Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sannan ya kalli wayar sau 'daya sai ya maida idanun sa ya sake lumshe wa sannan yace " _kinsan ta ne_ ? Amsa ta bashi da fa'din " _ah'ah naga tana kama dani ne shiyasa....! a ina take Yayah?_ Tana maganar tana sake kallon cikin wayar ita dai abin na bata mamaki matuka. Ce mata yayi " _a_ _zuciya ta take_ "! Teemah da mamaki ta kalleshi harda kwalalo idanu waje tace " _Zuciya dai Yayah_ _saboda me kuma_ ? " _Saboda ita Zahra ta ce, farin cikina kuma burin raina ina matu'kar sonta sosai........inda kinsan yawan 'kaunar da nake mata nasan har zaki tausaya wannan mijin naki, kusan hauka nayi abaya da_ ' _kaddara ya shiga tsakanina da ita ya sanya narasa ta sai daga baya kuma tadawo min alokacin da bana zato bayan har na yanke 'kauna_ _da samun ta_ " " _Ni kan ina so inganta Yayah plz ka kaini inganta even once_ " Kai ya jijjiga mata alamar " _ah ah_ " Sai t asake fa'din " _pls Yayah mana nice fa_ "! Yace " _Ke wa_ ? Itama sai bashi amsa da " _Fateema Kabeer_ " Cewa yayi " _Yes ai nasani_ " sai tace " _Toh ka kaini in ganta mana kaji Yayah, Allah bazan 'kara yima birgima ba daga yau 'din nan_ " Murmushi yayi dan kuwa maganar tata dariya taso sashi sai yace da ita " _bazan kaiki ba ai yanzu ma damuna kikayi kika hana ni bacci dan haka nima sai ranar dana ga dama zan kaiki_ " " _i'm sorry toh bazan sake ba Allah na daina daga yau_ " Tayi maganar harda kama kunnuwan ta duka biyu. Abbaskuwa ya jijjiga kansa. Da sauri sai tace " _Yayah toh sai yaushe kenan_ ? " _Bayanzu ba akwai steps b4 aganta kinsan Zahra ta ta da bance_ "! Teemah shiru tayi tana kallon fuskar sa dake kan cinyar ta yana murmushi har dimple 'dinsa na lotsawa. Ita kam abin na birgeta har ma bata san lokacin da ta kai hannu wurin ba. Tuna waye ne yasa tayi saurin 'dauke hannun ta tana sake kallon shi. Ganin be motsa ba kuma be kulata ba yasa ta sake maida yatsan ahankali tana latsawa. Abbas sai ya kai hannun sa ya ri'ke nata hannun dake masa yawo a fuska. Yana cire hannun sai ya sake gyara kwanciyar sa akan cinyar tata. Teemah sai ta tura bakin haushin ya hana ta ta6a dimple 'dinsa bayan ya'ki amincewa ya kaita wurin Zahran sa. Zuba masa idanu tayi cike da takaici, da ta rasa abin yi sai ta fara jan 'kafar ta tare da fa'din " _''daga min kafata nima tagaji Yayah_ " Be ce da ita ko 'kala ba sai ya maida kan nasa yayi matashi da pillow kamar yanda yake da farko tare da juya mata baya. Teemah ma tashi tayi ta ajiye masa wayar a kan drawer sannan tafice zuwa 'dakin ta fuska babu walwala, wanka tayi cikin sanyin jiki. Yau ko kwalliya ma batayi ba powder kawai ta shafawa fuskarta, cikin rashin kuzari take yin komai dan tun barowar ta 'dakin sa take jin 6acin rai nataso mata, ga tunanin Zahran sa daya tsaye mata a zuci, bata san me yasa take jin haushin ta ba, sai taji bata 'kaunar ta ma sam, tasan wata'kila da Zahran ce ai da bazai hanata ta6a mai fuska ba. Yau kam bata fita ba zaman ta tayi a 'daki ko lokacin da door bell yayi 'kara ma tanaji amma ta'ki fita, Abbas ne yaje ya bud'e 'kofar wanda tun da ga jin yanayin gaisuwar su ma ka'dai yasa tagane ba Hannah bace yau takawo musu breakfast 'din. Sai lokacin ma ta tuna ashe yau monday ne Hannah nada lectures a makaranta. Ashe kuwa ya taho mata da tarkacen wayoyin ta da sauran kayan ta na anfani ciki kuwa harda wayar Mahmud aka ha'do. Dama ta sanar da Mummy cewa wayar ta na gida Hannah ta taho mata da wayar idan zata zo. Abbas da kansa ya kawo mata har 'dakin ta ko daya ga tana wani shan 'Kamshi ma sai ya share ta shima ya fice abinsa dan yasan mecece matsalar ta. Zuwan wayar ne ya 'dan sanyaya mata rai ta 'danji dama-dama sai duk ta bi ta sanya su a chaji gaba 'daya. *10:12am* Abbas ya buga mata 'kofa amma be jira ta bude ba kawai sai ya juya zuwa dinning. Tana kwance tana faman chatn jin an buga mata 'kofa yasa ta ajiye wayar ta fito sai ta hango shi zaune yawani hakimce yana amsa waya. Tasan shine ya buga 'kofar dan haka sai ta isa dinning 'din itama. Bata zauna ba sai ta koma kitchen ta 'dauko su plates da cups ta dawo tayi serving nasu kana ta zauna bayan ta tura masa nashi gabansa. Abbas na lura da ita amma be kulata ba dan yasan halinta sam magana be sata cin abin sai in har tayi niyyah sa6anin haka kuma sai de in kai ne zaka'dauki nauyin bata da hannunka dan haka be ma 6ata bakinsa ba, yasan idan taji yunwa zataci ne dolen ta ai tunda ita yunwa ba sabo ne da ita ba. Har suka 'kare cin abincin be ce da ita komai ba haka itama. Ranar kam Abbas be fita ko'ina ba har aka 'kira sallar azahar yana gida, sai de duk da agidan yake amma kowa na 6angaren sa babu wanda yaje wurin kowa. Kafin azahar 'din Teemah tayi wankan tsarki ganin cewa period 'din ta ya 'dauke, dama 4days takeyi. Shi kuma lokacin da yayi alwala zai fita sai yabi ta wurin ta inda yazo dan sanar da ita fitar sa sai kuma ya tarar da ita tana sallah, be jira ta idar ba ya wuce kawai abinsa dan ba yaso jam'i ya wuce shi. Bayan sun fito ne ya 'kira ta awaya dayake yasan wayar natare da ita yace mata shi yafita kuma ba zai dawo yanzu ba, yace m za'a kawo mata abinci sai ta kula idan taji door bell taje ta anso kuma ta tabbatar ta rufe jikin ta da mayafi kafin ta fitan kuma bece ta fita ko da harabar gida bane. Daga 'karshe dan ya sake tunzura ta sai yace " _zanje in dubo Zahra ta ne kwana biyu bana samun ta_ "! Teemah ta6e baki tayi tare da fa'din " _uhumm sai ka dawo_ " Koda ya yanke 'kiran kuwa abin yaso ya dameta dan sosai ya tsaya mata azuci amma sai ta tambayi kanta dalilin damuwar sai ma taga laifin tane na shishshigin damuwar, miye ruwan ta toh da al'amarin sa ai yace itace farin cikinsa toh ita miye nata. Tilastawa kanta tayi 'karfi da yaji ta ya'ki zuciyar ta dole ta kawar da tunanin Zahran Yayah aranta sai de duk da haka lokaci zuwa lokaci tana sake tunawa. Kamar yanda ya fa'da mata haka tayi domin tana jin 'karan door bell tafita bayan ta zun6ula hijabin ta wadatacce babbah da take sallah dashi. Driver ne yakawo sai ta kar6a bayan ta gaida shi tare da kawo masa coolers 'din safe sannan tace da shi kar ya kuma kawo wa anjima wannan ma ya isa. Ciki ta koma tana me jinjinawa 'ko'karin Ummah sosai gashi kullun abincin yawa yake yi musu idan sunci ne ma sai Abbas yayiwa mai gadi magana yazo ya tafi da sauran gaba 'daya ko ya yake yi dashi ma oho, ita dai nata kawai wanke warmers 'din ne. Zama tayi a parlour kawai tare da 'kiran layin Ummah tayi mata godiya da kuma bayanin abincin sannan ta yanke 'kiran. Bata ko sake bi takan abincin ba taci gaba da duba wayar ta. Abbas kuwa har se da yamma ya dawo gidan ya kuwa zo mata da fruits masu yawan gaske. Daya duba abincin shima sai yaga ko ci batayi ba, yariga yasan hakan amma na yau 'din sai yayi tunanin ko harda fushin Zahra ne, dan gudun kar ya shiga ha'k'kin ta da yawa daya watso ruwa bayan ya shirya sai ya fito yace tazo tayi serving nashi abinci. Sai da ta wuche kitchen ta 'dauko plates 'daya da table spoon 'daya sannan ta dawo ta zuba masa abincin dai-dai shi tare da 'dauko masa lemonjuice da ruwa harda fruits 'din da ta gama yanyan kawa tasa afridge ya 'danyi sanyi domin kanta duk ta kawo masa ganin fried rice yau aka kawo kuma nada mai'ko sosai. Tana shirin mi'kewa yadakar da ita inda yayi mata nuni da kujera. Sam batada ra'ayin cin abincin musamman data ga ma cewa shinkafa ce wannan kuma bata cikin ra'ayin ta shiyasa koda zauna 'din ma sai ta na'de hannu kawai tayi shiru tana tunanin 'kila so yake ta taya shi zama. Spoon 'daya, biyu yakai bakin sa na ukun da ya 'debo sai ya nufo bakinta dashi. Teemah cikin idanunsa ta kallah sai yayi kamar be ganta ba hakan yasa ta dawo da idanun ta kan hannun sa dake ri'ke da spoon 'din tare da bu'de bakinta ta kar6a. Sai da yaga ta ha'diye sannan yace " _bakya son cin abinci ko? Idan Zahra ta tazo raina ki zatayi dan kuwa ita_ ' _katuwa ce nikuma babu ruwa na_ " Take tayi fushi ta tura baki harda 'dan hararan sa ka'dan. Murmushi Abbas yayi kawai amma na gefen baki be kulata ba yanzun dan so yake ta 'dan ci abincin koma ka'dan ne shiyasa kawai ya shareta. ***** Washegari da asubah da ya tashi sallah sai itama ya tashe ta ganin tafara yi, amma Teemah ta'ki ta tashi sai ta ringa juye-juye. Har yaje yayo alwala ya fito bata tashi ba da yaga zata 6ata masa lokaci sai ya sa hannu ya 'dago kafa'dun ta ya ta data zaune wanda hakan yasa dolen ta tashi tare da bu'de idon ta. Sai yace " _ki wuce kiyo alwala idan kika 6ata min lokaci Allah zan 6ata ranki kema_ " Tanajin haka dolen ta ta mi'ke tana gunguni bata da'de abayin ba tafito bayan ta 'dauro alwalan. Abbas ne ya mi'ka mata hijab babbah daya 'dauko a'dakin ta ta kar6a ta sanya tare da bin bayan sa yajasu sallar asubah tare da 'daukan dogon lokaci yana addu'o'i tun kan su shafa Teemah take layin bacci suna shafewa kuwa ta koma gado ta du'kun'kuna cikin hijabin ko cire shi batayi ba sanadiyyan sanyin da ke tashi ka'dan-ka'dan da safiyar. Abbas kam Al-qur'ani ya 'dauko ya 'dora da karatu tsawon lokaci sannan ya kammala. Zuwa lokacin kuwa ruwan sama ya sa'k'ko sosai ganin hakan shima sai ya kishingi'da ya lumshe idanu yana me tasbihi ga mahallici. 'Karfe takwas da 'yan mintina Teemah ta farka daga bacci, jin ruwa na sau'ka yasa ta yin luf sosai take jin sha'awar shiga ruwan amma tarasa yanda zatayi dan tasan Abbas ba barinta zaiyi ba, juyawa tayi ta kalleshi sai taga kamar yana bacci ganin haka yasa da sauri ta fincike hijab 'din dake kanta ta ajiye. Cikin san'da ta ta kama hanyar barin 'dakin dama Teemah gwana ce wurin son wasan ruwa Allah-Allah take tagan ta cikin ruwan nan musamman ma da yanzu ya 'dan tsagai ta ka'dan. Abbas idanunsa biyu babu baccin dayake yi duk kuma abinda take yi yana kallon ta sai da yaga ta kama hanyar barin 'dakin ne yayi tunanin ko wani rashin ji zatayi dan haka sai ya dakatar da ita da fa'din " *ZAHRA* ! Cak ta tsaya a inda take amma bata juyo ba shima kuma be sake magana ba idanunsa yasake lumshewa tamkar wanda ba shine yayi maganar ba. Teemah kam jin be sake magana ba yasa ta waigowa sai taga still baccin sa yake yi sai tayi tunanin 'kila ko cikin baccin ne yake 'kiran Zahran sa amafarki murgu'da baki tayi. Taso ta koma ta tashe shi a baccin kodan ya daina mafarkin Zahran ma dan ta 'dan ji wani iri sanadin hakan amma jarabar son ta shiga ruwan sai ya fi rinjayar ta kawai ta juya. Abbas ma sai ya 'kyaleta kawai tatafi. Cigaba tayi da tafiyar ta ta isa har kofan parlourn ganin a kule da security lock yasa ta koma tabi ta baya tafita ta 'kofar kitchen. Da farko hannayen ta tasa tana taran wanda ke sakkowa daga bakin roofing tana tara tana watsa shi afuskan ta tana murmushi, data ga hakan baze mata ba sai kawai tafara 'ko'karin shiga gaba 'daya. Caraf taji an ri'ke mata hannu daga baya wanda ya matu'kar firgita ta domin bata ji zuwan mutun ba ita. Arazane ta juyo sai taganshi take kuwa ya janyo ta zuwa jikin sa yana kallon cikin idanun ta yace " _Kinyi ajiya aruwan ne_ ? " _Umm- umm_ " Tace da shi tana 'kif-kif da idanu. " _Toh me zakiyi_ ? Yasake tambayarta. In ina tafara tarasa me ma zata ce dashi sai yace " _ina jinki_ " Ahankali tace " _wanka... zan..yi ne fah....Yayah_ "! " _Shower ya lalace_ _ne_ ? Ya tambayeta Jijjiga mai kai Teemah tayi ranta har yasoma 6aci dan tasan ba barin ta zaiyi ta shiga ruwan ba tunda ya fito. Sai ya sake fa'din. " _bathtub fah_ ? Da muryar shagwa6a tace " _Yana nan_ " " _Bazakiyi ba toh, wuce muje bana son rashin ji_ " Kalar tausayi tayi tace " _Ayyah Yayah ka'dan fah zanyi.........._ " Kafin ta rufe baki ma ya tare ta da fa'din " _i said bazakiyi ba ko?.....ko ni sa'an ki ne dazan na magana kina jayayya dani_ ? _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* ๐Ÿ˜ [10/13, 1:56 AM] ๐ŸŒธSalmerh๐ŸŒธ: ๐Ÿ’• *CAPTAIN ABBAS* ๐Ÿ’• By *Salmerh MD* Luv story๐Ÿ˜ *Wattpad @* *Serlmerh-md* ๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* ๐Ÿ’ซ We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ๐Ÿ‘Ž๐Ÿป Wannan page 'din naku ne 'yan group *CAPTAIN ABBAS FANS 2* Allah sosai nake jin da'din Comment da conversation 'dinku ina matu'kar jin da'di, koda ace my ka'dai nake dashi nasan labarin CAPATIN ya isar, wannan page 'din naku ne kuyi yanda kuke so dashi.. ๐Ÿฅฐ *Bismillahir rahmanir raheem* _Never expect things to happen. Itโ€™s better to feel surprised than to feel_ _disappointed_ . ๐Ÿ…ฟ *81* Rausayar da kanta tayi gefe tana kallon shi, Abbas baya son taga kamar yana matsa mata ne dan haka sai yace " _owk, zan barki kiyi amma make sure that mura na kamaki ba sassauci Anty nurse zan'kira ta ringa yi miki_ _injections har sai muran ya tafi...kin yarda_ ? Tana jin haka ta karya mai kafa'da alamar bata yadda ba. Abbas sakin ta yayi tare da nuna mata hanya yace " _Toh oyah go inside!_ " Dolen ta ta shigo ciki tana 'kun'kuni 'kasa-'kasa, shima Abbas take mata baya yayi bayan ya rufe 'kofar. Teemah 'dakin ta ta wuce cikin fushin an hanata wanka inda tana komawa 'dakin ta hau cire kayan dake jikinta dan sun ji'ke sosai. Sai da ta cire su gaba 'daya kafin ta nemi towel ta 'daura ajikin ta sai ta shiga bathroom 'din ta ta cika bathtub da ruwa ta shige ciki afili ta furta " _in ka hana wancen ai baka isa ka hanani shiga wannan ba, mutun_ _kullum sai de ya hanaka rawan gaban hantsi.....abu ka'dan sai ya wani ce injection! Wannan da ace shine yake yin alluran ai da anshiga uku nasan da kullun sai ya min goma ko.biyar dan mugunta! "_ Ta 'karshe da jan tsaki daga 'karshe. Abbas ma a parlour ya zauna inda ya 'dau lokaci yana amsa waya sai da ya gama kafin ya wuce ciki dan watsa ruwa be ko sake bi ta kanta ba. Teemah kuwa ta jima cikin ruwan hankalinta kwance sai da ta fara jin hanjin ta na motsi ne sannan ta fita aruwan tayi wanka mai kyau tafito. Koda ta fito sai ta tsaya kuma ta 'debi wayarta dana Mahmud ta zauna bakin gado, layin Umar ta nema cikin wayar marigayin ta'kira shi lokacin 'karfe sha 'daya ta wuce sosai 11:42am. Umar yayi mamaki sosai data 'kirashin ya kuma ji da'di musamman dayake shima Maman Amal na yawan damunsa akan batun Teemah. Nan yayi mata al'kawarin zai ha'da su da zaran ya koma gida. Cikin hanzari ta shirya tare da kwaso wayoyin harma dana Mahmud saboda sauri ta fito dan nemawa cikin ta dake 'kugin neman agaji mafita. Turus taja ta tsaya ganin babu komai akan dinning, bata 6ata lokaci ba sai ta wuce 'dakin sa ta same shi yana sa kaya shima. Bata damu da yanayin dayake ba ta isa wurinsa ta ha'de goshi ta ita adole tana fushi dashi tace " _Yayah nifa yunwa nake ji kuma banga komai a dinning ba_ "! Be kalleta ba yace " _Ya za'ayi kenan_ ? _dama nace a daina kawowa ne saboda bakya ci....._ "! Da sauri ta tare shi da fa'din " _inaci mana bagashi yanzu ma ina jin yunwa ba_ " Kwafa yayi yana kallon da ta gira a'dage jin yanda tayi maganar, cikin salo yace da ita " _Harda fa'da ne kuma_ ? Baki ta tura gaba ta kauda kanta tace " _Ni ba fa'da nayi ba ai yunwa nake ji ne shiyasa_ "! Cigaba yayi da 6alle bottuns 'din longslip 'din daya sanya ajikinsa yace " _Sai kije kitchen ki samu abinda zakici ko noodles ma ki tafasa kici zaifi sauri_ " Dan haushi ma Teemah ko jira ya gama maganar batayi ba tafice abin ta, jitayi badan yunwa na damun ta ba da babu abinda zai sata shiga kitchen yanzu. A parlour ta ziba wayoyin dake hannun ta sannan ta wuce. Koda ta shiga kitchen 'din kuwa sai ta wuce fridge ta 'dauko fruits ta gyarashi ta hau sha har da zaman ta kan stool 'din dake cikin kitchen 'din. Sai da ta 'danji dama-dama acikin ta kafin nan ta kunna gas ta dafa indomien ta dai-dai cikin ta tajuye a plate tarufe da wani plate 'din harda 'dora forkspoon 'din ta akai, sannan tayi mixing fruits tayi juice 'din ta 'dan dai-dai a 'kasan glass jug da extra cup 'daya batare da wani 6ata lokaci ba kuwa ta kammala duka tafito. Kan dinning taje ta ajiye su sannan takoma kitchen 'din domin kimtsa shi dan bata son idan tafita tasake dawowa dan kim tsawa ba. Batafi 9mins a kitchen 'din ba ta kammala tafito da ruwan ta mai sanyi a hannunta kawai sai idanun ta ya sau'ka akan Abbas yana siffing mata drink 'din data ha'da cikin kwanciyar hankali kamar ance shi aka ajiyewa abincin. Ga plate 'din abincin ta ma bu'de a gabansa da ga dukkan alamu yana kan ci ne. Turus taja ta tsaya dan haushi ma sai tarasa me zata ce dashi, shima sai yayi tamkar beganta ba yaci gaba da cin abincin cikin natsuwa. Data ga haka ne sai ta taho da sauri har idanun ta na tara ruwa dan takaici sai ta tsaya agaban sa tace " _Yaya abinci na ne fah_ ! Gira 'daya ya 'dage ya kalle ta sai ya kuma kallon abincin yace " _really!_ ? _Ai ban sani ba ne i thought nawane kika ajiye min ai_ " " _Ai baka ce min zaka ci ba_ "! 'Da, zaro idanu yayi yace " _Au sai ma na fa'di zanci kafin adafa dani_ ? Shiru tayi masa bata yi magana ba sai hawayen ta da suka gangaro, harga Allah yau 'din yunwa takeji sosai kuma tayi niyyan cin abincin ta sosai take son jin wani abu acikin ta. Ganin tafara kukane yasa yayi murmushi tare da janyo hannun ta ya zaunar da ita kan kujerar kusa dashi, be yi magana ba sai kawai ya 'debo abincin ya nufo bakin ta dashi. Babu musu Teemah ta bu'de bakin ta ta kar6a. Sai yayi mata murmushi aransa yace da din waya gaya miki Borno gabas take? ai yunwa maganin kowani fitinanne ne yasan badan taji yunwa ba da yau 'din yanda tayi fushi dashi 'din nan dako kulashi ma bazatayi ba sai gashi kuma har abinci yabata abaki kuma ta kar6a, afili kuwa sai yace da ita" _ni ban ta6a ganin inda mata ta hana mijin ta abinci ba sai_ _yau awurin ki! wato cikin ki ka'dai kika sani ko?_ " Shiru taui kamar bada ita yake ba sai ma kauda kanta da tayi gefe, Abbas sai ya sake 'dibowa ya mi'ka mata itama sai ta bu'de baki ta kar6a. Sai daya bata kusan spoon biyar batare da yaci ko 'daya ba data kar6i na biyar 'din ne sannan cike da tsokana yace da ita " _cinye abinki tunda bakya so inci nima zanje wurin Zahra ta ta dafa_ _min_ " Tsayawa tayi tana kallonsa shima kuma haka dan kawai ta tabbatar da abinda yace 'din, ganin hakan shima ya tsare ta da idanu sai ta kauda nata idon ta maida shi gefe, duk iskancin ta da rashin jinta bazata ta6a iya kallon kallo da shi na tsawon lokaci ba, sosai kwarjinin sa ke karya mata zuciya, tsawon mintina kusan biyu babu wanda ya furta komai acikin sannan Teemah ta ha'diye abincin dake bakinta ahankali. Yana shirin 'kara 'debowa sai ta yi sairin rike mai hannu, bata kalle shi ba koda yabi ta da kallon mamaki ma bata san yayi ba, dan ita plate 'din abincin take kallo. Kar6i spoon 'din tayi ta 'dibo abincin tayi dauriyan kai masa bakin sa batare da ta sa idanun ta cikin nasa ba, Abbas kuwa sai ya'ki bu'de bakin sai ma kauda kansa gefe da yayi. Hakan ne yasa ta kalli idanunsa sai ya'ki bata hankalinsa. Cak ya mi'ke tsaye ya koma cikin 'dakin sa domin tsabtace bakinsa. Teemah tamkar statue haka ta zauna ri'ke da spoon a hannu sai ta rasa me yake mata da'di, Abbas be da'de da shiga 'dakin ba ya fito hannunsa ri'ke da makulli ko kallon inda take be sake yi ba ya kama hanyar barin 'dakin. Ganin haka yasa Teemah ta mi'ke da hanzari cikin sassanyan murya ta ce da shi " _Yayah wurin Zahran zaka tafi_ ? Da " _umm_ " kawai yabata amsa batare da waigo ba, yana me cigaba da tafiyar sa ahankali. " _Nima zan bika_ " Ta sake cewa da shi wanda jin hakan ne yasa shi waigowa ya kalle ta dai-dai lokacin kuma sai waya ta 'dau 'kara daga cikin parlourn dukkan su sai hankalin su ya koma wurin. Teemah ce taje da sauri dan tasan ita ta ajiye waya a parlourn, hannu tasa ta 'dauki wayar hannun ta har na rawa dan yanda zuciyar ta ta tsinke tun daga jin 'karan ringing 'din dan tasan ba wayar ta bace ta kuma riga tasan kalan ringing 'dinsa tun yana raye, gani tayi number ce ba suna. Aduk lokacin data ga wani abu daya danganci Mahmud sai ta tuna da shi balle wannan daya kasance 'karan wayar sa ne da ta saba ji atare dashi tuni sai ya sa zuciyar ta bugu cikin sauri. Kafin tayi wani yun'kuri har wayar ta tsinke. Abbas ma ganin wayar da kuma yanayin data shiga yasa hankalin sa ya dawo kanta shima ahankali ya dawo baya ya tsaya nesa da ita ka'dan yana sake karantar yanayin ta, be san wayar waye ba ce kuma yasan ba tata bace dan yariga yasan nata dayake shine da kansa ya canja musu bada jimawa ba ita da Hannah iri 'daya. Take wayar tasake 'daukan wani 'kara wanda yasa Teemah sai da ta danganta jikinta da kujera kafin ta iya amsa 'kiran tana me danne hawayen ta ta kai wayar kunnan ta da rawan jiki. Shiru tayi tana sauraran me ake fa'da mata wanda tuni hawayen tan suka kasa tsayuwa suka gangaro kan kuncin ta. Ganin haka yasa Abbas ya 'karaso kusa da ita ya kai hannu ya cire wayar akunnan ta ya ha'da ta da kunnansa. Yin hakan keda wuya sai Teemah ta fa'da jikin 'kafafunsa ta rungume 'kafafun tana mai cigaba da kukan ta. Yana sada wayar da kunnan sa yaci gaba da saurara batare da ya furta komai ba. Sai yaji ana fa'din"............ _kullum na'kira bana samunka yalla6ai_ _sai yau dan Allah kazo ka duba aikin daka bani, inaso in gaya maka cewar Innah_ _na cikin farin ciki yanzu ha kama yaranta kuma tanaso ta gode maka bisa_ _taimakon dakayi mata amma bama samun ka shiyasa ta damu, ni ma_ _kuma ina so kazo kaga aikin daka bani jagoranci bansani ba kona yi_ ' _ko'kari"_ __ ! Abbas be san kan maganar ba be kuma san inda ta dosa ba, tunda baiji farkon ba kuma ko yajin ma be san waye akan layin ba amma duk da haka sai yace dashi " _Allah yayi wa mai wayar rasuwa tun ba yau ba, amma karka damuni dan uwansa ne kuma insha Allahu zanzo kwanan nan idan nasamu lokaci... yama sunanka_ ? Jikin Rabi'u sosai yayi sanyi ya rinka maimaita innalillahi wa inna ilaihiraji'un....Daga 'karshe ne ya sanar da Abbas sunansa tare da jero adduoi wa marigayin. Da " _Ameen-Ameen_ " Abbas ya amsa

Chapter 48 of 67