Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
masa 'kiran Anty (Maryam), koda tazo kuwa mamaki tayi da ganin Abbah ita kam, domin bata ta6a zaton zuwansa adai-dai wannan lokacin ba. Sai ma taga ya 'dan murmure yanzun ba kamar da ba, fuskarsa se wani 6oyayyan annuri ke haskawa. Alhaji Muhammad ne ya nemi jin abinda ya faru daga bakinta karo.na biyu, sanin da Anty tayi cewa yariga yasan komai yasa bata bata 6oye masa ba ta kwashe duk abinda ta aikata da dalilin da Abban Mahmud ke fushi da ita duk ta sanar dashi. Alhaji Muhammad beyi mamaki ba dan yariga yaji duk abubuwan da yafaru 'din tun a Lagos sai de be san cewa hakan.ne ya kawo sa6ani tsakanin su ba, duk da kuwa cewa yasan ba kowa ne ne zai juri faruwar hakan ba, ko shi kanshi idan hakan yafaru cikin iyalinsa yasan da 'kyar ya iya sake zama da me shi shiyasa sam be ga laifin Abbah ba ko ka'dan sai ma ya jinjina masa da be aikata fiye da wannan ba, sake tambayar Abbah yayi inda ya tambayan ne kawai dan tabbatar wa. Nasiha dukkan su ya ha'da su yayi musu game da zamanta kewar su, sosai yaja hankalinsu game da tsoron Allah cikin al'amuransu, sai da ya gama nasihar kafin ya baiwa Abbah dama yace yana da ikon za6an duk abinda yaga yayi masa wanda ya dace dashi, yace " _karka damu dani Yusuf, ni tamkar mahaifinka nake bazan takuraka akan komai ba, sannan ina so_ _kayiwa kanka adalci karka dube ni kowani abu daya shafeni, Maryam matar kace,_ _kuma_ _kai ke da ikon za6an sake zama da ita ko kuma akasin haka, duk ra'ayinka_ _ne_ _Yusuf_ , _bazan ta6a tilas ta ka dan ka zauna da ita ba dan tana matsayin 'yah agareni, wallahi_ _Yusuf da ace ni ni ke da iko da kai da bazan ta6a barinka kasake zama da Maryam a matsayin_ _mata ba, kuma ko yanzun ma kana da damar za6a ni nawa_ _shawara ne koma me ka aikata ni.kam.ina maraba dashi Yusuf domin kuwa nasan kai 'din'dan halak ne me matu'kar ha'kuri sosai wanda ina zaton da iznin Allah rayuwarka bazata ta6a birkicewa ba Insha Allahu_ ". Tuntuni Anty take zubda hawaye tana 'karawa tasan koma me ya faru duk laifinta ne, laifinta ne da ta saka.son.zuciya ya rinjayi duk kan al'amuranta, yau gashi mahaifinta da kansa yake bada shawarar kar azauna da ita. Godiya Abbah yayi masa sannan ya sanar dashi cewa shi bashi da burin 'kuntata mata koka'dan kuma.duk abinda zaiyi zaiyi shi ne dan gyara duk wata 6araka da ke tsakaninsu, yace ha'kika Maryanlm.ta 6ata raina ta shammace ni alokacin da banyi zaton faruwar hakan ba, Maryam ta ninke ni a baibai da sunan ta kar6i maganar auren Mahmud bansani ba ashe mugun sa'ka tayi a6oye wanda warwareshi ke da matu'kar wahala, ban ta6a zaton Maryam zata aikata haka ga 'dan cikinta ba, wanda ya kamata ace ta so shi fiye da komai arayuwarta, amma kash! Mahmud be yi dacen samun hakan ba sa6anin haka sai ma ya rasa rayuwarsa. Bayan jin hakan na tsani Maryam irin.tsanar da banta 6a zaton zan mata shi ba, naso in hukunta ta ta yadda bazata ta6a ma tunanin sake aikata wani abu makamanciyar wannan ba, sai de banyi hakan ba saboda ganin girma da kake dashi Alhaji a idanu na, bayaga haka ma Fateemah sai ta nutsar dani muhimmancin yafiya da falalar ta, kuma na gamsu sosai sanadin hakan na yafi Maryam azuciyata sai de bakina nawi yamin in furta mata haka nabari har se naga nadama ya ratsata tukunna. Cikin hakan Allah ya nufe ni da neman aure kuma nasamu Alhaji zancen ana danake maka ayanzu kwanaki goma ne suka rage a 'daura aure " Fuskar Alhaji tuni ya cika da murmushi ya ringa sanya masa albarka tare da fatan alkhairi yace yayi matu'kar farin ciki da faruwar hakan kuma yana bayansa 'dari bisa 'dari. Anty kam hawaye masu zafi ne suka zubo mata wanda tun rasuwar Mahmud basu fasa zuba ba, sai de na yau yasha bambam dana kullum, akowani 'digon hawayen ta nadama ke lullu6e ta tare da wanke duk munanan halayenta dake zuciyarta, yanzu kuwa kukanta na godiya ga mahalicci ne da Abbah ya furta mata yafiya, ta tsani kishiya abaya amma yanzu kam ji take matu'kar ze yadda ya amince ya sake zama da ita toh a shirye take ta zauna da kishiyoyi uku ma ba 'daya ba. Komai faru laifin tane, Abbah be ta6a yi mata maganar kishiya ba tunda suke dashi sai yau 'din, yanzu kuwa da duk abubuwa suka yimata yawa ina ita ina 'daga hankali dan zeyi aure, tace Allah ubangiji ya ha'de kawunan mu ya sa hakan shine mafi alkhairi. ***** Abbas tunda ya tafi kusan 3weeks kenan har yanzu be dawo ba, kullum sai dai su gaisa dashi awaya sai ya ta cewa ayyuaka ne suka yi masa shiyasa be le'ko gidan ba, Ummah bata damuwa dan tasan yanayin aikinsa dama fiye da hakan ma zai iya faruwa shiyasa kullum da addu'ar nasara da kariya kawai take binsa. Daddynsa kam ko ajikinsa, sarai yasan matsalar Abbas 'din gudun ha'duwarsu yakeyi saboda batun aure shiyasa ya'kizuwa Abuja shikuwa babu fashi lokacin daya 'dibe masa na cika zaiga abin mamaki dan kuwa ba ze fasa ba. Ranar da Teemah ta gama watannin takabarta ranar har se da tayi mamaki dan yanda Ummah ta fitar da ita tsab, sai dama ta ha'da ta driver suka je saloon suka dawo sannan tabata wasu ha'da'd'dun gown 'yan italy matsu kyau da tsada sai alokacin ne Teemah take jin labari ashe wai Mummy ce ta aiko musu dashi tun zuwan Abbas kwanaki shine Ummah ta 6oye su sai yau ta fitar ta bata nata na Hannah kuma tace sai ta dawo zata ksr6i nata. Data shirya tafito kuwa ita kanta tasan tayi kyau har jin kanta takeyi, ji take yi kamar wata dabance ba Fateemah ba, for about 4months da wasu kwanaki tana ta fama da atampopi yau kam wani iska takeji yana shiganta me da'din gaske, tun ba ma da Ummah ta bata wasu turaruka masu kyau tace nata bane, take ta rungume Ummahn tana dariya tare da godiya. Haka taringa fesawa ajikinta tana 'karawa har se da 'kamshin ya 'dan fara yimata yawa kafin ta sarara. Jin kanta yau 'din takeyi tamkar wata sarauniya gaba 'daya ta dawo daban. 'Daki ta koma ta ringa kashe selfie kala-kala wasu abin dariya wasu kuma abin birgewa ita adole tana farin ciki yau tasamu freedom afa'darta. Ummah da kanta tace idan Hannah ta dawo da wuri ko da da yamma ne sai sunje shopping musamman kawai saboda Teemah. Ai kuwa Teemah taringa 'kiran layin Hannah amma baya shiga kusan 5 missed calls ta mata, data ga bata 'daga ba sai ta tura mata text " _Hii bae, pls ki dawo da wuri today is my day, Ummah tace zamu_ _fita_ " Hannah na can tana rubuta test dan haka bata ma bi takan wayarta ba sai da tagama rubuta test 'din tafito sannan ta ga missed calls 'din Teemah tare da text 'din da tayi mata, ai kuwa tana gani ta hau murnan yau zasu fita da 'yar uwarta , bata 'kara bi takan sauran lectures 'din da zata yi ba batare da jiran komai ba ta kamo hanya ta dawo gida. Tana zuwa suka rungume juna suna murna, Hannah da kanta itama sai da taga canjawar Teemah har ta kasa daurewa sai da ta tambaye ta aka wai yaushe kuma har tayi saloon batare da tasani ba? Murmushi Teemah takeyi ta bata amsa da fa'din " _yau da safe naje nayi lokacin already kina school ai shiyasa_ . 'Bata rai Hannah tay tace " _shine kuma kika 'ki jirana muje tare ba, duk laifin Ummah ne_ _ai da ta gaya min da wuri_ _da sai in fasa makarantar mutafi amma shine aka 'kyaleni harna tafi_ " Teemah tana kan haska selfie tace " _yanzu kam ai ya wuce ki, yi sauri ki shirya muje yawo yarinya yau zanga gari yarinya, kayanki ma na gurin Ummah, ke ko irin kice nayi kyau 'din nan ma baki fa'da ba kintsaya surutu_ " Tashi Hannah tayi taje wurin Ummah ta amsa kayanta tare da shigar da complain 'din bata je saloon ba ita. Ummah lalla6ata tayi har zancen ya wuce sannan ta wuce 'daki domin watsa ruwa. Abbas kam be dawo Abuja ba har sai da ya cika sati hu'du cif-cif kafinnan, ranar daya dawo 'din kuma sai yayi dai-dai da ranar da Teemah ta gama takabanta. Bayan shigan Hannah wanka ne Teemah ta 'kira Anty tana 'dauka tace " _Anty albishirin ki_ ? " _Goro fari 'kal-'kal_ " Anty tabata amsa tana murmushi. " _Anty yau zan fita_ _yawo nida___ _Hannah...._ " _Kai dan allah kice_ _yau sabuwar_ _rayuwa_ ' _yata zata fara_ " Labari Teemah ta bata na irin kayan da ta saka da sauransu. Daga 'karshe Anty tace mata itama insha Allahu gobe tana hanya zata zo Abujan, Teemah murna kamar tafasa wayar da ihu, sai da Anty ta kauda wayar akunnanta tana murmushi da gode wa Allah ga dukkan baiwarsa. Tana gama wa da Anty ta 'kira layin Mummyn ta. Mummyn ma tace ai tana ta 'kiran layinsu be tafiya tun jiya har na Ummah ma, tace Teemah ta ha'da ta da Ummahn pls. Fita tayi dan kaiwa Ummah wayar inda ahanyan ne take bawa Mummy labari akan yau zata fita yawo ita da Hannah tace Mummy kinga kayan da kika aiko manan nan kuwa yanda yamin kyau dan Allah Mummy ki 'kara siya min wani, idan nazo kawai in samu, zan ro'ki daddy ai yabar ni inzo. Mummy cewa tayi " _Nima zanzo ai insha Allahu gobe ko jibi_ " Wani tsalle da ihun da Teemah ta buga da jin furucin Mummy tare da gwalo idanun ta yasa Abbas dakatawa daga tafiyar dayakeyi ya tsaya kallonta. " _Dan Allah Mummy_ _dagaske_ _zaki zo_ ? Ta tambaya da murna kamar zata fasa wayar ta ganta agaban Mummy. Mummyn ma cewa tayi " _zanzo mana Teemah ina miki 'karyane_ ! Tsalle ta buga tace Anty ma zata zo tace min Mummy, dan Allah karku fasa kinji....... Maganar tata yankewa yayi jin an fizgo wayan daga kunnanta daga bayanta, juyi tayi da 'karfi zaton ta ma Hannah ce harta gama shiri ta fito hakan yasa ta fara furta " _banason iskanci_ _Hannah da_ _mum...._ ganinshi tsaye tayi yana kallonta, baki ta rufe da hannunta tare da zaro idanu waje. Wani kyau da kwarjini taga yayi mata, muryarta na rawa tace " _sannu_ _da zuwa Yayah_ " Kallonta yayi kawai batare da ya amsa mata ba, sai ma yace mata " _welcome back Nana_ _parrots_ ! _Ke ihun naki be_ _damunki ne_ , _ke 'daya amma kinbi kin cika gida da hayaniya kamar kasuwa_ ? Anutse yayi mata maganar bada masifa ba ita kanta tayi mamakinsa yau 'din. Amma duk da haka sai tayi shiru tai 'kasa da kanta batare da ta furta komai ba. Dayaga bata da niyyan yin magana sai ya huya kansa tare da fa'din " _Any ways, i heard u said zaki yawo ko?, har zuwa ina kenan haka_ ? " _Shopping zamu_" Ta bashi amsa atakaice. Sake tambayarta yayi " _ke da waye_ ? Tace da " _Hannah_ " " _inji wa_ ? 'Dago idanu tayi ta kalleshi jin yanata jero mata tamabayoyi kamar wani 'dan jarida, da suka ha'da idanu sai ya 'dage nashi idanun zuwa sama. Ta fahimci manufarsa dan haka sai tace " _inji Ummah_ ! Tana fa'din haka tafara ro'kon Allah azuciyarta akan Allah yasa kar ya hanasu fita tasan ka'dan ga aikin sa ne yace bazasu ko'ina ba, ita kuwa tana jin da ya hanata fitan nan gara yayi mata komai ma amma banda shi. Cikin haka wayan ta dake hannunsa yafara ringing 'dagowa yayi sai yaga Mummy ce ta'kira, yana ganin haka sai ya mi'ka mata wayar yana kallon cikin idanunta. Ahankali tasa hannu ta kar6a tare da sada ta da kunnenta tace " _hello, Mummy_ ! " _Ah ah ban kai ba tukunna bari nayi sauri inkai mata_ " Iyah abinda yaji ta fa'da kenan. Tana fa'din haka ta yanke 'kiran tare da juyawa da niyyar tafiya. Muryarshi tajiyo yana fa'din " _In kin kai mata wayan ki kawo min ruwan sha_ " Shima yana gama fa'din haka ya juya yafara tafiya, Teemah kam bayansa ta tsaya tana kallo tana kwa6a baki, mutun kullun kamar ghost be ta6a yin dariya. 'Dan 'karamin tsaki taja da ta tuna cewa duk da hakan da yakeyi bata san meyasa lokuta da dama takanji son ganisa ba duk da kuwa bawani abin kirki ke ha'da su ba amma zuciyarta na yawan janta zuwa tunaninsa ko son ganinsa. Kamar yanda yace 'din kuwa tana kaiwan wayan ta taho domin kawo masa ruwan tasa meshi tsaye yawani zuba hannaye acikin aljihun army green 'din wandon dake jikinsa. Ita kanta da ta shigo tayi mamakin yanda 'dakin yayi 'kura ko dan an kwana biyu ba ayi amfani dashi bane oho. Tana shirin fita daga 'dakin ya dakatar da ita da fa'din " _Zo ki kintsa min 'dakin nan_ _please_ " Waro idanu tayi waje idanunta har ya fara tara hawaye bata san ma lokacin da bakinta ya furta " _Yayah yanzu fah zamu fita mun gama shiryawa_ ! Gira ya 'dage zuwa sama yace " _So_ ? _Come on zo ki kintsa min 'daki, kwaje shopping 'din gobe in Allah ya kaimu_ " _Comment_ _Vote_ _Share_ (Ga duk me son farkon *CAPTAIN* *ABBAS* har zuwa inda aka tsaya should follow me a shafina wattpad @ *Serlmerh-md* *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~Dedicated 2 my family~ *Bismillahir rahmanir raheem* _*3 C’s of LIFE* : Choice, Chance & Change – You must make a choice to take a chance or your life will never change._ πŸ…Ώ *72* 'Bangaren Hannah kuwa harta gama shirinta tafito bata ga Hannah ba sai ta yi gurin Ummah dan ganin ko tana can ne, amma kuma sai ta tarar da Ummah zaune ita ka'dai, tambayar Ummahn tayi tace " _Ummah ina Teemah fa ko de tagaji da jirana ta wuce abinta dan naga_ _yau zumu'di_ _takeji_ _dashi_ " Murmushi Ummah tayi tace kafin ma ta rufe bakinta sai Ummah tace mata " _Ta kaiwa Yayanku abin sha ne bari ta dawo_ " " _Yayah ya zo ne dama Ummah_ ? Hannah ta tambaya lokacin tana shirin zama agefen Ummah. Amsa ta bata da fa'din " _ehh be ma da'de da isowa ba yanzun nan ya shiga ciki, kije mana ku gaisa_ ". 'Dan 'karamin tsaki Hannah tayi tace " _barshi Ummah sai mun dawo kawai naje kafin nan ma kinga ai ya 'dan huta_ " 'Dan hira suka 'dan fara ta6awa da Ummahn kafin Teemah tazo, anan ne Ummah ke sanar da Hannah batun zuwan Mummy harma da Anty da Teemah tafa'da mata. Hannah tayi murna sosai har zuciyarta da jin cewa Mummy zata zo saboda ita kam tana son Mummy ko dan goya mata baya ma datake yi akan komai sa6anin na Anty data kya6e baki tace " _Allah ya kwaota lafiya_ " Teemah kuwa nacan tana aiki tana share hawaye, haushi gaba 'daya ya bi yacikata shima Abbas yana tsaye har yanzu be motsa ba har ta shiga tagama kintsa bedroom 'din ta wanke bathroom ta fito yana nan tsaye ,tasan cewa zefi fara bu'katan can 'din kafin parlour shiyasa tafara gyara cikin. Tana aikin takaici fal zuciyanta tarasa meke damunsa shi akullum yafi son yaga ya 'kuntatawa mutun in bahaka mi ye ruwansa da fitan su harda zai ce wani bazasu fita yau ba sai gobe, salon yanuna halinsa afili kawai, bayan gobe Mummy da Anty zasu zo shine kuma zata fita yawo? tama rasa me ya dawo dashi wallahi, mutum sai fitinan tsiya. Yana nan tsaye, yana tunanin yanda yaga yau duk ta canja tayi wani kyau na musamman da ita, duk da yake dama ita 'din me kyau ce amma na yau 'din na musamman ne, sai de har yanzu tana nan arame bata mai da jikinta nabaya ba. Hawayen da yaga take ta sharewa ne ya 'dan 'dauki hankalin sa sai ya fara bin duk wani moves 'dinta da idanu, gani yayi da gaske kuka takeyi da hawaye, alokacin ma barta kammala shara ta goge ko'ina saura goge center table 'din dake tsakiyan parlourn ne ka'dai yarage take kan yi, sai ya taka ahankali ya isa inda take. Hannunta ya kama ya mi'kar da ita tsaye sai kuma ya tsaya yana 'karewa cikin idanun nata kallo, 'kasa tayi da nata idanun jin gaba 'daya sun mata rauni, sam yanzu bata iya juran kallon tsakiyar idanunsa, intayi hakan kuwa jikinta har rawa yake 'dauka gaba 'daya, Yayah Abbas kwarjini yake yi mata sosai. Ko yanzun ma 'kasa tayi da nata idanun hawayenta na sake gangarowa ahankali. Da yatsan sa 'daya ya shafo hawayen nata sai ya sake nuna mata a saitin idanun ta wanda dolenta ta 'dago ta kalli yatsan daga nan ta 'dan kalle shi ka'dan, suna ha'da idanu sai shi ya sake bu'de nashi tare da 'dage gira sama da sauri tayi 'kasa da kanta ahankali yace " _dan nasaki aiki kike yin kuka_ ? Kai ta jijjiga masa alamar " _ah' ah_ " " _Toh menene_ ? Ya sake tambayarta. " _bakomai_ " Teemah ta bashi amsa ahankali. " _Ohh dan na hana fita yawo ne ko_ ...? Kafin ma ya rufe ba kinsa cikin shagwa6a66iyar siririyar muryarta ta tare shi da fa'din " _Na da'de fah Yayah banje ko'ina ba, kuma kullun ina son siyan abu_ _amma bana fita ko'ina, sai yau Ummah tace zamu ni da_ _Hannah...kuma...kuma_ ... Sai ta 'karashe da in-inah ta kasa 'karasawa illah sabon hawaye hawaye daya gangaro . Abbas ne ya 'karasa mata da fa'din " _Kuma sai na hana_ _ko_ ? Shiru tayi masa bata tanka ba, sai ta sake kwa6a fuska kawai. Abu 'daya ke sanyaya ranta idan ta tuna zata ga Mummynta shiyasa ma take 'danjin dama-dama. Abbas kam tsayawa yayi yana kallonta yarintarta na birge shi, komai nata ma shi birgeshi yake yi sai de kukan da takeyi 'din har zuciyarsa yake jin ciwonsa, tausayinta yaji ya kamashi, hakan yasa shi lowering voice 'dinsa yace mata " _banace gobe zakuje_ _ba_ ? Kai ta 'daga masa alamar " _ehh_ ". " _so why d tears_ ? Yayi maganar tare da 'dage gira 'daya. Cikin wani shagwa6an tace " _gobe fa Mummy zatazo, kuma banaso tazo bana nan_ " Murmushi yayi mata da jin wannan shirmen kuma sai yace mata " _kin fiye kwa6a ke kam,_ _angaya miki idan tazo 'din zata koma kafin ki dawo ne_ ? Jijjiga kai tayi. " _Toh oyah wipe all those tears ban son shirme_ " Fara share hawayen tayi da hannunta 'daya, sai ya 'dago 'dayan hannunsa ya fara tayata gogewa ahankali, yana gogewan yake fa'din, " _kar na 'kara ganin_ _hawayen nan kinji, idan bahaka ba naga kin sake yin wani kuka toh goben ma baza'a je_ _ko'ina ba kuma zance da Mummyn ma karta zo_ ...... Hannah ce ta iso da sallamarta da niyyar duba Teemah ganin lokaci na tafiya kuma tajita shiru. Cak ta tsaya tana mamaki ganin su tsaye daf da daf Kamar ze mai da ta cikinsa yana share mata hawaye. Abbas kam ko ajikinsa sallamar Hannah kawai ya amsa tare da 'dauke hannunsa daga kan fuskar ya yi kamar babu abinda yayi. " _Ina yini Yayah_ " Hannah ta fa'di tare da kawar da kanta gefe. Da " _lafiya_ " kawai ya amsata daga nan ya juya ya shige cikiabinsa, itama Hannah bata damu ba dama tasan iya amsar dazata samu kenan dan haka sai ta nufi gurin da Teemah ke tsaye da sauri ganin ta wata iri. Hannunta takama taja ta suka nufi hanyar fita, sai da suka 'danyi nisa da 'dakin nasa kafin Hannah ta tsaya ta tambaye ta cewa " _me Yayah yake miki afuskarki yau kuma_ ? Bata bata amsar tambayar taba sai tace " _Yayah yace wai ba zamu fita yau ba, sai de gobe_ " Duk da taji haushi sosai da jin abinda ya fa'da 'din amma ita bashi take son ji ba dan haka sai tace " _that a side Teemah bani amsar tambayata_ " Shiru Teemah tayi mata dan bata san me zata ce mata ba,tace da hawayen ta ya goge mata ko kuma tace me? Juyawa Teemah tayi ta nufi hanyar 'dakinsu. Shan gabanta Hannah tayi tace " _to shikenan tsaya,_ _wai dagaske cewa yayi bazamu_ _ba_ ? Cikin sanyin murya tace " _Dagaske ne mana Hannah zan miki karyane_ "! Hannah cewa tayi " _Toh shi dama baya zo ba sai ya damu mutun, sarkin kwafsi ai nasan ze aikata tunda naga kin da'de baki dawo ba sai dana ayyanah, Allah Yayah ya cika bada mutun wallahi, sai dana gama 'daga wa kaina hankali nagama shiri ina murnar zan kaiki kiga gari shine ya hana kuma_ " 'Dakinsu suka koma ko wajen Ummah basu kuma zuwa ba. sai can da Ummah taga shirun yayi yawane shine tafito dubasu. Direct 'dakin Abbas ta nufa dan tayi zaton ko shi yari'kesu. Koda ta isa 'dakin nasa zaune tasame shi akan cujera ya na duba system 'dinsa ganinta yasa shi 'dago kansa zuwa kallonta. Ummah kam ganin ko'ina fes sai tayi mamakin yaushe kuma aka gyara shi, atake ta tuna ashe fa ba'a gyara 'dakin ba shaf ta manta wallahi, wata'kila akan aikin yari'ke min yarinya. Kauda zancen tayi ta jefa masa tamabayar " _ina yaran nawa suke_ ? " _Ummah ai sun da'de da barin nan_ " Mamaki tayi tace masa " kamu su wani abin 'kila dan nasa haka banza bazan ji shiru har haka ba" Murmushi yayi yace mata " _toh ni me zan musu Ummah_ ? Tace " _Ni da kai ne ai idan_ _naji wani abu_ " Be yi magana ba kawai ya sunkuyar da kansa yana murmushi da jin maganar Ummahn. Ahankali Ummah tace " _ya bangansu ba toh, bari dai_ _induba ko suna 'daki_ " Tayi maganar tare da juyawa ta koma zuwa dakinsu. Tana tafiyar take tunanin kardai tafiya sukayi batare da sun mata sallama ba, in kuwa haka ne tasan duk tsirin Hannah ne. Tura 'kofar Ummah tayi ta ri'ke ahannunta batare da ta 'karasa ciki ba ganin kowa na sabganshi a'dakin tamkar sun manta da batun fitan da zasuyin gashi har yamma ta kawo kai basu tafi ba. Sukuwa 'karan bu'de 'kofan ne yasa dukkansu hankalinsu ya kai gurin 'kofar afirgice domin basuyi zaton mutun ba sai suka ga ashe Ummah ce Cewa tayi " _har kunje kun dawo ne_ ? Hannah ce tayi saurin bata amsa da fa'din " _ba Yayah ya hana mu ba, wai sai gobe zamu_ " Murmushi Ummah tayi cikin nuna halin ko'in kula tace " _toh Allah_ _ya kaimu goben_ "! Zaburowa Hannah tayi tace " _haba Ummah kema haka zaki ce kuma?_ " _Toh me kike so in ce Hannah bayan lokacin daya hana ku fitan baku zo kun sameni ba, yanzu da lokaci ya 'kure kuma me zance in banda Allah ya kaimu goben_ "! Kwafa Hannah tayi tace " _Allah Yayah yaban haushi Ummah, kuma fah shi ya ri'ke Teemah da aiki har sai da yaga_ _lokaci ya 'kure tukunna_ " Teemah kam ko 'kala bata ce ba dan kwata-kwata ma bata san me zata furta ba ita. 'Karasowa ciki Ummah tayi ta zauna akan stool 'din dressing mirror sannan ta dubesu tace. " _kuyi ha'kuri ai inda rai gaben ma kamar yau ne karku damu kunji?_ Kallonta ta mayar kan Teemah tace _Fateemah kiyi ha'kuri kinji halin Yayan naku ne_ _sai a hankali_ " Murmushi Teemah tayi itama ta sunkuyar da kai 'kasa yanzun bata jin yin magana ne. ***** Washe gari kuwa dawuri suka gama shirin su tun 11am, saboda su samu su sake sosai sun gama tsara cewa yau 'din sai sun sha yawo sosai kafin su dawo duk da suna tsammanin ayau 'din bazasu fasa ba. Hannah ce ma data tsaya waya da Bilal ita ce ta 'dan 6ata musu lokaci, dan Bilal baya 'kasar shi kuma ba ko da yaushe suke samun damar yin waya ba sai lokaci zuwa lokaci saboda abubuwan dake gabansa hakan yasa duk lokacin da ya 'kirata hirarsu bata yankewa da wuri, Teemah haushi kamar ta 'kwace wayar ta jefar ganin har kwalliyarsu na shirin dusashewa amma basu fita ba, musamman idan taji yanda Hannah ke 'ko'karin lan'kwashe muryarta idan tana waya da Bilal 'din sai haushin Hannah ma ya 'kara kamata tace ai

Chapter 40 of 67