yasaki ransa yake amsa gaisuwa agurin har inbaka sani ba zakayi zaton ko shine ma angon domin azahiri annurin da ke kan fuskarsa ta nunka ta Mahmud 'din banbancin kawai shine kasantuwar Mahmud 'din a matsayin ango ya riga ya bayyana domin shike sanye da fararan kaya harma da babbar riga, Abbas kuwa be sa babbar riga ba shi kam.
Dukkansu suka ha'du suke amsa gaisuwar da duk aka mi'ko musu sai de kowa abinda ke ransa daban, kowa damuwar shi kala dabance, da haka har suka isa wurin da su daddy ke tsaye da sauran abokan Mahmud 'din dake tare dashi suna binsu abaya, suma su daddy sai faman gaisuwa suke yi da jama'ah suna kuma mi'ka 'dumbin godiyarsu marar iyaka.
Daddyn Abuja ne yafara ganin tahowarsu take sai ya fa'da'da fara'arsa fiye da ta baya.
Hararan Abbas yayi yana murmushi irin ka shammace mu 'din nan sa'annan ya mi'kawa Mahmud hannu da sauri, Mahmud sai da ya 'dan rissina tare da 'ka'kalo murmushi ya ya6awa fuskarsa kafin ya mi'kawa Daddyn hannun nasa suka gaisa Daddy nata yi masa addu'ah da sanya alkhairi cikin zolaya ya'kara da fa'din
_" saura abokin ka ko Mahmud tunda kai 'din ansamu kayi da 'kyar saura kuma shi dan na_ _lura ra'ayoyin kusan_ _iri 'dayace "._
Murmushi kawai Mahmud yayi tare da sosa 'keyarsa yana wani sukuyar da kai.
Abbas kuwa gurin Abbah ya nufa ya fara gaidashi sannan yadawo kan Daddy babbah ( daddyn Teemah).
Daddy bai amsa gaisuwar da Abbas ya mi'ka masa ba sai ya mi'ka masa hannu kamar zasu gaisa sai kawai ya zarce da hannun ya kamo kunnan Abbas dashi yaja " _Awshhhh daddy_ _zafi"_
Sake ja daddy yayi sai kuma ya sake atake yana murmushi. Abbas yasan dalilin yimasa hakan da daddy yayi ba zai wuche baki biyun dayayi bane akan zuwan shi shiyasa daddy yake purnishing 'dinsa da haka
dan haka sai yace da daddyn
" _ango nake fah yau 'din daddy"_
Dariya suka sanya dukkansu dake wurin inka 'dauke Mahmud da 'yar murmusawa kawai yayi sai shi Abbas 'din da haryanzu hannunsa ke kan kunnansa yana shafawa su ka'dai ne basuyi dariyarba.
Sai da suka gama dariyar sannan daddy ya juyo da kallonsa gurin Mahmud suka sake gaisuwa akaro na biyu shima daddy yasa masa albarka a auren nasa.
Daddy gurin Abbas ya juyo ya kamo hannunsa suka fara tafiya ahankali kamar masu yin wata shawara sai daddy yace masa " _ya akayi kuma na ganka bayan kace babu dama?_
" _Da 'kyar na taho daddy sai da nayi roko tare da cancelling wata tafiya da zamuyi tun aji yan kafin nasamu dama"_
_" amma ba wata matsala_ _ko ?_
Daddyn ya sake tambayarshi
Da _" insha Allah babu komai Daddy"_ Abbas ya amsa mishi tare da fa'din anjima ka'dan ma zan koma.
_"Toh Allah ya tsare ya bada_ _sa'a_ " daddyn yafa'da dai dai isowarsu su daddyn inda suke.
Sallama Abbas yafara yi musu dan afa'darsa cewa yayi zai koma dama wai 'daurin auren ne ya kawo shi.
Abbah ne yace da Abbas 'din wai ko dan bikin ba da'di ne shiyasa zai tafin ,Abbah yace abokin ka ne yace ba zaiyi kowani event ba da 'kyar ya yadda mahaifiyarsa ta shirya yin dinner inajin shi ka'dai za'ayi "
Sai da Abbas ya juya ya kalli Mahmud sai ya dawo da kallonsa gurin Abbahn kafin yace _" ai mu Abbah_ _albarkar auren kawai muke bu'kata"_
Abbahn ma cewa yayi
_"Hakane, hakan ma yayi Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya albarkace ku gaba 'daya"_
_"Ameen Ameen_ _Abbah"_
Abbas ya amsa masa dashi.
*****
Yanda aka tsara wa Teemah kwalliya ba 'karamin fito da ita yayi ba, tayi kyau cikin wani code-less 'din ta blue-green mai kyan gaske da ratsin golden ajiki,'dinkin dai dai jikinta akayi shi, Head, net, bridal shoe and purse 'dinta ma duk golden colour ne sai wani set 'din 'dan kunnan ta na gold da daddy ya sai mata kwanaki, ba'karamin kyau tayi ba, light make-up akayi mata daya 'kara fito da asalin kyaunta afili.
'Kawayenta nata rawar kai amma ita banda ita, ko ajikinta kamar ma ba bikinta akeyi ba, photuna suka yita 'dauka da 'kawayen nata har sai taji tagaji, da ta ga kamar sun dame ta sai ta ce da Hannah su tafi 'dakin Mummy hayaniyar ta isheta haka.
'Dakin mummyn suka tafi suka yi zaman su acan suka bar 'kawayen nasu. Teemah cewa tayi " _wallahi ba dan ina tsoron masifar mummy ba da cire kayan nan zanyi Allah insha iska, duk sun bi sun_ _dameni"._
_" ke kika sani ni dai baruwana idan ta kamaki dan kina cire kayan tafiya zanyi inbarki kinga_ _bata ganni tare da ke bama balle abin ya shafe ni"_
Tsaki Teemahn tayi kawai ta cire takalman dake 'kafarta tana wani yatsina fuska duk da haka sai data 'daga net 'din da aka rufe mata kai dashi zuwa sama.
Hannah tace yauwa bari na 'dauke ki a pic.
Su mummy da Ummah nacan hararabar gidan ta baya inda ake shirya abinci suna ta 'ko'karin ganin komai ya kammala saboda ba'kin daddy da suka zo kuma an riga an gama 'daurin aure shiyasa suke ta hanzari dan suga sun ha'da musu abinda zasu bu'kata.
Lokacin da Abbas ya shigo domin ya gaisa da su Mummyn ya kuma yi musu sallama dan daga nan wucewa yake so yayi be gansu ba shikuma ba son ratsa cikin taron matan nan yake ba takaici yake ji idan ya gansu ayanzu bashi da burin daya wuce yaga ya bar garin Damaturu, yana ganin zai fi jin sassauci.
Koda yashigo bai gansu mummyn ba sai ya ciri wayarsa ya 'kira layinta sai kuma bata 'dauka ba, haka ma na Ummahn sa itama bata 'daga ba.
Hakan yasa da ya shigo kawai sai ya wuche 'dakin Mummyn direct dan zatan shi acan suke tunda bai gansu a babban palourn ba.
Da sallamar sa ya shiga 'dakin Hannah ce kawai ta amsa sallamar yayin da Teemah taji ta wata mummnar fa'duwar gaba ta zubawa 'kofar idanu har ya shigo, shima yana shigowa idanunsa akanta ya fara sau'ka.
Kallon kallo suka tsaya yi wa junansu, Abbas kyan da Teemahn tayi ne ya tafi da imanisa sai yaji wani 'daci azuciyarsa na takaicin dakilin kwalliyar tata.
Tunowa da yayi cewa yanzu fah Fateema matar mutun ce bashi da damar yi mata irin wannan kallon, take sai ya kauda kansa gefe tare da yin istigfari acikin ransa.
Dubansa ya mayar gun Hannah data tsaya tana 'kare musu kallo da mamaki inda ta kasa tsaida idanunta kan mutun 'aya sai juya idanunta take idan ta kalli wannan sai ta dawo ta kalli wannan.
_"Hannah ina Ummah na 'kira layinta bata 'daga ba?"_
Cikin sanyi yai maganar.
'Ko'karin fita daga 'dakin Hannah take yi tare da fa'din " _bari_ _indubo ta"_
Dakatar da jta yayi da fa'din _" a'a '_ _kyaleta ki sanar da ita na wuche kawai "_
_"Bata yi nisa bafa Yayah kuma ma dama tana so ta ganka injita"._
_"Toh sauri ki dabata karki 6ata lokaci "_ Inji Abbas 'din tare nufar wajen window ya tsaya yana kallon waje.
Teemah ma bayansa ta kalla ahankali ta tashi tare da saka takalmanta ta bar masa 'dakin dan bata san me zata ce dashi ba, wani lokaci sai ta ji tarasa 'kwarin gwiwar da har zata iya yimasa magana , ballantana yanzu da taganshi duk yayi sanyi sai taji ya cika mata idanu bazata iya ce da shi komai ba shiyasa ta yanke shawarar barin 'dakin.
Sallama yayi da su bayan Teemah ta'kira Mummyn saboda Ummah abubuwan dake gabanta dayawa, dama Hannah tace ya tsayan ne saboda ta tunawa Ummah fa'da mishi batun sar'kar ta data ke so ya siyan mata itama sai kuma Ummah bata samu daman zuwa sai dai Mummy duk da haka sai da ta tuna wa Mummyn.
Murmushi mummy tayi sannan tace.
_" ki bari bayanzu ba bayan kwana biyu idan ya koma da kaina zan sanar dashi kin ga lokacin_ _taro duk ya 'kare kowa hankalinsa ya dawo jikinsa zai fi_ _fahimta amma yanzu kinga al'amuran jama'ah_ _ko"_ .
_"Hakane mummy amma pls karki manta fah"_
" _Bazan manta ba insha Allahu"_
Duka akan tafiya sukayi wannan maganar daga nan suka yi shiru suka 'karasa 'dakin mummyn inda Abbas yake, Ummah ma ana tasame su bayan tagama abinda ke gabanta.
Abbas yau ko hanyar maiduguri be kalla bakawai ya shiga Tasha ya hau motar Kaduna dan takaici bai ko tsaya ya wuni agidan ba.
Ana idar da sallar azahar alace za'a tafi da amarya saboda yanayin nisa n da gurin ke da shi.
Tun lokacin da Teemah taji labarin tafiyar tafara kuka, hatta sabo shirin da ake sake yimata ma acikin kuka aka yishi har aka gama sai de ba'ayi mata make-up ba saboda hawayenta ya'ki tsayawa.
Daddy da kansaya ratso cikin matan yazo har 'dakin Mummy yakama hannunta izuwa sashen sa. Shi kanshi dadyn dauriya kawai yakeyi amma zuciyarsa ba da'di sam sai dai bazai iya barin hakan ya baiyana afili ba dan baya son Fateemah taga kasawarshi koka'dan, dan haka sai ya zaunar da ita agefensa akan kujera ganin su Daddyn Abuja na 'dakin sai ta zamo ta dawo 'kasa ta zauna tana maici gaba da kukanta.
Mahmud ne yasgigo shima da sallamarshi dan Abbah ne ya'kira shi awaya yace yazo nan'din yanzun nan shiyasa ya taho.
Dukkansu aka ha'da si aka yi musu fa'da sosai akan rayuwa Abbah ne yafara nasa akan kyautata mu'amala sai Daddyn Abuja yayi nasa akan tsoron Allah da bin dokokin sa azaman takewarsu, Daddy ne yayi daga 'karshe inda yaja hankalinsu akan ha'kuri da kaiwa zuciya nesa, Sosai nasihohin nasu suka ratsa su Teemah sai kuka takeyi harda shashshe'ka.
Dasuka gama ne Abbah, Daddyn Abuja harma da Mahmud 'din suka tafi suka bar 'dakin domin zuwa fara arranging yadda tafiya da amaryan zai kasance aka bar Daddy da Fateemansa ka'dai.
Dawowa tayi da kanta akan cinyar Daddyn ta kwantar dashi tana mai cigaba da kukanta.
Daddy sai ya fara bubbuga mata kai 'din ahankali alamar rarrashi tare da fa'din _" Haba_ _Daddy's Angel stop crying mana"!_
Cikin kukan tace
_"Dad...dy ni bana son in....tafi inbarku, bana son......auren Da...ddy "_
" _Kiyi ha'kuri Fateema!, aure dole ne zakiyishi, ko bakiyi yanzu ba dole watarana sai kinyishi ko dan cika sunnar ma'aiki sallallahu alaihi wa sallam (S.A.W), balle ma yanzu ke da kike tare da yayanki Mahmud, ga Antyn ki, ga Abbahn ki ma duk akusa dake, ai can 'dinma kamar gidane, karki damu kinji"_
Cikin shagwa6a tace
_" a' a ni Daddy nan nakeso"_
_"Toh shikenan kiyi shiru, zanje kwanan nan inkun tafi sai dai bazan gaya miki ranar ba, zanje amma idan naga kina kuka da rashin ji kullum toh bazan dawo dake gida ba, idan kuwa bakyayin ko 'daya daga ciki kika kwantar da hankalinki kika zauna da mijinki lafiya kika yi masa biyayya toh zan 'dauko ki in kawo ki gida kiga mummyn_ _ki kinji"._
Da kai ta amsa masa alamar taji.
Sai yace _" yauwa_ _my Angel share hawayen ki toh karki sake yin kuka"_
Share hawayen ta tayi harama da murmushi sai Daddy ya'kira mummy awaya yace zuso su tafi da ita.
Suma su mummy nasiha suka mata sosai sai dai Mummy kasa ri'ke nata hawayen tayi daga 'karshe ma kasa magana tayi dan yanda kuka yaci 'karfin ta.
Kusan duk wa'danda suke wurin sai da suka share hawaye dan ganin yanda Mummyn ke kuka.
Baranma Teemah data ji mahaifiyarta na kuka ai shikenan, da sauri tatafi jikin mummyn ta rungumeta tace " _Mummy ni bana so intafi inbarki.......mummy tunda ba...kyaso nima ba zanje ba"_
Kuka take tana maganar yayainda tausayinta ke 'kara cika zuciyar mummyn kamar tace Teemah bazata ko'ina ba, kamar tace babu inda yarta zata, karo na farko kenan da Teemahn zatayi doguwar tafiya batare da ita ba , she can't bear the pain, bazata iya jurewa ba , tayaya bazata tausayawa yarinyar da tsawon rayuwarta bata yishi batare da iyayenta ba,dai dai da rana daya bata ta6a kwana a inda ba mahaifiyarta ba sai gashi kwatsam zata tafi inda zai dauke ta tsawon lokaci kafin sugana. Kai Mummy ta dagata sama tace _" Allahu ga amanar ka nan Allah ka kula min da ita ka kareta daga sharrin masu sharri ka kareta daga dukkan abin kii!"_
Dai-dai nan Daddy ya shigo da niyyar sanar da su cewa angama komai lokacin tafiya tayi, sallamarsa ma bai 'karasheta ba ganin irin abinda ke faruwa a'dakin.
Cikin tsawa yace " _menene kuma haka Khadija_? _Yazakisa yarinya agaba kina aikin kuka inabaso kike ki karya mata gwiwa ba ?"_
Bai jira ji, cewar kowa ba ya 'karaso yaja hannun Teemahn yatada ita tsaye, _" tashi_ _mamana kyalesu ba mun gama magana ni da ke ba, meyasa zaki zo nana kuma_ _kina_ _kuka ?_
_"Daddy kuka_ _mummy takeyi_"
Baiyi magana ba kawai yaja hannunta suka bara 'dakin daf da 'kofa yatsaya yace _" mai_ _niyyan tafiya ta fito motoci na ready"_
Yayi maganar batare da ya juyo ya kalle su ba yana gama fa'da kuwa yasa kai yafice hannunsa ri'ke dana Teemahn.
Da kansa yahe yasanta amota,Ummah ne tazauna agefenta 'daya yayinda wata 'kanwarsu daddy da suke cousins tazauna 'daya gefen, Hannu da waus 'kawayen Teemahn su biyu suka zauna awata motar daban .
Mummy ko gurin tafitar ba ta fito ba ita kam tana ciki kawai tana jimamin rabuwa da 'yartata tana so ta tashi ta ko leke su ta window ma takasa ji tayi ga6o6in ta duk sun mata nauyi aranta sai take jin tamkar ta rabu da Teemahn nata ne rabuwa ta har abada, tana jin dirin tashin motocin kawai sai ta rintse idanun ta.
Basu tsaya ko'ina ba sai a Airport na Maiduguri inda daga nan suka hau jirgi sai garin ikko (LAGOS).
*****
Zaune acikin mota shiru ko wanda ke gefensa be kalla ba tunda ya shiga motar tunani ya sako shi agaba, tunanin yadda kunnan sa suka jiyo masa 'daurin aure tsakanin
" MAHMUD YUSUF MUH'D da Fateemah, yanaji yana gani aka 'daure sunan Fateema da waninsa, bashi ba.
Har suka isa kaduna babu wanda yako samu kallon arzi'ki acikin motar daga gurin Abbas, yana sau'ka ya tari adaidai ta yayi drop zuwa _Barrack 44_ dake cikin kadunan
inda Saleem abokinsa yake.
*Wash........*
*Naso yafi haka amma wallahi ansamu akasi, Please ayi ha'kuri da wannan* *insha Allahu zuwa gobe zakujini*
_Ina Team Mahmud ina jira daga gareku , idan naga sharhi ruwa-ruwan ta insha Allahu I_ _ll not fail_ _you agoben_ _zakujini idan muntashi cikin rayayyu._
_Team *ABBAS* ina kuke kuma 'din ku matso domin Abbas yace ayi muku albishir da new_ _catch 'din da_ _zai muku._ π
*Much luv MUTANE NAHπ da sauran drama fah agaba* .ππ»
*Keep following me* ππ»
ππ»
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerhn ku ce* π
[10/2, 6:02 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_This page is specially dedicated_
_to CAPTAIN ABBAS FANS 1&2 your comments always drive me crazy Allah ya barmin ku._ π
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
_Dreams are like starsβ¦....you may never touch them, but if you follow them they will lead you to your destiny._
π
Ώ *53*
Agidan Anty akayi musu masau'ki inda Anty ta matu'kar bawa kowa mamaki, sau'ka tayi musu na mutunci da karramawa tamkar ba ita ba.
Anty da wasu 'kawayenta 'yan bani na iya da suka yi ruwa suka kuma yi tsaki abikin sune zazzaune a palour suka tari amaryar Mahmud 'din.
Bayan gaishe-gaishe da ban gajiya sai su Ummah suka mi'ka amanar amarya Teemah ahannun Anty inda Anty ta matu'kar nuna vajinta wurin kar6ar amanar harma ta nuna musu ai bakomai duk 'daya suke tace ai itama amaryar 'ya ta ke agurina, mu'karraban Antyn kuwa cewa suka yi wai su Ummah su kwantar da hankalinsu domin amanar su ta kar6u sai fatan Allah ya bada zaman lafiya mai 'dorewa, mutane nata amsawa da Ameen,Ameen Anty kuwa acikin ranta ta ce _" ba Ameen ba, can da su gada gayyar tsiya Allah ya tarwatsa"_!!!
Har su Ummah sun mi'ke zasu tafi masau'kin su sai wasu daga cikin mutanen Antyn suka ha'da bakin cewa su basu ga fuskar amarya ba gaskiya abu'de mata fuska su ganta.
Murmushi Ummah tayi tare da umartan Hannah data bu'de mayafin Teemahn.
Ahankali Hannah ta matsa jikin Teemahn dan ita iyayin wa'dannan matan yafara isanta.
'Daga lullu6in tayi ahankali kamar mai tsoron ta6awa sai data dangana shi da saman kan Fateeman kafin ta barshi.
Dukkan su sun yaba da kyaun amaryar hatta Anty sai da ta yaba da amaryar Mahmud 'din dan ta jima bata ga yarinyar ba tun tana 'yar 'karama, tace ashe Khadija harta haifi 'yah kamar wannan?!
Sosai suka yabi kyau da tsariwar amaryarta su dan duk munafurcin ka baka isa ka kushe kyaun Teemah ba ballantana kuma an ha'da da kwallliya da 'kyalkyalin amarci.
Dai-dai nan Anty Chiddy ta shigo dayake taje gida bada jimawa da niyyar daman zata dawo sai kuma aka samu akasi kafin ta dawo har amarya ta iso, tana shigowa kuwa idanunta ya sau'ka akan fuskar amaryar.
Anty Chiddy kam baki ta sake tana kallon inda tsagwaron kyawun halitta yake, sosai tayaba da Teemah har aranta, tace kamar daga indiya tazo yanayin shiga da kwalliyarta shigen taau ce, banbancin ta au ka'dan ne sai dai su nuna mata hasken fata ita kuwa 'daurin kai zata nuna musu domin 'daurin da akayi mata ba'karamin zanuwa yayi ba, indiawa kuwa basu 'daure kai irin namu na Naija .
Take taji masifar son yarinyar yashige ta karaf 'daya, a hankali ta tako ta iso ta samu gurin zama ta zauna itama tare a zubawa yarinyar idanu.
Hannah rarraba musu idanu taringa yi jin yadda kowa ke fa'din albarkcin bakinsa akan Teemah, haka taringa binsu da idanu tana kallon su itama, garin 'kare musu kallon ne idanunta ya kai ga Anty Chiddy data zubawa Fateemah idanu kamar zata cinyeta 'danya, kallon kallo tayi atsakanin Fateema da Anty Chiddyn sai data 'kara tabbatar wa idanunta inda Anty Chiddyn ke kallo sannan ta buga uban tsaki tare da ha'de rai kamar anzagi wani nata ne, jan mayafin tayi ta maida shi ta rufe fuskar Teemahn sannan tasake 'dagowa karaf sai suka ha'da idanu harara Hannah ta banka mata tare da murgu'da bakinta aranta tace _" aniyar_ _ki ta biki inma maita ce dake dan mu jinin mu tamkar acid yake sai gani sai hange sai ta Allah bade ta mutun ba, mutun 'dinma irinku, daga ganin tama arniya ce wannan, tawani baza attachments kamar mahaukaciya....mthewwww "_ ta 'karashe da jan tsaki.
Anty Chiddy kam gurin Anty ta nufa ganin an rufe fuskar data ke kallo 'din, sai data kai kanta kusa da kunnen Anty kafin ta furta _" your_ _daughter in-law is so beautiful"._
('Kalubale na farko)
Anty murmushi kawai tayi mata dan hankalinta naga matar da taga ta mi'ke tana 'ko'karin tada amarya, Ummah ce tace mata zasu wuche masau'kin su saboda suna da uzirirrika ciki kuwa harda sallah da basuyi ba, lokacin anyi suna kan hanya.
Kamar gaske gmsu Anty suka bisu da godiya da kuma fatan alkhairi sannnan Anty tasa aka kaisu 6angaren Mahmud tare da sawa aka wadatasu da dukkan wani abin bu'kata domin anan aka shirya tar6ar amarya ayau 'din har se an'kare hidiman gobe kafin asada ta da gidan mijinta na ainahi.
Bayan fitar su Ummah ne Anty da mu'karrabanta suka zauna maida zance akan amaryar da danginta inda suka yabi na yaba tare da kushe abinda suka ga be musu ba, Anty kanta aranta cewa tayi " ha'ki'ka Mahmud yayi dacen mace kyakyawa da kyakykyawan asali, sai de hakan bazai hanani cin uban yarinyar ba, har se da kanta ta nemi saki daga gurin mijin dan neman sassauci, dama tajima da yin wannan al'kawarin tace sam babu zancen zaman aminchi tsakaninta da dangin miji, afa'darta wai duk munafukai ne, auren ma na 'daya daga cikin munafurcin nasu saboda sama taka taji wai za'a yi aure tsakanin Mahmud da 'yar Kabiru (Daddy) batare da anyi shawara da ita ba ko kuma a tambayi ra'ayinta ba, dan anga yaronta mai hankali son kowa 'kin wanda yarasa shine aka li'ka masa ita daga zuwa bautar 'kasa agarin dan haka itama sai inda 'karfinta ya 'kare bazata ta6a amincewa dasu ba itama _shege ka_ _fasa._
Washe gari ma tun kafin wasunsu su gama tashi a bacci har breakfast ya iso su mai rai da lafiya, inda akaiyshi kala daban daban kusan kala uku sai wanda yayi maka zaka za6a kaci.
Ta wannan fannin sosai Anty tayi 'ko'kari dan tun zuwan su basu nemi komai sun rasa ba agidan, sau da dama ma tun kafin su nemi abu ake bayyanar dashi agabansu, su Ummah sun matu'kar yabawa da karamcin Antyn hankalin su sam be tashi ba Ummah bata damu ba koka'dan tatafi tabar Teemah da tunanin zata samu farin ciki da yardar ubangiji, tunda ita bataga wani abu na daban daga mahaifiyar Mahmud ba har ma sai taga kamar tsoron da Mummy kullun take anbata wata kila hasashen ta ne kawai dan ita ko ka'dan bata ga haka daga Antyn ba, bataga alamar komai ba.
Ummah da sauran manyan matan ne suka wuche aka bar Teemah da 'kawayen domin yin shirin dinner, inda already Anty tariga ta shirya komai hatta 'yan mata sai data kawo wasu daga 6angarenta inda suka ha'du da sauran 'kawayen Teemah sai suka bada ma'ana instead of su hu'dun da suke dukda amaryar.
Kaya da zasu saka duk Anty ta tanadar musu gaba 'daya hakama amarya dan wani kaya ta 'dinka mata mai kyau da tsada pitch colour da Teemah tasa kuwa ba'karamin fito da ita yayi ba, Hannah ce tace sai dai Teemah tasa wannan set 'din earings da Abbas ya kawo mata 'dazu acewarta zaifi fito da ita.
Ammah sun nema acikin kayan sa suka zo dashi basu samu ba ashe mummy ce ta6oye bata bari yabiyo kayansu ba tace daga zata bawa Daddyn ta ya kaimata.
Dole tasa wanda Anty ta ha'do dashi shi'dinma mai kyau ne yafi 'karfin kushe.
Ummah na isa gida Abuja ta nemi layin Mummy tasanar da ita irin kar6ar mutuncin da Mahaifiyar angon tayi musu tace gaskiya sai de su godewa Allah domin ita sam bata ga wata matsala atattare dasu ba tace may be Allah ne yashiryeta tun ma kafin Teemahn tazo, mummy ba'karamin da'din hakan taji ba, sosai canjawar Antyn yabata mamaki matu'ka, dama burinta kenan, burinta taga 'yarta tasamu farin ciki agidan auren ta, dama ita ba Mahmud take gudu ba halin mahaifiyarsa ne yake yawan sata damuwa, yanzu kam sai de tace " _ALHAMDULILLAH_" tunda Antyn ta sau'ko.
Tun daga lokacin da Mummy tasamu labarin meke faruwa sai ta warawre walwalarta ta dawo dukkan damuwarta ta kau , dama abinda ya dame ta kenan kuma yanzu taji good news akai so no more worried.......
Zakayi mamakin yanda event centern ya 'dinke da jama'ah kuma duk Anty ce ta gayyato su musamman dan suzo su kwashi shokky.
Ai kuwa ba 'karamin cashewa akayi ba awurin dinner 'din, Mahmud kuwa 'kin zuwa yayi ballantana abokansa, sai gurin yakasance mata zallah ne agurin babu maza sai 'dai'daiku hakan sai ya maida dinner 'din ya riki'de ya juya izuwa mother's night.
Teemah duk inda ta juya walwali takeyi kuma idanun Anty Chiddy 'kur akanta har mantawa takeyi da abinda akeyi agurin idan ta tsaya kallon Teemah.
Idan kuwa akace Teemah na tsakiyar fili itama bata iya zama, fitowa takeyi ta bu'de bakin jaka tayi zazzaga mata li'ki wanda hakan sai yazama na tamkar gasa kowa yafara 'ko'karin ganin ya nuna tasa bajintar, hatta Munira ma ba'a barta abaya ba dan itama da ita akayi komai agurin taron haka kuma tayi ta zuwa tana watsa wa amarya li'ki wanda garin yin li'kin ne ta samu ta ha'da ku'din da wani hatsabibin maganin dake hannunta ta watsa asaman kan amarya Fateemah, duk kuwa maitar mutn bazai ta6a fahimtar abinda yafaru agurin ba, tana gamawa kuwa ta koma tayi zamanta tana dariyar mugunta tun daga nan bata 'kara tashi ba har taron ya watse domin tariga tagama abinda ya kawota.
_('Kalubale na biyu)_
Fateemah na tsakiyan jama'ah tafara jin kanta na matsanan cin sarawa sai ta dafe kan nata jiri na neman kadata, Hannah ce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 67