Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
salma na yaba maki da wannan novel naki mai suna *captain Abbas* Allah ya kara basira ameen summa Ameen. *From* _Abubakar Saleh Al~Quyraemey_ *Ngd 'dan uwa, i really appreciate....nd i dash ths page specially 4u where ever u ar*👍 😍 *Dr.Khausar* Allah ubangiji ya baki lafiya ya kuma albarkaci baby ya sa ta cikin bayinsa salihai.( *AMEEEN* ) *Bismillahir rahmanir raheem* _Every heart has a pain......only d way of expression is different.....some hide it in eyes while some hide it in their smile_ 🤞🏻 🅿 *90* Kwance take akan kujera mai zaman mutun uku jikin ta da wata rigar bacci sharara mara nauyi, rigar 'yar 'karama ce dan ko cikin ta bai gama rufe wa ba sai 'dan wandon rigar mai d'an fad'i da ka'dan ya wuce mata gwiwa shima, sosai take jin da'din kayan dan rashin nauyin su da kuma yanda take sakewa cikin sa idan ta sanya su. Yayin da Abbas ke zaune facing nata akan wata kujerar daban yana kallon CNN gaba 'daya hankalinsa na kai ganin an kai hari ma wani 'kauye inda aka yi musu kisan gillah manyan su da yaransu kuma gwamnati takasa yin komai akan hakan, abin haushi yake bashi na yanda ake 'daukan rayukan al'umma batare da wani 'kwa'k'kwaran dalili ba tamkar baza'a mutu watarana aje fadar Allah domin kar6an ayyuka ba, mutane mantawa sukeyi da hakan...... time to time yana sipping mango juice da Teemah tayi masa 'dazun nan. Hannun ta 'daya na kan cikin ta sai aikin shafawa takeyi a hankali tana lumshe idanu tana feeling yanda cikin nata ya 'dan d'ago ka'dan wanda tun ba yau ba ta fahimci hakan, hatta Yayah ma sai da ya tsokane ta akai last three days wai Fatee bombom mai tummy, ta kuwa ji haushi sosai dan ranar kuka ta ringa yi masa kafin da 'kyar ya daina tsokanan nata amma sai ya cigaba da yi mata dariya. Ita kanta ma ba so take yi ba abin na bata haushi sosai, musamman da yake tasan cewa ba komai ne ya jawo mata hakan ba face yawan cin abincin nan da take yi. Murmushi tayi lokacin da ta tuno yanda kwa'dayin awaran 'kwai ya sa ta a gaba 'dazu da rana lokacin ita 'daya ce a gida Abbas na office, sai ta tashi taje ta ha'da komai ta yanyan ka 'kwan bayan ta dafa shi sannan ta sake ka'da wani 'kwan ta wadata shi da albasa da da 'dan maggi dan yanzu bata fiya son taji 'dan'danon gishiri abakin ta ba, tafiya son tajishi da nisa sama-sama, in abinci ya kasance hakan kuwa har wani santi yake sata tana jin da'din sa sosai. Dududu da 'kwai biyar tayi amfani har ta gama. Sauce tayi na zallan attaruhu da shima yaji albasa na fitan hankali da spices ta harhad'a abinta a plate tazo ta ajiye, bata ma tsaya a parlour ba sai ta wuce 'dakin ta da abincin, bata bu'katan wani juice a lokacin ruwa kawai take jin ya isheta dan haka sai ta 'dauko mai 'dan sanyi ta shige ciki. Har Allah-Allah take yi taji shi cikin bakin ta dan yanda take jin kwa'dayin nasa abin har na bata mamaki. Bata 6ata lokaci ba ta fara aikawa dasu bakin ta inda da'din sa ke ratsa mata har cikin zuciyar ta tare da sauk'ar mata wani nutsuwa na bam mamaki irin rai ya samu abinda ke so d'in nan kuma at d right time. Ci takeyi a hankali tana korawa da ruwan sanyin ta, in kaga yanda ta nutsu take cin abincin har zakayi zaton ko shine abu na farko da yafara shiga bakin ta a yau 'din. Sai dai bata ko ci rabin sa ba taji lokaci d'aya amai ya yun'kuro mata, ido ta zaro ta tare da gumse bakinta da k'arfi tana mamakin silar faruwan hakan sai taji ya sake yun'kuro mata da karo 'daya ai bata san lokacin da ta ajiye plate 'din agefe ba tayi cikin bathroom, amai ta ringa kwarawa har sai da ta amayar da duk abinda ke cikin ta a lokacin sannan ta fara sau'ke numfashi. Sosai taji ta galabaita sai ta jingina bayanta da jikin sink 'din tana maida numfashi bayan ta tsabtace wurin. A hankali ta fito daga bathroom 'din tazo ta zauna a parlour kan kujera tana sauke numfashi har da 'dan tattaba wuyan ta zuwa jikin ta wai ko zataji tashin zazza6i amma bata ji komai ba banda d'umi da jikintan ke dashi, wannan kuma tasan ba sabon abu bane awurin ta, kusan kullum haka jikinta yake...." _to me ya kawo hakan kuma_ ? Ta tambayi kanta. Bata raba d'ayan biyu wannan cinye-cinyen da takeyi ne ya kawo mata hakan. D'an k'aramin tsaki taja a hankali tana yawo da kanta gefe da gefe tana sau'ke hawaye tare da tuno yanda tun farko ta tsinci kanta tsundum cikin son cin abinci na fitan hankali, ita kanta bata son hakan amma tarasa ta yanda zata daina shi, ko tace zata 'ki ci ma bata iyawa, coz wani lokaci har bata tunawa da batun bari 'din har sai ta gama ci, sosai ta gaji da wannan rayuwar, gashi yau abinda hakan ya jawo mata har da she'ka amai, tasan Yayah na jin wannan labarin to ko ta'ki ko taso sai ya kaita clinic ita kuwa tsoron kar ace za'a yi mata allura ya sanya ta ja bakin ta tayi gum. Kafin ma ya dawo ta warware ras kamar ba ita ba shiyasa sam Abbas bai fahimci komai tattare da ita ba, balle da ya samu ta tanadar masa 'kayataccen girki ai sai ya ringa sanya mata albarka kawai yana cin abincin sa. Teemah tana ta murmushi, abinda yasa yake birgeta kenan, ko da kuwa bata jin da'di ko kuma wani abu makamancin hakan takan daure ranta tayi masa abinda yake so, sam bata samun natsuwa har sai taga ta tanadar masa abinci kafin nan, ba dan komai ba kuwa sai dan yanda yake yabawa da hakan a kowani lokaci baya raina girkin ta idan tayi masa koda kuwa wani iri ne, yana matu'kar nuna mata jin da'din sa idan tayi masa abu musamman girki. Sai itama ta zauna ta sashi a gaba tana zuba 'kayataccen murmushi har suka bar table 'din cin abincin. Har zuwa dare bata sanar da Abbas batun aman da tayi ba, yanzu kuwa da take ta faman shafa cikin ta sai take 'kara jin haushin yanayin saboda yanda duk take ganin ya sauya mata abubuwa da dama na jikinta da kuma tsarin rayuwar ta ma gaba 'daya. Hannun ta nakan cikin nata har yanzu, tana kan shafawa har zuwa marar ta da taji ya 'dan yi mata tauri ya dunkule wuri guda, kawai sai hawaye ya sau'ko mata sirara masu 'dumi da bata san asalin silan sau'kan su ba. Take kuma sai taji wani matsancin son Fresh milk na asalin fulani ba na company ba ya taso mata sai ta rintse idanu da 'karfi. Ta so ta basar amma ina zuciyar ta wani irin son nonon yake yi mata da bazata iya hawa kai ta zauna ba sosai take jin son sha har a bakinta. A hankali ta d'ago kai ta kallo shi daga inda yake ya zaune, sai ta tashi ta zauna ta fuskance shi. Abbas bai 'dauke idanun sa daga abinda yake yi ba duk kuwa da yaga ta tashi ta zauna tana kallon shin dayake facing juna suke yi so yana kallon ta, zaton shima already tayi bacci dan babu wadataccen haske a 'dakin. A hankali ta 'kira sunan shi sai ya amsa da " _Inajin ki 'yan matan Yayah ya akayi_ ?" Yayi maganar batare da ya juyar da kansa ya kalleta ba. Sai tace " _Yayah dan Allah fresh milk irin na fulanin nan nake so_ " Abbas cewa yayi " _ki bari gobe idan Allah ya kaimu za'a nemo miki"_ K'afa ta shura tare da zun6ura baki cike da sakalci tace " _sai gobe kuma Yayah? ni fa yau 'din nan nake so... tun fa 'dazu banci komai_ _ba kuma yanzun yunwa nake ji shi nake son sha_ " Sosai ta marairaice tayi kalan tausayi ha'de da shagwa6a, Abbas yanzun kam ido kawai ya zuba mata har ta kawo k'arshen maganar tata, yanda tayi 'din sai ta bashi tausayi har ransa amma daya ke yana ganin kamar iskancin nata yayi yawa sosai ne da har zata ambaci abinda tasan sai an nemo shi da wannan daren.... sai shima ya ha'de rai a cikin ransa ya tambayi zuciyar sa. A ina zai samu? Yaso ya balbale ta amma daya tuna halin rigimar ta sai ya saki wancen layin dan baya so abin yayi tsayi. Cikin natsuwa yace da ita " _Zahra da wannan daren ina zan samo miki wannan abin plz....ina ce ni dake ne a gidan tun 'dazu me yasa baki fa'da min tun 'dazun ba an nemo miki_ _kika bari har sai da daren nan ya kike so inyi ne ke kam? Ki duba fa almost 9mins to 10 ki ringa abu da lissafi plz_ ? Sai cewa tayi " _ai d'azun bana so ne, yanzu ne na fara son sha_ " " _Hmm_ " kawai Abbas yace yana kallon ta tsawon da'ki'ku yana tunanin halinta, yarinyar nan is so rude sosai abin yake bashi haushi........sai da ya gama karantar yanayin ta sannan yace " _owk...naji aike ka'dai ce kika isa da haka amma ki bari idan Allah ya_ _kaimu gobe insha Allahu zan kawo miki har sai ya_ _ishe ki_ " Yayi maganar da sigar lallashi dan har ga Allah shi ba son fita yakeyi ba a wannan lokacin. Teemah kam da jin ya ambaci goben sai ta sanya masa kuka ta taso ta dawo gefen sa ta zauna ta kama 'dayan hannun sa ta rungume shi ajikin ta tana squeezing 'dinsa tana fa'din ita yau take so dan Allah ya nema mata" Hayaniyan kukan ta da kuma na TV sai ya sanya shi cikin wani hali sosai ya nemi nutuwar sa ya rasa. Allahn da take ta ambata cikin maganar ne yasa shi fahimtar dagaske takeyi, sai ya kai 'dayan hannun sa ya 'dauko remote ya rage volume 'din TV sannan ya samu 'dan nutsuwan rarrashin ta yace " shikenan.....ba fresh milk kike so? Sai ta 'daga kai Yace "Ai akwai a fridge kin manta akwai wanda nakawo jiya?" Sam shima ya manta ne har ya bar ta tana ta masa rigima. Ga mamakin sa sai yaji tace "ai nasan da shi ni ba irinsa nake so ba" Abbas kwafa yayi yana kallon ta sai yace "Yanzu dan ba kya sona sai ki yadda na fita da daren nan? Shiru tayi masa kawai tarasa mai zata ce, ganin haka sai ya fara 'ko'karin mi'kewa yace "bari inje to, amma idan kika ji shiru ban dawo ba babu ruwana nikam kinji" Zuciyanta ne ya tsinke da k'arfi wanda take Mahmud ya zo ranta sai ta rintse hawaye ya sau'ko mata sirara take kuma sai ta sake bu'dewa ta sau'ke su akansa lokacin ma har ya kusan barin dakin ba dan ma girman da parlourn ke dashi ba da tuni ya 6acewa ganinta. "Yayah! ta ambata sai cak ya tsaya tare da waigowa a hankali ya dubeta hasken TVn dake haskawa ne yasa yake ganin ta da hawayen ta. Sai ta tashi da gudu taje ta rungume shi shima take ya sar'ke hannun sa ajikin ta. Teemah a hankali ta furta " don't leave me please Yayah kaji, na fasa shan milk 'din just stay with me" Abba bai yi magana ba sai ya sake hugging nata tied. Shiru ne ya 'dan ratsa wajen na tsawon mintina sannan Abbas ya fara 'ko'karin rabata da jikin sa Teemah kam ta zaci tafiyan zaiyi dan haka sai ta'ki sakin sa cikin muryar kuka tace "....Yayah...plz...dnt go" "I ll not Zahra i'm here with u kinji? Jin haka ne yasa ta sakin sa sai ya kama hannun ta suka koma suka zauna hawayen ta share mata batare da magana ba while takasa daina kukan wanda tunanin rasa shi yasa hawayen kasa tsayuwa mata. Fuskarsa ya matsar kusa da nata sai ta lumshe idanu a hankali sai ya ha'de bakin su. Tsawon mintina biyu yana bata passionate kiss sannan ya saki bakinta sai ta komar da kanta ta kwantar jikin hannun sa. Abbas murmushi yayi yace " kukan fa na menene bayan kin requesting abu kuma zan miki nd why all dis? "Nafasa" tace a hankali. Sai yace "dalili" Cewa tayi "Saboda bana so ka tafi ka barni" "Karki damu zan dawo ai bazan da'de ba kinji" "Nidai ah ah" tace tare da tashi ta zauna ta fuskance shi. ".....i insist" Baki ta dano gaba tana kallon fuskar shi tare da 'kif-'kif da idanuwa. Sai yayi murmushi Yace " wai me kike tsoro ne tell me?" Cike da shagwa6a tace "ai kaine kace in katafi bazaka dawo ba" "Hmmm.... matsoraciya kawai...ni ai wasa nakeyi miki, kuma ma in kina tsorn hakanne an gaya miki akwai abinda yake shiga tsakin rai da mutuwa ne?....abu 'daya ne shine lokaci bayaga haka kuwa...."sa ya juya kansa left& right yace " babu wani abu...ki bari yanzu zan dawo kinji insha Allahu zan kawo miki" Yana fa'din haka sai ya mi'ke Teemah da sauri ta kamo hannun sa ta ri'ke tare da sau'ke hawaye tana jijjiga mai kai idanun su cikin na juna. Abbas sai ya koma ya zauna gefen ta sannan ta saki hannun sa, sai ya kalli hannun sannan ya kalle ta hawayen ta har yanzu hawayen ta na cigaba da gudu. Sai ya sa hannun sa yayi knocking goshin ta kad'an yace " ur sturbborness is always increasing....oyah stop crying nd tell me how u ll miss me when i'm not around" 'Kirjinsa ta fada tare da kai masa bugu a hankali cikin shagwa6a tace " ni dai ba ruwana" Murmushi Abbas yayi wanda har ha'koron sa suka bayyana. A saman la66ansa yace "silly girl" Sannan ya kai hannun sa akan batanta yace "kin san wani abu? sam bana son kukan nan nd seriously bana son ki haifi baby mai irin kukan ki, i need a little soldier just like me a hero nd my little princess" Murmushin yasata itama dan jin dadin wai duk ita zata haifi wannan harma bata san lokacin da bakin ta ya furta "Yayah to yaushe zan haihu? Abbas cewa yayi "Tashi in gaya miki" yana maganar yana 'dago ta daga jikin sa. Dariya tafara a hankali tare da k'ank'ame shi sosai. Shima Abbas dariyar yayi sannan shiru ya dan ratsa wajen. Abbas ne ya yanke shirun da fa'din " "tashi ki mi'ka min phone 'dina" Tashi tayi ta 'dauko wayar ta bashi sannan ta koma gefensa ta zauna tayi shiri tana kallon sa ganin ya maida hankalin sa ga wayar. Numbern wani friend dinsa ya 'kira wanda shima yake nan cikin barikin, sun rabu dazu da yamma akan zaije night party 'din wata babe 'dinsa dake birthday yau a hotel. Christian ne shi kuma bashi da aure sunan sa Samuel amma da Sam ake 'kiran sa. Koda Abbas ya 'kira shin kuwa tambayar shi yayi ko ya dawo sai ace "ah ah but he is about to" Abbas bayani yayi masa na abinda yake so 'din da sunan shi tare da sanar dashi inda zai mu nan kan hanyar da zai 'dauko zuwa gida ba sai yayi yawo ba. Take Sam ya yi masa al'kawarin siyowa sannan sukayi sallama. Abbas nada tabbacin matu'kar samuel ya samu dama zai cika al'kawarin sa musamman da yake cewa ya san baya shan hiya so cikin hankalin sa zai dawo. Bai wuci 40mins da yin wayar ba kuwa sai wayar sa ta 'dauki 'kara, ganin Sam ne sai ya tashi tare da 'daukan wayar ya fita harabar block 'din nasu wanda anan ya hadu da Sam, hannu suka sha sannan ya bashi sa'kon. Abbas sosai yaji da'di, koda ya ciro kudi ya bashi kuwa Sam 'kin kar6a yayi kawai yayi gaba abinsa. Abbas ma sai ya koma ciki yana 'kara maimaita tunanin abin a ransa, murmushi yayi 'dan ta k'aitacce yace " _Zahra rigima_ "! Teemah kuwa duk da haka sai taso ta kawo masa rigimar ita ba na company take so ba ai ta gaya mishi, sai yace "yanzu kam sai kizo ki tsotse ni Zahra k'ila hankalin ki zaifi kwanciya tunda ke ba'a miki gwanin ta, banyi kokari bane ko da da daren nan a ina zan samo miki wancen?" Ita kanta tasan hakan amma daya ke tasa ba rigimar ne shiyasa. Ciki-ciki take mita akan maganar daya gama yi yanzun wanda ita ka'dai tasan abinda take cewa Abbas kam share ta yayi yaci gaba da al'amuran sa. Dan haka sai ta sa hannu ta 'dauki wanda ta ciro da farko 'din ta bu'de a hankali ta 'danyi tasting. Sosai taji ya ratsa mata zuciyar ta, baran ma sassanyan k'amshin da yake yi gashi da kauri sosai ai sai taji yama fi na asalin da'di. "Nagode Yayah" tace masa tana murmushi sai ya kauda kai yace "yi ki gama ni dai kiji dani" Bata tanka ba sai ta cigaba da shan abinta kamar wasa sai gashi ta tada roba guda ta kuma ciro wani wanda ko rabin sa ma bata shaba sai bacci yayi gaba da ita. Abbas duk na lura da ita, harta yi baccin, kai ya jijjiga kawai daya kalle ta aransa yace "sarkin rigima, bayan tace tafasa kuma da taga an kawo kuma harda mita" Sai da ya gama kallon abinda yake yi sannan ya juyo gareta, tana daga zaune ta kishingi'da a hakan kuma tayi baccin. Kiss ya bata a bakin ta yana 'dan murmushi. Teemah sai ta 'dan motsa ka'dan. Shima sai ya 'dan ja baya dan kar ya takura ta, sauran fresh milk 'din ya 'dauka ya je ya sassaka mata su cikin fridge sannan ya 'dauke ta ya maida ta bedroom ya kwantar da ita sai kuma ya sake dawowa parlourn ya kakkashe komai sannan ya koma shima ya hau shirin bacci. ***** Har kwana biyu bayan haka Teemah bata 'kara neman wani abu ba, sai dai ta kanyi da kanta idan taji tana so. Duk ranar da tayi wani abin kwa'dayin to dole shima yake ci dan bata sake yin wani abincin kuma, wasa-wasa har Abbas ya saba da irin cimar tata dan in dai tayi sai ta ajiye masa, tun yana 'kinci har dai ya saba shima dan ma da rana ne tafiya yi masa hakan da dare kam zagewa takeyi tai tayi masa girki mai rai da lafiya wanda tasan ba zai ci da takaici ba. Girki salo-salo.kuwa duka ta iya su, kuma ko a TV tgaa anyi kalan girki bata wasa sai ta gwada shi tagani in tgaa yayi kyau sai ta ta jin da'di shikenan daga lokacin kuwa ko a wani akace ta koya toh zata iya. ***** Ranar ya kasance saturday ne tun bayan da sukayi sallar asubah suka yi karatun al-kur'ani sai ta koma gado da niyyan koma wa bacci, Abbas ne ya hana ta baccin dan shima dawo wa yayi kusa da ita ya fara aika mata sa'konni, tun qcikin idanun sa ta fahimci sauyi tatare da shi, daya ke kusan kwana uku kenan yau bai samu kanta ba, ita kanta tana jin kewar sa amma kawai take basarwa. Sosai Abbas yau 'din ya rikitata da salo da tsarin sa na zallar 'kauna da soyayya wanda ke tafiyar gangan jiki da zuciyan duk ma'abota soyayya, ita kanta sai da tasan cewa mijin ta cikakke ne, gwani ta kowani 6angare domin sosai ya tafiyar da 'kananun matsaloli da damuwar dake cikin zuciyar ta, Abbas bai barta ba har sai da ya tabbatar da cewa ta 'dauki darasin sa kuma irin 'daukan nan ma mai wuyan mantawa. Sai bayan da komai ya lafa kafin suka koma bacci baya sun tsarkake jikin su. Shine ya riga ta tashi in da ya tashin a hankali dan kar ya tashe ta, A gadon ya zauna daga gefen ta 'kafar sa 'daya na 'kasa yayin da 'dayar ke lan'kwashe daga saman gadon ya zubawa system idanun sa. Around 10:04am itama ta farka daga baccin ganin shi zaune a gefen ta yasa tayi luf daga kwancen tana kallon sa. Jikinta da wata riga ce pink mai dogon igiya daga gaba wanda aka saka igiyoyin ya zama tamkar bottle, sai ya kasance shine ya tare gaban rigar ya hana aga jikin ta, daga rigar kuwa babu komai ciki dan ko bra bata sanya ba, wandon skinny ne daga 'kasan ta shima pink mai zanen flowers a jiki sosai kayan suka yi mata masifar kyau ta koma tamkar 'yar yarinya. Abbas ne da kansa ya za6a mata kayan yace shi zata sanya ajikin ta kuma shine ya siya mata dan ganin kamar zai mata kyau wani ranar da suka je shopping tare da shi. Gashin kanta har yanzu babu kitso sai ta kama shi ta 'daure da ribbom kanta babu 'dan kwali. Kallon sa take yi tana sakin 'kayataccen murmushi, daga zuciya har ga6o6in ta take jin masifaffan son mijin ta na ratsa mata, tana jin kamar duk duniya ita tafi kowa son shi, bata kuma 'kaunar ganin ranar da za'a ce yau ya kasance da wata matar wacce ba ita ba bata ko 'kaunar wannan irin hasashen. A hankali ta bu'di baki tace "Yayah ina kwana?" Sai da 'dago ya kalle ta sai ya sau'ke ajiyan zuciya kafin ya amsa mata da " lafiya Fatan komai normal?" Ya 'karasa da murmushi, itan ma murmushin tayi tare da 'daga masa kai. Sai da ya gyara zaman 'kafafun sa da kyau inda duk biyu ya hawo da su gadon ya mi'ke straight tare da 'dora system 'din akai sannan ya cigaba da dubawa. A hakan suke 'dan ta6a hira sama-sama idanun sa na kan system 'dinsa. Cikin hirar ne yake mata mitan rashin kitson nata har ma yace zai nemo inda za'a samu musulmai masu kitso suyi mata. Shiru ne ya biyo bayan maganar tasa, saboda ita abinda yake ranta daban ne a dai-dai wannan lokacin, tunanin pepper soup 'din da Ummah take kawo mata sa'ilin da baya nan ne yazo ranta take kuwa taji matsanan cin kwa'dayin cinsa ya bijiro mata. A hankali sai ta d'aga kanta ta dawo dashi kan 'kafar sa ta lafe luf, ta 'kira sunan shi a hankali har sa jan sunan tamkar bata so tayi maganar. Abbas yaji ta amma sai yayi shiru bai amsa ta ba dan so yake ta 'kara saboda yanda yanayin maganar tata ya ratsa masa kwanya sosai tsigar jikinsa ta ta shi. "........Yayah! Ta sake fa'di a hankali cike da shagwa6a. Sai ya amsa ta da " Uhumm ya akayi ne?" Yayi maganar batare da ya kalleta ba. Teemah kam bata damu ba sai ta cigaba da fa'din "Lokacin da baka nan katafi course ko kullum Ummah na aiko min pepper soup mai da'di na hanta" Abbas sai cewa yayi " Ummah ta kyauta sosai, Allah ya biyata" Itama Teemah da "Ameen" ta amsa sannan taci gaba da fa'din " kasan wani abu?" Yace " ah ah, sai kin fa'da min" Teemah sai tace "Shi fa nake son in ci yanzu" Tayi maganar cikin marairaita. Abbas kwafa yayi yana duban bayan kanta da mamaki, zaton sa ko tsaban ta tsokane shi ko kuma taji bakin sa ya sa ta 'kirkiro wannan maganar, in ba haka ba miye ala'kar wancan lokacin da wannan ko de ta manta garin da suke ne a yanzun...... Wannan tunanin ne yasa shi fa'din "Sai ki ci mana to Zahra tunda shi kike so ko na hana kine?" Da gangan ya fa'di hakan ba dan komai ba sai dan cewa da akayi "silly magana or tambaya need silly answer" Daga nan ya maida idanun sa kan system 'din yana tunanin yau kuma da wannan zata hana shi natsuwa, sarai yasan halin ta idan ta riga ta furta abu to matu'kar ba samu tayi ba bata ta6a natsuwa balle shi ma ta bar shi ya rintsa, sosai abin nata ya fara isan sa, sai a ciki- ciki ya 'karasa da fa'din " ni kam wannan abin idan cuta ce hakan Allah ya yaye miki?" Sam baya son hayaniya a kansa amma 'karfi da yaji sai da ya saba da nata, balle ma ita da ta ha'da hayaniyar harda tsirfa da fitina. Kuma yasa a ransa cewa dole ne suje ganin likita domin a san mekecdamun ta har yake sata hakan, bawai dan ya gaji da kashe ku'din sa ko kuma ya gaji da halintan ba ah'ah sai dan kawai yaji musabbabin hakan

Chapter 59 of 67