Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tayi wankan 'kar'kashin shower tana yi ma tana kallon sa dan kar ya lura da ita bata wanke fuska ba ma sai bayan ta d'aura towel jikin ta sannan ta wanke fuskar tata daga nan sai ta 'dauko shi suka fito. Tsawon mintina biyar tana lalla6a shi tare da mai wasa cikin kunnan sa da hannun ta sannan ta samu baccin ya 'danyi nauyi, sai ta sau'ko daga gadon a hankali ta baro mishi 'dakun bayan ta daidaita masa 'karfin fan yanda iskan baze yi masa yawa ba....jikinta bomshot ne na blue jeans da wata 'yar 6ingilar riga mai bu'da'd'den gaba sky blue sosai tayi kyau cikin kayan kamar 'yar turawa. A parlour ta hango shi zaune idanunsa a lumshe ya kishingi'da ga dukkan alamu agajiye ya dawo domin yanayin sa ne ya fallasa asirin zuciyar sa, 'kafafunsa kawai ya iya sa6ewa daga cikin boot 'din dake 'kafar sa baya ga haka babu abinda ya sauya daga yanayin shigar sa. Isa tayi ta zauna daga gefen sa taja hancin sa a hankali tana murmushi, shima 'din murmushin yayi batare da ya bu'de idanu ba. Sai da ta zauna da kyau kafin tace " Saura 'kiris ka hana min yaro na bacci da wannan ihun naka fa, da bai yi ba kuwa yau 'din zaka koyi goyo babu ruwana" Bu'de idanun yayi ya sau'ke su a kan fuskar ta a hankali ya kuma sau'kar da idanun yabi jikinta yana murmushi yace " really?" Itama murmushin tayi tare da jinjina mai kai sannan ta mi'ke ta 'dauko mai ruwa mai sanyi da cup dayake tasan halinsa matu'kar ya dawo gidan ruwa yake fara nema kafin sauran hidimomin su biyo baya. Shi kam a fakaice yabita da idanu har taje ta dawo in baka sani ba zakaui zaton ko idanun a rufe suke saboda yanda ya 'kan'kansu. Da isowanta sai ta cika mai glass cup 'din da ruwan ta mi'ka mai sai yasa hannu ya kar6a. Ganin ya riga ya cire takalman dake 'kafan sa ne yasa sai ta zauna daga gefen sa tare da 'dago hannun ta tana shirin 6alla mai bottles 'din gabar rigar sai ya cire cup 'din daga bakin sa ya kalle ta suna ha'da idanu sai tace " a kara ne?" bai yi magana ba kawai ya dire cup 'dib tare da janyo hannun nata ta fa'do jikin sa, baki ta tura gaba tana 'ko'karin tashi daga jikin nasa sai ya 'daga kanta ya sau'ke mata kiss a samna lips din ta kad'an yana raba bakin su sai idanunsu ya sar'ke cikin na juna tuni ma har gannunta ya keawaya bayan wuyan sa, ganin hakn kuwa yasa shi mi'kewa tsaye da ita ya nufi bedroom 'din su yana fa'din " wariyar da ake min ya isa haka nima yau dole ki kar6i ajiyar princess 'dita na san ita ba zata na ware ni ba" Bai dire ta ko'ina ba sai a tsakiyar gado sai ya kuma sau'ke wani kisa 'din gefen wuyan ta sannan ya 'dago ya kalle ta bai yi magana ba illah gira 'daya da ya 'dage mata yana murmushi, Teemah ma sai ta maida masa martani tare da fa'din " nifa ban ware ka ba Allah Yayah, ai kasan duk yanda zan so Annur ba zai ta6a kamo 'kafar Yayah na ba cuz shine farin cikina kuma haske na " Tayi maganar ne a hankali cikin sanyi da shagwa6an ta kamar yanda ta saba yi masa a kullum. Fuskar sa ya kawo kusa da nata hancin su na gugan na juna, idanun su ma sar'ke da na juna sannan shima a hankali yace da ita " ban yadda ba ni, sai kin nuna min zahiri na gani" Yayi maganar yanda ita ka'dai ce za taji tare da kai hannun sa zuwa marar ta yana shafowa a hankali still idanun su sar'ke da juna. Itama hannayen ta kai ta dafa kafa'dun sa da shi batare da tayi magana a zahiri ba illah murmushi a cikin ranta take aytana irin yanda take jin son shi a zuciyar ta wanda yariga yayiwa dukkan ga6o6inta dabaibaiyi ta maimaita kalmar " i love cikin ranta har sau biyu na ukun ne bata san cewa har ya fito fili ba tsaban yanda shau'ki yake 'diban ta. Shi kam yana jin abinda ta furta 'din sai ya lumshe idanu domin har tsakar kansa yaji sau'kan kalmar. Bai amsa ba sai da ya sau'ke bakinsa kan nata ya ya sumbaci lips 'dinta daya furta maganan kafin yace " Love u more habibty" Hakan da ya fa'da ne yasa ta fahimci cewa maganar tata ta fito fili domin amsa shi'din ya bata. Yana fa'din hakan sai ya bar jikin ta ya koma gefen ta ya kwanta duk idanun su na kallon saman ceiling, hannun ta dake gefen sa ya kamo ya sau'ke shi saman 'kirjin sa saitin zuciyar sa sai ya lumshe idanu yace " bansan asalin lokacin dana fara son ki ba i just found my heart cike da 'kaunar ki, sometimes har mamakin kaina nake yi cuz bana iya controlling feelings 'dina akan ki matu'kar zuciya ta ta bu'kaci ganin ki ban iya jurewa har sai na gankin sannan nake nutsuwa, tun ada na tsani inga kin fifita wani akaina duk da kuwa nasan rashin sha'kuwa ta dake ne zai sa hakan amma duk da haka ban tantance meke damuna ba a lokacin nayi ta dulmiya cikin 'kunci da takaici, ban tabbatar da girman son da nake miki ba sai lokacin da Mahmud yazo min da labarin auren ku, a lokacin jinayi tamkar 'karshen farin cikina kenan a duniya, ji nayi tamkar nayi hauka... idan na tuna za'a yi auren ki, wallahi Zahra a lokacin tafiya kawai nake yi amma komai idan inayi sai inji tamkar bani bane har sai dana 'kwammaci mutuwa ta fiye da rayuwa duk da kuwa nasan hakan zunubi ne but i cant help it, saboda irin suyar da zuciyata keyi min a duk lokacin da na tuna kin zama mallakin wani ba ni ba sanadin haka na tafi Borno duk da nasan suna shan fama da 'yan ta'adda saboda ina ganin shine hanya mafi sau'ki da zan iya rabuwa da soyayyarki idan na daina numfashi, ban ta6a zama na fa'dawa wani damuwa ta ba balle na samu shawara saboda ban saba hakan ba, sa'a 'daya nayi kawai saboda wani 6angare daga zuciya ta na bani shawara akan na sanya dangana cikin al'amurana, wannan shawarar nabi na mida damuwa ta wurin ubangijina sai dai ban ta6a accepting d fact that wai kin bar ni kenan har abada ba, shiyasa salon addu'ah ta bata canza ba akanki amma ban ta6a tunanin mutuwa ce zata dawo da ke hannu na ba hakan bai ma shigo cikin tunani ba sam kuma ban fatan Allah ya rabaki da mijinki ba, ni dai fatana a kullum shine Allah ya bani Zahra musamman da nake da yak'inin cewa u too had feelings d same as i had 4u is just that babu wanda ya bayyana shi ga 'dan uwansa shine ka'dai damuwa ta da kaina na fahimci son da kike min tun kafin auren ki da marigayi. Sai gashi a lokacin da dangana ya fara zama a raina, na sanyawa raina cewa 'kaddarata kenan, shine soyayyar da babu ranar cikar ta sai kuma Allah ya nuna ikon sa akan hakan ya dawo min dake hannuna.... Zahra our love is like an eternal flame that no one can touch or break it, it can't be blown out, it carries many colors, until the end of time....our love is like d wind....i can't see it, but i can feel it all over me....idan nace miki zan misalta miki girman farin cikin dana tsinci kaina a ciki lokacin da akayi min albishir 'din auren ki bazaki ta6a fahimta ba...all i knew ws u ar my woman, my life, my everything....may be 2 d whole world u may be only one, but to me u ar my world, my happiness my weakness also d strong part of me.....banajin akwai kalaman da zan iya furtawa Zahra to tell u all d love i have 4u within my heart....i wan't u to always remember that i do love u, i'm with u, still with u, nd always be with u 4ever.... ko yau Allah ya 'dauki raina nasan na cika BURINAH a kanki tunda na mallake kuma muka so juna wannan ka'dai ma ya isheni alfahari". Juyo da kansa yayi ya kalle ta tare da bu'de idanu ya sau'ke shi a kan fuskar ta da suka ji'ku da ruwan hawaye bakin ta sai rawa yake yi kamar tana so furta wani abu amma takasa still kuma hannun ta kan 'kirjin sa da ji'ka'k'un idanun ta sanya 'kwayar idanun ta cikin nashi tana jin wani sonshi mai ha'de tarin kwarjinin 'kaunarsa na ratsa dukkan gangan jiki da zuciyar ta hawayen tane kawai suke 'kara 'karfin speed suna sake sau'kowa batare da ta janye daga kallon nasa ba. Idanun su sar'ke da juna yace " I so much luv u 'yan matan Yayah, ke na fara so a rayuwata kuma insha Allahu dake zan ru'fe murfin zuciya ta, ha'ki'ka ke ta dabance a rayuwa ta gaba 'daya......" Rintse ido tayi da 'karfi tana jin yanda zuciyar sa ke bugawa da sauri, ko haka ya bar ta ko da bai furta komai ba ita kanta tasan Yayah na matu'kar 'kaunar ta ko daga bugun da zuciyar sa ke yi bazata 'karyata kalaman sa ba. She is totally speechless, bata san mai zata ce da shi ba da har zata iya kamo kwatankwacin irin son da shi yake yi mata ba, tana jin nata son ba komai bane compare to nashi duk kuwa da cewa tana jine a yanzun tamkar idan babu shi rayuwar ta bashi da da anfani, tana jin bazata iya rayuwa batare da shi ba bama ta fatan wani abu da zai zo ya shiga tsakanin su koda kuwa menene shi, hatta mutuwa in so samu ne zata fison ya 'dauke ta kafin shi. Bata bu'de idanun ba taji shi a saman ta yana faman shinshinan wuyan ta tare da share mata hawayen dake fuskart kamar ba shine ya gama zayyano mata kalaman 'kauna cikin sanyin hali da nutsuwa ba, dai-dai kunnan ta taji ya ra'da mata " kin shirya kar6an ajiyan belove baby nurse 'din nawa?" Shiru tayi bata yi magana ba shima bai damu ba kawai yaci gaba da abinda ya keyi inda kamar wani ba'a son ran shi ba yake shafo ta very slow but so romantic tare da 'ko'karin kaiwan hannun sa can 'kasan marar ta, ita kanta yanda yake yi 'din yafara 'daukan hankalin sa har ta fara tunanin irin abin birgewan dazata yi masa a yau 'din in return to his tadaddun love words 'din da taji daga bakin sa yanzun, wanda ta tabbatar zai faranta ransa shima. Shikam har ya fara 'daukan layi inda ya gama bu'de gaban rigar dake jikin ta yana yamutsa ta yayin da hannun sa 'daya ke kan mararta 'ko'karin 6alle hook 'din bomshort 'din dake jikinta yakeyi caraf kunnuwan su suka jiyo muryar Annur yana fa'din " Daddy! "Subhanallah"!! yace acikin zuciyar sa tare da barin abinda yake yi cikin sauri, amma bai juya ya kalli Annur 'din ba sai ya tsaya kallon cikin idanunta kawai a hautsine. Itama Teemah sai yanzun ta bu'de idanun ta da jin muryar Annur 'din tafara 'ko'karin jan rigar ta rufe jikin ta da kyau, suna ha'da idanu a hankali sai yace "shine dagangan kika 'ki rufe 'kofan ko?" Tasan ba laifin ta bane cuz shine ya kawo ta 'dakin kuma shima 'din tasan yasan hakan kawai dai rasa abin fa'da yayi ko kuma ya mance a yanayin da suka shigo shiyasa, dan haka sai ta saki murmushin mugun ta da guntun hawayen ta tayi masa fari da ido tare da fa'din " Ai kaine ka bar 'kofan bani ba kuma kaga Annur ma yace ka 'kyaleni baya so shima" Lakatan hancin ta yayi da hannun sa yace " zan kamaki ai" sannan ya bar jikin ta ya sau'ka daga gadon ya nufi wajen Annur dake 'ko'karin tahowa inda suke, Abbas 'daga shi yayi sama yace " Oyoyo my boy na dawo bangan ka ba" Dariya Annur yayi masa yana jan hancin sa duk da kuwa bai warware daga baccin daya tashi ba amma yanda yake son Abbas 'din ya sanya shi 'dan warwarewa dan sosai Abbas ke yi masa wasa idan yana gida shiyasa suka sha'ku hatta Teemah 'yar kallo take zama idan Abbas na gida wa'kan da yake yi masa ma yanzu har Annur 'din ya iyata dan sama zai idaga shi yana dariya yana cewa " wah...wah...waladin...Muhammad Nury waladin...., yaron Daddy waladin, yaron Mummy waladin, mai sunan Daddy waladin" Annur ya rin'ka dariya kenan idan yaji wataran kuwa hannayen sa yake kamawa kamar sa'ani suyi ta wa'kar su a tare. Haka hatta wanka shike yi masa idan yana gida ya kuma bashi abinci sannan ya kaishi 'dakin dayake kwana yayi masa addu'ah yana lalla6asa har sai yayi bacci. Sau tari Teemah sai dai ta ta binsu da idanu ko kuma tana rakashi musamman idan zai kaishi bacci sai ta bisu abaya ita kanta tana jinjina wannan sha'kuwar cuz idan kaga Annur ya manne mata to Abbas baya gida ne in kuwa yana nan kallo ma bata ishesa ba. Sha'kuwa ce mai mugun 'karfi a tsakanin su hatta yawo wataran fita suke yi su biyu su barta agida wani sa'in ne idan zasu fita Annur sai ya je ya janyo mayafin da duk yagani a fili ya kawo mata yace " mummy let's go" Abbas idan ranar baiyi niyyan fita da ita ba sai yace "ah ah banda mummy, ita ta ta zauna a gida zamu kawo mata abin da'di". Cuz wataran office suke zuwa wataran kuma yawo kawai zai kaishi, wani gyaran kai da Abbas ya kaishi akayi masa wai wanda yagani, Annur yaro ne amma ba laifi yana da suman kai sosai, hakan yasa Abbas yake kulawa da kan nasa kamar wani babba yasa akai masa low cut aka gyara gashin kamar ba 'dan hausawa ba, kafin Abbas ya zama ma aikacin soja ba irin gyaran kan da baya yi, amma tunda ya shiga aikin sai ya zamana gashin ma ba bari yake ba shikuwa yana da masifar son tara gashi shiyasa ma daga ya 'dan 'dauki hutu zaka ga har ya tara suma ya kuma gyara shi gwanin birgewa kafin cikar hutun Teemah kanta yana bata sha'awah da zarar hutunsa ya 'kare kuma shikenan zai je ya cire su, wannan dalilin ne yasa yake yiwa Annur dan shi bai da damar yin hakan, shi mutun ne mai son cika BURIKAN SA, sai dai baya binsu a gaggauce cikin natsuwa take binsu shiyasa idan bai samu daman yin abu ba sai ya 'dorawa wani nashi burin, kamar yanzun burinsa na son Teemah ta zama doctor wanda ta'ki bai yi fushi ba sai ya 'dauke burin daga kanta abin na nan a cikin ransa amma sai ya bari akan 'yarsa idan har Allah ya bashi....ita zata cika masa wannan burin. Yanzun kuwa da Annur yake ri'ke a hannunsa sai yake ta faman jan hancin Abbas yana dariya, Abbas kuma yana kaucewa tare da mai wasa acikin sa da bakin sa da yake jikinsa babu riga illah pant ne kawai so idan ya hura cikin sai yayi 'kara wanda yake matu'kar sa ka Annur dariya idan yayi masa hakan. Gurin da Teemah take ya koma da shi yana fa'din " Annur baya son zama da kaya agida da alama halin ki yayo" Teemah kam murmushi mai sauti kawai tayi batare da ta tanka masa ba sosai take jin da'din yanda Abbas yake kulawa da Annur duk kuwa da abubuwan dake gaban sa amma sam bai sa sun rinjayi tattalin iyalinsa ba, sosai yake 'ko'kari akan hakan har tausayi yake bawa Teemah wani lokacin idan taga Annur na ma'kal'kale masa, ita kanta tana so suna 'dan barinsa yana samun natsuwa, sau tari sai dai in tana son ya barshi sai ta yi masa wayo tace "bamboo Annur, come on zo in goya ka kayiwa Daddy dariya" Annur idan yaji goyon ne kafin yake zuwa ya bar Abbas 'din, wataran ma har datse 'kofa take yi da key dan ya samu yayi bacci, tun Annur bai gano ba har ya gane so idan baiga Daddyn nasa ba kuma yaga 'kofa arufe sai yaje yayi ta bugawa yana 'kananun kuka tare da 'kiran "Daddy"! A gefenta Abbas ya zauna inda ya maida idanunsa kan fuskar Annur batare da ya kalle ta ba ya fara yiwa Annur wa'kansa ta waladin " wah...wah...waladin.... Annur kam sai dariya yake yi Teemah kuwa binsu take da kallon 'kauna tana murmushi, tasan idan kowa irin Abbas ne to da babu macen da zatayi 'korafi akan raino amma ina tasan bakowa ke sa'an samun hakan ba dan hgaka sai ta furta " Alhamdulillah" da dacen samun miji nagari da tayi mai son ta mai kula da dukkan al'amuranta, mai baiwa bu'katun muhimmanci uwa uba kulawa da ahalin gidan sa. Sai da ya gama wa'kar tasa kafin yace da Annur " Yaron Daddy... you need a baby sis to play with right?" Annur sai ya 'dage kai sama tare da fa'din " yes Daddy just like Anty Ummah's baby" yana washe fafaren 'kananun ha'koran sa waje. (Anty Ummah wata mata ce a block 'dinsu data haihu sati biyu yanzu da suka je da Teemah ta 'dauki babyn shine ya 'kare mata kallo harda wasa da 'kafafuwan ta ). Abbas kam kamar Annur ya ziga shi sai ya ya sake fa'din " Oyah tell ur mum that u want ur baby sis from her like Anty Ummah's baby.." Annur kallon ya dawo da shi kan Teemah data zuba musu idanu tana murmushi cikin maganar sa da bata gama mi'kewa ba yace " yesh Mummy ...i wan my lil prinshesh right away" Teemah zaro idanu tayi tace " see u, right away 'din 'kaniyar ka a ina zan samo maka yanzun?" Abbas kam murmushi yayi ya bashi hannu tare da kama chicks 'din sa yace " That's my boy, we need our princess right now ko ?" Kai Annur ya 'daga masa yana washe baki, Abbas kam yana murmushi yayi pecking 'dinsa a goshi. Teemah kuwa tashi tayi da sauri ta fita taje 'dayan 'dakin ta 'dauko teddy bear 'din sa da yake wasa dashi ta kawo masa tace " ga lil princess 'din taka....bana son damuwa ni" Tana maganar tana cusawa a tsakanin sa da Abbas. Annur yana ansa sai yayi jifa dashi gefe tare da fa'din " Not ths mummy i want d yeal one" Dariya dukkan su suka sanya ilah Annur, Teemah kam harda zama Abbas yana cikin dariyar yace " yaro na na son d real princess ba fake ba sai ki shirya kar6an lil sis 'din Prince 'dina an jima " Kafa'da ta no'ke tace " ni dai ah ah...Allah Yayah duk kai kake koyawa yaron nan iyayi.....har da wani now sai kace an gaya masa haihuwan sau'ki ne dashi, nawa ma yake shi'din 19months ne fa yake har yanzu dan Allah, ni dai gaskiya ba yanzu ba....kuma ya dameni da zancen babyn nan zane shi zan fara ni kam" Abbas sai yace " Kina ta6a min yaro to kuwa sai kin haifi triplet ba ruwana " Sai tayi saurin no'ke kafa'da kamar 'yar yarinya 'karama tana tunzura baki gaba. Abbas ma sai yace " do ur worst 'yan mata zaki kuwa sha mamaki...yaron da nake planning kai shi school kwanan-nan 'din ne zaki ce min bai kai ya samu sister ba? Kin ma yaudari kanki yarinya is better ki fara shiri ma cuz next year like ths insha Allhu i'm with my 2 kids". Jikin sa ta fa'da tana kukan shagwa6a tare da kaimar bugu a 'kirjin sa shikam dariya ma ta bashi da shegen tsoron nata Annur ma ganin yana dariyar shima sai ya bu'de bakin sa da 'kananun ha'koran sa guda 12 yana taya Abbas 'din dariya. _They live happily ever._ *ALHAMDULILLAH WASSALATU WASSALAMU ALA NABIYUL KAREEM*. Anan na kawo 'karshen littafin *CAPTAIN ABBAS* Wanda na 'dauki tsawon lokaci ina rubuta shi amma bazan iya fa'da muku tsawon lokacin ba gaskiya dan kar kumin dariyaπŸ™ˆ.....lolz *Yabo da godiya sun tabbata ga Allah ma'daukin sarki mai kowa mai komai wanda* *ya kawo mu har wannan lokacin muna cikin rayayyu.* Fatan darasin dake cikin labarin ya isar, wanda suka ha'da da tsoron Allah, ha'kuri, da kuma tawakkali...ha'kurin ma dai shine kusan mafi rinjaye cikin labarin so ina fatan zaku fahimci manufata duk da nasan bakowa ne zai fahimci hakan ba amma ko da tsirarune daga cikin makaranta labarin idan suka fahimta toh Alhamdulillah *BURIN SALMERH* ya cika...... rayuwar d'an Adam de dukkanin ta aya ce mai girman gaske... nasan munsan hakan, sai dai still bamu fasa aikata son zuciyar mu ba, musamman idan mukayi duba da yanda rayuwa take tafiya a wannan zamanin, mafi yawancin mu mu muna aikata abinda ran mu yake so ne koda kuwa munsan ba akan dai-dai muke ba amma sai zuciyoyin mu su rinjaye mu sai muna ganin kamar dai-dai muke aikatawa azahirance, wanda bazamu tashi yin Allah wadai da hakan ba har sai ranar da Allah ya nuna ikon sa akan mu alokacin ne dayawan mutane ke gane kuskuren da suke aikatawa. Son zuciya, son kai, buri da kaiwa kanmu inda Allah bai kaimu ba shima babu amfani tunda kunga yanda rayuwar Anty, Munnira da kuma Anty Chiddy ya kasance saboda son zuciyoyin su daga 'karshe kowa sai da ya yi nadaman halin sa wanda tun farko rashin ha'kuri ne ya haifar da shi....Yayin da ha'kurin Mahmud yasa ya amsa 'kiran mahaliccin sa ayan yardajje cikin natsuwa. ALLAH UBANGIJI KA KASA MU GANE GASKIYA GASKIYA CE KUMA KABAMU IKON YIN AIKI DA SHI. ....fatan zaku fahimce ni....kuraren dake cikin labarin kuma ku yafemin dan Allah kar ku tuhumeni akan hakan ayi min uzuri saboda littafina na farko kenan duk dama bashi na fara rubutawa ba amma dai kusan zance shine farko tunda al'kalamin sa ya kai 'karshe. *MY MENTOR* Kullum kina raina, 'yar uwa abar alfahari *SAFIYYA ALIYU WAKILI* jagorata, kuma hasken idanuna....ha'ki'ka ina alfahari dake cuz irin ki ka'dan akaf 'din rayuwa, ke ta dabance, alkhairin ki gareni mai girma ne, bani da bakin godiya, dan nasan duk matsayin dana kai a duniyar gizo to sanadin kine...nasan da bazar ki nake taka rawa ta. Fatana Allah ubangiji ya raya mana Khairy da Haidar da ma mabiyan su bisa tafarkin gaskiya. *JINJINAR BAN GIRMA GA* πŸ‘ Anty na (Anty maimunat O.G MAHNOOR) KIN FI 'KARFIN GODIYA SAI DAI FATAN ALLAH UBANGIJI YA SAKA MIKI DA MAFIFICIN ALKHAIRI ALLAH YA RAYA MANA ZURI'A YASA KIFI HAKA YA BAKI HA'KURIN KULAWA DA MU. *BAN MANTA DAKU BA MUTANE NAH* . Anty Rahama Maman Ahmad Mrs Abubakar Rukyn mama Safiyya A W Mama Queen Maryam Abdul Queen Ameena dama wa'danda ban ambata duk Salmerh na gaisuwa.🍭 *SA'KON MASOYA* Fans 'dina na 'kwarai wa'danda sukayi ha'kuri dani da rashin typing 'dina akan lokaci, kurakuraina, da sauransu, suka kuma bada lokuta, si suna faranta min da da'da'dan sharhin su ha'ki'ka bazan ta6a mantawa da ku da addu'o inku ba🀞🏻. Groups 'din duk dana ke ciki nagode sosai da ha'din kan da kuka bani da kuma 'kwarin gwiwar ku gami da sharhin ku Allah ubangiji ya bar 'kauna Ameen.πŸ‘πŸ» πŸ€™πŸ» Umm Haibat, Aisha Aliyu (Zumunta novel ina godiya sosai). *AysherudAhmad*(wattpad)...... yau dai burin ki ya cika Captain ya kammala sai godiya. *JINJINA TA MUSAMMAN GA* πŸ‘ŽπŸ» Readers 'din Captain Abbas dake facebook da wattpad duk ina godiya sa'konnin ku duk na iso ni da addu'o'i...kuma ina muku fatan Alkhairi Allah ya bar 'kauna. Bazan iya lissafo sunayen ku anan ba amma kusani kuna zane cikin zuciyata kuma nima ina sonku sosai.😍 *MUST READ* 🀞🏻 Sai mun ha'du a sabon littafina✍🏻 mai suna πŸ’• *NOORUL πŸ’• (Haske nah)* Ta'kaitaccen labarine mai matu'kar 'daukan hankali, amma wanda ya bibiyeni ne ka'dai zai fahimci hakan.πŸ‘ŒπŸ» πŸ‘‡πŸΌ Daga πŸ–Šal'kalaminπŸ‘‰πŸ» *SALMERH MD* follow *Serlmerh-md* @ wattpad and instagram.🀝 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu

Chapter 66 of 67