ita kuwa bata gane shi ba koka'dan saboda akwai 'dan rata atsakanin su kuma bata ta6a zaton ganinsa awannan lokacin ba, hakan yasa kawai tayi masa kallon kamar tasanshi sai ta kauda kanta gefe da sauri.
Sai de kuma sam taji zuciyarta takasa nutsuwa da hakan sai ta 'kara juyawa ta kallo wurin, wayam tagani babu kowa abin ya matu'kar bata mamaki hakan kuwa yasa tafara tafiya ahankali ta baro cikin mutanen.
Tsoro ta fara ji kardai ace ba mutun tagani ba yanzun, amma ace daga ganin mutun sai kuma tarashi.
Allah yasa dai mutun ne inbahaka ba ai nashiga uku!
Haka taketa nanatawa azuciyarta,yayinda tsoro yake 'kara cika mata zuciya aduk wani step 'dinta.
Caraf taji ancafko hannunta tabaya,wani firgita da tayi shi kanshi sai da yaji wani iri, tana shirin k'walla ihu sai yasake hannun nata dawuri ya rufe mata baki da hannun.
Bakinsa ya matsar daidai kunnanta ahankali yace mata " bana son hauka ki juyo ki ganni I'm your b...........
Sai kuma yayi shiru ya 'kirasawa, ido ta zazzaro waje dan tana jin amon muryarsa tagane shi, muyrasa ko acikin dubun mutame zata iya ware shi.
Bakintan daya rufe yasake mata, yana sakewa kuwa ta juyo da sauri ta fuskance shi, da 'karfi tace " Yah Abbas kaine dagaske"?!
Tsaye yake agabanta ya maida hannayensa duka cikin aljihun wandonsa ya 'kurawa fuskarta idanu tamkar yau ne farkon ganinsa da ita.
Koda ta tambayeshin ma be ko nuna alamun yaji ta ba sai data 'kara maimaitawa sannan ya 'daga mata kai alamar ehh shi 'dinne.
Take sai 'yan shagwa6anta suka motsa mata ta ha'de rai ta tura baki gaba yanda tayin sai ya 'kara mai data 'yar 'karamar yarinya.
Murmushi yayi aransa yace " mai hali kenan".
Azahiri kuma sai yace mata " me kuma yafaru naga kin 6ata rai ohh aren't u happy 2 see me?".
Sai ta 'daga kanta sama.
Waje ya fito da idanunsa tare da fa'din " saboda me"?
"Bakai bane ka tafi ka manta dani?"
" ohh sorry sis who told that na manta dake?, Allah kullun kina raina kinji"
Idanunsa akanta yake maganar da dukkan kulawa amma sai ta'ki yarda tawani karya wuya irin ita bata yadda ba 'dinnan.
" toh shikenan tunda yanzu nazo bashikenan ya wuche ba"?
Sai ta jijjiga kanta alamar "a'a".
Daya rasa yadda zaiyi da ita sai 'daga hannayensa duka biyu yakamo kumatun ta dashi, jijjiga kan yayi yana murmushi yace " stubborn head 'dinnan har yanzu yana nan ko?.
Yanda yayi 'din ita kanta yabata dariya amma sai ta juya masa baya tana dariyar 'kasa-'kasa.
A'dan nesa dasu kad'an ta hango wata 'kawarta dasuka fara 'kawace lokacin da aka fara waec, ta yaba da hankali da nutsuwa irinna yarinyar shiyasa ma bata yi mata mugun hali ba irin yadda tajewa sauran 'kawayenta.
Tana ganin yarinyar sai tafara tafiya da nufin 'kiran ta taga yayanta.
Takunta biyu kafin tayi na uku taji Abbas ya 'kira sunanta " FATEEMA" cikin wannan lion voice 'dinsan nan me ratsa mata zuciya.
Take ta tsaya cak tare da waiwayowa ta kalle shi, ahankali ya tako ya iso inda take tsayen, shima ya tsaya.
"Tafiya zakiyi ki barni anan?"
Da sauri ta jijjiga kanta.
" toh menene"?
ya sake tambayarta?.
Kasa magana tayi awannan lokacin domin irin kallon da yayan ke mata ya banbanta dana kullum, jikinta duk taji ya mutu sai kawai tayi 'kasa da kanta.
Bata zata ba sai taji yasa hannunsa yakamo hannun ta nadama ya bu'de yasa ka mata wata takarda sannan ya maida hannun ya rufe mata.
Da ido tabi hannun nata da kallo yayinda ta matse hannun nata gam-gam ta ri'ke takardar da kyau dukda bata san ta menene ba amma tanaji ajikinta tamkar takardan nada wani kyakkyawan muhimmanci arayuwarta.
Sai daya sake mata hannun ya maida nashi 'daya cikin aljihu yayinda 'dayan ke sau'ke daga gefensa kafin yace mata " zan tafi Fateemah inada aiki a office banida isheshen time yanzu "
Dasauri ta 'daga kai takalleshi sai yayi murmushi yace " sai munyi waya".
Yana fa'dar hakan yajuya yakoma mota be ko sake waiyowa ya kalleta ba, yana shiga kuwa driver yaja kamar daman jira yakeyi ashigo.
Ita kuwa mamaki hanata motsawa yayi saboda data ganshin ko dawasa bata kawo cewa ze koma dawuri haka ba.
Har suka 6ace daga wurin bata sani ba, tana can tana tunani.
Lokacin da runanin ya tsaya kuma koda ta kalli inda taga yayin gani tayi babu kowa.
Dasauri ta 'daga 'kafa ta taho gudu gudu ko zata ganshi amma ina bata ga kowa ba illah 'kuran wata ba'kar mota data hango awajen gate tana shirin fita.
" wai dagaske ne......yah Abbas ............kuma ka sake komawa".?!
Kamar ta fasa ihu haka taji amma kuma bazata iya ba.
Tana tsaye bata bar wurin ba taji ana mata horn sai tajuya dasauri takalli wajen zatonta shine yadawo amma sai taga motar gidansu ne wannan 'din.
Mummy ce ta bu'de motar tafito ta nufo ta dasauri domin yanda taga Teemahn abin ya 'dan bata tsoro.
Mummy na isowa inda take kawai tafa'da jikinta tayi lamo, sai da mummy ta 'dan bata 3mins tayi backin up kafin ta 'dagota ta tsayar da ita agabanta sannan ta tambayeta " me yafaru?.
" mummy Ya.....yah.. ne "
Tayi maganar tana nuna hanyan gate.
" wani yayan me kuma yafaru dashi?"
Mummyn tafa'da tare da jijjiga ta da 'dan 'karfi.
" mummy yah Abbas ne......yatafi.....
Tana gama fa'dan hakan sai ta fa'da jikin mummyn tayi shiru.
Mummy data fahimci 'yartata sai kawai tabarta ayanda take ajikin nata taringa bubbuga bayanta har tasamu ta d'an dawo daidai kafin tasamu da 'kyar ta lallesheta har se da taga ta warware sannan takama hannunta suka shiga ciki.
Tun daga lokacin Fateema bata 'kara yin wani abu da kuzari ba yayinda mummy kuma take jin bada'di tare da tausayin 'yartata.
Tana tsoron kar dai ace yarinyar nan soyayya ce takamata domin kallo 'daya zaka mata ka fahimci badaidai take ba, inkuwa hakane ai ta shiga uku!, yaza tayi ta iya sada Fateemah da farin cikin ta, idan yazamana shi'din ba haka bane azuciyarsa?".
Domin tasan it's hardly ace mutun kaman Abbas yaso Fateemah, kai Allah ma ya sauwa'ke Alla ya kiyaye ya tsare mu da sharrin zuciya.".( Ameen)
Atare suka koma gida koda aka tashi a wurin......ahankali Teemah ke tafiya tamkar mai tsoron taka 'kasa mummy kuma na bayanta itama tana binta ahankali .
Jijjiga kai mummy tayi data ga Teemah ta nufi 6angaren da 'dakinta yake daga shigowanta parlourn ko tsayawa bayiba ta wuce abinta.
Babu komai atare da ita sai mayafinta da kuma wannan takardan da Abbas ya bata, tun lokacin da yabatan har yanzu bata canja masa ri'ko ba bata kuma bu'de taga miye aciki ba.
Tana shiga 'dakin ta tura 'kofar ta datse da makulli sannan tacire head 'din dake kanta tayi jifa dashi akan gadon tare da mayafin baki 'daya tana niytan cire rigar ne taji hannunta da abu, da sauri ta bu'de hannun tare da kallon shi da wuri domin sai alokacin ta tuno da cewa Yah Abbas ne yabata takardar.
Amma saboda ri'kon ' karfi datayiwa takardan ga kuma gumin hannunta da yake gimtse tsawon lokaci, su suka had'u suka narkar da takardan a hannunta.
Da6as ta zauna abakin gado idanunta nakan hannun nata koda tayi 'ko'karin raba takardar da hannunta sai taga ya 'kara yagewa.
Duk iya 'ko'karinta naganin ta fahimci abinda takardar ke 'dauke dashi takasa saboda daidai inda akayi rubun daidai wurin ne yafi samun matsala.
Dolenta ta tattara ta cire da me 'dan girma da wanda
ya raki6e ahannun nata ta ajiyesu acikin side drawernta.
Sannan tacire doguwar rigar dake jikinta yarage daga ita sai pant, underwear da bra, ahakan takoma takwanta rigingine akan gadonta.
Ita kanta bata mecece damuwarta ba, haka kawai sai take jin ta wata iri, tamkar bata da ishashshen lafiya.
Nocking 'din 'kofa taji anfara yi kawai sai ta mi'ke ta nufi bayi batare da ko cire ragowar kayan dake jikinta ba, towel ma ahannu tashiga dashi bayan ta jashi akan 'kofar bayin.
Ba ita fito a bayin ba sai kusan 5:00 hakan ma dalilin tunowa da sallar la'asar 'din da batayi bane shiyasa tafito dasauri.
Tana fitowa kuwa idanunta suka sau'ka akan wannan kwalin da Abbas ya ajiye ma da tun shigowanta bata lura dashi ba sai yanzun.
Sallar dake gabanta ne ka'dai ya dameta adai dai wannan lokacin, dan haka kallon arziki ma kwalin be samu ta nufi wurin kayayyakinta ta 'dauko wanda take son sakawa ta sakashi sannan ta shimfi'da dadduma tare da zunbula hijab ta tada sallahnta.
Comment, vote and share pls๐ค๐ป
*Salmerhn ku ce* ๐
[10/2, 6:00 PM] Ummiyo: ๐ *CAPTAIN ABBAS* ๐
By
*Salmerh MD*
Luv story๐
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
๐ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
๐ซ
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ๐
*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi masoyana*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
โTime is free, but itโs priceless.
You canโt own it, but you can use it.
You canโt keep it, but you can spend it.
and once youโve lost it you can never get it back.โ
๐
ฟ *37*
Koda ta idar bata bi takan kwalin ba har yanzu, kwanciyarta kawai tayi sai dai tana kwantawan mummy ta fa'do mata arai kawai sai ta mi'ke da hanzari tatafi wurin mummyn dan tasan dole zata damu idan tajita shiru.
Murmushin 'karfin hali ta 'ka'kalawa fuskarta yayinda ta tunkari inda mummyn take, koda mummy taganta ahakan kuwa sai ta 'dan ji dama dama.
Murmushin tayi itama sannan tace
" yanzu kuwa nake so na aika aduba minke sai kuma gashi kin fito"!
Batayi magana ba sai da ta 'karasa kusa da mummyn ta zauna kafin tace " kaina ciwo mummy sosai"
tayi maganar tana wani yatsine fuska tare da dafa goshinta da hannunta 'daya.
" haya niya ai, bari anemo miki magani kisha zaki d'anji daidai".
Mummy tayi maganar tata cikin kulawa sai ta 'kara da fad'in " ki koma 'daki ki kwanta ki 'dan huta idan ankawo maganin sai kisha ".
Kai Teemah ta 'daga alamar " toh tare da mi'kewa tsaye ta kama hanyar 'dakin nata.
Koda takoma 'dakin kuwa kwanciya tasakeyi, so take tayi bacci amma sam sai taji takasa yin baccin ma fuskar Yayanta ka'dai ke yimata gizo tana ganin tamkar bashi 'din bane dagaske tagani.
Wayarta da tun safe take ajiye a gefen mirror itace tayi 'kara alaman shigowan sa'ko kuma 'karan ne ya yanke mata tunanin yayantan datakeyi.
Kuma sai alokacin ma ta tuna da wayarta saboda tunda tafara shiri bata 'kara bi takan wayar ba sai da tagama shiryawa ne ta 'dauko wayar ahannunta ta kashe selfii bayan tafito da nufin tafiya wurin graduation d'in sai kuma ta ji ri'kon wayar ya dameta shine ta aiko aka ajiye mata ad'aki.
Toh shiyasa bata 'kara bi takai ba sai kuma yanzun dataji wayar tayi 'kara.
Ahankali ta tashi taje ga wayar bawai dan 'karar sa'kon dataji ba " a'a " kawai jii tayi tana bu'katan ganin cikin wayar tata da ta 'dau tsawon awanni batare da sun gana ba.
Dawowa tayi ta kwanta rigingine kanta nakan pillow yayin da 'kafafun ta ke ajiye akan katifa ta wani had'esu guri d'aya.
Koda ta bu'de wayar sa'kon Mahmud tafara cin karo dashi a fuskan wayar ga dukkan alamu shine sa'kon da ya shigo 'karshe 'dan mintina 'kalilan dasuka gabata .
Bud'e sa'kon tayi domin ganin me aka rubuta mata .
" wai nayi laifi ne bansani ba? "
Haka taga anrubuta
Sai tayi reply da " haba laifin me zakayi kuma yayah"!
Daga nan tabar wurin messages 'din ta koma taga tarin missed calls 'din data tara duk daga yayanta Mahmud.
Data ta bud'e tashiga whattsap anan ma takuma cin karo da sa'konni da dama na groups dakuma na wasu contact d'inta ciki kuwa harda na Mahmud inda yake mata good wishes na gama makarantar ta, cikin sa'a kuwa sai taga yana online hakan yasa ta rubuta
" Yayah"
Tayi sending.
" Na'am, lil sis yau me nayi ne haka" ?
Tasan wannan tambayar duk bazai wuce akan tarin missed calls d'in data gani yayi mata bane hakan yasa ta bashi ha'kuri tare da yi masa bayanin rashin fita da wayar da bata yi ba ne shiyasa.
Tace sai yanzu ne dawowarta taga missd calls d'in kuma ciwon kai yasata agaba.
" eyyah sorry lil sis zakiji sau'ki kinji, ina kinsha Magani?"
" a'a mummy ta aika asiya min yanzu"
Yace
" wish u quick recovery owk".
Itakuma ta rubuta masa " Thanks".
Sannan ta 'kara rubuta " Yayah "
Shikuma yace
" Na'am 'kanwa".!
" Yah Abbas yazo yau "!
" Haba ai be gaya min zaizo ba, amma gaskiya ya kyauta sosai , ki gaishe min dashi before muyi waya".
" Ai ya riga yakoma ma "
" Ok ba matsala kinsan yanayin aikinsa ai sai a hankali".
Bata 'kara yin wata magana ba bacci ya 'dauke ta da wayar akan cikin ta, koda mummy ta zo kawo mata maganin ma tun a'kofa data hango ta tana bacci sai ta juya kawai batare da ta shigo ba.
Shima Mahmud 'din daya ga bata 'kara magana ba sai ya 'kyaleta azaton shi ko ciwon kan ne ya matsa mata, shiyasa ya barta yace ta huta .
*****
Washe gari bayan ta idar da sallahn asubah tayi addu'o'inta kamar yadda tasaba yi kullun, sai data karanto adduar safiya da maraice ta shafa sannan sai tasa hannu ta jawo wannan kwalin da nufin ganin abinda ke ciki.
Ledan dake jikin ta yage sannan tasa hannu ta bud'e cikin kwalin.
Hannu tasa ta ciro jakan dake sama aciki ta ajiye ta 'kara ciro wani tagani.
Dogin riguna ne aciki masu kyaun gaske irin 'yan italy 'din nan kusan kala hud'u wanda idan ka saka ajikinka ako'ina kowa yasan sunsha kud'i ba 'karya, sai takalma suma masu tsada guda biyu abinda kad'ai ke cikin kwalin kenan.
Ita kanta sun mata kyau sosai yayin da 'daya daga cikinsu yafi 'daukan hankalinta mai kalan coffee.
Tashi tayi ta tsaya sai ta d'aga rigar ajikin ta tana kallo kamar mai gwada tsayi nta da rigar.
Adaidai lokacin kuma sai ga mummy ta turo 'kofarta tare da yin sallama wanda tazo ne da niyyan ji da ganin jikin Teemahn ko yaya ta kwana.
Kafin Teemah ta amsa sallamar sai mummy a firgice tace.
" ke wannan fah daga ina kika samu".
"Anan na nagani nima "
tafa'da tare da nuna gurbin da ta ga kwalin a ajiye.
Da mamaki mummyn takalleta tace
"anan kuma Fateemah".
Sai Teemah ta d'aga kai alamar " ehh"
" toh wah ya ajiye"?
Inji mummyn
Sai Teemah ta jefa mata tambaya inda tace " mummy bake kika siya min bane"?.
Tayi maganar tana kallon fuskar mummyn nata.
Mummy bata kulata ba sai tasa hannu ta kar6i rigar dake hannun Teeman aranta take wassafa kyau da tsaruwar rigar, sannan kuma ga uban kud'i, idan batayi kuskure ba tace rigar tana kaiwa kusan Eighting thousand Naira (18000) akasuwa, zama tayi abakin gadon Teemahn tare da jawo kwalin ta firfito da ragowar kayan dake ciki.
" yah salaam "
Tace aranta
" toh daga ina haka"
Ta sake tambayar kanta.
tace kuma ba daddyn Teemah bane ya kawo domin shi tasan yariga yabata gift 'dinta tun lokacin daya dawo daga tafiya and she believe that matu'kar zaiyi abu toh sai ya sanar da ita.!
" toh wannan daga ina haka!".?
Zuwa Teemah tayi ta zauna akusa da mummyn saboda yanayin dataga mummyn tashiga itama kuma sai alokacin tunani wanda ya kawo kayan ya shige ta musamman data ga duk hankalin mahaifiyarta ya tashi da ganin kayan ,sai ta dafa ta tace " mummy wani abu ne?".
" a 'a ina tunanin ta inda kayan nan suka fito ne"!
Daga nan mummy n tasake yin shiru tana kallon Teemahn badan tariga tasan halin 'yarta ta ba da sai tace tasan daga inda kayan suke tunda har acikin 'dakinta aka gani, amma kuma ahalayyar Teemah babu 'karya sai dai uban rashin ji da taurin kai sannan bata 6oye gaskiyarta ko kad'an ita.
_ABBAS_ shine ya fad'o ran mummy atake wanda hakan yasanya ta sauke sassanyar ajiyar zuciya tare da hamdala acikin zuciyarta.
Domin da farko har kanta yafara caji hankalinta ya d'an soma tashi narashin sanin asalin takamamman inda kayan suka fito.
Amma tuno cewa Abbas yazo ayau d'in duk sai wad'ancan abubuwan suka kau, mussamman data tuno lokacin data ganshi ze shiga parlour hannunsa rik'e da wani abu wanda tun alokacin bata 'kara tunowa da neman sanin miye abin ba, zaton ta jakar kayansa ne tagani ahannun nasa , sai kuma yanzu tafahimci menene abin tunda shi da be zo zama ba ina yaga ta shigowa da jaka har gida.
Murmushi tayi abayyane data tuno halayyar Abbas d'in shi sam baya son inzaiyi abu wani yasani komiye dalili oho, sai dai hakan da yakeyi d'in ita kanta yana birgeta domin halayya ce tagari ga dukkan wani musulmi abin kwaikwayo ga kowa.
Kallon Teemah tayi da tun 'dazu ta zuba mata idanu tun sanda tafara murmushin nan tace
" inajin Abbas ne yakawo dan naganshi da kaya 'dazu dayazo lokacin hankalina nakan aiki".
Sake 'daga rigunan mummy tayi tare da jujjuya takalman ahannunta tace " size 'dinki ne kuwa beyi kuskure ba".
Kar6an takalmin Teemah tayi tana 'ko'karin gwadawa a'kafarta.
Yayinda mummy taringa sanya masa albarka, fatan alkhairi, da kuma fatan gamawa da duniya lafiya da ganin haske adukkan al'amuransa.
Acikin zuciya Teemah taringa amsawa da Ameen.
Sai mummy tace
" ki ajiye bari anjima anunawa daddynki shima yagani " .
Da
" toh "
Teemah ta amsawa mummyn, kuma sai asannan ne mummyn tace " ya ciwon kan naki "
Dariya Teemah tayi tace " sai yanzu kika tuna da ni ko mummy".
" 'kaniyarki wannan 'dinma ai duk saboda kene kikaga nashiga tunani."......
Daganan suka kwashe da dariyar dukkansu har mummyn gaba 'daya.
*****
Kwana biyar bayan graduation d'in Abbah ya sau'ka a damaturu..............
_Comment,vote_
_and share_ ๐ค๐ป
*Salmerhn ku ce* ๐
[10/2, 6:00 PM] Ummiyo: ๐ *CAPTAIN ABBAS* ๐
By
*Salmerh MD*
Luv story๐
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
๐ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
๐ซ
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ๐
*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Donโt be ashamed to be different........ Be proud that Almighty Allah made you like no one else.
๐
ฟ *38*
Mummy na can uwar 'dakinta taga daddy ya 'kirata awaya akan wai tafito parlour yanzu yanzun nan.
" lafiya kuwa?"
Ta tambaye shi
Sai yace " lafiyar kenan Khadeeja".
yana gama fad'an haka ya yanke 'kiran sai kwai ta tashi ta fito parlourn domin ams a 'kiran Daddyn.
Sai dai tun kafin ta 'karaso tafara jin zuciyarta na tsinkewa, bata san dalili ba amma sai dole hakan yasa yanayin saurinta ya ragu ba kamar yadda ta farao tafiyan da farko ba.
Koda ta iso parloun ma ciki-ciki tayi sallama bata damu da ko daddyn yaji ko be ji ba domin damuwar luguden da zuciyarta keyi ne ka'dai aganbanta awannan lokacin.
Bata ankara da ko mutune nawa bane zaune a d'akin ba har se da ta iso sannan ta 'daga kai a'ko'karinta na neman inda ya yadace tazauna sai kawai idanunta suka hango mata yah yusuf zaune agefen daddy.
Yatsa ta 'daga tare da fa'dan sunan shi cikin tsananin mamaki
" Yah........... Yusuf.........kaine ko............ko.........i"adanuna ne...?
Murmushi yayi mata sannan yace " Nine nan ba idanunki bane Khadija 'Karaso ki zauna".
Ya 'karasa maganar tare da nuna mata wajen zama.
Bata 'karaso inda yake 'din ba sai zune jagwab a inda take tsayen tama kallon shi yayinda idanunta suka da'de da fara zubda ruwan hawaye.....
" Ashe zan sake ganin 'dan uwana aduniya........ashe da rabon in sake ganin ka, Yah Yusuf me yasa ka manta dani, kamanta da koni wacece agareka...ka manta da............
Daidai nan daddy ya dakatar da ita da fad'in " Khadija " !
Da 'karfi yayi maganar wanda yasa dan dolenta tayi shiru sai dai hawayenta dasuka kasa tsayuwa.
Teema ce ta taho da niytan zuwa gurin mummyn ta ta sai ta tarar dasu a parlour dukkansu shiru sai mummynta dake zaune a'kasa kamar me neman gafara tana kuma share hawaye.
A sukwane ta iso gurin mummyn ta zauna itama kusa da ita tafara tayata goge hawayen batayi magana ba amma ga dukkan alamu kukan take shirinyi itama.
Daddy da yaga haka sai ya 'kirata akan tazo wurinshi sai kawai ta kalleshi batare da tayi niyyan tashi daga jikin mummyn ba tace
" daddy me yasami mummy"?
Rashin sanin abin da zai ce da ita yasa shi yin shiru " toh me ze mata yasaka mahaifiyarta kuka?".
Juyawa yayi ya kalli Yah yusuf instead of ya bata amsar tambayar da tayi masa, cikin sa'a kuma daidai nan mummy ta dakatar da kukanta ta kamo Teemah, ta rungumeta ajikinta, tana 'dan bubbuga bayanta.
Daddy da yah yusuf ne suka ha'da baki wajen bawa mummy ha'kuri.
Sai tace bakomai ai ya wuce tunda taganshi yanzu, tace abinda yasa ma har yaga tana kukan bakonai ba ne face tunawa da tayi da Mahaifansu, ta tuna irin gwagwarmayan da mahaifinsu yasha arayuwa 'karshe kuma Allah ya kar6i abinsa, daga baya kuma mahaifiyarsu, wacce tayi iyah 'ko'karin ta wajen ganin ta kula da rayuwarsu yanda ya kama ta bayan ba ran mahaifinsu amma ita ma Allah ya kar6i ranta tun ba aje ko'ina ba.
Tace " Iyayenmu sun barmu mu biyu da tabbacin zamu had'e kanmu mu kala da kan mu da rayuwarmu, amma hakan sai ya kasa faruwa muka kasa yiwa kanmu wannan gatan, nasan da mahaifan mu na raye sai sunyi Allah wadai da faruwar wannan al'amarin"....
Daga nan ta 'daga kanta ta kalleshi taci gaba da fad'in " yah yusuf bansan me yasa ka 'ki ni ba ka gwammaci rayuwarka takasance babu ni aciki duk da kasance wata matsayin 'yar uwa agare ka wacce duk iya rayuwata kai ka'dai ne wanda zan yi tutiya dashi amatsayin 'dan uwana, Allah ne kawai ya dubeni ya bani miji nagari badan haka ba da ban san ya rayuwata zata kasance ba, amma Alhamdulillah ko yanzu na godewa Allah na tunda ban nemi komai na rasa na jin dad'in rayuwa ba ".
Tana gama fad'in hakan tayi 'kasa da kanta sai Yah yusuf ne ya bud'i baki da kyar fara bata hak'uri yace shi kansa bai san me yasa duk wannan abubuwan suka faru ba amma insha Allahu yayi mata al'kawarin matu'kar yana numfashi kuma yanada lafiya bazai 'kara maimaita irin hakan agareta ba."
Bai tsawaita magana ba yayi shiru shima duk tunanin iyayensa ya dawo masa fil aransa .
Sallahr maghrib suka fita da daddy suka nufi masallaci, koda suka suka dawo kuma sai suka zauna aharabar gidan suna tattaunawa akan maganar Mummy anan ne Yah yusuf ya ke cewa shi yanzu wata alfarma zai nema awurinsu duka bayan yafiya yana so idan har zai yiwu su basu auran Fateema saboda kar Khadeeja tayi zaton ko nan gaba zai 'kara barinta duk da ahima ba ason ranshi hakan ke faruwa shi kansa be san har yaushe ne ya aikata irin hakan ba amma zaiso Khadeeja tasawa ranta salama da kuma yadda akan cewa shi 'din yana nan amatsayin 'dan uwan ta bazai ta6a gujan ta ba har abada, yace sai dai yana ganin hakan zai kasance ne idan har sun had'a wata kyakykyawan ala'kar da zata 'dore har abada.
Daddy kuwa shiru yayi yana sauraransa domin be san manufar maganar Abban ba da kuma inda ta dosa abinda ka'dai ya tsaya matsa shine cewa da Abban yayi " _abasu_ _auran_ _Fateema_ "
................
" toh shi da su waye?".
Abbah da yaga daddy yayi shiru batare da ya fa'di ko kalma 'daya ba kuma daya lura sai yaga kamar ma abokin nasa hankalinsa naga wani tunani sai ya sa hannu ya dafa kafa'dar sa anan daddy ya fuskanceshi sai Abban yace " baka ce komai ba kabarni inata surutu".
Gyaran murya daddyn yayi tare da fad'in bana fahimceka ba ne yalla6ai " ya 'karasa manmganar yana murmushi.
"Manufar magana ta shine inda hali ina nemawa Mahmud auran Fateema awurinka saboda sake 'karfafa dan'kon zumunci ".
Kallon Abbah daddy yake yi da kyau sai yanzu ya gama fahimtar me yake nufi tun farko.
Shikanshi da hakan zai faru zaiyi matu'kar farin ciki ko dan saboda sanin irin sha'kuwar dake tsakanin Mahmud da Fateemahn, amma bai sani ba ko kowa ma zai so faruwar hakan bataga shi da Abban.
Bai bawa Abbah amsar maganar tasaba ba ya dai ce ya bari tukunna zasu 'karasa maganar anjima ko zuwa gobe ne insha Allahu.
Duk da Abbah na tunanin komawa agobem amma be tankawa daddy akan maganar daya fad'a d'in ba dan yana ji aransa cewa in dai akan maganar ne he is ready to sacrice everything dan kawai yaga yiwuwar auran. Saboda shi aganinsa idan akace Fateema natare da su toh hankalin Khadeeja zai fi kwanciya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 67