Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya shiga koda ya fito ya shirya ma sai da yayi sallah sannan ya hawo gadon, jikinta yazo ya matso ya rungumo ta Teemah take ta fara 'ko'karin barin jikinsa da sauri dama 'dari-'dari takeyi dashi shiyasa tun 'dazu bacci yakasa 'daukan ta, Abbas sai ya ra'da mata " _come on... ki nutsu ban son rigima i thought rage miki wahala zanyi, naga anjima dakan ki ma zaki shige min jiki_ _ko da banaso_ " Shiru tayi kawai ta zubawa 'kirjinsa idanu tana jin tsoron sa har ranta amma data ga bai yi mata komai ba sai ta saki ranta ajikin nasa har bacci ya 'dauke ta. Abbas ma dagangan ya 'kyaleta be mata komai ba dan ya fahimci tsoronsa dake cikin 'kwayar idanun ta, kuma baya so tsoron yayi tasiri azuciyar ta shiyasa. Washe gari da safe bayan sunyi sallah Abbas wanka ya shiga yafito da hanzari yake yin komai yayin da Teemah ke bin sa da idanu, yana gaban mirror yana gogec ruwan kansa ta cikin mirror ya hango yanda take kallon sa. Juywa yayi yace da ita " _kallon fah_ " Tare da 'dage gira. Take ta tura baki ta tayi sama da idanun ta zuwa kan photon sa dake sama tace " _ni kai nake kallo ne_ ? " _Toh wa kike kallo gaya min_ ? Ya sake tambayar ta. Sai ta nuna masa photon da hannu. Murmushi yayi yace " _photon ki ne toh wannan 'din_ ? " _Umm-umm_ " Tace a hankali. Sai ya sake fa'din " _Photon mijin ki kike gani ko_ ? Shiru tayi masa tana 'kun'kuni Abbas kam 'dauke idanun sa yayi a kanta yaci gaba da abinda yake yi. Shine yaje ya raja su Mummy da Anty ranar duk suka wuce kano gaba 'daya, Mummy ma naso ta gaida dangi wa'dan da ba su ha'du da su ba dan basu samu halattan bikin ba. Kafin ya dawo kuwa Teemah ta tashi dayake taji 'karfin jikin ta yanzun bata jin zafin komai, aiki tayi agidan sosai inda ya dawo tsab da shi sannan tayi wanka ta shirya cikin 'kananun kayan ta riga da ta kai mata ko gwiwa ba da dogon wandon skinny tayi kyau kamar asace ta, gashin ta ta kama ta 'daure a tsakiyar kanta da 'karamin ribbom. Abbas kansa daya dawo yaji da'din hakan sai ma yaji wani sabon san kasancewa da ita a lokacin. Zama yayi a kujera yana kallon ta da lumsassun idanu yace " _nagaji yau 'din nan zo ki tayani rage kaya na plz_ ! 'Kasa-'kasa tace " _kai baka da hannu_ _ne_ ? Sarai yaji ta amma sai yayi kamar be ji ba sai ma cewa da yayi " _quickly plz yunwa nake ji fah_ ! A hankali ta 'kara so inda yake ta fara 6alle masa bottuns 'din rigar batare da ta kalli idanun sa ba. Abbas hannu yasa daga bayan ta ya tura ta ta fa'do jikin sa tana 'ko'karin mi'kewa Abbas ya 'ki bata dama sai ya matso da fuskar sa kusa da tata, rintse idanu tayi da 'karfi hannun kan 'kirkinsa tana so ta ture shi amma hakan ya gagare ta dan ko motsi be yi ba, bakin su ya ha'de ya fara bata lafiyayyan kiss me tsayawa azuciyar masoyi. Teeemah kam tsintan kanta tayi awani irin yanayi bazata ce ga yanayin data tsinci kanta ba amma duk da haka sai take mutsu-mutsu dan ta 'kwaci kanta, Abbas be bar ta ba sai da ya tabbatar cewa sa'kon sa ya isa sannan ya 'kyaleta. Muryar sa ciki-ciki yace " _tashi ki bani abinci_ "! Shiru tayi kamar bata ji ba tana maida numfashi a hankali kanta akan 'kirjin sa " _kina son 'kari ne?_ Ya tambaye ta sai ta mi'ke a hankali ta isa dinning shima Abbas a baya yabita yana 'ko'karin daidaita nutsuwar sa. Haka Abbas yaci gaba da kulawa da ita be 'kara ra6an ta ba duk kuwa da cewa yana tsananin bu'katan hakan amma ya danne saboda tausayin halin da zata shiga. Sai de yakanyi 'ko'kari wajen koyar da ita karatun sa mai wuyar fassaruwa musamman idan suka zo bacci, sosai yake 'daura ta akan alayi mai wuyan mantawa, dan baya barin ta kwanciya haka batare da yayi wasa da albarkatun jikin ta ba koda kuwa da wani lokaci ne yakan ritsata da hakan. Wani lokaci idan zatayi masa gardama yakan yawaita tsorata ta da Anty nurse abu ka'dan sai yace zai 'kirata tayi mata allura tun Teemah tana masa taurin kai har tazo ta daina balle data ga baya mata irin na rannan me zafi sai kawai itama ta rin'ka barin shi koda wani lokaci ne kuwa. ***** Kwance take ajikin sa wani dare, idanun Abbas na lumshe lokacin har ya fara bacci ma sai ta rin'ka 'kiran sunan shi ahankali, bai bu'de idanun sa ba ya amsa mata da fa'din " _inajinki_ " Muryarta a sanyaye tace dashi " _Yayah yaushe zaka kaini inga Zahra_ ? " _Sai ranar da kika zama cikakkiyar doctor_ ? Ya bata amsa da lumsassun idanu. Teemah ta 6ata rai tace " _Hum-umm ni nace ma inason zama likita ne_ ? " _Zaki zama ai da iznin Allah ki rin'ka yiwa wasu allura kema harda Zahra ta sai kin mata_ _dan bataji kullum rashin kunya take min.... irin alluran Anty nurse zaki nayi mata mai zafi_ " Yatsina fuska Teemah tayi harda karya wuya tace " _Ni kam banaso_ ! " _Toh kuwa babu ke babu ganin Zahra ta_ "! Shiru tayi kawai tana tunanin wannan Zahran. ***** Kwana biyu bayan hakan da wata safiya fitowan ta daga wanka kenan ta tsaya gaban mirror tana goge ruwan dake jikinta, al'adar ta ce wannan, kusan ma za'ace tasaba da hakan tuntuni idan ta fito daga wanka bata damuwa da komai take raba jikin ta da towel 'din wani lokaci ma dashi take goge jikin ta sannan idan tagama sai ta shanya shi, sanadin haka yasa har yau bata son yin wanka a 'dakin Abbas saboda gudun masifar sa. Turo 'kofa kawai taji anyi batare da ko sallama ba sai ma " _excuse me_ " daya fa'di dai-dai da tura 'kofan. Firgita tayi daga inda take tsayen take kuwa ta fara lalu6en towel 'din da sauri. Koda ta 'daukan kuma garin sauri sai ta kama ba daidai ba bakin sama dana 'kasa ta kamo sai ya kasance a mur'de kamar ta kama, kamar ta tsala ihu haka taji dan takaici gashi ya 'kura mata idanu kamar zai cinyeta. Sai data samu ta daidai ta towel 'din kafin ta juya baya, 'kasa-'kasa tace " _sai kace ba musulmi ba zaka wani shigowa mutun 'daki babu ko neman izini_ " Caraf taji an kama hannun ta tare da juyo da ita, Teemah bata san lokacin daya iso kusa da ita ba sai hakan ya 'kara tsora tata. Cikin idanun ta yake kallo ita kuwa sai tayi 'kasa da nata idanun ta sau'ke su akan 'kirjinsa, bata juran irin wannan kallon daga gareshi, kwarjininsa rauni yake sata. Abbas idanun sa ya mayar kan wuyan ta sai ya 'kara matso da ita zuwa jikinsa sosai daf da juna yace " _zagina kike yi ko_ ? Kai ta jijjiga masa da sauri " _toh menene_ ? Ya sake tambayar ta tare da sake rage 'yar 'karamar tazarar dake tsakanin su. Yayinda Teemah tayi shiru sosai ta ke tsorata da wannan yanayin. " _Me kika ce fa'da min naji_ " A hankali yayi maganar yanda ita ka'dai ce zata ji. Itama a irin yanayin tace " _da kaina nake yi fah!_ Tun kam ma ta 'karasa yace " _shiyasa nake so in sani ai_ " Baki ta tura gaba dan bata san me zata ce dashi ba a wannan halin gashi ya takurata banda numfashin sa bata sha'kan komai. Murmushi yayi tare da 'dage idanu sama ka'dan yace " _kinji haushi ne dana kalli jikin ki?_ Shiru tayi dan takaici sai ma idanun ta suka fara tara hawaye. Abbas kam sai yasake fa'din " _an gaya miki haramun nagani ne toh ko kin manta jiya da da_ ...... Da sauri Teemah ta toshe masa baki da hannunta 'daya dan kar ya 'karasa fa'da, ita kanta ta manta cewar yagama ganin dukkan ilahirin jikin ta musamman jiya da yi mata wani mahaukacin romance 'din da be ta6a yimata irin sa ba, ita kanta sai da taji cewa ta isa, yanzun daya tuna mata kuwa bata so tasake ji ya furta da bakinsa, kunyarsa zataji sosai. Idanun ta cikin nashi suna kallon kallo, take kuwa hawayen ta suka gangaro wanda yasa dole sai data lumshe idanunta. Abbas kam hannun ta ya cire daga bakin nasa sai ya samu daman ha'de musu baki, bai barta ba kuwa har se da ya tabbatar ya danganta ta da gadon dake cikin 'dakin. Sosai ranar ya sake maimaita wa, gara ya kwasa son ranshi sannan ya 'kyale ta. Teemah kam yau bata ji zafi ba amma kuma hakan be hana ta kuka ba inda taringa ha'dawa har dana shagwa6a ma. Tare sukayi wanka a bathroom 'din ta Abbas nata tsokanan ta wai ai ranan tace zata ha'dashi dasu Daddy da Ummah su cire masa kunne, meyasa yau kuma bata fa'di hakan ba sai ma ita ke 'ko'karin cire masa kunnan nasa saboda santi. Dayake yau 'din da 'dan karfin ta ba kamar rannan ba, duk dama Abbas din bana wasa bane sosai ya galabaitar da ita amma hakan be sa bakin ta ya mutu ba, sai ta bu'di baki a hankali ta maida masa martani da fa'din " _bawani santi ita kam dataji banda azaba....... kuma ai sai ta gaya shi da Daddyn tunda baze_ _daina yi mata muguntan ba_ " Abbas kam cemata yayi " _bari na 'kara toh sai ki ji da'din fa'da musu mai dalili_ " Tana jin haka ta tashi ta fito ta barshi abayin da sauri. Dariya yabi bayan ta dashi kawai, daman ma tsokanan ta kawai yakeyi. Sai da yafito kafin ta koma tayi wankan tsarki Abbas na sake cewa da ita wai " _matsoraciya_ ". *SORRY 4 THE LATE UPDATE PLZ.* πŸ‘πŸ» ~Kai ur comment always make me felt like am d best wlh, godiya nake 'yan uwa na.~ *KEEP IT UP MASOYANA* 🀞🏻 πŸ‘ŽπŸ» *Ummu haidar* da *Sis Mar-yerm* _sako daga Teemah tace wai ita bata son kishiya abin mamakin kuma_ _shine Abbas ma ya amince wai redcard zai baku amma gaskiya Ummah bata goyi bayan hakan ba tace wai tana son ku_ _saboda bakwa fa'da da junanku_ 🀠. 😍@ *TAMAMA* _Hhhhhhh_ _wa'kar ki fah nasani rawa da juyi har ana min dariya wai_ _na zauce gaskiya ngd 'yar uwa jinjinar ban_ _girma_ .πŸ‘ ~MOST READ~ πŸ‘‡πŸΌ *KUNGA DA YAWA NAYI MUKU KO?TOH HARDA NA GOBE NAYI , IN DA RAI KUMA SAI SATURDAY MU HADU IDAN ALLAHU YA KAIMU, IN KUMA NASAMU* *DAMA BA MAMAKI KUGA UPDATE* . _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerhn ku ce* 😍 [10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* I _dedicated this page to my fellow *Wattpadians and Whatsapp fans* , Ha'ki'ka *SALMERH*_ _najin da'din kasancewa tare daku comment 'din ku addu'o'in ku, tare da conversation 'dinku na matu'kar 'karamin karsashi, wannan page 'din kyautar kuneπŸ‘ŒπŸ»_ .πŸ₯° *Bismillahir rahmanir raheem* _I learn that life is a book, every day is a new page, every month is a new chapter and every year is a new series._ πŸ…Ώ *84* Kwana biyu bayan hakan Abbas ya koma Rivers dan dama hutun 1week aka bashi, kafin hakan kuwa sun sha drama da Daddyn Abuja akan tafiyar, Abbas ya so su koma tare da matar sa amma Daddyn Abuja ya hana shi, dan cewa yayi baza'a tafi masa can wata uwa duniya da yarinya ba, salon aji da'din cutar da ita acan ba, shi be yadda da zaman sun ba har yanzu yana ganin kamar Abbas mugun hali zai yi tayi mata, amma idan tana kusa da su toh abin zai zo da sau'ki kuma dole ne ya rin'ka kulawa da ita ko dan ganin idanun su ma. Daddy gani yake kamar a bayan idanun su Abbas zai na zalintar ta ne kawai, shiyasa yace tukunna sai yaga yanayin zaman nasu kafin ta bishi. Shi kansa daddyn cewa yayi bazai bar Abbas 'din yaringa daukan tsawon lokaci ba dole zai na zuwa duba ta. Abbas be iya musu ko jan magana ba dan haka sai ya yi shiru kawai amma ba wai dan ransa ya so hakan ba, ya so ya sanar da Daddy babbah saboda yasan shi ka'dai ne zai sa Daddy amincewa amma kuma nauyin sa yake 'dan ji yanzun kuma ma dan kar Daddyn nasa yaga kamar yana jayayya ne da maganar sa shiyasa kawai ya fasa. Ya dai 'dora hope 'din sa akan Teemah da tunanin ko zata yadda itan tace zata bishi, amma ko daya zo ya same ta da batun sai ta nuna 'kin amincewar ta sai ma tace zata koma gidan Ummah kawai idan ya tafi. Bai san dalilin ta na 'kin amincewan ba, amma ba 'karamin haushi yaji ba yasan da ita ta amince toh da Daddy ma zai yi shiru akan lamarin. Ai kuwa shima Abbas yace babu inda za taje agida zata yi ta zama ita ka'dai tunda bazata bishi ba. Sosai ta tsorata da zaman da zata yi a gida ita ka'dai 'din saboda tuna baya da tayi, amma sai take ganin da ta bishi 'din gara ta zauna agidan in yaso idan ya tafi sai ta koma abinta ai baze sani ba. Sosai Teemah ta 'dauki abin wasa. Haka har Abbas ya tafi da haushin ta ha'di da kewar ta da zaiyi azuciyar sa. ***** Anty ma a cikin week 'din ta bar kano ta koma Lagos, yanzu kam zuciyar ta fes ba wani damuwa, bata da burin cutar da kowa aranta illah taga ta gyara tsakanin ta da ubangijin ta ta kuma gyara lahirar ta, gidan ta ma ba 'daya da kishiyar ta ba amma bayan ta koma Abbah ya kawo amaryar sa har gida suka wuni tare dan Abbah kansa zuwa yanzun ya yadda da cewa Anty ta yi nadama ta gaskiya ta gyara halin ta gaba 'daya ta canja su daga munana zuwa kyawawa musamman daya ga yanda taje har Abuja musamman saboda Fateemah shiyasa ma batare da fargaban komai ba ya bar amaryar sa tare da ita. Anty ma a'dan zaman nasu ne ta fahimci cewa kishiyar ta irin alkahiri ce mai sanyin hali, dangin albarka, tariga ta 'dauri aniyar kar6an kaddarar ta aduk yanda tazo mata, ta yarda cewa zata zauna zaman amana da kishiyar ta, cikin aminci da salama shiyasa ma bata damu ba ta budewa Anty Sadiya zuciyar ta gaba 'daya. Haka kishiyar ta ma bata nuna mata komai ba suka ha'de kansu tamkar 'yan uwan juna, kowa ya ri'ke matsayin dayake kai. Raba kwanakin su sukayi kamar yadda dukkan ilahirin masu kishiya keyi wato kwanaki bibbiyu. ***** Ummah ma taso Abbas ya koma Porthacourt da matar sa sai Daddy ya hana, tayi ko'kari sosai wajen ganin ta gyara abin amma be yiwu ba, bayan haka kuma sai tayi tunanin ko Teemahn zata dawo gida ne kafin ya dawo, sai kuma Abbas shima ya yi nasa ikon ya hana. Mamaki Ummah tayi sosai akan hakan kuma sai ta tambayi Teemahn ko tayi masa wani laifi ne tace ah ah wai dan ta'ki binsa ne shiyasa, Ummah batayi mamaki ba dama tasan sai da dalili kafin zaiyi hakan dan tasan baze yi purnishing 'din ta akan laifin Daddy ba, tasan yayi hakan ne dan yayi purnishing 'dinta akan 'kin amincewa binsa da tayi, Ummah sam hakan beyi mata da'di ba, aganin ta tunda abaya nema ake yayi auren amma ya'ki har sai da akayi masa za6i, Alhamdulillah kuma sai ya kar6i za6in nasu da hannu bibbiyu toh me yasa kuma ba za'a bar shi ya nutsar da hankalin sa wuri guda ba, me yasa baza'a barshi ya tafi da iyalinsa ba ko dan ma sha'kuwar su ta 'mara 'karfi. Aranan da ya tafi Ummah ta 'kira Abbas akan zaman Teemah ita ka'dai agida 'din tace masa ai be yiba tace yayi ha'kuri Teemah ai yarinya ce kar yana biye ta akan wasu abububuwan tunda yasan bazata iya ba, shi kam rufe ido yayi yace da Ummah abar ta kawai, akwai security aciki da wajen gate babu komai insha Allahu, yace Ummah ai kowa ma haka take zama agidan auren ta so ba wani sabon abu bane, Ummah taso tayi convincing 'dinsa amma Abbas yakasa fahimtar ta dolen ta tabar shi akan ra'ayin sa kawai sai ta tura Hannah akan su zauna tare. ***** Teemah yanzu hankalin ta a kwance yake bata da damuwar komai, duk kuwa da cewa Abbas ya hana ta zuwa ko'ina amma hakan be dame ta ba, yace ta zauna a gidan ta bai yadda taje ko wajen gate ba, suna zaman su da Hannah lafiya domin Hannah na taya ta surutu sosai ta 'dauke mata tunanin komai dan Hannah ba dai surutu ba, lokacin zuwa makaranta sai ta tafi, in sun gama lectures sai ta dawo gida. Suyi fa'da suyi da'di dan Hannah akwai tsokana na fitan hankali. Abbas tunda yatafi yau kwanan sa biyu amma sau 'daya tak ya 'kira ta shi' din ma da tunanin ta ya ishe shine ya 'kira ta dan kawai yaji muryar ta, Teemah kuwa gaishe shi tayi tare da tambayar sa ya ya isa. Jiya yai muryar ta ras hankalinta akwance lokacin datake tambayar tasa bata tare da wata damuwar komai. Bai amsa maganar ta ta ba sai ma ya tambaye ta yace " _wato ke bakya missing 'dina ko_ ? Dan ransa yakasa yin ha'kurin bata damu da rashin sa ba. Shiru tayi masa bata yi magana ba, sai dariya datakeyi 'kasa-'kasa, sosai Abbas yaji haushin hakan sai ma yaga kamar farin ciki take yi daya bar ta a Abujan dan haka shima sai ya kashe 'kiran kawai ya dafe kansa. Teemah kam bata damu ba taci gaba da walwalar ta bata 'kara bi ta kansa ba haka shima. Tana waya da su Anty da Mummy harma da Daddyn ta ha kama maman Amal itama suna waya akai-akai musamman dataji cewa Teemahn tasake yin aure ma sai ta ke yawan bata shawar wari wa'dan da bazasu cutar da rayuwar kowa ba, Anty ma kullun maganar ta kenan guda 'daya shine ta kula da mijinta ta kula da hakkin da ke kanta, kuma ta daina rashin ji da taurin kai. Sosai maganganun sun yake tasiri azuciyar ta musammman sai dai bata san ta yanda zata yi handling wasu abubuwan ba dan ta fahimci Yayahn 6au'da'd'de ne. Amma data ga ya 'kara kwana da wuni be 'kira ta ba sai abin sai ya fara damun ta, da kanta ta fahimci bata kyauta masa ba. Wasa-wasa kusan kwana biyar bai 'kirata ba sai dai Hannah ce ke yawan sanar da ita cewa ai Yayah ya 'kirata data na school kusan kullun hakan Hannah ke sanar da ita, amma idan tana gida bata ganin yana 'kiran Hannah, kuma Hannah bata ta6a cewa da ita ya neme ta ba ko yace a gaida ta ba abin na 'daure mata kai sosai. Hannah kuwa bata san cewa basa waya ba da yake ba'a gida take wuni ba, sai dai itama daga baya tafara yiwa Teemah mitar bata ta6a ganin suna waya da Yayah ba shin basa missing juna ne ko kuma sai abayan idon ta akeyi. Teemah "hmm" kawai ta ce da ita, dan ita kanta zuwa yanzun tafara shiga ru'du, missing 'din sa takeyi sosai shi kansa, muryar sa, fitinar shi, touches 'din sa da komai nasa. So ma take ta ganshi gaba 'daya dan ba 'karamin missing 'din sa takeyi ba, tunanin sa kullum na damun ta musamman ma idan taje bacci da dare. Sau tari idan ta tuna da Zahran sa takanji ba da'di har zuciyarta, inda take sai taji hankalin ta yakasa kwanciya wani sabon tsanar yarinyar take ji na tsarga mata. Hannah ma da kanta ta fahimci Teemah ba daidai take ba a kwanakin nan dan tafiya ganin ta cikin tunani amma data ga bata sanar da ita meke faruwa ba sai itama bata tambaye ta ba. Ranar daya cika kwana bakwai da tafiya ranar Teemah na kwance da dare takasa bacci sai juyi take yi, Hannah har ta gama waya da Bilal ta kwanta har ta 'dan yi bacci ta farka garin yin juyi sai ta ga Teemah zaune idanun ta biyu lokacin kuwa sha 'daya da kusan rabi na dare, batayi mamaki ba sai ma tausayin Teemahn daya kama ta. Tashi tayi ta zauna tare da dafa Teemah tace " _Me yafaru ne naga har yanzu idanun ki biyu, bakya jin da'di ne_ ? Kai Teemah ta jijjiga mata tare da fa'din " _bakomai Hannah ki kwanta abinki nima yanzu zan kwanta_ ". Tana gama maganar sai ta juya ta kwanta ita bata so Hannah tasan matsalar data ke ciki. Hannah kam da kallo ta bita ganin 'karfi da yaji take 'ko'karin 6oye damuwar ta bayan fuska da yanayin ta sun riga sun bayyana komai. Teemah kam baya ta juya mata da tunanin zata kwanta itama, yayin da Hannah ta bi bayan nata da kallo tsawon da 'ki'ku biyar tausayi Teemahn take bata ita musamman daya kasance auren ta biyu amma har yanzu batayi dace da samun farin cikin daya kama ta ba duk da yanzun tana mata kwa'dayin samun farin ciki da Yayahn amma tana ga hakan bazai yiwu ba dole sai ta yi nata yun'kurin kafinnan, dan duk wacce Allah ya jarabce ta da auren miji irin Yayah Abbas toh dole sai ha'kurin ta yazarce nakowa sai tayi nin kin wanda kowacce mace keyi agidan mijin ta sannan ta'kara da du'a'i saboda neman agajin mahalicci. Duk mijin da ze nuna maka abu bai damesa ba ya nuna maka bashida matsala da komai bacin ba hakan bane aransa toh kuwa dole mace sai ta tsaya tsayin daka wurin ganin ta sai ta hankalin sa wuri guda, bako wani namiji bane wanda soyayya ke sashi bin duk abinda kike so, wanin shi ba damuwar sa bane koda kuwa yana yi miki irin son da ya zarce nakowa ne a duniyan nan. A hankali kamar ba zatayi maganar ba tace da Teemah " _matsalar Yayah ne ke damun ki ko_ ? Zaro idanu Teemah tayi tana daga kwancen sannan ta juya a hankali ta kalli Hannah bata so Hannah tasan abinda ke faruwa tsakanin su dan haka sai ta jijjiga wa Hannah kai tare da fa'din " _ni fa bance miki haka ba Hannah plz mukwan ta dare yayi fah!_ Kwafah Hannah tayi ganin yanda Teemah keso ta bin ne ta abaibai bayan kowa yagan ta a wannan yanayin yasan tana tarexda damuwa, ita kanta Hannah bataso yin shidshigi wa lamarinsu ba musamman ma daya kasance mijin Teemah 'din wanta uwa 'daya amma wani lokacin idan abu ya so barin hanyar da ta dace inkana da dama taro shi zai yi matu'kar amfani ko dan saboda gaba ma. A hankali ta kuma fa'din " _Karki maida ni shashasha mana Teemah, kin 'dauka bansan meke tafiya bane har yanzu_ ? _na jima da fahimtar kina tare da damuwa a gidan nan kawai 6oye_ _min kike yi shiyasa nima na 'kyale ki, kuma nasan ba zai wuce matsalar Yayah ba hakane_ ?. "Ah ah" Teemah tace da sauri. Hannah kuwa cewa tayi " _Allah idan baki gayamin ba ina fita gobe Ummah zan samu in fa'dawa_ _nasan zata sanar da daddy kamar yanda nasan cewa Daddy ba zai yi shiru hakanan ba dole sai ya tambayi Yayah_ _kinga ai lokacin dole ki bu'di baki kiyi magana ko_ ? Teemah da hanzari ta kamo hannun Hannah tace " _dan Allah Hannah kiyi ha'kuri karki fa'dawa Ummah, Hannah yaushe_ _ma akayi auren da har irin haka zai fara faruwa ki taimake ni karki fa'da ma kowa plz_ "! Goshi Hannah ta ha'de irin boss din nan tace " _sanar dani toh if dont want me to tell Ummah about it_ " Baki Teemah ta tura gaba " _tace ai nagaya miki bakomai tun 'da zu_ " "Kin tabbatar? Hannah ta tambaye ta. Kai ta daga kamar yarinya 'karama. Hannah kuwa tace " shikenan toh, ni bazan musa ki ba amma kisani babu abinda zai hanani sanar da Ummah gobe sai dai in ban tashi cikin rayayyu ba"! Tana maganar ta juya ta kwanta. Teemah ri'ko ta tayi tace " _Haba Hannah nice fah_

Chapter 51 of 67