sai da yaje ya watso ruwa kafin yazo ya kwanta, yana sa jikinsa akan gadon kuwa ko addu'ar bacci be gama ba yaji wani bacci me shegen nauyi from no where yana firgarsa har idonsa ma baya iya bu'dewa, be masan lokacin da baccin ya 'daukesa ba danko addu'ar yin baccin be gama karantowa ba, be tashi sanin kansa ba har se lokacin sallar asubah, har alokacin kuwa baccin be bar idanunsa gaba 'daya ba still yanajin idanunsa na masa nauyi, da 'kyar ya ya'ki zuciyarsa ya samu ya tashi, koda yatashi sai be ga Fateema akan gadon ba, sai yayi zaton ko tana bayi, zaman kusan minti biyar yayi amma beji motsinta aciki ba kamar yadda bega alamun ta a bayin ba, tunowa yayi yau ko motsinta beji ajikinsa ba _"where_ _is she_ _toh_ ? dan har yanzu wutar 'dakin akashe yake, in kuwa Fateemah ta tashi ne yasan dole sai ta kunna wuta saboda tsoron da ya san tana dashi.
Sai da ya duba cikin toilet yaga bata nan kafin ya wuche parlour 'a'dan rikice dan zuwa yanzu ya 'dan fara shiga ru'du da rashin ganin Fateeman, switch ya kunna na parlourn sai ya hangota kwance a'kasa ta kwanta akan ruwan cikinta tana baccinta cikin kwanciyar hankali, ajiyar zuciya ya sau'ke daya gantan sai ya sake kashe mata wuta ya wuche ya yo alwala, sai da ya idar da sallah ya 'daga hannu ya jero addu'o'i sosai kamar yanda yasabayi kullum, sannan ya tashi ya koma parlourn domin yatashe ta.
Lokacin data tashin ita kanta taso tayi mamakin inda ta ga kanta saboda kalle-kalle tafari da mamakin meyasata kwana ana 'din, sai daga baya da ta'dan yi recalling abin da yafaru sannan ta tuna ashe da 'kafafunta tazo parlourn.
Koda ta ganshi agefenta kuwa take sai ta tura baki gaba tare da kau da kanta gefe tana wani yatsina fuska
_" meya faru ne Fateema, meyasa kika dawo nan kika kwanta ke 'daya"?_
Mahmud yayi maganar cike da kulawa.
Yana kaiwa ayar tambayar tasa kamar jira take yayi shiru sai kawai ta mi'ke tsaye bata ko 'kara kallon inda yake ba, binta yayi da idanu harta 6acewa ganinsa yana mamakin 'kin kula shin data yi, wanka tayi tafito , lokacin ma gari har gari yafara haske, gurin dressing mirror ta nufa tana goge jikinta da towel , Mahmud kuwa yana zaune agefen gado yana kallon bayan ta, sai da tazo ta bu'de closet 'din kayanta kafin tace _" ina_ _kwana yayah"_ tayi maganar kanta akan kayan batare data ko kalli inda yake ba, shima be amsa mata ba illah hannunta da ya jawo ta dawo gefe dashi ya zaunar da ita, tana 'ko'karin sake tashi ya dakatar da ita da fa'din " _inajinki me kika ce_ " yafa'da yana kallonta, " _ina_ _kwana_ " tasake fa'di atakaice kanta na 'kasa.
Murmushi yayi batare da ya amsa gaisuwar ba yasake fa'din _" sallar fah sai yaushe zakiyi?"_
_" Nayi"_
Yace
_"Yaushe?_
_'"Dazu"!_
Tabashi amsa tana yun'kurin tashi.
_" a ina kenan?"_
Yasake tambayarta.
Sai ta bashi amsa da fa'din _"a parlour._ "
Jijjiga kansa yayi dan yasan 'karya take bawani sallar datayi.
_" wai laifin menayi ne haka lil sis please tell me kinji_ _banson kin......_
Be 'karasa maganar ba ta tare shi da fa'din _" bakai bane,_ _jiya ciki na ciwo yatayi dadare_ _nakasa bacci, ina ta tashinka kai kuma ka'ki ka kulani, bayan nasan kana_ _jina "_
Kansa yadafe tare da fa'din
_" innalillahi, ya akai duk bansan anyi haka ba, pls_ _Fateemah kiyi ha'kuri kinji aikinsa bahaka nake yi miki ba ko, wallahi jiyan_ _ne baccin ya min nauyi ni kaina nayi mamaki, amma insha Allahu hakan_ _bazai sake faruwa ba kinji"_
Shiru tai masa batayi magana ba,
_" bazaki ha'kura ba_ _ko Fateemah?_
Tashi yai kamar zai tafi irin yayi fushi 'din nan shima, take sai Teema ta kamo hannunsa koda ya juyo kuwa sai suka ha'da idanu, kai ta jijjiga masa sai yace mata _"kin_ _ha'kura"_ da kai ta amsa masa alamar _"ehh",_ yana ganin hakan sai yadawo gefenta ya zauna yace toh tayi dariya yagani, murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta 'kasa shima murmushin yayi yace cikin zolaya yace _" wato dan na 'ki kulaki shine kika yi fushi kika koma parlour kika barni ni 'daya a 'daya a'daki ko?._
Dariya sukayi atare daga nan maganar ta wuche suka shiga harkokinsu kamar kullum.
'Karfe takwas 8:am na safe Mahmud ya wuche offfice tare da rakiyar Teemah har wajen da zai shiga motar sa, tana 'kara jaddada masa wai ya dawo fah da wuri dan ita tsoro take ji, kullum dama inzai fita sa'kon ta kenan, sai kuma tace ya siyo mata tarkacen fruits da har yau tafi sansu akan abinci, takan sha ko ci aduk lokacin da Mahmud ya matsa mata akan taci abinci, wani lokaci kuma sai taci abincin musamman ranar da ya 'ki siyo mata fruits 'din, yauma daya tambayeta abinda zai kawo mata sai tace masa Apple kawai takeso yau, murmushi kawai yayi ya juya ya shige mota dan baya so ta sake yin fushi dashi akaro na biyu badan haka ba da bazai siyo mata ba, dan yasan idan tana ganin fruits 'din bata ta6a waiwayar abinci akan lokaci sai ta ga dama.
Bye-bye ta masa daga nan yaja mota ya fita agidan shima yana me 'daga mata hannu.
*****
Duk wani abu daya rage na tafiyarsu Daddy yayi ya kammala komai harma yarage saura kwana biyu kacal su tafi, Mummy taso taga 'yarta kafin su tafi amma Daddy ya hana ko awaya ma yahana ta sanar da ita saboda baya so ta 'daga hankalinta, yafi son tayi zamanta hankali kwance agidan mijinta batare da sa damuwar komai aranta ba, Mummyn ma damuwarta ayanzun bai wuce tasan irin zaman da Teemahn keyi da Anty ba abinda yafi damunta kenan, dan tasan 6angaren Mahmud da sauki duk dama tana zargin bason auren yake ba, amma koda ta 'kira Teemah awaya bata samun labarin komai, Teemah bata sanar da ita matsalar dake damunta, akullun cikin farin ciki take jinta, tun tana zargin ko Teemah na 6oye mata ne har tazo ta yarda cewa Teemahn bata tare da damuwa, fatanta dai Allah yasa hakanne, Allah ya wanzar da farin ciki da zaman lafiya a tsakaninsu gaba'daya.
Wata'kila shiriyace tazo wa Antyn shiyasa ta yada makan ya'kinta ta ri'ki Teemahn amatsayin matar 'danta Mahmud.
Mummy takanyi murmushi ita ka'dai idan hakan yazo ranta domin babu abinda ya fimata da'di da farin ciki ayanzu irin taga Teemah na rayuwa cikin walwala ga dukkan alamu kuma burin ta ya cika.
Hatta Ummah da su Hannah basu sanar da ita tafiyar da iyayentan zasu yi ba, dan gaba 'daya Daddy ya hana kowa sanar da ita, bayan kwana biyu ranar wata litinin da 'karfe biyar na yamma jirgin su yatashi zuwa dubai tare da rakiyar Abbas daya baro bakin aikinsa anan cikin maidugurin dan yakusan sati anan 'din da aka kawo su, domin kwantar da tarzoma da irin matsalolin 'yan ta'adda dake addabar yankin na arewacin Nigeria musamman ma jihar Borno, koda zasu rabu ma su Daddy na ta sa masa albarka da zuba masa ruwan addu'o'i na kariya daga dukkan munafukai da mahassada dama dukkan wani abin 'ki musamman ma yanzu daya taho nan domin yin ya'ki da 'yan addacin 'kasar tamu ta Nigeria, da Ameen kawai Abbas ke amsawa dan shi kanshi yasani zuwa yin aiki a Borno a wannan zamanin shi yafi komai risk ga rayuwar duk wani ma'aikaci irin sa, zuwa borno awannan lokacin tamkar sai da rai ne, 'kalilan daga cikin ma'aikatan nasu kan ajiye aikinsu dazarar sunji cewa zasu jihar borno, masu 'karfin imani, zuciya da tawakkali sune ke aimincewa zuwan sa6anin Abbas da dakansa ya sa aka sanya sunanshi acikin jerin list 'din amatsayin jagoran batallion nasu, domin yana ganin zamansa a borno shi yafi masa dan yasan akoda yaushe zai kasance ne cikin shirin kota kwana tunaninsa zai kasance ne akan aikinsa akowani lokaci bazai samu lokacin tuna past dinsa ba yafi son yamanta da komai.
Daga 'karshe Daddy yace masa
_"Nabar Fateemah agidan mijinta bai san awani hali take ciki ba, yace Abbas_ _duk lokacin daka samu lokacin zuwa Abuja ka daure ka 'karasa ka dubo_ _min ita amma bawai nace dole sai kaje bane karka takura kanka sai in_ _kaga kana da lokaci sannan,"_
_" bakomai daddy insha Allahu zan 'ko'karta inje da iznin Allah."_
" _Yauwa Babana Allah ya ma albarka yabaka sa'a_ _adukkan al'amuranka "_
_"Ameen Daddy_ _nagode sosai"_
Kallon daddy yayi da kyau sannan yace
" _Inason zuwan farko da zan sakeyi awannan 'kasar yakasance taron daurin auran_ _Babana nazo"_
Mummy najin haka ta dawo da kallonta ga Abbas din sai kuwa taga yayi shiru ya tsurawa Daddy idanu amma ga dukkan alamu hankalinsa da tunanainsa ba akan daddyn yake ba, sai daddyn ya dafa shi kafin ya dawo dai dai.
_"Tunanin me kakeyi kuma ?,ina fatan dai kaji abinda_ _nafa'da"._
_" ehh naji daddy insha Allahu zan_ _'kokarta."_
Jinjina kai daddy yayi cikin farin jin kyakykyawar amsa daga bakin Abbas .
Abbas sai da yaga tashin jirginsu kafin yajuya ya tafi yakoma bakin aikinsa yana me alhinin rabuwa dasu tare da tunanin dalilin dayasa su irin wannan tafiyar _.(safe trip mummy and Daddy)._
Daddy ya yanke wannan shawarar ne sanadiyyar tashe-tashen hankula da suka yi yawa a jihar yobe, har ya kasance akullum ba'a kwana atashi cikin kwanciyar hankali harin kullun da kalan yanayin sa, so 'yan uwa da dangi duk sun masa cha akan yabar garin ko dan yawan hare-haren da ake yawan kaiwa, da farko ya yi biris da maganar amma daga baya da yaga abin na neman yin yawa kawai da kansa sai ya aminche.
Daddy ya shirya musu komawa Dubai 'din ne tun kafin ayi zancen auren Teemah, da maganar auren yataso ne kuma sai ya danne nashi 'kudurin azuciyarsa har sai da aka kammala komai ya mi'ka Teemah gidan mijinta kafin nan.
*Ur comment is getting low, I feel like nima in 'dan huta, saboda gaskiya banjin dadi'n hakan da* *kukeyi* π.
_Agyara pls_ π€π»
_Nasan ana yi but_ _anunka_ ππ»
*inason ganin sharhinku kalakala ne dan idan ina karantawa ji nake kamar kar in daina wlh, INAYINKU IRIN......,,,,,,,,,,,,'Din nan .*
ππ»
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce* π
[10/2, 6:02 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ π
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
_Never argue with a fool because People might not know the difference....._
π
Ώ *57*
Ciwon cikin Teemah da yamma ya 'kara dawo mata sabo fil, gashi ita ka'dai ce agida kuma har alokacin bata sha magani ba, data rasa yanda zatayi sai kawai ta fara kuka tana mirgine-mirgine dan tayi iya 'ko'karin ta dan ganin ta danne ciwon amma sai da ya fi 'karfinta tafara kuka.
Acikin wannan halin Mahmud ya dawo gida ya sameta, ai kuwa jifa yayi da jakar dake hannunsa arikice ya kinkimeta yayi waje da ita be ma tsaya tambayarta dalilin kukan ba saboda yaga tana ta ri'ke cikinta tana mur'kususu, be manta ciwon datace cikinta yamata jiya cikin dare ba, shiyasa yana ganin ta awannan halin kawai ya nufi asibiti da ita.
Allah ma ya taimaka ba wani nisa sosai ne tsakaninsu da asbitin ba, dan haka be 6ata lokaci akan hanyar ba, duk dama zuwa lokacin hold-up yafara taruwa amma dai yasamu ya isa akan lokaci, kanta ko mayafi babu lokacin da suka isa asbitin, amma duk wannan be zo kan Mahmud ba shi dai damuwarsa aduba masa lafiyarta a kuma bata magani.
Cikin sa'a ma sai yasamu wani likita ya duba masa ita akan lokaci tare da yimata allurai guda biyu, cikin ikon Allah kuwa daga nan tasamu bacci ya 'dauke ta.
Bayani likitan yamasa game da abinda ke damunta, da kuma yadda za'a magance shi cikin sau'ki, sosai Mahmud ya fahimce shi, dan shi da farko hakan ma be zo ransa ba sam, yama manta da cewar mata na irin wannan abin lokaci zuwa lokaci, dan ko data fa'da masa cewa jiya cikinta yayi ciwo ma shi zaton shi wata matsala ce daban be kawo hakan aransa, ko data masa 'karyar tayi sallah ma yau da safe be yi wani dogon nazari akai ba dukda yana da tabbacin bata yi sallar ba.
Ya 'dauka ko abinda tasaba yi ne kullun cikin dare shiyasa ma yau daya fita ya 'kara zuwa wani 'kwararren asbitin daban domin asake duba masa lafiyarsa da kyau, yafi so yaji gamsashshiyar amsa game da matsalar dake damunsa, amma ako ina baya samun amsa mai kyau su kan tabbatar masa da cewa lafiyar sa 'qalau baya tare da wata damuwar da har zata hana shi amfanuwa, sai dai ko 'dan abinda ba'a rasa ba, ko yau 'din ma wasu magungunan daban aka sake rubuta masa tare da tabbatar masa abinda likitan daya ganshi da farko ya fa'da masa inda yabaro asbitin da zummar bada himma ga shan maganin ko dan matsalar da matarsa ke ciki domin kar ya kaita ma'kura, shikan shi yana so yaji kansa amatsayin cikakakken namiji yanaso mazantakar sa ta dawo kamar da, dukda ma acikin jikinsa baya ji kamar yana tare da wata matsala ajikinsa, jinsa yake garau, amma me yasa ba ze iya biya wa matarsa bu'katar ta ba bayan likitoci ma sun shaida cewa lafiyarsa 'kalau?
Wannan abin na 'daure masa kai ba 'dan ka'dan ba.
Baccin kimanin mintina talatin Teemah tayi sai ta farka, Mahmud tagani zaune agefen gadon da take kwance ya 'kura wa 'karfen gadon idanu, sai da ta juya ta kalli 'karfen sannan ta dawo da kallonta gareshi, _"Yayah "_! tace da dasashshiyar siririyar muryarta da bata gama warwarewa daga baccin da tashi yanzun ba.
Mahmud be ji ta ba domin be amsa sunansa data ambata ba kamar yadda be kawar da idanunsa daga inda yake kalla tun 'dazun ba.
Ganin haka yasa Teemah ta yun'kura ta tashi ahankali ta kai hannunta ta dafa kafa'darsa tare da sake 'kiran sunansa, juyowa yayi ya kalle ta take sai ya 'ka'kalo murmushi tare da dawo da dukkan hankalinsa gareta
_" kin_ _tashi?_
Ya tambayeta yana 'ko'karin kamo hannunta dake kan kafa'darsa.
Da kai ta amsa masa alamar
" _ehh_ "
" _Ya jikin naki_ ?
Ya sake tambayarta da kulawa.
Sai ta bashi amsa da fa'din
" _na daina jin komai_ _yanzu"_
Fa'da'da murmushinsa yayi tare sa fa'din
" _Masha Allah, ubangiji Allah ya 'kara sau'ki, zaki iya tafiya kuwa ko de na 'dauke ki?_
yayi maganar yana kallon cikin idanunta.
_" a'a zan iya tafiya_ _ma da kaina_ "
Teemah tabashi amsa tare da yun'kurin sau'kowa daga gadon, sai de bata kaiga ajiye 'kafafunta a'kasan ba taga gurin wayam ba alamar takalmin ta, sai ta juyo ta kalleshi tace. " _Yayah takalmi_ !
Mahmud kai ya dafe tare da fa'din
" _oups, ni ai duk ma na manta, ko tunawa banyi da batamun takalmanba garin_ _sauri, kin rikitani sosai Fateemah har ma bansan inda_ _hankalina ya tafi_ _ba"_
Murmushi tayi masa kawai dan bata san mezatace dashi ba alokacin.
Tambayarta ya sakeyi da fa'din
_" yanzu ya za'ayi ne_ _toh ?_
sai tace yakoma gida ya 'dauko mata kawai sai yazo su tafi.
Ido yazaro waje yace
" _kina nufin wai har gida zan koma in kuma sake dawowa nan?_
Da kai tabashi amsa alamar _ehh_ , jijjiga kai Mahmud yayi tare da fa'din se kace bani da hannaye, yana maganaar yana 'ko'karin cicci6anta, be zame ko'ina ba, sai inda ya faka motarsa, daya ke already likita yariga yagama dasu yagama sallamarsu
,dama Mahmud zaman jiran farkawanta kawai yake su wuche gida.
Dakansa yasata acikin motan sannan yazaga 'dayan 6angaren yashiga.
Tun kan ya 'karasa daidai ta zamansa tafara fa'din
_"alluran da wannan likin yamin fah akwai zafi sosai "_ tayi maganar tana kaiwa hannuta wurin da aka mata alluran tare da langa6ar da kanta .
_"Eyyah sorry , very soon zaki daina jin zafin ai"._
_"Ni de karka 'kara_ _kawoni gurin nan Yayah ..........!_
_"Bana ma fatan 'ki 'kara yin ciwon har_ _abada"!_
Ya tari bakin ta da fa'din haka.
Sai itama tace _"Ameen Yayah, Allah mutumin mugune, ai har nayi niyyan cizon shi danaga ya 'dauko allura kawai de_ _nabarshi ne yamin dan yanda cikina kemin zafi sosai, amma fah har guda biyu yamin dan mugunta"_
Murmushi yayi mata kawai tare da shafo fuskanta sannan yace " _Alluran ai shine daidai baki ga acikin 'kan'kanin lokaci kin samu lafiya ba"_ .
Dai-dai wani babban store Teemah tace ya tsaya tana son ta siyi abu, kallonta Mahmud yayi da sauri yace _" ina fatan de ba dangin su choculates bane, dan doctor yace ki rage shan su saboda ciwon cikin nan naki"._
_" ah ah Yayah basu bane wani abu daban nake so"_
Sai da yayi parking agefe kafin yace ta fa'da toh yaje yakawo mata yanzu sai su wuce gida dawuri ko dan tasamu ma ta'dan huta gashi maghrib takusa.
Teemah kuwa cikin shagwa6a tace masa.
_"Ni fa zan sayo dakaina "_
Kwafa yai yana kallon ta da mamaki, ganin ta'ki ta fa'da masa abinda take so 'din sai yace mata _" ba_ _takalmi ba mayafin zakije "_
Jijjiga masa kai tayi tare da fa'din masa yanda za'ayi.
Tana gama masa bayanin yafice amotar batare da yayi magana ba.
Minti goma me kyau be yi ba yadawo da leda ya mi'ka mata, kar6a tayi ta ciro takalmin ta sanya a'kafarta dayake ya san size 'din 'kafar ma sai ba 'a samu wani kuskure ba, 'dan 'karamin mayafin dake cikin ledar takuma cirowa ta yafa shi akanta.
" _Muje toh_" tafa'da tare da bu'de bangaren data ke zaune, shima fita yayi ya bi bayanta bayan ya dannawa motar lock.
Dakanta ta 'debi duk abinda takeso Mahmud na gefe yana kallonta sai da aka zo wajen biyan ku'di kafin ya ga abubuwan da ta kwaso, harara ya doka mata sai ta kauda kai tare da yin fi'ki-fi'ki da idanu, tasan daman ai hakan sai yafaru shiyasa ma tace da kanta zata shigo dan tasan inshi 'din ka'dai ne yazo 'kin siya mata zaiyi.
Be kulata ba yabiya ku'din tare da 'daukan ledan itama sai bishi abaya suka fito suka koma mota, har suka isa gida be 'kara yi mata magana ba.
Data ga haka sai ta dawo kusa dashi lokacin yana zaune akan cough a palourn su, _" Yayah_ _inkawo maka ruwa kasha_ ?
Be yi magana ba sai ya jawo ta zuwa gabanshi ya nuna ta yatsa yace _"wato_ _ke ba kya ji_ _ko?,_ _ciwon cikin be ishe ki ba ko"_
Hannayenta ta 'da go tarufe gefe da gefen fuskarta dan zaton ta marin ta zaiyi yanda taga yake maganar sosai yaso ya firgita ta.
Ledar ya sa hannu ya janyo ya ajiye agabanta yace
_" oyah fara ciro su 'daya bayan 'daya kina min bayanin su"_
Haka ta yi kamar yanda ya bu'kata amma sai da ta ciro su pads 'din data siya da farko ta ajiye ta ciro wani turare ma ta ajiye sannan ahankali tana kallon fuskarsa tafara ciro dangin choculate 'din data ta jida kusan kala hu'du.
Harara ya doka mata yakai hannu zai kamo kunnanta take tayi saurin matsawa baya tace _" Allah Yayah sunmin kyau ne shiyasa fah na 'dauko, kuma fah sabon product_ _ne baka ta6a kawo min irinsu ba shiyasa ne 'debo, bama yanzu_ _zan sha ba sai na sami sau'ki"_
_"Waye yace miki sabo ne "_ ?
Yafa'da atsawace
Sai Teemah tace " _ni ai ban ta6a gani_ _bane"_
Mahmud 'kyaleta kawai yayi ya tashi ya wuche ciki domin ya watsa ruwa ajikinsa dan yasan inya biye wa Fateemah har ciwon kai sai ta sashi abanza.
*Bayan kwana biyu*
Mahmud sosai ya dage yana kula da shan magungunan sa akan lokaci saboda shi kansa ya 'kagu yaji shi cikin 'koshin lafiya, hakan yasa sam baya wasa da lokutan shan maganinsa ko agida ko a office baya ta6a sa6a lokaci.
Acikin kwanakin kuma Anty Chideh ta ziyarci Teemah inda tasameta ita ka'dai agida saboda Mahmud na office ita ka'daice gida.
Alokacin ma Teemah na kwance tana ta trying layin su Mummy taji baya shiga abin sosai yadameta ya 'daure mata kai, dan ko no. 'din Daddyn ta ma baya shiga a'yan kwanakin, kuma kullum haka takeji in ta 'kira su Hannah da Ummah kuma sai suce mata wai sede in matsalar network ne amma su kam wai suna 'dan yawan gaisawa da mummyn ko basu kira ba ita tana 'kiran Ummah su gaisa.
Mamaki yakan cika wa Teemah zuciya, tarasa meyasa se da ita hakan zai faru, takan yawaita tambayar kanta _"toh me yasa Mummy zata 'kira kowa amma ni ta manta dani, ko dama in akayiwa mutun aure shikenan kowa agidansu mantawa yake da shi?........_
Tana cikin wannan halin taji door bell na kara, tsaki taja ta share kawai, sai da akayi tayi kusan sau uku kafin azuciye ta tashi taje ta bu'de sai taga wannan 'kawar Antyn ce tsaye ita ka'dai, dariyar ya'ke ta 'dan saki tare yi mata maraba da zuwa sannan ta bata hanya ta shigo ciki.
Anty Chideh na gaba Teemah na biye da ita abaya, sai ta ta6e baki tare da 'karewa shigar Anty Chidehn kallo.
Sanye take da wani ba'kin mini skirt wanda be ko rufe gwiwarta ba hakan ma da 'dan tsago ka'dan daga baya wanda hakan ya taimaka wurin ganin fararen cinyoyinta afili, sai wata riga wanda ta wadaci jikinta domin bata kamata sosai ba, yadin rigar kamar yadin material ne da zanen 'kananun flowers ja, kanta kuwa yasha fixing na ba'kin attachment irin wanda kana gani kasan hula ne ba gashinta bane ba.
Duk cikin 'yan da'ki'ku tayi wannan lissafin sai ta ta6e baki tare da 'fa'din _" arnanci de beyi ba, har yaushe zaka rin'ka yawo da_ _irin wannan 'dan iskan kayan acikin gari kamar baka da mafa'di."_
Afili kuwa sai ta saki fuskarta tare da yiwa Antyn barka da zuwa, bata zauna ba sai data kawo mata abinsha Kafin nan ta zauna nesa da Anty Chidehn ta gaidata.
Cikin fara'ah ta amsa mata sannan ta tambayeta ya zaman gida Teemah ta amsa da " _lafiya_ ' _kalau"_
Sake tambayarta tayi wai ina Mahmud sai *Teemah* tace " _ya_ _tafi office"_
Jinjina kai tayi tana murmushi, 'yar hira ka'dan taja Teemah dashi ganin Teemah bata saki jiki sosai da ita ba yasa bata da'de ba ta mi'ke da niyar zata tafi Teemah ma mi'kewa tayi tsaye kamar yanda Anty Chidehn tayi.
Sai alokacin data mi'ke sannan ta lura da irin she'danin kallon da Anty Chideh ke binta dashi musamman ma 'kirjinta daya kasance ana 'dan ganin kusan rabinsa awaje dan wata armless red top ne ajikin ta mai bu'dadden round neck wanda ya 'kara bayyanar da haske fatarta afili, ba karamin kar6an jikinta rigar tayi ba, ta sanya shi da wani jeans trouser daya kama jikinta sosai, gashi kanta ko 'dan kwali babu gashin kawai takama da wani 'karamin jan ribbom ba mayafi balle tacire ta lullu 6a dashi.
Afakaice ta samu taja rigar sama yarufe mata 'kirjin sannan tama ta rakiya iya bakin parlourn tadawo ciki tare da jan wani uban tsaki.
Wayarta ta 'daga ta buga shi akan kujera kamar shine Anty Chiddyn afili tace
" _Duk sharrin wayar nanne, in bahaka da nasan bazan manta 'dauko mayafi ba balle har matar nan ta ganni ahaka ba, kamar mayya sai ta ta kallon mutum tana_ _murmushi_ ."
_Your Comments always encourage me, pls kar ana manta wa........I heart u all_ *CAPTAIN ABBAS* *COMMENTERs* , _Allah yabar 'kauna._
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmern ku ce* π
[10/2, 6:02 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ π
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
_NO matter how talented you are, not everybody is going to like you, but thatβs life, just_ _stay strong and
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 67