Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mother-inlaw 'dinki ba ko?, toh let me clear up_ _your doubt"_ kirjinta ta nuna tare fa'din _" sunana Maryam matar kawunki Yusuf kuma mahaifiyar mijinki Mahmud, sannan wannan da kike gani itace lespartner 'dinki as from now kuma banson taurin kai and you must obey my rules in bahaka ba..........kasheki zanyi Fateemah in kuma binne gawarki_ _yadda babu wanda zai 'kara sanin labarinki da abinda yasameki_ ." Kukan Teemah sosai ya tsananan ta ta ha'da hannaye tana ro'kon ta tana bata ha'kuri akan bazata iya ba pls karta kasheta ta barta ta tafi wurin Mahaifiyarta. Anty ko kulata bata 'karayi ba ta juya abinta ta koma ta zauna. Anty Chiddy ne ta iso wurin Teemahn da sauri tafara 'ko'karin share mata hawaye tana fa'din " _it's ok babe.... stop crying huh........please just trust me i only_ _love u I ll not going to harm u ok...."_ Teemah duk da hankalinta yagama tashi amma hakan be hanata kau da kanta gefe ba tare da yiwa Anty Chiddyn wata muguwar harara. Ashe Anty na kallonta sai kuwa tace " _gara ma ki saki jiki yarinya ki fara 'daukan darasi domin bagudu babu ja da baya wannan tamkar cikar_ *BURINA NEH!!* ". Tana gama fa'din hakan ta tashi ta nufi 'kofar fita, harta kusa barin 'dakin sai kuma ta juyo ta dawo baya, tsayuwa tayi ta fuskanci Teemahn sannan tace _" ban baki izinin sanar da kowa abinda yafaru ba da ma wanda zai cigaba da faruwa,_ _ciki kuwa harda Mahmud da duk wani wanda kika sani, idan kika sake wani yasanda_ _labarin nan wallahi Fateemah yanka wuyanki zanyi da_ _wu'ka inkuma farka cikinki inba karnuka hanjinki,_ _kuma kar ki kuskura kiyi mata gardama like I told_ _u before nasan ai baki_ _manta ba"._ Idanunta ta mayar kan Anty Chiddy tace _" in 'taki baki ha'din kai ko tayi miki gardama pls let me know"_ Tana gama fa'din haka ta wuce ta tafi abinta. Teemah kam kuka takeyi tunda Anty ta tafi kusan mintina ashirin tana ta kuka abin tausayi sai yanzu tafi jin ba'kin cikin rashin samun mummy awaya, inba dan haka ba da babu abinda zai hana ta sanar da mummy sai de in kashetan zasuyi su kashe, amma yanzu wa take dashi , waye yarage mata?........Tasan idan tasanar da Mahmud toh dole ne Anty tasani domin ayanda tasan halinsa ba shiru zai yi ba shikam zuwa zai yi yasamu Antyn wanda hakan dai-dai yake da tsayuwar numfashinta. Tun tana kukan da sauti harta komayi azuci Anty Chiddeh kuwa tagumi kawai tayi ta zauna jigum tana kallonta, acikin ranta takejin babu da'di, saboda kukan Teemahn ba 'karamin 'daga hankalinta yake ba, ita haka kawai ta tsinci kanta da son yarinyar kuma bata jin zata iya janye ra'ayinta koka'dan akanta tariga tasanyawa ranta sha'awar kasancewa da ita amma ga dukkan alamu hakan ba ze faru ayau ba, dole ne tayi mata uzuri zuwa wani lokaci kafinnan ta warware, in hakan ya'ki yiyuwa kuwa zata yimata na dole ne koda ranta be so she can do anything just to have her as her lover. Taso ta rarrasheta akaro na biyu amma Teemah ta nuna mata 'kyama da tsana azihiri dan haka kawai sai ta tashi tafice ri'ke da tablet 'dinta ahannu. *Toh fah readers* ~Yah kuke ganin~ ~abin zai kasance ne.....?~ ~Shin Teemah zata amince da 'kudurin Anty ko kuwa akasin haka?~ ~Menene ma'kasudin~ ~na'kashewar Mahmud~ ? ~Zai sami magani~ ~~ko a 'a?~ Wai shin ina labarin~ *Captain* ne ? ~Shin akwai yiyuwar aure atsakaninsa da Fateemah ko~ ~a'a?~ ~Ku dai kuci gaba da~ ~biyoni domin~ ~jin 'karashen labarin~ *CAPTAIN ABBAS* _Ga duk mai bu'katan farkon labarin zai iya garzayawa shafina na wattpad @_ *Serlmerh-md* . 🀞🏻 _Sai kuma idan Allah ya kaimu bayan sallah da rai da lafiya zamu 'dora daga inda muka tsaya._ ~MASOYANA ACIGABA DA GASHI SUYA SAI RANAR~ ........... *ohh namanta ashe ma lokacin Gashi da suyan yazo* 🀣 _kar_ _dai amanta_ _da nawa kason_ . πŸ‘ŽπŸ» ~HAPPY EID' EL KABIR ( SALLAR CIN NAMA) IN ADVANCE.~ πŸ˜ƒ πŸ‘‡πŸΌ *ouww na manta ban sanar daku ba..... kowa yarage min nawa share 'din zan kaifa ha'kwarana sosai na kuma zauna da babban daro na domin nasan* *nama sai ya isheni.* hhhhπŸ™ˆ *SALMERH NAYI MUKU FATAN ALKHAIRI* 🀞🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmern ku ce*😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Indedication to all muslim Ummah..... brothers and sisters in islam_ *HAPPY EID'EL* *KABEEER* 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Ability is what u’re capable of doing, motivation determines what u do, and attitude_ _determines how well_ _u do it._ πŸ…Ώ *60* Da yamma Mahmud yadawo gidan kamar yanda yasaba dawowa a mafi yawan lokuta, kallo 'daya yamata ya fahimci bata cikin hayyacinta duba da yadda idanunta suka 'kan'kance suka kuma yi ja tare da yin luhu-luhu, ga kuma fuskarta ma data nuna alamun kumburi 6aro-6aro musamman saman idanunta. Da ta bu'di baki kuwa tayi masa barka da dawowa sai gaba 'daya yanayin nata yasake rikita hankalinshi, domin muryarta ma adashe take da 'kyar ta harha'do maganan ta furta masa. Tambayarta yayi abinda ke damunta cikin kulawa tare da ri'ko hannayenta zuwa kusa dashi. 'Kasa tayi da idanunta ta kasa furta masa komai, sai ma wani sabon kuka daya kubce mata. Arikice yajata ya ha'de ta da jikinsa ya rungumeta tare bubbuga bayanta ahankali, shikanshi ji yayi hankalinsa ya tashi tsoronsa 'daya kar Fateemah tafara gajiya da zama da shi ayanayin da yake ciki ne, abinda kawai tunaninsa yabasa kenan dan haka sai yabarta ajikinsa tayi ta kukanta son ranta harta gaji tayi shiru tafara sau'ke ajiyan zuciya. Sai a lokacin Mahmud ya 'dagota daga jikinsa ya zuba mata idanu yana sake karantar yanayinta. " _me yasami Fateemah na ?,pls sanar dani me aka miki, waye ya ta6a minke ?_ 'daya bayan 'daya ya jero tambayar ta sa cikin natsuwa wanda hakan yasamo asali daga karyewar da zuciyarsa tayi shikanshi jinsa yayi gaba'daya yayi laushi ganinta awannan yanayin, baya so hasashensa ya kasance gaskiya, domin in har hakanne yasan tashin hankalinsa yazo kenan. Kanta ta komar kan 'kirjinsa tayi shiru domin aha'ki'kanin gaskiya ita bata san me zata ce dashi yasa meta ba. _" please Fateemah ki sanar dani damuwarki kinji I'm always here 4u, nima hankalina_ _yakasa kwanciya, zargin kaina nakeyi akan duk wani abinda ya sameki_ _nakan rasa sukuni nima pls daure ki sanar dani kinji"_ Yanzun ma shiru tayi masa sam bata da niyyan bashi amsa ko labari dangane da abinda yafaru tsakaninta da Anty. Ko dan kasheta data ci alwashin yi akan hakan, ita kuwa ba mutuwar take tsoro ba ayanzun dan akan wannan 'kazamin aikin da suke son tayi tanaji gara mutuwan yafiye mata sai de ahalin yanzu bata so mutuwa ta risketa batare data san ainihin meke faruwa da iyayenta ba, tanaso taji daga garesu taji meyasa ta daina samunsu awaya kuma suma suka daina nemanta suka manta da ita, abinda ke gabanta kenan awannan lokacin. Ahankali cikin sanyin murya ta furta " _Yayah_ !" Sai ya amsa mata da irin yanayin data ambace san da fa'din _" Na'am matar_ _Yayah"!_ Murmushi maganar tasa yasata jin ya kwaikwayi kalar muryarta sai ta 'kara yin luf akan 'kirjin nasa ta lumshe idanunta sannan taci gaba da fa'din " _Mummy da Daddy na sun manta dani ko_ _Yayah_ ? 'Dagota yayi daga kan 'kirjinsan da sauri sai yace mata _" waya gaya miki Mummy sun manta dake,? Mummy kullun idan muka yi waya sai tace in gaisheki hakama_ Daddy shima yake fa'damin kullum" Idanu ta waro akansa alamar " _dagaske?_ Sai ya jinjina mata kai tare da medata ya sake kwantar da ita akan 'kirjin san shima ya lumshe idanunsa shiru yayi yana jin bugawar da zuciyarta keyi da 'dan sauri-sauri ,sannan yaciga ba da fa'din _"Daddy yace zaizo yaganki da kansa amma sai inyaga kin kwantar da_ _hankalinki tukun na, mummy kuwa bata son ku ringa yawan waya ne saboda ita aganinta_ _kamar inkuna waya da ita akai-akai tunanin gida bazai barki da wuri har ki_ _kyautatawa auranki ba, itama tafiso sai kin saba da gidan mijinki tukunna."_ Wannan duk shirin Mahmud ne ya ha'da ya irga mata ayanda zuciyarsa ta lissafa masa sai ya gaya mata da sunan abinda iyayenta suka fa'da masa kenan akanta, kuma yayi hakane domin ya kwantar mata da hankali badan komai ba, saboda yasan da zaran Fateemah tasan iyayenta basa 'kasar nan rigimarta ba zai ta6a 'karewa ba. Aikuwa yana gama fa'din haka ta 'dago ta kalleshi _" kuna waya da mummy kullum ko Yayah?_ Yace " _ah 'ah fah Fateema ni bance ba, ba kullum muke waya ba lokaci_ _zuwa lokaci ne yawancin 'kiran ma sai na fita office muke wayar"_ " _meyasa kuma bakuyi idan kana gida?, Yayah_ _Mummy bata sona yanzu saboda anmin aure ko?, ko to gaya mata idan_ _kunyi waya kace mata ni na fasa auren zan dawo_ _gida muyi zaman mu tare da ita"_ cikin dasash shiyar shagwa6a6-6iyar muryarta ta yi masa maganan. " _waye ya gaya miki auran nan zai rabu Fateemah?.....wannan auren babu wanda ya isa yaraba shi sai mahalicci wanda yayi dalilin faruwarsa.....ke ba kya tunanin halin da zan shiga ne idan kika barni?, pls karki sake cewa zaki tafi ki barni kinji"_ Jin yace auren nasu ba me rabuwa bane take sai ta turo 'dan 'karamin bakinta dake zagaye da pink lips 'dinta gaba alaman ta ji haushin hakan kenan. Sai daya kai ayar maganar tasa kafin ta 'daga masa kai alamar taji amma still bakin ature. Mahmud kam Sosai yanda tayin ya matu'kar birgeshi, idanunsa ya sau'kar akan la66anta da sukayi jajir dasu dayake tayi kuka sosai, take sai ya 'dago hannunsa ya wari yatsa 'daya yashafa su ahankali. Teemah kuwa 'dan jan jikinta tayi daga na Mahmud da niyyar tafiya tabar inda yake, amma Mahmud be bari tayi nisa ba yasa hannu yadawo da ita jikinsa, duk da jikinsa be nuna alamun son kasancewarta ra6e ajikinsan ba amma zuciyarsa na matu'kar son hakan shiyasa ya dawo da ita. " _kin gaji da zama da niko Fateemah_ ? Idanuta ta 'dago da sauri ta sau'ke su akansa. " _pls tell me kinji, banaso hakkin ki yamin yawa akaina dan nasan Allah sai_ _ya tuhumeni akan zama na da k......."_ Da hannunta tayi saurin rufe masa baki wanda hakan ya tilasta masa yin shiru da maganar da keyi . _" Kinsan wani abu?_ Ya tambayeta da nutsatstsiyar muryarsa. Da kai ta bashi amsa yadda zai fahimceta. Sai kuwa yaci gaba da fa'din " _kinason yin waya da Daddy_ ? Da sauri ta 'daga masa kai alamar " _ehh_ " Sai yace " _alright...., zan 'kira miki shi amma da shara'din sai kin_ _sanar dani_ _abinda yasaki kuka_ _da bana_ _nan........"._ Tunkan ya 'karasa rufe bakinsa tabashi amsa da fa'din _" cikinta ne yadameni da ciwo shiyasa tayi kuka"_ _" toh me yasa baki 'kirani awaya ba ki ka zauna da ciwo har haka, kuka yana magani_ _ne Fateemah...?, kin ga kuwa yadda kika dawo , Allah_ _dana ganki hankalina yatashi sosai"_ Shiru tayi tana jinsa sai da taji yayi shiru kafin ta ce " _Yayah kira min Daddyn toh mana yanzu !_ Murmushi yayi ganin yanda ta 'kagu dajin muryar Mahaifinta, hannunta yaja suka koma kan cushion suka zauna sannan ya lalu6o phone number 'din daddy ta Nigeria dagangan yayi dialling dan yasan sarai bashiga zaiyi ba. A speaker yasaka wayar dan haka ba sai ya bu'di baki yayi mata dogon bayani ba akan wayar daddyn, saboda da kunnuwanta taji ance numbern is switch up. Langa6ar da kai tayi gefe kamar zatayi kuka ganin haka sai Mahmud ya hau bata baki akan wai tayi ha'kuri may be Daddyn ya 'danyi wata tafiya ne, yace nikuma kinga bani da numbers 'dinsa na waje ko'daya balle muyi trying, amma bari zan tambayi Abbah I'm sure bazai rasa agunsa ba. " _Toh yayah 'kira ka tambayeshi mana tun yanzu kar ajima kuma ka manta_ " Ajiyan zuciya ya sau'ke tare da ajiye wayar agefensa bayan ya dannata tashiga security dan kar ma Teemah ta 'dago 'karyar da ya shirga mata, sai yace da ita _"Nagaji kinji yanzun lil sis ki bari idan na 'dan huta anjima sai naje gidan ma gaba 'daya da kaina inkar6o inajin_ _hakan zaifi ko?"_ Yana maganar ne tare zamowa ya kwantar da kansa akan cinyarta. Teemah kuwa zuciyarta tsinkewa yayi dajin ya ambaci zuwa can gidan ita ayanzu in akwai abinda ta fi tsana aduniya toh be wuce Anty ba ta tsani ko ganin tama , amma bata yi masa magana ba sai kawai ta 'daga hannunta 'daya ta cusa acikin kwantaccen ba'kin gashin kansa tana shafawa ahankali. Mahmud kuwa lumshe idanunsa yayi tausayinta na 'kara ratsa shi, akullum yanajin kamar baya mata adalci a zaman su, balle yau 'din dayaga yanda ta dawo duk sai komai nasa ya tsaya cak, in ba tunanin mafita ba baya komai. Kusan minti sha biyar suna ahaka kafin Mahmud ya yun'kura yatashi yace zai watsa ruwa. Fita yayi bayan yagama shiryawa be zame ko'ina ba sai gidan Umar abokin aikinsa yayi masa bayanin meke tafe dashi yace yana so in zai yiwu su tafi gobe, daya ke dama Umar yace masa akowani lokaci idan ya shirya zasu iya tafiya shi ba shi da matsala. Hakan kuwa akayi domin Umar take yabashi tabbacin samun rakiyarsa aduk lokacin daya bu'kata yanzun ma cewa yayi babu komai Allah ya tashemu lafiya". Da farin cikin sa yabaro Umar din yana me jin 'kwarin gwiwa da fatan samun nasara ji yake ajikinsa kamar matsalarsa ta kusan zuwa 'karshe, da yardar Allah komai zai daidai su shida matarsa kamar yadda kowa su irin ma aurata ke rayuwa agidajensu. Daga wurin Umar Mahmud gidan mahaifinsa ya nufa amma be samu Abbah agida ba sai de Anty da ya samesu tare da Munnirah suna tattaunawa be san akan miye bane amma yanda yaga fuskarsu kamar gonar auduga yasa yagane anin farin ciki ne agare su, saboda musamman Anty tayi 'kiranta tazo domin tayi mata albishir 'din abinda take shirin aikatawa daughter inlawn ta, takuma 'kara lallashinta akan sun kusan rabuwa ai tunda Anty Chiddy yanzu matar Mahmud 'din take hari, kuma da zaran burinta yacika zata sada ta da gidan bokan dake mata aiki,shikuwa aikinsa kamar ayi yanka da sabuwar rezor blade yana yi maka aiki toh labari ze canja shiyasa nafi gane zuwa wurinsa, shegiya itakuma dan iskanci sai take ta min yanga da 'kyar nasamu ta amince zata kaini amma sai ta samu abinda take so. Dariya Munnirah tayi tace " _kice nafara shiri na kusa zama amarya"_ Anty ma dariyar tayi tace _" ai ki kwantar da_ _hankalinki ina gaya_ _miki aure tsakaninki da_ _Mahmud tamkar_ _anyi shi angama ne!_ Sunan cikin wannan yanayin Mahmud ya shigo yasame su sai de be ji abinda suke fa'di illah dariyar ya tarar. Mahmud ganin Munnira na gurin yasa be ko kula da su ba yayi wucewarsa ciki bayan sun amsa masa sallamar da yai musu. Munnira bin bayansa tayi da kallo tana murmushi musamman dataga yanda yawani basar yai shigewansa ciki aranta tace " _ohh boy.....ka gama fa'din ranka da girman kanka yanzu..... domin very soon ka kusan dawowa hannuna, kuma nawa ni ka'dai injuya ka yanda nakeso babu me takurani"_ Anty ne tabi bayansa zuwa 'dakin daya shigan bayan ta gama sallamar Munnirah ta tafi gida dan tasan ganin Munnirah ne yasa shi shigewa cikin. Gaishe da ita yayi tare da sanar da ita batun tafiyar da ta taso masa amma be gaya mata ainahin tushen tafiyar ba sai kawai yace da ita zashi katsina gobe in Allah ya kai rai domin akwai wani urgent meeting 'din da ze je yi acan. Fatan alkhairi tamishi daga nan be zame ko ina ba ya koma gida wurin matarsa. Yana zuwa kuwa ta tare shi da batun numbern Daddy sai yace mata ashe Abbah ya tafi cotonou shi be ma sani ba, amma de yana kyautata zaton dawowarshi cikin satin. Dolen ta ta ha'kura sai kuma tabawa zuciyarta tabbacin Abbah na dawowa zataje dakanta ta kar6o no. ~Barka da Sallah 'yan uwa nah,~ *ALLAH UBANGIJI YA NUNA MANA SALLAR NEXT* *YEAR LAFIYA MUNA MASU KUSANCI DA* *UBANGIJINMU.* πŸ‘‡πŸΌ ~GAREKU DUKKAN CAPTAIN~ ~ABBAS~ ~FANS DAKE KOWANI GROUP NA WHATSAPP, FACEBOOK HARMA DA WATTPAD~ _ha'ki'ka Ur comments always drive me crazy ina_ _matu'kar jin da'di, kuma yana sani nisha'di, bansan me zance da ku ba_ _masu samba'da min addu'o'in nan wallahi idan nagani_ _ji nake tamkar banda masoyi sama da me_ _min addu'ar, fatana akullum shine Allah ubangiji yabiya muku_ _bu'katunku na Alkhairi yaji'kan_ _mahaifa._ 🀞🏻 _Godiya ta ragaggiya ce compared to soyayyar da ku ke wa Littafin nan Allah ubangiji_ _ya_ _bar min ku._ *KUSANI ANA* *MUGUN* *TARE* 🀝 πŸ‘ŽπŸ» *ACIGABA DA GASHI* *MASOYAN* *ASALI...........* _wai_ _akace suya sai_ _ranar_ *SALLAH* πŸ₯°( ~aww ashe fah yau~ ~ce ranar~ ~suyan kardai amanata da nawa kason~ )πŸ™ˆ _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmern ku ce* 😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Life is so confusing, sometime what we want we don’t get it, what we get we are_ _not satisfied with it, what we expect never happens & what we hate generally_ _repeats......._ πŸ…Ώ *61* Sai da dare Bayan sallahr isha'i Mahmud ya sanar da Teemah batun tafiyan nasa, take kuwa tafara mai daru akan ita wallahi sai de sutafi tare ita bazata zauna ita ka'dai agidan ba, yace toh zai kaita wurin Anty su zauna kafin ya dawo. Ai tana jin haka sai kawai tafara yi masa kuka tana cewa ita bata so dashi zata tafi, wai dan Allah yatafi da ita, da 'kyar yasamu ya shawo kanta tayi shiru bayan ya amince cewar bazai kaita wurin Antyn ba kamar yadda baze barta ita ka'dai agida ba. Washe gari da sassafe bayan kowa ya shirya suka tafi tare zuwa gidan Umar, sai da suka tashi tafiya kafin ya sanar da su cewa Teemah zata zauna da iyalan abokinsa Umar 'din kafin su dawo, saboda tace tana tsoron zama agida ita ka'dai. Matar Umar murna tayi sosai da zuwan Teemah dan dama ba 'karamin kewar 'yan uwanta hausawa take yi ba. Bayan tafiyar su Mahmud matar Umar ta ringa jan Teemah da hira ganin ta zauna shiru kamar me tunanin wani abu. Tun Teemah bata sakewa da su har tazo tasaki jiki gaba 'daya ta saki ranta suka rin'ka surutu da yaran Umar 'din. Tare da matar Umar suka shiga kitchen suka yi girkin abincin rana (lunch) suka ci bayan sun yi sallar azahar. Sai de duk yadda Teemah ta so ta 6oye damuwarta abin ya faskara, takan zauna tayi shiru wani sa'in har se matar Umar ta ta6ata kafin take dawo da hankalinta garesu. Hakan yasa matar Umar ta fahimci akwai wani abinda ke damun Teemah. Sai de bata tsawaita tunanin ko mene ba ta de barshi akan wata'kila tafiyar da Mahmud 'din yayi ne ke damunta dayake amarya ce ita batawani da'de da yin auran ba, bayaga haka ma kuma Teemah yarinya ce dole zata damu tunda da shi tafi sabawa agarin. Bayan sallar la'asar ne Mahmud ya'kira Teemah awayarta dan yaji ya walwalarta take agidan. Cikin sa'a kuwa lokacin Teemah na tsakiyar yaran Umar suna ta hayaniya, kuma koda ta 'dan matsa gefe da su ma kafin ta ankara sun 'kara biyota dan haka kawai sai ta zauna tayi maganar acikinsu hakan yasa be wani fahimci komai daga wajenta ba har suka 'kare wayar , se ma yaji da'di ganin tasaki jikinta agidan Umar 'din. Matar Umar nada mutunci sosai kuma tana da son jama'a gata da kula da duk wani abu da ya shafi mutuncin auranta hakan yasa take da son taga duk wata 'ya mace na da babbar fada awurin mijinta bata son taga mace na wulan'kanta sanadin aure. Awayar da Teemah tayi da Mahmud sau uku a wunin ranar sai ta fahimci rayuwar auren sun kamar ba daidai yake tafiya ba, domin bata ga wani kula ko nuna damuwa da rashin junan sun da sukeyi ba awayar da sukayin face jin lafiyarta da kuma ko wata matsala na damunta abin da ka'dai Mahmud yadamu yaji kenan daga gareta duk da suna matsayin sabbin ma aurata, sa6anin ita data ke da 'ya'ya har biyu ma amma sam bazata iya yin waya da mijinta agaban kowa ba saboda bako wani irin magana zata iya fa'da agaban mutane ba idan suna waya da mijinta. Zatonta zataga fiye da natan awajen Fateema da mijinta saboda ita 'din har yanzu amarya ce amma sai taga yanayin sha'kuwa da kulawarsu yayi 'kasa da nata ne ma sosai, ko irin missing 'din junansun nan bataga alama acikin kalaman su ba. Hakan yasa taci 'damarar ankar da Fateemah babban matsayi da muhimmancin mijinta agareta. Da dare bayan anyi sallar Mahgrib suka ci abinci inda duk cin abincin Fateemahn ya kasance kamar kullum sai de ta 'dan caccakula tabari wanda matar Umar ta fahimci ko darana ma hakan ne ya kasance. Abin na bata mamaki yanda damuwar Fateemah na rashin mijinta ya bayyana kansa afili amma kuma cikin kalamanta sam babu hakan. Sai da sukayi sallar isha'i sannan suka yi zaman su apalour suna 'dan ta6a hira inda ba awani da'de ba yaran duk sukayi bacci sai su biyun suka rage. Da wannan damar matar Umar tayi amfani ta dinga jan Teemah da magana da kuma shan cikinta akan rayuwar aurensu, anan ta 'dan fahimci wani abu ka'dan, sai de bata gama fahimta ba sai washegari data bata wani magani sinadarin mata tayi mata bayanin yadda ake amfani dashi da kuma irin tasirin dayake dashi harma ta nuna mata cewar zata ji da'din mu'amala da mijinta matu'kar tayi anfani da maganain, anan ne Teemah ta nuna mata cewar ita bata san me take nufi ba kwata kwata. Matar Umar batayi 'kasa agwiwa ba ta bayyana mata komai a yanda zata fahimta. Nan kuwa Teemah ta to na ma kanta asiri dan atake ta nuna jin kunya da maganar da matar Umar 'din ta mata ta kuma nuna bata san komai akan hakan ba, sai tace da ita ai su ba irin wannan zaman sukeyi da Mahmud ba, ta ce ai yayah Mahmud ba irin mutanen nan bane shi baze yi mata haka ba. Mamakin matar Umar 'karuwa yayi akan nada da jin maganar da Teemah tayi mata ayanzun. Take sai ta saki ranta ahankali ta ringa yiwa Teemahn bayanin menene aure da kuma abinda ya 'kunsa, ita matar Umar duk akan Mahmud ta 'dora laifin tunaninta ko shima yana 'daya daga cikin irin mutanen da ke raina mace idann an aura musu ita da sauran 'kuruciyarta, amma ai zuwa yanzun Teemah tayi girman dazata iya 'daukan bu'katun mijinta duk kuwa yanda yake tunda a'kalla zata kai 18yrs da haihuwa ayanzun, dayake bata san da batun matsalar dayake damunsu ba shiyasa ta ke gani kamar laifinsa ne da har yanzu be fahimtar da Teemah ma'anar zamansu aguri 'daya ba, amma duk da haka tayi 'ko'kari wajen jawo hankalin Teemah inda ta bayyana mata asalin manufar aure a addinance. Teemah ta 'dan fahimce ta harma hakan yasa ta 'dan saki jiki ta baza kunnuwa tana 'daukan darasi domin ita sam bata san da wannan batun ba. Daga nan matar Umar ta bata wani ha'din magani me zuma aciki, maganin yamata da'di dan haka ta ringa sha abinta tana lasan baki dama ta nan tafi kauri gurin kananun ciye-ciye da kayan zaki. Daga nan suka zarce hiran rayuwa acikin hiran ne Teemah ta tuna da mahaifiyarta, take kuwa sai jikinta yayi sanyi tafara bawa Matar Umar labarin rashin jin iyayen nata da batayi ba gashi tarasa yazata yi ta same su tace kota 'kira gidan 'kanin mahaifinta ma (Daddyn Abuja) bata samun gamsashshiyar amsa daga wurin su. Ta tausaya wa Teemah har ranta da jin cewa tun bayan aurenta da kwanaki ka'dan bata 'kara jin iyayenta ba,

Chapter 31 of 67