bud'e mata get d'in tashiga.
Da sallama suka shiga parlourn,babu kowa aciki dan haka kowa yanufi d'akinsa.
Teemah na shiga ta fara ciccire kayan jikinta,sai da taga tacire komai sannan tafad'a kan gado tare da fad'in
"wash wallahi nagaji"
takai tsawon mintina biyu akwancen kafin ta mik'e tsaye
Towel ta d'auka akan k'ofar bayinta ta d'aura sannan tayi unhooking bra d'in jikinta ta ajiyesa,ta nufi k'ofar fita,harta kusan fita daga d'akin sai ta tuna abinda ke jikinta dawowa tayi sai kuma ta tsaya ta fara kwalla k'iran Baabah Lami,bakinta uku taji shiru babu amsa sai ta d'auki hijab d'inta ta saka sannan ta fito,kitchen ta shiga ta d'auko ruwan goran c'est,garin fita daga kitchen d'in ne ta had'u da Baabah Lami ita kuma tana k'ok'arin shigowa kitchen d'in.
"Baabah Lami inata k'iranki kika k'i kulani"
"Yi hak'uri fatee,naje wurin hajiya ne,
"Owk dama ruwane kuma ma kinga na d'auko abuna"
"Babu wani abinda kuma kike buk'ata?
Baabah Lami d'inne ta tambayeta da dukkan kulawa.
"Ah ah bakomai "
Teemahn ta bata amsa.
Daganan tawuce d'akinta da ruwan ahannunta,tun kam ta k'arasa cikin d'akin sai ta cire hijab d'in ta rik'e a hannunta, zama tayi akan side drwaer d'inta ta d'aga goran ruwan takafa abakinta,dan ko kofi ma bata d'auko ba,sai data sha kusan rabi kafin ta rufe ta ajiye
"Gaskiya yau kam masha Allah akwai zafi"
Wanka ta tashi ta shiga kusan 20mins tana bayin sannan ta fito,wajen dressing mirror ta nufah tana goge jikinta,sai yanzu taji d'an dama dama,domin ruwan sanyi tahad'a tayi wankan dashi,shiyasa take so tad'an shafa mai koda ak'afarta da hannunta ne dan kar suyi mata wani iri.
Har taje ta tsaya gaban madubin sai kuma ta tuno ashe man nata ya k'are gaba d'aya,ai kawai sai ta fito ta nufi d'akin mummy ahakan datake,shaf ta manta da batun wani Abbas agidan shiyasa take al'amuranta cikin sake wa kamar yanda tasaba.
Sallah tasamu mummyn nayi take ta tuna ashe fah batayi azahar ba itama.
Zama tayi tajira mummyn harta idar sannan ta tambayeta batun man shafuwan.
Mummy cewa tayi "aini mantawa nayi ma gaba d'aya,ki bari da yamma zan aika asiyo miki"
"Toh"
tace sannan tamik'e da niyyar fita daga d'akin,
"Teemah"Mummy tak'irata tana daga zaune akan sallayar datayi sallahr.
"Na'am"ta amsa tare da juyowa
"Kindai san yanzu bamu kad'ai bane agidan nan ko?
"Kai ta d'agawa mummyn alamar "ehh"
"Toh ki daina fita da irin wannan shigar dan Allah."
"Toh mummy yan zunma mantawa nayi ne kuma dana fito ma ban had'u da kowaba"
"Ki dai kiyaye"
"Uhm"
Teemahn tace sannan ta fito daga d'akin.
Bata lura dashi ba har sai da tazo tsakiyar parlourn sannan taganshi,abu yake k'ok'arin d'auka a gefen TV,jitayi kamar tajuya tunda bai ganta ba,amma kafin tayi yunk'urin juyawan har ya d'ago daga inda yake tsayen.
Salati tafara acikin zuciyarta dataga yakafeta da idanunsa,ko kyaftawa bai yi,shikenan wannan mutumin yau kan nashiga uku ahannunsa,tun daga k'afarta yafara bi da kallo ahankali har zuwa cinyoyinta,dayake towel d'in k'arami ne sosai sai hakan yabashi damar kallon surar jikinta da kyau.
"Masha Allah" yace
azuciyarsa,yarinyace amma babu laifi take yaji wani sabon yanayi yana ratsa shi ta ko ina.
Ido yad'aga ya kalli fuskarta sai suka had'a idanu,kunyar ganin jikinta da yasan tasan yayi ne yasashi d'aga k'afafu ahankali ya tunkari inda take,itama kuma da tayi ya fara nufo inda take tsayen, sai ta rintse idanunta da k'arfin gaske jikinta har rawa yakeyi."wayyo Allah nah" take ta nanatawa acikin ranta.
Daf da ita yazo ya tsaya ya wani k'ank'ance idanu kamar gaske bayan yagama morewa kallonta.
Har ya d'aga hannu zai kamo kunnanta sai kuma yafasa ya mai da hannun nasa k'asa,dan yana ganin kamar idan ya mata hakan zai iya sawa d'an guntun Towel d'in dake jikinta ya kunce saboda yanda yaga duk jikinta na rawa abin har yaso bashi dariyah,amma sai yayi murmushi kawai,"shegen tsoro da rashin kunyah duk ta tara".
Jin shiru datayi bayan ta riga ta tabbatar da ya iso inda take tsayen,dan tanda tashi alamun mutun agaban,tsammanin sauk'ar mari tayi amma sai taji shiru 6ud'e ido tayi ahankali.
Sai taganshi tsaye agabanta yana sake kallon k'asan wuyanta.
Baya ta d'anyi da sauri tare da bud'e idanun gaba d'aya.
Matsawan datayi sai ya bada gaf mai d'an tsayi atsakaninsu.
Kuma sai hakan yasa taji wani k'warin gwiwa ya shigeta.
"Ba kijin magana ke ko?
"Nan d'in gidan iskanci ne aka gaya miki"
Ya fad'a da wani serious tune kamar gaske nan kuwa rasa abin fad'a ne yashi cewa hakan.
Batayi magana ba illah kallonsa data keyi itama kamar yadda ya k'ureta da idanu.
"Kunnan k'ashine da ke ko"
Hannunta ta d'aga ahankali ta sada shi da kunnanta, ta6a kunnan tayi,kamar wanda batasan da zamanshi ajikinta ba sai yau.
Jitayi kunnan da laushi.Sai ta sauk'e hannun nata.
"Tambayarki nake kin min shiru"
Ya sake daka mata tsawah.
"Kunnan k'ashi ne dake nace ko"?
Yafad'a awani hasale.
Jijjiga masa kai tayi tana kallonsa,
"Umhm"
ya sake fad'i.
"Kunnena bana k'ashi bane "!
"Toh menene?
Ya sake tambayarta shima.
"Na nama ne "
Ta bashi amsa.
Ji yayi dariya takamasa sosai,da kyar ya samu ya tsare,amma saida ya d'an kalli gefe da gefen sa sannan ya samu ya basar ,maida dariyar yayi tazama murmushin gefen baki.
"Zan kuwa koya miki hankali yau d'in nan"
Yafad'a yana me k'ara nufar inda take,
Ai da gudu tayi hanyar d'akinta,tana shiga ta tura k'ofar ta rufe ta jinginu tana maida numfashi.
Tsayawa yayi yabi bayanta da kallo,yanda mazaunanta ke juyawa lokacin datake cikin gudun har sai da ta 6acewa ganinsa.
Jijjiga kai yayi tare da fad'in " ~astagfirullah~ "
Mena keyi ne wai?.
Sai da ya isa d'akinsa sannan yaji dariyah ta k'wace masa,ya kuwa yi abinsa son ransa,zuwa yanzu duk lokacin day tuna Teemah jiyake kawai tana bashi dariyah,saboda irin ta'asar data iyah
"Yarinyan wallahi tafara bani tsoro"
Ficewa ya sakeyi daga gidan ya tafi yawonsa.
Teemah kuwa tashi tayi ta d'auro alwala sannan ta zira wata bak'ar abaya ta tada sallar azahar,
Bayan ta idar ne tacire abayar,kuma se alokacin tafara tunanin abinda ya faru,"mugu kawai dana tsaya k'ila da sai de mummy ta d'auki gawata,dan nasan jibgata zai yi,babu ruwansa.
(Kunjifahπ€ ita damuwarta lpyar jikinta ne bawai kallon bati da ya yiwa jikin nata ba).
shiryawa tayi cikin uniform d'in islamiyarta da zindimemen hijab ta fito.yanzun kam a parlour tasami mummy tana zaune,cewa tayi
"Ah yau har kin shirya dawuri haka,babu latti kenan",murmushi tayi wa mummyn sannan tace
"hadda ta tarumin ne mummy inaso in rage"
"Abinci fah"
"Kai mummy,may be sai na dawo"
Daganan tafitah daga d'akin zuwa cikin gidan.
Bata fi 7mins da fita ba ta dawo ciki,sai da tayi sallamah,kafin tace "mummy gidan fah babu mota ko guda d'aya"
"Haka akayifah namanta ne,Habibu bai dawo ba har yanzu,Abbas kuma inaga ya fitane,zoki d'auki #200 ajakata inaga de kamar akwai,maza ki hau adaidaita ki tafi,kuma in antashi kar ki tsaya jiran driver ki dawo abinki dan ko Habibu ma yadawo zai hutane babu inda zashi sai dai zuwa gobe in Allah ya tashemu.
Da "toh " ta amsawa mummyn tare da shiga d'akin.
Fitowa tayi sannan tace "toh na wuce mummy"
"Uhm Allah ya tsare"
"Ameen" tace sannan tafice daga parlourn.
Abbas ma bai dawo gidan ba sai da yamma,koda ya dawo d'inma kuma zamansa yayi a gaban gidan yana duba abu a system d'insa.
Dawo wanta kenan daga islamiyah ta ganshi zaune aharaban gidan.
Harara ta banka masa kasancewar baya kallonta,tana isowa inda yake kuwa dan dolenta tace masa "ina yini yayah"
"Lafiya "ya amsa mata dashi batare da ya d'ago ya kalleta ba,harta d'an gotashi sai kuma taji yace "ke kinga zonan!
dawowa tayi baya ta tsaya d'an nesa dashi.
"Waye ya kawoki gidan?
"Babu" tabashi amsa dan bata san inda tambayar ta dosa ba.
"i mean keda wa kika dawo, banji anbud'e get ba sai kawai na ganki"?
"Ehh ni kad'ai dawo"
tabashi amsa.
"Habibun fah ko har yanzu bai dawo bane?
"Nima bansani ba" tabashi amsa.
"Ok jeki"
Juyawa tayi tawuce ciki aranta tace
"Mutum sai mugun hali da bak'ar zuciyah"
(Toh fa,ni nakasa gane wanda keda mugun halin acikinsu)
Baijima ba awurin shima ya taso ya shigo ciki,zuwa yayi ya tambayi mummy akan batun rashin dawowar habibun har yanzu,anan takece masa itama abin na ranta wallahi,amma bari tak'irashi taji.
Koda ta k'irashin ma cemata yayi yana hanya yama shigo cikin gari.
Sai da taji haka sannan ta tsinke wayar tare da fad'in "toh Allah ya tsare.
Ba'a dad'e ba kuwa sai gashi ya iso.
Ashe accident yasamu bayan ya sauk'e daddyn ahanyar ta dawowa gida,daya ke ma bai bar cikin maidugurin dawuri ba,sai da yayi sallahr azahar acan,sannan yakamo hanya
cikin tsau tsayi kuma sai wani mai golf yamar karo daga bayan motar,toh shine ya tsaya aka d'an daidaita natsuwar motar kafin yasamu ya iso,jimami sukayi gaba d'ayansu,daga nan mummy tace toh yaje gida yad'an huta koda na sati d'aya ne,sannan tashiga ta kawo mar 'yan kud'ad'e tabashi.
Godiyah yata zubawa mummyn.
"Nagode hajiyah Allah yayi albarka, Allah ya kare zuri'a........Allah ya......... Allah yah.....
Hakade ba iyaka,mummy kuwa sai Ameen taketa fad'i dan acewarta ba'a raina addu'ah ko yaya take bakasan bakin wa yafi albarka ba.
Kafin yafita sai Abbas ya rigashi barin d'akin Habibu nafitowa sai suka had'u a hanya.
Hannu ya mik'awa habibun suka yi musabaha,raba hannun nasu keda wuya habibun yafara zuba wata sabuwar godiyar,shi kuwa bai tsaya ba ya wuce abinsa zuwa d'akinsa.
Ashe shima kud'i yabawa habibun,saboda yana tunanin Habibun da kud'in jikinsa yayi gyaran motar kuma karsu shiga hakkinsa arashin sani,amma dayake bai bari kowa yagani ba sai babu wanda yasan nawa ne.Amma de inaga bazai wuce 20k ba.
Ranar kam ko agun dinning ma basu had'u ba,dan Abbas bai nemi abinci ba ba ranar,
Kuma mummy bata aika ta k'iransa ba.
Tade neme shi a waya anan yace mata,bai jin ci ne yau d'in,tace anya lafiyarsa kuwa ?
"ehh lafiya mummy kawai de ak'oshe nake ne.
"Toshiken Allah ya k'ara lafiya"
"Ameen summah Ameen"yace mata daganan sukayi sallama.
Teemah ranar farin ciki kamar ya fasa mata k'irji haka taji.
_Share nd drop ur_ _comment pls_ ππ»
Farin cikina shine comments d'inkuπ
*Salmerhn ku ce* π
[10/2, 5:54 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated_
_2 dukkan masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs.Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ π
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Sometimes we must get hurt in order to grow, we must fail in order to know, sometimes our vision clears only after our eyes are washed away with tears.
π
Ώ *12*
Washe gari kuwa Abbas da sassafe ya fice agidan,ko da Teemah tayi shirin makaranta ma sai dai kud'in adaidaita mummy tabata, ranta ma baya son hawan adaidaitan amma babu yanda zatayi tunda Habibu bayanan.
Haka taje ta tari adaidaita ya kaita makarantar,koda aka tashima haka tadawo,amma sai bata dawo dawuri kamar yanda tasaba dawowa kullum ba,koda tadawo d'in kuwa zube wa mummy tayi ajiki da fitina wai kanta na ciwo saboda tsayuwan data yi abakin titi dan jiran adaidaita,gakuma gari akwai zafin rana sosai.
Haka mummy yau kam tayi ta biye mata,dan gaskiya ta d'an tausaya mata ganin yanda duk tayi sanyi.
Ranar ko islamiyah ma batajeba,sai da aka nema mata panadol tasha tayi bacci kafin nan ta warware.
Wasegari ma ba taje makarantar ba,k'in zuwa tayi,ganin haka yasa d following day
Mummy ta kaita ta kuma d'auko ta,next kuma ta tafi a napep Abbas ne yakawota gida.
Kwanan daddy biyar ya dawo,Abbas ne yaje har maiduguri ya d'auko sa zuwa gida,dayake daman tafiyar ba wata qasa bace yaje, lagos ya tafi batun kasuwancin su da suke yi kusan atare shi da yayan mummy,tare ma ake sauk'e musu kaya,yayan mummyn acan yake da zama shida iyalansa.
Dawowar daddyn Teemahn ne yake sanar musu cewa ai Mahmud (d'an yayan mummyn) anan zai zo yayi service d'insa kuma nan da two days zai iso,nextweek zasu shiga camp.
Mummy dataji wannan batun kawai sai ta fara hawayen farin cikin zata ga jinin d'an uwanta bayan tsawon wasu shekaru,babu wanda ya hana ta kukan dan daddy ne kad'ai yasan dalilin kukan nata,Abbas da Teemah kam babu abinda suka sani dan haka suka zuba mata idanu,Abbas mamaki yake yi akan dalilin kukan nata daga jin zasuyi bak'o..............kodai.......kodai.......
Teemah kam dataga mummynta na kuka,da farko itama tsayawa tayi kallon mummyn amma daga baya itama sai ta fara kukan dan bata ta6a kallon mummy tana zubda ruwan hawaye ba tunda tayi wayo.
Mumm ganin da tayi y'arta na taya ta kukan sai ta yi k'ok'arin dakatar da nata hawayen,tana murmushi.
Janyo Teemah tayi ta rungume ta kiyi shiru,ki daina kuka kinji,kukan farin ciki nakeyi Teemah cikin ikon Allah bayan wasu tsawon shekaru zanga wani daga cikin danginah,Teemah jinin d'an uwana,maganar take tana murmushi amma still hawayenta bai daina zuba ba,kana ganin yanayinta zaka gane tana cikin wani irin yanayi ne marar misaltuwa.
Daddy ma ido ya zuba mata yana k'ara jin tausayinta acikin ransa.
Sallar la'asar ne ya tada su awurin,Daddy da Abbas suka wuce masallaci,Teemah kuma da mummy kowa ta nufi d'akinta.
Kafin isowar Mahmud d'in mummy akullum annurinta k'aruwa yake yi,komai tana yinsa cikin walwala da farin ciki,da ka ganta kasan annurin daya ke kwance asaman fusakrta har cikin zuciyarta yake,musamman yau daya kasance suna saka ran isowarshi agobe.
Musamman taje kasuwa tayi siyayyah sosai wai afad'arta duk na taran d'anta ne.
D'akin da zai zauna kuwa tun jiyah aka gama gyarasa tsaf,aka sa dukkan wani abin buk'ata aciki.
Washe gari asabar mummy dawuri ta tashi ta taso k'eyar Teemah ma,seda suka koma ta sake duba d'akin da zai sauk'a aciki ta tabbatar da babu wata matsala kafin suka fito,Teemah mamakin wannan al'amarin yabi ya cikata.
Kitchen sukaje da mummyn anan suka samu Baabah Lami,dukkansu mummy taraba musu ayyuka,yau da kanta tayi girkinta duk wanda take ganin zai burgeta shi tayi kusan kala uku,juice kuwa sun had'a d'aya already ansa afridge,gasu kuma suna kan had'a wani daban,inka ga yadda mummy ta dage agirkin,ka kuma dubi yawa da kalolin abincin zakayi tsammanin family guda ne zasu zo,abin ya d'aurewa Teemah kai,ita de jitayi ance mutun d'aya ne zaizo amma ga mamakinta sunyi girkin da kusan mutane goma ma zasu ci su kuma rage saura.
Kallon mummyn nata tayi sannan tace "mummy wai bak'i nawane zasu zo?
Mummy cikin murmushi tace "Mahmud ne zaizo Teemah."
"Mahmud d'in shi nawa ne mummy?
"'D'aya mana Teemah,wai miye matsalarki ne ke kam.?
Kauda kai tayi daga kallon mummyn ta cigaba da blending d'in data keyi,amma sai taji zuciyarta ta kasa hak'uri da wannan abin.
"mummy amma de kinfi sanshi akaina ko?
Dariya sosai tabawa mummyn hakama Baabah Lami,dariyarta sukayi san ransu,Teemah kuwa ta wani basar ko kallon inda suke batayi ba dan ita tambayarta har zuciyarta tayisa,so ta ke taji amsarta amma kuma sai suka maida maganar abin dariyah.
Saida suka tsagaita ne Baabah Lami tace "kai Fatu tun yanzu harkin fara kishi ne?
Fushi ta k'ara akan nada d'in datayi,dan maganar baabah Lami duk abin haushi ne awurinta.
Wai fatu........
Kuma wai tana kishi..........ita aganinta ai gaskiyarta ne,dan yanda taga mummyn na zumud'in isowar Mahmud d'in dole ya sosa mata zuciyah amatsayinta na y'a k'walli d'aya tal agun mummyn,aiko zuwan Yah Abbas ma mummy batayi wannnan azar6a6in ba,koda yake shi zuwan bazata yai musu basu san da zuwan nashi ba,kawai sai de suka ganshi.
Turo baki ta k'ara yi gabamummy ce tace mata
"ki rabu da Baabah Lami d'innan kinji yayanki ne fah,ana kishi da yayah ne kuma ai ba'a yi,
kinga ni kuma ai dole nayi farin ciki da zuwansa shekaru nawa rabo na dasu Teemah."
Lalla6anta mummyn ta cigaba dayi da kalaman kwantar da hankali,dan tasan halin Teemahn nata ba dai kishi ba,haka tayi ta binta a hankali har suka gama aikin gaba d'aya.
Sai bayan la'asar kafin Mahmud ya iso gidan, lokacin Abbas da mummy ne kad'ai agida.
A babban parlourn gidan suka fara sauk'ar dashi, lokacin da mahmud ya iso daddy baya nan,Teemah ma tana islamiya,mummy tayi murna da farin cikin zuwansa sosai,Abbas kuwa sai dai ido,dan mummy murnar tata tanayi ne had'e da hawaye tana tambayarsa labarin iyayensa,shima d'in duk jikinsa yayi sanyi dan anjima ba'a had'u ba amma shi bai wani yi kuka ba,ganin mummy takasa daina hawayen ne yasa Abbas ya fara bata hakuri duk da bai san manufar kukan nata ba.
Koda teemah tadawo ma sannu da zuwa kad'ai tamasa,dan ba saninsa daman tayi ba,gara shima yasan da ita,kawai dai rashin zumunchi ne yasa babu shak'uwa atsakaninsu.
"Fatima zarah "
Ya k'ira sunanta lokacin data mar sannu da zuwa d'in,dayake sunzo sunanta kuma fatima zarah shine sunan da aka ambaceta dashi aranar.
Amsawa tayi daganan tawuce ciki abinta batare da ta zauna a inda ta tarar dasu d'inba.
Sallar maghrib ne ya tadasu a parlourn,Abbas masallaci suka tafi suna idarwa kuwa suka dawo gida sai a sannan suka tarar da daddy yadawo,gaisawa sukayi da daddyn daganan ya wa mahmud d'in Barka da isowa dan shi ya riga da yasanshi ,dayake suna yawan had'uwa idan yaje Lagos.
Ganin sun dawo d'inne sai mummy tafara kwallawa Teemah k'ira,bakinta d'aya ana biyu Teemah ta amsa.
Akan dinning tasame su,nufo wurin tayi tana fad'in mummy dawuri haka yau kuma?
"Uhmm"
Kawai mummyn tace mata.
Daddy ne yace "yau mummyn ki ta sauya mana tsarin mu angel saboda taga sabon d'anta yazo"
Yana murmushi yayi maganar.
Mahmud ne yace "a daddy harda kaima ko ?
"Ahh toh mahmud ai munga ana mana wariya ne,dole inyi k'orafi"
Sai asannan mummy tayi magana tana murmushi tace
"Bafah haka bane,ina gudun hucewar abincin ne kunsan dawuri aka gama shi kuma nasan idan ya huce bandaro zaiyi"
Dukkansu sai suka murmusa,sai asannan ne mummy tad'an sake ta rage damuwar data ke ciki,da kanta tayi serving d'insu abinci,kowa yayi bismillah ya fara cin abincinsa,amma banda Teemah da take ta kora ruwan juice tana binsu da kallo d'aya bayan d'aya.
Cikin haka suka had'a idanu da Abbas yawani sakar mata harara,murgud'a mai baki tayi sannan ta d'auke kanta gefe,Mahmud kuwa har yanzu haushi yake bata,dan ta lura mummyn ta tafi sonshi akanta,shiyasa shikam ko kallon arzik'i ma bai samu ba,gani yayi tana ta wasa da cokalin bata ci ba, baifi spoon biyu taci acikin abincin ba,
"Yah dai" yace mata
Bata san ma da ita yake ba amma sai ta d'ago idanu,had'a ido sukayi dashi,sai tawani d'ago baki sama,
"Me aka miki ne?
Ya sake tambayarta.
"Kyaleta mahmud daina 6ata bakinka indai wannan ce"
Daddy ne yafad'i hakan.murmushi kawai mahmud da mummy sukayi,Abbas kuwa sai ya kalleta.
caraf suka yi 4 eyes dashi sai tayi k'asa da kanta tana gunguni,minti biyu bata k'ara ba agurin sai ta mik'e tsaye,juice d'in tak'ara tsiyayah ta wuce d'akinta dashi kowa bayanta yabi da kallo,amma banda Abbas.
Sai da suka gama cin abincin kafin suka mik'e suka fice ad'akin,Mahmud da Abbas ne suka fita harabar gidan suna d'an taba hira atsakaninsu.
Sosai suka fahimci junansu dan Mahmud gwani ne a surutu shikam,bakamar Abbas d'in ba.
Tun daga lokacin wani shak'uwa ta shiga tsakaninsu sosai dayake kowa yaji d'an uwansa yamasa har aransa.
Abbas da mahmud kusan sa'anni ne,Mahmud yasamu delay d'in yin makaranta ne dalilin mahaifiyarsa,shiyasa sai yanzu zaiyi service d'insa.
Koda suka dawo daga sallar isha'i ma ad'akin Abbas suka yada zango,kuma sai alokacin mahmud yake d'an bawa Abbas labarin d'an abinda yasani,shima Abbas d'in sai yaji mummyn tabashi tausayi sosai.
Anan suka ci kusan 2hrs ,sai 10:15 Abbas ya koresa yace "kaje kai ka kwanta ka huta mana,kamanta nisan tafiyar dakayi ko"?
Dariyah mahmud yayi kad'an tare da fad'in "kai de nagano ka so kake in baka wuri ka sake"
"Ehh naji ni dai jeka"
Tashi yayi yabar d'akin yana fad'in mu kwana lpy.
"Allah ya bamu alkairi"
Abbas d'in yabashi amsa.
Sannan ya mik'e yarage kayan jikinsa yayi shirin bacci.
********
Dangantakar mummy da Mahmud tasamo asali ne daga iyayen su mummyn.
Iyayensu asalin 'yan kano ne,dan tun tashinsu a kano suka tsinci kansu,Malam mamman sada shine sunan mahaifinsu,kayan miya yake siyarwa a kasuwa mahaifiyarsu kuma ummah fatsin kusan kowa haka yake k'iranta dashi, iyayensu su biyar suka haifah,amma duk sauran Allah ya kar6i abinsa,su biyu ne kawai suka saura agaban iyayensu har suka girma,suna rayuwarsu cikin rufin asiri da wadatar zuci,yayan mummy mai suna yusuf yana gama secondary mahaifinsa ya dage har seda yaga yasamu gurbin karatu a BUK kafin ya samu nutsuwa,cikin ikon Allah ya fara karatun da sa'a dan bai sami wata matsala ba,shigansu 200level ne suka had'u da kabiru shikuma yazo D.E ne,kuma shine yakasance abokinsa har suka k'are makarantar dan kusan halayyah d'aya garesu.......
Tare suke komai a makarantar inka gansu zaka zaci y'an uwan juna ne ma su,dan basu fiyah rabuwa da juna ba.
Lpy lau suka gama makarantar su,
Cikin ikon ubangiji kuma kamar abinda babansu yake jira kenan yace ga garinku nan,dan kwanan yusuf hud'u da gama makaranta ranar da yamma Baban yana dawowa daga kasuwa mota takad'e shi,garin tsallaka titi hannunsa rik'e da ledar y'ar tsarabar daya saba kawo musu idan zai dawo daga kasuwar,abin ya faru ne akan titin unguwarsu ,hakan yasa ba'a sha wani wahalar ganeshi da gidansa ba.
Dawuri labari ya iso musu,duk kansu suka fice bakin titin da gudun gaske su ummah na kukan fitan rai,dasuka ganshi kuwa take mahaifiyarsu ta suma a wurin.
khadija kuwa kuka ta zube tanayi dan rasa kan wa zata fara zuwa tayi.
Da k'yar aka samu aka tattara su aka kai gida,shikanshi wanda ya kad'e mahaifin nasu kuka yakeyi da hawaye, ba'a wani d'au lokaci ba aka masa sutura, kanshi ne yafashe dan bazama kaso kaga yanda kan yayi ba hatta likkafanin ma sai da yayi ja,dukda an d'an ninka a wajen kai d'in amma sai da ya ratso,Yusuf ne kad'ai mai dauriyah addu'a kawai yakeyi azuciyarsa har suka sada baba da makwancinsa na gaskiyah.
Dayake wanda ya kad'e baban ma zuciyarsa mai kyau ne,dashi akayi komai har zuwa sadakan bakwai,kuma aranar ne ya bayyana abinda ke ransa game da batun diyyah.
Yusuf ne yace su basu son wani diyyah akan mutuwar baban,koda akaso fahimtar dashi akan musulunci ne yazo da hakan ma cewa yayi ya sani,kawai bazai iya kar6ar komai akan dan babansa yarasu ba,mutuwa ai ta Allah ce.
_Drop ur comment_ as u do alwaysπ€π» _pls_ ,
_and i don't need that_ *heart* β€
or
*tnx* / *Thanks*, _even the_ *sticker* ππ» _I don't like it,all i_ _need is ur_ _comments_ .π€π»
*Salmern ku ce* π
[10/2, 5:54 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
masoyan_ _CAPTAIN ABBAS. Kusani ina yinku irin sosai sosai d'innan,Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ π
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Free your heart from any hatred. Free your mind from any worries. Live simply. Give more. Expect less.
π
Ώ *13*
Da malaman suka ji ya fad'i haka sai suka ce toh shikenan daman hakkin addini ne kuma dan gudun siga hakki ake son sauk'e shi,amma tunda yace haka shikenan,Allah ya k'ara musu hak'urin rashin dasu kayi,amma duk da haka sai sunji daga bakin manyansa tukunna,wasu daga cikin y'an uwan baban haushi sosai sukaji dan aganinsu Yusuf bak'aramin bak'in ciki yayi musu ba,amma da sukaji za'a tambayi manyansa sai suka d'an ji dama-dama dan sun zaci za'a samu sa6anin harshe ne.
Sai dai basu yi sa'a ba,dan da aka tambayi ummahn suma cewa tayi
" _a'a yanda idonta yaga jinin Baban ya zuban nan ko da sun kar6i kud'in gani zasuyi kamar jinin baban suka fansar,tsautsayi da k'addara ai abokan tafiyar dukkan wani halitta ne,babu wanda ya isa ya gujewa k'addararsa,Allah ya riga da ya rubuta inda ajalinsa yake kenan dan haka su basu da wani abin fad'a fatansu kawai Allah yah kyautata makwancin Baban"
Ummah tana hawaye take wannan maganar,kusan kowa dake zaune agun sai da ya share hawaye,duk da zuwa yanzun abin yad'an bar zuk'atansu,sun riga da sun dangana tsakaninsu da Baban yamzu addu'a ce kawai.
"Allahu akbar",
"Allahu akbar"
"Allahu akbar"
Babban malamin dake zaune agun ne yafad'i hakan tare da jijjiga kansa,d'ago wa yayi ya kalle su gaba d'aya sannan yaci gaba da cewa
"Hak'ika wannan kad'ai baiwa ce da Allah ya riga ya halicci ahalin wannan gidan dashi,kalamanku su suka bayyana hakan,ga dukkan alamu ba wani k'arfi ne daku ba amma wannan furucin naku yah tabbatar mana da cewa wadatar zuci abokiyar tafiyar ku ne,Allah kad'ai kuka dogara dashi,Hak'ik'a agurin Allah ku masu arzik'i ne da yardarsa,Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairi ya kyautata rayuwarku gaba d'aya daga yanzu har yaumul sa'a.
"Ameen-Ameen"!
sauran dake gurin suka amsa masa dashi,amma kowa jikinsa ya matuk'ar yin sanyi.
Sake kallon Ummah yayi dake faman goge hawaye tun d'azu,sannan yace
"Kuyi hak'uri insha Allahu mutuwar malam hutu ce agare shi muna mishi fatan alkhairi insha Allahu,malam mutum ne da kowa yaji wannan mutuwar tashi ta matuk'ar ta6a zuk'ata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 67