!
Da jin haushi Hannah tace " _ai nima nice!!_
Shiru Teemah Teemah tayi na 'dan lokaci sannan bayan har Hannah ta cire rai da cewa zatayi nagana ma sai taji a hankali tace
" _Hannah laifi ne dan ina yawan tunanin Yayah?Inajin kewar sa sosai Hannah kuma gashi kinga baya ko 'kirana nima_ _kuma tsoron 'kiran sa nakeji dan bansan me zance da shi ba_ "
Hannah muguwa duk da haushin dataji 'dazu amma hakan be hana ta darawa ba dataji abinda Teemah tafa'da.
Teemah kam tsayawa tayi kallon ta idanun ta na tare hawaye dan bata san dalilin dariyar ba, HANNAH sosai ta dara son ranta ganin Teemah na zubo da hawaye ne yasa ta 'dan tsagai ta da dariyar tace " _ashe lokacin da sauri zai zo haka_ ? _Kin manta nace miki naki son idan kika fara sai kin fini amma kika 'ki yadda gashi nan tun ba'aje ko'ina ba abu ya bayyana kansa_ , _yanzu kam ai kin yadda cewa banyi 'karya ba ko_ ?
Teemah shiru tayi mata sai ma tafara 'ko'karin kwanciya dan taga alama abin dariya tazama harta regretting fa'da matan da tayi ji take badan ance magana zarar bunu bace da babu abinda sai hanata mai da maganar ta cikin ta ta rike damuwar ta ita ka'dai.
Hannah naganin ta kwanta sai ta ha'diye dariyar tata tace " _yi ha'kuri matar Yayah tashi muyi magana plz na daina dariyar_ "
Teemah 'kin kulata tayi sai Hannah ta dawo ta gabanta ta fuskanceta tare da fa'din " _I'm serious Allah tashi kiji, nayi al'kawarin bazan sake yimiki dariya ba yanzu"_
A hankali Teemah ta yun 'kura ta tashi ta zauna.
Hannah ma zamanta ta gyara da kyau sannan tace "Kin san Allah ko tun ranar da naga Yayah yayi 'kirana awaya nayi tunanin ko dai be same ki bane shiyasa amma daga baya sai naga ya zage da 'kirana ba gaira ba 'dan dalili sai na fahimci akwai dalilin hakan dan ba haka muka saba da shi ba, Yayah be fiya 'kiran layin na ba sai dai in akwai wani dalili, na fahimci bakwa waya ne kuma saboda ban ta6a ganin kunyi ba, nasan halin Yayah da zuciya akan abu koda kuwa yana son abin zai iya basarwa idan ransa ya 6aci wannan kadan ne cikin halayyar sa.
Ni kaina banso kika 'ki binsa ba tunda yanason hakan bazai ta6a cutar dake ba, wallahi Teemah Yayah na matu'kar son ki tun ba yau ba na fahimci hakan, ya na 'kaunar ki da dukkan zuciyar sa irin son da be ta6a yiwa wata 'ya mace irin sa ba a dunitan nan bama na tunanin ko agaba akwai wacce zata taro ki a zuciyar sa bansani ba ko in wani ikon Allahn ya sanya, Yayah na miki son da kowacce mace take burin mijin ta yayi mata irin wannan son, Teemah ki lura mana yanda kike yiwa Yayah abu son ranki wanda na tabbata ba ze 'dau hakan daga wurin kowa ba koda kuwa nice danake autar 'kanwar sa Yayah ba ze sarara min ba shiyasa ma kika ga bana farawa, sau tari ina mamakin yanda kuke rayuwar ku dashi kamar abokan gaba wani lokaci kuma na kanji kuna birge ni sosai, a hankali sai na fahimci 6oyayyan soyayyar dake tsakanin ku wanda bakowa ne yasan da shi ba, daga zuciyoyin ku sai de ko Mummy"!
Da sauri Teemah ta 'dan bu'de idon ta akan Hannah da Mamaki, sai Hannah ta jinjina kanta tace
" _Yes... Mummy ce ka'dai tasani, lokacin auren ku ta sanar dani yanda tayi farin ciki da ha'din auren_ _naku take ce min ta jima da fahimtar son Yayah Abbas dake 6oye a zuciyar_ _ki, wanda tana ganin kamar ke kanki ma baki san dashi ba, tace damuwar ta Abbas_ _ne bata sani ba ko zai kar6i auren ko ah h, nice nan take_ _na bata tabbacin Yayah baze 'ki ba danshi ma yana tsananin sonki_ _fiye da zaton mutun_ .
_Bazan 6oye miki ba Teemah duk da nasan kin fini sanin menene aure tunda kinyi shi har sau_ _biyu, amma har ga Allah kina sakaci da kulawa da mijin ki, lokuta da dama_ _nakan ji wani iri idan naga kina nuna halin ko in kula da shi, mijinki ne fah, naki ne_ _Teemah me yasa zaki 'ki binsa bayan kinsan yana da bu'katar hakan zaman me zakiyi_ _anan 'din tunda wanda kike zama domin sa baya nan, ba 'da ba ba komai_ _ba me yasa kika za6i raba muhalli dashi?_
_idan baki kila dashi yanzu ba yaushe kike son rayuwar auren ki tayi saiti_ ? _kin fi son sai ranar da wata ta shigo tsakanin ku ko kuma yaushe_ _Teemah_ ?
_Ki duba fah duk da ransa a 6ace amma bai fasa 'kirana dan yaji lafiyarki ba_ _ke da kanki ki duba wannan lamarin dan Allah_ "
A hankali Teemah tace
" _Ni kaina Hannah naga kuskure na kuma Allah yayah fushi yake yi dani ban san yanda zanyi ba banson fushin san_ _koka'dan_ "
Hannah cewa tayi
" _Nima banaso Teemah, dukkan ku 'yan uwa nane kuma mafi soyuwa abin 'kaunata, lokacin danaji auren ku bazan iya misalta miki_ _irin farin cikin dana shiga ba, inson ku sosai bazan ta6a son 'daya na bar 'daya ba har abada kamar yanda bazan so ganin ba'kin_ _cikin 'dayan ku ba ballan tana na dukkan ku biyu_ "
_Wannan laifin kinsan naki ne ko_ ?
Kai Teemah ta 'daga mata, sai ta cigaba da fa'din " _so kinga ke ya kamata ki gyara laifin, nasan Yayah ma be kyauta ba daya share ki amma kema da naki laifin me yasa da kika ga baya ko 'kiran_ ki _baki 'kira shi ba......._
_kinsan wani abu ne matar Yayah_ ?
Kai Teemah ta jijjiga wa Hannah alamar " _ah ah_ " sai Hannah tace
" _wannan taurin kan dake kan kin nan shine ya haifar miki da girman kai, zaman aure_ _da hakan kuwa baya ta6a yiwuwa, ki sau'kar da wannan shirmen ki nutsu ki gyara auren ki ki jawo mijin ki ajiki ki kula dashi da hakkin sa, sannan_ _ki dinga ro'ka muku haske wurin mahallici, Allah_ _Teemah banaso ko da wasa inga wata ta ra6i rayuwar ku, ke kanki kinsan hanyoyin kulawa_ _da mijin ki dan nasan Anty da Mummy suna_ ' _ko'kari sosai akan haka ni shaida ce......._
" _..........Harda maman Amal ma Hannah itama tana bani shawara sosai_ "
Teemah ta tare da fadin hakan.
Hannah jinjina kai tayi tace " _toh kin gani ma ashe suna da yawa masu sin ganin rayuwarki cikin farin cikin_ , _amma abinda ke kanki ne yah hana ki fahimtar cewa Abbas 'din nan_ _dai yanzu shine rayuwar ki kuma aljannar ki, dole_ _ne ki sauke naki dan biyu bata ha'duwa kinga kece 'karama akanshi, kafin yazama miji agare ki Yayan ki ne, kinga dole biyayya naki ne kuma ke ka'dai_ _banda shi, sai kin dage dan maza yanzu babu ruwan su tun kafin_ _yaje yayi miki kishiya awaje ba fata ba amma ki dage gaskiya"_
" _Hannah plz ni yanzu ya zanyi toh ki gaya min"_ Teemah ta fa'da tare da kamo hannun Hannah.
Agogo Hannah ta kalla tace " _yanzu dare yayi may be yana bacci, amma ki daure ki 'kira shi gobe, in kinyi sa'a zai sau'ko, sai kisan me zaki ce dashi wanda zai sanyaya_ _masa rai tunda ke ce da laifi sai ki bashi ha'kuri ki kuma kiyaye gaba"_
" _Bakomai insha Allahu gobe zan gwada 'kiran sa naji"_
Hannah tace
" _Toh Allah ya kaimu ya kuma daura ki akansa_ "
Da haka suka rufe maganar zuwa safiya.
Washe gari Hannah na da lectures a makaranta ita ka'dai tayi break fast 'din ta daya ke Teemah babu inda take zuwa so ba da wuri take yi ba ita, tare sukayi aiyukan da zasuyi dukka 'dakin Abbas ne ka'dai Hannah bata taya ta gyarawa ba ita ka'dai take yin abinta, 'karfe bakwai da rabi Hannah ta bar gidan dan 8:00 zata shiga lecture.
Teemah data gama komai tayi wanka tayi shirin ta tsab kamar me zuwa unguwa, sai ta dawo 'dakin sa tayi dialling number 'din sa, sai de har ta gama ringing bai 'daga ba, sake 'kira tayi shima still har yayi miss called be 'daga ba.
Take ta rintse idanun ta da 'karfi sai ga hawaye ya gangaro mata baya tayi ta kwanta, fuskarta na kallon cielling 'din 'dakin afili tace " _plz Yayah na ka yafemin, ka 'dauki wayata"!_
Abbas na bayi lokacin data 'kira 'din shiyasa be 'daga ba ko daya fito yaga miss called 'din kuwa sosai yayi mamaki amma sai ya ajiye wayar batare da ya 'kirata ba.
Shi kansa yana rayuwa ne amma kewar matar shi na damunsa sosai, tunanin ta na matu'kar hana shi sukuni da walwala yayin da soyayyar ta ya tsaye masa azuciya koda yaushe tana cikin ransa.
Abinda kullun yake fama da shi kenan tare da jin haushin rashin ta a kusa dashi, duk kuwa abin nan dayake yi mata yanayi ne dagangan duk da cewa shi kansa hakan na cutar dashi amma ya nuna mata cewa bai ji da'din 'kin biyo shin data yi ba yasa ya daure ransa, dan yana tunanin idan hakan ya ishe ta next idan yace su taho bazata masa gardama ba koda Daddy ya nuna bai so, dan yasan ita bata fiye 6oye 'kudurin ta ba.
Teemah bata tashi a kwancen ba sai ta sake gwada 'kiran sa da niyyan daga wannan bazata sake ba in har be 'daga ba.
Cikin sa'a kuwa sai ya 'daga Teemah har sai data toshe bakin ta dan farin cikin data tsinci kanta aciki.
Abbas shiru yayi yanajin yanda ta sauke ajiyan zuciya, shima sai ya lumshe ido ya kuma bu'dewa atake.
Teemah a hankali tace " _Yayah_ !
" _Na'am_ " shima ya amsa ta da shi kamar wanda akayi masa dole.
Kuka kawai Teemah ta sanya mai me tsuma zuciyan ma'abocin sauraro.
Cikin kukan ta furta " _Yayah shine ka manta dani ka daina 'ki rana ko_ ?
Yace
" _Ni ban manta dake ba abubuwa ne sukayi min yawa ma shiyasa_ "
Da sauri tace " _Amma Yayah ai kana 'kiran Hannah nice ka'dai baka 'kirana_ !"
Dan ya takaita zancen sai yace
" _Shikenan toh zan na kiranki... owk_ ?
Shiru tayi masa tana share hawaye.
Da yar ka'dan 'din muryar tace " _Yayah fushi kake yi dani ko?_
Sosai yanayin data yi maganar ya ratsa shi har 'kwa'kwalwar shi amma ya basar.
Sai ma yace " _i ll hang d call now office zan je.....see u later ummm_ "
Bata yi magana ba har ya yanke 'kiran sai kawai tabi wayar da kallo da mamaki, lalle ta 6ata ran Yayah sosai acikin muryar sa ta fahimci hakan dan duk wasu abubuwan shi dayake yi abaya bata ta6a jin muryar sa a irin wannan yanayin ba, sai dai abinda takasa ganewa shine haka 'din da yake yi soyayyar da Hannah tace yana yi mata ne yasa ko kuma haushin kawai ta'ki binsa?
Share hawayen ta tayi tare da tabbatar wa kanta cewa zata bishi aduk yanda yake so 'din harta gano asalin matsayin ta awurin sa.
Abbas ma daya yanke 'kiran sai daya jinginu da jikin kujera ya lumshe idanu baya son irin wannan na faruwa tsakanin su koka'dan amma tunda hakan take so, so be it!, shi zai daure rashin ta na tsawon lokaci ko dan ya koya mata yanda ake kewar masoyi da yanda tasirin soyayya yake a zu'kata.
Tun daga ranar Abbas yafara 'kiran ta safe da kuma dare, amma kullum daga gaisuwa baya sake fa'da mata komai, duk da hakan Teemah najin da'di domin yafi ace baya 'kiran gaba 'daya, sau tari har 'kaguwa takeyi ya 'kirata dan kawai taji muryar sa ita hakan ma ya isheta.
Baya yi mata magana mai tsayi sai in har bu'katan hakan ya taso, farkon dogon maganar su shine ranar da ya ta6a tambayar ta cewa bai ga debit alert ko sau 'daya har yanzu ko bata da bu'katan komai ne?
Sai tace masa Hannah na zuwa musu shopping every week.
Ya sake tambayar ta cewa ku'din fa sai ta bashi amsa da fa'din " _Ummah ce ke bada ku'din idan Hannah zata_ "
Shine ranar da maganar tsakanin su tayi tsayi, na biyun sa kuma ranar da Hannah zata je saloon kuma itama Teemah tanaso tayi dan kanta cunkus take jinsa.
'Kiran safiya da yayi mata sai ta tambaye shi zuwa saloon 'din, ai kuwa hana ta Abbas yayi sai ma yace in har yazama dolene sai tayi 'din toh Hannah taje ta siyo komai zai turo ayi mata agida, Teemah sosai taji haushi dan kuwa ba 'karamin gajiya tayi da zaman gidan ba.
Sosai take so ta'dan fita amma Yayah fir ya hana ta.
Hakan kuwa akayi dan da yamman ranar wata mata tazo gidan Teemah bata san ta ba, Hannah ce dai ta gane ta dan ta ta6a zuwa gyaran gashi wurinta sau 'daya, sunan ta madam Mansoora, agida tayi musu komai harda Hannah ma, hatta da gyaran farce sai da tayi musu mai kyau ta kuwa yi 'ko'kari dan su kansu sai da suka yaba da aikin nata.
Sai daga bayane ma da Hannah taje gida n Ummah sai suka ji labarin ashe Ummah yasa ta turo ta.
Duk abin nan dake faruwa bai sa Teemah taji haushin sa ba sai ma 'kara ganin shi data ke sonyi ga begen sa dake yawan damun ta.
Ita kanta wani lokaci mamakin kanta takeyi, yanda ta damu sosai da rashin sa kusa da ita yanzun bata san dalilin wannan canjin ba, sosai take kewar mijin ta a yanzun sai dai bata bari ko Hannah tasan hakan ba saboda Anty tace mata komai dake tsakanin ta da mijin ta sirrine mai girma, kar ta yarda ta ringa bari wani na sani, shiyasa ta ri'ke sirrin ta aranta.
Kullum take shiga 'dakin sa ta share koda babu dattin komai amma bata gajiya da share shi, ta tsaftace bayi kullum ta kunna burner, anan take wuni da rana har in bacci yakama tayi abinta da dare kuwa tare da Hannah suke kwana a'dakin ta, idan gari ya waye suka kammala ayyukan su gaba 'daya sai Hannah ta shirya ta wuce makaranta.
Teemah kuwa nan 'dakin san take komawa tayi baccin ta kwanta tana kallon photon sa tare da rungumar pillow a 'kirjin ta.
Tana fitowa sai ta kulle 'dakin ta kai key 'din cikin drawer 'dakin ta ta ajiye shi.
Duk weekend Hannah ke zuwa shopping idan ta dawo kuma sai ta gudu gidan Ummah ta 'karasa yinin both saturday & sunday acan haka takeyi, amma bata kwana sai ta dawo, hakan ma Ummah bata barin taringa mitan ta baro Fateemah agida ita ka'dai.
In kuwa zata dawo Ummah sai ta ha 'data da wani abin ta6awa na zamani ko na gargajiya tace ta kawo wa Teemah.
Su hajiya Teemah kam najin da'din hakan har sai ya zamana ma duk ranar da Hannah taje gida bata cin komai jiran ta kawai takeyi ta dawo sannan taci abinda Ummah ta ha'do ta dashi, tasan Ummah na 'ko'kari sosai dan kamar tasan abinda ranta ke 'dan iya bi takan rin'ka yiwa Hannah santi musamman ranar da aka kawo mata pepper soup 'din hanta ko dambu mai ha'din isassun kayan lambu, ranar kam har rowa take yiwa Hannah ma.
Haka rayuwar ta ya kasance agidan auren ta batare da mijin ta agida ba, satinsa uku yanzu da tafiya, zuwa wannan lokacin kuwa har ma Teemah ta riga ta saba da rashin san azahiri amma sai dai damuwar datake ji aranta koka'dan be ragu ba sai ma abinda ya 'karu musamman data ga cewa dagaske yakeyi bazai dawo Abuja dawuri ba, sau tari idan ya 'kirata takanji kamar tayi masa mitan hakan amma sai ta danne ranta dan tafi son idan suna tare burinta ma be wuci tasan matsayin ta ba, amma a yanda tasan halin sa ma tasan idan yaga dama baze ma tsaya ya saurare ta da kyau ba dan shi bai fiya son jan magana ba.
Dramar su da Hannah kuwa sai ma abinda yayi gaba musamman da har yanzu Hannahn bata fasa 'kiran ta da suna mrs dodo ba, yanzu kuwa sunan na 6ata ranta, sosai yake jin haushi idan Hannah ta 'kirashi da dodo.
Ranar da Hannah ta ishe ta kuwa ce mata tayi " _kar ta 'kara 'kira mata miji da suna dodo, tace ita mijin ta ba dodo bane koma miye ne ita a hakan yafi birgeta_ "
Hannah ido ta zaro da zolaya tasake fa'din " _iyeeh, kice abin yafi najiya bansani ba, yi ha'kuri toh matar Yayah bazan sake ba"_
Teemah a tsare tace da Hannah
" _Daya fi miki_
_in bahaka ba kuwa in tona miki asiri awurin Ummah ince kina da 6oyayyan saurayi bata sani_ _ba_ "
Cikin ko in kula Hannah tace
" _Toh miye aciki ban kai nayi saurayin bane?_
" _kin kai harma kinfi, karki damu yarinya zaki gani zan baki mamaki ai_ "!
Da sauri Hannah ta dakatar da itada fa'din
" _Ah'Ah baiwar Allah abin be kai haka ba, wasa fah nake yi miki, indai mijinki ne ai nace na bar zancen sa ko, da Allah rufe wannan_ _chapter 'din bana so Yayah yasan ina da wani saurayi dan da kaina nace masa makaranta zanyi kinga kuwa ai_ _idan yasani na 6allo ruwa_ "
Teemah cewa tayi
" _Sai ki kiyaye bakin ki in kina so nima na rufa miki asiri_ "
Hannah ma da sauri tace
" _Kwantar da hankalin ki matar Yayah wannan shi yafi komai sau'ki_ "
" _Dayafi miki_ "
Fa'din Teemah daga 'karshe.
Murmushi kawai Hannah tayi tace
" _ni kaina ya kulle fah Allah, wai yaushe yafara yi miki ne_ ?
Atakaice Teemah tace
" _Jiya da safe_ !
Hannah ma sai tace
" _Ai kuwa ba mamaki gaskiya, amma fah kin ban tausayi wallahi, abin yakama ki da 'karfi sosai_ ?
Ringing 'din da wayar ta ta 'dauka ne ya katse musu hiran, Hannah kam naganin me 'kiran sai tayi murmushi tare da 'dagawa.
*****
Tun ranar da Abbas ya cika sati hu'du da tafiya be 'kiran ta ba tun daga ranan, itama kuwa bata damu ba dan halin san yanzun tafara sabawa dashi, itama batayi tunanin 'kiran sa ba kamar yadda bata sanar da Hannah meke faruwa ba, wasa-wasa har suka kwana biyu amma shiru ba labarin sa, ranan na ukun ne abin yafara damun ta sosai, tanaso ta 'kira shi taji me ya faru amma sai zuciyar ta ta rabu kashi biyu, inda 'daya ke bata 'karfin gwiwan ta'kira shi yayin da 'dayan ke bata shawaran ta 'kyale shi itama, kamar yanda yayi 'din wata'kila tana damun sa ne shiyasa.
Wannan 6angaren tunanin ne yayu tasiri azuciyar ta har ma sai ya rinjaye ta gaba 'daya.
Bata 'kira shin ba amma kuma sam nutsuwa ya'ki zuwa mata, haka ta wuni wata iri da ita, hatta wayar ma yau ko bi ta kanta batayi ba tsaban yanda tunani ya yawaita a brain 'din ta, 'dakin nasa ma yau ko bu'de shi batayi ba acikin nata 'dakin ta wuni.
*1:13pm*
Ta tashi tafara rage kayan jikin ta a hankali dan so takeyi ta watsa ruwa ko zata 'dan ji dai-dai, ga mararta ma dake 'dan mur'da mata ka'dan-ka'dan wannan karan period 'din ta yayi mata jinkirin kwanaki dan kuwa wata har yawuce da kwanaki amma bai zo ba, jin mur'dawan da yake yi mata sama-sama ne yasa ta saka ran zuwan sa daga yanzun zuwa kowani lokaci, ga tsoron ciwon maran dayake tasan baya yi mata da wasa, sosai yake damun ta.
Tana tsayen sai taji 'karan door bell tasan Hannah ce dan haka sai ta 'daura hijab kawai akan skirt 'din dake jikinta, dayake tariga ta cire riga sai bra ne ka'dai yarage asaman ta shiyasa ma tasa hijabin, a haka ta nufi 'kofan ta bu'de batare da tunanin komai ba dan tasan bayaga Hannah bata tsammanin kowa.
Turus tayi ha'di da wani bugu da zuciyan ta yayi har sai da yasata 'dauke wuta na 'yan seconds kafin ta dawo dai-dai, kallon-kallo suka tsaya yiwa juna na 'dan lokaci kowa na ayyana irin yanda yaga 'dan uwansa ya canja, kowa ji yayi aransa babu da'di ganin duk da irin 'kuncin da zu'katansu ke ciki amma be hana 'dan uwansa yin wani sihirtaccen kyau da 'kiba azahiri ba.
Teemah kam harda mamakin ganin sa ma duk suka cikata.
Abbas ne yayi gyaran murya sannan Teemah ta bashi hanya ya shigo, bata sake kallon shi ba ta tura 'kofan ta rufe sannan ta dawo ciki itama, haka tawani 'dauke kanta gefe tana tafiya tace dashi " _sannu da_ _zuwa_ "
bata ko jira taji ya amsa ba balle tayi tunanin kar6an jakan sa talkless of welcoming nasa da abin sha ko kuma wani abu daban ba ta wuce ciki abinta.
Abbas ma be amsa ba sai ya bita da idanu kawai, tana shigewa 'dakin ta sai ya jijjiga kansa tare da nufan hanyar nasa 'dakin, amma sai ya jita akulle, beyi mamaki ba dan haka sai ya koma nata 'dakin har yanzu da jakarsa akan kafa'dan sa.
Ga mamakin sa kuwa yana shigowa tana fa'dawa bathroom ga dukkan alamu wanka zatayi.
Jakar tasa ya sau'ke ya ajiye sannan ya zauna abakin gadon nata, he wish yasan inda ta ajiye keys 'din da bazai tsaya jiranta ba 'daukan abinsa zai yi ya.
Zaman sa keda wuya sai kuma yakoma ya kwanta rigingine akan gadon yayiwa kansa matashi da hannayen sa biyu dake bu'de kuma sarke da juna, 'kafar sa 'daya na lan'kwashe akan 'dayar yayin da 'dayan 'kafar ke tsaye yana faman jijjiga su.
Teemah tana bayi tayi zaman ta sarai tasan yana cikin 'dakin nata amma haushin irin wannan zuwan dayayi matan yasa ta share shi duk kuwa da tasan cewa 'dakin sa a kulle amma hakan be sa tayi tunanin tayi hanzarin fitowa ba.
11mins ya 'dauke ta a bayin kafin ta fito d'aure da towel ajikinta, koda ta fito 'din ma idanun ta kansa suka fara sau'ka amma sai ta 'dauke kanta tamkar bata ganshi ba, shirin ta ta hau yi a tsanake tayi light make up tare da zura wata doguwar riga da hijabin sallahn ta. Sam Teemah 'dauke hankalin ta tayi daga kansa tamkar bata san cewa akwai wani abu mai rai dangin halittar mutun acikin 'dakin ba.
Dadduma ta 'dauko ta shimfida ta tada sallah abinta.
Duk abin nan dake faruwa Abbas na kallon ta shima be tanka ta ba, iya gudun ruwan ta yake so yagani, ganin ta fara sallah batare da ta ko kalli inda yake ba yasa yatashi a hankali ya zauna yana kallon bayan ta dayake yana daga bayan ta ne, kamar an tsikare shi kuma sai ya mi'ke, daukan jakarsa yayi ya juya yafice agidan ma gaba 'daya.
Sai da ya tsaya a masallaci ya sallaci azuhur kafin 'dan adaidaita ya sau'ke shi a 'kofar gidan mahaifinsa.
Teemah koda tayi sallamah bata juyo da wuri ba sai data 'dan 'dauki lokaci tana ro'kon ubangijin ta bu'katun dake gabanta sannan ta shafa ta tashi, taji motsin fitar shi tana sallahn amma batayi zaton gidan yabari ba, tayi zaton ko parlour ya koma ne.
Tana na'de daddumar taji aranta cewa bata kyau ta ba dan haka bata 6ata lokaci ba tafito parlourn sai kuma taga empty babu kowa, da mamaki tajuya zuwa 'dakinsa nan ma adatse yake tun rufewar ta na safe, 'dakunan gidan duk tabi ta dudduba amma bayanan arikice ta dawo 'dakin ta da tunanin inda ya shiga.
Wayar ta ta 'dauka ta ta 'kiran layin sa amma baya 'dagawa.
Take taji komai ya tsaya mata cak.
Abbas kam ga mamakinsa gani yayi kowa dake gidan su na farin ciki da zuwan sa tun daga kan ma'aikatan gidan har mahaifiyar sa gaba 'daya, sa6anin ita waccen yarinyar da ko kallon arzi'ki ma bai samu daga wurinta ba.
" _Toh me ya faru ne_ ? _Me ke damunta?_ ya tambayi kansa.
Wani 6arin zuciyarsa ne yabashi amsa da fa'din " _babu komai iskancin ta ne kawai yau 'din ya motsa mata_ ".
Firgigi yayi lokacin daya tsinkayi muryar Ummah ya daki dodon kunnan sa da 'dan 'karfi, ga dukkan alamu ba farkon maganar ta kenan ba " _Muhammad meke faruwa ne wai_ ?
Yaji ta fa'da da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 52 Chapter of 67