Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gaskiya tayi sannan yace hakan ma darajar Fateemahn zataci in ba dan haka ba da beyi niyyan sake waiwayanta ba. Sosai Teemah taji da'di harma takasa ri'kewa sai da ta gayawa Antyn abinda Abbah ya fa'da, Anty tana jin haka kuwa ta rarumo Teemah ta rungumeta tana mata godiya tare da sanya mata albarka . Duk wani kulawa da ya kamata uwa tayiwa 'yarta Anty nayiwa Teemah shi inka gani sai kayi zaton tun tasowarta tare suke da ita, gata babu irin wanda Anty bata mata shi komai takeyi hankalinta nakan Teemahn motsi ka'dan tayi kuwa sai ta ji dalili ita kanta Fateemah wani lokaci murmushi kawai takeyi da canjuwar Anty. Anty tariga ta yanke shawarar Teemah agidanta zata yi duk watannin takabanta dan haka tasaki jiki sosai ta rungumi rayuwarta dana Teemahn tare da kiyaye duk wani abu da ze sa Abbah ya zargeta daga wani abu. Kwanan Abbas shida agida amma sam zuciyarsa ta gagara saduda da barin Teemah da akayi a Lagos, gani yake kamar 'kara salwantar da rayuwarta ne akeso ayi abanza. Gashi shi ba ze iya 'kara tunkarar Ummah da batun ba kawai abin nacinsa ne azuci, wani lokaci ko dadare kasa bacci yakeyi, sai ya ringa tuno da mafarkin da yayi kwanaki, idan ya fasa mafarkin nasa sai yaga kamar azahiri abin ke faruwa, tunda kam gashi Mahmud yatafi yabarsu, toh in hakane kuwa meyasa za'a bar Teemah wajen Anty data so ta lalata mata rayuwa abanza. Haushin wannan al'amarin yasashi ya kasa zama a Abuja, rana tsaka kawai ya fito da shiri yace zai tafi Porthacourt, dayake ma saura kwana bakwai za'a yi musu 'karin girman su shiyasa ma Ummah bata yi wani tsokaci game da tafiyar ba tunaninta ko wani abin zeje yayi kafin ranar dan haka kawai sai ta bishi da addu'an Allah ya kiyaye ya bada sa'a. Koda ya isa can ma bawani abu yakeyi ba dayake yana hutu bashi da aiki, tunanin nan dai ne yakasa barinsa, kusan kwanansa biyu amma still be samu nutsuwa ba, cikin hakane ya tuno da amanar da Mahmud yabashi kafin rasuwarsa, take kuwa yaji wani 'kwarin gwiwa ya shige shi. Be bari yasake kwana a rivers state ba sai daya ganshi a Lagos. Wani ha'da'd'den hotel ya nema ya sau'ke gajiyarsa dayake shigan yamma yayi washe gari misalin 'karfe sha 'daya yayiwa gidan dirar mikiya. Abbah na shirin fita sai kawai ya ganshi ya shigo daga ba'kin gate, dayake da taxi yazo so tun a wajen gate aka sau'keshi. Fuskarsa ba yabo ba fallasa bazaka ce ga asalin yanayinsa ba, amma shikam zuwansa ayanzun gaba 'daya ya tuno masa da Mahmud komai yadawo masa sabo fil. Abbah kam ba 'karamin farin ciki yayi ba da zuwan Abbas 'din dan yasan albarkacin Mahmud yaci bayaga haka yasan da baze ta6a waiwayar inda suke ba, yana godiya ga Allah sosai daya kasance abokan marigayi 'dansa Mahmud duk mutanen kirki ne hakan ma na 'daya daga cikin alamomin nagartar mutun, dan jiya Umar da iyalansa gaba 'daya suma suka zo gaishe su, daga rasuwar Mahmud zuwa yau yasamu kar6ar ba'ki da dama ta sanadin Mahmud 'din, su jafar, da wasu friends 'din sama sun zo sun gaisheshi sosai hakan yake sashi farin ciki ko bakomai yasan cewa 'dan sa yayi mu'amala ne da mutane masu kyawawanan halaye. Kar6a me kyau aka yiwa Abbas agidan dan Abbah be samu nutsuwa ba sai da yaga an wadata shi da komai da komai, musamman dayaji cewa ya kwana a hotel ne acikin gari so yasan dole zai bu'kaci wani abin zuwa yanzu. Shikuwa Abbas sam duk ba wannan bane agabansa damuwarsa tasha bambam, aikuwa ko ruwa be shaba batare da jan wani dogon lokaci ba ya bayyanawa Abbah abinda yakawo shi. Abbah yayi mamaki sosai amma yace meyasa baze barta anan 'din ba, koda watanninta ne ta 'karasa. Sai yace " _Hankalina yakasa nutsuwa ne Abbah, amanarta Mahmud ya bar min hakan yasa rashin ganin irin rayuwar data keyi yake 'daga min hankali, kayi ha'kuri Abbah ba wai na raina kulan datake samu anan 'din_ _bane kawai de inaga can 'din zaifi kaga bazatana tunani ba tunda ga Hannah nan suna tare kuma zanfi kulawa da amanarta dana kar6a idan tana kusa dani_ " Abbah beyi masa musu ba take ya amince masa, sai de yasan ba wannan dalilin bane yakawo Abbas 'daukan Fateemah ba, ta iya yiyuwa tarbiyar gidan nashi ne be yadda dashi ba ko kuma wani abu daban amma ba de wanda ya fa'da ba, duk da haka bega lafinsa ba, dan yasan koma menene yafaru bakowa bane yaja hakan face matarsa, shiyasa duk abinda zakayi ka kula kayi shi akan dai-dai in kasan farkon abu toh ganin 'karshensa ne damuwa. Fateemah kam bazeyi ba'kin ciki da tafiyarta ba duk da ransa be so hakan ba amma idan zata fi samun farin ciki acan 'din falillahil hamdu, shi bashi da haufi akan hakan, duk da ze so taci gaba da zama awurinshi amma tunda hakan baze samu ba bakomai yasan wannan ka'dan kenan daga halin rayuwa, sede ze yi ta binta da kykykyawar addu'ar dacewa har 'karshen rayuwarta. Atake ya 'daga wayarsa ya 'kirata yace tazo, itama tayi mamaki dan basu jima da rabuwa ba yace mata ze fita sai kuma gashi taji wai akawo masa kayan tarar ba'ko and now kuma wai ita taje. Hijabinta ta nema tasaka akanta, dama kullum ahaka take zuwa gurin Abbahn bata ta6a zuwa inda yake batare da hijabi ba. Amma yanzun kam tunda ta tunkari 'kofar Abbahn ta rin'ka jin zuciyarta na dokawa, haka de ta daure tashiga da sallamarta. Tana shiga kuwa idanunta ya sar'ke cikin na Yayanta Abbas. Ahankali ta 'karasa ta zauna nesa ka'dan da su, tace " _gani Abbah_ " Yana murmushi yace " _baki ga yayanki bane, naji baki gaishe shi ba_ ." 'Daga idanu tayi ta kalleshi sai taga yawani kauda idanu tamkar ma be san da zuwanta 'dakin ba. Sai itama tayi 'kasa da nata idanun tace " _Ina kwana Yayah_ ? Yace " _lafiya 'kalau_ " Kamar ba ze sake magana ba sai can yace " _ya 'karin ha'kuri_ " Can 'kasan ma'koshi yayi maganar albarkacin Abbah ne ma yasa yayi tambayar badan haka ba ze tambayeta ba. Itama ahankali ta amsa da fa'din " _Alhamdulillah_ ". Murtarta na 'dan rawa Kamar zatayi kuka, hakan yasa ya 'dago ya kalleta da kyau jin yanayin muryarta. Aikuwa sai yaga tana share hawaye, tsayawa yayi kallanta da mamaki wato har yanzu bata daina kuka ba kenan da rasuwar shiyasa ma yaga tayi fayau da yawa duk ta rame kamar ba ita ba, aransa yace " _toh ki bishi mana tunda kin fi kowa damuwa da rashinsa._ " Abbah ne yayi mata bayanin abinda yakawo Abbas 'din inda ya 'karashe da lallashi ganin cewa tunkan yafara magana ma harta fara kuka yasan be wuci tambayar da Abbas yayi mata bane yasata kuka, dan kusan kullum haka takeyi indai za'a ambaci abinda ya danganci Mahmud toh sai tayi kuka koda kuwa gaisuwa ce shima Abbahn hakan datakeyi na damunsa shiyasa ma gara ya barta ta koma Abujan ko zata 'dan samu sassauci ta 'dan manta wasu abubuwa. Abbas kam haushin kukan nata yakeyi jiyake kamar ya maketa idan yaga tana share hawayen, dan haka sai yayi 'kasa da kansa yayi shiru yana sauraren yanda Abbahn ke bata baki. Yanzu kimanin kwana ashirin kenan da rasuwar Mahmud amma ace har yanzu yarinyar nan bata bar kuka ba yaushe kenan zata daina? Abbas ne yake wannan tunanin aransa. Abbah kam sallaman ta yayi yace taje ta shirya yanzu zasu wuche dashi. Tashi tayi salaf-salaf ta fita ahaka ta isa har gurin Anty, ita yanzu duk ba wannan bane matsalarta, ko ina ma tana so ta zauna dan zuwa yanzu tayi sabo sosai da Anty yanda bata jin koka'dan zataji da'din rabuwa da ita, sannan zata so zama a Abuja musamman ma tare da Hannah, saboda ita ma tana sonta kuma 'yar uwa ce ita mai damuwa da damuwar waninta, amma duk wannan bashi ze hanata son zama da Mummyn ba, gurin mummy take son zuwa, sai de ga dukkan alamu mummy ta sallamata ne, tun da akayi mata aure da Yah Mahmud Mummy take gudunta, gashi yanzu ma da mijinta ya rasu take bu'katan 'kirjin lallashi mummy ta tsallake ta tatafi ta barta. Anty kawai ganinta tayi tana kuka da sauri ta kamo hannun ta tana tambayarta me akayi mata me ya faru? Kuka tacigaba dayi da 'kyar tasamu ta bu'di baki tafa'di abinda Abbah ya sanar da ita. Anty bata hanata ba, kamar yanda bata nuna damuwa da hakan ba, da kanta ta lallasheta hartayi shiru sannan ta ha'da mata kayanta gaba 'daya da kanta, harma tace ko akwai abinda zata 'dauka acan gidan nasu, Teeemah da wuri tace " _a'a_ " dan ita koka'dan bata son gidan yanzu tsoro yake bata, bata son duk wani abu da zai dangantata da zuwa gidan ayanzu bazama ta iya zuwa ciki ba tanajin ita da wannan gidan har abada. Haka Anty ta gama shirya mata komai kuma tanayi tana bata baki tare da janta da hira, dan kawai taga Teemah tasaki ranta har tace mata bazata da'de ba zata je ta dubo ta dakanta har Abujan. Duk iya dauriyar da Anty taso tayi amma kasawa tayi musamman da suka yi musu rakiya zuwa inda zasu hau mota bayan ansaka kayan Teemah a boot taga Teemah nayi musu sallama tana share hawaye take itama sai hawayenta ya gangaro, dama ri'ke nata kukan taketa faman yi tun 'dazu dan kar ta 'dagawa Fateema hankali amma yanzu kam dataga ehh dagaske Fateemah zata tafi ta barta sai kawai takasa ri'kewa, tasan yanzu ne zatafi jin mutuwar Mahmud, idan Fateema ta barta shine zata san tayi rashi babbah domin ka'daici ne gadan-gadan ya tunkaro ta. Ga wani son yarinyar daya bi yacika mata zuciya jitake tamkar Khadija ma bata kaita son ta ba, sai gashi kuma Abbas na 'ko'karin rabasu, sai dai tasan bakomai yajawo hakan ba face banzan halinta, data kasance me son kanta fiye da komai, da ace ta kasance uwa tagari tasan da babu wanda ze yi shayin rayuwar waninsa tare da ita, kuma tana da tabbacin wannan dalilin ne yasa Abbas zuwa musamman dan ya koma da 'yar uwarsa Abuja. Kuka takeyi Teemah ma nayi haka suka rabu, Abbah kam daure ransa yayi yayi musu bankwana, rayuwa kenan, babu abinda baya faruwa idan kana raye zakaga abubuwa da dama najin da'di da rashinsa, duk akwai sai fatan Allah yasa mu dace [AM££N]. Tun a mota kukan da takeyi ya ishesa sosai kukan ke sosa ransa amma ya 'kyaleta ganin suna tare da driver in badan haka ba da shi ka'dai yasan abinda ze mata. Duk da haka sai da ya ringa sakin tsaki akai-akai kafin su isa kuwa yayi tsakin sau ba adadi har se data fahimci cewa da ita yakeyi tukunna. Suna sau'ka kuwa bayan wucewar drivern ya watsa mata kallo yace " _Idan kika kuskura kika min kuka acikin mutane ni da kene, angaya miki ke ka'dai akayiwa mutuwan ne_ ? Lokacin ma hawaye kawai take sharewa, daya kasa tsayuwa mata, ahaka ta 'daga idanun nata dake cike taf da hawayen ta kalleshi. " _Wipe all those tears kafin in sa6a miki, banson kukan nan ni_ " _Wannan addu'o'in naku na matu'kar sani annashuwa, tare da 'kara min kaimi wajen ganin na faranta muku kuma......._ *GODIYA SOSAI MASOYANA, ALLAH UBANGIJI YA BIYA MUKU BU'KATUN KU NA ALKHAIRI KUMA HASKAKA RAYUWARKU.* _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated 2 my family._ *Bismillahir rahmanir raheem* _God is the best listener and you don’t need to shout, nor cry out loud. B’coz he hears even the very silent prayer of a sincere heart..........._ 🅿 *69* Yanda yayi maganar atsare dole yasa ta goge hawayen nata ta ringa ajiyan zuciya kawai ahankali. Hotel 'din da ya kwana anan suka koma yace tajira shira shi yaje ya nema musu flight 'din zuwa Abuja sannan yadawo. Ummah na zaune a parlour tana kallon wani Hausa Movie kawai taji muryar Abbas nayi mata sallama kamar daga sama. A mamakance ta amsa sallamar tare da maida dukkan hankalinta gareshi. Fuskan nan atamke ya 'karaso ciki Ummah da mamaki take dubansa ganinsa ayau 'din bayan be da'de da tafiya ba, baya ga haka ma tasan yana da uzuri acan, mamakinta ne ya 'karu ganin Teemah ta shigo da sallamar ta itama kanta a'kasa ta 'karaso wajen Ummahn. " _Ah'ah, Teemah kune tafe_ ? _Keda waye haka_ ? Ummahn ta tambaya tana me waro idanu ko zata ga abokin tafiyan Teemahn tare da kamota ta zaunar da ita kusa da jikinta. Abbas kam 'dauke kai yayi tamkar be san da zancen ba dayaga hakan ma be masa ba sai kawai ya mi'ke ya wuce ciki. " _Keda waye kuka zo ne Teemah naga shiru har yanzu banga kowa ba_ ? Ummah ta sake tambayar Teemahn akaro na biyu. " _Ni da Yayah ne muka_ _zo_ ? Teemah ta bata amsa ahankali. Da wuri Ummah tace mata " _wani Yayahn kenan_ ? Sai tace " _Yayah Abbas_ " " _Abbas dai_ ? Ummah ta sake tambaya da mamaki. Kai Teemah ta 'daga mata alamar _ehhh_ . " _Toh garin yayah haka ta faru_ ? _a ina kuka ha'du_ ? _Ko ke kika ce masa zaki zo nan 'din, ina_ _ita Antyn_ _naki_ ? Shiru Teemah tayi dan bata san wanne daga cikin tambayoyin Ummahn zata fara amsawa ba. Ganin haka yasa Ummah kam ta fassara shirun da abinda hasashen ta ya bata. Kafin tayi magana sai ga akwati an shigo da shi wanda kallo 'daya tayi masa ta fahimci cewa na Teemah ne. Jinjina kai tayi tace " _lallai yaron nan wato sai da yaje ya taho dake ko,_ _ai dama tun ranar da_ _yaji labarin kina can_ _naga sai wani huhhura hanci_ _yakeyi yana kauda kai gefe ashe shirin da yayi aransa_ _daban_ . _Zai zo ai yasame ni neh sai naji dalilin_ _hakan_ " Kallonta ta dawo dashi kan Teemah tace " _maza shiga ciki ki watsa ruwa ki huta kinji Fateemah_ " Duk wannan dramar Teemah bata ga Hannah ba tun zuwanta Ummah ce tayi mata kwatancen inda 'dakin Hannah yake tace mata Hannahn na ciki. Koda taje 'dakin ma bata ganta a'dakin ba motsin ruwa data jiyo abayi ne yasa ta gane cewa tana bathroom, cigaba da tsayuwa tayi kamar me jiran abata umarni, bakomai take tunawa ba kuwa sai Mahmud tare da tausayin Anty dayayi matu'kar tasiri a zuciyarta. Tana tsayen har Hannah tafito daga bayin tagama firgita da ganinta dan bata ta6a zaton ganinta awannan lokacin ba, har kuwa tazo ta fahimci cewa itan ce dagaske ita Teemah bata ma san ta fito ba, sai da Hannah ta taho ta dafa kafa'dar ta tare da 'kiran sunanta kafin tayi firgigi ta dawo hankalinta. Ai kuwa tana ganin Hannah ta sanya kuka tare da rungumarta zuwa jikinta sannan tacigaba da kukanta. Hannah kam shiru tayi tama kasa magana dan mamakin zuwan Teemahn tare da farin cikin ganinta duk su suka cika mata zuciya ayanzun. Sai da taga kukan Teemahn bana 'kare bane kafin tafara bata ha'kuri tana bata baki da 'kyar ta sarara da kukan wanda hakanne yabawa Hannah damar tam bayarta tace " _ke dawa kika zo ne Teemah kinsan kuwa yanda naji haushin zamanki acan ai wallahi dama niyyata in je in zuga daddy ko kuma Yayah a'dauko ki haka kawai sai awani barki agurin muguwar matar nan, ni ai kin min dai-dai da kika taho wallahi_ , _Allah yasa bazaki sake_ _komawa ba_ " Cikin rawar murya Teemah tace " _Anty tana bani tausayi sosai_ _Hannah nasan zata shiga damuwa sosai dana barta_ " Fa'din Teemah tana me cigaba da zizaro hawayenta. Hannah kam kwafa tayi tana kallon Teemah sai daga baya tace " _ke wallahi wani lokaci rasa inda wayoki_ _yake tafiya nakeyi, ina ruwanki da ita? tausayinta na banza da wofi, ita ta_ _tausaya miki ne lokacin da take neman cin mutuncin ki duk da kina matsayin_ _matar 'danta kuma 'ya agurin mijinta? Sai yanzu ne data ga babu 'dan shine zata wani kalallame_ _ki dan ki zauna tare da ita tasamu hanyar_ _sake cutar da ke_ _cikin sau'ki ko_ ? Teemah cewa tayi " _Hannah ba haka bane fah, Allah Anty ta canja yanzun ba kamar da take ba_ " Hannah tace " _ni ya isheni haka da_ _Allah bari kiga nayi sallah lokaci na 'kurewa kema jeki yi alwala, ni yau_ _farin ciki ma_ _inajin baze_ _barni na samu bacci_ _ba_ " Agurin cin abinci suka ha'du dukkansu Abbas kam sai wani shan 'kamshi yakeyi kamar besan me ya aikata ba nan kuwa duk yana hakan ne dan kar Ummah ta samu daman yi masa fa'da akan maganar . Hannah ce " _tace Yayah bakaga Teemah bane_ ' _dazunnan fah tazo itama bata jima ba_ " Tunanin ta wai ko Teemah tariga shi isowa ne shiyasa ta fa'di haka dayake bata san lokacin daya zo ba. 'Dago kai yayi ya sauke shi akan Teemah yaga yanda ta ke kallon abincin tana wasa da spoon aciki sai ya maida kansa 'kasa asaman la66ansa yace da Hannah " _na ganta mana!_ " Ummah ce tace " _Hannah ai shi tun kafin ki ganta shi yariga yaganta_ " Hannah kam waro idanu tayi da mamaki tace " _haba dai, Ummah a ina toh suka ha'du tun 'dazu fah muna_ _'daki_ ? Atakaice Ummah tace mata " _shine dakansa ya_ _kawota_ " Hannah kam kallonta ta miyar kan Abbas 'din da fara'arta tace " _wallahi Yayah ka kyauta kamar kasan meke cikin raina, ni dama_ .... " " _Stop talking and eat your food Hannah later then kyayi surutun, okay_ " Cin abincin tafara cikin farin ciki tanayi tana murmushi dan ita yanzu komai normal ne a6angarenta bata da damuwar komai tunda kam ga Teemah agefenta zaune. Cikin hakan ta waiwaya 6angaren Teemah sai taga ba ta cin ma abincin ita kam. Zungurinta tayi da kafarta, data 'dago ta kalle ta sai ta mata nuni da abincin Teemah ma sai ta fara kaiwa kamar gaske. Ummah ma ta lura da hakan amma bata nuna ba dan zatonta ko idanun mutane ne yayi mata yawa shiyasa takasa ci, sai ta bari akan idan sun gama zatace da Hannah ta 'diba mata zuwa 'daki wata'kila can zatafi sakewa. Abbas kam da hanzari yake cin nashi abincin 'ko 'karinsa yayi ya tashi ya bar gurin dan yasan Ummah dole ne sai ta tuhume shi shikuwa be san ma me zece da ita ba. Ummah ma duk tana lura dashi sai ta 'kyaleshi kawai tana jiran su Hannah su tashi dan bata son yimasa surutu agaban 'kanwarshi sam shima kuma yasan hakan shiyasa yake hanzari yayi ya rigasu barin table 'din. Yagama kenan yana niyyan tashi sai yaga Hannah ta rigashi mi'kewa tana shirin yin magana sai Ummah tari bakinta da fa'din " _'Dauka wa Fateemah abincinta naga bata ci ba sam may be a'dakin zata fi sakin jiki taci_ " " _ah' ah nifa nama koshi Ummah basai_ _ta 'diba min_ _ba_ ! Cewar Teemah tana 'ko'karin mi'kewa itama. Wani kallo da Abbas ya watsa mata yasa take tayi kasa da 'kanta 'kirjinta na harbawa. Ummah cewa tayi " _ah'ah Fateemah ni banga wani abin kirki da kika ci_ _anan ba_ , " _Hannah maza 'diba mata ko ka'dan ma tasamu taci zama_ _da yunwa ai bashida da'di koka'dan_ , _dubi fah yanda duk kika 'kare abanza_ " Hannu Hannah tasa ta harha'da mata komai sannan tace da ita " _tashi muje_ " Shima mi'kewa yayi daniyar barin gurin sai kuma Ummah tace masa " _zauna Abbas_ " Dayake yana kusa da ita shiyasa shi ka'dai yaji maganar da Ummahn tayi. A'darare ya koma ya zauna yana me shafo kansa da hannunsa 'daya. Sai da su Hannah suka shige ciki kafin nan Ummah tace masa " _sannu ko_ " Kallon " _me nayi_ " ya yiwa Ummahn yana murmushi " _Haba Muhammad yazakayi haka dan Allah bayan da kai rannan mukayi_ _magana akan yarinyar nan, shine kuma ka san'di jiki ka koma ka taho da_ _ita_ ? " _Kai ko kunya ma bakaji ba, ka duba halin da matar nan take ciki amma sai_ _ka yi wannan rashin mutuncin, itace fah da kanta ta nemi_ _abar mata yarinyar nan_ _agurinta harta gama watannin takabarta kuma aka amince mata_ _sai daga baya kuma_ _haka yafaru kai kana ganin zata_ _ji da'di_ _ne_ ? Ta 'karashe maganar tana kallonsa. " _'kyale ta kawai Ummah yariga ya_ _wuce ai yanzu tunda gashi mun_ _taho_ " Ya bata amsa yana me duba agogon hannunsa. Shi koka'dan bega rashin kyautawar sa ba a wannan lamari dama me yasa za'a barta acan 'din in ba ahanata mantawa da mutuwar ba. Ummah kam kwafa tayi tana dubansa jin irin amsar daya bata sai tace masa " _Toh na barta tunda haka kace, amma shikuwa kawun nata fah, miye laifinsa acikin_ _lamarin ko kuma shi 'din kana ganin zaiji da'dine ace rana tsaka_ _kawai ka dira masa ka wani ce zaka tafi da ita bayan sun saki ransu cewa_ _zata zauna tare dasu, kuma ai baka ji ra'ayin yarinyar ba akan haka baka_ _sani ba ma ko can 'din yafi mata fiye_ _da nan_ ..." " _i don't care Ummah, shi 'din lokacin da_ _abubuwan sukayi ta faruwa yana ina?, da ace an samu_ _nasarar cutar da ita Ummah da ya za'ayi, nifah banga abin damuwa_ _anan ba dan tausayi ina jin tausayinsa mana amma gaskiya_ _bazan sake barin yarinyar nan ta zauna tare da muguwar matar nan ba, domin_ _amanar ta aka barmin, koma menene zatayi tayishi tagama anan babu inda_ _zataje_ " " _Muhammad_ !! Ummah tafa'da tana kallonsa. Juya kai yayi ya tare ta da fa'din " _bazaki gane bane Ummah, wallahi na_ _tsani matar nan, ki fahimce dan_ _Allah Ummah, wani lokaci fah jinake kamar inje_ _in sa akamamin ita nayi ta dukanta har se_ _ta suma......amma bazan iya ba, bazan mata haka ba_ _saboda darajar_ _Mahmud_ , _albarkacin 'dan data haifa take ci_ _awurina da kuma Abbah in badan_ _haka ba da ni ka'dai nasan me zan_ _mata.... kiyi ha'kuri Ummah amma gaskiya yarinyar nan bazata_ _koma ba koda kuwa me ze_ _faru_ " Ummah kam shiru tayi tana kallonsa yanda yasata agaba da masifa, amma bata wani yi mamaki ba dan tasan abinda ke cikin ransa yake fa'da mata and kuma tasan iya gaskiyarsa kenan dan haka tayi shiru tana sauraransa. Yana gama maganar ya tashi ya wuche zuwa 'dakinsa da ido kawai Ummah tarakashi har ya shige ta daina kallonsa sannan ta dawo da idanunta gabanta. Koda ya koma ciki ma tunani ne duk yabi ya ishe shi, sosai yake jin haushin Anty tare da Allah wadai da halinta, at d same time yana tausayawa Fateemah, cikin haka ya tuno da abinda yafaru 'dazu a wajen dinning, yasan halinta sarai tana dai-dai 'dinta ma bata bawa abinci daraja ba balle kuma ance tana cikin damuwa ai se ahankali. Shiyasa ma yaga duk ta rame ta lalace. Wayarsa ya 'dago ya 'kira layin Hannah. Hannah na 'ko'karin shiga wanka taji 'karar wayanta, zuwa tayi ta 'daga tare da yin sallama. Ciki-ciki ya amsa mata tare da fa'din " _Hannah me kikeyi_ _ne pls_ ? Sai da ta 'daga idanu sama ta kuma juya su kafin tace " _wanka zan_ _shiga Yayah_ "! yace " _Okay, akwai abinci_ _agurinku_ _ko_ ? " _Ehh sai na Teemah ne wanda bata ci ba_ " cewa yayi " _Yauwa ki bata ta_ _kawo min_ _yanzu_ " Hannah da mamaki tace " _Toh, amma Yayah baka ci abinci 'dazu_ _ba_ ? Be bata amsar tambayarta ba kawai sai yace da ita " _hope kinji me nace_ _ko_ ? Da sauri ta bashi amsa da fadin " _Umm naji_ " Be sake magana ba ya yanke 'kiran kawai. Bin wayar Hannah tayi da kallo sannan ta 'karaso wurin Teemah tace " _Yayah yace wai ki kai masa abinci inajin tsutsar ciki ke damunsa, 'dazun nan fah yaci abinci_ _amma kiji wai a'kara kai masa wani_ " Teemah tuni tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka tace " _Hannah ni kuma zankai masa dan Allah_ ? " _nima haka yace min ko baki ji ba sanda nace masa_ _wanka zanshiga, ki daure ki kai masa yanzu zaki dawo ai_ " Hannah tana maganar tana 'ko'karin 'dauko mata plate 'din abincin. " _ungo ki kai masa_ " Kar6a Teemah tayi ta kama hanyar fita. " _'Bangaren yamma zakiyi 'kofarsa ce ka'dai zaki fara gani agabanki_ " cewar

Chapter 38 of 67