ko kuma wani abu dai daban da shi baida ikon d'aukan mataki amma sai kuga rashin goyon bayan iyayen da kuma rashin tsayawa mu fahimci 'ya'yanmu da kyau sai kuga abu yazo ya lalace sai daga baya kuma azo ana dana sani wanda ta kansance k'eyace bata kuma ta6a dawowa gaba, koda abun ba haka yakeba yi k'ok'ari dai ki fahimci y'ay'anki kodan gyaran kuskuren da ba'ason ma ya auku idan kuwa ya aukun matuk'ar wahalan gyara ne dashi.).
Teemahn kuwa cewa tayi
"Mummy kullun fah cewa yake ni incinye abincin wallahi kokad'an bayaci shi, kuma kona k'oshi sai yace dole sai naci in bahaka ba wai harbeni zaiyi"
Mummy dataji haka take ta sauk'e ajiyar zuciya, sai tayi istighfari aranta akan tunanin daya d'arsu azuciyarta d'azun, wani sanyi ne taji azuciyarta tare da wani nutsuwa dan sai yanzu taji dama-dama.
Amma sai ta wani had'e rai tace "zoki wuce ki dubo min yarona ni banason shashanci"
Wani kukan tasake sanyawa tajuya da nufin zuwa duboshin kenan sai wayar mummyn yafara ringing.
Tsayuwa tayi cak dataji mummy na fad'in " au kaine?
"Naga sabuwar number ne"
Okay ba matsala ai, amma lafiya kuwa?
toh shikenan za'a kawo d'in"
Abinda mummyn tafad'i kenan daga d'aukar wayar zuwa ajiyeta.
Hakan yasa Teemah tagane da Abbas mummy tayi wayar kenan.
Bata juyo ta kalli mummyn ba haka kuma bata cigaba da tafiyan ba sai ta sake jiyo muryar mummyn na fad'in " zo Teemah ki had'a abincin ki kai masa kinji"
"Dawowa tayi ta wani tura baki kana ganinta kasan aiken ne bata so duba da yanayin data koma gaba d'aya ta wani canja.
Sai mummy tace mata " wai ni da kike ta wannan abin so kike ni nakai ne ko yayah"
Sai Teemah ta jijjiga kanta ahankali alamar "a'a.
" Toh wa kike tunanin zai kai masa idan bake d'in ba?"
Sai tace " ga baba mai gadi ko kuma ak'irashi awaya mana mummy ya dinga zuwa yanaci da kansa"
" Ai yau d'in baijin dad'i yace shiyasa"cewar mummyn.
"Ai kullum haka yake cewa mummy"
" nidai kiyi sauri "
Teemah kuwa haushi sai ya hanata yin wata magana dan tasan bawani rashin jin dad'i da yake saboda tasan halinsa yanzu tana zuwa zai fara wani bubbud'awa da iyayi dan ya ganta k'arama afad'arta, duk da yau d'in tanajin yunwa sosai amma ita ba agurinsa taso taci ba tafiso taci atare da mummy zata fi ci a nutse amma shi nashi harda na haramun yake sata taci (injita nefah amma)π€£
Had'a abincin tayi ta kai masa d'akin nasa amma yau d'in sai tayi sa'a dan cewa yayi tare zasuci dashi, sai ya bata mamaki daya fad'i hakan har sai da ta d'aga kai ta kalle shi sai ya d'aga mata gira d'aya sama, aranta tace
"dama ai nasani bawani rashin jin dad'i kawai so yake yaga nazo ya wulanka tani abanza"
Tare suka fara cin abincin dashi sai kawai take jinta wani iri dan abun ban barakwai ya mata saboda tunda ya zo garin nan hakan bai ta6a faruwa atsakaninsu ba.
Dayaga ta tsaya bata ci sosai sai ya d'iba yakai mata bakinta ita kuwa batayi wani musu ba kawai ta bud'e baki ta kar6a taci.
Daganan yace mata sudinga d'iba atare dan bayaso yaga ta tsaya batare da taci abincin ba.
Ahakan kuwa har suka gama ci gaba d'aya sai ta tattaro ta dawo da plates d'in kitchen, yau d'in dai da d'an sauk'i batajita a sama ba dan yau d'in ya tayata cii bakamar na baya dayake sata ci ita kad'ai ba.
*****
Wata ranar laraba da azahar tana parlour akwance har aka idar da sallah tanaji gaba d'aya kasantuwar tana fashin sallah yasa bata tashi taje tayi ba, sai ta mik'e kawai tanufi d'akin Abbas dan tasan yana masallaci adai dai wannan lokacin.
Ahankali ta tura k'ofar tashiga idonta baikai ga kan doguwar kujeran dake d'akinba gado kawai takalla dataga wayam shikenan dayake tariga da tasa aranta yana masallaci ne shiyasa bata wani damu da ko yana d'akin ko bayanan ba ita dai oho.
Zuwa tayi bakin gadon ta zauna can kuma sai ta tashi ta nufi gaban madubin dake d'akin, turarensa tafara d'auka dan dama turaren ba k'aramin birgeta yake yiba musamman idan taji ya fesa ajikinta feffeshe jikinta dashi tayi itama dukka sai data fesa turatukan nasa sannan tajawo stool ta zauna sai ta buga tagumi agaban madubin tunaninta ya tsaya cak dan yanzu jitake kamar Yah Abbas kar ya tafi.
Tun shekaran jiya dataji suna maganan komawarshi da Daddynta tarasa meke damunta.
Bata so taji wai zata yi missing d'insa irin yanda tayi missing Yah mahmud dan shi Yah Abbas ba sonta yake ba, amma ga mamkinta sai taga tagagara samun natsuwa gaba d'aya.
Ko yanxun ma ita kanta bata san me yakawo ta d'akinsa ba jitayi kawai tana sha'awar shigowa d'akin.
Shikuwa yana kwance yana ta kallonta da mamakin abinda ya kawota d'akin nasa.
Dayaga hankalinta bai zo gareshi ba ne yagane cewa tayi zaton baya d'akin ne shiyasa ta shigo.
Akwance yake shima tun d'azu, duk ya rasa sukuni yana ji aka k'ira sallahn har aka idar amma bai motsa ba,for the first time yayi missing jam'i tunda ya girma ya san kansa.
Dayaji anyi sallama ne kawai ya yanke shawarar cewa zai bari kawai ya watsa ruwa idan yaso kawai sai ya fita gaba d'aya daganan sai yawuce shagon barbing amar aski da gyaran fuska.
Toh yana kwancen ne sai yaga shigowar Teemah cikin d'akin.
Ita kuwa tana zaune agaban madubin kusan mintina takwas sai kawai ta mik'e tsaye da nufin ficewa daga d'akin dan kar ya dawo ya sameta yaci k'aniyarta.
Fara tafiyan datayi kenan dayake tana rarraba idanu ad'akin sai ta hango shi kwance akan doguwar kujera tsoro yaso ya kamata amma koda taga kamar yana bacci ne sai ta dake ta wani tsaya k'arewa fuskarsa kallo.
Gani tayi yayi mata kyau sosai a yanda yake d'in,take sai tunanin waccen yarinyan yazo ranta wato _Muhibbat_ take sai taji ranta ya 6aci atunaninta itama taga kyan nan dayayi sai ta fara d'aga k'afanta ahankali-ahankali harta tsinci kanta tsaye gaban kujerar dayake kwancen.
Tsayinta ta rage tayi k'asa ta tsugunna daidai yanda kujerar take.
Cigaba tayi da kallonsa sai taji kamar tasashi acikin jaka kar ya tafi yabarta amma tasan inah no way.
Har ta d'ago hannu zata kai kan fuskar tasa sai kuma take fuskar muhibbat ya bayyana mata a idanu dai-dai sanda tafito daga gida ranar daska je dashi d'innan, fuskar _Muhibbat_ d'in k'unshe da murmushi har ana hango wushiryarta, tuna hakan ne yasata ta maida hannun nata k'asa dan wani sabon 6acin rai ne taji ya lullu6eta.
Take ta mik'e kamar an bata umarni bata kuma tsaya wata-wata ba ta fice daga d'akin ta nufo nata d'akin.
Sai da yaga ta fita kafin ya bud'e idonsa yabi k'ofar data fitan da kallo.
Mamakinta yaji dan duk abinda ta aikata yana kallonta itace kawai tayi zaton bacci yake, abinda yake zuciyarta ne kawai bai sanda shi ba sai kuma yanda yaga tafita d'akin da zafi-zafi da kuma had'e rai wannan ma bai san manufarsu ba.
Idansa kawai ya bud'e bayan ya gama tunanin kuma yasake kulle su baiyi zaton zata dawo ba amma cikin ikon Allah kwata-kwata bai san dalilin daya sa yagagara motsi ba dan koda d'an yatsansa bai motsa ba murmushi kawai yayi sai ya sake maida idanun ya kulle su.
Cikin haka ne yaji an sake bud'e d'akin an shigo bai wani damu yasan wanda yashigo d'in ba dan baya raba d'ayan biyu itace tashigo jin babu alamun sallama daga bakin mai shigowar.
Ita kuwa kansa tazo ta tsaya hannunta rik'e da robar hair removal cream.
K'asa ta maida idanunta daga gefensa ta k'asa.Tunani takeyi a zuciyarta dan gani take wannan abin da take shirin aikatawan kamar ba dai-dai bane.
Shikuwa hakan da tayinne yabashi chance d'in ganin abinda ke rik'e ahannunta batare da tasan yana kallont ba.
Ahankali ya maida idanunsa ya lumshe bai bari ta lura da bud'e idanun dayayi d'in ba.
Muje zuwa fans,Teemah fah zata yo rigima ananβΊ
_Vote, share and_ _comment pls_ π€π»
*Salmerhn ku ce*π
[10/2, 5:58 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ π
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
π
Ώ *25*
Tayi tsayuwan mintina yakai hud'u tana tunanin tayi abinda zuciyarta ke raya mata ne ko kuma kartayi.
Kawai sai ta yanke shawarar data ga yafi kwanciya mata azuci......musamman idan ta tuno irin muguntar daya ke yimata da masifah ga kuma _Muhibbat_data mata karan tsaye itama azuci.
Sai take ganin ai idan bahaka tayi masa ba bazata rama abinda yake mata ba.
Dawo da kallonta tayi kan fuskarsa sai taga har yanzu baccinsa yakeyi bai ma san tana tsaye akansa ba.
Kamar wata mai hankali haka ta tsugunna agabansa ahankali idonta na kansa tafara matso mai d'in, koda ta matso sai ta tsaya kallon hannun nata, jin wani kuzari tayi yazo mata farat d'aya ai kuwa batare da wani dogon tunani ba tafara shafa masa man afuskarsa gaba d'aya duk gurbin data ga akwai gashi (beard) sai da tabi tashafa shi.
Shikuwa mamaki ne yaci kasa dayaji abinda take yi masa a fuskarsa, saboda ko lokacin daya ga abin rik'e a hannunta baiyi tunanin shine target d'inta akan abin ba.
Sosai yayi mamakin hali irin na Teemahn da ko da wasa bai ta6a tunanin rigimarta har ta kai haka ba.
Sai yanayin rashin tsoro da kuma k'warin gwiwarta akan abu yaji ya birgesa, duk dama ga dukkan alamu kafin ta aikata hakan sai da tayi d'an nazari akai, duba da yadda tayi tsaye akansa batare da wani dalili ba hakan yana nuni ne da cewa tana jin tsoro, amma still tsoron bai hanata aikata abinda zuciyarta tariga ta sak'a mata ba.
Teemah kuwa harda cije baki sanda take shafawan dan ita a tunaninta idan ta gama shafawa sai tayi tafiyarta ta barshi so ko ya tashi daga baccin ba zaiyi tunanin ita ce ta aikata masa ba.
Sake matso manli d'in kuwa tayi dayawa ahannunta tafara shafawa amma tana cikin shafawan sai taga ya bud'e idanunsa ras akanta, " yah subhanallah" tace ahankali garin janye hannayenta cikin gaggawa kuma sai ta d'an goche hannun ya shafu a goshinsa, dayake bawani gashi mai yawa bane akannasa sai mai d'in yayi saurin ratsawa har k'asan gashin.
Sa ke lumshe idanu yayi yace " yah salam" dan ya riga yasan ba k'ara min aika-aika tayi masa yau d'in nan ba.
Da sauri ta mik'e tsaye zata gudu shima kuma kamar yasan hakan zai faru sai ya sake bud'e idanunsa sai ko ya ga tana shirin guduwa,sai ya mik'e da sauri ko taku hud'u batayi ba taji anrik'o hannubtaShikuwa mamaki ne yaci kasa dayaji abinda take yi masa a fuskarsa, saboda ko lokacin daya ga abin rik'e a hannunta baiyi tunanin shine target d'inta akan abin ba.
Sosai yayi mamaki hali irin na Teemahn da ko da wasa bai ta6a tunanin rigimarta har ta kai haka ba.
Sai yanayin rashin tsoro da kuma k'warin gwiwarta akan abu yaji ya birgesa, duk dama ga dukkan alamu kafin ta aikata hakan sai da tayi d'an nazari akai, duba da yadda tayi tsaye akansa batare da wani dalili ba, amma still bata ji tsoron yi masa abinda zuciyarta tariga ta sak'a mata ba.
Ita kuwa harda cije baki sanda take shafawan dan ita a tunaninta idan ta gama shafawa sai tayi tafiyarta ta barshi so ko ya tashi daga baccin ba zaiyi tunanin ita ce ta aikata masa ba.
Sake matsowa tayi dayawa kuwa tafara shafawa amma tana cikin shafawan sai taga ya bud'e idanunsa ras akanta, " yah subhanallah" tace ahankali garin janye hannayenta cikin gaggawa kuma sai ta d'an goche hannun ya shafu a goshinsa daya bawani gashi mai yawa bane akai d'in sai mai d'in yayi saurin ratsawa har k'asan gashin.
Sa ke lumshe idanu yayi yace " yah salam".
Da sauri ta mik'e tsaye zata gudu shima kuma kamar yasan hakan zai faru sai ya sake bud'e idanunsa sai ko ya ga tana shirin guduwa, sai ya mik'e da sauri ko taku hud'u batayi ba taji ya rik'o hannunta d'aya, okda ta gwada ja kuwa sai tajita k'yam dan dolenta ta waigo ta kalle shi, suna had'a idanu sai tayi k'asa da kanta.
Shikuwa jan hannun tan daya kama yayi batare da yayi magana ba yajata zuwa gaban madubi suka tsaya awurin, kallon kansa yayi acikin mirror d'in sai ya maida idansa kanta, gani yai idanunta na kallon k'asa a hankali ya k'ira sunanta " _Fateemah_".
Ciki-ciki ta amsa da " na'am" batare da ta d'ago ta kalleshi ba dan tasan yau d'innan mai raba su sai Allah, ita sam bataso yatashi yanzun ba taso sai bayan tagama abinda zatayi tatafi kafin ya tashi amma sai ya 6ata mata plan yatashi da wuri.
" D'ago ki kalleni"
Ta sake jiyo muryar shi yafad'i haka.
Amma sai ta gagara aikata yanda yake so d'in sai ma ta k'ara yin k'asa da idanunta.
Cikin tsawa ya sake cewa " nace ki d'aga kanki ki kalle ni ko!"
Take jikinta yafara 6ari cikin idanunta yafara tara hawaye.
Tsura mata ido yayi yana kallonta batare da ya sake magana ba itanma a hankali tafara d'ago idanunta yayin da ruwan dake cikin idanun suke k'ara yawaita.
Da farko lokacindata fara d'ago kai d'in idonta a bud'e yake amma data ga tana gab da d'agowa gaba d'aya sai tayi saurin rintse idanun take kuwa hawayen daya taru a gurbin idanun ya gangaro zirr ya jik'a kumatun ta.....ahakan ta k'ara sa d'agowa takuma k'i bud'e idanun nata.
Tsayawa yai yana kallonta da kyau, a kullum gani yake yarinyar na k'ara yin kyau ne tafiya take da imaninsa da kuma tunaninsa gaba d'aya.
Kusan mintina uku babu wanda yayi magana a tsakaninsu illah jikin Teemah dake ta faman 6ari dan yau tasan tashigo hannu sai yanda Allah yai da ita abanza ma yaya balle ta aikata laifin azahiri.
Ganin yanda jikinta ke karkarwa ne yasashi murmushi aransa yace " halin yarinyar nan sai ita, ga uban tsoro ga kuma fitina da neman magana".
Sai kuma yaji ta bashi tausayi sosai sai ya tsurawa crying face d'in nata idanunsa shima na tsawon sakanni bai d'auke idanun san daga kallon fuskarta ta ba yace " open ur eyes"! Atsare yayi maganar amma bada zafi ba.
Duk da tana son bud'ewan amma sai ta gagara bud'ewa saboda tsoron yanayinsa dazata gani takeyi, shikuwa da ya ga bata da alamun bud'ewa sai ya sake maimaita mata " I said open ur eyes Fateemah"
Wannan karan ma asanyaye yayi maganar.
Ita kuwa jin yana yi mata magana da muryar rahama sa6anin yanda ta zata da farko sai hakan yasa ta jin d'an sanyi-sanyi sai ta bud'e idanun kamar yanda ya buk'ace dayi.
Cak idanun nata suka sauk'a a cikin nasa tana niyyar sauk'e nata idan ne yayi saurin dakatar da ita da d'an k'arfi..." don't try it!"
Dan dolenta itama ta bar idanun tan akan san duk da yanda take jin bugun zuciyah aduk lokacin data had'a ido dashi, amma haka ta daure batare data so ba.
Tambaya taji ya jefa mata amma sam ta kasa bashi amsar tambayar tashi saboda kwata-kwata ita bata ma san me zata ce dashi ba koda ta bud'i bakinta.
Sai tayi shiru kawai tana rarraba idanu, ganin tayi shirun shikuwa sai ya sake maimaita mata tambayar kamar yanda ya fad'i da farko batare daya canja ko kalma d'aya ba " me yasa kika shafa min nace"!
Wannan karon ma a nutse yayi tambayar sai hakan da yayi yasa taji kusan 40% daga cikin tsoron data ke ji d'in ya kau.
In-ina tafara sai yayi saurin dakatar da ita da jijjiga kansa.
Hannu ya sa ya kamo fuskarta ya d'ago saitin fuskarsa suna kallon juna " then tell me now" Ya sake fad'i.
Ita kuwa sai tak'i magana sai ta sake jin jikinta wani iri tsoronsa ya k'ara kamata ga kuma bugun zuciyarta dake k'ara yawaita, zuwa yanzun koda tace zata yi masa magana toh bata san me zata ce masa ba domin bakinta kansa yayi mata nauyi.
Da yaga bazata yi masa magana ba sai ruwan hawayen ta dake matuk'ar ta6a masa zuciya, sai ya sake mata fuskarta ta ya mik'e tsaye singlet d'in dake jikin sa kad'ai ya cire sai ya dawo inda take ya kama hannunta ya fara tafiya da ita.
Bata yi turjiya ba tunda tasan itace da laifi sai kawai tabisa.
Shikuwa bayi ya nufa da ita,koda taga yana niyyar shigar da ita bayin ne sai ta d'an turje, juyo yayi ya bata wani dirty look take kawai ta d'aga kaf'afu tabishi.
Shahada tayi ta bishin duk da bata san mai zai biyo baya ba sai kawai ta rink'a addu'a azuciyarata akan cewa Allah ya ubangiji ya d'ora ta akansa Allah ya ku6utar da ita.
Suna shiga bayin yayi zamansa akan wani stool da ke ajiye musamman acikin bayin.Sai yace mata " bismillah k'arasa aikinki".
Bata gane mai yake nufi ba amma dana haka sai taja tayi tasaye tana wasa da yatsun hannunta.
Tsawon mintina sai yakuma fad'in "banaso idan ina ma mutun magana ana shareni ki kula sannan kuma warning naki na k'arshe kenan"
Haryanzu bata fahimci mai yake nufi da bismillan ba amma tsab ta fahimci warning d'in daya mata kawai dai bata san mai zata yi ba ita.
Shi da kansa ya fahimci bata gane manufarshi ba sai yace mata " ni nace miki ina buk'atar aski ne ko shaving?"
Sai ta jijjiga kanta alamar " a'a"
" Ni nace ki shafa min mai jikina?"
Nan ma jijjiga kanta tayi.
" Ni sa'anki ne agidan nan?"
Harta fara jijjiga kai sai taji ya daka mata tsawa inda yace open your mouth and talk to me or are u deaf?"
Da sauri tace " umm-umm"
Dan gani tayi take ya juye mata tamkar mayak'i idanunsa taga sunyi jajir.
" Raini ne kenan yasaki yimin haka ko?"
Da rawar murya ta ce " ah....'ahh..... yayah..... dan.....dan girman Allah kayi hak'uri.
Bai sake yi mata mata magana ba kawai ya sa hannu ya matso da ita kusa dashi ya d'aga mata fuskar sai da da lumshe idanu kafin ya furta " clear it".........
Dan dolenta tasa hannu ta kunna tap sannan tafara wanke masa fuskar tasa duk inda cream d'in ya ta6a sai da tabi ta wanke tas.
_Comment and share_ _pls_ π€π»
*Salmerhn ku ce* π
[10/2, 5:58 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ π
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
π
Ώ *26*
Tana k'arasa wankewa sai ta d'age hannunta daga fuskar tasa shima daidai sai ya bud'e idanunsa ya sauk'e su akan madubi, tacikin mirror d'in suka had'a idanu ai kuwa tana ganin yanda yakoma sai taji dariya yakamata.
Hannunta ta d'ago ta rufe bakinta dashi wani shape da goshinsa yacire ne yasa takasa rik'e dariyar tata sai ta juya kawai da gudu tabar bayin.
Bata zame ko'ina ba sai a d'akinta tana shiga kuwa ta tura k'ofar ta danna lock.
Dariya tayi taci abinta harda rik'e ciki.
Abbas kansa shima dariyar taso kamashi amma sai kawai ya maidata murmushi ya k'yale dariyar, haka ya k'urawa mirrorn idanu yana kallon kansa yanda Teemahn ta sauya mar kamanni, ita kawai yake hangowa lokacin da ta ke shafa masa cream d'in gani yake kamar yanzu ta ke yi masa hakan, sai kawai ya lumshe idanunsa bai dad'e ba ya kuma bud'esu.
Tunanin yanda zai je agyara masa kan nasa ne yafad'o masa, take sai yaji ba dad'i jiyayi ransa na so ya 6aci akan hakan, amma sai ya danne 6acin ran nasa, taimako d'aya Allah ya mata dan dama he is about to leave kuma dole kafin ya tafin sai yayi aski, amma badan hakan ba yace " hmm"
kawai sai da yakai hannu ya na shafa kannasa kafin yace " yayarinyar nan ta gama raina ni wallahi dole inkoya miki hankali".
Tashi yayi yafara rage kayan jikinsa dayake daman bai cire su ba d'azun.
Sai da yayi wanka kafin ya fito daga bayin d'aure da towel yana tsane ruwan dake jikinsa.
Shiri yayi dolensa cikin captan mint green yasa hula ya daidaita ta da kyau ta rufe gurbin kannasa sannan ya fice daga gidan ya nufi barbing saloon d'in dayafi kwanta masa arai domin a gyara masa 6arnar da Teemahn tayi masa.
*****
Teemah ce kwance ad'akinta akan gado sai kwasar dariya take harda hawaye, ko tayi niyyan bari amma sai taji sabuwar dariya na k'ara zuwa mata seconds-seconds take sake jin wata dariya na kamata, cikin dariyar take fad'in " kad'anma kagani ai tunda dai ni kace zaka sa agaba kam sai dai mu zuba mu gani".
Juyi tayi ta kifu agadon sai tunanin yanda suka kwashe da Leemah yazo mata a washegarin ranar daya hanata zuwa birthday.
Har kusan fad'a suka so yi da ita dan tagama saka ran Teemahn zata je sai kuma taga shiru ga shi kuma babu waya a hannun Teemah balle tak'irata sai hak'an ya k'ona ran Leemah sosai.
Haushin mitan da Leemah ke wa Teemah ne aranar ya had'u da haushin da yah Abbas ya k'unsa mata sai kawai ta fara yiwa Leemahn masifah toh dayake Leemahn itama ba baya bace wurin magana sai suka dinga yi atsakaninsu da k'yar suka yi shiru sai da Fauzee(class representative d'insu) tace zata had'a su da Uncle d'insu (Uncle Hasheem) kafin sukayi shiru dayake suna jin tsoronsa sosai.
Har kuwa kusan kwana uku sukayi basuyin magana da junansu kafin daga baya suka zo siluka shirya kowa ya huce.
Shiyasa ko yanzun data masa hakan kokad'an batayi dana sani ba acewarta tunda itama yana had'ata fa'da da mutane gara ta rama.
Wunin ranar kuwa kaf d'insa acikin d'akinta tak'arasa shi dan k'in sake fitowa waje tayi dan ma kar su had'u da shi yaci k'aniyarta ko kuma ya had'ata da mummy.
Batama san ya fita agidan ba dan hatta islamiyah ma yau k'in kulawa tayi da al'amarinsa, Mummy cema data ga shirun yayi yawa ga kuma lokacin islamiya har ya wuce bata ga gilmawarta ba shine tazo ta bubbuga mata k'ofar, amma sai tak'i bud'ewa tace da mummyn wai kanta naciwo ne sosai shiyasa bata fito ba tanaso tayi bacci ne.
Mummyn dataji haka sai tace mata "toh Allah ya sauwak'a" sai kawai ta juya ta koma d'akinta.
8:02 pm
Abbas bai dawo gidan ba sai da dare yana shigowa kuwa yawuto parlourn domin ya gaida mummy kasancewar tun gaisuwan safe da yayi wa mummyn basu kuma k'ara had'uwa da ita ba.
Yana gab da shiga parlourn sai wayarsa tafara ringing, dakatawa yayi da tafiyar sannan yaciro wayar ya duba mai k'iran nasa Saleem ne abokinsa wanda sukayi course tare dashi sai ya tsaya awurin yayi receiving k'iran.
Teemah na daga cikin parlourn suna zaune da Mummy sai taji ringing d'in wayarsa daga waje aikuwa ta wani razana hatta mummy sai data tsorata da yanda tayi d'in, da gudu ta tashi tayi d'aki batare da ko mummy tayiwa magana ba.
Abin ya d'aure kan mummy sosai yau Teemahn na yin wani abu kamar marar gaskiya ta kasa gane inda gakan kuma ya dosa, ko d'azaun da k'yar tasamu tafito bayan sallar maghrib sai da mummyn ta kusan 6ata ranta kafin tafito daga d'akin ahkan ma tana wani d'ar-d'ar da kalle-kallen gefe.
Shikuwa d'an dakali yasamu aga hanyar shigowan parlourn ya jingina sannan yasamu damar amsa wayar da kyau saboda wata gajiya yake ji sosai.
Duk magana ce sukayi da Saleem d'in akan komawarsu wurin aiki dake k 'ara k'aratowa, bayan sun kammala da wayar ne ya dawo ya shiga cikin parlourn da sallama abakinsa.
Mummyn ce ta amsa masa sallamar ta sa dan tuni Teemah kam ta ware d'akinta.
Sai da suka gaisa kafin mummy take tambayarsa ko akwai abinda ya had'a au da Teema ne dan ta lura da ita kamar tana d'ari-d'ari da shi.
Shi kuwa bai 6oye mata ba ya sanar da ita abinda Teemahn tayi masa yau d'in kaf bai 6oye mata komai ba.
Salati mummyn tasanya da jin abinda Teemahn tayi fad'a tafara bayan ta kammala da salatin kamar ta ari baki.
Daga k'arshe kuma sai fad'an yadawo kan Abbas d'in shima dan acewarta shi yajawo har hakan ya faru ai tana lura da shi bata ta6a ganin ya hukunta Teemahn ba duk da irin iskancin data ke masa".
Shiru yayi yan jinta sai da ta dasa aya kafin yafara bata hak'uri
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 67