Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daga gare shi koda kuwa zasu dawwama ahaka ne bazata damu ba. Abbas ma kansa wannan moment 'din yatafi dashi he wish da ace Rivers zai koma da babu abinda zai hana shi 'dauke matar sa su tafi, shi ka'dai yasan yanda yayi kewar ta a wata 'dayan nan, bai ta6a zaton zaiyi missing komai nata har haka ba sai daya tsinci kansa acikin damuwa sosai da rashin ta, yarinyar ta, rashin jinta, 'kun'kunin ta, 'dan 'karamin bakin ta na rashin kunyan nan, jikinta da komai nata kafin ya ya gama amincewa zuciyar sa cewa itace farin cikinsa, haushin 'kin binsa datayi kuwa har yaso ya ninka haushin daya shiga lokacin da aka bawa marigayi ita suka tafi. Yanzu kuwa da yake da ita a gidan sa take kuma kwance akan 'kirjin sa sai yake jin kaf duniyan nan bayaga ahalin sa baya jin akwai abinda yakai girman matsayin ta a zuciyar sa. *4:30pm* Yabar gidan domin flight 'dinsa na zuwa Ekiti 'karfe 5:00 ne inda suka rabu da matsananciyar kewar junan su afili da kuma zu'katan su. 5:28pm Hannah ta dawo gidan sai taga Teemah cikin annashuwa ko bata bu'di baki ta fa'da ba amma farat 'daya zaka gane cewa yau walwalar ta na daban ne, musamman idan ta tuna kalmar I LUV U daya fizgo daga bakin sa 'dazun hakan ka'dai ke sata sakin murmushi, jin kanta take sosai tana jin tamkar tafi kowa she feel very exiting, wai Yayah na son ta. Hannah kam dayake bakin ta baya gani ya 'kyale sai tace da ita " _albishir 'din menene ya iso ki haka da kike irin wannan walwalar_ ?" Da sauri tace da ita " _uwar sa 'ido kawai........to Yayah ne yazo yau_ " Tayi maganar da cikakkiyar murmushi kwance akan fuskanta. Hannah 'dan gwalo idanu tayi tace " _dan Allah?_ _Kice intattara in koma kunkumin uwata_ " Hannah tayi maganar tare da mi'kewa tsaye dayake dama a parlour suka zauna. Dariya ka'dan Teemah tayi tace " _sai ki je 'din kuma ai, abinda har ya tafi ma_ " " _Haba dan Allah dagaske, shi kuma kamar ana koran sa haka?_ Hannah tayi maganar da mamaki. Teemah kam hankalin ta kwance ta bata amsa da fa'din " _Ekiti state ya nufa dama yana kan hanya ne shine fa yabiyo ta nan 'din"_ Hannah komawa tayi ta zauna da jin abinda Teemah tace, sai data zauna sannan da sigar zolaya tace " _Yayah yazo duba amarya kenan_ " Teemah cewa tayi " _To ko laifi ne yin hakan_ ?" " _Haba! wace ni ince haka? Ai ban isa ince laifi bane dan ban san sirrin dake 6oye bayan wannan gagarumar fara'ar_ _ba, abinda kawai nasani shine rai yasamu abinda yake so that's all_ " Fa'din Hannah kenan tana watsa hannu sai Teemah ma tace " _toh ya za'ayi ne Hannah abinda yafi haka ma inajin idan_ _nayi ai ba laifi bane, mijina ne fah Hannah tsawon wata guda bangan shi ba..._ " _hmmm bazaki gane yanda nayi kewar sa bane yarinya_ " Ta 'karashe da murmushin tsokana. Hannah ma murmushin tayi tace " _ke kika so hakan ai, amma yanzu da kika ganshin fah_ ? Da sauri Teemah ta tare ta fa'din " _sai naji tamkar kar yatafi wallahi_ " Baki Hannah ta ta6e tace " _ehh lallai yarinya kin hau layi Yayah ya koya miki halin sa ni dai ba ruwana_ " Dariya ma tabawa Teemah wanda cikin dariyar ta furta " _dai-dai kenan, ai baki san wani abu ba Hannah? har fa da kyautar I LUV U na samu yau daga wurin sa_ " Ido Hannah ta zaro tana dariya tace " _kice dara taci gida kenan_ ?" Dariyan sukayi dukkan su, suka sha hannu cikin so da 'kaunar junansu. (TeemHan) ***** Yanzu kam sau 'daya yake 'kiran ta a duk lokacin da ya samu dama wata rana kuma ma ko 'kiran nata baya yi. Haka kuma salon 'kiran nashi bai canja ba sai ma abinda ya ragu dan yanzun baya fin 2-3mins kullun idan ya 'kirata saboda abin da yake gabansa, daga gaisuwa baya jan magana ahakan ma yafi yin 'kiran da dare wani lokaci ma har sai tayi bacci kafin ya 'kira da safe ne kawai take ganin missed call. Tana kuwa jin haushi sosai idan hakan yafaru kuma ko ta 'kira shi baya 'dagawa har sai lokacin da ya ga dama sannan sai yayi calling nata back, daga baya ma sai ta ha'kura ta daina 'kiran nasa gaba 'daya. Shikuwa Abbas rashin sakewa da ita a wayan ya samo asali ne da kasancewar Hannah na tare da ita, sam baya iya tambayar ta komai daga yaji lafiyar ta da damuwar ta shikenan dan baya so yayi wani abinda zai sa Hannah ta ringa yi masa kallon wani abu daban. Satin sa shida (6weeks) A Ekiti yanzun amma sau 'daya tak yabata daman zuwa gaida Ummah tun farkon tafiyar sa daga nan bai 'kara barin taba, takan yawai ta mamakin hakan aran ta sau da dama Hannah ce ke 'dan wayar mata da kai akan wasu abubuwan da suka shige mata duhu. Damuwar ta 'daya yanzun shine yanda 'karfi da yaji ta zama chop-chop daga wayewar safiya zuwa dare tana cin abinci a'kallah kusan sau shida ko ma fi, wani lokaci har cikin dare ma yunwa na damun ta wani lokaci dole sai ta tashi ta nemi abinda zata saka abakin ta koma wani iri ne kafin take jin dai-dai. Abin na damun ta sosai musamman ma da taga sai 'kara huruwa takeyi tasan bakomai ne yake sata yin 'kiban ba sai lodin data ke yawan yi acikin kwanakin nan, bata so amma dole zuciyar ta ke tilastata yawan cin abincin. Gashi wani sa'in sai ta kasa bacci da dare sai dai tayi ta gadin Hannah har sai ta kusan raba dare kafin bacci ke 'daukan ta. Takan yawaita blaming sabon salon cin abincin datake yi yanzun game da komai dan aganin ta duk shine yake sata yawan baccin dama shiyasa ta tsani cin abu mai nauyi ita tun asali, Hannah na tafiya school itama take yin bacci dayake sai sun kammala dukkan ayyukan su kafin Hannah take wucewa shiyasa take iya yin baccin ganin babu wani aiki a gabanta, dan ma baccin nata baya tsayi dududu in tayi dayawa shine takai 30mins tana baccin. Lokacin data lura da yanda ta 'kara haske boobs 'din ta ma ya 'kara huruwa shima yawani cicciko bakin yayi ja sai abin yafara bata tsoro ma data yiwa Hannah mitan hakan sai Hannah tace " _ki bari idan Yayah ya dawo sai ki sanar dashi in ciwo ne zai nema miki magani ai, in kuma kiwona ke da kyau kinga sai in samu kyauta da lambar yabo daga wurin sa_ " Hannah na maida abin wasa kullum while Teemah kam abin har ranta yake damun ta. Ranar da zai dawo ya sanar da ita da safiyar ranar bayan har Hannah ta wuce makaranta. Ranar kuwa Teemah sam bata jin da'din jikinta sai dai bata ko sanar da Hannah ba dan kar tace bazata je school ba saboda hakan, jitake kamar anyi mata dukan tsiya a ga6o6in ta duk nayi mata ciwo. Da 'kyar ta samu ta shiga 'dakin sa dan yau 'din ko le 'kawa batayi ba, babu ma wani 'kura da yake kullun tana gyara shi yau ne kawai bata yi ba, amma duk da haka sai ta daure ta fara da tsabtace bathroom sannan ta dawo 'dakin ta share ta kunna burner tare da canja bedsheet 'din dake kan gadon ta fito ta jawo 'dakin yana tashin dadda'dan 'ka mshi. Kitchen ta shiga inda sai data samu wuri ta zauna tukunna ta 'dan huta harda maida numfashi, zazza6i ne take jin kamar zai kamata. Adaddadfe ta ha'da masa lafiyayyan abinci irin na hausawa wanda yaji kayan lambu dan ita yanzu sune cimar ta bata son ganin abinci batare da veggies ba. Juice 'din zo6o ta ha'da masa mai 'dan karan santi ta sashi a fridge abincin kuma ta kai su dinning, tana dafe kai dan sosai take jin ba da'di a duk ilahirin jikinta, gajiya take jin na damunta. Koda ta koma 'daki ma da 'kyar ta samu ta watsa ruwa tana yi tana hutawa yau ka'dai sai data fita a hayyacin ta, shirin ta tayi cikin wata doguwar rigar atampa data kama ta sosai daga 'kirji, ganin rigar zai takurata ne yasa ta cire ta canja da wata mai 'dan fa'di marar nauyi maroon colour sai ya 'kara fito da hasken ta afili. Duk yanda take jin jikinta kuwa hakan bai hana ta neman abincin ba saboda mur'dan yunwan da cikin ta keyi mata. Sosai ayyukan suka ja mata lokaci, tana idar da sallar la'asar tajiyo 'karan door bell, zuwa tayi ta bu'de 'kofan da fatan Allah yasa shine kowani wanda zai iya taimaka mata dan tasan Hannah kam da sauran lokaci tace ma zata bi gidan Ummah kafin ta dawo so zuwan ta yanzun da 'kyar ne. Cikin sa'a kuwa shi'din ne, tana bu'de wa taganshi tsaye kafa'darsa rataye da jakar sa, fuskarsa ba yabo ba fallasa koda ya gantan beyi wani reaction ba sai ma ya tsaya yana mamakin canjywar ta na yanzun. Teemah kam gaba 'daya sai tayi loosing control tasaki murmushi sai sannan ya maida mata martanin murmushin nata, dan farin ciki ma har bata san lokacin data fa'da jikinsa ba sai kuma tafara hawaye a tun safen da take jin ta wani iri 'din batayi kuka ba sai yanzu da ta ganshi, a hankali ta furta " _sannu da zuwa Yayah_ " Abbas kam fuskar sa ba yabo ba fallasa sa6anin zuciyar sa dake cike tab da farin cikin ganin ta. Bai amsa mata sannun data masa ba sai hannun sa 'daya dayasa shima ya rungume ta, jikin ta babu zafi illah 'dumi da yayi shiyasa ko'ka'dan Abbas be fahimci yanayin datake ciki ba. Dayaji sau'kan hawayen ta a'kirjin sa ne ma sai ya 'kara sakin murmushi, zaton shi duk kukan na ganinsa ne. A kunnan ta ya ra'da mata " _kin koyi rashin kunya ke ma ko? Shine harda kukan farin cikin gani Yayah_ " Duk da yanayin datake ciki amma sai datayi murmushi ta 'dan motsa ka 'dan sai ya sake fa'din " _jakata zaki kar6a nagaji sosai fah_ " Da sauri ta tashi a 'kirjin san tana mai sau'kar da idanun ta 'kasa dan kar yayi saurin fahimtar halin datake ciki. Kar6ar jakan tayi batare da ta kalli fuskar sa ba tana jin ta cikin wani yanayin farin ciki marar misaltuwa. Sanyin da ga6o6in ta sukayi ma duk sai taji ya ragu batasan dalili ba. Abbas kam 'kura mata ido yayi da mamakin yanda take avoiding ha'da idanu dashi yau 'din bai san dalilin ta ba amma sai yaji hakan ya birgeshi ganin kamar tafara yin wayo ne tunda har take kunyar shi. Cikin hakan sai kuma ya fahimci kamar akwai abinda ke damunta. Bayan ta yabi da kallo har ta shige 'dakin sa da jakar sannan ya 'karaso cikin parlourn inda ya yada zango akan kujera tare da 'daga kansa sama ya lumshe idanu, yana tunanin damuwar tata ko ta mecece oho. Wani zazzafan iska ya huro daga bakin sa take sai ajiyan zuciya ya biyo baya. Teemah bata fito ba sai da ta ha'da masa ruwan wanka sannan ta fito inda ta same shi zaune ya jingina da jikin kujera, afili ta fahimci tsantsan gajiyan daya kwaso sai taji tausayin sa sosai dan tasan irin aikin su babu sau'ki sam. Fridge ta wuce ta 'dauko masa ruwa mai sanyi da cup ta zo gefen sa ta zauna wanda hakan yasa shi ya 'dan bu'de idanu yabi jikinta da kallo. Sai data tsiyayi ruwan sannan ta mi'ka masa, ya kuwa kar6a ya shanye, koda tayi yun'kurin 'kara masa sai ya girgiza mata kai tare da mi'ka mata cup 'din. Komai cikin 'karfin hali take yinsa dan bata so tabawa 'dan 'karamin zazza6in data ke ji 'din 'kofar da zai sanya har ya dawo mata babba balle ayi mata zancen injection, she hate it at all. Cup 'din ta ajiye agefe sai ta sau'ka ta tsugunna dai-dai 'kafafun sa tafara warware igiyar boot 'din dake 'kafar sa tare da socks 'din gaba 'daya ta cire su ta matsar gefe. Tana jin 'dan nauyin sa amma haka ta daure ta kama 'kafar tasa ta dinga mammatsawa ahankali tana mi'kar da yatsun 'daya bayan 'daya. Sosai Abbas yaji da'din hakan sai ma yasake lumshe idanu yana jin tamkar karta daina yi masa. Bata wani da'de a hakan ba ta tatashi ganin agajiye yake dole zai bu'kaci freshing up saboda ya'dan warware sai ta dawo ta zauna inda ta tashi 'dazu daga gefen kujera a hankali ta fara 6alle masa botilan rigar tana 'kara sau'kar da idanun ta 'kasa. Abbas kam yana jin hannun ta a'kirjin sa ya bu'de idanu yana kallon kan fuskar ta zuwa idanun ta amma ta'ki bari su ha'da idanu. Bai hana ta ba dan yanda yake jin gajiya bai 'ki wan kan ma ta taimaka masa ba saima yake 'kara mamakin wannan sabon sauyin dayake gani daga gareta komai ma canja masa yayi, daga ita har rayuwar ta gaba 'daya. Idanun sa ya lumshe ya sake yin baya da kansa Teemah kam har ta ji da'di taci gaba da 6allewan cikin natsuwa bata sani ba ashe a hakan yake 'karewa halittar ta kallo. Gani yayi ta ko'de sosai farin ta ya 'karu, ga wani 'dan 'kiba datayi hips 'dinta ma suka 'kara fitowa sosai, aransa yace " _sam bata damuwa da rashina ji yanda tayi kyau ta 'kara 'kiba abinta ta manta dani da rayuwata."_ Har ta gama 6alle bottles 'din yana karantar yanayin ta, sai data gama kafin tayi 'karfin halin 'dago idanu ta sau'ke su akan nasa sannan tace " _Yayah saura kayi wanka ko sai kaci abinci tukunna_ ?" Bakin ta kawai ya tsaya kallo harta gama maganar bai ko yi yun'kurin nuna alamun yaji bama balle tasaka ran samun amsar ta, aransa yake tunanin.....how on earth zai gaji da kallon wannan yarin yar? Angel 'dinsa, kyautar Allah, amanar sa, matar sa, kuma 'kanwar sa, his first and last lover wacce yake fatan ta kasance uwar 'ya'yan sa gaba 'daya kuma 'kar'kashin ikon sa har abada. Acikin muryar ta ya 'dan fahimci damuwar dake tare da ita inda ya gaskata zarginsa saboda muryar ta kansa fizo shi takeyi ta harha'da kalaman data furta masa. Tana shirin mi'kewa yasa hannun sa ya janyo ta sai ta fa'do jikinsa, zafi taji acikin ta dan yanda ta tafi ba shiri da sauri ta yamutsa fuska sannan tace " _awwshhh....Ya...._ " _.......Tell me! Me ke damunki_ ?" ya tare ta da fa'din hakan. Take sai ta tura baki dan bata san me zata ce dashi yake damun ta ba. Turo bakin datayi ne yasa shi ya kai yatsan sa 'daya kan bakin ya shafa slowly tare da 'kara rage 'dan tazaran dake tsakanin su sannan ya sake fa'din " _gaya min mana inji me yake damunki ko ciwon rashin Yayah ne ya shige ki sosai haka_ ?" Goshi ta ha'de tare da niyyan fara gunguni sai yayi saurin 'daura bakin sa akan nata wanda hakan ya tilasta mata nutsuwa. Passionate kiss ya bata wanda ya matu'kar ratsa ta har cikin jikinta tare da sake matso ta zuwa jikin sa sosai. Door bell ne ya fara 'kara wanda yasa ta tafara mutsu-mutsun 'kwace jikin ta, ganin hakan sai Abbas ya sake mata bakin amma be raba jikin sa da nata ba, taga kamar baida niyyan 'kyaleta ga door bell nata bada sauti sai ta juya ta kallo 6angaren 'kofan tare da da dawo da kallon ta gareshi duk yana kallon ta. Bu'dan baki tayi zatayi wata maganar sai yasa 'dan yatsan sa akan bakin nata hakan sai yasa tayi shiru tabi hannun da kallo sannan ta kuma maida kallon nata kan fuskar sa. Sake matso da kansa yayi yabata wani peck a tsakiyan goshin ta wanda yasa ta har sai data lumshe idanu sannan yaraba jikinsa da nata sai ta mi'ke tsaye ahankali ganin ya sake ta shima take ya mi'ke tsayen kamar yanda tayi ya nufi 'dakinsa. Teemah binsa tayi da kallo har ya shige sannan tasa hannu ta 'dauki mayafin ta ta rufe kanta dashi ta tafi ta bu'de 'kofan. Tana bu'dewa Hannah tace " _hala bacci kike yi da la'asar 'din na ko, tun 'dazu fah nake ta faman aikin danna bell amma shiru_ "? _Comment Vote and Share_ *Salmerhn ku ce* ๐Ÿ˜ [10/13, 1:58 AM] ๐ŸŒธSalmerh๐ŸŒธ: ๐Ÿ’• *CAPTAIN ABBAS* ๐Ÿ’• By *Salmerh MD* Luv story๐Ÿ˜ *Wattpad @* *Serlmerh-md* ๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* ๐Ÿ’ซ We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~Dedicated to my family~ ๐Ÿฅฐ *Bismillahir rahmanir raheem* _Never be afraid to help others in their time of need. You never know when you may need that_ _shoulder to lean on_ . ๐Ÿ…ฟ *86* Muryar ta ciki-ciki tace da Hannah " _har kin dawo_ "? Hannah dake 'ko'karin shigowa tace " _ehh na dawo ai ban bi gida ba kawai na taho nan, bana ma sam inje ni ta rin'ka kora 'din_ _nan wai ita a dole ina barin ki ke ka'dai a gida_" Teemah cewa tayi " _Hmm, gaskiyar ta ne ai Hannah ba 'karya bane....._ " Hannah da sauri ta tare ta da fa'din " _Ba wani nan naga kona zauna 'din ma baccinki kike sha ki barni ina gadinki, kuma Allah ki daina_ _baccin la'asar 'din nan kin ganki ne yanzun yanda kika zama tamkar mara lafiya fa"_ Hannah ce tayi gaba sai Teemah tabiyo bayan tana me fa'din " _ai ba lafiyar ce dani ba Hannah ko dan ban fa'da miki bane shiyasa, Allah yau ban jin da'di........._ " Maganar tata tsayawa tayi dalilin cafko hannun ta da taji Hannah tayi sai ta nuno takalman data gani a parlourn a mamakance 'kasa-'kasa tace " _ya dawo ne_ ? Da kai Teemah ta bata amsa alamar " _ehh_ " Hararar ta Hannah tayi tare da sakin hannun ta, Teemah kuwa sai tayi murmushi. " _ina yake to_ ?" Hannah ta tambaya. Teemah ma sai ta bata amsa da fa'din " _d'akinsa_ " A takaice Hannah sai tace " _Ki sanar dani cewa mijin ki ya dawo ne mana kika wani barni nake ta zabgawa bacci sharri_ " " _Ke kika sani ai_ " Teemah tace tare da wucewa cikin parlourn ta kwashi takalman nasa tayi gaba dasu zuwa d'akin sa. Hannah ma d'akin Teemah ta shige da niyyan tattara kayanta ta koma gida tunda ya dawo. Shigan Teemah d'akin nasa sai ta tarar dashi har yashiga bathroom, kayan daya cire 'din ta kwashe ta fitar masa da wasu marasa nauyi riga arm less da 3quarter trouser dan taga idan yana gida da ire-iren su yafiya amfani. Fita tayi ta koma wurin Hannah anan ta same ta tana kan ha'da kayan ta. Turus taja ta tsaya tana kallon ikon Allah, data ga cewa dagaske take yi kaya take ha'dawa sai ta 'dan matso tare da fa'din " _Hannah wai miye hakan kike yi ne dan Allah_ ?" Hannah bata 'dago ba tace da ita " _inda nafi wayo zan koma ko so kike in zauna har sai mijin ki ya_ _korani kafin in tafi_ ?" Amsa Teemah tabata da fa'din " _Ce miki akayi zai koreki? Ko kin ta6a jin ya kori wani ma agidan sa ballantana kuma ke_ ?" " _ke nifah 'kyaleni Teemah gara na ware yafi, ya za'ayi gandamemiya dani kuma in zauna agidan amare_ ?" Hannah na maganar tana zuge zip 'din akwatin kayanta. Teemah kam tsaki tayi cike da haushi ta koma parlour Hannah ta rakata da murmushi tana murnar yau sai kwana a gida wurin Ummah. Teemah zama tayi a parlourn ranta duk ajagule, Bata da'de da zama a wurin ba sai gashi shima yafito cikin shigar kayan data fitar masa yana amsa waya. Sosai taji da'din hakan domin yau ne karo na farko data ta6a aikata masa irin hakan kuma tayi sa'a bai gwale ta ba. Dinning ya nufa da wayar a kunnan sa itama sai ta tashi ta bishi abaya. Koda ya isa wurin ma bai zauna ba har sai daya kammala da wayar kafin yaja kujera ya zauna. Teemah kam bata zauna ba abincin tafara zuba masa dai-dai nan Hannah ta fito. A hankali ta 'karaso wurin tayi masa barka da zuwa, Suna ha'da idanu da Teemah sai ta banka mata harara, sannan taci gaba da abinda takeyi. Hannah kam dariya ma Teemah ke bata . Abbas gaisuwar datayi masa yayi tare da tambayar ta ya makaranta. Inda ta amsa da " _Alhamdulillah_ ". " _Allah ya taimaka_ " Yace 'kasa-'kasa. Zama sukayi dukkan su bayan Teemah tagama serving nasu kafin su fara ci sai tace " _Yayah kaga Hannah ba! wai tafiya zatayi dan ka dawo har ta_ _gama ha'da kayan ta ma_ " " _Ah ah ba yau ba_ " Yace atakaice tare da saka abinci abakin sa. Teemah kam murmushi tayi itama tayi bismillah tare da fara cin abincin. Tana murmushin ta kallo Hannah da suka ha'da ido sai Hannah ma ta harareta ita kuwa Teemah tayi mata gwaliyo. Hannah bata wani ci na kirki ba ta tashi ta koma 'dakin Teemah ta turo 'kofar. Shiru sukayi kowa nacin abincin a hankali, Abbas kam ma daina cin nashi yazo yayi ya tsaya kallon ta ganin yanda take cin abincin, duk da bata ci ko rabin plate ba amma sosai yake 'kara ganin sauyi ta wannan 6angaren tattare da ita. Saboda kwanaki ba haka take yi ba. Yana ganin ta gama sai ya mi'ke tsaye ya koma parlour ya zauna, Teemah kam sai da ta tattare komai kafin ta bar wurin taje tana shirin wucewa 'dakin ta wurin Hannah sai yace da ita ta dubo masa 'dayan wayar sa a 'dakinsa. D'akin ta wuce ta fara dubawa amma bata gani ba, shima 'din yasan bazata gani ba saboda bai ajiye inda zata yi saurin ganin ba dama dagangan ya turatan dan so yake yaji 'dumin matar sa, dan haka sai ya tashi ya bi bayan ta. Ko yanzun ma waya yake amsawa wanda take kyautata zaton da abokin aikin sa ne saboda yanayin maganar dataji yakeyi, aranta tace " _wannan dai yau inajin cutar amsa wayace takama shi_ " Tsayawa tayi tana kallo da jin yanda yake maganar da ta'kama tamkar wani sarki sai kace dole aka saka shi, tana ganin ya gama sai ta kauda kanta gefe da sauri. Yana cire wayar a kunnan sa yace da ita " _come on, zo nan ki gaya min how u missed me_ " A hankali ta taho sai ta zauna agefen sa 'dan nesa ka'dan dashi. " _What is ths kuma?, bayan kin gama min rashin kunyar ki 'dazu shine zaki zo kimin wani fi'ili anan ko? Zo matso nan ki gaya min_ _wama ya koya miki......_ Tun kafin ya rufe bakinsa tace " _ni babu kowa_ " Gira ya 'dage sama yana kallon ta yace " _Really_ ? Shiru tayi ta kauda kanta gefe. Sai yace " _to naji shikenan, zo in koya miki wani da bakiyi 'dazun ba ko baki so ki koya?_ Kai ta 'daga masa alamar " _ehhh_ " Bata ankara ba taji ta ajikinsa inda yazo ya rungume ta bayan ta hannun sa daga cikinta ya sa'kalo su yayin da ya kwantar da kansa kan kafa'dar ta a hankali kamar ra'da yace " _guduna kike yi ko_ ? Kamar zatayi kuka tace " _umm-ummm_ " tambaya ya sake jefa mata da fa'din " _To meyasa baki son zuwa kusa dani?_ " _Ni....ni... bani da lafiya ne fa shiyasa....._ " " _Shiyasa kike gudun mijinki_ ? Sai tayi shiru. " _what's wrong with u then, meke damunki_ ? Sai yanzu ne tabashi amsa da fa'din " _Nima bansani ba 'dazu ne naji kamar banda lafiya amma yanzu yayi sau'ki_ " Sai yace " _muje wurin Anty nurse ta dubaki ko?_ Kafa'da ta 'daga da sauri ta kwa6e fuska sannan tace " _ai na warke yanzu_ " Hannun ta dake cikin nashi ya kamo ya 'dago shi sama ya 'kara kalla da kyau sannan yace " _Kuna sayan lightning cream kuna amfani dashi da bana nan ko_ ? " _Ah'ah_ " Tace dashi dashi. Da mamaki yace " _ya akayi haka to ke baki ga kin canza sosai ba, miye dalilin_ ?" Cewa tayi " _Nima fa bansani ba Allah Yayah_ "? Shiru yayi yana feeling 'dumin jikinta kawai sannan ya cusa kanshi 'kar'kashin wuyan ta ya sumbace ta sai ya 'dago kansa a hankali yace " _Zaki fara zuwa makaranta kema, gaya min wanne kike so kiyi_ ? Tace " _bana son ko wanne_ " " _Kamar Yayah_ ? Ya tambaya da mamaki. Sai tayi shiru bata bashi amsa

Chapter 54 of 67