bata dariya ma dan ta da'de da sanar dashi cewa ciwon kan ya daina amma sam ya 'ki yadda motsi ka'dan intayi sai ya tambayeta ko menene.
Ranar da kansa ya tafasa musu indomie da rana suka ci da dare kuwa yace ta shirya suje eatry suci acan dan ba ze iya girkin komai ba yanzu duk ma be fi exercise ba, Teemah tace yaje yaci ya dawo ita kam bata jin cin komai yanzu, Mahmud kuwa yace dole sai taje, tayi-tayi dashi ya'ki barin ta har tace toh yaje in yaso yazo mata da nata still ya'ki amincewa saima ya 'kara da fa'din wai idan ya fita bazai dawo gidan ba sai 11:pm yace in dai zata iya zama agidan ita 'daya toh shikenan sai yatafi karkuma ta kuskura tayi masa complain idan yadawo, dagangan Mahmud yafa'di haka dan yasanta gwanar tsoro ce ita, aikuwa yaci nasara dan yana fa'din haka tami'ke taje ta 'dauko zunbulelen hijab tasa akan kayan dake jikinta suka fita tare.
Mahmud nata cin abincinsa yayinda Teemah tari'ke spoon 'ahannunta tana ta juyawa tare da kallon abincin, murmushine ya kubce mata sai ta 'dago kai ta kalli Mahmud sai kuwa suka ha'da idanu " ' _yanmatan Daddy ya_ _dai_ yace mata.
Sai itama tace bakomai.
" Yah Abbas na tuna wallahi, shifa sam be son cin abincin waje ko yunwa zata masa illlah ne baya ta6a ci har se yadawo gida"
Murmushin shima yayi tare da fa'din " _Abbas zakin fama ba, haka halinsa shikam ai kominsa yana da nasa tsarin."_
Hirar Abbas suka tayi har suka 'kare cin abincin inda Mahmud ne kawai yaci Teemah 'dan cakula tai tayi kawai daga nan kuma sai suka wuce shopping store suka 'dan siyi wasu abubuwan anfani.
Mahmud gidan mahaifinsa yawuce dasu basu sami Abbah agida bama sai dai Anty na nan sun same ta tana waya ne sai suka yi zaman jiran ta, jisuka yi tana fa'din "ehh lafiyan ta gasu nanma yamzu suka zo, ok ta'kqre maganar dashi tare da mi'kawa Teemah wayar kar6a tayi tare da fa'din "Hello" atakaice duk da bata san waye akan layin ba amma sai ta tsinci zuciyarta da rashin son yin magana alokacin.
Daga cikin wayar taji wata murya da bata san ta tana fa'din _"Baby how are_ u?.
Da 'yar muryarta da haushi yafara cikawa ta furta
_" Fateemah ce !"_ atakaice
_" i know naa, don't_ _worry u ll_ _soon........._
Bata bari ta 'karasa jin mai matar zata fa'da ba tacire wayar akunnanta tare da mi'kawa Anty wayar, afakaice Anty ta doka mata harara batare data bari sub lura ba sannan ta kar6i wayar dan ayanayin response 'din Fateeman Anty ta fahimci ba gaisuwar kirki suka yi ba hakan kuwa sai yasata 'kara jin haushi amma bata bari yanuna akan fuskarta da yanayinta ba sai ta tsare ta daidai ta nutsuwarta atake.
Tana kar6ar wayar ta yanke 'kiran tare da 'ka'kalo murmushi tace " ga dukkan alamu dai amarya tayi uwar 'daki, kinga kuwa yanda ta damu kullum sai ta tambayeki idan ta'kira awaya ,ai dan tayi tafiya ne ma inbahaka ba nasan da yanzu har kun saba ma da ita tun ranar da kuka sau'ka agidannan taji kin manta.................
Teemah baki ta ta 6e lokacin da idanun Anty yabar kanta, aranta tace " _su uwar 'daki manya, shine har da wani cemin baby, ce_ _mata akayi ni inason uwar 'daki ne?, mummy na_ _ma ta isheni nikam_ "
Mahmud kuwa shiru yayi kawai yana nazari dan kuwa yasan wannan uwar dakin bana gaskiya bane, bazai so ya tankawa mahaifiyarsa magana a gaban Teemah bane dan gudun watarana kar kuma yazamana shine da kansa yabada kofar raini ga mahaifiyarsa, inba dan haka ba daya ce baya son wannan ala'kar saboda yasan duk wani abu dazai tunkaro su ta 6angaren Anty toh ba alkhairi bane shiyasa yake tsoro, amma azuciyarsa sai yayi alwashin cewa ze tsaya tsayin daka dan ganin ya ruguza wannan ala'kar tun kafin tayi 'karfi.
'Bangaren Anty
kuwa kar6an su tayi ba yabo ba fallasa suka gaisa, tare da gabatar musu da abinsha agabansu sai dai suna gama gaisuwan ta tashi ta shige ciki tace dasu tana zuwa, zaman kusan 1hr sukayi ba Anty ba labarinta, Mahmud daya gaji sai yace mata ta tashi su wuche be ko sake neman Antyn ba sukayi tafiyarsu dan yasani sarai Anty dagangan tayi musu hakan.
*****
Tun ranar da Abbas yabar garin damaturu bayan 'dauri auren Mahmud be 'kara samun lokacin kansa na kirki ba, harma hakan sai ya zamana kamar taimako ne agareshi da zuciyrsa harma da rayuwarsa dan sam be samu lokacin da zai zauna har yayi tunani akan rayuwarsa da rabuwarsa da Fateema ba sai dai duk da haka 'yar walwalar dayake da ita yanzu babu shi koka'dan, yanayin komai ne ayanda sabuwar rayuwarsa ta zo masa da shi.
Saleema kansa tunda Abbas 'din ya sau'ka a wurin shi be gane kansa ba, kuma sam ya'ki ya bu'di baki yayi masa bayanin meke faruwa dashi, ya dai ce masa daga damaturu yake yaje 'daurin auren sister 'din shi, tun daga nan be 'kara yi masa wani bayani akai ba, dayake Saleem yasan halin kayanshi sai ya 'kyale shi dan yasan matu'kar Abbas be yi niyyan yin magana ba toh babu wanda ya isa yasashi dole, dan haka sai shima yabarsa kawai yaci gaba da abinda ke gabansa, toh dama ma yaya lafiyar kura......
Washe garin ranar daya bar Barrack 44 Kaduna, aranar ko zama beyi ba ogansa ya wakiltashi zuwa wani taro acikin garin porthacourt 'din.
Ranar lahadi ne ka'dai ya 'dan samu ya huta washegari kuwa rakiya yayiwa ogansa zuwa Biu Borno state domin halartar wani taron bu'de wata makaranta acan cikin garin Biu Nigerian Army Institute of Technology & Environmental Studies (NAITES).
Sosai hakan ya'kara taimakon Abbas dan kuwa taron sosai ya me dashi busy man harma sai ya 'dan manta da damuwarsa ya ajiyeta agefe guda ganin cewa saka damuwa aransa ayanzu tamkar yana kashe kansa tabaya ne dan kuwa cutar kansa kawai zaiyi batare da yasami dan taimako ba idan har yace sai ya zauna yayi tunaninta, yarinyar datariga ta tafi ta barshi, bari na har abada toh miye abin 6atawa kansa lokaci shi kuma akanta.
*LAGOS*
Mahmud duk wani 'ko'kari dayasan ze wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna atsakanin sa da matar shi yayi 'ko'karin ganin ya aikata shi duk dama har yanzu beji cewan shima magidanci me iyali bane shi gani yake kamar wata 'kaddara ce tasasu kasancewa atare, amma hakan bai hana yabata dukkan kulawan daya dace ba, ko dan kasancewarta matsayin matar sa da jama'ah da dama suka shaida, sannan kuma 'kanwa ce mafi soyuwa azuciyarsa, abu 'daya ke 'daure masa kai yanda akowani dare sai yanayin Fateema ya canja yakasa fahimtar inda matsalar take tasowa yama rasa gane meke yawo akanta da har yake sata lalu6ansa akowani dare bayanshi hakan kokadan baya gabansa.
Ranar da suka cika 16days da aure aranar anyi ruwan sama sosai kuma duk ruwan akansu ya 'kare dan Fateema duk ranar dataga za'ayi tunkan ruwan ya sakko take fara shirin shiga ruwan , shiri zatayi cikin riga da wando marasa nauwi ko bra bata sawa idan zata yi shirin wasan ruwan sai ta rufe kanta da shower cap.
Da farko Mahmud 'kin barinta yayi amma data rin'ka rokonsa dolensa sai daya amince ya barta, daga baya kuma sai ya fara tayata shiga ruwan, tun daga lokacin be 'kara hanata ba kodan lura da yayi hakan na 'daya daga cikin abubawan dake matu'kar sata farin cikima, sai ma su shirya dukkansu sushiga ruwan sunata juyi suna dariya wataran kuma sukama hannaye suyi ta juyi aruwan suna tsalle-tsalle kamar 'kananan yara.
Mahmud da kansa yafara mamakin kansa dan irin kayan da take sawa su fita wasan ruwan dashi shika'dai ma abin kallo ne, sau da dama yana mamakin kansa yanda yake ganin Fateemah akowani irin yanayi amma be ta6a jin wani sauyi tattare da shi ba, sau da dama yakan tsaya ya ta kallon yanda kayan jikinta suka manne mata suka bayyana dukkan surorin jikinta sanadiyyar ruwan saman da ya ji'ka su, awannan lokacin kowani irin 'da namiji yaganta sai yaji wani abu aransa da jikinsa koda kuwa ya yake amma ga mamakinsa shi be ta6a jin wani canji ajinkinsa game da hakan ba, da farko abin baya damunsa dan ya 'dauka ko rashin 'daukar auren nasu amatsayin aure ne yakawo hakan amma daga baya abin sai ya fara damunsa, shikansa yaji yana so yaji wani sauyi tattare da shi amma sam yarasa dalilin hakan, tsakaninsa da ita sai de kallo da ido and nothing more.
Exactly that day kamar yanda Fateemah tasaba yi masa hakan tayi, zuwa yanzun ma yafara sabawa da yanayin nata ya fahimci kawai hakan take bawai rigima bane kawai ko wani abu daban, saboda tun ranar data fara yi masa irin wannan 'din dai-dai da rana 'daya bata ta6a fashi ba akullum sai ta lalu6e shi, tun baya kulata har ya fara taimaka mata, wasu lokutan yakanyi romancing 'dinta duk dan yataimaka wa yanayin nata dake ciki bawai dan yana jin da'din hakan ba, cikin sa'a kuwa sai yaga bacci ya 'dauketa bayan hakan wataran kuwa idan abin yafaskara baya sanin lokacin dayake fara jero mata addu'o'i ma da ikon Allah kuwa sai yaga tayi la'kwas tayi bacci tare da jero ajiyar zuviya acikin baccin.
Idan darana ne kuma kamar ba ita ba sam bazama kace ita ce ke neman sa arikice da dare ba.
Na yau 'din kam yasha bam-bam dana kullum, dan kukanta ne yatashe shi abacci, kukan take sosai tana danne cikinta tare da takura kanta guri 'daya tana shiga jikinsa, koda ya nemi yi mata kamar yanda yasaba 'din sai ta nuna masa alamun bahaka take so ba ita.
Rasa yanda zaiyi da ita yayi gashi sosai take bashi tausayi, mamakin kansa sai ya hana shi taimaka mata illah tsayuwa dayayi saroro yana kallonta, so yake ya lalu6o dalilin amma yarasa dan ayanda yasani da ba haka yake ba, be san me ya maida shi mara anfami yanzu ba, gashi yanzu taimakonsa ka'dai Fateemah take nema awannan yanayin while shikuma badama.
Dayaga kukan data keyi yana so yayi yawa sai ya koma yajawota jikinsa ya rungumeta da 'kyar, tausayinta ya da'da karya masa zuciya ganin da kanta take neman raba jikinta da kayan baccin data ke sanye dashi, zafi rau yaji jikintan kamar wacce take tsaka da zazza6i, hawayene yaji ya gangaro masa sai ya lumshe idanu ahankali yafurta
_" ki yafe min Fateemah, bansan haka ne zaizo yafaru dani ba_ _kamar yanda bansan haka yanayin ki yake ba tun farko, wallahi_ _dana san haka ne da bazan amince da auran ki ba ko dan gudun kar nashiga hakkin_ _ki, da ha'kuri zan bawa Abbah na da Daddy akan afasa 'daura mana aure, amma nasan 'kaddara ce ta ha'da auren mu kuma ni ban isa na dakatar da ita zuwa garemu ba, ki yafe min kinji......_ _ki yafe min Fateemah insha Allahu zan nema miki mafita.........."_
_Comment vote and_ _share pls_ π€π»
*Salmerh ce*π
[10/2, 6:02 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ π
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
_A rumor goes in one ear and out of many mouths._
π
Ώ *56*
Washe gari Mahmud asibiti ya je aka duba shi aka bashi magani hadda allurai daga nan sai ya wuce office 'dinsu amma ko 2hrs mai kyau beyi ba awurin yadawo gida kafin haka kuwa yayita 'kiranta yafi sau biyar yanajin ya take.
Yana komawa gidan kuwa Fateemah tafara yi masa rigima akan wai dole sai sunje sun yi wasan basket ball dashi, Mahmud duk da yana cikin damuwa amma haka ya daure ransa ya amince mata suka fita wurin wasan dan kawai ya faranta mata, daya ke akwai wurin yi 'din acikin gidan nasu daga 'dan nesa ka'dan da bakin get, wurin 'dan daidai ne bawani babba ba musamman aka tsara shi saboda masu gidan.
Bomshort ne ajikin Teemah wanda yakama jikinta sosai sai wata 'yar 6ingilar ba'kar riga da bata ko rufe cibiyanta ba kanta kuwa wani bakin shararan hula ne da aka sa'ka shi da zaren lilo, ba 'karamin kyau tayi acikin shirin nata ba, Mahmud kansa gani yayi tayi masa kyau sosai ba 'karamin birgeshi tayi ahakan ba, yakan juyo ya kalleta lokaci zuwa lokaci dan yasan iya abinda Allah yabashi iko kenan akanta tunda ga halin daya tsinci kansa aciki, duk dama yana saka ran samun sau'ki akowani lokaci tunda likita yayi masa bayani mai kyau kuma ya gamsu, ya sa hope 'din sa akan magungunan da aka bashi tare da taimakon Allah da kuma izninsa zai sami sau'ki.
Isar su filin keda wuya suka fara buga wasa, Fateemah daman bawani iyawa tayi ba tsabar rigima ce, garin shige shigen ta acikin gidan ne idonta yaci karo da wurin wasan shine fah ta dage sai anyi, 3:0 Mahmud yamata tana ganin haka kuwa tafara tsalle tana fa'din a'a bata yadda ba gaskiya wai itama yajefa mata ko sau 'daya tunda ita ta kasa.
Dariya ma abin yabashi, yakuwa dara, acikin dariyar yace " _a ina kika ta6a ganin anyi haka, nine kuma zan jefa miki?_ _Hhhhh_ ya 'karasa maganar tasa da dariya." _U ar so funny Fateema "_ tare da nunata da yatsa.
Baki ta turo tayi fushi har zata juya yasa hannu ya cafko hannunta 'daya yace mata " toh shikenan amma sau 'daya zai jefa mata tana jin haka tace ehh ta amince.
Jefawan yayi da sunan nata ne, ai kuwa take tafara tsalle da murnan taci 'daya, da ya 'kara yi kuma take sai yabata 4:1 daga nan kuma tace ya 'dagata itama tasaka da kanta, yazaro idanu tare da fa'din _" kai....... ke 'katuwan nan ne zan 'daga ?_ Yafa'da da sigar zolaya, _"gaskiya kina cutata haka ake wasan ne?_
Bubbuga 'kafafu tafara yi a'kasa cikin shagwa6a tace _" ni de sai ka 'daga ni bayan sai shana kake yi kawai dan ka ga ka fini tsawo, ai da yah Abbas na nan nasan da zai tayani nima"_
Kwa6a fuska tayi kamar zatayi kuka ganin haka sai yace toh tazo ya'daga ta, tana jefawa tasake sakin murna tana dariya kamar wanda yin kanta ne bada taimakonsa ba, tsalle take tana fa'din " _yeehhhh naci_ _biyu"._
Shima sai ya yatsaya kallon ta yana dariya yace.
_" kinmanta 4:2 muke, ratar biyu fah nabaki"!_
_"Ehh ai biyu ne kacal kuma nima yanzu zan taro ka"_
Tana fa'din haka sai taci gaba da murnarta abinta.
Horn sukaji an danno daga waje, mai gadi yaje da gudu yale'ka sannan yadawo ya tura gate 'din batare da yayi magana ba dan ganin wanda ke cikin motar.
Teemah kam jin horn 'din koka'dan be dakatar da ita daga murnar data keyi ba dan bata ko damu da waye yazo acikin motar ba.
Mahmud kuwa bin motar yayi da kallo ganin dayayi cewa motar ta gidan sune ta shigo sai dai bai gane wacce ke cikin motar ba dan sun 'dan yi nesa dasu ka'dan, motar na tsayawa su Anty suka fito atare ita da 'kawarta daga cikin motar idanunsu gaba 'daya nakan su Teemah, dan tun shigowansu suka hango su a filin wasan.
Wani tuku'kin takaici ne yacika zuciyar Anty ganin cewa wai har lokacin yin wasa suka ke6e acikin gidan domin kawai su sha'kata, lalle nayi sake, shirun nawa yayi yawa, shiyasa har yarinyar dana so na wargaza auren ta tun ranar farko tasami saken da har zata buga basket ball agidan da na tsani ganinta aciki har ma da 'dana 'daya tilo dana mallaka aduniyan nan kuma na tsani ganinsu atare.
Zagayawa tayi da sauri 'daya 6angaren da 'kawarta take tsaye dan ita tun fitowanta daga motar bata 'kara ko motsin kirki ba awajen, ta tsaya saroro tana kallon Teemah kamar zata cinyeta 'danya.
Dafa kafa'dar ta Anty tayi sai ta juya da hanzari, akufule Anty tafara magana
" _kin gani ko, kinga abinda nake ta faman gaya miki amma kika 'ki_ _taimakona saboda wani dalili bayan kinsan sai da kene nasara take zuwar min, yanzu gashi_ _shirun danayi na zuba ido yasa har sha'kuwar su tayi nisa, dubesu kiga........"_
Ta 'karashe da nuna su.
" _Come down mana mum Mamud,_ _everything ll be alright since am here komai zai zo da sau'ki in dai har kika goya min baya_ _zan taimake ki kirabasu kamar yanda kike so amma sai kin tayani cika_ _*BURINAH* "_
Kallon Anty Chideh kawai Anty keyi dan koka'dan bata fahimci manufarta ba, karta ce har yanzu tana kan bakanta na wancen maganar ne, in de kuwa har hakane toh sai de kowa ya ha'kura da 'kudirinsa dan bazata iya aikata wancan aikin ba da girmanta ba yarinya , infact tunda ma har ta iya bari akayi auren akan ta'ki amince mata toh kuwa bayan auren bataga dalilin da zai sata ta aikata ba.
Anty Chideh kuwa murmushi tayi ganin Anty ta tsaya shiru tana tunani, tasan cewa maganar su nabaya take tunawa dan haka sai ta dago hannu tashafi fuskar Anty ,baya Anty taja da sauri, Anty Chideh kuwa sai ta sake murmusawa tare da fa'di.
" _feel free mum Mamud this time around daughter in-lawn ki nakeso not_ _u, tunda ke kin'ki bani ha'din kai na ha'kura dan nasan bazaki amince ba, amma yanzu kam matu'kar kika tayani fighting_ _nasameta toh na miki al'kawarin raba auren nan rabuwa_ _na har abada, zan kaiki duk inda kike so kika kuma za6a_ _dan kawai ki cika naki burin._ "
Sosai maganar Antyn Chideh ya suprising Anty, bata ta6a zaton iskancin nata har zai koma kan 'yar cikinta ba, no wonder shiyasa tun ranar da aka kawo yarinyar ta yabeta dan ma tayi wata 'yar tafiya ne inbahaka ba tasan da tunda wuri tagama ya'da manufarta, tunowa tayi lokacin da Anty Chidehn bata nan kullum sai ta 'kirata awaya takuma tambayi lafiyar amarya ashe akwai 'kunshin abu aranta, harma ranar tace abawa Fateeman waya dan kawai taji cewa sunzo suna kusa, amma Anty bata wani damu ba jin cewa abin ya bar kanta ya koma kan makiyarta ai ita hakan yafi komai yi mata da'di tunda kuwa hakane dole in goya mata baya.
Daga nan ta tabbatarwa Anty Chidehn cewa duk yadda take so haka za'ayi dai dai nan Mahmud ya iso wurin da suke tsayen cikin ya'ke yace " _ahh barkanku da zuwa Anty ya kuka tsaya anan kuma?, mu_ _'karasa daga ciki pls"!_ ya 'karasa maganar tare da juyawa.
Anty batayi magana ba illah kallon bayanshi datake yi sai kuma bata ga Teemahn ba.
Kasa ha'kuri tayi sai da ta tambaya inda tace " _ina amaryar taka kuma Mahmud batare_ _naganku bane_ _'dazu",_ kai Mahmud ya sosa tare da fa'din _" ta_ _wuche ciki yanzu?_
Sababi Anty ta fara akan wai " _tsabar ta raina ta ne shiyasa tana ganinta ta wani yi wucewarta_ _inbahaka ba me yasa bazata zo ta tar6eta anan 'din ba kamar yanda Mahmud 'din yayi, kodan tana ganin ba nice na haifeta ba, na tabbata da Khadija tagani anan da sai ta riga ka ma zuwa inda isowa"._
Mahmud be yi magana ba da be san me zai ce da Antyn tasa ba, toh yace mata kunyar kayan jikinta yasa tayi 'dakin ko kuwa yace mata tatafi suturta jikinta ne.
Murmushi ne ya kubce masa daya tuna lokacin da zai taho inda su Anty suke Teemah ma fara biyo shi tayi ahakan dan ko damuwa batayi da kayan da yake jikinta ba kota manta ne oho, sai da yace " _kiyi sauri ki wuce ciki ki saka gown akai kar su ganki ahaka ko bakya jin kunya ne_ _su ganki ahakan.......?_
Yana fa'din haka ta juya da gudu ta koma ciki, may be lokacin data wuche 'din hankalin su Anty baya kansu shiyasa ma basu lura ba.
Anty Chideh ce tace da Anty tayi shiru mana bata son yawan fa'da bayan tasan cewa yanzu Teemahn propertyn tace, tace mata kayan jikinta 'kanana ne may be tana jin kunyane shi yasa bata zo nan 'din ba.
'Kasa-'kasa tayi maganar yanda Anty ka'daice zatajita.
Duk da Anty Chideh cikakkiyar bayerabiya ce amma yawacen yawacen data tayi a wurare da dama yasa tasan dayawa daga cikin al'adun hausawa shiyasa tayi saurin kare Teemah da wancen maganar.
Anty kuwa ta6e baki tayi, 'kasa-'kasa tace _" iskancin banza da 'din me yasa ta saka kayan tunda tasan tana jin_ _kunya aganta dasu"_
Mahmud ne agaba lokacin da suka shiga cikin parlourn, bayansa Anty ce sai Anty Chideh daga 'karshe, a'kofa ma suka ha'du da Teemah tana 'ko'karin fita ganin su yasa ta basu hanya suka shishshigo, hijab tasako babba akan doguwar rigar data saka 'din sosai tayi kyau acikin hijab 'din dan ya 'kara fito mata da hasken ta da kuma 'dan madaidaicin fuskarta tayi 'das aciki.
Abinsha tawuce ta 'dauko musu sannan ta zo ta zauna ta gaidasu Anty Chideh ce kawai ta amsa da fara'ah tana wani kallon cikin idanun Teemah, Anty kuwa ayatsine ta amsa mata, bata wani damu da yanayin da Anty ta amsa gaisuwar ba, illah kallon da Anty Chideh ke binta dashi ne ya 'dan so ya 'daure mata kai dan haka sai tayi 'kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta.
Tashi Mahmud yayi ya shiga ciki da niyyar saka ko jallabiya ma akan wandon three quatern dake jikinsa, da wannan lokacin Anty tayi anfami tayiwa Teemah bayanin wacece Anty Chideh awurin ta, tace saboda watarana ko bani zata iya zuwa duba ki ita 'daya ina so ki san cewa matsayina danata tamkar guda ne awajenki karki kuskura ki yi mata badai dai ba, kinji ko baki jiba, da _" Naji "_ Teemah ta amsa mata ahankali.
Mahmud na sako rigar ya fito yadawo parlourn.
Su Antyn ma basu wani da'de ba dan ko 10mins basu yi ba suka ce zasu tafi dama Anty Chideh ce ta matsa sai sun zo wai tanaso taga daughter in-law 'din nasu ne, Anty bata so zuwan ba dan haka tace bari kawai ta 'kirasu suzo sai Anty Chideh ta'ki amincewa da hakan, dolen ta ta shirya suka taho, alokacin ma Anty bata san meke ran Anty Chideh ba sai bayan isowarsu ne da ta mata bayani.
Har gurin mota su Mahmud suka musu rakiya, Teemah nata ra6ewa ajikin Mahmud dan avoiding ha'da idanu da Anty Chideh datakeyi, Mahmud kansa ya lura da haka amma ya basar dan be san dalilinta na yawan kallon Teemahn ba, sam ta tatsani ganin matar ita, ganin cewa 'katuwar babbar mace da ita amma tana mata abu kamar mara hankali ,inbahaka ba miye abin yawan kallo awurina, sai kace bata ta6a kallon mutum kamar ni ba".
Acikin ranta taketa wannan masifar, azahiri kuwa kanta na gefe bata ma kallon inda suke.
Sai da suka ja motar sannan ta sau'ke ajiyan zuciya tare da dokawa bayan motar harara, ta kalli Mahmud sai suka ha'da idanu take sai yayi sama da girarsa, ga dukkan alamu yaga abinda tayiwa bayan motar su Antyn, da sauri tace _" wallahi Yayah banason matar nan ni koka'dan"_ hannunta yakamo suka fara tafiya sannan anutse yace
_" wacce daga ciki?_
_"Wannan inyamuran matar mana, sai ta ta wani kallona tana smiling bayan ni banma_ _santa ba, ban ta6a ganin ta ba ma ni, haushi tabani sosai yau 'din nan"!_
Murmushi yayi sannan yace mata " _'kawar sirikar ki ce kinga kuwa dole ki_ _sota ai "_
_" ehh ai Anty ta fa'da min 'dazu."_
da wannan hirara suka koma parlour suka zuzzube , Teemah na shiga ta fincike hijab 'din tare da rigar data saka wai zafi yadameta, dama garin sauri ko na cikin bata tsaya ta cire ba ta 'dora doguwar rigar akai.
*****
Mahmud har 10:00pm ya kai a parlour yana kallon News a NTA, yayinda Teemah tayi kwanciyarta tai bacci dan dama ita ba gwanar zama tayi kallo bace, sam kallo be dameta ba arayuwarta.
10pm cif Mahmud yatashi tare da kakkashe switch 'din sannan ya shige ciki,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 67