Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
har zaki nemi sata a mummunan harka irin ma'digo_ , _Anty_ _bakya tunanin alhakin Allah ne_ ?, _Kun hana yarinya rayuwa me kyau agidan aurenta kun hanata sakewa, kun sanya tsoro yazama abokin tafiyarta duk meyasa hakan Anty dan kawai kin tsaneta, wallahi ni cewa kikayi insake ta takoma wurin iyayenta daya fimin da wannan alhakin!!_ _Itan fa jinina_ _ce......Fateema_ _dangina ce da ko ba aure atsakanin mu ni me iya ri'keta ne_ _awajena, banda haka ma Anty_ _me kike so ingayawa mahallici na idan ya tsaida ni akan amanarta_ _dana kar6o a hannun iyayenta ?_ _Anty_ _bakya tunanin ranar da Allah ze tuhume mu gaba 'daya_ ......... " _Ya isa haka ni Mahmud_ ...... Anty ta daka masa tsawa tare da 'dago Munnira ta jingina ta da jikinta. Taci gaba da fa'din " _ai kariga kasan dalili, nasan baka manta ba, lokacin dana yi ta fama_ _daku kaida mahaifinka akan karka auri yarinyar kun saurareni ne?_ _ko kana zaton dama i ll give up so easily ne haka da har kayi saurin manta abinda_ _yafaru? .....Mahmud wannan da kake gani ita ce_ _za6ina agareka kuma har abada bazan canja ra'ayi ba, ko ka 'kyaleta ko ka illata ta_ _Munnira itace uwar 'ya'yanka bawata ba, dan haka kama kama kanka ka_ _nutsu banason hauka, duk abinda na aikata kuma ina yi ne_ _saboda kai, ai nagaya maka bana 'kaunar ganinka da yarinyar nan,_ _banaso, bazan iya juran ganin jinina na rayuwa da dangin matsiyata_ _ba_ . _Kuma da kake batun ancutar da ita ka je ka tambayeta mana, ita tace tanason a tallafa_ _mata dan tana da bu'kata shiyasa na ha'da ta da 'kawata saboda akore mata_ _kishirwar dake damunta, bayaga haka me kuma na aikata agareta_ ? Mahmud hawaye kawai yaji ya zubo masa na ba'kin ciki yanzun kam yasan Anty bazata ta6a canjawa ba yariga yasan tayi nisa tunda har ta iya tsayawa gabansa amatsayin sa na 'dan data haifa ta gaya masa maganganu son ranta gameda aurensa, ha'ki'ka yasan idonta ya rufe da tsanar da take yiwa dangin mahaifinsa wanda kwak'kwaran dalilinta nayin hakan bazata iya fa'da ba. Har ya juya zai tafi sai yakuma dawowa gaban Antyn idonsa taf da hawaye ya furta " _Anty ki yafemin........_ _ni 'danki ne ke kika haifeni, albarkar ki dole in nema_ _adukkan al'amurana, ke da Abbah kun yi fama dani tun ina 'karami_ _har girmana..... kun bani dukkan gatan daya kamata, ban_ _ta6a yin kuka dan rashin wani abu ba, amma Anty ki_ _gafarceni..... wannan karon bazan iya 'dauka ba, bazan iya zuba_ _ido ina gani aci zarafin yarinyar da bataji ba batagani ba..... zuciyan_ _Fateemah awanke yake tas bata da hakkin kowa dan haka bazan bari_ _acutar da ita ba , kicewa Abbah na ya yafemin idan ya_ _dawo Anty_ " Be 'kara magana ba ya juya ya tafi yana share hawayen sa daya kasa controlling 'dinsu. Yariga ya sanyawa ransa cewar zai 'dauke Fateemah su bar Lagos bari na har abada, zai yiwa Anty nisa, nisan da zai sa ta harse ta manta da kalar fuskan Fateemah ma balle rayuwarta, abu 'daya zai iya dawo dashi shine Abbahn sa, yanaso yasake ganin Abbah kafin yatafi sai de hakan baze samu ba dan haka dole watarana ze dawo kawai domin Abbahn sa. Tafiya yake yana share hawaye, damuwarsa gaba 'daya ya tattaro ya taru masa akan idanunsa zuciyarsa kuwa cike take da hanzari jiyake ko awa 'daya ba ze iya 'karawa acikin garin Lagos ba, zai 'dauke matarsa suyi nisa yanda ze nisanta ta da dukkan ma'kiyanta. Kwakwata ma Mahmud mantawa yayi da cewan yana driving ne, ya manta duk wani doka da tsarin tu'ki abinda ya dameshi ne ka'dai yake yawo a 'kwa'kwalwar sa. Be ta shi sanin hakan ba har se da yaji 'karan wani horn ha'de da taka birki me 'karfin gaske take ya rikice yarasa me ma zaiyi dishi dishi idanunsa suke gani hakan ya sa be ma lura sosai da gabansan ba bayan 'karan da ya ji be sake gane komai ba, kafin ya ankara kuwa rabin motarsa tashige 'kar'kashin wata babbar motar da ke gabansa . Mafiya yawan mutanen dake gurin Hannu kawai suka 'dora akawunansu wasunsu na fa'din " _jesus crist_ " yayin da tsirarun su ke maimaita _innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ .............. _Comment vote and_ _share pls_ 🀞🏻 *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _People change, love hurts, friends leave, things go wrong but just remember that life goes_ _on........Love_ is _so strange.......Sometimes it becomes reason to live life and sometimes to leave life._ πŸ…Ώ *66* Umar na tsaye jingine da jikin mota, Fateemah kuwa na gefe har yanzu 'kirjinta rungume da kayan Munnira idanunta banda ruwan hawaye babu abinda yakeyi, ita kanta bazata ce ga abinda ke sata kukan ba amma yanayin datake jin zuciyarta ayanzun shi yafi komai 'daga mata hankali, tare da karya mata zuciya. Abbas ma tsaye ya juya musu baya, sam baya son ganin hawayen Fateema koka'dan hakan na matu'kar soya masa zuciya, baya jin cewa ha'duwar su da Mahmud ze yi kyau koka'dan, jiyake kamar babu wanda ya ta6a 6ata masa rai kamar Mahmud 'din aduk fa'din rayuwarsa ,hannunsa 'daya cikin aljihunsa yayinda 'dayan yake ri'ke da wayarsa bayan ya gama 'kiran Mahmud yaga baya 'dagawa, ransa duk a6ace shi tunaninsa yabashi akan Mahmud ya'ki 'daga wayar ne dagangan dan kawai ya wula'kanta Fateemah . ***** Cikin 'kan'kanin lokaci mutane suka zagaye wurin kowa na fa'din albarkacin bakinsa, da 'kyar akasamu aka ciro motar Mahmud 'din daga 'kar'kashin 'dayan motar se da ma suka 'daure motar Mahmud daga baya 'dauri sosai yanda ba ze motsa ba, tare da jan babban motar zuwa baya ka'dan sannan akasamu aka raba tsakaninsu. Da fitowar Motar Mahmud 'din kuwa sai da kowa jikinsa yayi sanyi wasu ma kauda kansu sukayi dan baza su iya kallansa ahaka ba. Sai da ambulance yazo kafin aka ciro shi tare da duk wani abu nashi na amfani dake cikin motar aka me dashi cikin ambulance 'din zuwa asbiti. Tun a cikin ambulance aka fara bashi taimakon gaggawa har zuwa asbitin suna zuwa kuwa aka wuce dashi A&E (Accident & Emergency) likitoci kusan uku ne suka ha'du akansa domin ceto rayuwarsa cikin gaggawa. Da 'kyar suka samu suka daidaita numfashinsa tare da yi masa dressing 'din raunikan daya samu. Bayan hakan ne wani daga cikin wa'danda suka taimaka masa har zuwa asbitin da kuma drivern babban motar da wani likita sune suka fara neman wanda zasu 'kira cikin 'yan uwansa. Misscalled 'din _Oga_ _Abbas_ Suka fara gani da be wani da'de da 'kiran wayar ba dan haka shi suka fara dannawa 'kira. Abbas na tsaye a inda yake tsayen tun 'dazu be motsa ba, ya dai 'kira layin mahaifinsa yasanar dashi cewa yashigo Lagos sannan ya'kira wani abokinsa ma sukayi magana, daganan yaci gaba da tsayuwa jira kawai yake yi yaga zuwan Mahmud gidan tunda kam baya office dole ai idan yagama abinda yakeyi 'din gida ze dawo. Wayarsa ce tafara 'kara alamar shigowan 'kira, yana 'dagota kuwa yaga sunan Mahmud na yawo a fuskar wayar. Da sauri Abbas ya amsa 'kiran tare da yin shiru danjin wace 'karya Mahmud ze shirga masa. Ga mamakinsa kuwa sai yaji ba muryar Mahmud bace ke tashi acikin wayar yake fa'din " _hello_ ! _helloo_ !! Da mamaki da kuma izzah Abbas ya amsa da fa'din " _Yes, who is on the_ _line_ ? Bayani aka yi masa akan abinda yafaru ata'kaice. Sosai Abbas yaji zuciyarsa ta karye da jin al'amarin amma be nuna afili ba yanda zasu gane koda ya juyo ma cewa kawai yayi da Umar su shiga mota suje wani guri. Har se da suka hau titi kafin Abbas ya sanar da shi asbitin da zai kaisu. Teemah kam bata magana sai aikin hawaye bugun zuciyarta ne yasake 'karuwa fiye ma dana baya koda suka isa asbitin ma ita da 'kyar take ciran 'kafa take binsu abaya domin gaba 'daya 'kafafun nata nawi suka yi mata, hakan ma bata ji abinda yafaru gaba 'daya ba dan har suka isan Abbas beyi musu bayani cikakke ba, zuciyarta ce ke gaya mata cewan Mahmud ne ya illata Munnira shine har aka kawota nan shiyasa suka zo. Daga Abbas sai suka 'kira layin Abbah shima sukayi masa bayani. Hankalin Abbah ba 'karamin tashi yayi ba dan shi baya ma 'kasar dan haka ya 'kira Anty ya sanar da ita sunan asbitin yace taje ta duba halin da Mahmud ke ciki kafin ya dawo, yace mata zuwa anjima shima ze dawo insha Allahu. Isan su Abbas keda wuya sai ga Anty ma ta taho itada da Munnira dayake har alokacin basu rabu ba suna tare lokacin da Abbah ya 'kira Anty. A reception suka zauna gaba 'daya suna jiran ji daga likitocin, domin sun ce sai zuwa nan da 30mins zasu ganshi kafin nan an 'dan kintsa shi kuma watakila ze farfa'do ya dawo hankalinsa. Duka abin nan dake faruwa Abbas da Umar ne ka'dai suka sani shima Umar 'din be da'de da samun labarin ba,bayan isowansu ne suka je tare wurin likitan inda shi yayi musu bayanin komai, Teemah kam har yanzu bata san abinda yafaru ba. Shigowarsu Anty ne ma ya 'dan fara bata mamaki ganin ta tare da Munniran ga kuma Antyn hankalinta duk atashe. Da farkawar Mahmud kuwa doctor ya basu damar shiga su ganshi, nan suka shiga gaba 'dayansu zuwa ciki. Anty ne ta wuce gaba da sauri ta isa gaban gadon tana 'kiran sunan shi. Wanda Teemah ma sai alokacin ta farga da wanda ke kwance agadon, ai bata san lokacin da ta zubar da kayan dake hannunta ba ta taho da gudu itama tana fa'din " _Yah Mahmud kaine anan?_ me _yasameka haka,Yayah Mahmud dan Allah ka tashi, ka tashi kaga Yayah Abbas yazo_ ?" Anty na kuka tana 'karawa tare da kamo hannunsa wanda be samu raunin sosai ba, Teemah ce tashiga tsakaninsu dan ita ta na zuwa sai ta shige gaban Antyn tana kukan fitan rai. Abbas da Umar kam tsayuwa sukayi suna 'kara jinjina al'amari na ubangiji, Umar tunani yakeyi awanni 'kalilan da suka wuce rabuwarsu da Mahmud yana cikin 'koshin lafiyarsa, sai gashi yanzu kwance agado cikin yanayin da bama ze iya fasaltashi ba. Ahankali ya bu'de idanunsa ya sau'ke su akan Teemah gefe da ita kuma Anty ce yaga dukkan su suna kuka. Ga Munnira ma daga 'dayan 6angaren itama tana share hawaye, can tsaye kuma Umar ne shida Abbas da rabuwarsu yanzu kusan wata uku kenan. Murmushi yayi tare da motsa hannun nasa da 'kyar ya ri'ke hannun Fateema dake risgar kuka iya son ranta. " _Yah.....Mahmud me yasame ka haka?....._ Teemah tasake fa'da cikin kuka. Anty kam kasa magana tayi banda hawaye babu abinda take sharewa, Abbas kansa dauriya kawai yayi beyi 'kwalla ba amma inkaga yanda jijiyoyin kansa duk suka mimmi'ke, idanuwansa suka yi jajazur take zaka fahimci halin da ke ciki da inda zuciyarsa ta dosa. " _Yayah Mahmud ina hannunka..... guda 'dayan yake......waye ya cire maka_ ? Teemah tasake tambayarsa tana bin jikinsa da kallo har zuwa fuskarsa. Murmushi yayi tare da waro idanunsa akanta nan ta 'kara ganin yanda cikin idanunsa suka koma tamkar jini gaba 'daya sun riki'de sun canza launi. Ahankali takai hannunta saman idanunsa tace " _Yayah......idanunka ma sun koma jini....Yayah......_ " _Allah ne ya min haka Fateemah kiyi min addu'ah kinji_ " Yayi maganar da 'karfin hali domin shi ka'dai yasan abinda yakeji acikin jikinsa, 'kafafuwansa ma gaba 'daya sun sami matsala dama ana shirin shiga dashi 'dakin thearter ne a'karasa cire 'kafafun domin bazasu sake yi masa amfani ba. Kafin hakan ne ya nemi ganin iyalansa bayan farkawarsa daga 'dan gajeran suman daya yi shine aka shigo dasu. Toh yanzun ma likitocin da suka ga kamar hayaniyan zai masa yawa zuwa sukayi suka ce su fita su barshi ya samu hutu. Da kansa yace a'a abarshi yagana da iyalansa bayi son hutun komai. Gurin shiru ko motsin kirki babu me yi acikinsu, kowa yayi tsit hatta su Fateema ba ihun kuka sukeyi ba sai de hawaye kawai suke sharewa. Da 'kyar muryarsa ke fita amma ahakan ya dubi Anty yace " ku daina kuka mana Anty, ku daina min kuka, ba gani nan ba zan warke ai insha Allahu" " Haba Mahmud ka dube ka fa bakaga yanda ka dawo bane? " _Karki damu Anty! haka dama Allah yaso gani na, kuyi min addu'ah kawai kinji Anty, idan kina kuka Fateemah ma bazatayi shiru ba!_ Sai ya juya ya kalli Munnira yace " _Share hawayenki ki daina kuka kinji, na riga na yafe miki tun lokacin dana san gaskiya, kema ki yafe min nasan nayi ta 6ata ranki abaya, dan... Allah_ _kiyafe min kinji Munnira, ban'ki auren ki dan bana sonki ba kawai de bani da burin yin_ _aure da wuri ne alokacin shiyasa, amma kun kowa ya kasa fahimta_ _ta.........._ Kai ta jijjiga masa itama Munniran tare da fa'din " _kabar ro'kona Mahmud ni ya kamata ince kayafeni, har abada ni me laifi ce_ _agareka nasani ni kaina bazan ta6a yafewa kaina ba, domin nasan na_ _cutar da kai, ayanzu kam bani da kalmar da zan ro'ke'ka gafara_ _sai de fatana Allah ya baka lafiya Mahmud ya in ganta rayuwarka_ _kai da zuri'arka gaba 'daya_ " Murmushi yayi mata itama 'kasan ma'koshi yace " _nagode Munnira_ " Hawaye yaji ya sau'ka akan hannunsa, sai ya waigo ahankali ya dawo da kallonsa wurin, ganin Fateemah yayi tana ta na ta 6ul6ulo da hawaye. Suna ha'da idanu hawayenta yasake 6ul6ulowa fiye da na 'dazu. " _Ya...yah Mah........_ Tanaso tayi magana amma sai taji gaba 'daya harshenta yamata nauyi. " _Shiiiiiii_ " ya dakatar da ita yana murmushi yace " _Maza share hawayenki kinji, kin manta nace zamu je Katsina tare_ ? Kai ta 'daga masa alamar ehh idanunta taf da hawaye. " _Har Abuja ko_ ? Ta sake 'daga kanta sama. " _Yauwa toh yi shiru kiji, share hawayenki_ " Hawayen tayita 'ko'karin sharewa amma baya tsayuwa kamar sake turosu akeyi haka taji. " _kinji abinda Munnira tafa'da 'dazu ko_ ? kai ta 'daga masa. Sai yaci gaba da fa'din " _nima ba nagaya miki ba_ _rannan_ " Da kai kawai take bashi amsan dukkan maganarsa. " _Toh ki yafe mana kinji, ni nasan dukkanmu masu laifi ne agareki har Anty, amma Fateemah wani abin sam ni bansan da faruwarsa ba, abakin Umar naji kuma koda na_ _tambayeki ma baki fa'damin ba kika 6oye min, bansan ta yadda zan tunkari_ _al'amarin ba saboda banji daga bakinki, kaina gaba 'daya ya kulle narasa mafita, cikin haka sai Allah_ _ya kawo Munnira ta bayyana miki komai agabanki wanda Allah yasa nima sai ya fa'da kunne na, hankalina yatashi_ _sosai Fateemah dajin sunan Anty aciki, bansan wani mataki zan 'dauka akai ba dan Anty mahaifiya tace_ _ita ta haifeni, daga 'karshe kawai sai na yanke shawaran zamu tafi mu bar_ _musu garinsu, zan 'dauke ki muyi tafiyarmu yafi amma kafin inje inda kike sai gashi yanda Allah ya maida ni, duk da haka nagode wa Allah na dayasa_ _nasan komai tunda ran numfashi na_ " Bu'dan baki Anty tayi zatayi magana Mahmud yayi saurin dakatar da ita da fa'din " _Karki ce komai Anty, ni komai yawuce agurina, sai de ko in Fateemah kuma itama nasan tahakura tuntuni_ " Kan Abbas ya maida idanunsa, suna ha'da idanu sai Abbas 'din ya taho wajensa ya zauna abakin gadon yace " _sannu Mahmud Allah yabaka lafiya cikin_ _gaggawa_ " Ido ya lumshe tare da bu'de su akan Abbas 'din yace " _Abbas idan na baka amanata zaka_ _kar6a min_ ? " _Me ze hana Mahmud zan kar6a_ _mana_ " Abbas ya bashi amsa da kulawa dan gaba 'daya tausayin Mahmud 'din yabi yacika masa ziciya ya maye gurbin haushinsa da yakeji lokuta 'kalilan da suka gabata. " _Amanar Fateema zan bar maka Abbas ka kula min da rayuwarta kaji, dan Allah....... kabata farin ciki dan tunda nake da ita bata ta6a 6ata min ba..... naso Allah ya bani tsawon rai nima in cikata da farin ciki.... amma ban samu wannan damar_ _ba Abbas, dan Allah kacika min burina kaji......_ " _bar fa'din haka Mahmud nasan da yardar Allah zaka warke, ka rayu da matar..... ka cikin farin ciki da walwala....._ " " _Hmm_ " kawai yace da Abbas 'din sannan yakomar da idanunsa kan " _Fateemah yace bazaki bar kuka ba ko?, in kina kuka fah bazanji da'di ba ko ba kyason in_ _warke ne_ ? " _inaso yayah inaso ka warke acire maka duk wannan farin abin_ "! " _Ko anciremin wannan Fateemah ai dole za'a sake sakamin wasu masu yawa ma, amma kiyi shiru kinji share hawayen ki bana son gani, in bahaka ba zan yi tafiyata in barki ke ka'dai.....,Anty kice mata tayi shiru banasan kukan nan_ ! Anty ne ta kamo ta ta share mata hawayen tace " _bar kuka kinji Fateema kukan ya isa haka_ _nan_ " Dayaga tayi shirun ne yace mata " _yauwa Angel 'din Daddy,_ _zakuje da Abbas kinji Umar ma zai rakaku........idan kinje kice da Innah ni yanzu bani da lafiya ne shiyasa banzo_ _ba, kice mata taringa yi min addu'ah, duk ranar da na samu sau'ki zanje in dubo su da kaina."_ Teemah kam wani sabon kukan ne ya 'kwace mata tace " _Yayah.....da kai zamuje, ni da kai zani idan kasamu sau'ki zamuje kaji, kai da kanka zaka sa mamanka_ _amakaranta kamar yanda kayi al'kawari da izinin_ ........ Tun kafin ta 'karasa maganar tari ya sar'keshi ganin haka yasa likitan cewa su 'dan fita su barshi ya huta please surutun yayi masa yawa ne" Anty ce tafara fita sannan Munnira followed by Teemah, Abbas kam be ko yin yun'kurin tashi ba hakama Umar da sai yanzu ma shikam yasamu damar matsowa kusa da shi. Godiya Mahmud yake 'ko'karin yi masa saboda sosai umar yabada babbar gudum mawa arayuwarsa amma karan nan maganan yakasa fita gaba 'daya, da sauri Umar ya dakatar dashi yace karya damu basai ya gode masa ba,yace komai dayayi yayi ne saboda Allah and for d sake of there friendship bakomai ba, yace Allah ya baka lafiya Mahmud" Lumshe idanu kawai yayi tsawon mintina uku kafin ahankali bakinsa ya furta sunan _Abbas_ kasancewar yana kusa dashi ne yasa ma yajishi da wuri sai ya amsa masa da fa'din " _gani nan Mahmud me kake_ _so_ ? " _Abbas..........'kaina.....kir....jina_ _bayana....._ Sai ya kuma yin shiru. " _ciwo ko_ ? Sosai Abbas ke jin tausayin Mahmud, gaba 'daya zuciyarsa ta karye da al'amarin dan yasan Mahmud ba 'karamin dauriya yake yi ba har yake bu'dan baki yayi magana, kana ganinsa zakasan yana jin jiki sosai bayaga haka ma ga wasu munanan raunikan dayaji wanda su ka'dai ma masifa ne amma ahakan yake daurewa yayi magana. Likitocin Abbas ya bawa guri yace su kula dashi suyi masa abinda ya dace. Har sun juya zasu fita a'dakin sai suka ji shi yana wani wahalallan tari, Da sauri suka koma kanshi suna yi masa sannu, idanunsa alumshe gefe da gefen idanun kuwa wasu sirarun hawaye ne yake bi ahankali. Bakinsa duk ya bushe yayi fari fat kamar wanda yayi sati be sha ruwa ba, " _Ab...bass_ ! " _Na'am Mahmud gani nan agefenka_ " " _Abbas_ _inajin....tamkar.....laifina_ _ya girmama.....ka tayani ro'kon Fateemah tayafemin dan Allah"_ " _Haba Mahmud ba anwuce wannan gurin ba, ka daina fa'din haka ka_ _kwantar da hankalinka kaji, batace ta yafemaka_ _ba_ ? Kansa ya 'daga har sau uku alamar ya tuna. Daga nan yayi shiru, still idanunsa alumshe. Matsawa Abbas yayi inda likitoci suka ci gaba da aikinsu, shi da Umar 'dinne suka juya zasu fita, Abbas har ya ze juya sai kuma yaga kamar bakin Mahmud 'din na motsi, sai ya dawo da sauri kusa dashi yayi 'kasa da kansa zuwa wajen bakin Mahmud 'din. " _Rasulullah_ " kawai yaji Sai ya 'karasa da fa'din " _sallallahu alaihi wa sallam_ " amma beji farkon abinda yace ba, sai de yana kyautata zaton kalmar shahada ya jero, daganan kuwa be sake ganin ya motsa ba, duk da yake dama ba yawaita motsin yayi ba amma yanzun daya 'kura masa idanu sai yaga kamar yanayinsa yacanja damma yanayin fuskar cike take da murmushi shiyasa ma yake 'dan jin dama dama. Umar ne yayi saurin ankarar da likitocin abinda ke faruwa, take kuwa ya iso ya dudduba shi, ganin dayayi cewa nunfashin sa baya tare da shi ahalin yanzun yasa shi jan farin mayafin dake jikinsa ya lullu6e shi zuwa sama har kansa. Sannan ya jiyo garesu, yanda yaga Abbas ya 'kuresa da kallo baya ko 'kiftawa yasa shi tsaida idanunsa akansa yace " _i'm_ _sorry_ ......."! Tsam Abbas ya kasa 'dauke idanunsa daga kallon likitan hakan yasa likitan ganin cewa ko be fahimce shi bane sai ya sake cewa " _i mean Allah yayiwa 'dan uwanku rasuwa_ ". Yana gama fa'din hakan ya juya ya fita sauran biyun dake taimaka mishi suma suka bi bayansa. Yayin da Abbas ya 'daga 'kafafun sa da 'kyar ya koma gaban gadon ya 'daga lullu6in da aka yimasa. Gani yayi fuskarsa shar har yanzu da murmushi, sai ma wani 'kara yin fari dayayi kamar yace tashi Mahmud amma wai babu shi. Acikin zuciyarsa yace " _Allah ya ji'kanka Mahmud yayi maka rahama, Allah ya haskaka 'kabarin ka yasa aljanna itace makomarka, Allah yasa mutuwa hutunka ce Mahmud_ " *Masoyan Mahmud ayimin afuwa, tun asali ahaka labarin yazo, ina fatan zaku cigada bina dankin 'karshen labarin.* ~Team Abbas ku kuma muna jiran jin yadda zaku ri'ke mana amanar Teeman mu~ . _Comment_ _Vote and share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _Every moment of life is a step towards death......._ πŸ…Ώ *67* Ahankali suka fito daga cikin 'dakin tamkar wa'danda basu so suyi tafiyar, kawunan su duk na kallon 'kasa. Anty ne tafara tambayar su " ya jikin nasa ? yasamu yayi bacci ne? Ta jero tambayoyin nata ajere. Abbas ne yayi dauriyar yin magana dan shi kam Umar yana daga bayan Abbas 'din yana faman share hawaye. " _Muje akaiku gida_ " Abbas yafa'da idanuwan sa na kallan gefe, sosai mutuwar Mahmud 'din ya bige shi, acikin idanuwansa ka'dai zaka gane hakan. Anty ne ta hango Umar daga baya ka'dan da Abbas yana faman share hawaye take ta maida hankalinta gurinsa tace. " _Umar me ya samu Mahmud kake kuka?,nunfashinsa ya tsaya ko_ ?. Ganin Umar be tankata ba kuma be 'dago ya kalleta ba yasa ta furta " _Nashiga uku na Mahmud ya rasu Munnira_ " Tayi maganar tare da 'dora hannu akanta, sai luuu ta zube a'kasa sumammiya. Tsawon mintina ashirin kafin ta farfa'do inda ta tsinci kanta kwance agadon asibiti, farko idanuwan ta akan Teemah ya fara sau'ka dake gefenta azaune tayi tagumi ta 'kurawa gadon idanu, yayinda Munnira ke zaune agefen gadon da Antyn take kwance itama tayi shiru. Ita da Munnira ne kawai a'dakin su Abbas kuwa na can suna preparation na tafiya da gawa. Anty na farkawa ta gansu zaune jigum-jigum ai sai kawai tasa kuka wanda kukan nata ya sa suka farga da cewa ta dawo hayyacinta. Cikin kukan take fa'din " _Dagaske ne Mahmud 'dina yarasu ko Munnira_ ? _Dagaske ne yarona_ _ya tafi ya_ _barni_ ? " _Yi ha'kuri Anty dan Allah ki daina kukan nan haka nan, addu'ah zakiyi masa kinji_ " Cewar Munnira dake 'ko'karin tallafota . Teemah kam binsu kawai take da idanu bata san me zata furta ba sam. Sai da aka wuce da Mahmud gida kafin Umar yaturo driver yazo ya koma dasu Anty gida, kafin nan kuwa gidan harya fara cika da mutane. Abbah ne yace a 'dan jinkirta masa ka'dan yazo yaga gawar 'dansa da idanuwansa hakan yasa aka 'daga jana'izar Mahmud 'din sai zuwa bayan sallar juma'ah. Kafin hakan kuwa jama'ah da yawa sun iso daga 6angarori da dama, ciki harda su Daddyn Abuja, Ummah, da su Daddyn Teemah mutanen Dubai, Abbah ma ya iso tuntuni inda ganin gawar 'dansan kwance yasa yakasa ri'ke zuciyarsa sai da ya share hawaye kusan sau uku amma be tsawaita ba dan yasan kukan bashida wani amfani koka'dan ga dukkan mamaci. Amma shi ka'dai yasan me yake ji azuciyarsa , 'dansa 'kwaya 'daya tak daya keso kamar ranshi amma yau gashi kwance agabansa da gawa, wanda yafishi ya amshi abinsa, Allah ka jikan Mahmud ka haskaka

Chapter 36 of 67