abin ta.
Shine da kansa ya kwaso dukkan bags na shopping 'din ya shigar mata ciki dan bai san matsalar ta ba.
Bai ta6a zaton batun yarinyar ne zai sata yin hakan ba dan shi bai ma sata aka ba.
Da yake dab maghrib suka dawo sai bai bi ta kanta ba kawai yayi alwala ya wuce masallaci, sai da yayi isha'i kafin ya dawo gidan anan yatarar da ita zaune a parlour tayi tagumi, yana shirin zuwa ya ji dalilin tagumin sai yajiyo 'karan 'dayan wayar sa a 'daki, wucewa yayi kawai ya 'dauki wayar sai yaga new no. dayake yasan hakan na iya faruwa akowani lokaci saboda yanayin aikinsa shi yasa bai tsaya wani tunani ba ya 'daga wayar.
Muryar mace yaji tana fa'din " _yalla6ai Leesah ce, da fatan kun isa lafiya yasu Mummy da baby_ ?"
Ajiyan numfashi ya sau'ke a hankali sannan ya furta
" _Kowa lafiya_ " yace da ita a takaice.
Sai ta sake yi masa godiya once again, ta kuma requesting yardar sa akan su rin'ka gaisawa time to time yace " _ba matsala_ "
Daga nan sukayi sallama tare da sa'kon gaida mata baby sis
yace " _owk zataji_ "
daga nan ya fito da wayar a hannun sa yadawo kusa da ita ya zauna.
Remote ya 'dauka yana canza channel yace da ita " _Leesah na gaida ki_ "
Kamar jira takeyi kawai sai ta sanya masa kuka da ita kanta bazata fa'di dalilin yinsa ba abu 'daya ne ya tsaye mata rai shine yanda taga sun sha hannu da yarinyar abin ya kasa barin ranta, toh tayaya ma zata iya manta sunan ta, bayan k'unci da takaicin data haddasa mata azuciya shine harda k'iransa.
Abbas kam jin ta sanya kuka yasa shi juyowa da mamaki ya kalle ta yace " _me kuma akayi miki_ ?
Ya tambaye ta cike da mamaki, Teemah kam bata ce da shi uffan ba sai taci gaba da rera kukan ta, koda yayi 'ko'karin zuwa kusa da ita sai ta matsa da sauri tana fa'din "ni _bana amsawa karta sake cewa tana gaishe ni, kuma sai na fa'da ka da Ummh tunda kam kowa ma ta6a jikin su kake yi har wanda baka sani_ _ba ma shaking hands kakeyi dasu_ ?
Sai yanzu ya gano asalin manufar fushin tan tun na 'dazun da bai ma kawo ha'kan aransa ba duk da yafa saurin fu wurinta amma bai zaci har haka zata ja abin ba.
Murmushi ne yaji ya k'wace masa aransa yace " _jealousy_ "
Murmushin da yayin sai ya 'kara tunzirata ta 'kara sautin kukan ta akan nada.
Abbas ma sai ya matso kusa da ita ya fara lallashin ta amma sam ta'ki sauraron sa sai sake cewa takeyi ita sai ta ha'da shi da Ummah.
Abbas kam sai yace " _toh shikenan na yadda kije ki fa'da mata amma fah karki manta ki fa'da harda naki duk abinda nake yi miki ai basu ka'dai_ _nake ta6awa ba har da ke_ "
Tana jin haka ta kwanto jikinsa ta ri'ke hannun rigar sa da kyau tamkar yace mata zai gudu ne, abin tausayi taci gaba da rero kukan ta ajikinsa, " _cikin kukan take fa'din aini matarka ce kuma ita wancen_ _din ai ban san taba_ "
Kafin kace kwabo har ta ji'ka masa gefen rigar jagab da ruwan hawaye.
A hankali ya kai hannayen sa ya rungumo ta da kyau ajikinsa yana fa'din " _sorry.....i'm so sorry kinji bazan sake ba tunda bakyaso kinji_ "
Sosai ya jinjina wa kishin nata, sai da yaga tafara rage kukan sannan yaci gaba da lallashin nata a hankali har ta nutsu amma bata daina ajiyan zuciya ba.
Shima sai ya sake rungumo ta sosai har bacci ya 'dauke ta.
Ganin da yayi baccin ta yayi nisa ne yasa shi maida ta 'daki ya kwantar da ita.
Washe gari da safe ma da ta tashi sai take jin babu da'di har aranta, amma sai ta daure tayi duk wasu abubuwan da ke gabanta ta gama, tare suka yi break fast kuma awurin ma babu wata maganar kirki data shiga tsakanin su har suka tashi awurin.
Har zuwa yamma maganar tsakanin su bata yi yawa ba, dan tsakanin ta da Allah take jin haushin sa ita shikuwa sai ya rin'ka binta ayanda take so 'din bai takurata akan komai ba, dama abinci ne damuwan kuma da kanta ma tana ci basai yayi magana ba.
Dare kuwa data zo bacci a'dakin sa sai ta juya masa baya ta tafi can 'karshen gadon ta du'kun'kune wuri guda.
Yana kallon ta amma bai kulata ba sai daya ga ma abinda yakeyi gaba d'aya sannan ya hauro gadon ya janyota jikinsa.
Kokuwan k'watan kanta tafara sai ya sar'keta da 'kafafunsa takasa motsa wa.
Kansa ya cusa cikin gashin ta yana sha'kan 'kamshin da gashin keyi a hankali yace da ita " _fushi kike yi dani ko kuma kishi_ ?
Sai tace
" _ni kan ka barni Yayah banaso_ "
Tace da nishi.
" _Ni ai inaso, kuma kema k'arya kike yi kina so........kin manta ranar da kika wuni agidan Ummah da kika 'kirani harda cewa yaushe zan zo in dauke ki mu dawo gidan mu...ai nasan kewata kikeyi_ _alokacin kuma abinda kenan kikeso_ "
ya 'karasa maganar tare da maida kansa 'kar'kashin wuyanta yana hura mata numfashin sa.
Teemah kam kukan shagwa6a ta sanya inda cikin kukan tace " _ni bawani bahaka bane_ "
"Naji toh bahakan bane, amma ai naji abinda kika ce da Hannah jiya da safe ko sai na maimaita kafin ki yarda?"
Rintse idanu tayi da 'karfi tana tunano yanda sukayi da Hannah ajiyan, hakan ma yana bathroom ne lokacin da Hannahn ta 'kira take mata tsiyar wai ta tashi bata ganta ba ina ta shiga ?
Sai tace inaga gida mana irin atsare 'din nan Hannah kuwa tace wani gidan kenan bayan banganki ba.
" _Toh ina gida wurin mijina abinda kike so kiji kenan ina kam_ "
Haka tace da Hannah a 'dan hasale.
Hannah kuwa take sai ta wani kwashe da dariya tace " _ai dama na gaya miki Yayah ba zai barki ki kwana ba kika'ki yadda yanzu waye ma'karyaci tsakanin mu_ ?"
Teemah sai tace " _ke de kika sani ni ai banga laifinsa ba 'kauna ce ke sa hakan kin sani kuma ma ai kinga ladan nan 'din yafi nacan so abarmu_ _mu huta please 'kiran naki yayi sassafe madam_ "
Hannah tana dariya tace
" _ehh aikuwa naga 'kauna anan ba 'karya_ "
Iya abin da sukayi da Hannah kenan kuma wannan 'dinma duk batayi zaton yajita ba ashe yaji.
Shiru tayi bata sake yi masa magana ba.
Shikuwa daya ga haka sai ya sake fa'din
" _Wato kina min bu'kula ne dan nayi kasuwa nasami wacce zata so ni ko?, ke bakiga bani da kowa mai sona bane bakya tausayina ko_ ?
Hawayen ta ta goge dake sau'kowa ka'dan-ka'dan sannan ta 'dora hannunta kan nashi.
Sai ya cigaba da fa'din
" _Nima ai inaso asoni ko laifi ne dan na samu wacce zata soni_ ?"
Kamar an matsi bakinta tace
" _Ai kana dashi ba sai ita bace zata so ka "_
Shima sai yace
" _Ni ai bansan kowa ba to in ke kin sani gaya min naji su waye"_
Teemah sai tace
" _Ga su daddy ga Hannah da su Ummah, ga...ga... ga..Nii...ma_ "
Ta 'karashe da in ina.
Cewa yayi
" _Oww dagaske kema kina sona? amma ai banta6a ji kin gaya min ba, wannan kuwa nasan kullum sai tace min I LUV U SWTHRT kuma_ _bazata na min rashin ji ba_ "
Da sauri tace
" _ai nima zan na fa'da maka kuma zan daina rashin jin ni dai bana so tana 'kiranka awaya_ "
" _In_ _baki so to fara fa'da tun yanzu inji ko kin iya, ranar dai naji da ina miki wannan_ _abin nan kamar kince min Yayah i luv u amma bansan ko dagaske bane ko kuma kawai_ _kunnuwa na ne"_
Batayi tunanin wani abu daban yake nufi ba dan haka ranta wasai tace masa " _dakana yi min miye_ ?
Bai yi magana sai kawai yakai hannu 'kasanta cikin panties d'in ta ya shafo da sauri takai hannu ta ri'ke hannunsan da kyau tare da 'kiran sunan shi cikin shagwa6a.
Kiss yabata agefen wuyanta tare da fa'din " _let me Zahra...plz_ "
Kai ta jijjiga masa tace " _tsoro nake ji ni Yayah_ "
Yace mata
" _Ba zafi ai_ "
Yana maganar yana shafa mata mara.
Batayi magana ba illah jijjiga kai.
Sai shine ya sake fa'din
" _Bari in gwada toh mu gani ko da zafin, idan yamiki zafi zan bari amma fah karki min rashin ji gwadawa kawai zanyi kinji_ "
Da wautar ta sai ta 'dage kai sama alamar ta amince.
Abbas be maida hannun ba sai yaci gaba da sunsunan wuyanta har zuwa kirjinta yana bata lafiyayyun kisses a hakan har ya rabata da kayan ta gaba 'daya.
Sosai ya kashe mata jiki da salon wasannin sa masu wuyar bayyanawa yana yi yana tambayar ta akwai zafin?
kai kawai take juyawa tako'ina bata magana tsabar yanda ta hau network.
Gaba d'aya ta manta da damuwar kishin datake ciki illah masifaffaen so da kaunar mijinta dake yawo aduk ilahirin jikinta.
Washe gari data tashi sai ta nemi fushin tarasa gaba ya.
Yau kam bayan sun idar da sallar asubah bai barta tayi bacci ba yasa ta agaba sukayi karatun al-qur'ani mai girma sannan yayi musu addu'o'i.
Sai da suka gama komai kafin ta sake komawa ta kwanta idanunta akan photon sa tana kallo tana murmushi tace
" _Yayah wai dan Allah yaushe zamu sake komawa inje inga Nasreeen ne_ ?"
" _babu rana_ " yace da ita kawai a takaice.
Sai ta mi'ke zaune azabure tace " _haba Yayah dan Allah nifah ina son in ganta ne kawai_ "
" _ba za dai aje 'din ba koma menene_ "
Yace da ita yana shirin shiga bayi.
Kun'kuni tayi 'kasa-'kasa tace " _mutun sai rowa dan ma ba 'yar ka bane_ "
Sai ta murgu'da baki.
Afili kuwa tace masa " _ai nima na ro'ki Allah ya bani nawa in huta da rowa_ "!
Da 'dan 'dagun murya tayi maganar dan ya kusan shigewa ciki.
Sai shima yasake fa'din
" _Dayafi miki ai_ "
yana fa'din haka ya shige bayi.
Teemah sai ta dawo da kallon ta kan photon sa dake sama tana murmushi kuma, wani sabon so da 'kaunar sa ke ratsa dukkan ga6o6i, zuciya da gangan jikinta, tuno abinda yafaru tsakaninsu jiya sai tayi saurin rintse idanu ta juya baya, yanzu kam tana jin bazata iya bari wata banza ta zo ta 'kwace mata miji tana ji tana gani ba, ai in dai biyayyan ne itama ta iya shi babu abinda bata sani ba daya danganci zaman aure kawai dai halin Yayahn ne yake sata yi masa wasu abubuwan kuma wani lokaci sai taji bazata iya daina masa rashin jin ba, amma yanzu dole zata tashi tsaye domin ganin ta katange tsakanin mijinta da dukkan wasu mata musamman masu sharri marasa alkhairi atare dasu, ji takeyi bama zata iya rintse ido ta bu'de ta juri ganin Yayah da wata macen ba, ko ma badan su ba ko dan ta gyara rayuwar auren ta da kyau ta kuma nemi aljannar ta.
Duk rayuwar datakeyi a har yanzun rayuwa ce kalan wadda tayi shi agidan Mahmud bata canja ba, bambancin kawai shi Mahmud baya tilasta ta yin abu, sannan komai tace tana so baya hanata yi baya 'kin sayo mata duk abinda tace tanaso baya mata tsawa ko ihu amma duk tasan hakan dama tun can asali ba halayyarsa bace bashi da fitina shi tun asali, hakan nema yasata tasaki jiki dashi sosai har sukeyin wasu abubuwa tare suyi wanka cin abinci kwana tare da komai ma, tun auren ta da Mahmud basu taba raba makwanci ba, sai dai shi bai ta6a kusantan ta ba har ya koma ga mahallicinsa wani lokaci ne dai ya kan 'dan romancing 'din ta amma ba sosai ba shima dan zata iya irga sau nawa hakan yafaru, iya abinda ke tsakaninsu da shi kenan now that Mahmud yarasu ta dawo mallakin wani daban kuwa wanin ma irin Yayan ta Muhammad Abbas so dole ne sai ta sauya dan ko wani tsuntsu da kalan kukan sa, tana son mijinta kuma tana son zama dashi tana son ta rayu dashi har 'karshen rayuwarta tana so ta haifi babyn ta masu kama dashi da kwarjininsa dayawa, musamman ma data fahimci cewa yana son ta shima so take sai ta 'daura aniyar canza salon ta tabar duk rashin kunya da rashin jin nan a gefe ta runguni mijinta ta dawwama faranta masa.
Da irin wannan tunanin har wani baccin ya sake daukan ta kafin fitowar sa daga bayin.
*****
Acikin kwanakin sosai natsuwa ya shige ta dan Abbas yayi proving kansa akan ba bu wani ala'ka dake tsakanin su da Leesah illah zumunci sai ya zamana ma har awaya yana ha'da su su gaisa, da kansa ya sanar da Leesan cewa Ai Teemahn matar shi ce ta sunnah ba wai sistern sa ka'dai ba.
Leesah tayi matukar mamaki sosai dan koka'dan data gansu bata ji ajikinta cewa matarsa bace dukkuwa da cewa sosai taga dacewar su ganin yanda ta ke zuba masa shagwa6a son ranta kuma yana biyeta kamar yarinya 'karama sai ta bari akan sister take awurinsa.
Yanzun kuwa dataji cewa matarsa ce Fateemahn sai ma taji ya 'kara birgeta sosai musamman idan ta tuno yanda Teemah ke yi masa sakalci da shagwa6a kuma ya kar6a mata, bakowa ke iya kar6an hakan daga wurin mace ba face cikakken namiji wanda ya san kansa yasan darajar matarsa.
Amma bata nuna hakan ya dame ta ba sai ma ta sanya musu albarka tare da basu tabbacin kawo musu ziyara idan ta samu lokaci kuma in sun bata damar yin hakan.
Tana yawan k'iran Abbas su gaisa daga baya ma har da numbern Teemah take 'kira, dan ranar da kanta tace Teemah ta k'irata da numbern ta.
Acikin kwanakin da basufi biyar ba sukayi sabo da juna dan Teemah yanzun tafahimci abota ce kawai bakomai ba a tsakanin su, duk da shi'din na yawan tsokananta game da Leesah amma sam bata wani reaction sai dai tayi murmushi.
Leesah ta 'dan girmi Teemah ka'dan dan ita 25-6yrs take yayin da Teemah har yanzu take da 19yrs.
Amma duk da haka bai sa Leesah 'kiranta da sunan ta ba dan soyayyar da tafara yi masan sai ya juye ya dawo ta abota da 'yan uwantaka, jin Abbas take yi tamkar d'an wanta na jini.
Takance dashi *bross* Teemah kuwa *sister* take k'iranta.
yayin da Teemah ke k'iranta da *Anty Leesah*, har labarin Hannah take bata idan suna waya itama Leesah na bata labarin wanta da yanzu ma baya k'asar yana waje.
*Duk naji za6in ku yanda kowa yafa'di ra'ayinsa game da ranar da za'ana update kuma na fahimce ku gaba 'daya, duk da cewa ra'ayoyi bai zo 'daya ba amma ni na* *yanke cewa zamu rin'ka posting CAPTAIN ABBAS 2-2 days saboda ganin hakan yafi ni awurina, kuma ma zan fiyi anutse, sannan kuma zakufi* *samu dayawa* .
*Wa'danda suka ce aringa yi kullun 'din nan kuyi ha'kuri dan Allah ba wai na'ki taku bane amma kunsan komai cikin natsuwa yafi.* 🤞🏻
👎🏻😰
*Sannan kuyi ha'kuri babu wuta ne a garinmu shiyasa kk jini shiru kwana 2....... kuma jiya nayi rubutu na dayawa har saura nayi editing ma kawai sai whattsap 'dina yayi clearing komai narasa chats gaba 'daya, wa'danda suka min magana basu ga amsa ta ba suyi min ha'kuri dan Allah domin bangani bane shiyasa*
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce*😍
[10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_This page is specially dedicated_
_to my hard&die fans 👇🏼
*Mar-yerm, Mum Haidar, 🌹Tamama🌹, Mom inteesar(mai ku6ewa), Ummin Diga, Faateemaah🥰, Ummy Aliyuu, Nanerh, Hassan Adam Kagadama ('dan Nigeria* 🇳🇬 *)Fatee Duguri, Nusaibateey, Maamah love, Khadija Hussain,i Fiddausi, Bebin soo, 💅🏻Zulaihart💅🏻,Ayshah🍃 Humaira,* *mj, mom Ansar, A.S, Mum Khady, Maman Muhammad, Mumyn Minal, Aneesa, Zb, Teemah baby, Fatima2(, AMINA, Maman Arfat, Maman* *Nawwara, 💋Sheerdert💋, Khadeja Abdulhameed, Baby on top, Ummu Zahra, AbdullahiZainab, Maman Zahra, Oum Farhan, Hauwa Gulumbe, HafsatJabyr, Asma'u Usman, Maryam Wakili, Mommy F's, Zainab Bala Abubakar..........anya zan iya kuwa?🤔Allah yawa ne da ku sosai, ha'ki'ka 'kauna ta da ku ta musamman ce, daku* *dama wa'danda ban fa'de su anan ba inaso kusani cewa ur COMMENTS nd* *DU'AHS na matu'kar faranta raina, Allahu ya bar* ' *kauna ya kareku ya haskaka rayuwar ku a ko'ina kufi 'karfin ma'kiyanku......INA MATU'KAR YIN KU MUTANE NAH...........IRIN UN LIMITED 'DIN* *NAN🤞🏻.* 😍
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
_We are all here for some special reason......Stop being a prisoner of ur past..... Become d architect of ur future_ .
🅿 *89*
Anty Leesah nada mutunci sosai dan ko ka'dan bata sanyawa ranta 'kiyayyar Teemah ba sai ma 'kara janta a jiki da tayi tana kula da dukkan al'amuran ta tamkar sistern ta na jini, Abbas kansa najin da'din yanda take bi da Teemahn sosai hakan ya 'kara mata fada awajen sa kuma dalilin kenan daya sanya shima yake girmama zumuncin dake tsakanin nasu.
*****
Satin sa biyu da dawowa Abuja sai ya 'kira layin Umar sukayi magana akan zuwa katsina da ke gabansu, har suka shirya batun tafiyar ma bai sanar da Teemah ba Coz da farko be yi niyyan tafiya da ita ba amma da kansa kuma daga baya sai yaga dacewar zuwa da itan ko dan cika niyyar marigayi Mahmud ma tunda da ita uayi planning zuwa kafin rasuwar sa.
Duk da haka sai ana jibi tafiyar sannan ya sanar da ita, Kwana biyu kacal yace zasu yi acan dan haka bata sha wani wahalar shirya musu kaya ba da kanta ta za6a musu harda shi ma kayan da zai yi amfani dasu har su dawo gida.
Washe gari gidan Ummah suka wuce inda suka yi mata sallamar tafiyar ta su da yamman ramar Umar kuma ya iso Abuja inda yazo wa Teemah da tsarabar sirri daga Maman Amal, Abbas binta da idanu ya rin'ka yi Teemah kam idan sun ha'da ido sai ta murgu'da baki ta yi kamar bada shi take ba, duk yana kula da ita, kuma itan ma tasan kallon na menene shiyasa take ta kakkauda kanta gefe.
Kamar jira suke Umar ya wuce sai Abbas yace dole sai ta nuna masa abin yagani dan bai yadda da wannan sabon salon 'kawancen ba, haka ya dage akan shi bai yadda ba sai yaga menene abin da aka kawo mata.
Teemah kam tashi tayi da sauri ta koma daga bayan kujera tare da yin baya da hannun ta ta 6oye laidan sai 2seatern dake parlourn yazama atsakanin su, tana tsayen itama tace ai kuwa ba zai gani ba ai sirri ne aka kawo mata kuma babu kyau gulma da sa ido"
Abbas najin tace gulma da sa idon nan sai ya zabura da sauri zai kamo ta ai kuwa tayi 'dakin ta da gudun gaske tana dariya ta shike dayake shine akusa da ita bai kamata ba kuwa, tana shiga sai ta datse 'kofan harda murd'a lock sanna tafara maida numfashi sama-sama.
Sai data gama sau'ke numfashin kafin ta tashi taje ta 6oye shi inda ba zai ma gani ba koda kuwa ta bashi garin nemowa.
Soasai taji 'kishin ruwa na damunta
dan haka bata 6ata lokqci ba ta sake bu'de 'kofan ta fito tazo tasame shi zaune akan kujera ya na'de 'kafafu.
Jikinsa ta fa'da tare da furta "ruwa"!
Baiyi wani musu ba ya tashi da kansa bayan ya gyara da kyau yaje fridge ya 'dauko mata ruwan da kofi.
Koda tasha 'din ma sai data 'dan huta kafin taji ta dawo normal dan tsokana sai ta kalli idanunsa tayi murmushi, shims sai yace "ina kika 6oye min wato kin yadda da wasu fiye da ni ko Zahra?"
Sai tace
"Ayyah Yayah bafa haka bane kawai dai tace ne fah kar kowa yagani"
Gira 'daya ya 'dage yace "Shine harda ni? Kuma kika yadda?
"Ai bakomai idan nagani ai kamar ka gani ne ko?
Cewa yayi " ni fah kin san ba na son shirgin 'yan Lagos 'din nan kin manta abinda sukayi miki ko?
Ahankali tace "ah ah ban manta ba ai wannan 'din daban ne"
"Nine dai ban yadda nuna min inga ko menene"
Rungumarshi tayi ajikinta tana murmushi ta 'dage masa kafa'da tare da fa'din bazai gani ba tunda ya koyi gulma shima"
Yanda yaga ta dage akan bazai gani 'din ba yasa dole ya ha'kura da ganin.
Amma da shara'din idan tayi amfani da wani abin dake ciki har ya samu nasaran cutar da ita toh yayi mata al'kawarin har ita kanta bazata tsallake wa hukuncin sa ba" Teeemah tace " ehh ta amince"
akan haka maganar ta 'kare.
The next day suka 'dunguma garin Katsina bisa jagorancin Umar dayake shine ka'dai yasan asalin inda suka dosa.
Umar sosai yaji da'din yanda Abbas ya cire lokaci musamman dan ganin ya cika wa marigayi Mahmud burin sa da kafin cikarta Allah ubangiji ya kar6i ransa, yasan ko ba komai hakan ma na 'daya daga cikin halin girma, sosai Abbas ya birge Umar, baran ma daya ga yanda ya ri'ke Fateemah da kyau yake kula da ita sai yaji ya 'kara birgeshi, saboda yasan banda wahala da rashin kwanciyar hankali babu abinda ta tsinta agidan auren ta da Mahmud amma Allah cikin ikon sa sai ya musanya mata da wani mai so da tausayin ta wanda duk a yanayin su ya fahimci haka.
Koda suka isa Katsinan kuwa Umar mamaki yayi na yanda ska tarar da gidan Innah gaba 'daya ya canza dan yasan shi ada, sa6anin su Abbas kuwa da basu san komai ba nasu sai dai ido ne kawai.
Duk kuwa da cewa gyaran ba wani na kirki bane amma cikin rufin asiri akayi komai kuma bu'kata ta biya, gidan Innah ya canza sosai haka ma yaran ta dan wannan dattin nasu ya 'dan ragu ba kamar da ba, duk dama zuwa yanzun sun 'dan fara shiga wani hali saboda 'karewar ku'din da Marigayi Mahmud ya bar musu danma sunan da kayan abinci dai-dai gwargwado shiyasa ma abin yazo musu da 'dan sau'ki sai wahalar ta 'dan 6oye kanta.
Umar ne yayi musu bayanin rasuwar Mahmud 'din gaba 'daya a takaice inda Innah ta ringa kuka da hawaye tana binsa da kyakykyawar addu'ah.
Hatta Rabi'u sai da ya zubda hawaye duk dama ba wai yau ne ya fara jin labarin ba amma irin karamcin Mahmud 'din yasa sam bai mantawa dashi yake kuma jin alhinin rashin sa sosai.
Teeemah ma sai da ta tuna da shi itama ta taya su hawayen rashin nasa da suke yi.
Kunyar matar ka'dai ya hana Abbas rungumo matar sa ya share mata hawayen amma duk da haka bai iya jura ba sai da ya maida hankalinsa gaba 'daya kanta suna ha'da ido sai ya yi mata alamar bai son kukan ta daina.
A hankali ta yi 'kasa da idanu batare da ta daina hawayen ba dan ko tace hawayen ya tsaya ma hakan ba zai samu ba.
Dukkan su sun yaba da 'ko'karin Rabi'u akan a halin Innah dan sun fahimci cewa yaro ne shi mai zuciya da amana, Teemah kam da farko ta sha shima 'din 'dan Innahn ne sai daga baya cikin maganganuns u ta fahimci basu da wata ala'ka sam.
Nan take Abbas ya ce da shi kafin gobe ya samu ya bu'de account kafin su koma.
Kafin su tafi zuwa masau'kin su kuwa sai da suka je gidan mahaifin Rabi'u suka gaida shi tare da yimasa alkhairi na ban mamaki wanda sam bai yi zaton samun sa aranar ba amma sai gashi dalilin 'dansa ya samu hakan, shima dan farin ciki rasa mai ma zai ce dasu yayi illah albarka da ya ringa sa ka musu tare da fatan alkhairi.
Daga nan masau'kin su suka koma bayan sun sau'ke musu tulin tsarabobin da suka taho musu dashi, gasassun kaji da kayan itatuwa masu yawan gaske sun kuwa ji da'din hakan sosai.
Innah bata bar yaranta sun 6ata tsarabar duka ba sai da ta ware na Rabi'u da kuma wanda zai kai gidan mahaifin sa kafin suma yaranta ta basu sauran.
Teemah kam har suka isa masau'kin su bata daina share hawaye ba, Abbas sai ya share ta duk da abin na damunsa amma dan kar ta sashi yin abinda bai dace ba acikin jama'ah yasa ya 'kyaleta taci gaba da kukan, coz yasan fa'da da baki bazai sata tayi shiru ba,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 57 Chapter of 67