stereotype people and think like we know it all. *The* *truth is we donโ€™t!* ๐Ÿ…ฟ *6* Da zasu dawo su baro katsinan Abbas bai bi su ummahn sa zuwa Abuja ba sai yabiyo daddyn Teemah suka taho tare. Yanda yatarar da gidan ya matuk'ar birgesa,musamman yanda aka canja tsarin gida ya koma na zamani,hakan ya k'ayatar dashi.Aransa yakejin ai hakan yafi da ace ana ta canje canjen muhalli ana bin zamani ai gara ka renovating wanda kake dashi in hakan zai yiwu. Sosai yaji daddyn ya burgesa da irin yadda ya maida gidan "so take away๐Ÿ˜˜ Bakamar daddynsa da kullum cikin canja muhalli suke ba. Lokacin da suka dawo Teemah na school,bayan ta dawo ne ta tarar da daddyn ta ya dawo,murnar kamar tacinye sa d'anye.Inka ganta sanda ta ke murnar zaka zaci tafiyar shekara guda yayi,nan kuwa kwanansa uku kacal da barin gidan.Sai data gama murnar sannan daddy yace toh taje ta gaida yayanta,shima yazo yana d'akinsa,Zaro ido tayi waje sannan tace "daddy wani yayannawa?" "Abbas neh angel ,Abbas na Abuja." Daddy ya bata amsar tambayar data yi. "Owk" Tacewa daddyn Sannan ta k'ara da "amma daddy barinje incire uniform d'innan tukunna" Tafad'a tana kallon fuskar daddyn nata. "Uhm,jeki cire abinki" Daddyn ya bata amsa da haka. Tashi tayi ta sannu ta d'auki school bag d'inta,harta fara tafiya sai kuma tace ''daddy ina mummy fah" "sai yanzu kika ga daman tambayar inda nake ko? "Wato dan kinga daddynki ko? Muryar mummy tajiyo tana fad'in hakan,yayinda daddy yafara dariya k'asa 'kasa. Waigowa Teemah tayi nan ta hango mummyn awajen dinning tana k'ok'arin daukan abu. Karakata kai tayi gefe . Mummyn ko kulata ma batayi ba,data d'auki abinda zata d'auka ficewarta tayi tabarta a inda ta ke tsaye. Daddy ma kauda kai yayi kamar bai san meke faruwa ba. Ganin haka yasa ta fice kawai daga parlourn, d'akin ta ta nufa,kamar yanda tasaba sai da tacire uniform d'in kaf,kafin nan tanemi towel ta d'aura ajikinta. Toilet tashiga ta watso ruwa tare da d'auro alwala,Shiryawa tayi cikin wata gown na material marar nauyi,d'inkin ya mata kyau yayi cifcif dajikinta wani k'ara min gyale ta d'auko wanda bai ma fi ak'ira shi da d'ankwali ba,ta yafa akanta. Parlourn ta koma ,dan ita kwata-kwata tama manta da batun wani yayah,amma haka sai tana jin ranta wani iri sai taji bata da nutsuwa. Daddy tasamu still azaune yana kallon news d'in rana,aranta tace "daddy da news badama." Shiganta keda wuya tun ma kafin ta zauna kamar had'in baki sai ga mummy ta 6ullo ta itama har tayi wanka tacanja sutura. muryar Mummyn tajiyo tana fad'in "yauwa Teemah yiwa yayanki magana kinji,lunch is ready". Dum taji zuciyarta ta amsa,bata san dalili ba,amma tafi kyautata zaton k'ila dan ta jima bata had'u dashi bane shiyasa. Dayake daman bata kaiga zama ba,sai kawai tajuya ahankali ta fara tafiya dan zuwa aiken mummyn. "Ni kinma je kin gaidashi kuwa?" Tasake jin muryar mummyn tafad'I. Kai ta jijjigawa mummyn batare data waigo ba dan duk jitayi jikinta yasaki. "baki san yazo bane? Mummyn tasake tambayarta. Ynzun kam saida ta waigo kafin tace "nasani mummy,d'azu daddy ya fad'amin,daman inada niyyar zuwa" Kai alanga6e tayi maganar kamar zatayi kuka. "Hmm" kawai mummyn tace,daganan bat qara kallon inda Teemahn ta ke ba. Daddy kam k'ala bai ce musu ba. Juyawa tayi taci gana da tafiya,koda taje k'ofar d'akin nasa ma jitayi kamar karta shiga,amma data tuna cewa mummy ce ta aiketa aikawai sai tayi shahada ta tura k'ofar ahankali tashiga sannan ta maida k'ofar ta rufe,gani tayi d'akin duhu bak'i k'irin ba haske,neman inda switch yake tayi ta danna,amma still ba haske. Hakan ya tabbatar mata da cewa bulb d'inne suka lalace,kuma dayake ba'a cika amfani da d'akin ba shiyasa babu wanda yabi takansu,ballantana a canza su. Ahankali ta k'ara cikin tsakiyar d'akin jitayi shiru ba alamar motsi,sai de uban k'anshin turaren da yau ne farkon fara jinta dashi,da kyar ta tattara la66anta ta harhad'a sunansa. "Yah....yah Abbas"! Shiru taji "Yah Abbas"!! Ta sa ke maimaitawa amma still no answer.Juyawa tayi tafita daga d'akin,taje tasanar da mummy akan bayanan Yah Abbas d'in. "Babu inda Abbas yaje Teemah,k'ila ko zuwa bakiyi ba" Cewar mummy Teemahn ne ta kar6e da fad'in..... "Allah naje mummy,kuma fah d'akin duhu ba haske". D'auki wayata ki haska,maza kije ki dubo minshi, inaga ma bacci yake saboda gajiya" Tana d'aukan wayar tace "mummy harfa k'ira nayi amma babu wanda ya kulani" "Shine ai nace ki duboshi in bacci yake karki tasheshi,ki dawo kawai"k'ila ma dakika ga duhun k'in shiga kika yi ko? Kwa6a fuska tayi "Nashiga mana mummy " "Naji toh ni sauri ki dawo" Mummyn tafad'a sannan takawar da kanta gefe. Fita Teemah tayi ta nufi d'akin Abbas d'in,data isa bakin k'ofa zai ta tsaya ta kunna hasken wayar kafin ta tura k'ofa tashiga. Ko sallama batayi ba don ita azatonta babu kowa ad'akin kamar yanda ta tarar dashi d'azu. Saida ta maida k'ofar ta rufe kafin ta d'aga hasken hannunta haska,Hasken ya gama haska ilahirin d'akin ,don wayar mummyn badai haske ba. Mutum ta hango a tsaye dogo mai d'an hasken fata,k'ugunsa d'aure da towel,wuyansa ma wani towel d'inne rataye kuma duka farare,hannunsa d'aya riqe da man shafawan daya d'auko da niyar shafawa, jin an6ud'e masa k'ofah batare da neman izini bane yasa ya tsaya,dan yaga wani gwani ne wannan. Ko tsoro bataji ba tasake daidaita hasken asaitinsa a k'ok'arinta naganin wannan mutumin da akace wai shine yayanta. Hannunsa d'ayan ya d'aga ya kare hasken dashi,dan ta saita masa ne afuska,sannan ya mik'a d'ayan hannun ya ajiye man shafar. Kallon mai haskashin yake da mamaki,so yake yaga waye wannan d'in,amma dayake hasken ahannunta yake sai hakan ya hanashi ganinta dakyau. Takowa yafarayi zuwa inda ta ke tsayen,amma still bai sauk'e hannun daya d'aga dan kare hasken dashi ba. Bata motsa ba,kamar yanda bata kawar da hasken daga saitinsa ba,sai da taga yakusan cimmata kafin tajuya bayan ta yada wayar agurin,ta nufi k'ofa da gudunta. Tsayawa yayi cak,daga inda yake tsayen, sai ya kama kunkumi da dukka hannayensa biyu gefe da gefe,yabi bayanta da kallo,harta k'arasa bakin k'ofar. Jijjiga kansa kawai yayi jin yanda ta ja k'ofar da k'arfin gaske. Idonsa ne yakaiga wayar data jefar d'in garin gudun rashin gaskiya. "Hmm" afili,sannan ya k'arasa ya d'auki wayar ya kashe hasken.Daganan ya koma ya d'auki mansa ya shafa ya shirya ya fito da wayar a hannunsa. Ahankali yake takawa danko k'arar takalmansa ma ba'aji. Abakin k'ofar shiga parlourn yayi sallama,daga ciki daddy ya amsa masa,jin amsawan da akayi ne yasa shi d'aga labilen yashiga fuskarsa cike annuri........ _Share pls_ ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป *Salmerh* ๐Ÿ˜ [10/2, 5:51 PM] Ummiyo: ๐Ÿ’• *CAPTAIN ABBAS* ๐Ÿ’• By *Salmerh MD* Luv story๐Ÿ˜ *Wattpad @* *Serlmerh-md* ๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* ๐Ÿ’ซ We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Dedicated* *2* _my family_ ๐Ÿ˜ ๐Ÿค™๐Ÿป Masoya ina godiya nima da soyayyar ku ga littafinnan Allah ubangiji ya barni daku.Ameen๐Ÿ‘๐Ÿป *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* ๐Ÿคž๐Ÿป๐Ÿคž๐Ÿป๐Ÿคž๐Ÿป Being quiet and gentle doesnโ€™t mean youโ€™re weak. Such people show deep, inner strength thatโ€™s under control. Itโ€™s knowing when to speak and when to listen; when to take action and when to wait. Donโ€™t underestimate such people. *They walk* *the earth with the* *greatest strength!* ๐Ÿ…ฟ *7* Tana fita daga d'akin nasa waje tayi tana haki,taje tasamu k'ark'ashin wata bishiyar mango da ke acan bayan d'akunan gidan tayi zamanta dayake akwai abin zama agurin,aranta take ta tunani wai daman wannan neh yah Abbas d'in,? Wannan ai babba ne,wata zuciyarta tace ta ce mata amma fah yah had'u,mtssew taja tsaki afili ,toh sai a gidanmu zai zauna neh,ni bana sonshi wlh, nafi son yah Abbas d'ina na dah,don mummy tace har makaranta yake rakani da islamiyah harda yawo muke zuwa,amma wannan dagani mugunta zai yi. Haka ta zauna ita d'aya agurin tana ta tunani batare da ta je tafad'awa mummy sakamakon aiken ba. Daddy da mummy neh kad'ai suke zaune a cikin parlourn sanda ya shigo,cikin hikima yad'anyi yawo da idanuwansa acikin ilahirin d'akin ta yanda babu wanda zai lura da abinda ya akaita ko kuma manufar yin hakan,amma bai ganta ba,ya k'araso inda yakamata ya zauna,harya samu wuri ya zauna mummy bata ga Teemah ba, da farko ta zaci abayansa zata shigo tunda basu shigo tare ba,amma sai taga wayam,hakan yasa ta dube shi sannan tace "ina kuma 'yar aiken ta tsaya?" "Tun d'azu fah ta taho mummy" Abbas d'in ya bawa mummyn amsar tambayanta,fuskar sa cike da murmushi. wayar dataje dashi d'in ya miqawa mummyn "Harta manta wannan ma" "Hmm" mummyn tace tare da miqk'a hannu ta kar6i wayar,sannan ta k'ara da fad'in kaga kuwa bata biyo tanan d'in ba,ta fad'a tana me daidaita zamanta, "kode yasar min wayar tayi garin haukarta ko? Mummyn ta tambaya tana kallonsa Jijjiga kansa yayi alamar a'a. Daddy kam bai kulasu a maganar tasu ba,don gaba d'aya ya tattara hankalinsa ne akan kallon labarai. "Yah gajiyar hanya toh? mummyn tasake tambayar Abbas d'in tana kallon labaran itama. Da Alhamdulillah ya amsa mata. Daganan mummyn tamiqe ta isa ga dinning,Bismillah ta musu tana me k'ara shishshirya wajen da kyau. Abbas ne ya fara mik'ewa tsaye,kallon Daddy yayi sai yaga kamar ma bai san dasu awajen ba gaba d'aya,dan bashi da alamar miqewa,gaba d'aya labarun ne suka d'auke masa hankali,murmushi ya saki sannan ya isa gaban TV d'in ya tsaya k'ik'am ya tare komai,Daddy bazata kawai ya gansa tsaye agabansa,waiwaya wa yayi ya kalli gefensa tukunna kafin ya sawo da kallonsa ga Abbas d'in,dan bai san ma sanda ya bar gefensa ba. Hannu ya ware ya dan k'wali ๐Ÿ–๐ŸปAbbas d'in dashi,tare da fad'in "kaci gidanku" Dariyah Abbas ya k'yalk'yale dashi,yana kallo, daddyn. "Abinci zaiyi sanyi kuma naga alamar baka da niyyan tashi"Abbas d'in ya fad'I bayan ya tsagaita dariyar tasa. Mik'ewa daddy yayi ya isa ga Abbas d'in,hannu yasa ya kamo kunnan Abbas d'in d'aya yana murmushin shima,fara jan sa yayi ahakan ya nufi gurin cin abincin dashi. Yana kama kunnan Abbas d'in take yayi k'asa ya rage tsayi kad'an, dan ba bak'aramin zafi yajiba.Daddy da k'arfi ya kama kunnan nasa. "Awchhh daddy zafi"Abbas d'in yafad'I tare da dafe kan hannun daddyn da duka hannayansa biyu. Ahaka har suka isa gurin dinning d'in bakin Abbas baiyi shiru ba sai cewa yake "afuwan,afuwan daddy wlh bazan k'ara ba". Daddyn sakinsa yayi har se da suka isa daf da wajen cin abincin. Dariyah suka ji an k'yalk'yale dashi daga bayansu. Daddy dayasan wace mai dariyar ko juyawa baiyi ba yasake kunnan Abbas d'in,dan yasan wannan aikin sai Teemah,dama yamasa hakan nema dan ganin bata nan,datanan da ko farawa bazaiyiamba dan sanin halinta dayayi. Waigawa Abbas yayi inda yaji sautin dariyar,four eyes sukayi da ita,take ta zaro ido waje tare da d'ago hannunta ta rufe bakinta dashi,da gudu tajuya tayi hanyar d'akinta,daman shigowarta kenan,sai taga daddy yana jan kunnansa shine ta tsaya dariyar mugunta. Mummy da tunda taji dariyar itama ta waiga tana kallonta da mamaki."Allah ya shirya"mummyn tace bayan Teemahn ta wuce ciki. Cigaba tayi da zuzzuba musu abincin,tana aikin zubawan ne tace wannan yarinyar akwai shakiyanci wallahi,Zo ka zauna Abbas manta da ita zanyi maganinta ai....... Tahowa yayi yaja kujera ya zauna d'in kamar yadda mummyn tafad'a, yana zama mummy ta tura masa nasa abincin danshi daddy kam ma har ya fara aikawa da su. Bismillah yayi shima yafar ci,kamar yanda kowa dake gurin yayi,amma ga mamakinsa har suka kusan gamawa babu Teemah babu alamarta kuma babu wanda ya damu da rashinta awurin. Baisan cewa su sun riga da sun saba da rashin cin abincinsu batare da ita ba. Gyaran murya yayi kad'an sai yaga duk sun kallo sa. Ganin hakan sai ya d'aga hannunsa ya nuna inda tabi d'azun tare da fad'in wancen yarinyar bata cin abincin ne ita? yayi maganar ne batare da kallon kowa ba daga cikinsu.kuma hakan kenan yana alamta cewa daga bakin kowa ma amsa kawai yake da bukata inda hali. Daddy ne ya d'an murmusa sannan yace "kamanta kaika koya mata?, "Wannan yarinyar ai rainonka ce Abbas"sai da yad'an bud'o idansa kadan sannan yasake fad'in "ta kware yanzu kuwa a wannan tafiyar" Abbas kallon daddy yayi da fuskar mamaki. "Ehh" Daddyn yasake tabbatar masa da abinda ya fad'i. "Tun barinka gidannan Teemah bata bar al'adarta ba na k'in cin abinci da rana ba sai ranar data ga dama take ci. K'asa yayi da kansa yaci gaba da cin abicinsa batare da yayi magana ba. Mummy ce taci gaba da fad'in "Aini bakina har kusan tsayi yayi akan cin abincin nan,sai da naga da gaske takeyi sannan na kyaleta nima na hutawa raina." Murmushi kad'an Abbas yayi acikin ransa yace "zakuwa musa k'afar wando d'aya da ita". Babu wanda yasakeyin magana acikinsu har suka k'are cin abincin. Daddy ne yafar tashi awurin ,yabar mummy da Abbas wanda shima tun d'azu ya ajiye spoon d'insa dan already yaji shi full,amma bai bar kan dinning di'nba illah baya da yayi ya jingina da jikin kujeran dayake zaune akai. Har sai da yaga tashin Daddy tukunna kafin ya dawo da jikinsa kan kujerar da kyau,sannan ya fusaknci mummy. K'asa yayi da muryarsa yanda ba kowa zaiji sa ba. "Mummy " Ya ambata ahankali Kallonsa tayi batare da ta amsa ba,ko dan ganin suna kusa ne oho, "Kardai waccan Teemah ceh"yafad'a tare da nuna hanyar databi d'azun kamar yanda yayi da farko da zai tambaye su ita. 'Daga masa kai mummy tayi alamar "ehh"tana d'an murmushi,daganan tacigaba da duban cikin wayarta data keyi tun da farko. Abbas kuwa baya yayi yakoma ya jinginu tare da lumshe idansa yakuma bud'esu atake. Arannasa yake jinjina al'amari irinna ubangiji da ba'a ta6a yimasa gyara. Tsinkayo muryar mummy yayi tana cigaba da bashi labarin irin rigimar da suka sha bayan wancen tafiyar tasa. Mamaki yaringa ji aransa danshi bai ta6a zaton ma zata jima batare data manta dashi ba,saboda bawani jimawa yayi tare da ita ba alokacin, its just 3month l,bud'an baki yayi yace "lallai mummy kinsah rigima. Murmushi mummyn tayi sannan taci gaba da fad'in aikasan halin yaro sai ahankali, yaro yana da saurin saboda kamar yadda yake da saurin mantuwa,dan idan yaro ya riqe abu akansa zaka samu ba fiya mantawa ba,sai dai idan akayi rashin sa'a ya manta d'in toh kuwa da wuyah yasake tunawa. Jinjina kansa yayi alamar gamsauwa da maganar mummyn,dan kuwa shima yasan da hakan dan baya raba d'ayan biyu yanzu Teemah tamanta da ko shi d'in waye ne agurinta. Koda ya koma d'akinsa ma kwanciyah yayi bayan ya cire rigar da ke sanye ajikinsa,rigingine ya kwanta yana tina yarintar Teemahn, Murmushi yasaki daya tino inda mummy tace wai Teemah tace mummy tak'irashi da yah Abbas ba Abbas ba,So ths stubborn girl bata manta dani da wuri ba kenan,take yaji yana ma son yaganta dakyau, dan duk haduwar da suka yi ba haduwar arzik'i bace tunda yazo gidan.so yake ya ganta da kyau yanzu. Juyi yayi zuwa d'ayan b'angaren hannunsa,ya cigaba da tuno rayuwar da suka yi abaya,muguntar yarinyan nan har yanzu bai barta ba. "Hmm" yace afili sanda ya tuno irin dariyar data k'yalk'yale dashi dan kawai taga daddy yana jamasa kunne. Tashi yayi ya zauna ya d'au wayarsa yak'ira wani abokinsa.sukayita surutusu.Daganan ya tashi ya canza kaya sannan yabi jikinsa ya feshe da turarukansa masu dad'in k'anshi,wayoyinsan yasa hannu ya d'auka,ya fice daga cikin d'akin cikin tafiyarsa mai k'ayatarwa. Gurin habibu ya nufah yaje ya anshi key d'in mota,da kansa yayi driving ya fice daga gidan zuwa inda zashi. *ur comment is* *needed* ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป _Share pls_ โ˜๐Ÿป *Serlmerh* ๐Ÿ˜ [10/2, 5:53 PM] Ummiyo: ๐Ÿ’• *CAPTAIN ABBAS* ๐Ÿ’• By *Salmerh MD* Luv story๐Ÿ˜ *Wattpad @* *Serlmerh-md* ๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* ๐Ÿ’ซ We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Dedicated 2 _my family_ ๐Ÿ˜ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Never let the experiences of your past bring harm to your future. Remember, your past canโ€™t be altered and your future just doesnโ€™t deserve the punishment. ๐Ÿ…ฟ *8* Teemah kuwa tun fitar ta d'azun bat k'ara fitowa ba,bacci ne yad'auketa bayan tagama dariyar muguntar ta,ita adole in anbarta wai taga babba yanan kuka,"kai daddy ya iyah purnishment tafad'a cikin dariyar,nima fah haka mummy take min inna yi mata laifi,gashi nima yau daddy yarama min,Horhh daddy kabiya ni wallahi" Haka tayi ta sumbatu ita kadai,har tafara jin bacci,takuwa kwanta tayi baccinta bayan tacire doguwar rigar dake jikinta. Ba ita ta tashi ba sai kusan la'asar,tashi ta yi ta watsa ruwa tare da d'auro alwala. Sai da tayi sallar kafin tashirya cikin uniform tafito taahiga kitchen neman abinda zata ci,duk ba wani abin kirki taciba,amma ita tana ganin hakan yafi mata akan ta zauna taci abincin. Koda tagama kale kalen nata a kitchen d'in d'akin mummy taje,bata samera a parlourn ta ba,hakan yasa ta wuce bedroom d'in mummyn,sallah tasame ta ta nayi,amma azaman tahiya take,ganin haka yasa tawice gaban mirror tana k'ara gyara fuskarta da kyau. Tacikin mirrorn ta hanago mummy ta yi sallama,ganin hakan sai ta baro wajen datake tsayen ta taho ga mummyn, "Mummy natafi islamiyah" Kallonta mummyn tayi batare data yi magana ba dan bat so ta yanke azkar d'in datakeyi,sai d'an yatsanta data d'aga ta nuno Teemahn dashi tana d'an juya shi kad'an. "Mummy bacci ne fah ya d'auke ni shiyasa na makara'?" Tafad'a da d'an ta6e baki alamr shagwa6a dan tasan ma'anar hakan da mummyn tamata. Jijjiga kai mummyn tayi kawai tare da d'auke idanta daga kan Teemar. Ganin hakan yasa Teema ficewa daga d'akin,dan mummy ta gama sallamarta. Waje tayi tanufi cikin gidan,tana fita kuwa tafara kwalla wa Habibu k'ira,shima yanaji ya taso da d'an saurinsa ya iso inda taken dan wajen da ake parking motocin gidan ta nufah ita. "Y'ar gidan daddy ganinan ya akayi" Cewa tayi "yauwa malam habibu ka kaini makaranta mana, yau na makara wallahi" baki yakama sannan yace "ta6, "kinga kuwa babu key awurina,shiga ki kar6o key saiki zo mutafi dawuri" Kallonsa tayi sannan tace "toh ina na wurin naka"? "Wannan bak'on ne yafita dashi."Ya bata amsa. "Wai yah Abbas kake nufi?"Tasake tambayarsa. "Oho ai bansan sunansa ba."Zaro ido yayi kamar wanda yaga wani abin tsoro "Kar dai wannan shine Abbas d'in gidan nan"ya yi tambayar yana kallonta. "Ehh wai shine inji mummy"itama ta bashi amsa. "Baki habibu ya sake kamawa cikin tsananin mamakin gani wannan murd'ad'd'en ne wai Abbas,ta6d'i" Habibun ne yasake cigaba da fad'in "Abbas ne yayi irin wannan girman h............. Kafin yajai ayar magabar tasa sukaji adanno horn daga wajen gidan,da gudu mai gadi yaje ya lek'a sannan yadawo da kansa ciki ya wangale get d'in. Ahankali motar ta shigo tazo tayi parking gefe dasu kad'an, Habibu ne yace "yauwa gashinan ma yadawo" Teemah kam batayi magana ba illah ido data tsurawa motar. Tsawon mintina

Chapter 3 of 67