Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta lura da hakan sai tayi saurin ri'keta ta maida ita mazauninta tana tayi mata aikin sannu sannan tatafi wurin Anty ta sanar da ita abinda ke faruwa. Anty waya ta lalubo ta'kira Mahmud akan cewa yazo yatafi da Fateema gida saboda bata jin da'di, da " okay" Mahmud ya amsa tare da yanke 'kiran tsawon mintina ashirin ya 'dauke su isowa wurin daya ke daman ba da nisa suke ba already sun riga sun shirya zuwa 'dauko sun. Ba'a maida su gidan Anty ba sai aka kaisu asalin gidan da Fatima zata zauna, Hannah ce ta yi 'ko'karin ganin ta aikata komai da Ummah ta tsara mata kafin tatafi dan haka dazasu shiga gidan sai tace da Teemahn tayi bismillah kuma 'kafar dama zata fara sawa agidan, hakan tayi niyyah dama domin already tu, a Damaturu Mummy ta karantar da ita hakan takuma 'kara da nata addu'o'in na neman kariya daga dukkan ma sharranta daga 'karshe ta rufe addu'ar tata adaidai 'kafar shiga palour da fa'din (A uzubillahi minash shai'danir rajeem, Bismillahi tawakkaltu alal lah wala haula wala kuwwata illah billah) tana gama fa'din hakan tasa kanta tashiga parloun gida. Cikin sa'a ma data 'dan watsa ruwa ajikinta sai taji dama-dama aranar kam basuyi da'de ba sukayi bacvi dan duk sun gama gajiya. Da safe da Teemah tatashi ji tayi kanta yayi mata nauyi sosai sai data nemi panadol tasha bayan sunyi breakfast kafin tajita 'dan dai dai. 12:00pm nayi abincin rana ya iso musu daga gidan Anty lokacin ma duk basu fara jin yunwa ba kasancewar basu ci break fast 'din da wuri ba gashi Anty tasake lodo musu wani abincin. Sai da suka yi sallar la'asar kafin suka fito dan tafiya gida, Mahmud da kansa yagama musu komai na tafiya inda sukkansu zasu sau'kane a Abuja zasu kwana agidan Ummah inyaso washe gari sauran 'kawayen Teemah sai su bi mota su wuche gida. Dazasu tafi Teemah kuwa sosai takeyi ji tayi kamar ta bisu amma badama, haka ta 'karaci kukan ta tayi shiru danko mai lallashi bata samu ba,Mahmud daga wajen gate ya tsaya ya turo aka ce su fito dan haka ko ganin sa bata samu daman yi ba balle har tasamu ban baki daga gareshi. Bai dawo gidan ba sai 'karde tara na dare 9:00pm wanda alokacin idanun Teemah tsuru tsuru duk tsoro yagama cika mata zuciyata na rashin jin motsin kowa acikin gidan sai ta samu guri 'daya ta takure akan kujera tunda suka tafi bata tashi awurin ba ko sallah bata je tayi ba dan tsoro, motsin kirki intayi jitaje tamkar za' a cafkota ne, anan maghrib da isha duk suka sameta batayi su ba, kuka kuwa tayi shi har sai da idanun ta suka daina fitar da ruwa ta komayi azuciyarta. Tana zaune agurin taji an mata knocking tare da sallama duk alokaci 'daya, sanin muryarsa ne yasa tatashi da sauri taje tabu'de masa 'kofar dan dama a'kage take taji motsi sai kuwa taji yazo ai ba 6ata lokaci. Mahmud shi ka'dai yazo gidan nasa batare da neman rakiyar kowa daga cikin abokansa ba. *Keep following me da sauran chakwakiya fa agaba.πŸ‘ŒπŸ».* πŸ‘ŽπŸ» *Kunsan wani abu?.... yau an 6atan raina ka'dan amma bakomai !* ~Tambayace~ β“πŸ€” *|-* Shin mu ba musulmai bane kam? *||_* Ko munfi 'karfin jarabtar Ubangiji ne? *|||*_Ko kuwa akwai wanda ya isa yace Allah be ta6a jarabtarsa da wani abu bane wanda yakasance abun 'ki agare shi? _Ni aganina bakomai_ _bane dan hakan ya faru ga bawa tunda daga_ _daga ne,_ _kuma kafin kai million dubunka sunyi experiancing makamancinsa_ _sannan abayanka ma fiye da dubu na jiran jarrabawa daga mahallici_ . _Sai de fatan Allah yasa kyakykyawa ce kuma yabamu_ _ikon amsarta da_ _hannu bibbiyu_ . πŸ‘ŽπŸ» _So wanda suke ganin kamar *SALMERH* tayi babban laifi ko kuma ta canja_ _salon labarinta data_ _ha'da auren_ _Teemah da Mahmud harma suke ganin kamar labarin yabar kan hanya ko kuma suke_ _jin daga yanzu labarin yabar kansu ma'ana sun daina bibiyarshi_ *pls* ' _kofa abu'de_ _take ba' ayi muku dole ba, dan labarin CAPTAIN ahaka yazo kuma_ _babu canji ahaka zamu_ _tafi wa'dan da suka fahimta ne ka'dai zasu gane manufar_ _labarin da kuma abinda yake nufi._ _Jinjina ga wa'dan da suka fahimceni suka kuma 'daura 'damarar bin bayana domin jin 'karshen labarin *CAPTAIN ABBAS* ina godiya sosai ina kuma fatan zaku cigaba da bibiyata dan jin 'karshen labarin.........Much luv mutane nah soyayyata daku ta musamman ce Allah yabar 'kauna._ _Masu tausayin Abbas kuma kuyi ha'kuri ni kaina yabani tausayi sai dai kuma kunsan_ _wani abu.......... yace kwananan zai mana new catch muyi ha'kuri inajin_ _sunanta...........ohh so sorry namanta ashe yace kar na fa'da yanzu shida kansa zai zo ya sanar damu.........._ Wattpadians, Facebook followers and most af all Masoyan CAPTAIN na whattsapp jinjinar bangirma sosai nake yabawa da kokarinku......kuma ina yinku iriin trillions 'dinnan.❀ *ACIGABA DA GASHI* ..........🀞🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_πŸ‘ŒπŸ» *Salmerhn ku ce*😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ⚠ ~NOT EDITED~ _In dedication_ _2 my Famliy_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Nobody wants to hear this but it's true that sometimes the person you want_ _most is the person you are best_ _without._ πŸ…Ώ *54* Mahmud shika'dai yazo gidan nasa batare da neman rakiyar kowa daga cikin abokansa ba, fuskarsa ba yabo ba fallasa lokacin daya ganta ,be yi mata magana ba kawai yasa kansa zuwa ciki itama sai ta bishi abaya ahankali bayan ta tura 'kofar. Babbar rigarsa yacire ya ajiye sannan yakoma ya kukkule 'kofofin gidam gaba 'daya ya daqo yasameta zaune akan kujera. Umartan ta yayi da tayi alwala taje tayi ta dawo sai ya mata nuni da dadduma ma'ana ita yake jira. Ahankali tace masa " _banyi maghrib ba_" dan ita zaton ta sallar isha'i zasuyi. Kallon ta yayi da mamaki ya ce " _meyasa bakiyi ba tun 'dazun"_? " _Ni tsoro nakeji Yayah tun 'dazu fah nika'dai ce agidan kuma su Hannah tafiyar su sukayi suka barni"._! Cikin shagwa6a tayi maganar tamkar zatayi kuka. Shi kuwa sai ya samu ya zauna yace mata ta hanzarta tayi toh dan lokaci na tafiya yace kuma kiyi harda isha'i ma. Sai data jero sallolinta duka biyu sannan ya tshi ya jasu suka yi wata raka'ah biyu ,sosai yajero musu addu'o'i kusan na mintina ashirin sannan suka shafah zuwa lokacin kuwa Teemah tayi hamma yafi sau a 'kirga idanunta duk sunyi luhu-luhu. Cemata yayi taje kitchen ta 'dauko plate da cups takawo. Batayi musu ba kuwa ta tashi taje har wani jiri jiri takeji tsabar baccin daya ci idanunta, babu ma inda tasani acikin gidan ita dan tunda tashigo gidan bata je ko ina ba su Hannah keta shige da ficen su tana kallonsu batare data nemi sanin ko'ina agidan ba. Ko yanzun ma da ta tashin bata da'de ba ta dawo ta e masa ita bataga kitchen 'din ba. Sai kawai ya 'mi'ke yakama hanyar zuwa itama sai ta bishi abaya, dakamsa yashiga ya 'dauko plate 'din suka dawo parlourn. Yayi-yayi da ita taci abinci ta'ki ci sai kawai tayi kwanciyarta akan kujerar dake gefensa tare da yin pillow da 'dan 'karamin throw pillows 'din dake kan kujerun, take sai bacci ya 'dauke ta awurin bada jimawa ba, shima be wani ci abincin ba dan shi'din ma ba ra'ayin cin abincin yake ba dama dan ita ne kuma ta'ki ci dan haka sai ya ture daga gabansa. 'Debe tarkacen yayi gaba 'daya ya mai da su kitchen sannan ya dawo ya tsaya akanta kamar ya tasheta dan ta koma 'daki amma sai ya barta ganin yanda ta saki ranta take baccin cikin kwanciyar hankali ga dukkan alamu akwana kin bata samu wani baccin kirki ba. Sai de duk da haka yana ganin kamar kayan dake jikintan zasu mata nauyi, anyways bari na barta in sun dameta ai dakanta ma zata tashi ta nemi rabuwa dasu. Komawa bedroom yayi yawo shirin baccinsa sannan ya 'dauko pillow yazo ya jefa akan carpet for d first time arayuwarsa ya kwanta bacci ba akan gado ba. Duk da sanyin da tiles 'din ke badawa amma haka ya daure ya kwanta awurin dan kawai ya kasance kusa da ita, domin cika amanar aya kar6a baya so hakkinta yafara hawa kanshi tun daga ranar farkon auren su. Da zai iya kwantawa akan kujerar shima amma kuma 2seater yayi masa ka'dan bazaiji da'din kwanciya akai ba, Teemah kuwa baccin ta ya riga yayi nisa akan 3seatern shiyasa kawai ya yanke shawarar kwanciya a'kasan. 'Karfe biyu da mintina sha takwas 2:18am tafarka garin yin juyi sai idanunta ya sau'ka akansa taga yanda yatakuru ga dukkan alamu sanyi sosai yakeji, sai data ta tashi ta zauna ta fahimci manufar kwanciyarsu aparlourn tunowa datayi cewa tariga shi yin bacci dan ta barshi ne yana 'ko'karin cin abinci. Sake kallonsa tayi sai taji tausayinsa ya kamata "Allah sarki Yah Mahmud" tafa'di aranta. 'Dakin da duhu amma ta daure ranta ta tashi dayake ma akwai hasken farin wata kuma ya 'dan ratso ka'dan ta jikin windown glass 'din dake parlourn dan haka batayi wahalar gane mashigar bedroom ba, sai data shiga kafin ta kunna bulb 'din bedroom 'din sannan haske ya gauraye ko'ina a'dakin, abin rufa ta 'dauko ta dawo ta lullu6a masa ahankali sannan ta koma ta sake yin kwanciyarta ko kayan jikinta ma bata tuna cirewa ba haka ta dawo ta kwanta. Kusan 22mins ta 'dauka idanunta biyu kafin wani baccin yakuma 'daukanta. Washe gari Mahmud ya rigata tashi, koda ya tashin kuwa mamaki yayi daya ga jikinsa lullu6e da abin rufa domin a iya saninsa shi be 'dauko wani abin rufa ba jiyan amma sai gashi ya tashi yagansa dashi, kallon inda take yayi sai yaga tana ta baccin ta kamar dae jiyan be ga wani canji atattare da ita ba. Ture abin ruafar yayi ya tashi yaje yayo alwala dan gabatar da sallar asuba sai da ya idar da nashi salkahn yayi azkar kafin yatashe ta dan itama tayi tata sallar. Koda ta idar sai ta hau gado tasake bu'de wani sabon babin bacci. 'Karfe shida da kwata 6:15am Mahmud ya shiga bedrrom 'din da kayan da yayi amfani dasu wurin bacci sai yaganta na'de agado, dama yayi tunanin haka tun daya ga shiru bata fito ba kuma tun 'dazu baiji motsin ta ba. Ajiye su yayi sannan yashiga yayo wanka ya dawo ya shirya cikin 'kananun kaya ya fita parlour ya zauana tare da bu'de system 'din sa. Teemah kuwa bata tashi ba sai takwas saura 7:46am ta tashi wanda ba 'karamin baccin safen datayin taji ba dan in har batayi baccin ba da wannan farkawan daren datayin ba'karamin ciwon kai zai sata ba kuma bacci zai dameta darana sosai amma yanzun kam tasan kozai dameta da sau'ki. Sai da tayi wanka ta shirya cikin atamparta suoer holland mai kyaun gaske 'dinkin dai dai jikinta, powder kawai ta shafa afuskarta sai kwalli data saka acikin idanunta ta, simple'dauri tayiwa kanta amma duk da haka sai gata tayi fess da ita, fitowa tayi parloun tasame shi zaune yana aikin duba system 'dinsa. Sai data zauna agefensa kafin tace _" ina kwana Yayah"_! Tafa'da tana kallonsa, shima sai ya 'dago ya kalleta sannan ahankali ya amsa da "lafiya 'kalau Fateemah kin tashi lafiya?" Da kai ta amsa yanzun kam tare da kauda kanta gefe dan ganin irin kallin dayake binta dashi. Tunani yake aransa wai dama haka auren yake ne?, shi be ta6a zaton haka ba, ba yau ya fara kallon Fateema ba, ba yau yafara kallonta cikin kwalliya ba amma yanayin dayake ji azuciyarsa yau 'din ya bambanta da kullum, ko 'kanshinta na yau 'din ma daban yake. Maida idanunsa yayi wurin da system 'din daniyar vmcigaba da abinda yakeyi sai ya tsinkayo muryarta tana fa'din " Yayah nifa yunwa nakeji sosai". Kallonta yayi shima sai suka ha'da idanu take yagane cewa asalin gaskiyarta kenan tafa'da masa dan yadda yaga tawani marairaice ta lan'kwasa kai gefe. Tashi yayi bayan ya rufe system 'din yace tashi muje kitchen mu samu abinda zamuyi " yayi maganar tare da juyawa ya nufa kitchen 'din Teemah ma sai ta biyo shi abaya. Tambayarta yayi me takeso taci ita kuwa tace Tea kawai takeso, Mahmud kuma yace "alright nikuma inaso da irish chips dan haka araba aikin, ki 'debo irish ki fara fere shi nikuma zan 'dora Tea 'din idan nagama sai inzo intayaki mu fere tare dan yayi sauri ko? Kai ta 'daga masa alamar "ehh" Da haka suka gama duk abinda zasuyi suka dawo kan dinning domin karyawa. Da rana ma tare dashi sukayi girkin abincin su suka ci, dan ranar Mahmud beje ko'ina ba agida ya wuni abinsa. Sai da dare ne yafita yace mata bazai da'de ba zai dawo, koda ya fitan kuwa gida yaje ya gaida iyayensa Abbah nata saka mai albarka yayinda Anty keta ta6e baki daga gefe amma bata bari kowa yaganta ba. Sai da zai tafine tace ya gaida amarya. Sai daya biya ya siyo mata kayan za'ki dangin su choculates kafin yadawo gidan dan yasan halinta bacin abinci zatayi ba musmman da dare, da ranan ma da 'kyar ta 'danci dayawa sai dayayi ta bata abaki kafin na 'dan kar6a, dan cewa takeyi wai ita bawani yunwan datakeji ai basu da'de da yin breakfast ba, shikuwa yace dole sai ta jar6a tunda har shima yaji yunwa ai yasan itama zataji saboda tare suka ci abincin. Yana komawa gida ya Teemah tafara yimasa rigimar son yin waya da Mummyn ta Mahmud kuwa yace bayanzu sai zuwa safiya dan yanzu dare ya 'danyi yace dasafe zasu 'kirata, 'kin amincewa tayi har fushi tayi dashi wai dan yace se da safe, sai da yayi mata cakulkuli kafin yasamu ta sau'ko bayan tasha dariya. Kamar yanda yafa'din kuwa washegari ya 'kira mummyn suka gaisa sannan ya ha'data da Mummyn yayi tafiyarsa cikin gida dan yasan tsakanin 'da da uwa dole akwai wani sirri. Mummy kuwa ba'karamin da'di taji ba yanda taji muryarsu ka'dai ma ya wadace ta, domin dama tana 'dan jin tsoro dan sarai tasan Mahmud ma bason auren yake ba duba da yanda ya nuna halin ko inkula da Teemah kafin ayi bikin, amma yanzu dataji muryarsu wasai batare da wata damuwa ba sai ta 'kara godewa mahallici daya sau'ka'kawa Teemahn abubuwa. Duk da haka sai data 'kara tambayarta cewa ko akwai wani damuwa, Teemah ta bata amsa da " a'a bakomai mummy ni dai inaso in ganku ne, daddy yace min zai so shi idan muka taho kuma har yanzu banganshi ba ya'ki yazo" Ashagwa6e tayi maganar, mummy kuwa sariya abin yabata ma, tace " haba Teemah dududu yaushe ma kuka tafin , kiyi ha'kuri ai kinsan yana yawan zuwa lagos 'din akan lokaci kuma duk ranar dayaje zaki ganshi tunda shi yayi al'kawari, yanzun yana da wata tafiya ne agabansa Dubai zashi kuma inajin zai 'dau lokaci kafin ya dawo" _"Toh mummy ke yaushe zaki zo"?_ _" zanzo insha Allahu, amma ba yanzu ba sai naga kin nutsu kin kwantar da_ _hankalinki_ _tukunna"._ Zata sake magana mummy ta dakatar da ita da fa'din " ina Yayan naki,? "Bari inkai maa mummy baya kusa " Da " toh mummyn ta amsa mata sannan tacigaba da jan kunnan Teemahn akan tayi wa Yayah Mahmud 'din biyayya, banda taurin kai tace komai yace kiyi masa kiyi kinji inde bana sa6on Allah bane, dan dah da tanzu ba 'daya bane komai yanzu inkika masa Allah zai rubuta miki lada kuma banda rashin kunya kinji" "Toh mummy" Yauwa 'yar albarka kuma banda 'kazanta, nama sanki da kwalliya kidingayi kullum, kuma banda taron 'kawaye barkatai, ki ringa ri'ke sirrinki kinji ko"? "Uhmm" Teemah ta amsawa mummy. Sai mummyn tace " Yauwa ina yayan "? " bari inkai masa da sauri" Koda ta kaiwa Mahmud 'dinma Mummy ce masa tayi kar fa yace zai biye mata dan tana 'yar uwarshi yace komai tayi daidai ne, tace dan nasan halin Teemah da rawar kai, idan tayi badaidai ba ka hukuntata dan ta kiyaye gaba kaji" Murmushi yayi tare da amsawa mummyn sannan yayi mata godiya sosai daganan suka yi sallama tana me sanya musu albarka. Yana gamawa Teemah tace " saura Hannah " "Me kuma ya sami Hannahn"? Ya tambayeta dagan gan batare da ya kalli inda take ba yariga yasan manufarta na fa'din hakan. Teemah kuwa sai ta wani turo baki gaba cikin shagwa6a tace _" zamu gaisa ne harda sauran friends 'dina dasuka tafi tare"_ _"Duk da wacce wayar za'ayi wannan gaisuwar, wai nikam ina taki wayar take ne ?_ Mahmud ya tambayeta yana 'ko'karin mi'kewa. _" Banda credit ko ka'dan aciki Hannah duk ta gama dashi "_ ! Cewa yayi _"jeki_ ' _dauko ingani "_ Zuwa tayi ta lalubo wayar da kyar tasamota cikin drawer dan tun tafiyar su Hannah bata 'kara bi takai ba. Gani tayi ma anmata har 12misssedcall dayake wayar na silent shiyasa bata ji. Atsaye tasame shi lokacin da ta kawo mishi wayar, sai ta mi'ka mishi tare da fa'din _" har ma ta'kirani ashe duk_ _banji ba"_ Mi'ka hannu yayi ya kar6a yana dubawa yace _" taya zakiji bayan ke da kanki baki san inda kika cusa wayar ba"!_ Yana gama maganar ya mi'ka mata yace _" sata a_ _caji naga ma 1percent yarage dab yake da 'daukewa, inya 'danyi cajin sai_ _kiyi 'kiran bari_ _na miki VTU kona bari sai na dawo_ ? " _a a yanzu_ " Tabashi amsa da sauri. Har ya juya zai fita sai ta dakatar dashi da fa'din " _Yayah pls_ _karka da'de"!_ Murmushi yayi sannan ya dawo baya ahankali zuwa inda take yace " _karna da'de kika_ _ce?_ Da kai ta bashi amsa, sai yace mata _"saboda_ _meyasa?"_ " _Tsoro nakeji ni agidan idan ni ka'daice"_ " _idan nafara_ _fita office_ _fah"_ _"Rakaka zan nayi_ _ai kullum"._ Murmushi ya sakeyi tare da kaiwa nannunsa yaja kumatunta ka'dan sannan ya juya ya nufi 'kofar fita, har ya kusan fita daga parlourn sai yace mata " _me zan kawo_ _miki?"_ _" Berries da pineapple"._ Tabada amsa da sauri. Da kai ya amsa mata kawai daga nan sai yasa kai yafice zuwa harabar gidan hannunsa ri'ke da makullin motarsa. Koda ya shiga cikin motar be tada ta ba sai da ya tabbatar yayi mata VTU 'din kafin ya tada motar tare da dannah horn, wani 'dan guntun bayaraben me gadinsa yazo da gudu ya bude masa gate yafice daga gidan. ~AFUWAN~ πŸ‘ŽπŸ» _Kuyi ha'kuri da typing errors pls wallahi bansami lokacin yin editing_ _bane shiyasa_, _And jina shiru da kukayi ma 2days amin afuwa please ,banji da'di ba ne amma yanzu kam Alhamdulillah komai zam zam._ _Comment_ _Vote_ _Share_πŸ‘ŒπŸ» *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _In dedication 2 my_ _lovely Family._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* *_Friends,* *Health* & *Love* ......... _These_ 3 _things_ _don’t come with a_ _price tags, but when we lose then we realize the *COST* ._ πŸ…Ώ *55* A kwana na hu'du da auren nasu, da dare suna cikin bacci Teemah taji tamkar ana tashin ta abaccin, ahankali tabu'de idanunta sai kuma taji tsoro ya shige ta karab 'daya, zaune ta tashi afirgice tana rarraba idanu tare da yin salati acikin zuciyarta. Matsawa tayi jikin Mahmud ta sake kwantawa tare da shigewa cikin jikin sa kamar wata 'yar baby tayi luf amma still sai taji hakan be yi mata ba, jitayi zuciyarta na fisgarta zuwa wani abu daban daya girmi tunanin ta, hakan kuma sai yasa tsoron ta yasake 'karuwa, danne fuskarta ta 'kara yi sosai ajikin katifar haka zalika kafafunta da hannayenta duk ta baibaye su ajikin Mahumd 'din. Dole tasa Mahmud sai da ya farka daga baccin daya ke yi, yana farkawa kuwa idanunsa ya sau'ka akanta mamakin abinda yasata yin hakan yayi, sai kuma yaji jikinta da 'dan 'dumi ka'dan, tunani yayi ko bata jin da'di ne, 'kila ko zazza6i ke damunta. Yun'kuri yayi da niyyar tashi sai yaji ta 'kara 'kan'kame shi kamar me tsoron kar ya gudu ya barta, _" Fateemah"!,_ Ya 'kira sunan ta ahankali adaidai kunnuwanta yanda ya tabbatar zata jishi. Teemah kuwa bata amsa ba sai ma 'kara yin luf datayi tana mai 'ko'karin cusa kanta a'kirjinsa. _" meke damunki ne_ _Fateemah?"_ Shiru ba amsa. " _Zazza6i kike jine_ ?" Yasake tambayarta. Yanzun ma shiru be samu amsar tambayarsa ba. Mahmud binta yayi da idanu mamakinsa na 'kara yawaita, ganin bazata yi masa magana ba sai ya koma ya kwantar da kansa akan pillow ya barta ayanda ta ke so 'din, yace 'kila sanyi take ji ne shiyasa, dan in bahaka ba yasan Fateemah baza tayi haka ba, tunda ba yau ne farkon ranar da suka kwanta tare ita ba, be wani da'de da kwantar da kansa ba yaji hannunta akan a'kirjinsa tana shafawa ahankali. Rintse ido yayi tare da fa'din " _innalillahi_ _wa_ _inna ilaihiraji'un, wai meke faruwa_ _ne?,meke damun Fateemah? , kardai ina shiga hakkin Fateemah azaman mu da ita batare da na sani ba?, amma har yaushe Fateemah tayi wayon da zata san haka?, this is unbelie..........."._ Tunanin sa ya yanke ne lokacin daya ji numfashin ta awajen kunnansa, ga dukkan alamu tayi nisa acikin yanayin da take 'din, dan ko daya 'dan matsar dakansa ma sake biyo shi tayi da nata kan da azama. Afirgice ya mi'ke da 'karfinsa sanadiyyar wani sabon salon daya ji take 'ko'karin yi masa. Dafe kai yayi tare da zuba mata idanu yaga yadda hannunta ke yawo akan gadon a inda ya 'daga jikinsa ga dukkan alamu shi take lalu6awa " _Fateemah!,_ " _Fateemah_ !!........ _Tashi kiji...._ _tashi_ _ki gaya min_ _meya faru, meke damunki?_ Yayi maganar yana me kusanta kansa da kunnuwanta yanda ya tabbatar zata jishi da kyau koda kuwa bancin me take yi dole zata jishi. Amma ga mamakinsa kota nuna alamun taji anyi magana da ita ma bata yi ba balle yasa ran zata bi umarnin daya bata, ganin haka sai yasa hannayensa ya tada ta zaune, tana tashi ta zauna 'din sai ta yi luuu tadawo kan jikinsa ta kwantar da kanta akan kafa'dar sa tare sar'ko shi izuwa jikinta da hannayenta. Kai ya dafe duk abin Fateeman yabi ya 'daure masa kai gaba 'daya yama rasa me ze yi mata, jiyake tamkar ba Fateema bace kamar ba Fateemansa ba, tamkar an canja masa ita haka yake gani, asanin da yayiwa Fateemah ma sam bata da gigin bacci balle yace ko mafarki ne ko kuma gigin baccin ne yasata yin hakan. Shima kawai sai yasa nasa hannun ya rungume ta izuwa jikinsa ya jinginu da jikin fuskar gadon yana shafa bayan ta ahankali, ahaka bacci ya 'dauke su gaba 'daya har zuwa asubah. Da asubah da ya tashi sai ya gyara mata kwanciya ahankali yanda baze farkar da ita ba, sannan yaje yayo alwala ya tada sallah, bayan ya idar addu'o'i yadinga jerowa yana ro'kon Allah ya sanya zaman lafiya da fahimtar juna atsakaninsu, Allah ya tabbatar da alkhairin dake cikin wannan auren yakuma kawar musu da Sharrin dake 'kunshe dashi, kuma ya shirya masa mahaifiyarsa shiriya na gaskiya. Sai daya idar da sallahn kafin yaje yatashe ta dan itama tayi nata sallahn, yana tashinta kuwa ta tashi ta zauna tare da rero salati tana kallonsa. Kanta taji yayi mata nauyi sosai sai tasa hannu ta dafe kan tayi shiru tare da sunkuyar da kanta. _"Ya dai"_ Ya tambayeta bayan ya zauna daga gefenta. _" kaina ciwo Yayah_"! " _Ohh very sorry, ki watsa_ _ruwa kafin kiyi alwalar zakiji sassauci bi'iznillah_ _inyaso ingari yawaye sai mu je_ _clinic abaki magani_ _ko"?_ Kai ta 'daga masa alamar "toh". Sai yasa hannunsa ya tayata ta mi'ke tsayen ya rakata har bakin toilet sannan yace mata ta shiga. Nuni tayi masa da towel sai ya 'dauko ya mi'ko mata da sauri dan yanda yaga idanunta yanda take bu'de su ma da 'kyar sosai yaji tausayinta ya kamashi. 8:00am ya kaita wani 'karamin private hospital aka dubata aka rubuta musu magani kawai suka taho gida, amota ya ce ta jira shi yashiga wani babban chemist dake kan hanya ya sissiyo magungunan da aka rubuta musun sannan yazo suka koma gida. Ranar Mahmud beje ko'ina ba ya zauna ya dinga kula da ita, sosai yake bata kulawa ita har yana

Chapter 27 of 67