ba.
Cigaba yayi da fa'din " _kin fi son kiyi ta zaman ki a gida haka kawai kenan_ "
kai ta 'daga masa up&down.
Sai yace " _saboda me to, baki ga Hannah na zuwa tana karatun ta ba......_
Taran sa tayi da fa'din
" _Ni fa banaso ne kawai Yayah_ "
Juyo da ita yayi ta fuskance shi sai yaci gaba da lalla6an ta dan ta yarda yace " _baki son ki zama doctor ne irin na Anty nurse?.......ba wahala fah idan kika gama kinga_ _sai ki haifi babyn ki dayawa ko ba haka ba?_
Teemah najin zancen baby tasaki fuska tana murmushi amma duk da haka sai tace dashi " _to ni Yayah shikenan bani da daman in zauna agida batare da yin wani makaranta ba_ ?
Idanun sa cikin nata yace " _Yes kinada shi mana, Fatima nada wannan daman a ko'ina sai dai akasin da aka samu shine ita wannan 'din Zahra_ _ce!, Zahran Abbas kuma,_
_Zahran Abbas kuwa batada wannan damar ita_ "
Baki ta turo gaba tayi fushi sai ya kamo chicks 'din ta duka biyu da hannun sa yace
" _Angel 'din Yayah a daure a cikawa Yayah wannan burin plz kinji_ "
Batayi magana ba illah bugan 'kirjin sa da tayi a hankali da hannun ta 'daya tana 'kif-'kif da idanu.
Shikuwa kamar gaske sai yayi baya akan gadon ya 'dora kansa cikin hannayen sa ya wani lumshe idanu.
Da sauri tabishi tanaq 'kiran sunan shi " _Yayah_ !
_Yayah_ !! Tare da jijjiga shi.
Abbas 'kin tashi yayi ya kuma 'kin motsawa ko ka'dan, sai daya ga ta rikice sosai sai ya 'dan bu'de idonsa 'daya ya kalleta caraf sai akan idanun ta.
Da sauri ya maida idon ya kuma rufe shi.
Ita kuwa dan mugunta harda cije baki ta kai kanta a hankali zuwa saitin fuskar sa kamar zatayi abin kirki sai kawai ta cije mai hancin sa.
Zafin dayaji ne yasa shi bu'de idanun da sauri tare da fa'din " _awwshh_ " yana shafa hancin.
Tana 'ko'karin guduwa ya cafkota take ya maida ta 'kasan sa, suka fara kokuwa tana dariya take fa'din " _Allah Yayah bazan sake ba please kayi ha'kuri_ "
Shima yace " _Babu ruwana ramawa zanyi, in ada kin min mugunta na barki yanzu kam ba'a cutata na 'kyale mutun_ "
Kokuwa suke ta faman yi kowa na 'ko'karin ida nufinsa, Teemah so take ta 'kwaci kanta dan ta riga ta gano inda ya dosa ita kuwa a yanzun bata shiryawa hakan ba musamman ma data ke 'dan jin marar ta na 'dan mata ciwo sai take jin bata son damuwa sosai yanzun, kuma tasan muddin ya raba ta da rigar ta to ba 'kyale ta zaiyi ba, bazai barta ba uwar wuya zata sha a wurinsa.
'Karfin su koka'dan ba 'daya bane dan haka tana ji tana gani ya raba ta da kayan jikin ta sai suka tsaya kallon kallo dashi, hannu takai ta rufe 'kirjin ta tana ci gaba da kallon sa.
Ganin tana rurrufe jikinta hakan yasa shi yasa hannun sa duka biyu ya bu'de hannayen ta zuwa gefe da gefen ta sai ya zuba mata idanu yana kallon canjin da jikin ta yayi.
Kwa6e fuska tayi a hankali cikin muryar shagwa6a tace " _Yayah ba nace sorry ba_ ?
Shiru yayi be kulata ba ganin haka sai ta sake ce dashi
" _Plz kayi ha'kuri ka kaji Yayah?, ina ciwon ciki fa_ "
Dawo da idanun sa yayi kan fuskarta ya kalleta, sai ta lumshe masa idanu a hankali ta kuma bu'de su alamar yayi ha'kuri.
Murmushi yayi mata dan ya gama fahimtar ta, Teemah tafiya tsoro dayawa shi kuwa baya son hakan sam.
Kansa yakai a hankali yayi kissing 'din ta a wurin wanda yasa dukkan su lumshe idanu dan dukkan su sai da kowa yaji a jikinsa.
Yana bu'de idanun sai ya sake mata hannun ta ya koma gefen ta ya kwanta, shima yana kallon ceilling kamar yadda take.
Sai yace " _wa ya fa'da miki Abbas na ha'kuri idan akayi masa laifi_ ?
" _Zuciyata_ "
ta bashi amsa a hankali.
sai yace " _to tayi 'karya_ "
Juyowa tayi ta kalle shi sai tace " _to karama_ "
" _Kin amince_ ?
Ya tambaye ta yana murmushi.
Da " _umm_ " ta amsa shi tana kallon shi.
" _Are u sure_ ?
Ya sake tambayar ta.
Kai ta 'daga masa ha'de da lumshe idanu ta kuma bu'dewa.
Sai yasaki wata munafukar murmushi wanda shi ka'dai ne yasan ma'anar ta.
Juyo da kansa yayi ya fuskance ta yana daga inda yake 'din yake kallon cikin idanun ta da nasa lumsassun idanun.
Teemah ma bata kawar da kanta ba sai suka tsaya kallon juna.
Tunowa datayi har yanzu jikin ta abu'de yake yasa ta fara 'ko'karin janyo bedsheet domin rufe jikin nata dashi.
" _Ban ce ba_ "
Yace da ita wanda still yana a yanda yake 'din bai motsa ba tamkar ba shine yayi maganar ba.
Dolen ta ta bari kamar yanda ya bu'kata 'din itama ta maida kallon ta gareshi.
Dai-dai sanda taji ya dawo kusa da ita sai ta rintse ido aranta take fa'din _innalillahi_ dan tasan yau kam mai 'kwatan ta sai Allahu, bata gama tunanin ba kawai sai taji bakin sa akan nata.
Babu abinda ya mata amma sosai ya galabaitar da ita sannan ya 'kyale ta, bakin ta har nayi mata zogi da boobs 'dinta.
Hannah bata 'kara ganin Teemah ba sai da maghrib lokacin ma masallaci ya fita sai ta samu tafito.
Already ma har Hannah tayi musu abinci tagama komai shigan ta 'daki kenan sai ga Teemah ma ta shigo a bayanta da idanun ta wuri-wuri na rashin gaskiya, ita kanta tasan bata kyau ta wa Hannah ba bayan ita ce tayi 'ko'karin ganin an hanata komawa gida, amma ai itama ba laifin ta bane laifin Yayah ne daya hanata sakat.
Murmushi Hannah tayi tace " _Amarya bakya laifi, barka da fitowa kinji_ "
Shiru Teemah kawai tayi ta wuce ta zauna sannan tace " _naga abinci a dinning wai har kin gama kirki ne bansani_ "?
" _Ehh nagama da 'din jiranki zanyi ne ko me?_ cewar Hannah, Teemah shiru tayi bata bata amsa ba.
Hannah ce tasake fa'din " _a irin hakan ne zaki wani ha'dani dashi ya hana ni tafiya dan gani banda wurin zuwa ko_ ?"
Sai yanzun Teemah ta bu'di baki tace
" _kai Hannah yau 'din nan fa ya dawo dan naje wurin sa kuma shine laifi_ ?
Hannah cewa tayi
" _Laifi nace miki kinyi ne?, ni ba damuwa ta kenan ba so nake in koma_ _nima kusa da uwata tunda kema mijin ki yadawo_ "
" _Hannah wai meke damunki ne dan Allah_ ?"
Temmah tayi maganar cike da haushi dan ta tsani Hannah tana maganar komawan nan sam ita.
Hannah amsa ta bata da fa'din
" _Bakomai dake damuna kawai so nake na baku space a gidan ku ba in zama mai gadi ba_ "
" _Hannah plz ki bar maganan nan in dai wurin Yayah ne ai kema ba'a hanaki zuwa ba_ "
Ido Hannah ta zaro sannan tace " _ni rufa min asiri ban shirya ganin abinda ya girmi tunani ba_ "
Teemah k'asa ta sau'kar da kanta tace " _naji ni dai kiyi ha'kuri karki tafi dan Allah"_
Hannah bata 'kara yi mata magana ba kawai tayi shiru tafara 'ko'karin shgia bayi.
Bawai zaman gidan nasu ne bata so ba, a ah, ita zama a gidan idan Yayah na nan ne sam ta tsana, tafi so takoma gida in yaso bayan ya tafi sai ta dawo amma duk sun ha'de mata baki sun kasa fahimtar ta, su bata damar tafiya, shiyasa take nunawa Teemah kamar taji haushin barin tan datayi ne duk da kuwa ba haka bane a zuciyar ta, in akwai wanda zaiso ganin kusancin su to be wuci iyayen su da suka ha'da auren ba na biyun su kuwa itace.
Basu 'kara ha'duwa da shi ba sai 8:00pm na dare wajen cin abinci, nan kowa ya 'dan tattaba yabari da yake bawani yunwa sosai sukeji ba.
Teemah bata 'kara komawa 'dakin sa ba shima 'din bai damu ba dan yasan dama bazuwan zatayi ba tunda Hannah na nan.
Hannah ce ma taso sata zuwa ita kuwa ta'ki tace bazata ba a haka suka kwana.
Washegari da safe data je gaidashi sai ya tsare ta da tambayar " _me yasa bata dawo jiya ba ko gudnyt kiss bata zo tayi masa ba_ ?
Sai tace " _Hannah na nan fa Yayah_ "
" _Shine me_ ?
_Ba gidanki tazo ba, ina ruwan ki da ita?, kawai kice kin fakecda ita kika gujeni_ "
" _Yayah.....!_
Sai kuma tayi shiru
tambayoyin nasa gaba 'daya sai suka mata kama dana son kai dan tasan shi babu ruwan shi ba kunya ne dashi ba.
" _Uhmm ina jinki_ "
Yace da ita.
A hankali tace masa " _ni dai kunya nakeji gaskiya_ "
Take yace da ita " _me 'karya, bayan kin gama enjoying mijinki shine kuma daga baya kike jin kunya_ ?
" _Ni ba wani enjoying 'din danayi_ ?
tafa'da tana ha'de rai.
Sai yace
" _dagaske_ ?
" _Umm_ "
tasake fa'da, sai yace " _to bari a gwada yanzu dan in sake tabbatar da gaskiyar ki_ "
Kanta ta 6oye ajikin sa tana murmushi shima 'din haka, sai yayi kissing kanta sannan ya sake rumgumar ta ajikinsa yana me cigaba da sha'kan 'kamshin jikinta a haka wani sabon bacci ya 'dauke su gaba 'daya.
Har Hannah ta wuce makaranta basu sani ba, sai da suka tashi a baccin ne kafin Teemah ta tuna da Hannah koda taje ta duba kuwa bata same ta hakan kuwa ya sanya ta taji babu da'di har aranta.
Hannah kuwa bata dawo ba koda suka tashi 'din ma gida ta wuce abinta, suka 'dai suka wuni agidan babu inda Abbas yaje sai masallaci yana idarwa kuwa yake dawowa gida.
Sai da yamma tayi lis Teemah taga Hannah bata dawo ba sannan sai hankalin ta yafara tashi dan bata saba yin irin hakan ba.
A waya tayi 'kiran ta sai Hannah tace ita kam tana gida, sai lokacin hankalin Teemah ya kwanta da taji inda Hannah take sai dai ta jinjinawa nacin Hannahn.
Da dare kuwa a 'dakinsa suka kwanta kanta akan 'kirjin sa yana ta mata mitan tazama 'katuwa wai zata 6alla masa 'kirji, ita kuwa tace dole sai anan zata 'dora kanta.
A haka suka yi baccin kuwa sai dai bai barta ba sai da ya yamutsa ta tukunna.
Sha biyun dare ta farka daga baccin shi kuwa lokacin yana kan baccin sa, amma sai da ta tashe shi dan rigimar ta, bayan ta gama 'kare masa kallo sai ta saka yatsanta acikin kunnan sa ta ringa juya wa a hankali wanda dole hakan sai da ya sashi ya farka shima.
Kallon kallo suka tsaya yi sai ya tashi ya zauna ya tambaye ta "me kuma ya hanata bacci"
Tace ita ma bata sani ba kawai takasa yin baccin ne, kuma tana jin yunwa"
Da mamaki ya kalle ta yace " _yunwa dai_ ? _Wai anya ke 'din nan lafiyar ki kuwa?_
" _Ni lafiya ta 'kalau_ " tace masa da sauri tun ma kafin abin ya kama ransa.
sai yace
" _Me kike so kici to da wannan daren dan Allah? Ki bari mana sai gari ya_ _waye inyaso sai ki nemi abincin_ "
Tace masa " _ah'ah ita dai yanzu takeso, kawai ya rakata ta ha'do tea shi ka'dai ma ya isheta_ "
Kai ya girgiza sannan ya mi'ke tabiyo bayan sa suka fita da kansa ya ha'da mata tea 'din sannan suka dawo 'dakin nasa.
Bai kwanta ba ya zauna yasa ta agaba yana tunain shikuma wannan salon daga ina tasame shi, sai kace 'karamar yarinya neman abinci da dare, sai da ta shanye tea 'din kafin yasata agaba sukayo alwala yarakata ta 'dauko doguwar riga da hijab suka tada sallah.
Addu'o'i ya dinga jerowa bayan sun idar da sallahn sannan suka koma suka kwanta.
Anan kam Abbas be barta ba har sai daya biya bashin sa na tsawon wata gudan da yayi bayanan kafin ya sarara mata, Teemah har sai da tayi dana sanin tada shi a baccin dan sosai ta galabaita a wurin sa, shikuwa banda albarka babu abinda yake sama ta.
Washe gari kuwa da wuri suka yi shiri suka tafi gida, Teemah jitake yi kamar tayi tsuntsuwa dan murna, tun bayan zuwan ta gidan sau 'daya tak ya barta ta fita kafin hakan ma kuma bata ta6a fita yawo acikin garin Abuja ba dan tana kammala iddar ta aka sake 'daura mata aure.
Sosai garin yayi mata ya birge ta taringa kallon hanya har suka isa, Ummah ma tayi farin ciki sosai da ganin su musamman dataga yanda Teemah tayi kyau ga dukkan alamu hankalin ta akwance yake yanzu, sai ma ta'kara fahimtar amincin dake tsakanin su daga yanayin su.
Hidima ta ringayi dasu kamar ta maida su cikin ta, Abbas har da tsokanan ta wai yasan badan shi take yi ba dan 'yarta ne dan haka shi babu ruwan sa baze ci komai ba.
Dariya tayi tace masa " _ai kai ka girma yanzu na yaye ka tuntuni kuma ma gara ka zage kaci tunda bana waje ka iya ci ba dan ya'ta bayan zu zata koma gidan ba balle kasa ran zata sama maka wani abin kaci_ "
" _Yace ni dai na'ki_ "
Teemah kam murmushi takeyi kawai tana kallon su suna birgeta musamman data ga yanda Yayahn yake wa Ummah sakalci son ranshi yama manta da cewa ta na wurin.
Haka suka ringa hira tsakanin su, Teemah kam bata fiya saka musu baki ba domin nauyin Ummah take 'dan ji yanzu ka'dan-ka'dan ba kamar da ba da har kwanciya take yi akan cinyar ta, hakan kuwa yasa ta kasa sakin jiki sosai, Ummah ce ma me yawan janta da hira dan kar ta zama shiru a gefe.
Daga baya Abbas ya tafi ya bar ta anan da Ummah, Allah ya taimake ta ma Hannah da wuri ta dawo.
Da suka ke6e ne sai Teemah take tsokanan ta wai " _sarkin fushi mai yaji_ "
Hannah tace " _ba fushi bane tsare mutuncina nayi kan a koroni, haka kawai sai ku ringa_ _shige wa kuna barina tamkar marainiya bayan nima inada uwata akusa, lalala kinga gara dana nemi_ _hanyata yafi min_ "
Dariya Teemah tayi tace " _ai kin taimaki kanki yarinya_ "
Hannah tace " _aww ashe kingane_ "
" _Ehh mana ai nima ba laifina bane kinsan idan ina tare da Yayah mantawa nake da kowa a_ _duniyan nan shiyasa kema nake mantawa dake_ "
Hannah dariya tayi tana nuna Teemah tace " _ai dama na ta6a gaya miki idan kika fara naki soyayyar sai kin ninkani kika 'ki yadda gashi tun ma ba'aje ko'ina ba kina confessing_ , _shine ranar har da 'kin zuwa dan wai karki barni ni 'daya ko? salon ki sa Yayah yazo ya tsaneni abanza_ _yace na ri'ke masa matarsa_ "
" _Haba kema kinsan ai yayah baze yi haka ba_ "
Cewar Teemah.
Sai Hannah tace " _ke de gama bakin ki anan wannan dodon mijin naki miye ma bazai aikata ba_ "
Teemah ha'de rai tayi tace
" _Ah ah Hannah ya haka kuma kike zagar min shi agabana dan Allah_ ? _Wanann ai cin mutuncine....ke kika san wani dodo amma ni bansan shi ba mijina ka'dai_ _nasani_ "
Dariya Hannah tayi tace " _Lallai!...... gaba-gaba dai amaryar Yayah.... kice abin ya zarce_ _tunani na, da'din abin ma dai inada Bilalu na nima_ "
Teemah ma dan ta tsokane ta sai tace " _may be shine dodon naki_ "
Da sauri Hannah tace
" _Allah ya kiyaye wallahi Bilal ba haka yake ba_ "
Baki Teemah ta ta6e ta kauda kai gefe.
Sai Hannah tace
" _ke ai baki sani ba, dana dawo fa Ummah ta tsare ni wai sai dai na koma ta ya zan taho nan da yamman Allahn nan na barki agida_ _ke ka'dai.....,dayake ban tsara fa'dan komai ba sai na rasa mai zan ce_ _mata ma sai dana ga zata fara masifa shine nace mata ai Yayah ya dawo ne shiyasa na taho_,
_Ummah najin haka kuwa kinsan shiru tayi bata 'kara yimin fa'dan ba_ "
Teemah cewa tayi
" _To dan taji ya dawo ne shiyasa tayi shirun ba dan wani abu ba dai hajiya parrot_ "
" _Ke de.... fa'di gaskiya...... malama_ "
Hannah ta yi maganar tana dariya.
Murmushi Teemah tayi tace " _Allah kin raina ni Hannah, nifa yanzu Yayar ki ce kin sani ko?...Anty_ _ma ya kamata ki fara 'kira na?_
" _Kuma gaskiyar ki ne fa Anty Fateeman Yayah_ "
Teemah sai cewa tayi
" _Yauwa ya kika ji sunan abakin ki dan Allah?_
Tashi Hannah tayi tsaye sannan tace
" _Hmmm, Allah ya shirye ki da son girma ke kam......ba nayo wanka in zo in baki labari, Bilal ya_ _kusan dawowa_ "
Tana gama fa'din haka ta shige bathroom.
Teemah kam baya tayi ta kwanta take sai fuskar Abbas ya zo ranta.
Tashi tayi ta lalu6o wayar ta ta 'kira layinsa yana 'dagawa sai yace " _y'an matan Yayah ya akayi_ ?"
Ita kanta bata san dalilin 'kiran nasa da tayi ba dan haka sai tayi shiru tana murmudhi daga 'dayan 6angaren sai ya sake fa'din " har kin fara missing 'dina ko?"
"Ah ah " tace da shi.
Sai yace " to me kikeyi yanzun?"
Da "bakomai" ta bashi amsa.
Sai yace " in zo in dawo dake gida wurin mijin ko? , ai nasan dama ba iya zaman zakiyi ba "
Tace
" _Nifa bahaka bane Yayah_ "
Tana turo baki.
Abbas cewa yayi
" _Oww murya ta kike son ji kawai_ ?"
Teemah kam kashe wayar tayi da hanzari tana murmushi, shima 'din murmushin yayi jin ta yanke 'kiran.
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce* ๐
[10/13, 1:58 AM] ๐ธSalmerh๐ธ: ๐ *CAPTAIN ABBAS* ๐
By
*Salmerh MD*
Luv story๐
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
๐ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
๐ซ
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated to my family_ .๐ฅฐ
*Bismillahir rahmanir raheem*
_The greatest thing in life is finding someone who knows all ur mistakes nd weaknesses nd still loves u nd thinks u ar d best thing in there life!_
๐
ฟ *87*
A haka Hannah ta fito daga bathroom 'din ta same ta tana murmushi ita ka'dai.
Batayi mamaki ba dan hakan sai tace " luv thing-thing"
"Ke kika sani ai amoebo"
Dariya Hannah tayi tace "na canka dai-dai kenan?
Teemah batayi magana ba sai tayi murmushi kawai ta sake d'ago wayar ta.
" _murmushin fa na menene ko duk na soyayyar Yayah ne_ ? Hannah ta tambayeta.
Teemah sai tace
" _ke ni 'kyaleni Mummy zan 'kira_ "
" _Zama ki fa'di gaskiya ai_ "
Hannah tace tana mai goge jikinta.
Teemah Mummy ta 'kira da Anty duk suka gaisa da yake tana cikin farin ciki tayi 'kiran shiyasa ta sanya zu'katan su suma cikin farin cikin sosai ganin ta saki jiki agidan ta.
Da Mummy ta tambaye ta lafiyar ta sai tace " _lafiyata 'kalau Mummy, amma yanzu kullun bana iya bacci mai kyau da dare kuma sai in tajin yunwa sosai kuma fah bana son hakan ni Mummy_ "
Murmushi Mummy tayi dan tashin farko ta fahimci meke damun Teemahn amma ganin bata sani ba itan sai Mummy ma ta bita a hakan tace da ita "bakomai ai is normal watarana bazatayi hakan ba"
Kafin tayi maganar Hannah tazo ta 'kwace wayar ta kai kunnan sannan tace da Mummy " _Allah Mummy Teemah chop-chop ta zama sai kinga yanda tazama, har ta nin kani sau biyu_ "
Hannah kam harda kari tayi dan bawani jikin kirki har na azo agani Teemah tayi ba kawai dai ta d'an canza ne kuma bai 6ata ba sai kyau da wani fresh ta sake yi abinta.
Teemah na daga inda take tace " _Allah Mummy 'karyan Hannah ne dama ita ai tsililiyace kawai tana kishi dan taga na fita kyau ne_ "
" _Hmmm, Toh Allah dai yasa lafiya ne_ "
Fa'din Mummy kenan tana murmushi.
Da haka suka gama wayar kowa na farin ciki haka kawai suka tsinci kawunansu cikin annashuwa da farin ciki mara misaltuwa.
Bayan sun gama da wayar ne Hannah ta bawa Teemah labarin zuwan Bilal, akan yace zai dawo ayi maganar auren su sai ya koma.
Teemah najin haka tace " _kice nima dai na kusa in huta da rainon ki kenan_ "
Hannah da wuri ta tare ta da fa'din " _kut amma kin gama dani wallah, ni dake waye me rainon wani fisabillahi, duk_ _wahalan da kike bani ki hana ni baccin dare ki hanani sakewa a gado shine zaki ce wani kina raino na, ni Allah ma yasa_ _Yayah ya tafi dake can garin na huta da rigimar ki_ _wallahi_ "
Musu suka hau yi a tsakanin su kowa na depending kansa kamar wasu 'kananun yara har sai da Ummah tazo sannan sukayi shiru.
Hannah da Teemah ne sukayi girki da dare, Ummah tayi-tayi su bari ko dan saboda Teemah ma amma suka 'ki, bayan sun gama suka sake yin wanka sukayi sallar maghrib da isha'i sannan suka ci abinci.
'Daki suka koma, Teemah kam ganin har 8:00 ta gota bai dawo ba sai tayi shirin bacci gashi dama duk jikinta ciwo yakei mata kamar wacce akaiwa dukan tsiya haka take ji, rigar bacci mai kyau ta 'dauka a cikin kayan Hannah tasa ka, riga da wando wanda bai gama kaiwa 'kasan 'kafarta ba, dan ita tafi son nighty mai wando dan tafi sakewa dashi.
Hannah na mata mitan an gaya mata anan zata kwana ne da har take wani saka nighty?
Da " _ehh mana baki ga dare yayi sosai bane_ " ta amsa mata tana mai cigaba da shirinta.
" _Hmm Allah yasa Yayah ya barki toh_ " kawai Hannah tace daga nan bata 'kara magana ba.
Teemah na kwanciya bacci yayi gaba da ita Hannah ce ma ta 'dan ja lokaci saboda tana duba wani handbook 'din ta.
Abbas be zo gidan ba sai kusan 9:30pm Ummah sai tace ya dubo su itama taji shiru tun 'dazu tana kyautata zaton sun riga sunyi bacci, tace dashi amma idan sunyi baccin ya 'kyale su yayi tafiyar sa.
Da " _uhumm_ " ya amsa mata bawai dan zai iya barin nata ba.
Ahankali ya tura 'kofar sai ya fara cin karo da fuskarta ta da yake basu offing switch ba wuta a kunne suka kwanta, mamaki yayi ganin yadda tayi 'da'd'daya akan gado kamar sunyi da ita akan zata kwana anan 'din.
'Karasawa yayi 6angaren da take ya tsaya,
Hannah na daga can 'dayan gefen bakin gadon ta juyawa Teemah baya.
Hakan yasa shi zama daga wajen kanta ganin Hannah bazata ganshi ba, a hankali yafara shafa gashin kanta har zuwa wuyan ta, Teemah kam har da gyara kwanciya ta 'kara gyara wa kanta matsuguni duk zaton ta mafarki takeyi, sai da ta ji abin na neman yin yawa ne sannan tafarka daga baccin, da idanuwan ta tafara motsi daga nan sai ta tashi a firgice ta zauna, ganin 'dakin da take ga kuma mutun azaune sai taji tsoro ya kamata, har ma hakan sai ya sata bu'dan baki da niyyan k'wala ihu sai yayi saurin toshe mata bakin da hannun sa 'daya sannan ya tsare ta da idanu.
Hawaye ne yafara gangaro mata a hankali idanuwan ta cikin nasa.
Tsawon mintina biyu suna a haka sannan sai ya bu'di baki in a whisper yace da ita " _let's go to our house_ "
Yana gama fa'din haka ya sakin mara bakin, sannan ya matsa ya bata daman tashi.
Teemah tana jin bakin ta ya bu'du sai tace a shi " _dare fah yayi sosai Yayah ni dan Allah ka barni anan zan kwana_ "
" _Ni kuma ban amince ba, in kuma kince ba haka ba to sai dai ki matsa min mu kwana_ _anan 'din dukan mu_ "
Ido Teemah ta ware a kansa sannan tace " _gidan Ummah ne fah Yayah_ "
Sai yace
" _Yes nasani, kinga tunda bazaki bini ba sai kawai ki matsa min in kwanta a gefenki in yaso da safe sai mu wuce idan Allah ya tashe mu_ "
Juyawa tayi ta kallo 6angaren da Hannah ke kwance sai kawai ta mi'ke tsaye tana hawayen ba'kin ciki tana 'kun'kuni.
Shima da murmushin ya bita dama yasan intji haka zata tashi da kanta ma ba sai ya sake 6ata bakin sa ba balle ro'kon ta.
Wurin kaya ta nufa da niyyar sauyawa, sai ya wuce gaban ta ya rigata isa wurin kayan, hijab kawai ya duba babba ya mi'ka mata, sai da yi ta6e baki kafin ta kar6a ta sanya, har 'kasa ya sau'ka mata kuwa taje ta dau wayarta tana huhhura hanci
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 55 Chapter of 67