kinnan take danne damuwar ta in dai ba abin yafi 'karfin ta bane sam bata bayyana wa cuz bata ga anfanin ya biya mata nata bu'katun shi kuma ya hana kansa ba, bacin ita ba wani ciwo ko wani abu take ji ba da zai hana shi sakewa da ita, amma ta rasa ta yanda za'a yi ya fahimce ta.
Ko yanzun ma tana iya feeling yanda gurbin zuciyar sa ke beating so fast, daya ke kwance take bisa 'kirjin sa sai take jin tausayin sa sosai yake kama ta.
Sai da ya dai-dai ta kansa ne kafin ya sau'kar da idanun sa kan fuskar ta ya kalle ta.
Muryar shi kawai ta jiyo yana fa'din " idan kin tafi Abuja kika barni zaki iya jure rashi na?".
Hannun ta na yawo akan fuskar sa dana faman shafa fuskar tashi zuwa gurbin dimple 'dinsa, jin yayai maganar ne yasa ta saukar da hannun ta daga kan fuskar tasa ta dawo dashi k'irjin sa sannan a hankali tamkar bata son yin maganan ta bashi amsa da fa'din " kai ma ai ka juri rashi na Yayah duk da ma ina tare da kai, balle ni ai kaga dole zan iya jurewa tunda na 'dan lokaci ne".
Ta karasa maganar hannun ta na yawo akan 'kirjin sa.
Zai sake magana yin magana sai Teemah ta jijjiga masa kai, shirun yayi kamar yanda ta bu'kata yana kallon kitson dake kanta.
Bazata kawai yaji ta sau'ke hannun ta ajikin sa wanda yasa shi sau'ke ajiyan zuciya ba tare da ya shirya ba.
Sosai Teemah tayi 'ko'kari wajen ganin ta faranta masa tare da rage masa abinda yake ji 'din batare da jin kunya ko 'kyan'kyamin sa ba, dan tasan ko da ta bashi dama da jikin ta bayi zaiyi ba, ada kullun inzai kusanceta sai yayi kusan salo a 'kalla kala uku da ita, koda tagaji kuwa sai yayi son ranshi sannan ya barta, sa6anin yanzu da kullun 'daya kawai ya keyi kuma duk tasan saboda condition 'din ta ne yasa.
Shima Abbas yau 'din ba 'karamin mamaki ta bashi ba, sosai ta birgeshi ta sanya masa nisha'di a zuciyar sa.
Bai ta6a zaton zata iya yi masa irin hakan ba domin bata ta6a ko kwatanta yi mai ba sai yau da tayi surprising 'dinsa, wani gurbi na musamman ta samu ke6antacce a zuciyar sa wanda yake jin babu mai iya ratsa wajen illah ita ka'dai, sosai yaji da'din yanda ta tafiyan tar da shi da bu'katun sa a wannan lokacin.
Albarka kawai ya rin'ka sanya mata da har sai da ta rufe mai baki da nata kafin yayi shiru.
Haka rayuwar su taci gaba da tafiya kowa na 'ko'karin ganin ya farantawa 'dan uwansa da duk wani abinda zai iya na kyautatawa, zaman su gwanin sha'awa inda suke shimfi'da zallar salon so da 'kauna tare da mutuntaka a tsakanin su.
Har watan ramadan yazo ya wuce Teemah bata koma Abuja ba, duk kuwa da cewa kusan kullun Ummah bata gajiya da yi masa tuni akan dawowar tata amma ya kasa kaita sai dai kullun ya ringa bata tabbacin insha Allahu suna hanya.
Da haka yayi ta jan Ummah har cikin Teemah ya kai 8months da kwanaki kusan ashirin, wanda a lokacin ne Ummah ta nuna masa 6acin ranta sosai barin ma da Hannah ke 'kara zuga ta a gefe dan itama sosai ta matsu taga Teemah a kusa da ita tana mamaki ita kam wai Teemah ne da ciki abin na bata dariya sosai.
B'acin ran Ummahn ne yasa shi fara tunanin kawai gara ya maida ta Abujan, ita kanta Teemah ma ta kan yawaita yi masa magana akan tafiyar amma sai yayi kamar be ji taba, da farko idan tayi maganar yana bata amsa da fa'din " zaki je ai amma sai na shirya tukunna"
ko kuma yace " Ina sane da batun karki damu"
amma daga baya ma sai ya zamana ko 'kala baya furta mata, ya daina tankata indai akan maganar ne, hatta Anty Leesah na yawan tambayar sa wai " yaushe zata dawo gida? ko can ports 'din zasu je sunan ?" sai dai yace mata " ah ah " kawai a takaice, dayake yanzu Leesah ma ta zama 'yar gida tun lokacin da suka fahimci cewa ita 'din sister 'din Bilal ce shikenan sai zumuncin su ya 'kara 'karfi, ko da akayi tambayar auren Hannah kuwa sai ya zamana date 'din auren su rana 'daya a kasa sanya Leesah da Hannah duk a watan December.
Itama Teemah da ta gaji da maganar sai ta kyale shi ganin cewa kullum abu 'daya suke ta maimaitawa.
Sai yanzun ne yafara yi musu shirye-shiryen tafiya ganin ya gama tunzira ran Ummah, cikin kwana biyu kuwa har sun gama komai inda a kwana na biyar da yin wayar Ummahn suka dira garin Abuja babban birnin tarayyar Nigeria.
Sau'kan su keda wuya kuwa Ummah ta ringa sau'ke masa buhun masifa da 'kyar ya samu tayi shiru, dayake dama fa'dan ba wai na zafi bane kawai na haushin rik'e Teemah da yayi ne acan da kuma wasa da hankalin ta da yayi tayi a banza.
Hannah kuwa abin nema ya samu ganin ga ta ga Teemah ga kuma tu'ke'ken cikin ta a gaba.
sai da ta gama dariya son ranta da kwatan ta irin tafiyar Teemah sannan tafara gwad'ata wai wlh cikin kyau ya 'kara yi mata tayi fresh skin 'din ta ya 'kara yellow da shai'ki, tace " sai dai kinyi bombom gaskiya da boobs sosai, har da kama baki tace "kai wannan babyn akwai wayo wallahi yana son Dad 'dinsa ya shana"
ta 'karashe da dariya.
Teemah kam bata damu ba sai ce mata tayi " soon kema ai kina hanya zan rama ne Hannah"
Hannah tace " Allah kuwa ba batun wasa anan, inaga ma shiyasa Yayah ya kasa dawo dake gida tuntuni 'din irin wannan kaya haka?, kai tubar kallah!"
Murmushi Teemah tayi tace " Hannah ke kam bazaki ta6a canza wa ba, inajin sai ranar da Bilal ya koya miki hankali tukun"
Hannah Tace
" kamar yanda Yayah ya koyar dake ba, ai naga kin wani nutsu ne duk kin canza ko dai kawai dan ana shirin zama uwa ne?".
Teemah sai tace
"Bansani ba Hannah kijira naki idan yazo kawai sai ki bani labari"
Dariya Hannah tayi tace " ai nawa daban ne da naki kema kin sani...., yauwa ni ya batun birgiman ki? Allah yasa de kin daina dan in ba haka ba yanzu kam sai dai ki koma 'dakin Yayah kiyi ta bajewar ki ke ka'dai da wannan 'katon cikin"
Teemah cewa tayi
"Zamu gani ai Hannah sai ki kore ni"
Murmushi kawai Hannah tayi ta tashi ta fita jin Ummah na 'kwalla 'kiran ta.
Washe gari Leesah tazo ta yi musu barka da zuwa, su Hannah sai sunkuyar da kai take yi ita a dole kunya, sai a bayan tafiyar Leesah ne sai Teemah tayi ta tsokanar ta wai mai kunyar iskanci bayan tana ganin yanda take satan kallon ta idan ta juya kai.
Hannah tana dariya tace " ai dan tana 'dan kama da Bilal ne shiyasa"
Teemah ma dariya tayi tana nuno ta tace " mara kunyar yarinya kawai, wato dan tana kama da Bilal ne shiyasa kike satan kallon ta".
Hannah murmushi tayi mai sauti tace " bazaki gane bane matar nan, Allah ina tsananin son Bilal fiye da yanda Yayah ke son ki ".
Ta k'arashe da zolaya.
Teemah kuwa take ta tare ta da fa'din " kar ma ki fara yaudaran kanki da wannan 'karyan, an gaya miki soyayyan Yayahn irin naku ne?"
Hannah 'kin yin magana tayi sandiyyan ganin Abbas tsaye a bakin 'kofa sai kawai ta fara 'kif-'kif da idanuwa Teemah bata san me ake ciki ba ita kam har sai da ta gama fa'din me zata fa'da ta mi'ke sannan ta ci karo da shi a tsaye.
Hannah tasowa tayi ta nufi 'kofar fita daf da shi sai tace " Ina yini Yayah?"
Da " lafiya" kawai ya amsa ta kamar yadda ya saba.
Teemah da idanu ta bi bayan Hannah har ta bar 'dakin sannan ne ta dawo da kallon kan Abbas, sanye yake da dogon wandon jeans da armless shirt, sosai kayi suka amshi jikin sa.
A hankali ya tako zuwa inda take ya zo ya tsaya a kanta batare da yayi magana ba.
Teemah 'daga kai tayi ta kalle shi suna ha'da idanu sai yayi sama da girar shi tan 'ko'karin sau'kar da idanun ta sai ya sa hannun 'daya ya 'dago ta tsaye ran'kwafowa yayi ya rungume ta baya hannun sa ya kai kan cikin ta yayin da kansa ke a wuyan ta saitin kunnan ta a hankali ya furta " na ji ana gulma ta!, laifin me na aikata kuma?"
"Ba komai"
Ta ce da shi itama cikin sanyin murya.
Kiss ya sau'ke mata a kunnan tare da fa'din " ban yarda ba "
Sai tace
"Da gaske Yayah ba komai......"
Maganar tata yankewa yayi sanadiyyan cizon dataji ya sake mata a kunnan sai ta 'karasa da fa'din
" awshh......Yayah ka cinye min kunne na".
Murmushi yayi yace " da zafi ne?"
Kai ta 'daga masa masa tana shafa kunnan tamkar zata yi hawaye.
Sai yace " tell your sister that dafin son Yayah ya zarce na kowa, bai ma da makamanci kinji?"
Shiru tayi masa kawai tana jin yadda yake 'ko'karin kai hannun sa har zuwa 'kasan ta.
Ri'ke mai hannun tayi tayi kalar tausayi tare da ro'kon sa akan " please yayi ha'kuri"
"Dalili?"
Ya ce da ita.
Sai tace " Ayyah Yayah gidan Ummah ne fah kuma kaga Hannah na iya shigowa ako wani lokaci"
Shima 'din ya san abinda ta fa'dan gaskiya amma duk da haka sai ya'ki sakin ta har sai da ya gama kashe mata jikin kafin nan ya bar 'dakin, Allah ma ya taimake ta har ta gama kintsa kanta Hannah bata dawo ba.
Satin Abbas 'daya a Abuja sannan ya koma Rivers, ranar daya koma kuwa a ranar Teemah ta bar 'dakin sa ta koma na Hannah bisa umarnin Ummah.
Sosai Teemah ke jin kewar sa musamman lokacin da tazo bacci, dan ta saba bacci ajikin sa yanzun kuwa sai take jin ta wani iri, in bama maganar da Hannah tayi mata akan birgima ba ai ita tuni ta mance da cewar tana yi, dan kullun yanda ta kwanta ajikin sa a hakan take tashi bata ganin ta canza wuri saboda baya raba jikinsa da nata har gari ya waye, so ta ina zata samu damar yin birgima a hakan, yau da gobe kuwa yasa har ta saba da bacci a nutsen especially ma idan tana jikinsa dan ko fa'da sukayi da shi kuwa wannan yanayin baccin nasu baya ta6a canzawa ko ta'ki ma dole sai ta ha'kura saboda ba barin ta zai yi ba.
Aranar da 'kyar bacci ya 'dauke ta da tunanin sa a ranta har kuwa cikin mafarki sai da ta ganshi.
Washe gari da suka tashi Hannah da yake bakin ta baya shiru sai tace " gaskiya Yayah ya iya displine kin koyi bacci mai kyau, da ai har ina fargaban ki danne ni da wannan 'katon cikin naki".
Teemah cewa tayi " ke de kika sani Aku uwar magana, ina nan in da raina watarana sai na rama insha Allahu".
Hannah murmushi kawai tayi bata yi magana ba tana tuno cewa wai itama watan watarana sai gata ga ciki. " hmm" kawai ta furta a fili with smile on her face.
Zaman Abuja yayi wa Teemah da'di, dan sosai Ummah ke bata kulawa tare da bata wasu addu'o'i tana karantawa kullum, bata da damuwar komai yanzu face tunanin mijin ta da kuma fatan Allah ya sau'ke ta lafiya.
Shima Abbas 'din suna waya akai-akai dashi dan a'kalla suna waya a rana kusan sau biyar in dai yana da lokaci baya gajiya da 'kiran ta.
Tun lokacin da watan haihuwar ta ya kama sai ya kasa jin kwanciyar hankali, kullum baya bacci mai kyau da dare haka zai 'dau lokaci yana yin sallah yana ro'ka mata ubangiji sau'kin na'kuda, haka ma Mummy ba'a bar ta a baya ba tana iya 'ko'karin ta.
Da yamma kullum sai sun fita cikin compound 'din gidan ita da Hannah su 'dan zaga tana warware ga6o6in ta, ko ina kuwa zata da ruwan ta a hannu take tafiya, dan yawan shan ruwane da ita akai-akai yanzun.
According to her EDD an ce haihuwar ta zai kama ne zuwa kwanaki takwas masu zuwa ko kuma 'kasa da haka, sannan kuma zai iya haura hakan it's depends basu da tabbaci, kuma duk ba matsala bane.
Dalilin haka ne yasa yanzun Ummah sam bata nutsuwa kullum hankalin ta na kan Teemah, hatta baccin dare ma bata yin shi gaba 'daya, ta ringa zarya kenan a 'dakin su, haka ta hana Hannah ma dogon bacci duk wai dan kar wani abin ya taso kuma basu sani ba.
*****
Ranar wata lahadi ne wanda ya kasance kwana na biyar cikin kwanakin da aka gindaya mata, kenan idan aka bi lissafin da aka tana da sauran kwanaki har uku kafin cikin EDD 'din ta, shiyasa ma bata damu ba koda taji marar ta na 'dan haura mata da ciwo ka'dan-ka'dan, zaton ta ko zai daina kamar yanda ya saba yi mata dan haka sai bata sanar da Hannah halin da take ciki ba ganin tana baccin ta, shiyasa ma ko motsin kirki ta 'kiyi dan kar ta ta she ta.
Zirga-zirgan zuwa bathroom ta fara dan yawan fitsarin dake matsata, in ta je 'din kuwa ba wani abin kirki take yi ba sai dai ta dawo tana cije baki tana tafiya da 'kyar kuma a hankali saboda azaba.
Gajiya tayi da yawon zuwa bayin ga ciwon marar nata na k'ara tsanani kawai sai ta sanya kuka a hankali ta dur'kushe daga bakin gado dai-dai farkawan Hannah ha'de da turo 'kofan Ummah a lokaci guda.
Da hanzari suka yo kanta Ummah kam sai ta daka wa Hannah tsawan rashin hankalin datayi inji Ummah da yake ta mata warning akan kar ta yadda ta ringa yin dogon bacci saboda irin hakan.
Take sai Hannah taja gefe tana rarraba idanu tayi kicin-kicin da fuska.
Ciwon Teemah kam kamar jira yake yi yaga idanuwa sai kawai ya tashi gadan-gadan, Hannah ma kuka ta sanya ganin halin da y'ar uwar ta ke ciki kafin kace kwabo har hawaye ya wanke mata fuska gaba 'daya.
Ummah fita tayi da sauri taje ta d'auko wayar ta da mayafin ta bata dawo 'dakin ba sai da ta fita waje ta yiwa driver magana, Allah ma cikin ikon sa yasa yau 'din agidan su drivern ya kwana saboda daren da yayi bai koma gida da wuri ba shiyasa kawai ya kwana be tafi ba.
Hannah kam sai aikin sannu take ta yiwa Fateemahn gwanin ban tausayi idan ka gansu.
Ummah na dawowa sai ta umarci Hannah data ta 'daukowa Teemah mayafi su wuce asibiti.
Gefe da gefe suka kama Teemah a hankali har suka fice waje wurin mota inda suna shiga driver yaja suka fice daga gidan.
Yayin da Fateemah ke jin ranta kamar zai bar jikinta dan azaba, ha'ki'ka haihuwa ko ka'dan ko yake bashi da sau'ki, babu kuwa wanda zai gane hakan har sai abin ya same shi.
Tun da suka je asbiti ake abu 'daya tun 'karfe uku na'kuda yasa ta a gaba da azaba sai ya tashi sai kuma ya kwanta har tazo tayi bacci ma kusan na mintina arba'in sannan ta farka da wani matsanancin ciwon, gaba 'daya Teemah ta fice a hayyacin ta ta gama saduda da rayuwar ta ya 'kare dan bata ta6a zaton akwai irin wannan ciwon a duniya ba, duk jarabar ta da son yara sai da taji bata 'kaunar haihuwa muddin ranta, fa'di take yi kawai " ku cire min wannan cikin wallahi banaso, ku raba ni dashi dan Allah mutuwa zanyi......waiyo kuyafe min dan Allah.....Yayah na waiyo zan mutu..."
Tun tana kukan da hawaye har tazo hawayen ya daina fita mata ta koma salati, duk wanda yazo mata yi take yi ko da bata kai 'karshe ba sai ta kamo wani, abin dariya abin kuma tausayi.
Hannah kam kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita haka takeji, a ranta take tunanin ashe haka haihuwa take sosai ta tsorata da haihuwa ita kam, lalle uwate abin girmamawa ne dole kabisu, tausayin Teemah gaba 'daya ya cika mata 'kirjin ta har ji take da zata iya data rage mata ciwon.
Ummah bata sanar da kowa halin da ake ciki ba hatta Abbas kansa, cuz gaba 'daya hankalin ta na kan Teemah ne yanzun ganin yanda take shan wahala gaba 'daya ta karya mata zuciya ganin na'kudan yayi tsayi.
Dai-dai an fara 'kiran sallahn shiga masallacin Asubah abu yataso mata gadan-gadan, bayan ta take jin tamkar zai 6alle biyu, Allah kuwa cikin ikon sa mintina biyu basu cika ba sai ga kukan jariri domin da kukan sa ya taho kamar an doke shi.
Yana fita daga jikin ta kuwa Teemah ta fara sau'ke ajiyan zuciya a hankali take furta "Alhamdulillah" har bacci ya 'dauke ta.
Sai hamdala kawai su Ummah keyi yayin da Hannah ke farin ciki da guntun hawayen ta a idanu.
Abbas na alwala yaji tsinkewar zuciya da bai san dalili ba, dan haka sai ya ringa maimaita _innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ har ya kammala alwalar tasa har kuwa ya idar da sallar bai ji zuciyar sa tayi dai-dai ba, kuma ya rasa dalilin da ya kawo hakan, Qur'ani ya 'dauka kawai ya yi ta karantawa har gari yayi haske.
Baby lafiyar sa 'kalau, Teemah ce dai ta 'dan samu matsala sai da aka mata aiki amma ba sosai ba 'dan ka'danne daga nan aka yi discharging nasu.
Ummah bata 'kira shi ba sai 'karfe 8:00am bayan har sun koma gida ta gama gyaran mai jego da baby inda aka shirya shi cikin kayan sa sky blue sun fito ras abinsu sannan Ummah ta 'kirashi da duk wa'dan da suka dace ta sanar mawa.
Abbas ne 'karshe da Ummah ta 'kira, shi kam godiya kawai ya ringa sake wa mahalicci yana tasbihi musamman dayaji cewa lafiyar su 'kalau ita da babyn har ma sun koma gida ai farin cikin sa da'duwa yayi akan nada.
B'angaren Teemah kuwa zama tayi gefen yaron ta tana kallon shi tana sau'ke murmushi, wai yau gata ga babyn ta wanda ita ta haifa da kanta, baiwar Allah kenan yawa ne da ita yakan kuma baka ta inda baka zato ko kuma akasin haka, sosai ta ringa gode Allah a zuciyar ta, bazata iya misalta yanayin farin cikin data ke ciki ba a wannan lokacin.
Babyn ta tsurawa idanu tana so ta gano kamar sa amma takasa, sam bazata iya iya ce ga kamar yaron ba ayanzu domin kuwa ita bagane kamar jinjiri takeyi ba, shiyasa dole ta ha'kura ta barshi, yatsun 'kafar shi ka'dai ta iya gane kamar su irin ta Abbas ne sak sai dai hasken sa da kamar kam takasa ganewa.
Baby baccin sa yake yi cikin kwamciyar hankali, tunda akayi masa wanka yake bacci, itan ma garin kallon shi har bacci ya 'dauke ta a gaban sa, ba ita ta tashi ba sai da azahar.
Hannah ce ke gaya mata wai ai Yayah ya yi ta 'kira abata wayar tana bacci kuma Ummah ta hana a tashe ta.
Shiru kawai tayi dan wani azaban zafi da take ji tun daga 'kasan ta har zuwa cinyoyin ta.
Da 'kyar ta daure ta tashi ta zauna tana cije baki, koda zata tashi tsaye kuwa zafin datajin har sai daya sata sau'kar da hawaye.
Matar da ta gani zaune a gefe ne tana bawa jinjirin zam-zam tace da ita " yi a hankali Fateemah, sai kin daure kinji"
Wa Hannah matar ta mi'ka yaron sannan da kanta ta tashi taje ta ha'da mata ruwa mai 'dumi a bathtub tace idan ta shiga zauna aciki.
Kafin ta mi'ke sai ga Ummah ma ta shigo, tana ganin ta zaune kuwa sai ta washe baki tare da yi mata sannu, Teemah ta amsa sannan ta tashi a hankali kamar mai koyon tafiya ta wuce bayin.
Da hawaye ta samu da 'kyar da azaba ta iya yin fitsari, da farko ma tsoron shiga ruwan tayi amma sai ta daure musamnan data tuna first night 'din ta irin yadda ruwan zafin ya taimake ta shiyasa yanzun ma ta daure ta shiga.
Sai data yi brush kafin ta fito daga bayin tana 'danjin da'din gabo6in ta ba kamar lokacin data
tashi a baccin ba.
Tana fitowa kuwa aka gabatar mata da abinci, inda ta 'dan tatta6a ka'dan ta bari domin ba da'din bakin ta takeji ba yunwar ma bata ji tun safe da Ummah ta bata wani ha'd'den tea mai kauri tasha har yanzu bata ji yunwa ba, sai 'kirjin ta dake 'dan yi mata zogi saboda cikar da sukayi.
Matar ne tace ko zata bashi yasha da yake tun safe daga zam-zam babu abinda ke cikin sa, take Teemah sai ta jijjiga kai alamar "ah ah" matar ma bata matsa mata ba cuz tayi zaton ko zuwa an jima zata bashi.
Kamar wasa kuwa har yamma Teemah bata bawa baby mama yasha ba wai tana tsoro yana mata zafi.
Ummah bata so ta matsa mata itama dan haka kawai sai ta bar ta, amma abin na damun ta azuci.
Da yamman aka sake yiwa baby wanka yana ta faman kaiwan hannun sa baki yana 'ko'karin tsotsa, tausayin shi sosai yake kama Ummah amma bata san yanda zata yi da Teemah ba sam, ko da aka gama shirya shi sai aka bashi ruwa yasha, yana sha kuwa tale sai ya koma bacci abin sa.
Itama Teemah wankan ta sake yi bisa jagorancin wata dattijuwar mata tayi shirin ta cikin riga da zani na atampa tayi simple 'dauri ba na 'daga hankali ba daya ke ma ba wani da'di sosai take ji ba shiyasa powder kawai ta murza a idanun ta tare da sanya kwalli, sai uban turaruka data ringa fesawa ajikin ta kamar baza su 'kare ba.
Fita sukayi dukkan su suka bar Hannah da Teemah a 'dakin yayin da ta sa Babyn agaba ta zuba uban tagumi, so da tausayin sa na ratsa ta, sai ta kamo hannun sa ta ri'ke cikin nata tare da kwantar da kanta agafen sa tana kallon fuskar sa, ita kanta tausayin sa take ji sosai amma tana tsoron sa mishi maman abakin shi dan yanda take jin yake yi mata zogi, koda za'a wanke ma da yamman nan har kuka tayi saboda zafi da zogi gashi sai 'kara cika yake yi base k'aramin takura ta yake yi ba.
Yayi baccin a'kalla mintina kusan hamsin kafin ya farka, sai kuma ya tashi da kuka, wanda ya rikita Teemah ta rasa ma ko ta yanda zata 'dauke shi dan haka kawai itama sai ta sanya kukan.
Hannah ce dake bayi tayi saurin fitowa ta 'dauke shi ta fara jijjiga shi amma kamar ziga shi take 'kara yi kukan nasa sai 'kara 'karfi yake yi ga dukkan alamu an 'kure ha'kurin sa ne.
Hannah tayi-tayi da ita ta bashi yasha amma ta'ki sai kuka kawai takeyi.
A haka Ummah ta shigo ta same su, sai tace
" wai ya akayi ne? Ya tashi ko?"
Hannah ce dake hautsine ta bata amsa da fa'din
" ehh ya tashi Ummah".
Kar6an sa Ummah tayi itama ta 'dan jijjiga shi da kukan ya 'dan ragu sai ta kifa shi akan 'kafafun ta tace da Teemah
" Yunwa fah yaron nan yake ji kar ashi ga hakkin sa dayawa ki daure ki bashi yasha kinji".
Kai Teemah ta 'daga wa Ummah kamar da gaske.
Ummah sai ta 'dago shi ai kuwa kamar yana jira sai ya saki wani sabon kukan kuma, mi'kawa Teemah shi tayi tace
" yauwa Fateemah maza bashi 'kilan zai yi shiru"
Ummah da kanta ta dai-dai ta mata zaman yaron a cinyar ta sannan ta koma gefe.
Teemah kam a hakan ta rungume shi tana bin bakin sa da kallo yanda yake kukan hawayen ta na cigaba da sau'ka.
Ganin hakan ne yasa Ummah ta fice tunanin ta wai ko kunyar ta ne yasa Teemahn ta'ki bashi a lokacin dan haka sai ta fita ta bar su da Hannah a 'dakin.
Hannah kam gaba 'daya taji zuciyar ta ya karye da kukan yaron ita kanta ji take tamkar ta taya shi kukan amma sai ta daure batayi ba.
Zama tayi agefen Teemah ta ringa bata baki akan ta taimaka ta daure ta bashi kar kukan yayi masa yawa daga zuwan shi duniya ya yi sabo da kuka.
Rashin kautawar ta tagani ga tausayin yaron ta daya cika ta dan haka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 61 Chapter of 67