ta zauna da ita mana basai taje can kanon ba amma fir tak'i yadda.
Data je d'in kuwa sai datayi wata uku kafin tadawo,ran da zata dawo ma Mahmud kuka yayi tayi dan azaman datayi ba k'aramin sabo sukayi ba,ita ke tayashi komai,homework,da sauransu.
Kabirun da kanshi yazo yatafi da ita gida.Yana tsokanarta wai tazo gida tazama k'atuwa,kuma azahiri bawani jiki ta k'ara ba kawai de tsokana ce irin tasa.
Wai ko dai tafison zaman kanon ne yabarta,cemasa tayi ehh"
Duk da bawani jin dad'in zama da antyn takeyi ba amma dai tana jin dad'in ganin ahalin gidan nasu kuma zuwa yanzu ta yi wayon da komai Antyn zata mata ba damunta yake yi ba.tunda kallo ne kawai yanzu tsakanin su sai de ko habaici da Antyn ta tsiri yimata marar dalili.
Har k'auye duk taje ta kai musu ziyara kuma sunji dad'i musamman data je musu da tsarabar kayan amfanin yau da kullum, sosai sukayi mata tar6ar mutunci da karramawa.
Daworta da kusan shekara kafin tasamu wani cikin kafin nan kuwa har ta d'an fara shiga damuwa,mijnta ne ke tausar tare sake tunatar da ita cewa komai k'addar ne kuma ikon Allah ne.
Da tayi hak'uri ta dangana kuwa sai gashi Allah ya bata yanzu.
Cikin yaso ya bata wahala da farko amma data kai 3month sai ta ji garau,wannan karon ma kokad'an bata saka ran abinda zata haifa d'in zai zauna ba,sai dai tana addu'ar Allah yaraba su lafiya a kullum.
Da ikon Allah kuwa lokacin haihuwar da tayi sai ta gagara haihuwa da kanta,hankalin dangi yaso yafara tashi,amma sai likita yakawo shawarar cewa amata C.S,da wuri Kabiru ya amince dan yasan hakan shine kad'ai mafita agaresu.
Cikin sa'a kuwa akayi aikin aka ciro mata 'yarta 'yar mitsitsiya da ita.
Kowa ya ganta sai yayi mamakin girman nata dahar ya hana a haifeta sai dai da theatre,Khadija kuwa hamdala kawai take da Allah ya rabasu lafiya da babyn duk dama de theatre ce amma dole ta gode wa mahallici.
Mahaifinta ne yayi mata hud'uba da FATIMAH ZAHRA a madadin k'anwarsa data rasu ashekarun baya.
Kafin suna kuwa gida ya cika mak'il da jama'ah abin gwanin birgewa,dangi ta ko ina,Anty ma sunzo da ita da Mahmud,ga dangin Kabiru ma kaca-kaca.
Iyalan Hassan (mahaifin Abbas) kenan suma kusan kullum suna gidan dasu ake komai.
Abbas alokacin suma suna da jinjirar su mai suna Hannah,so bai wani damu da ko ganin jinjira ba harkar gabansa kawai yakeyi,shi kuwa Mahmud har yau bashi da kowa,shiyasa ya nace wa wajen da jinjirar take duk inda akayi da ita toh shima nan zai yi.
Anty 'ki tayi ta sake haihuwa tun bayan data haifi mahmud,acewarta d'awainiyar yara wahala ne dasu,yah yusuf bai sani ba ma taje aka juya mata mahaifarta.
Koda taga yanda Mahmud yake ji da jinjiran nan kuwa haushi kamar ya kasheta,gashi daman zuwan dole tayi tace ma bazata zo ba da farko amma da yah Yusuf ya dage dolenta ta shirya ta taho.
Tunda tazo kuwa take ta shan k'anshi,ta na wani kallon raini a mutane,sukuwa babu wanda yabi ta kanta ma balle tankata suka ci gaba da sabgoginsu.
Ko kunya bata jiba ta tawo Mahmud ta jajja masa kunne akan nacin dayake wa yarinyar.
"Aranta khadija tak m
Sanin halinta da sukayi yasa babu wanda ya tankata,tunda d'anta ne ita ta haifi abinta,kuma ita keda iko da shi.
Khadija aranta take mamakin irin halin Antyn dan kwata-kwata batayi irin halin mahaifinta ba,shi ba haka yake ba sam.
Duk da haka bai fasa ba dan yaro idan yaso abu da wuya ake raba shi da abin,anjima kad'an ya faki idan mamar tasa ya dawo,lokacin Jinjira na hannun Khadija tana shan mama,hannun jinjirar ya kama,yace "Anty miye sunanta ?
Murmushi khadijan tayi sannan tabashi amsa da FATEEMAH sunanta"
"Lah Anty akwai wata 'yar class d'inmu ma sunanta haka amma da TEEMAH kowa yake k'iranta,itama babyn Haka zanna ce mata "
"ko Anty?
Kai ta d'aga masa tana murmushi alamar "ehh"
wasu dake zaune acikin d'akin ma murmushin sukayi suna jinjina wayo irinta yaron.
Kamar wasa kuwa sunan yabita har girmanta.
Haka har taron suna ya watse suka koma kano,kuma tun daga lokacin Antyn bata k'ara waiwayar Gombe ba.
Sai ita mummyn Teemah da zuwan yazame mata dole,domin su kad'ai gareta sai kuma mijinta da 'yarta.
Watanta hud'u da haihuwa taje Kano d'in, zuwa lokacin kuwa yarinya tayi 6ul6ul kamar ba ita ba.
Alokacin kuwa ba k'aramin wulak'anci tasha ba awurin Antyn danko y'ar ma bata ta6a d'auka ba,kuma ta hana d'anta zuwa inda Khadijan take,takaicin hakan na damunta,domin bata san dalilin da yake sa Antyn yin haka ba.
Samun sauk'inta d'aya idan yayanta ya dawo gidan,danshi d'aukan y'ar yake yayi ta mata wasa shida Mahmud yarinya kuwa tayita dariyah.
Khadija tayi ta murmushi ganin yanda suke son y'arta ta.
Koba komai hakan kad'ai ma na sata nishad'i Anty kuwa sai dai ta kauda kai gefe tsabar mugun hali dan babu yadda ta iyah dashi sai dai ido.
Da lokacin komawar ta yayi kuwa yayanta yacikata da kayan amfani sosai yayi mata siyayyah,na kayan sawan jinjirar da kuma nata bayan wanda ya aika mata a suna.
Siyayyah tsakaninsa da Allah yayi mata bawai dan bata dashi ba a'a kawai sai dan yafaranta mata a matsayinta na y'ar uwarsa kwaya d'aya tal daya mallaka.
Hakan da yayi kuwa ba k'aramin cika haushi yayi ba azuciyar Anty,wutar tsanar suce tasake ruruwa azuciyar ta fiye da na baya.
Mahmud kuwa kuka yayi tayi kamar zai shid'e,
"Teemah na!
Teemah na!!
Teemah nah.......!!!
Haka yayita ambata,yana kuka babansa ne yayi ta rarrashinsa dan uwar kam ko kallo ma bai isheta ba da kyar ya hak'ura kuwa yayi shiru.
Wash π’manage plsππ» nagaji wlh π
_Comment & share_ _pls_π€π»
*Salmerhn ku ce* π
[10/2, 5:55 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DA* *BAZAR MU MUKE* *TUN'KAHO* π
Dedicated to all masoyan CAPTAIN
ABBAS.kuyi hak'urin jina da kuka yi shiru kwana biyu,amin uzuri pls.kunsan jiki da jini......
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Itβs not the mistake that matters; itβs how you deal with it, what you learn from it, and how you apply that lesson to your life.
π
Ώ *16*
Zuwansu kano na k'arshe shine lokacin da Fatima take da shekaru hud'u da haihuwa.
sunje da farin cikin su kuma sun samu tarba agun yah Yusuf da Mahmud kamar yanda yake musu aduk lokacin da suka ziyarce su
Alokacin Mahmud ya yi girma sosai ya 'kara wayo,shine ya kama hannun Teemah ya rink'a kaita neighbours 'dinsu yana nuna ta wai suga 'kanwarsa shima
Daya ke surutacce ne shi hakan yasa itama Teemahn ta sake jikinta dashi aikuwa sunsha yawo babu ruwansa
idan yazo yasa su Khadija agaba da surutu har baya gajiya da yi
"Anty kudawo nan mana muzauna tare!
"Anty kibar min Teemah anan kinji mun zuwa makaranta da ita"!!
"Anty in zaku tafi zan biku nima indai bazaki barmin Teemah ba" !!!
Khadija murmushi take binsa dashi kawai dan tasan acikin maganganunsa faruwar d'aya daga ciki zai yi matuk'ar wahalan gaske.
Tunda tasan tafiyah da Mahmud bazai ta6a yiwu ba dan Anty bazata bari ba kamar yanda ita kanta bazata iya barin 'yarta a gun Antyn ba,itama daya ta tsira balle 'yar cikinta.
Tana iyah hango irin hararar da Anty take binsa dashi idan yana irin wannan maganar,
Afili zaka fahimci manufar Antyn dan k'iri-k'iri take nuna bata k'aunar alak'ar Mahmud d'in dasu
abinda kuma zaiyi mata wahalar gaske wato yanke alak'ar dake tsakaninsu.
Dan Mahmud jininta ne,kamar d'anta yake,ba kama bama Mahmud 'danta ne,me rabata da Mahmud kuwa sai dai Allah.
Sau tari takanyi mamakin halin Antyn ace k'arfi da yaji ka nuna baka son jinin mijinka,ada ta d'auka ko abin Antyn da yarinta ne idan tayi girma zata daina,amma sai taga sam bahaka bane,don zuwa yanzun ai Antyn ta manyanta,
ya kamata ace tasan dacewa da rashin sa basai an karantar da ita ba.
Satinsu d'aya tal suka koma Gombe abinsu,da d'umbin tsaraba daga Yah Yusuf harma da Alhaji muhammad.
Dawowar su kuwa baifi da 7months ba Yah yusuf ya tattara iyalansa gaba 'daya suka koma Lagos da zama.
Kafin su tafin ma Khadija (mummyn Teemah) taso ta koma suyi sallama amma yah Yusuf ya hanata zuwa yace tayi zamanta kawai babu komai.
Bazata kawai tagansu a Gombe shida Mahmud,cikin sa'a kuwa alokacin Daddy yana gari,ranar kam tayi murna sosai dan wannan ne ziyarar farko daya ta6a kawo mata musamman dan ita batare da wani dalili ba.
Amma washegari da yamma suka koma Kano dan k'arasa shirye-shiryen tafiyar tasu bayan ya cika mummy da d'umbin alkhairai.
The next day sukayi sallama da Kano suka d'aga garin ikko.
Toh tun komawarsu Lagos mummy bata k'ara zuwa inda suke ba saboda nisan wuri,haka suma shiru,
sai dai suyi gaisuwa awaya ko kuma idan Daddy ya kawo musu labarin su dayake suna d'an had'uwa da Yah yusuf d'in wani lokaci saboda kasuwancinsu.
Anty kuwa komawa Lagos 'din sai yazame mata abun farin ciki,dan ji tayi kamar dan ita akayi.
Da farko tana d'an d'agun kai da fad'i ma kowa,saboda tanajin kanta cewa ita d'in wata abace daban hakan yasa ta dad'e bata samu ko da wacce zasuyi maganar arziki ba ma balle huld'a.
Sai daga baya Allah ya had'a ta da wata jibgegiyar 'kabilar mata.
Awajen saloon suka had'u acikin unguwan tasu,dayake Allah ya riga da ya tsara had'uwarsu sai bata yiwa matar irin halinta ba,tun a shagon saloon 'din suka saba har da aka gama musu ma suka fito tare.
Ahanya ne suka fahimci cewa ashe ma a kusa suke da juna,shikenan tun daga ranar suka d'inke suka zama aminai na bugawa a jarida.
Anty chideh ake 'kiran matar dashi haifaffiyar garin Lagos ce,sosai tasan Lagos fiye da zaton mai karatu,kuma zata d'an girmi Antyn da kusan shekaru hud'u zuwa biyar ahaife.
Zakuyi mamakin rayuwarta idan kuka gani bata da matsala da komai,sannan bata da 'da ko guda d'aya rayuwarta take yi daga ita sai mijinta _na zo mu_ _zauna_ wanda ya kasance shine abokin rayuwarta alokacin.
Ba aure sukayi ba zamane kawai suke yi najin dad'i idan kaga yadda take ikonta shi abin har zai baka mamaki duk da yake ba 'karamin mutum bane shi amma sharrin mace yasa yazama sokon cikin gida.
Anty ne ta shiga gidan ranar wata asabar domin haka suka saba ajunansu kowa yanada ikon zuwa gun d'an uwan sa aduk sanda yake da lokaci basa ta6a wuni basuga juna ba tunda suka san junansu.
Aduk lokutan da Anty take zuwa gidan bata ta6a had'uwa da mijin Anty chideh ba sai yau.
Mamaki ta tsaya yi bayan tashigo harabar cikin gidan,ganin yanda Anty chidehn tasaka babban mutun agaba yana wanke mata inners d'inta,ita kuma ta kame akujera sai taunan chewing gum takeyi tana bashi orders shikuma jikinsa na rawa yana bin umarni.
Duk da masu aikin da ke gidan da kuma loundary machine amma hakan bai hanata sashi yimata aiki ba dan kawai ta muzanta shi.
Abin haushi abin dariyah,da sassarfa Anty ta k'araso gareta Anty chidehn na ganinta kuwa ta washe hak'ora tareda mik'ewa tsaye.
Hannunta ta kama sukayi ciki,aparlourn Anty chidehn suka yada zango.
Gaisawa sukayi sama-sama da Antyn,gama gaisawan nasu keda wuya Anty Chidehn ta fara kwalla k'iran maid d'inta jin datayi bata amsa ba alamar maid bata kusa sai ta mik'e da kanta dan kawo wa Antyn ruwa.
Dakatar da ita tayi akan cewa tabari kawai bata jin 'kishi ita.
"Why nah, ah' ah"
Mum Mamud u don't want to eat anything in this house why nah"
da fad'a da d'an 6acin rai.
Murmushi Antyn ta mata sannan ta bata amsa da harshen da zata fi fahimtar ta akan cewa bata buk'ata ne kawai shiyasa bazata sha ba.
Nan kuwa in kabar Antyn wai tana kyankyami ne ba zata iyah cin abincin daya fito daga hannun su ba.
Anty batayi k'auran baki ba kuwa tambayarta tayi ya akayi taga oga yana wankin inners bayan ga maid in ita bazata yi da kanta ba.
Nan Anty chidehn tayi dariya sannan tace mata kawai haka ta ga dama dama.
Antyn nuna mata tahau yi akan hakan ai bai kamata ba,tana rage masa darajar sa ne agidan kuma ma ai yafi k'arfin yin agareta.
Jin hakan yasa Anty chidenhn ta hau bata labari dan ita sosai ta yadda da Anty.
Dalilin da yasa ta ke mar hakan wai da farko aure suka so suyi amma danginsa musamman mahaifiyarta suka k'i ta wai bade ita ba sai de ya canja wata.
Alokacin kuwa suna son junansu hakan yasa suka gagara rabuwa har suka fara zaman su ba tare da kowa yasani ba.
Watarana Maman san sai takawo masa ziyara kawai sai ta ganta agidan,itama tayi mamaki dan atunaninta sun rabu da jimawa amma sai ta ganta agidan.
Atake kuwa ta tada musu bori da kyar yajata ya kaita gidanta yanata bata hak'uri harda alk'awarin zai sallameta aranar ma ba sai an kwana ba,don ko kad'an baya son 6acin ran mahaifiyarsa.
Itama Anty chideh taji haushin abin sosai zama tayi tafara tunanain mafita na yanda zata 6ullo ma al'amarin.
Shikuwa yana dawowa ya hau rarrashinta da bata baki akan tayi hak'uri akan abinda mahaifiyarsa tayi ma ya ciro kud'i masu yawa ya bata yace ta koma gida zuwa wani lokacin kafin yayi settling da 'yan uwansa.
Bata yi musu ba ta kar6i kud'in daganan taje ta tattara kayanta ta tafi danbata so ya ga nacewarta.
Amma ga mamakinta tunda suka rabu bai sake neman inda take ba har kusan wata biyu sai abin yafara damunta.
Sai ta yanke shawarar dawowa taji inda maganar su ta kwana,amma cikin rashin sa'a data zo bata same shi ba wai yana Cotonou,haka takoma gida cikin jin haushin rashin samun nasa da batayi ba.
Wata guda ta k'ara kafin ta sake nemansa wannan karon kam ta sameshi agida,mamaki yayi daya ganta danshi har ya fara mantawa ma da al'amarinta.
Kusa tasa masa tazo da gudu ta rungume shi tana fad'a masa yanda tayi missing d'insa,shikuwa sai bubbuga bayan ta yake alamar rarrashi.
Daga k'arshe sai yasake bata hak'uri tare da jaddada mata haryanzu mum d'insa tak'i yadda kawai su hak'ura da juna yafi.
Tana jin hakan ta tashi afirgice tana kallonsa shi d'inma tashin yayi yana k'ok'arin yin magana kawai ta suri jakarta tafice da sauri tana me share hawaye.
"Chiddy!
"Chiddy!!
yafara kwalla mata k'ira amma tak'i waiwayowa tayi tafiyarta.
Tun daga lokacin ta fara neman hanyarda zatayi maganinsu gaba d'aya cikin sa'a kuwa ta samu.
Domin dakansa yaje har gidansu ya d'aukota ya dawo da ita gidansa.
Tace yanzu ko cewa tayi ya mari maman nasa toh kuwa marinta zaiyi da rawar jiki ma,rabonsa kuwa da zuwa inda mamar take har ita kanta ta manta,uwar cema ta ke d'an zuwa da kanta,idan kuwa tazo sai tace masa ya kulata kafin zaiyi mata magana,inkuwa bahaka ba harta tafi bazai kulata ba.
Tace yanzu maman ta daina zuwa musu dan kusan kullum idan tazo da kuka take komawa shiyasa ta hak'ura ta daina zuwa inda suke.
Anan Anty ta tambayeta "toh shi miye nashi laifin da har zata dinga bautar dashi haka."
Anty chidehn cewa tayi wai haka ta ga dama."
Har suka rabu mamaki bai bar Anty ba,sosai abin yatsaya mata arai har yasa tafara jin sha'awar aikata irin na Anty chidehn itama saboda guntuwar tunani.
Tun daga lokacin kuwa suka k'ara d'inkewa da Antyn sosai kamar wasa tafara bayyana ra'ayinta ga Anty chidehn.
Da Antyn chidehn taji tasamu passenger kuwa sai ta tayata k'iyayyar itama,nan tajata sukaje gurin mai mata aikin suka fad'i abinda suke so ayi musu.
Takuwa ci nasara don ba k'aramar katanga ta gina atsakanin iyalan gidanta da kuma mummy Khadija ba.
Tun daga lokacin zumuncinsu ya yanke kat.danshi yah yusuf har mantawa yakeyi da batun yana da wata 'yar uwa aduniyah.
Sau tari zasu had'u da daddy har su rabu amma baya tuna tambayarta ma balle ya bada sak'on gaisuwa akawo mata.
Daddy kansa yana mamakin abin,shiyasa idan ya dawo in dai yasan mummy tasan da had'uwar tasu sai yace mata yah yusuf na gaisuwa.
Amsawa takeyi ita d'inma kawai bawai danta yarda shid'inne ya bada gaisuwar ba.
Dan ko awaya ta k'irashi ma bai fiyah tsaya wa ya saurareta ba,balle ya kaiga gaisuwa.
Uzuri ya fiya bata da alk'awarin sake k'iranta daga baya idan yasamu lokaci,ki'randa bazata ta6a gani ba kenan yawuce ta.
Sau tari kuka take yawan yi idan hakan yafaru daddy ne mai lallashinta ya kuma bata hak'uri akan abin.
Da k'yar ta zo tasaba da hakan dan da kanta ta ta fahimci ehh lallai Yah yusuf dagaske yakeyi yanzu yamanta da ita.
Daga baya sai abin yabi jikinta itama ta daina neman nasu koda awayar ma,amma bata ta6a mantawa dasu ba azuciyarta.
Watan su Yah yusuf hud'u da komawa Lagos Hassan (baban Abbas) shima ya k'aura yakoma Abuja da iyalansa.
Ganin hakan yasa daddyn Teemah yace suma su koma damaturun gaba d'aya tunda harkokinsa sunfi yawa acan.
Dasuka koma damaturun kuwa sau biyu Abbas yakawo musu ziyara alokacin daya samu hutu sosai sukaji dad'in zuwan nasa dan Abbas sam baida rigima irinta yaran nan,kuma mummy nason shi dan nutsuwar shi jininsu ya had'u da shi sosai.
Mummy taso Mahmud ma ya dinga kawo musu ziyara kamar yanda Abbas yayi sai dai inah haka bazai yiwu ba bata san dalili ba amma abin sosai ya ke damunta naganin har zuwa yanzu babu wata shak'uwa tsakanin 'yarta da jinin yayanta.
Zuwan Abbas na 'karshe a damaturun kuma sai alokacin suka fi sabawa da Teemah dan zuwa lokacin tafi da wayo sai dai kuma tunda ya tafi bai sake dawowa ba sai da ya girma yayi passing out d'insa.
Wannan dalilin ne yasa da daddy ya kawo mata maganar cewa Mahmud zai zo yayi service d'insa a damaturu kawai sai tafara hawaye dan tunowa datayi da yayan nata da kuma barinta da ya yi k'arfi da yaji batare da wani 'kwa'kw'kwaran dalili ba.
_Comment and share_ _pls_ π€π»
*Serlmerhn ku ce* π
[10/2, 5:55 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DA* *BAZAR MU MUKE* *TUN'KAHO* π
In dedication 2 my sorority sisters
*Ummie*
*Maijee*
*Zuwairah*
*Ameerah*
and my lil baby sis
*miemie.* Allah ya barmin ku....
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
God does not create a lock without its key & God does not give you problems without its solutions! *TRUST* *HIM* .
π
Ώ *17*
Da daren ranar da Mahmud ya iso ne mummy takewa daddy k'orafin rashin kammala makarantar Mahmud d'in dawuri tace Mahmud d'in fah sa'an Abbas ne amma dubi yanda Abbas ya jima da kammala karatun degree d'insa amma shi Mahmud sai yanzu"
Daddyn cema ta yayi shima abin ya bashi mamaki da Yah yusuf d'in ya ce masa wai Mahmud zai zo dan yin service a damaturu har hakan yasa shi tambayar dalilin dayasa har ya makara haka!
Yah yusuf d'in ne ya bashi amsa da cewa "wallahi matsalar daga mahaifiyar sa ne.
"Hmm Allah ya kyauta"kawai mummyn tace daga nan tayi kwanciyarta tana mai k'ara godewa mahallici.
*****
Mahmud ma ranar kwana yayi batare da ya runtsa ba tunani kawai yakeyi akan halin mahaifiyarsa.
Tun lokacin daya kammala secondary school ta dage wai sai dai an kaishi k'asar waje yaci gaba da karatun acan shi kuma Abbansa yace sam d'ansa bazashi wata k'asa dan yin karatu ba tunda ga makarantu nan a Naija sai wanda ya za6a shi ba zai kashe kud'insa dan zuwa wata k'asa karatu ba, shi bai ma amince wa Mahmud d'in yaje ko'ina ba in dai har ba cikin Nigeria bane toh bada yawunsa ba"
Wannan dalilin ne yasa Mahmud d'in yajima bai cigaba da karatu ba,domin Mahmud d'in kansa da farko ya yi na'am da batun fita abroad d'in amma daga baya daya ga abin kanshi yake shirin cuta sai ya hak'ura kawai,
dan ganin Abbansa bashi da niyyan canja ra'ayinsa kamar yanda Anty ma ta nace akan nata ra'ayin.
Ganin hakan yasa ya yanke shawarar cewa shifa zaiyi karatunsa koma a ina ne yafi mishi da wannan zaman banzan daya keyi.
Akan wannan maganar Anty har fushi tayi dashi wai dan yak'i amincewa da batun data zo dashi,kuma aganinta wai taimakonsa takeyi.
Da kyar ya sha kanta ta hak'ura sai da ya bata baki sosai akan hakan kafin ta hak'ura ta barshi.
Cemata yayi ta bari yayi wannan d'in inyaso idan yagama inzai cigaba sai ya nema awajen ai duk d'aya ne.
Ran Anty baiso ba ta hak'ura duk da irin aikin datasa akayi mata akan al'amarin amma wannan karan batayi nasara ba.
Koda Mahmud yajewa Abbansa da batun zaiyi karatunsa a Naija ba k'aramin dad'i Abban nasa yaji ba har hakan yasa ya bud'i baki yayi ta sanbad'o masa albarkatai gwanin birgewa.
UNILAG mahmud ya nema ya fara karatunsa kamar wasa sai gashi kuwa ya kammala lafiya k'alau.
Toh gurin cika service ne yayi abinsa batare da shawaran kowa ba,dan abin Antyn shima yafara damunsa gani yayi kokad'an bata son yayi ma zancen Antynsa Khadija balle yayi zancen zuwa wurinta.
Hakan yasa ya cika service d'insa da Yobe dan yana da labarin Anty Khadijan nasa a Damaturu jihar Yobe take da zama kuma abakin Antyn yaji hakan.
Itace da kanta ta fad'a masa watarana daya tambayeta,da fad'a-fad'a ma tabashi amsar amma shi ko ajikinsa bai damu ba tunda dai yaji.
Dama niyyansa ya sand'i jiki watarana ya taho Yoben batare da sanin kowa ba amma kafin hakan ya yiwu sai Allah ya dubi niyyarsa ya aiko masa da batun service alokacin da baiyi zaton hakan ba.
Dan har ya isa wurin cikawan ma tunanin cika yobe bai zo kansa ba,wani yaji daga gefensa ya ambato yoben a maganarsa
sai kuwa yaji.
Take shima sai ya tuno da batun Anty Khadijansa.
Murmushi yayi daya tuna wannan ma babban chance ne Allah ya aiko masa tunda iyayensa basu san zumunchi ba,shikam zai yi ne ko ta karfi ma sai yaje yoben nan ko nawa zai kashe kuwa bashi da matsala da hakan matuk'ar zaiga kansa acikin jihar yobe toh he can do anything just to see himself there.
Iyayen nasa dukkansu babu wanda yayi tunanin zai cika da nisa shiyasa ma babu wanda yasa al'amarin akansa.
Cikin sa'a kuwa list na fara fitowa sunanshi ya fito acikin sunayem y'an tafiya yobe state.
Farin ciki yaji kamar yayi fiffike ya tashi sama amma haka ya 6oye murnar tasa acikinsa adole ya sakawa fuskarsa 6acin rai lokacin daya shigo gida.
Koda yazo da slip d'in gida ma mik'awa Abbansa yayi tare da fad'awa kan kujera batare da yayi magana ba.
"Me nake gani ne haka Mahmud?
Abban ya tambaya yana mai sake kallon papern da kyau.
"Abbah yobe aka turani fah"
Zaro ido Abban yayi waje tare da fad'in yobe kayi mai kuma?
"Bautar k'asa Abbah" Mahmud ne yabashi amsa da wani tsarewa alamar shima bayason gurin.
"Haba Mahmud shine har can saboda Allah!
"Abbah toh ya zanyi an riga an cire list d'in bansan yanda zanyi ba,nima yamin nisa gaskiya,
amma dai zan gwada sa'a ta nagani ko za'a dawo dani kusa"
"gaskiya kam ka gwada amma ai yobe yayi nisa sosai."
Mahmud bai k'ara magana ba illah tsayawa da yayi yana kallon Abban nasa da mamaki,ganin dayayi kokad'an bai kawo batun y'ar uwarsa dake zaune acan d'inba ko kuma irin yayi farin ciki da hakan yaru ba kamar yadda ya saba.
Aganin Mahmud ai murna ya kamata Abban nasa yayi dayaji batun zuwansa yoben bawai yayi againsing ba,amma ga mamakinsa sai yaga ko ya nuna alamun irin da wani nashi ma acan d'in baiyi ba balle ace zai k'arfafa tafiyar kodan dalilin Anty khadijan.
Lokuta da dama yana mamakin irin
girman laifin da Anty khadija tayiwa Abban nasa da har yasa yake kaucewa duk wani al'amari dazai shafeta.
Gagara hak'uri yayi har baisan lokacin da ya bud'i baki ya tambayi Abban nasa ba.
"Abbah meyasa kamanta da Anty khadija ne?
Yah yusuf najin abinda Mahmud d'in yafad'i sai ya d'ago fuskarsa da sauri ya tsurawa fuskar Mahmud d'in ido kamar wanda akace zai ga wani abu akan fuskar Mahmud d'in idanuwansa har tara ruwa suka yi.
Gani hakan yasa Mahmud lumshe idanunsa tare da d'auke fuskarsa daga saitin daddyn yamaida shi inda yaji takun tafiyah anan ya k'arasa bud'e idanun nasa ya sauk'e su akan K'afar Anty dake tahowa da takunta na k'asaita.
"Ha- ah
"yah na ganku jigum-jigum haka?
"Meke faruwa ne?
Tana maganar ne tare da hanzarto wa izuwa garesu.
Abban ma sai da yaji muryarta kafin ya d'auke idanunsa daga kan Mahmud d'in ya maida shi kanta.
'Zuwa tayi ta zauna a gaf d'in dake tsakaninsu,sannan ta maimaita tambayar tata.
Mahmud bai kalli inda take ba ya bata amsa da fad'in Anty service d'ina Yobe state yafito"
Hannunsa yana yawo akan fuskarsa yayi maganar.
Karkuso kuga yanda Anty
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 67