gudu tayi cikin gida tana rusa kukan takaici bata zame ko'ina ba sai gurin mahaifiyarta.
Da k'yar tasamu Muniran tayi mata bayanin abinda ke faruwa ai kuwa take ta d'aga waya ta k'ira Anty tafad'a mata abinda Mahmud d'in yai wa 'yarta.
Ran Anty ya 6aci sosai aganinta ai tozarci yayi mata, inbahaka ba yasan baya so mai yasa tun farko yace mata yaya yadda da batun auran sai da ta riga da ta sanar da su amincewarsa kuma sai yaje yaci musu mutunci har cikin gidansu?
Safah da marwa take tayi tana Allah-Allah ya dawo ahima yazo yasameta tunda shi bai san mutunci ba.
Mahmud kuwa k'in komawa gida yayi da wuri yace su wuce yawo acikin gari basu suka dawo gidan ba sai kusan 11pm beyi niyyan shiga ciki bama dan yasan had'uwarsu da Anty yau bazaiyi musu dad'i ba.
Bai san cewa Antyn tun d'azu gadinsa takeyi ba yayinda Abbah ma duk yake kula da ita batare data sani ba.
Tana jin tsayuwar mota kuwa ta fito da gaggawa ta tare shi alokacin yana gab da shiga d'akinsa.
Mahmud!
Tafad'a ranta a 6ace.
A hankali ya tsaya tare da juyowa daidai kuwa yaji sauk'an mari tasssss akan kuncinsa.
Ido kawai ya rintse ta re da bud'e wa ya sauk'e su akan Antyn.
" baka da hankali ne Mahmud , ni zaka raina ma wayo , so kake ta tozarta ni ko,wallahi akan wannan maganar bari kaji zamu matuk'ar samu matsala ni da kai matuk'ar kace bazaka bi abinda nakeso ba..........
"Uhm-uhm fah Maryam kar muyi haka dake, karki ce zaki takurawa yarona akan abinda bashida ra'ayi domin ni bazan lamunci hakan ba ".
Bazata suka jiyo muryar Abbah nafad'in hakan sosai k'irjin Anty ya buga dan bata ta6a zaton idansa biyu ba awannan lokacin.
Shi kuwa Mahmud har yanzu kallon Anty yake da mamaki, aransa yake k'ara jinjina hali irin na Antyn tasa yana ganin cewa lalle halinta sai ita, idan dai har zata iya d'aga hannu ta mareshi akan waccen yarinyar tun yanzu toh ashe idan ya aureta ma har zanashi zata ce zatayi idan ya 6ata wa yarinyar rai, toh taya ma za'ayi na auri yarinyar da ake marina akanta, tun yanzu Anty hanyan raina ni ta bud'ewa yarinyar.
Abban sa neh ya taho ahankali izuwa inda Mahmud d'in ke tsaye,yana cikin tunanin yaji ankamo hannunsa, firgigi yayi ya kalli hannun sannan ya kalli Abban nasa.
" je ka kwanta Mahmud " kaji!
Baiyi magana ba still yaci gaba tsayuwa Abban ne yakama hannunsa ya shigar da shi cikin d'akin sannan yafito yaja masa k'ofar.
Zuwa yayi yabi ta gefen Antyn yace "wuche muje"
Ahankali ta bishi abaya har d'akin baccin nasu.
Abbah bai k'ara bi takanta ba yayi kwanciyarsa yayinda abin yaso daya farun yaso hana Anty bacci dan tana tsoron maganar Abban bata so yaji ba amma ya shammace ta, bata sani ba ashe ya biyo bayanta, dole nayi maganin abin tunda wuri tunkan abin yazo yafi k'arfina, dole nayiwa tufkan hanci.
Mahmud kuwa wayarsa ya lalub'o ya nemi Abbas a waya..........
Comment,vote and share plsπ€π»
*Salmerhn ku ce* π
[10/2, 5:59 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ π
*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Good or Bad, whatever you do will come back in one form or another; that would explain why the earth is ROUND.
π
Ώ *33*
Sau kusan uku wayar nayin ringing amma no response, har yayi shirin sake k'iransa karo na hud'u sai kuma yafasa kawai ya ajiye wayar.
Kishingid'a yayi ajikin gado na tsawon mintina shida ransa a hargitse yake jinta wai yau Anty ne ta mareshi akan wata banza, sai daga baya sannan ya tashi ya zauna abakin gadon, hannayensa ya d'ago duk biyun ya cusa su acikin gashin kansa tare da furzar da iska mai zafi daga bakinsa.
Halin Antyn sa na matuk'ar damunsa sosai, can you imaging ace mahaifiyarka amma bata k'aunar taganka cikin farin ciki akullum sai dai sa6anin hakan,abinda Anty bata masa tun yana yaro ba wai sai yanzu daya girma ne zata ce zata yi masa saboda me?
Idan da wani yake bashi labarin hakan zai iya k'aryatawa amma sai gashi akan kansa abin ke faruwa.
Ace Anty tarasa da wacce zata had'a shi maganar aure sai da waccen yarinyar??
Toh shi me zaiyi da ita?
Rashin mai bashi amsa yasa dolensa yah hak'ura da tambayar dayake yiwa kan nasa domin yasan idan ya matsa kansa zai jawo wa ciwo abanza and no body cares!
Tashi yayi ya cire rigar dake jikin sa sannan ya shiga bayi ruwa ya watsa tare da d'auro alwala yazo ya shimfid'a dadduma.
Sallar nafila ya gabatar tare da neman sauk'i daga gurin mahalicci akan dukkan al'amuransa rok'on haske, rahama da kuma kariyar Allah yayiwa iyayensa musamman ma Abbansa duk dama yaga kamar Abban ya d'an canja ba kamar kwanaki ba, amma yasan addu'a bata ta6a yin yawa a bawa kamar yanda bata tafiya abanza saboda Allah shida kansa yace a rok'eshi zai amsa.
yadad'e awurin yana Addu'o'i kafin yatashi ya kwanta ko daddumar ma be samu yah nad'e ta ba saboda bacci.
Alokacin kusan 1:06am bacci ne sosai a idanunsa shiyasa daga kwanciya sai bacci yah d'auke shi cikin natsuwa kuwa yayita shek'a baccinsa batare da yasake bi takan damuwarsa ba.
Washe gari ma da wuri ya farka domin tafiyarsa na nan aransa be fasa ba, dan haka yana dawowa daga masallaci yafara tattara d'an abinda yasan zai buk'ata ako'ina yake, abubuwan basu wuche tarkacen amfaninsa ba irinsu laptop wayoyinsa da sauran k'ananan abubuwa .
Dayake sun had'u da Abbansa da asbah a masallaci kuma yariga ya sanar dashi batun tafiyar tasa so bashi da damuwa akan haka yasan Abbahn bazai hanasa tafiya ko kuma wani abu daban ba indai bawani dalili ba kam.
K'arfe tara ya fito daga d'akinsa kafad'arsa rataye da jakansa hannunsa d'aya kuma wayarsa ce arik'e yayinda d'ayan hannun ke rik'e da key holder d'insa me tarin keys ajiki.
Guda d'aya ya ware yasaka ya rufe k'ofar parlourn nasa sannan yasake zareta.
Daga nan ya canja rik'on key d'in izuwa hannun sa na hagu sai ya maida wayar tasa zuwa hannun damansa.
password d'in dake kan wayar tasa ya cire sai yafara neman layin Abbas dan sosai yake da buk'atar ganin sa amma is hardly su had'u d'in shiyasa yake so ko samunsa awayar ma yayi.
Sai dai ko yanzun daya sake k'iran ma _call waiting_ ya gani sai ya dakatar da nashi k'iran ya d'an bashi time zuwa wani lokaci.
Kusan mintina biyar sun shud'e yana nan tsaye a inda yake still sai dai ad'an tsayuwar dayayin har ya samu chance na k'iran mummy suka gaisa yah tambayi lil sis da Daddy mummy tace masa suna nan lafiya qalau.
Hira kad'an sukayi sukayi sallama da mummyn sai yace mata shima d'in insha Allahu yau zai shigo , suna gamawa sai ya sake gwada layin Abbas d'in batare da yayi zuciyah ko fushi ba.
Amma still _call_ _wating_.
Wannan karon kam tsaki yaja tare da fara tafiyah ya tunkari sashin iyayensa da wayar tasa ahannu.
Mahmud irin mutanen nan masu son fad'ar abinda ke damunsu ga wani wanda ya kasance makusanci agaresu, yana son akan komai abashi shawara kafin yayi abin, idan ma damuwace tadameshi yafison yayi sharing ga wani sai dai wani lokaci idan ya rasa wanda zai tunkara da damuwarsa sai ya rik'e abinsa azuciyarsa duk da hakan na damunsa amma bazai fad'iwa kowa ba yafison sai wanda ya yadda dashi tukun na,kuma wannan dalilin be sa yazama mai yawan fad'e-fad'e ba, mutun d'ayan nan dai ne ke sanin damuwarsa baya kuma sake fad'i wa wani daban.
Yakan yanke hukuncin abinda zaiyi dakansa idan abu zaiyi saiyayi abun kawai ayanda ayanda yake ganin shine dai dai.
Adacan baya kafin had'uwarsa da Abbas _Anty_itace abokiyar shawaransa ita yake sanarwa da duk wata matsalar data kunno masa kai arayuwarsa, amma daga baya shikansa be san dalilin dayasa ya daina fad'a mata ba, ko dan irin shawarwarin data ke bashi ne oho, domin akowani abinda Anty zatayi selfishness take fara sawa agaba kafin wani abu, bai sani ba ko wannan dalilin ne yasashi ya janye jiki daga gareta ba, amma haka kawai yaji baya son sanar mata da wasu al'amuran da suka shafi rayuwarsa.
Daga baya ne sai yafara sanar da wani abokinsa dasukayi makaranta tare shikuma matsalarsa baya 6oye k'yashi da hassada afili yake bayyana su fahimtar hakan da Mahmud yayi sai yasa yadaina fad'iwa kowa kawai yake rik'e abinsa shi kad'ai .
Alokacin Abban sa ba sauraronsa yake ba dan abubuwa shima sun masa yawa sosai kasuwancinsa ya bunk'asa shiyasa kullum baya zama, akullum yana kan tafiye-tafiye banda matsalarsa tacikin gida, gara yan zuma daya d'an daidai ta al'amuran sa waje d'aya sannan yasamu yake d'an natsuwa agida.
Tunda suka had'u da Abbas sai yake jin har aransa yasamu aboki jin Abbas yake tamkar d'an uwansa kuma sai akayi sa'a ma jininsu ya had'u da Abbas d'in shiyasa wannan karon yake so yakai damuwarsa gurin Abbas ko zai samu sgawara me kayu daga garesa duk dama yariga ya yanke decision aransa kuma bazai canja ta ba amma dolene yaji ra'ayin Abbas akan hakan.
Yana gab da shiga shiga parlourn yaji wayarsa na vibration ahannunsa d'ago wayar yayi sai yaga sunan dake k'iran sa, nima sai na d'an lek'a kad'an dan ganin me k'iran nasaβΊ _Oga Abbas_nagani 6aro 6aro akan fuskar wayar.
Yana ganin Abbas neh sai yah dakata da tafiyar tasa cak ya tsaya sannan yayi picking call d'in yakai wayar kunnansa.
Abbas ne yafara fad'in "yah ne corper kana lafiya?
" qalau" Mahmud d'in yace agajarce, sannan ya cigaba da fad'in " tun jiya fah naketa neman layinka amma baka picking me yasa?
" ainasan sekayi magana tunda naga missed called d'inka jiya,nagaji ne wallahi ina hutawa shiyasa kuma banma jiba cuz' wayar na silent,inama da niyyan k'iranka fah se kuma k'iranka yashigo"
"Ba wannan bama tunda kasameni yanzun then fad'amin abinda ka k'unshe dan nasan wannan duk damuwar k'iran ba'a banza ba."!
Abbas ne yafad'i hakan yana murmushi tamkar Mahmud d'in na gabansa.
Mahmud d'inma murmushin yayi sannan yace "kana ina ne yanzun inaso mu had'u fah "
" tasamu kenan,
" a' a kai bakomai babu wani abinda yasamu" Mahmud ya dakatar dashi da fad'in haka.
Sai Abbas yace
" kuma kaga nad'anyi tafiya yanzu haka ina borno inajin kuma anjima kad'an za mu wuche".
"Shikenan toh nima yanzu nake shirin komawa sai dai da k'yar mu had'u may be kafin na iso kunwuce kasan nazo lagos 2days back"
" Haba mana 2days kuma har zaka koma?"
" ehh kamanta bautar k'asata nakeyi ne?, Kabari insha Allahu idan na sauk'a zamuyi magana."
Mahmud ya k'arashe maganar da d'an gaggawa dalilin hango mahifinsa dayayi
ya fito da shirin zuwa office dan hannunsa rik'e take da briefcase d'insa, bayan Abban kuma Anty ce itama ga dukkan alamu fitan zatayi.
Yana yanke k'iran suka had'u dayake dama ba wani tazarar kirki bace atsakaninsu.
Suna had'uwa sai ya gaishe dasu, Anty yafara gaisarwa dayake sun riga da sun gaisa da Abbah tun a hanyar dawowa daga masallaci sai dai ko gaisuwa ta biyu.
Antyn ma adak'ile ta amsa masa yayinda Abbansa ya cira hannu yah mik'a masa sukayi gaisuwar muslunci yana murmushi yace "harka shirya kenan"
" ehh Abbah inajin daganan ma sai airport"
" Abbane yace bakace tafiyar sai 11:30 ba?
" ehh zanbi wajen Jabir ne kafin na wuche".
" alright ba matsala Allah ya tsare ya bada sa'a"
"Ameen- Ameen Abbah".
Duk maganar nan da sukayi Anty kauda kanta gefe tayi tamkar bata jinsu, Mahmud kuwa yana gamawa da Abbansa ya dawo gareta yace mata zai wuche .
Tunani tafara aranta wai dama dagaske Mahmud ayau d'in zai koma?
Kar dai duk akan maganar Munira ne ya yanke wannan hukuncin? Toh idan yakoma ayau ai tamkar ya dakatar da batun auren ne, while itakuma dawuri takeso ayi.
Koda ta tambayeshi dalilin tafiyar sai ya ce mata akwai aikin dake jiransa ne acan shiyasa.
Sababi tafara ranta a matuk'ar 6ace take fad'in
" aikin banza aikin wofi, harni zaka nuna wa wani aiki, ince dai service kajeyi acan d'in ba neman aiki ba da har zaka min iyayi anan.
Cewa yayi " shi d'in dai service d'in nake fad'i bakomai ba Anty".
Bud'e baki tayi tacigaba da masifanta inda acikin masifar tace ai akwai mutane dayawa da wannan bautar k'asan duk ba yinta suke ba why not shima ya tura musu ko nawane suke buk'ata inyaso yayi zamansa agida basai ya koma ba"
Shikuwa yace a'a yafi buk'atar yayi bautan dai kodan saboda ya jaddada kasancewarsa cikakken d'an k'asa.
Aikuwa sai tacigaba da fad'in wai Mahmud ya raina ta sam baya bin maganarta dan me zai ringa ja inja da maganarta abinda daa ba haka yake mata ba , kenan ya je yakoyo banzan hali zai zo ya rink'a yi mata sai kace ba ita ta haife shi ba"
Kallonta suke yi daga Abbah har Mahmud suna mamakin masifar tata ta dosa da kuma dalilin yinta.
" wallahi indai kace ni zaka raina akan wata banza zaka..........
Da k'arfi cikin tsawa Abbah yace " shut up maryam....,stop it,how dare you zaki ringa fad'in hakan infront of me!"...
Yatsansa ya d'aga sama yayi nuni da gefensa kana yace " waccen d'in fah da kike so ki zaga 'yar uwata ce!, gudan jinina!!, ita kad'ai nake dashi !!!meyasa baki gane abu ne ke,.......yatsan nasa ya dawo dashi saitin Antyn sannan yace " kinsan Allah, idan nak'ara jin kin fad'i ba dai dai
ba akan Kha.....kha....di...........
Sai yayi shiru yaja tsaki.
Hannun Mahmud ya finciko ya yi gaba dashi har gurin da driver ya ajiye motar da Abban zai fita da ita.
Nan yace Mahmud yashiga motar sai dayaga yashiga sannan Abban shima yaxaga yashiga.
Mota d'aya suka shiga suka tafi suka bar Antyn tsaye agurin tamkar andasa ta.
Mahmud kuwa hamdala yake ta yi azuciyarsa duk dama ba hakan yaso ba, hak'ik'a duk d'ah nagari bazai so ya ringa kallon husuma na tashi acikin gidansu tsakanin mahaifansa kuma yaji dad'in hakan ba.
Amma shi kan sai yaji farin ciki kad'an bawai dan Abbah yayiwa Anty masifah ba " a'a "
Canjin daya gani azahiri tattare da mahaifin nasa shine yasashi farin ciki.
Lalle Allah maji rok'o ne yakan amsa addu'o'in bayinsa aduk lokacin daya so hak'ik'a yau ranar farin ciki ce ga Mahmud domin yau yaga mahaifinsa na acting as Magidanchi cikakke mai fad'a aji acikin gidansa, sa6anin baya da komai in za'a yi baya ta6a tankawa koda kuwa abin ba dai dai bane sai dai yayi shiru yasa ido yana kallo.
Abbah office d'insa ya wuche da Mahmud sukayi zamansu aciki suna d'an ta6a hira kamar bashi bane yayi masifah d'azun, ayyukan dake gabansa ma dakatar dasu yayi yah bada hankalinsa ga d'ansa suka fahimci juna sosai anan ne Abban ya nemi jin asalin ra'ayin Mahmud akan waccen yarinyar Mahmud kuwa bai 6oye masa komai ba ya sanar da shi akan sam baya so saboda yarinyar yaga kamar bata da tarbiya kuma ma shi ba yanzu zaiyi aure ba sai zuwa gaba.
Kwantar masa da hankali Abbah yayi akan batun auren da baya so d'in kuma yace insha Allahu babu mai yi masa dole matuk'ar yana numfashi, amma batun bayanzu zai yi aure ba yama daina fad'i dan aure lokaci ne idan kuma lokacinka yayi babu makawa sai anyishi koda kuwa ba'a so yana faruwa ne tamkar mutuwa.
Godiya sosai Mahmud yata yiwa Abbahn nasa take kuwa sai yaji duk wani damuwarsa ta kau dama dan haka yake so ya had'u da Abbas saboda idan ya yi magana da mutun akan matsalarsa yakanji kwarin gwiwa sosai sa6anin barinta azuciyarsa.
Magabar dayayi da Abbansa sai yaji yama fasa sanar da Abbas maganar tunda Abbansa yah bashi assurance mai kyau akai so yanzu baya buk'atar sake ji, komai daga wani.
'Karfe goma daidai Abbah yak'ira drivern office d'insu yace ya kaishi airport d'in saboda hold-up ma yasan kafin su isa lokaci zaiyi yak'ara da fad'in ya k'ira jabir d'in yabashi hak'urin rashin had'uwarsun yace masa Abban ne ya rik'esa a wurinsa.
Mahmud
Yana dariyah yace " haba Abbah bakomai zanyi masa bayani insha Allahu"
Daganan sukayi sallama Abbah yayita masa addu'a har suka rabu.
Comment vote and share plsπ€π»
*Salmerhn ku ce**π
[10/2, 6:00 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* π
HAPPY ANNIVERSARY
sis HUSSAINAH B ABUBAKAR (Mrs Abubakar)
*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Ya Allah, turn our sadness to happiness,frowns to smiles,hate to love, weaknesses to strengths, and cleanse us of our shortcomings.
π
Ώ *34*
Tun lokacin da Abbah ya fara yiwa Anty tsawa akanta taji duniyar ta tsaya mata cak, wani duhu taji ya mamaye ilahirin kanta har cikin k'wak'walwarta gaba d'aya, wasu abubuwan daya fad'a d'inma bata jisu da kyau ba ido kawai ta tsurawa fuskarsa yayinda yake mata masifar inka ganta alokacin zaka zaci hankalinta da nutsuwarta ta mayar akansa don ta fahimci me yake nufi da kyau, amma azahiri ba haka bane.
Anty ta kusan minti goma agurin tsaye tana tunani abin ne takeji wani banbara k'wai it seems different, kamar almara............wai yau ita Abbah ke yiwa tsawa akan abinda be taka kara ya karya ba.
Jijjiga kai tayi da k'arfi take sai tunaninta ya dawo daidai, gani tayi ba kowa agabanta ita kad'ai ce tsaye awurin, koda ta kalli gefe da gefenta ma duk haka tagani bakowa,da sauri ta juya takalli inda motar Abban ke ajiyeh sai taga wayam bakomai, alamar sun ma bar mata gidan gaba d'aya batare data sani ba tsabar yanda ta shiga zurfin tunani.
Ranta taji ya matuk'ar 6aci,wani 'kullutun daya kullera azuci ji tayi tamkar ta kurma ihu ko zai waraware, ahankali tafara d'aga k'afafunta tajuya da niyyar shiga cikin gida saboda fitar ma jitayi tafice mata arai.
Kan kujera taje ta zube sharab tamkar wata majinyaciya, sam takasa yadda cewa wannan ABBAn mahmud ne, ji take kamar an exchanging mata shi ne gaba d'aya, inkuwa wannan mutumin da kuma wannan al'amarin daya farun ya kasance gaskiya to kuwa hakika zama bai ganta ba.
Bazata ta6a bari aci nasara akanta ba matuk'ar tana numfashi,kuma nan take tayiwa kanta alk'awarin tarwatsa rayuwar duk wani mai shirin yiwa aikinta _zagon k'asa_ (khadija candy).
Tayi alwashin koda waye ke yi mata hakan sai taga bayanshi sannan wannan auren data fara magana akansan bata ga uban daya isa ya hanasa faruwa ba matuk'ar tana numfashi, ada bata d'auki al'amarin da wani girma sosai bama, saboda kawai tana tunanin zata lalla6e shine ahankali ya amince ya auri Muniran tunda ita ta nuna tana sonshi, amma yanzu ji takeyi aranta kodan abinda Abban Mahmud yayi mata ayau d'in sai ta bawa duk wani mai shirin shiga tsakaninsu kunya, sannan kuma daga baya ta kuma tarwatsa shi kamar yadda yafara had'a mata hargitsi acikin gida.
(Kunsan shi me yin abu akullum shi tunaninsa kowa ma yanayi ne, gani suke kamar duk abinda yasame su toh yi musu akayi, gaba d'aya mantawa sukeyi da k'addara)
Allah ubangiji kasa mufi k'arfin zuk'atanmu _AMEEN_ .
Koda Mahmud ya koma damaturun babu wani abinda yakeyi saboda already ya gama abinda zaiyi tun kafin yaje lagos kwanaki.
Abinda ANTY tace yayi d'in batasan yayi hakan tun kafin ta furta ba,so yanzu bawani zuwa wurin bautan k'asa daya keyi zamansa yake kurum agida, sai dai suje yawo, ko suyi karatu suje ziyara inda suka sani idan ta kama,wani lokaci kuma daddyn Teemah yajashi suyi tafiyah tare.
Yakan d'an ziyarci wajen dayake service d'in amma sai lokacin daya ga dama, kuma zuwan ma yana zuwa ne bawai dan yayi wani abu ba kawai yana zuwa ne dan ya san meke faruwa awurin kar shirun yayi yawa.
Wani lokaci acikin ransa sai yaji cewa bai kyautawa Anty ba daya k'i zama awurinta, yasan amatsayinta na mahaifiya dole tana buk'atar sa akusa da ita musamman ma daya kasance shi kad'ai ALLAH YA BATA dole tarink'a jin kewar d'anta.
Amma sam bazai iyah zama a Lagos ba yanzu, sosai yagaji da fitinar Anty, bata k'aunar azauna lafiya ita sai k'ak'ale-k'ak'ale.
Wannan dalilin ne yasa yaji zamansa a damaturun yafiye masa can tunda mahaifinsa bai hanasa ba.
*****
Lokacin da aka fara zana waec kusan tare Mahmud da Teemah suke yi dan baya ta6a barinta tayi karatu ita kad'ai ko exam d'inma zataje tare suke tafiya.
Ana tsakiya da waec d'in ANTY tasake hura masa wuta akan yadawo gida haka nan tunda already yagama service d'insa toh zaman me kuma yakeyi, tace masa ya dawo gida wai afara maganan aurensa da Munirah.
Tambayar ta yayi cewa "wani maganar aure kuma ?.
Dan shi shaf yama manta da batun tun sanda yadawo nan, bai sani ba ashe abin har yanzu yana ran Anty.
Koda ya tambayetan haushi taji bata bashi amsa ba sai kawai ta yanke k'iran daga 6angarenta tacigaba da masifah.
Acikin kwana biyu tak'ira shi yafi sau a'kirga kuma duk akan maganar ne, daya ga haka sai ya 'kira Abbansa yayi masa bayani.
Abban nashi ma cewa yayi ya koma gidan kawai tunda haka mahaifiyarshi keso shi yasan mai zaiyi akan maganar auren.
Bai 'ki maganar Abban ba amma yace masa sai an gama weac zaizo, daga lokacin zuwa agama d'in yakama kwana tara kenan ya rage.
Dahaka sukayi sallama da Abban nasa kowa ya yanke 'kiran.
Mahmud wannan karan kokad'an bai bari Mummy ta san da labarin ba, dan yasan tana sani zata sashi agaba sai taga yatafi itama kafin hankalinta ya kwanta,bawai dan ta gaji da zamansa tare dasu ba " a'a " kawai wai dan kar ashiga hakkin mahaifiyarsa ne.
Tun kafin a kammala waec kuwa yafara shirye-shiryen tafiya gida, kwana biyu bayan waec d'in ya shirya yatafi wannan karan kam shirinsa na barin garin ne gaba d'aya, saboda da wuya ya sake dawowa, duk wani abu da yyake nashine na buk'atarsa ya tattare su haka yatafi ya bar kowa da k'ewarsa agidan.
*****
Dawowar Mahmud Lagos shiyafi komai faranta ran Anty dan tana ganin kasancewar sa tare da ita shine zai sa burinta yayi saurin cika, musamman ma yanzu da take ganin yin auren nasa shine zai sa ya rabu da son rayuwa awurin Khadija, tunda idan da aure akansa ai bazai yi gigin son tafiya wani gari yabar iyalinsa ba.
Adole take sa shi ya shirya ya ziyarci Muniran batare da yaso ba, kuma wannan shine karo na uku kenan dayake zuwa wajen Muniran, sai dai abinda Anty bata sani ba shine zuwan nasa ba anfanan su yake da komai ba saboda a duk sanda zai baya fad'a mata wata magana daban face sake jaddada mata dayake akan baya kaunarta and he can't even marry her saboda bata dace dashi ba.Maganar arzi'ki bata ta6a had'asu ba.
Antyn ce da kanta tasa Mahmud ya sanar da Abbansa cewa ya samu matar aure wai aje ayi masa tambaya, afad'ar Antyn
wai in itace tayi ma Abbab maganar tasan ba amincewa zaiyi ba kuma zaiga kamar ra'ayinta bana Mahmud d'in ba. Shiyasa take so shi yaje dakansa yayi bayani.
Nan ma da 'kyar Mahmud ya yadda ya amince akan zashin d'in har sai da yaga ranta na shirin 6aci kafin nan ya amince da zuwa d'in.
Da farko kafewa yayi akan shi bazai iya ba, ita tayi magana wa Abban nasa mana ai ba dole sai shi dakansa ba, kuma dagangan ya ya kafe akan hakan saboda yasan tana tsoro yanzu bakamar da bah, bazata iya fad'an ba shiyasa shima ya kafe akan hakan.
Dayaga rantan ya 6aci kafin ya amince akan zaiyi magana wa Abbahn saboda shi wannan mitan ya tsana bakomai ba, itakuwa Anty babu abinda yafi birgeta akan tayita k'ananun maganganu......aganinsa fah.
Ranar wata talata da dare around 8:00pm yaje yasamu Abban bayan sallar isha'i,
Abban ma na ganinsa ya fahimci akwai abinda ke damunsa, domin jikinsa sanyi k'alau ya shiga gurin Abban, zuciyarsa duk ba dad'i don ya tsani yarinyar can bai san me yasa ba, gashi mahaifiyarsa ta nace akan dole sai ita zai aura, infact shi auran ma ba yanzu ya shirya yi ba gaba d'aya.
Zuwa yayi ya zauna akusa da Abban ya gaida shi, shiru ne yabiyo baya bayan Abban ya amsa gaisuwar cike da kulawa.
Mahmud rasa ta inda zai fara yayi bai san yanda zai fara fad'ar maganar ba, dayake asali Mahmud shirgin mata bai dameshi ba, shi sam bashi da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 67