Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
matsala dasu, aganinsa mata damuwa ne sosai su, ko lokacin da ya ke higher institution d'insa ma inka ganshi da mata toh friends ne ba komai ba, kwatsam sai gashi yanzu mahaifiyarsa ta 6ullo masa da maganar aure alokacin da shi sam bai shiryawa hakan ba, amma babu yanda zai yi dolensa ya kar6i maganar kodan darajar da take dashi na mahaifiya agareshi bazai bada ita ba, yayi alk'awarin cewa da iznin Allah sai ya nuna cewa shid'in d'aah ne, kuma na halak cikakke. Ido Abban ya tsura masa da dukkan kulawa yana kallonsa , sosai ya fahimci d'an nasa na cikin damuwa sai yayi gyaran murya ya fuskanci Mahmud d'in da kyau sannan yace masa " yah akayi ne Babana"!. Ahankali ya d'aga kai ya kalli Abban nasa suka ha'da idanu take sai yayi gefe da kansa kamar mace tare da k'ak'alo murmushin k'arfin hali. Da k'yar ya samu ya tattara bayanan dake bakinsa ya dunk'ula ya furta "Ab...bah wai dama maganan yarinyar da zan aura ne, wai ko za'a je ayi tambaya". Murmushi Abban yayi sannan yace "Mahmud ba dama, wai ko za'a je ayi tambaya ko kuma kana so aje ayi maka tambaya? Murmushin yakuma yi batare da magana ba. " babana yau d'in kai ke yin abu kamar mace!? " hmm toh a ina yarinyar take? Abban ya sake tambayarshi. Ahankali ya kwatantawa Abban nasa,daga yanda yake maganar sai Abban ya fahimci abin sam baya ran Mahmud d'in musamman daya tuno ranar da Antyn ta maresa akan wata yarinya,sannan ranar da Mahmud d'in ya 'kirasa alokacin dayake damaturu akan maganan auren da Anty take yawan yi masa harma ta uzzura masa yadawo gida duk akan maganar ba shakka wannan duk tilastawar Maryam ne, ni kuwa bazan ta6a tilastawa yarona abinda baya so akan wad'anda bama sanin asalinsu yayi ba. Lokacin da Mahmud yasanar da Anty cewa sun gama magana da Abban kuma ga abinda yace ji tayi kamar ta goyashi saboda farin ciki. Tayi zaton ai Mahmud d'in zaiyi mata taurin kai ne yak'i zuwa amma kuma sai yaje, hakan kuwa ba k'aramin farin ciki yasata ba. Abbah binciken yayi kamar yanda ya fad'ad'in yayinda binciken ya d'aukesa kusan sati kafin ya gama gamsuwa da duk wani abinda yake son sani game da wannan family d'in. Bai sanar da Mahmud ba ya k'yaleshi, yana so ne yaga ko Mahmud d'in zai zo dakansa yasake tambayarsa idan yaga shiru ko yayah ,yasani cewa matuk'ar da yaddansa a auren to shi zaifi kowa rawar jiki dan ganin an kammala komai dawuri inkuwa bahaka ba ma'ana bai sakeyin magana ba toh kenan shima be wani damu da maganar ba kenan rashin damuwarsa da maganar kuma na nuni da cewa baya ra'ayin abin har ransa. Hakan ya sanya Abbah yayi gum da magabar shima yana jiran yaji daga Mahmud d'in. Rashin ha'kurin Anty yasanya ta kasa ha'kuri da taji shiru babau wanda yasake bi takan maganar sai ta tuntu6i Abbah da maganar shikuwa yace mata bincike yake yi tukunna har yanzu, ita a ganinta tunda Mahmud yariga yayiwa Abbansa magana ai itama zata iya yi masa maganan irin kamar Mahmud d'in ne itama ya sanar da ita. Bata wani damu ba saboda ita kanta bata san asalin tarihin 'kawartan ba shiyasa koda Abban yace zaiyi binciken bata damu ba. ***** Teemah kuwa tana can sun gama hutun interval d'in dake tsakanin waec da Neco d'in har sun fara Neco yau suke na biyu,tun kafin ayi nisa tafara missing d'in Mahmud domin tasaba karatun dashi sosai yake highlighting d'inta akan wasu abubuwan da bata ganesu, yanzu kuwa babu shi, sai dai tayi ita kad'ai, dayake Daddyn ya sai mata waya a satin daya gabata, arana ta uku tana tsaka da karatun data ji ba sugar sai ta 'daga wayarta ta ta 'kira Mahmud tayi ta masa complain akan ita fah bata ganewa tunda yatafi take shan wahalan karatun gashi kuma ya'ki dawowa. Lalla6anta yayi tayi yana bata ha'kuri a itakuwa tayita masa shagwa6a,ahakan ya tambayeta inda bata gane ba d'in data fad'a masa sai yayi mata bayani ata'kaice yanda zata gane. Shikenan kusan kullum in tana da exam sai sunyi waya dashi a haka har aka kusan kammala Neco d'in . 2 days to candidate d'inta Daddy suka rabu da Abban Mahmud A lagos basu ma gama abinda sukeyi ba amma daddyn Teemah yace zai dawo gida saboda graduation na Teemah yana so ya halatta. Anan Abbah yayi mata fatan alkhairi harma yace badan akwai aiki agabansa ba da shima zai je shi, Daddy ne yace bakomai ai addu'ar ma ta wadatar, sai Abban yace duk da haka ma insha Allahu idan yasamu lokaci ko bayan graduation d'in ne zaije musamman ya ziyarcesu. Farin ciki ne sosai yacika ziciyar Daddy dan yajima baiji irin hakan daga bakin abokin nasa ba, so yana jin hakan yasan ikone kawai na ubangiji dayake kawo 'karshen duk wani al'amari inma me kyau ko akasin haka. Ko da yaje gida kuwa bai sanar da mummy ba saboda yana son koda Abban Mahmud d'in zaizo toh zuwan ya zamewa mummy na bazata, kar kuma ya sanar da ita yanzu cewa Abban zaizo zuwan kuma yak'i yiyuwa duk dama ba'a fatan hakan, amma kuma idan hakan ya faru zai kasance ne kamar shine ma'karyaci a idanunta. _Comment vote and_ _share pls_ 🀞🏻 (4 those that missed Abbas insha Allahu next page zaku jishi )πŸ˜ƒ *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Sometimes u have 2 4give & 4get,4give them 4 _hurting_ & 4get that they even _exist_ . πŸ…Ώ *35* Lokacin da daddy zai dawo gida sai ya siyo wa Teemah tsarabar set 'din 'dan kunnan gold mai kyaun gaske afad'arsa wai zatayi anfani da shi ne ranar graduation d'insu as his gift, mummy najin haka tace "a'a sam" badai aranar ba kam sai dai ordinary day haka ta saka dan bazai yiwu taje cikin taro da wannan sar'kar ba, yanda duniya ta lalace d'innan duk dama ba'a fatan wani mummunan abu amma ai _maganin kada ayi_ _toh kada afara_ . Daddy ma dayaji bayanan mummyn take yaji ya gamsu sosai tuni ya amince da batun mummyn, Teemah kuwa na tsaka da murna ta tsinkayo muryar mummynta na fad'in haka take sai murnar ta tsaya cak, sai ta tura baki gaba tare da sake matsowa kusa da daddyn ta tana ta wani muzurai. Babu wanda ya kulata sai da yagama da mummyn kafin ya juyo ya fuskanceta yace tayi ha'kuri za'a siya mata wani wanda zata saka ranar inyaso daga baya sai tayi anfani da wannan 'din...... Kafin ma ya 'karasa fad'a mummy tace " ai already ma na siya mata wanda zata saka d'in." "Yauwa shikenan ma kin hutar damu ko my angel " cewar daddy yana murmushi. Teeamah kuwa 'kasa tayi da kanta taci gaba da kallon bangles da zoben dake tare da sar'kar bata 'kara yin magana ba har mummy tabar gurin, sai da mummyn tatafi kafin ta 'dan sake har take tambayarsa labarin yayanta Abbas, dayake tafiyan dayayin sai da yaje Abuja tukun na kafin yawuce lagos sai ta tambayeshi wai ya ga Yah Abbas kuwa dayaje Abuja?. Dariya yayi mata tare da fad'in " wato yayanki kad'ai kika sani ko? Murmushi tayi harda wani sunkuyar da kai ' kasa kamar dagaske. Daddyn ma sai yayi murmushin sannan yace" Abbas ai baya Abuja porthacourt yake aiki" Tana jin haka sai ta 'dan tura baki gaba kana tace " aini ba ruwana ma dashi daddy tunda shima ya manta dani" Ido daddy ya zaro kad'an " ke da yayan naki"? " ehh mana daddy, tunda yatafi fah ya manta dani, kuma inaji ko suna waya da mummy baya tambayata, baya cewa agaishe dani kuma mummy ma bata ta6a cemin in kar6a mu gaisa da shi ba...........shiyasa nima da aka siya min wayata ban saka numbern shi ba, ta yah Mahmud kad'ai na............ shiru tayi ta 'daga kai ta kallo 'kofa sakamakon jiyo muryar mummy datayi tana fa'din " sai kiyi ta tura bakin nan ai har sai ya ta6o 'kasa tunda ke bakijin maganan mutun " Mummy dake 'ko'karin shigowa ne ta kar6e maganar Teemahn da fad'in haka. Shiru Teemahn tayi bata 'kara magana ba,sai kawai ta sunkuyar da kanta 'kasa taci gaba da kallon abinda ke ri'ke a a hannunta, sai da mummyn ta ta iso ta zauna kafin daddy yace tura bakin me kuma tayi ne hajiya? " " Ka 'kyale yarinyyar nan ,wallahi ko kad'an bata jin magana, dubi fah 'karfi da yaji yanda ta maida bakinta kamar tsuntsuwa........ Dai dai nan ta juya ta kallo Teemah sai idonta ya sau'ka akan hannun Teemahn ganin da tayi tana jujjuya d'an kunnan ahannunta take sai ta sake fad'in " bani ni karki 6alla shi abanza daga kawowa" tafad'a tare da mi'ka hannunta saitin Teemahn.. Teemahn ma sai ta mi'ka mata sar'kar batare da wani 6ata lokaci ba. Sai da mummyn ta kar6a kafin ta d'aga kanta caraf sai suka had'a idanu da daddyn, hannu ya 'daga tare da ware yatsa 'daya ya nuno mummyn dashi yana jujjuya kai da kuma yatsan nasa duk atare da murmushi akan fuskarsa alamar " ke bah" dayake kan Teemah na 'kasa duk bata lura ba. Mummyn ma sai ta saki murmushin tana maida sar'kar a gidanta take fad'in " naji ma ana gulmar yaro na laifin me kuma yayi muku?" Daddy fa'da'da fara'ar sa yayi sai ya bata amsa da fa'din " Laifin ai harda ke , ya za'ayi kullum kuna waya da Yayanta tanaji amma baza'a bata waya su gaisa ba,kuma laifin harda naki da kema bakya ce mishi gata nan akusa". "au laifin kenan dama? Mummyn ta tambaya tana 'dan murmushi idanunta na kan Teemah. " 'kwarai kuwa, wannan 'din 'karamin laifi ne aganinki? " hmm" kawai mummyn tace. Sai daddy yace " ba hmm ba, so muke agyara adaina ware min angel 'dina agefe, shima Abbas 'din zan had'u dashi ai" Take sai yah 'daga wayarsa da niyyan 'kiran Abbas 'din sai kuma cikin rashin sa'a 'kiran be shiga ba. " Allah ya taimake shi ai" daddyn yafad'a yana mai ajiye wayar agefensa. Daganan ya cigaba da lallashin Teemahn da bata ha'kuri akan wai duk ranar daya samu Abbas d'in awaya zai yi masa masifan dan me baya son tambayanta idan suna waya da mummy." Bata dad'eba ta sau'ko daga fushin suka cigaba da hirarsu anan daddy yake tambayan ta yanda aka tsara graduation d'in duk ta fad'a masa,tana gama fad'a tace ta tashi tace zata tafi 'dakinta,sai yace ta kunna masa NTA kafin tafita. Tana kunna masa tafice bayan ta mi'ka masa remote 'din TVn. Labarai yaci gaba da kallo abinsa,dama daddy gwani ne a kallon labaran duniyah idan yana watching news hankalinsa gaba d'aya suke tafiya awurin. ***** Ranar Saturday shine ya kasance ranar da za'ayi graduation d'in Teemah, sosai wannan family d'in suka yi shiri na musamman a wannan ranar just to make their one and only daughter happy, ga wanda bai sani ba idan ya shiga gidan aranar ze yi zaton ko wani d'an hidiman biki akeyi agidan, amma ga wanda yasani sai de yace masha Allah. *'Karfe 9:00am* Teemah ce tafito cikin wata ha'da'd'diyar gown d'inta d'inkin tela kalar ja, d'inkin ba 'karamin kar6anta yayi ba, 'dass ya zauna mata kamar ajikinta aka yi 'dinkin rigar, yayinda kanta yake 'daure da head golden colour kamar ba da hannu akayi 'daurin ba, tsabar yanda ya zauna akanta , wata mata data amsa sunan ta ce afagen make-up ita tayi mata 'daurin, wanda mummy musamman ta sa aka nemo mata matar dan kawai tayi wa Teemah kwalliyan graduation d'in, gefen kafad'anta shima golden colour veil ne mai kyan gaske , ba naa ce ga adadin kud'insa ba dan ko nima bansan lokacin da mummy tayi wannan siyayyan ba,ga wani high hill d'inta mai kyau shima duk kalan gyalan nata. Turare kuwa ba laifi 'kanshin na tashi dai-dai ajikinta bata saka daya wa ba dayake Teemah ba son anfani da turare mai 'karfi take ba body spray kawai ta fesa ajikinta tafito. Kallo 'daya zaka yiwa Teemah kayi zaton ko amarya ce dan tsabar yanda tafito tamkar wata tauraruwa. Ahankali take tafiya tana wani basarwa, ita adole irin an girman nan. Kalle-kalle takeyi acikin harabar gidan tana 'dan waiwaya wa, sai kuma tacigaba da tafiya yayinda ta tunkaro inda mummy ke zaune ahankali. Tun daga nesa da mummy ta hango ta fara'arta ya 'karu aranta take fa'din _tubar kallah masha_ _Allah_ Allah yah ya raya minke 'yata. Kafin Teemahn ta iso gurinta ma harta mik'e tsaye tana murmushi Teemah na isowa kuwa ta bud'e mata hannu Teemah kamar jira takeyi tafad'a ciki tana dariya. Dariya mummyn ma tayi dukkansu sai ya zamana ha'koransu kawai zaka gani afili tsabar yanda suke jin dad'i fuskarsu kawai zaka kallah kasan cewa ehh lallai suna cikin farin ciki. Mummy aranta take tayiwa Teemahn addu'an kariya daga kowani irin abun k'i. Koda ta saki Teemahn ma abinda tafara fad'i azahiri shine " Masha Allah, yarinyata anzama 'yanmata, Allah ubangiji yasa wannan level d'in yah 'kare kenan har abada, Allah yasa anyi a sa'a, Allah yasa ba'a yi gaba anbar baya da 'kura ba". " Ameen yah Allah " Teemahn ta fad'a tana d'an dariya. Sannan tace mummy ni nagama shiri yanzu zan wuche,kinsan ance mana kar muyi african time, gashi ma yanzu 9:00 d'in kusan da rabi ma "! Ta 'karashe tana mai duba agogon cikin wayarta.Dayake ance 'karfe goma ake bu'katan su awajen gaba d'aya candidates d'in. " toh kije ki samu Habibu ya sauk'e ki, sai mun iso muma" Juya wa tayi tare da fad'in " toh mummy sai kun iso " " yauwa kar amanta da addu'an barin gida fah" Wannan karan kam da kai ta amsa batare data juyo ba. 10:00am aka fara programme d'in,Teemah na can ita kad'ai daga ita sai 'kawayenta, akai akai take duba hanya ko zata hango mummy amma shiru harta gaji ta ha'kura ta maida hankalinta ga abinda ke gabanta. *10:35am* Mummy na tsaka da aiki sai ta tashi ta je kitchen ta d'auko abu fitowan da zatayi kamar ance ta kalli harabara gidan sai idanunta suka sau'ka akan Abbas daidai ya bud'e mota ya fito. Aikuwa mantawa da abinda ta 'dauko in tayi da ke ri'ke a hannunta,da sauri tafara tafiya ta nufi wajen data hango shi d'in, shima da farko be lura da zuwan nata ba sai da ta kusan isoshi kafin ya ankara da ita, aikuwa sai yafara murmushi kana yace " mummy har kin ganni ne ". " ai dole in hango ka wannan irin suprise haka Abbas"! " wallahi kuwa mummy". Tafiya suka farayi ska nufo cikin gidan atare yayinda mummy take tambayarsa ya wajen aikinsa yace " aiki kam Alhamdulillah sai godiyan Allah kawai". Zuwan nashi ya matu'kar bawa mummy mamaki domin bata ta6a kawo cewa zai halacci taron ba, sai kuwa gashi nan yazo. Sosai taji dad'in zuwan nashi, basu ko gaisa da kyau bama dashi dan hankalinta na wajen aikin data bari anayi acikin gidan, data d'an tako masa tace mishi yaje 6angaren daddyn su yana ciki be fita ba tukun na, bari ta dubo abu tana nan zuwa yanzu itama, tana gama fad'a sai ta juya ta wuce cikin gidan. Shikuma sai ya tsaya awajen, sai da yaga takoma kafin nan yajuya ya koma inda suka yi parking motarsu ya je ya ciro wani kwali me d'an girma amma ba sosai ba,wanda suke taren na jikinsa na rawa yake 'ko'karin 'dauka masa sai Abbas ya dakatar dashi da hannu yace yayi zamansa ba matsala zai 'dauka kawai ga dukkan alamu drivern sane mutumin duba da yanda yake ta ambaton " sir " adukkan maganar dazata had'a shi da Abbas 'din. Lullu6e kwalin yake da wrapping sheet baka gane kami game da kwalin faa ce size 'din kwalin. Sai da ya kai dubansa inda yaga mummy ta nufah 'dazu sai yaga hankalinta gaba d'aya baya wani guri aikin dake gabanta kawai ne tasa agaba ga da alama a'kage take taga aikin ya kammala ganin hakan dayayi yasa ya taho da sauri ya nufi 'k'ofan babban parlour, amma cikin rashin sa'a daf dazai shiga parlourn idanun mummy ya hango shi akaro na biyu, hannunsa ta duba da wuri ganin cewa yana ri'ke da abu ahannun sai dai bata wani gane abun ba sai tayi zaton ko jakar kayansa ne. Da yake yasan kan gidan sosai batare da an jagoran ce shi ba sai ya wuce direct 'dakin Teemah ya ajiye kwalin dake hannunsan kafin ya mi'ke tsaye sai da ya tsaya ya 'karewa 'dakin kallo kaf kafin ya fito ya nufi 6angaren daddyn. Koda yaje 6angaren daddyn kuwa sallama yafarayi sai yaji shiru ba'a amsa masa ba, sai da ya sake yin wata sallamar sau d'aya yaji still ba'a amsa ba sai ya d'an tsaya na 'dan da'ki'ku, 'karan TVn daya jiyo ne yasa shi fahimtar dalilin dayasa daddyn be ji amon muryarsa ba, kuma yana da yak'inin cewa koda zai yi sau ba adadi ne daddyn bazai ji ba matuk'ar TV d'in akunne yake. Sanin cewa daddyn shi d'aya ne acikin 'dakin yasa ya tura k'ofar tare da sake yin wata sallamar ciki-ciki, ahankali ya maida 'kofar ya rufe bayan ya shigo d'in, sai ya tsaya kamar an bashi umarni, daddyn ya tsaya yana 'karewa kallo yanda yasha manyan kaya yawani fito shar dashi tamkar wani sabon matashi. Ahankali yafara takawa yayinda salon tafiyar tashi ya matu'kar amsan zubi da tsarinsa ga duk wanda yasan menene had'uwa toh ba sai na gaya masa yana kallon Abbas yasan cewa ya ha'du sosai, be tsaya ko'ina ba sai dayaje gaban TV d'in kafin ya tsaya, sai dai kuma be bari daddyn yaga fuskarsa ba,baya ya juya wa daddyn da sauri ya maida fuskarsa take fuskantar inda bangon da TVn yake bayansa kuma na kallon daddyn. Daddy da bai san anshigo bama balle yasan waye ya shigo kawai sai yaga mutum tsaye ya tare masa news d'in dayake gani, lumshe idanunsa yayi dayaga hakan tsawon dak'ik'a goma kafin ya bud'e tare da fad'in " _ABBAS_ " . Dariya Abbas d'in ya kwashe dashi sannan ya juyo yafara tahowa zuwa inda daddyn ke zaune. " ya akayi ka gane ni da wuri haka daddy bayan baka kalli fuskata ba " ya tambaya yana kallon daddyn bakinsa d'auke da murmushi. " toh wa nake dashi da zai min haka banda kai" Daddyn ma yabashi amsa yana murmushin shima. Dukka sai suka yi d'an takaitaccen dariya. sai daddyn ne ya kuma cewa " ja'iri daga ina haka kamar an jeho ka?" " wallahi kuwa, escaped nayi daddy yau d'innan za koma ma kafin anemeni, ba shiri nataho kuma akwai ayyuka agabana". " haba kuma sai kace dole ai daka bari zuwa wani lokaci in kasamu isasshen time basai ka zo ba." " ba na so na.....,,. Daidai nan mummy tashigo da sallamarta abakinta. Sai Abbas d'inma ya dakata daga maganar da ya yi niyyan fad'i duk sai sukayi shiru suka jira harta iso ta zauna. Barka da isowa tayi masa tare da fad'in " dazu ina sauri bamu wani gaisa da kyau ba ". Murmushi yayi mata kawai sai ta sake fad'in " gaskiya ka shammace mu Abbas gashi bansan da zuwanka ba ko muhalli ba'a gyara maka ba" . " Ai ba komai mummy ina ma kan hanya ne yanzu zan wuce" " dawuri haka?, ka de bari ka 'dan huta ka'dan de ko,ai nayi zaton ma graduation d'in kazo halatta dana ganka"! Abbas cewa yayi wai " a'a shi yama manta da wancen batun ai tuntuni tun bayan data sanar da shi abin be kuma zuwa kansa ba.". Su kuwa duk sai suka yadda akan ehh dagaske yamanta d'inne ba mamaki ko dan saboda irin aikinsan,wani lokaci abubuwa kansha kan mutun sosai. Abinci aka shishshigo dashi da abin sha aka jejjera sai da aka gama sannan mummy tace toh bismillah ya d'an samu ya ta6a ko kad'anne ma kafin ya wuce d'in. Dukka atare suka mik'e har daddyn suka nufi wajen da aka jera abincin, mummy na zuzzubawa tace " kamar kuwa kasan kullun sai anmin mita agidan nan, harda su kaiwa 'kara na wai bana bata waya kuma kaima baka tambayarta ko ka 'kira wayan ". " daddy ne ya kar6e da fad'in toh dah d'in 'karyane?, ai da gaskiyarta" , daganan sai ya dawo da dubansa wurin Abbas yace " me yasa baka tambayarta awaya idan ka'kira kuma ko sa'kon agaishe ta ma baka ta6a fad'a ba." Dukkansu sai maganar daddyn da yanda yayita kamar titsiye sai ya basu dariya, shima daddyn sai ya taya su dariyar, sai da suka tsagaita kafin yace " toh haka nayi al'kawarin zanyi ku kuma naga kuna min dariya". Abbas baiyi magana ba sai mummy ce tace "ai idan kabiye Teemah kam abinda yafi haka ma zakayi shi". Murmushi sukayi daganan suka fara cin abincin da mummy tagama zuzzuba musu, mummyn kuma tafita abinta ta basu waje tatafi domin ta shirya. Abbas na gamawa yacewa daddyn shi zai wuce dama ya shigo ne brief ya gaishe su, cikin sa'a ma kuma saiya samu daddyn nagida. Albarka da addu'o'i sosai daddy yata yimasa sannan ya rakoshi har wajen parking inda drivernsa yake, tambayar drivern daddy yayi wai anya kuwa yaci abinci yace" ai be san cewa tare suke ba da an masa iso shima", sai ya 'daga hannu ya d'an mari 'keyar Abbas yace " ai duk laifin kane dabaka fa'da cewa dawani kuke ba " Abbas 'kasa ya d'anyi kad'an tare da shafa gurin kamar irin yaji zafin nan, sai yace " Afuwan daddy Allah na manta ne shiyasa". Murmushi sukeyi gaba d'aya har drivern ganin yanda Abbas yake yi agaban daddy kamar bashi ba amma idan awurin aiki ne ko ha'koransa da wuya kake gani. Sai drivern ma yace " yalla6ai aina ci abinci Hajiya ta aiko an kawo min anan" " Ahh toh shikenan sai ya juya ya kalli Abbas d'in ya sake cewa "Allah ya taimakeka da sai ka jira yaci abinci duk da saurin naka". Abbas da daddy kawai yayi sallama ko mummyn be jira sun sake had'uwa ba yayi tafiyarsa. _Comment,vote and_ _share pls_ 🀞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* ⚠ *NOT EDITED* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* SMILE ….. It irritates those who wish to destroy you. πŸ…Ώ *36* Suna fita ya fad'awa drivern sa inda yake so ya kai shi, koda suka je kuma basu tarar da kowa ba face mai gadi. Zuwa yayi ya mi'kawa mai gadin hannu suka gaisa sannan ya tambaye shi inda 'daliban suke take mai gadin ya sanar dashi. Abbas godiya yayi masa tare da juyawa ya koma cikin mota driver yaja suka nufi wajen. Da kwatance drivern ya gane wurin koda ya isa yayi parking a wurin Abbas kamar bazai fito ba kusan 10:mins kafin ya 'daga hannu ya duba agogon dake hannunsa sai yayi maza ya fito daga motar. Tsaye yake jingine ajikin motar yana ta 'karewa 'dai'dai kun mutanen dake wulgawa kamar me karantar wani abu tattare dasu. Tafiya ya fara cikin 'kasaita in ka ganshi zaka zaci daga wani gidan sarauta yafito, ahankali yake tafiya ya nufi hall 'din daya fi tunanin nan ne ake programme d'in dan anan ya ga anfi taruwa. Daf da zai shiga hall 'din daga gefe ka'dan ya idonsa ya hango masa ita cikin gungun 'dalibai sunata surutu ga dukkan alamu shirin yin pix suke yi ko kuma har sun 'dauka domin dukkansu zagaye suke da photo grapher ne. Tsayuwa yayi kamar andasa shi awurin shi bai shiga ba shi kuma be matsa daga inda yake tsayen ba. Be san mai suke tattaunawa atsakaninsu ba shi dai kawai sai yaga ta fara dariya, yayinda da dariyar tata ta matu'kar birgesa, sosai ya tafi da yanayin tsari da kwalliyar da ta tsantsara ayau d'in. Aransa sai yaji kamar tunda yake da ita be ta6a ganin kwalliyar sata amsheta irin wannan ba. Yanda ya 'kura mata idanu sai ajikinta taji tamkar ana kallonta, tana cikin dariyar sai ta 'dan fara dube-duben gefen ta. Garin dube-duben nata sai idanunta ya hango shi take kuwa idanunsu ya sar'ke cikin na juna, Abbas lumshe idaunsa yayi

Chapter 17 of 67