ma dukkansu mazan dayake lokacin damina ne sai yace suyi aikin gona dashi.
Hakan dayayin ba 'karamin farin ciki ya sanya azu'katansu ba, nan kam be kwana ba aranar suka wuche kuma ko tsaraba 'kin kar6a yayi yace bagida suka yi ba tukunna kuma kayan zai zama musu damuwa ne tunda motar haya suke hawa.
'Karfe hu'du na yamma suka baro 'kauyen suka dawo kano.
Da 'kyar suka sami flight 'din da zai sau'ka a Lagos da daren ranar, dan haka suka je suka gabatar da salllolinsu kafin nan.
'Karfe 11pm suka sau'ka acikin garin Lagos ganin dare yariga yayi yasa suka wuche gidan Mahmud suka kwana acan sai washe gari da safe suka shirya suka fita atare inda Mahmud ke jan motar Umar na gefensa.
Dayake ma already Teemah tasan da dawowar shin so tun dawuri tagama ha'da kayanta suna zuwa bawani 6ata lokaci tabi mijinta suka wuche gidansu amma zuciyarta cike da kewan matar Umar da 'yaranta musamman ma little Amal.
Aranar Mahmud beje shi ko'ina ba acikin gidansa ya wuni dayake ma ranar takama ranar asabar ce shiyasa ma be fitan ba, sai da akayi sallar azahar kafin yafita yaje masallaci yayi sallah daga nan yawuche gidan mahaifinsa.
*****
Washegari kuwa tunda sassafe suka tattaro inner wears 'dinsu gaba 'daya wa'danda basu sawa a loundry machine suka wanke atare, Teemah natayi masa dariya wai be iya wanki ba, itanma bawani iyawa tayi ba amma yanda taga Mahmud 'din keyi sai yana bata dariya shiyasa take ganin kamar tafishi iyawa.
Kasuwa suka shirya suka tafi bayan sungama wankin, sukayo siyayya ni'ki-ni'ki tarkacen kayan abinci.
Dangin su stock fish, ice fish, naman kaza dana 'karamar dabba, cry fish, ganyen su oghou, tarkacen fruits da sauransu kaya de dayawa suka siyo.
Atare suka shiga kitchen suka adana komai a inda yadace nasawa a fridge suka saka na , ajiyewa haka duk suka adana abinsu.
Fruits salad Teemah ta ha'da musu mai da'di suka sha aranar wanda shi ka'dai dasuka sha basu 'kara neman abinci ba har sukayi bacci.
Washe gari tunkan yagama shirinsa Teemah ta shirya ta yi zaman jiransa yagama nasa shirin, suna gama yin breakfast yatashi da niyyar tafiya anan Teemah ma ta ce itafa bazata iya zama agidan ba gaskiya tsoro takeji sai de sutafi tare, bayason ta 6ata masa lokaci dan haka yace toh sutafi .
Gidan Umar yakaita daga nan yawuche wurin aikinsa.
Matar Umar ta'danyi mamakin zuwan Teemahn amma bata tambayeta dalili ba haka suka wuni abinsu dan yanzu kam Teemah tariga da tasaba dasu sosai.
Da yamma Mahmud yabiya ya 'dauko ta suka dawo gida.
Mahmud kansa yanzu yana mamaki yanda yake samun damar yin baccinsa cikin natsuwa da kwanciyar hankali tun bayan da ya fara amfani da magungunan da aka ha'da mai, yanzu kam Alhamdulillah, dan ko jiya da Teemah ta tashi cikin dare ma dakansa ya farka dayaji motsinta, gashi yauma har ya kwanta suna hira da Fateemahn sa6anin da da yana 'dora jikinsa akan gadon zaiji wani bacci me shegen nauyi harma baya sanin lokacin da baccin yake 'daukansa.
Labarin duk abinda yafaru wajen tafiyar sa yake bata, na yanda yaga wannan matar da 'yarta dama duk abinda yafaru agidan yace tausayin matar da yaranta yakasa barin zuciyarsa, duk lokacin dayasamu chance zai koma yasake duba su, Teemah najin haka tace itama zata bishi tana so tagansu itama.
Be musa taba ya amince, dan yasan ko yace baza bishi bama ba yadda zatayi ta zauna agidan ita ka'dai ba dan haka gara yatafi da abinsa yafi masa.
haka suka ci rabin satin yana fama da ita, sam ta'ki zama agida kuma ya kaita gurin Anty ta'ki, sai de ko su tafi office 'din tare ko kuma ya kaita gidan Umar.
Sosai abin yafara isansa yarasa takamamman dalilin dayake sata wannan abin while ada da bata saba bama bata yi masa haka, ya tambayeta kuma sai de tace bakomai kawai tana tsoro ne.
Toh tsoron na menene sam yarasa.
Anty Chiddy kuwa zuwa yanzun hankalinta sam ya daina kwanciya da rashin samun Fateemah, domin tagama saka rai da samun yarinyar sai gashi kuma bata samunta agida, kullum bata nan tarasa ina take zuwa, gaba 'daya ta 'dora ranta akan yarinyar har hakan yasa ta sallami yaran datake hul'da dasu ganin tasamu sabuwa.
Tayiwa Anty maganar ma kuma duk abanza dan da kunnanta taji ranar da Mahmud yake fa'din wai ai islamiya take zuwa shiyasa bata zama agida.
Da yamma kuma ai Mahmud nagida babu damar taje.
Daga baya sai tayi wani tunani wanda take ganin shine dai-dai, ta yanke shawarar kawai gara tasa ayi mata kidnapping yarinyar taje ta 6oyeta sai ta gama abinda zatayi da ita sannan tadawo musu da ita gida.
Wannan shawaran ita ka'dai tayishi azuciyarta ko Anty bata sanar mawa ba, domin dama kawai tana yaudarar Anty ne akan zata kaita inda za'a warware auren bawai dan tana da tabbacin hakan ba, dafarko taso ta samu kan Anty ne sai kuma ta'ki amincewa da ita suna cikin haka kuma saita yi arba da amaryar Mahmud yarinyar sai ta gama tafiya da imaninta taji kaf duniyan nan ita ka'dai take da burin kasancewa da ita shiyasa plan 'din yadawo kan Teemahn madadin Anty, sai gashi kuma itama Teema tana neman fin 'karfinta ita kuwa bazata iya ha'kura da ita ba sam.
*****
Haka yauma Mahmud suka fito daga gida shida Fateemah ya sau'keta agidan Umar yatafi wurin aikinsa.
Abin nabawa matar Umar mamaki na yanda Teemah take 'kin zama agidan mijinta ta gwammaci zama agidan mutane domin tariga tasani Teemah bata son zama agida, matu'kar bata gidanta toh Mahmud yawuche office da ita, dan haka yau ta yi 'damar sanin dalilin hakan bawai dan ta gaji da zama da ita ba, sai dan kawai ta gyara mata kuskurenta domin tasan Mahmud bazai ta6a jin da'din hakan ba sai de yabiye mata kawai saboda jin da'di da farin cikinta, sam babu namijin da za'a ce matarsa bata son zama agidanta kuma yayi farin ciki da haka.
Koka'dan bata ta6a canjawa Teemahn fuska ba aduk zuwan datakeyi saima ta'kara jawo ta ajiki tare da bayyana mata wasu sabbin abubuwan da suka shafi zamantakewar aure, wanda zuwa wannan lokacin sosai Teemah tayi nisa da sanin menene shi auren kansa takuma gane irin zaman da sukeyi da Mahmud 'din daban yake da kowa.
Gata da jarabar son yara musamman ma yarinyar Umar 'yar karamar da bata wuce 1yr da haihuwa ba ( Amal), kullun idan tazo yarinyar najikinta, ita take mata kitso kullun
watarana jitake yi kamar tatafi da ita gidansu.
Matar Umar nayi mata dariya amafi yawancin lokuta idan taga tana 'ko'karin goya yarinyar amma kamar wata me wasan yara sam bata iya ba.
Takance da ita
" _zanga ranar da zaki goya naki' dan ai Fateemah gaskiya zansha dariya in 'koshi_ "
Sai Fateemah cikin za'kuwa tace mata " _da gaske nima maman Amal zan haihu na sami 'dana da 'yata watarana_ ?
" _Zaki haihu mana lokacine ai, in Allah ya yarda kamar yau_ _ne_ "
Fateemah na matu'kar jin da'di idan taji ance zata haihun nan har ta 'kagu taganta da babyn ta itama.
Matar tana so tayiwa Teemah magana amma kwata kwata tarasa ta ina ma yakamata tafara dan tasan ko ayaya tayi maganar zai iya bada cewa tagaji ne da zuwan Teemah gidanta itakuwa bahaka bane manufar ta burinta Fateemah ta kasance mace ta gari abin alfahari agidan aurenta.
Duk wani motsinta tanayi ne da tunanin yanda zata fara tunkarar Teemah batare data jahilci niyyarta da manufarta ba.
Bayan sunyi sallar azahar sunci abincine da suka gama matar Umar take ce da Fateemah " _yanzu idan Mahmud yadawo gurin aiki_ _me zaici_ "
" _bakomai_ "
Fateemah tabata amsar tambayarta atakaice.
Sai tasake fa'din
" _kode shima irin kinne duka bakusan cin abinci hala_ "
" _Ah'ah maman Amal muna ci mana harma shi yafini!_
" _Toh meyasa bazakiyi zauna agida kiyi masa girki ba"_
Fateema Sai cewa tayi
" _shima yasani bana gida ne da ina nan zanyi masa ai_ "
" _Me yasa toh bazaki zauna agida kiyi masa ba, Fateema kinsan kuwa 'dimbin ladan da_ _mace ke samu idan tayiwa mijinta hidima yaji da'di?" inji matar Umar_ .
Narai-narai Fateemah tayi da idanu tace " _Allah ni Maman Amal tsoron zama agidan nakeyi ni ka'dai shiyasa_ "
" _daurewa zakiyi kinji ahaka sai kiga kinsaba, amma idan kika ce bazaki na zama ba toh yaushe_ _zaki saba Fateemah_ "
Shiru Fateemah tayi tana tunanin taya za'ayi ta zauna agida bayan Anty da 'kawarta so suke su maida ita 'yar ma'digo tace gara tayi ta yawo agurare data zauna agida su tarar da ita har zuwa ranar da daddynta zaizo sai su tafi abinsu yafi mata.
Ji datayi matar Umar nasake lalla6a ta akan taringa zama agida yasa ta fayyace mata duk abinda ke faruwa, wanda ya matu'kar 'dagawa matar Umar hankali fiye da zaton mutun , abin ya kulle mata kai dataji cewar mother in-law 'din ta ce ke jagorantar abin, wannan wani irin al'amari ne haka.
Fateemah dataga hankalinta yatashi tana ta maganganu sai tace mata tayi shiru dan Allah kar kowa yaji tasake tunatar da ita cewar Anty tace kashe ta zatayi idan tafa'di maganar wa wani tace dan Allah karta fa'dawa kowa.
Jinta kawai matar Umar tayi domin bazata iya yin shiru akan maganar ba sam dole ne Mahmud yaji domin ya 'dau matakin daya dace tunda kam mahaifiyarsa ce, ze iya dakatar da ita.
Koda Mahmud yazo 'daukan Fateemah kuwa cikin sa'a sai be shigo ba horn kawai ya danna mata daga waje dayake tunkan ya 'karaso yake 'kiranta ya sanar da ita.
Fita tayi ta sameshi suka tafi.
Matar Umar kuwa yanda maganar ya tsaye mata arai yasa takasa ri'keshi har sai da ta sanar da Umar komai.
Umar kansa yayi mamaki, ya de san Anty bata son auren Mahmud da Fateemah amma be ta6a zaton 'kiyayyar Anty har yakai haka ba, domin be ta6a zaton Anty zata nemi lalata rayuwar yarinya 'karama irin Fateema ba.
Umar har gani yayi dare yayi masa tsayi dan kawai yanda ya 'kagu gari ya waye ya ha'du da Mahmud.
Mahmud kuwa tunda ya 'dauko Teemah sai yaga kamar ba'a daidai take ba haka dai ya 'kyaleta yana karantar duk yanayinta, har kusan 'karfe 8 na dare bata dawo daidai ba, tana kwance akan 2 seater yayinda shi kuma yake zaune daga gefenta ta 'dora kanta akan 'kafarsa tayi shiru, sai alokacin ya tambayeta meke damunta.
Shiru tayi masa kamar bata ji abinda yace da ita ba, sai ma tayi yun'kuri ta tashi ta wuche bedroom, bayanta yabi da kallo har ta shige ciki, jijjiga kansa yayi tare da dawo da hankalinsa kan labaran da yake kalla.
Minti shabiyar be 'kara ba yatashi yabi bayanta bayan yakashe dukkan swich 'din, domin gaba 'daya daina fahimtar labaran yayi zuwa wannan lokacin hankalinsa gaba 'daya ya tashi da ganin Fateemahn ahaka, ya tabbata akwai abinda ke damunta.
Koda ya shiga 'dakin akwance yasameta dan haka sai ya wuce bathroom tsawon mintina biyar kafin ya fito yadawo kusa da ita ya zauna wanda tana ganin hakan tawani lumshe idanu kamar me bacci.
Duk ya kula da hakan dan haka sai yayi murmushi kawai tare da 'kiran sunanta ahankali, sai da ya 'kira ta kusan sau uku kafin ta amsa kamar me yin baccin gaskiya.
" _Tashi maza ki zauna tambayarki_ _zanyi_ "
In a serious tune yayi maganar dan haka dolenta tami'ke zaune badan ranta naso ba.
" _meke damunki ne wai yau 'dinnan please Fateemah banason ganinki a_ _irin wannan yanayin koka'dan, gaya min_ _kinji_ "
ahankali tace
" _bakomai fah yayah ni babu abinda ke damuna_ "
" _me 'karya_ "
ya fa'da da sigar zolaya.
murmushi kawai Teemah tayi masa .
" _Haba akwai mana, nasani akwai abinda ke damunki_ ........"
Yana fa'da yana murmushin shima.
" _Allah yayah babu komai_ "!
Fateema ta tareshi da fa'din haka.
Shiru yayi ya zuba mata idanu ita kuwa sai tayi 'kasa da idanunta tana wasa da yatsunta.
Mahmud kwata-kwata kansa ya kulle ma yarasa ya zaiyi da ita.
Hannunsa ya mi'ka yakamo nata hannun datake wasa da shi 'din yace mata
" _me kike so toh gaya min kinji, i promise ko menene zanbaki shi_ "
Jikinsa ta dawo ta kwantar da kanta akan kafa'darsa tayi shiru tana tunanin _toh me ma zatace dashi_ ?
Ganin tayi shirun ne yasa Mahmud yasake ce mata
" _gaya min mana Fateemah karkiji tsoro kinji_ "
Murmushi tayi data tuno hirarsu da matar Umar 'dazun sai ta 'daga kanta ta kai bakinta kusa da kunnansa ahankali tace " _Yayah kasan me nake so_ ?
Jijjiga kansa yayi alamar " _ah'ah_ ".
" _Ni baby nakeso_ ".
Tafa'da tana murmushi tare da komawa daga bayansa ta 6uya.
Mahmud kam mamaki ma hanasa magana yayi kawai ya bude baki tare da zaro idanu.
_Comment Vote and Share_
*Salmerh ce* π
[10/2, 6:02 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
*Bismillahir rahmanir raheem*
_Beauty catches the attention but character catches the heart........_
π
Ώ *63*
Tausayin ta ne yakama shi dan yasan kamar yanda bakinta ya furta hakan toh ko cikin zuciyarta ma hakan ne, kuma duk wanda yace ma yanasan 'da toh yana so 'dinne da dukkan zuciyarsa, saboda soyayyar 'ya'ya 'ka'k'karfar soyayya ce dake wanzuwa azu'kanta dukkan iyaye.
Juyawa yayi gaba 'daya ya fuskance ta sai ta fara 'ko'karin guduwa daga inda yake.
Hannu Mahmud yasa ya dawo da ita inda take zaunen sai tayi maza ta me da kanta 'kasa yanda baze ga fuskarta ba, 'kafafunsa dake tan'kwashe ta kifa kanta akai tana murmushi, hannunta kuwa ri'ke acikin nasa.
Hakan kuwa datayi sai yasa Mahmud baya ganin komai sai bayanta.
Shima murmushin ne ya kubce masa yana murza yatsunta dake hannunsa yace mata
" _kinsan cewa abin kunya ne meyasa dama kika fa'da_ ?
Luf tayi ta'kiyin ko motsi kamar ma bada ita yake maganar ba illah murmushin data keyi 'kasa-'kasa.
Kunyan iyayin nata ba karamin birge shi yake yi ba, aransa ya yanke shawaran gara kawai ya gaya mata gaskiyan abinda ke faruwa dashi tunkan shirun nashi ya 'kurewa ha'kurinta.
Mahmud jan jikinsa yayi ya jinginu da jikin gadon ya lan 'kwashe hannunsa akan 'kirjinsa tare da mi'kar da 'kafafunsa wanda hakan yabawa Fateemah daman kwantar da kanta da kyau akan 'kafafun nasa tana kallon gefe, har yanzu ta'ki ta kalli inda yake ma balle har su ha'da idanu dashi ita adole kunya takeji.
Mahmud ne yafara magana da fa'din
" _Fateemah kinsan kwanan nan nayi tafiya ko_ ?
Shiru tayi masa taki yin magana, shima yasan bazata tanka sa ba dan haka sai yaci gaba da maganarsa.
" _Daga Umar abokina babu wanda yasan dalilin tafiyar danayi wacce nayi ta ne dan neman magani wa matsalar data same ni da ni kaina bansan_ _takamamman lokacin da hakan ya faru ba, daga zuciyata sai Umar sai kuma ke da zan sanar dake ayanzun bayaga haka babu wanda yasan abinda ke damuna. Fateemah ada na kasance mutun ne ni lafiyayye ta ko wani 6angare wanda ni kaina na shaidi hakan bana bu'katar sai nayi_ _wani dogon nazari akan haka, dai-dai da rana 'daya ban ta6a tsintar kaina cikin wata matsala_ _acikin jikina ba, wanda badan nasan hakan ba da babu abinda zai sa in amince da batun auranki, bama ke ba koda kuwa wata_ _macece daban bazan taba yadda in aureta ba ko dan gudun kar na shiga hakkinta_ _ma_ .
_Kwatsam bayan aure na dake sai na tsinci kaina cikin wani hali, halin da baze ta6a barina in rayu da iyalina cikin kwanciyar hankali ba, nakan gode Allah amafi yawancin lokuta daya sanya kece kika kasance mata agareni ba wata daban ba, wanda na tabbata da wata daban ce da yanzu mun da'de da samun matsala da ita ko ma mun_ _rabu, saboda ba kowacce mace bace zata iya zama dani ahaka yanayin da nake mu zauna cikin rufin asiri ba sai ko in nayi sa'a_ , _kinga ke kuwa kin zauna dani ahakan baki ta6a nuna min damuwarki akan haka ba baki ta6a_ _nuna min_ _gazawarki ko canjin fuska akan zama dani ba duk da nasan ba asan ranki bane, ni da kaina_ _nasan kina da bukatar kasancewa da mijinki alokuta da dama ba sai an_ _sanar dani ba ni ni shaida ne akan wannan.Fateema_
_kinga ko awannan 6angaren ma ka'dai dole in godewa Allah na tare da yabawa da za6in_ _Abbah na, domin shi yayi ruwa yayi tsaki wajen ganin kin kasance mata agareni. Ko_ _yanzun ma banyi mamaki ba dan kince kinada bu'katun baby_ _domin nasan wannan shine burin dukkan ma'aurata, ni kaina Fateemah inason baby amma_ _ayanayin dana tsinci kaina kinga dole ne na ha'kura na sanyawa_ _zuciyata salama har zuwa lokacin da Allah ya bani lafiya inda rabona sai kiga yabani"_
Hannuntan yasake kamawa ya rike cikin nashi tare da ran'kwafo da kansa kusa da nata kan sannan yaci gaba da maganarsa.
" _Fateemah kema ina so kiyi ha'kuri kinji kitayani ro'kon Allah ya bani lafiya cikin gaggawa_ _wala Allah ko zamu dace dasamun farin_ _cikinmu_ "
Yana kaiwa nan yasa hannunsa yadafa kanta sai ta juyo ahankali ta kalleshi, take kuma sai ta kauda kanta da barin kallon shi, ita bazatace ga yanayin datake ciki ayanzun ba domin maganganun Yah Mahmud gaba 'daya sun karya mata zuciya tama rasa tunanin me zatayi kwata-kwata, data san hakane ma da bazata kawo maganar babyn ba, ashe ita bata sani ba ashe matsala ce dashi har da take ganin kamar wai shi daban yake harda cewa matar Umar cewa su ba irin zaman dasukeyi ba kenan dashi, batasani ba ashe sirrin aurenta ta fitar.
Mahmud kuwa hannunta dake acikin nasa ya kallah tare da 'dora 'dayan hannun nasa ya lullu6e natan dashi sannan ya 'kira sunanta ahankali.
Kallonsa tajuyo tayi batare datayi magana ba jin yanayin da ya ambace tan cikin slow voice da sanyi, shima Mahmud be saurari jiran amsawarta ba ko hankalinta data bashi ma ka'dai ya wadace shi sai yace.
" _Fateemah......ki yafe min_ _kinji......kiya femin dan Allah nasan ban kyauta miki_ _ba koka'dan ban miki adalci ba dana zauna dake ahalin danake ciki, amma inaso kisani banyi_ _haka dan na 'kuntata wa rayuwarki ba koka'dan face_ _dan rufin asirinmu dana mu, kuma insha Allahu inasa saran samun sau'ki acikin kwanakin_ _nan.......ki daure dan Allah ki taushi zuciyarki ki yafe min hakkinki dana kasa sauke miki a iya zamanmu_ _dake kinji........._
Da sauri ta 'kwaci hannunta ta tashi ta toshe mai baki da hannun nata sai suka tsaya kallon kallo dashi, kanta ta jijjiga masa ahankali tare da fa'din
" _Ni baka min komai ba yayah kuma nasan har abada bazaka_ _ta6a yin wani abu dan ka cutar dani ko rayuwata ba, don Allah ka daina_ _neman gafara ta kaji Yayah_ !
_Kaifa kace ka godewa Allah da ya sanya nice matarka_ , _toh ni me yasa bazaka bani dama ingode masa ba da ya Yah Mahmud yakasance_ _shine miji ba agareni, dan kawai Allah ya jarabcemu da wata kaddara sai hakan_ _ya sanya ka neman yafiyata?, toh in hakane Yayah ni agurin nemo_ _yafiyar_ ?
Hawaye ne yaji suke shirin gangaro masa saboda yanda kalaman nata suka ratsa shi, da sauri ya janyo ta ya rungume ta acikin jikinsa sannan ya lumshe idanu take hawayen nasa suka 'karasa gangarowa suka sau'ka akan wuyan Teemah.
Akan la66ansa ya furta " _Allah ya miki albarka matata Allah ya albarkaci rayuwarki duniya da lahira_ "
Yana gama fa'din haka sai ya rintse idanunsa da 'karfi tare da sake matse ta ajikinsa tamkar wani na shirin 'kwatarta.
Damshin dataji asaman wuyanta ne yasa ta yunkuri ta 'kwaci jikinta daga nashi ta kalli fuskarsa sai taga still yana hawaye.
Da rawar murya ta furta " _kuka kakeyi_ _Yayah_ ?
Yatsansa yasa ya rufe mata baki alamar tayi shiru sai yasake janyota ya rungume ta akan kirjinsa tare da gyara zaman nasa zuwa kwanciya yayinda idanunsa ke kallon ceilling fan 'din dake saman 'dakin, Fateemah kuwa kanta akan kirjinsa ta kwanta tayi shiru itama gaba 'daya jikinta yayi sanyi.
Hannu Mahmud yasa yana bubbuga bayanta ahankali tamkar wata yarinya 'karama yayinda yakejin wani sabon yanayi tattare dashi da be ta6a tsintan kansa aciki game da ita ba sai yanzun, ahankali bakinsa ya furta " _I love u Fateemah, i really love u with all my_ _heart, ha'ki'ka ke daban ce acikin mata, Allah ubangiji yabani lafiya da tsawon rai_ _dan kawai inkula dake da rayuwarki, in cika rayuwarki da soyayya ta yadda bazaki ta6a dana sanin kasancewa tare dani ba_ "
Rasa takamamman yanayin da take ciki tayi alokacin farin ciki ne ko akasin haka kasa ganewa tayi, aru'de ta bu'di baki da niyyar magana
"Ya.......
da sauri Mahmud ya dakatar da ita da fa'din " _shiiiii_ "
Take kuwa tayi shiru kamar yadda ya bu'kata 'din bata 'kara yin magana ba, shima kuma shirun yayi yana cigaba da kar6an duk wani sa'kon da zuciyarsa ke bashi game da Fateemahn, ahaka bacci yayi awon gaba dasu gaba daya.
'Karfe ukun dare yaji Fateemah na mutsu-mutsu ajikinsa sai kuwa ya bu'de idanu akanta gani yayi tana sake cusuwa masa ajiki tare da yamutse jikinta guri guda.
Sunanta yafara 'kira ahankali yana 'ko'karin tada ita, bata amsa masa ba sai ma kuka data sanya tare da 'ko'karin janye rigarta tamkar rigar na mintsinin jikinta ne fincika take yi da 'karfinta kamar rigar nayi mata 'kai'kayi.
Ganin haka yasa Mahmud ya ri'ke hannun nata sannan ahankali yajanye mata rigar yacire kamar yadda yaga take da burin yi.
Mahmud idanunsa ya 'kura 'kur akan 'kirjinta wanda suka matu'kar tafiya da imaninsa.
Tun aurensa da ita be ta6a tsayawa ya 'kare musu kallo har haka ba sai yanzun, ha'ki'ka Allah yayi halittarsa awannan gurin.
Hannu yakai da niyyar ta6a wa sai yaji sau'kan numfashinta ahankali, dubansa ya mayar kan fuskanta sai ya ga ma har tayi bacci.
Ajiyar numfashi ya sau'ke tare da hamdala azuciyarsa daya kasance abin nata be ja tsayin lokaci ba yau 'din.
Fasa ta6awan yayi kawai sai yaja mayafi ya lullu6a mata.
Yana rufa mata mayafin ya mi'ke ya wuce bathroom alokacin 'karfe uku da mintina ashirin (3:20am) dan haka alwalarsa ya 'dauro yazo ya tada sallah raka'ah hu'du yayi ha'de da sallamarsa guda biyu sannan ya 'daga hannu ya dinga zuba musu addu'o'i na kariya da zaman lafiya harma da nemawa aurensu albarkar mahalicci, yana shafawa ya janyo Al qur'ani yafara karantawa kafin lokacin sallah yayi saida ya karance suratul Ankabut sannan ya rufe karatun nasa da suratul Ikhlas, Nasi da Falaq ya shafa da salatin Annabinmu Muhammad ( S.A.W).
Saida yayi raka'atanil fajri kafin ya kawo sallar asubarsa abayanta.
Be tashi agurin ba sai da yayi azkar 'dinsa na safiya kafin yatashi yaje ga Teemah domin yatashe ta itama tayi tata sallar, alokacinma gari har ya 'dan fara haske.
Koda yatashe tan ma da 'kyar ta bu'de idanunta saboda nawin dataji kanta yamata ga kuma bacci da har alokacin be bar idanunta ba, tana daga kwancen ta bu'de idanunta sai kuwa ta hango windo gani tayi gari har ya fara haske.
Da wuri ta mi'ke arazane ganin lokaci yatafi, sai kuwa takoma da sauri sanadiyyan ganin jikinta bakaya.
Mayafin data yaye ajikin tan ta kuma janyo wa ta 'kara rufe jikinta dashi.
Mahmud yi yayi kamar be ganta ba ya wani fuske ya kauda kansa gefe.
Teemah kuwa baki ta turo gaba tana gunaguni 'kasa baya ma gane mai take fa'di.
Mahmud kuwa murmushi yayi mata kawai tare da fa'din
" _Gara ma ki bu'di baki ki fa'di abinda ke ranki yafiye miki dan kukkuni ba ze kaiki ko'ina ba_ "
Baki ta 'kara turawa gaba tana kalle kalle shikuwa sai ya rin'ka binta da kallo kawai murmushinsa na 'kara yawaita.
Data ga bata samu abinda take neman bane sai ta bu'di baki cikin shagwa6a tace
" _Ni kam wallahi Yayah ka daina ciremin rigata idan ina bacci_ "
Ido ya 'dan zaro waje yace " _waye yagaya miki ni ne_ _na cire miki_ ?
Kamar zatayi kuka tace
" _Ehh mana kaine idan ba kaiba wayene naga ni dakai ne kawai acikin gidan_ "
cewa yayi
" _Dan ke da ni ne kawai agidan kuma sai aka ce miki ni ne na cire ko_ ?
" _Toh waye ne yacire min_ ?
Da muryar kuka
ta tambayeshi tana kallonshi.
" kai ya kaudar gefe cikin ko inkula yace " _toh idan ma ni 'din ne ai ke kika sani, kece kika ce incire
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 67