gashi guri da nisa ba kusa ba balle ta je ta ganosu, bayan hakama garin ba zaman lafiya ake yi ba dole hankalin Teemah yatashi.
'Dan tunani ka'dan matar Umar tayi sai tace da Teemahn ta 'dauko wayarta suyi wani abu.
Tashi tayi taje ta 'dauko wayar sai matar Umar tace ta gwada 'kiran Mahmud su gaisa tunda basuyi waya da safiyar yau ba sai ta tambaye shi ko yanada layin Umman Abujan kode wani haka acan tace yatura mata domin tayi loosing wasu contact 'din ta kuma tana son ta 'kira su ne.
Koda ta 'kira shin kuwa sai yace bashi da numbern kowa sai na Abbas, amma zai tambaye shi sai ya tura masa idan yaturo zai mata sending.
Da " _toh_ " ta amsa masa daga nan sai ta kashe 'kiran.
Shiru matar Umar tayi tana tunanin wata mafita dan kuwa tana ganin kamar idan Mahmud ya turo numbers 'din shirinta ya wargaje, taso ne kowa ya zamana bashi da contact 'din tsakaninsu.
Teemah kuwa tsayawa tayi tana kallon ta domin jin manufar hakan daga bakinta.
Tsawon mintina biyar suna ahaka sai ga 'kiran Mahmud yadawo wayar Teemah, bin wayar tayi da kallo kafin daga bisani ta 'daga wayar ta sada shi da kunnan ta.
Daga 'daya 6angaren Mahmud jikinsa da sanyi yake ce mata " _Tayi ha'kuri zuwa wani lokaci dan Abbas_ ' _din yanzu_ yana cikin maiduguri yana kan aiki kuma anyanke gaba 'daya network 'din Borno harma da wasu garuruwan dake makwabta ka dasu, so ba zai same shi ayanzun ba sai de ko inya 'kira shi ko kuma idan yadawo sai suje gurin Abbah yabasu numbern Daddyn Abujan inyaso sai ya ha'da ta da su Hannah. Daga 'karshe yace taringa yiwa Abbas 'din addu'a pls, yanzu shima ake fa'da masa cewar maidugurin ba lafiya ahalin yanzu an kai musu harin bazata.
Teemah ji tayi hankalinta yatashi da batun Mahmud 'din na 'karshe.
Tana sau'ke wayar tafara dialling numbern Abbas amma baya tafiya, tayi harta gaji ta ha'kura.
Yanda abin ya tsaye mata kuwa har yasa tafara hawaye, yanzun hankalinta yafi kullum tashi saboda damuwarta sun kara yawaita ne musamman data ji cewa Yah Abbas na cikin maiduguri kuma ankai hari ga kuma iyayenta a damaturu kuma bata samunsu awaya ga kuma sarka'kiyar Anty to me ke faruwa ne ? Abin nan na matu'kar damunta sosai.
Da 'kyar Matar Umar ta lallashe ta ta samu ta 'dan nutsu sai ta ringa kwantar mata da hankali ta ce mata bari suyi wani game wata'kila zata samu jin labarin iyayen nata idan tayi sa'a.
Tace Teemah ta 'kira Hannah tace mata tana hanya yau zataje dubo iyayenta.
Hakan kuwa akayi Teemah ta 'kira Hannah ta gaya mata abinda matar Umar 'din ta ce ta fa'da sai taji Hannah ta rikice tana mata masifar waye yace mata ta hau hanya, tasan kuwa irin abinda ke faruwa awancen yankin, tace tun wuri ki nemi damar da zaki koma gida inba so kike kiyi tafiyar banza ba"
Cikin sanyin murya Teemah tace
" _tafiyar banza kuma Hannah, nida zanje inga mummy da Daddy nah_ ?
" _angaya miki mummy tana can ne? Me yasa baki_ _fa'dawa Ummah ba kafin ki fara shirin tafiyar?_
arikice Hannah take duk wannan maganar.
Matar umar najin haka aranta tace " _anzo gurin_ "
Domin wayar a handsfree take duk atare suke jin komai.
Suna jinta ta cikin wayar tana ta kwallah 'kiran _Ummah_ arikice, _Ummah_ !...... _Ummah_ !!......... _Ummah kinji abinda Teemah ta ke shirin_ _yi kuwa? Wai fah takama hanyar zuwa_ _damaturu ayau 'din nan._
Kar6ar wayar Ummah tayi tana kar6a itama tafara fa'din " _Fateemah meyasa kika yanke wannan shawaran batare da kin sanar_ _dani ba!_
shiru Teemah tayi Ummah kuwa sai taci gaba da magana tace " _ina Mahmud 'din yake?_
Sai alokacin Teemah tace
" _Nabarshi agida yasani a mota ne shi ya koma gida_ "
Azabure Ummah tace
" _kina nufin amota zakiyi duk wannan doguwar tafiyar_ _Fateeemah kuma ke_ _ka'dai?_
" _a ina kuke yanzun?_
Ummah tasake tambayarta.
Kame-kame Teemah tafara kamar irin zata fa'di wurin 'din nan sai Ummah ta tare ta da fa'din " _koma a ina ne ki maza ki dakatar da tafiyar nan ki koma gida dan kuwa Khadeeja basu_ ' _kasar nan a halin_ _yanzu suna Dubai"_
Wani sanyin da'di Teemah taji ya ratsata take farin ciki ya bayyana akan fuskarta tana murmushi tace " _har Dubai mummy ta tafi shine bata sanar dani ba_ _Ummah.....toh ki tura min numbernta idan na koma sai_ _in' kirata."!_
Da sauri Ummah ta tare ta da fadin
" _Ehh zan tura miki amma ki kula da zarar kun shigo cikin gari ki ce da su su sau'ke_ _ki ki nemi mota ki koma gida indai bakuyi nisa ba, in kuma_ _kunyi nisa ki iso_ _nan Abuja"_
" ah ah bamuyi nisa ba Ummah"
Teemah ta da ita.
" _toh maza ki koma gida zansa Hannah ta tura miki layin Mummyn naki_ _yanzu"_
Ummah ta 'karasa da mita inda take cewa
" _amma ni wallahi wannan karan Mahmud be birge ni ba, taya zai biye shirmenki yasaki_ _amota ke ka'dai kuma ya kwantar da hankalinsa agida_ _da sunan kinyi tafiya, wannan ai rashin hankali ne, inkin koma gida ki_ _ha'da ni dashi dan_ _Allah"_ !
Da " _toh_ " Teemah ta amsa mata sannan ta yanke 'kiran tana me farin ciki da wannan al'amarin har tsalle ta buga ta rungume matar Umar da 'karfi tana me zuba mata ruwan godiya da wannan babban kyautan datayi mata, itama dariyar takeyi tana me nuna farin cikinta afili ganin yau Teemah tasaki ranta sosai.
Mintina biyu basu cika ba taji wayar ta tayi 'karan shigowan text, da sauri ta 'daga ta duba sai kuwa taga international number aka turo mata harda 'karamin plus a afarkon numbers 'din.
Godiya ta 'kara yiwa Allah tare da fa'din " _Yah mahmud ka gafarceni na maka sharri nasan yanzun zuciyar_ _Ummah acike take taf da jin haushinka amma_ _zan warware komai_ _daga baya_ ".
Take ta gwada 'kiran layin da aka turo matan sai kuwa taji yashiga.
" _Assalamu alaikum_ "
Tajiyo muryar Mummy na fa'din haka.
Lumshe idanu tayi sai taji zuciyarta ta karye take hawaye ya ratso tacikin lumsassun idanun ya gangaro kan kumatunta,
Ahankali tace " _mummy ke ce_ ?
Ita kanta mummy jikinta rawa yafara da jin muryar 'yar tata bayan tsawon wasu kwanaki, sai tace " _nice mamana ya kike"_
" _Mummy shine kika manta dani keda daddy kuka yi tafiyarku wata 'kasa kuka barni anan ko_ _nemana baku 'kara yi ba, mummy daman idan anyiwa mutun aure_ _mantawa ake yi dashi?,mummy ina daddy na yake inji muryarsa"_
Shiru mummy tayi tausayin 'yartata na ratsa zuciya da gangan jikinta ita ma ba 'karamin dauriya tayi ba harta kai tsawon wannan lokacin bata nemeta ba, takan yawaita jero numbers 'din Teemah kamar zata 'kira amma sai ta fasa saboda bin dokar da Daddyn yakafa mata bata son ta karya masa dokarsa har ransa ya 6aci shiyasa takasa 'kiran Teemah koda sau 'daya ne.
ahankali tafurta " _hoo Teemah irin wannan tambayoyin wanne daga ciki zan fara amsa miki?_
" _Duk kansu mummy_ "
Teemah tabata amsa cikin za'kuwa.
Murmushi kawai mummy tayi sai ta fara bata ha'kuri tana mai tambayarta yanayin zamanta da Anty da kuma mijinta. Teemah tace komai normal babu matsalar komai.
Teemah taso ta sanar da Mummy matsalar dake tsakaninta da Anty amma tana tsoron abinda ze biyo baya dan tasan mummy ba shiru zatayi ba idan taji maganar dole sai ta nemi fitar da ita daga al'amarin wanda hakan ke dai dai da tsayawar numfashinta akowani lokaci.
Suna cikin yin wayar daddy ya shigo sai kuwa mummy ta mi'ka masa wayar batare da tayi masa magana ba " _waye_" ya tambayi mummyn 'kasa 'kasa yanda mummyn ka'dai zataji shi.
Sai dai Teemah ta jiyo shi itama sai ta ce dashi " _daddy_ _nice fah_ " cikin shagwa6a tayi maganar.
" _ahh ah Angel 'dina kece yau akan layi?_
" _daddy shine kaima ka manta dani ko?_
" _Waye ya gaya miki haka? bana so mu ringa damunki ne shiyasa kika jimu shiru amma yanzu_ _ma haka ina planning zan shiga lagos 'din next_ _week"._
Take tace
" _Allah daddy dagaske?_
Murmushi kawai yai mata batare da ya yi magana ba.
Sai itace tasake fa'din " _daddy dan Allah idan kazo karka tafi bamu ha'du ba akwai maganar danake_ _so ingaya maka!"_
Sai yanzun yace
" _Toh shikenan insha Allahu zan zo har gida karki damu ki kwantar da hankalinki muma_ _bamu ta6a_ _mantawa da ke ba_ _kinji_ "
*****
Yau ba 'karamin da'di take ji ba, tana gama waya dasu ta 'kira Mahmud tasanar dashi cewa yau sunyi waya da Mummy harda daddy ma"
Tambayarta yayi taya hakan yafaru kode sune suka kirata, sai tace ah ahh ita ta 'kirasu daga nan tabashi labarin yanda akayi harma da maganar da Ummah tafa'da akansa, yana dariya yace " _lallai yarinyar nan wuyanki yayi 'karfi wato harda ni acikin shirin 'karyan_ _naki_ _ko_ ?
Dariya itama tayi tare da yanke wayar.
Ba'a jima ba sai ga 'kiran Ummah tana me sake tambayarta kota koma gidan, sai Teemah tayi mata 'karyar yanzu ta sauka za'a sata motane yanzun, sai tace idan ta koma gida zata 'kirata
" _yauwa Fateemah maza ki koma gida kinji, Allah ya tsare ya kare ya kuma_ _bada sa'a_ "
cewar Ummah
" _ameen Ummah_ , _nagode a_ ".
Farin cikin Teemah yau baya 6oyuwa yanda taji muryar iyayen nata ita ka'dai sai tana sakin murmushi musamman idan ta tuna cewa daddy zai zo nextweek sai take ganin kamar matsalarta ta kusan zuwa karshe, dan tagama sawa ranta cewar daddy na zuwa zata ma'kale masa sai ya tafi da ita ko dan ta huta da fitinar su Anty ma.
Sosai take jin farin ciki wanda hakan yagama bayyana kansa azahiri kowa ya kalleta take zai gane hakan, sai de deepdown her heart tana jin zuciyarta ajagule kamar bata da nutsuwa, da 'kyar tasamu ta lalu6o damuwar tata da dare bayan ta kwanta bacci alokacin ta zurfafa tunanin ta sai data gano 6oyayyiyar damuwar tata.
Lumshe idanu tayi take tausayin sa ya tsarga mata azuci ta ringa tuno rayuwar su dashi abaya abu na 'karshe data tuno shine ranar da za'a 'daura auren ta da Mahmud daya zo yabata gift har cikin 'dakinta.
Tsintar kanta tayi da tausaya wa rayuwarsu shida ita take ta tashi tayo alwala tazo ta tada sallah bayan ta sallame ta ringa jero addu'o'i na nema musu kariya wurin mahallici, musamman ma shi da yake fama da 'yan ta addah.
Mahmud kuwa sosai ya samu tarba wurin shehin malami kakan Umar abokinsa, yayi masa tambayoyi akan abubuwan da ke faruwa dashi, Mahmud duk yayi masa bayani.
Sosai ya jinajina wa al'amarin tare da sanar da Mahmud 'din cewa matsalarsa ba abin damuwa bace matu'kar za'a yi anfani da abinda 'qur'ani ya karantar, yace matsalar sa bakomai bace face matsalar aljanu amma da iznin Allah komai zai daidaita.
Atake yabashi wani ruwan addu'a ha'de da ganyen magarya yace yayi bismillah yasha ya kuma wanke fuskarsa.
Hakan Mahmud yayi kamar yanda malamin ya umarce sa da yi daga nan yabashi wasu addu'o'i yace ya ringa yi akoda yaushe sannan ya yaiwata yin istighfari, sadaka da neman yardar Allah akowani lokaci.
Washegari malamin ya ha'dawa Mahmud magunguna na islamic medicine tare da bashi wata jarka da ke chike da ruwan rubutu yayi masa bayanin yanda zai na anfani dasu.
Sosai Mahmud yaji da'din al'amarin harma yarasa da me zai sakawa malamin, banki ya tafi yaje ya chiro ku'di kusan 200 thousand naira ya kawo yabashi, amma fir ya'ki kar6a, sunyi-sunyi ya kar6a ya'ki Mahmud kamar ze yi kuka domin gani yayi kamar in be kar6a ba tamkar wani nauyi ne akansa.
Dayaga sun dage ne shine ya kar6i twenty thousand yace ya isa Allah ya sa adace yakuma bada sa'a, yace da Mahmud 'din shi bashi da matsala da ku'di amma ze iya ya bayar da sadakan ku'din ga koma wanene inyaga me shi nada bu'kata.
Godiyar Mahmud kamar su yi wa malamin rumfah suka masa sallama suka fito da niyyar tafiya.
Taxi suka tara suka hau tun acikin unguwa suka samu, dayake cikin unguwa ne sai suke tafiyar ahankali.
Wani gida suka wuce daf da zasu fita a unguwar ginin 'kasa duk ya lalace ma katangar gidan ruwa duk ya wanketa ta dawo yar guntuwa har kana hango abinda ke faruwa acikin gidan, 'kofar gidan ma da wani tsohon buhu aka tare shi daga shi kuwa babu komai.
Acikin 'yan sakanni Mahmud ya gama karanto fasalin gidan, take kuwa zuciyarsa ta karye, tausayin wahalar da al'ummah suke ciki duk yabi ya cika masa zuciya.
Gaba ka'dan sai yaga wata yarinya da bazata wuche 10-11yrs ba, kayan jikinta kuwa ko goge takalmansa aka ce za'a yi dasu sai ya hana ayi balle har su kasance ajikin mutun, tsabar yanda ko'diya da datti suka cikasu ko gane zanen zanin da kyau ma ba'a yi.
Dur'kushe take tana kwasan wani farin abu a'kasa hankalinta duk yabi ya tashi tana yi tana waiwaye ga dukkan alamu bada sanin ta ba ya kuskure ya zube.
Mahmud dakatar da drivern taxi 'din yayi bayan sun wuce yarinyar ka'dan, amma kafin Mahmud ya yi yun'kurin fitowa har wata mata ta fito ta iso inda yarinyar take tsugunne tana masifa itama ta tsugunna tana tayata kwasan abun.
Ahankali ya tako ya iso kusa dasu basu ma lura dashi ba hakan yasa wannan matar bata dakata da masifar datake yi ba amma ba da hayaniya takeyi ba tanayi ne yanda yarinyar ka'dai zata jita sai ko Mahmud daya musu la6e.
Jiyayi matar na fa'din " _yanzu fisabilillahi meram bazaki dinga kulawa ba, akullum_ _magana 'daya kike son inyita maimaita miki?, ke ko duba yanayin da aka samu 'dan_ _ku'din nan bakiyi kika zo kika zubar da alabon nan yanzu dan Allah a_ _ina kike so mu shiga mu samu ku'din da za'a siyi wani ga yara duk yunwa tabi ta ishesu,_ _badan albarkacin surfen nan da matar yakubu takawo_ _bama da yau Allah ne ka'dai yasan yanda zamu kasance, kuma muna murna zamu_ _samu abin ta6awa sai kizo kuma ki zubar?_
Ahankali Mahmud ya 'karaso kusa da su tsabar yanda yaji tausayinsu har idanunsa na tsatstsafo da ruwan hawaye amma be bari sun sau'ko ba kawai ya dinga fa'din _Alhamdulillah_ azuciyarsa da rufin asirin da Allah yayi musu, ha'ki'ka rayuwar bin Adama ma aya ce babba, yanda damuwoyin junanmu suka bambanta kowa da kalar tashi damuwar, kamar shi yanzu yanda Allah ya rufa masa asiri takowani 6angare bashida matsala da komai sai kawai ya jarabce shi da dakushewar wani sassa na jikinsa wanda hakan ya matu'kar 'daga masa hankali, balle wa'dannan, ya zasuji da damuwar su takasance akan rayuwa ce gaba 'dayanta, ha'ki'ka Allah buwayi ne gagara misali domin shine yayi al'kawrin jarabtar kowa daga cikin mutane harma da ajannu da kowani irin al'amari, sai de fatan Allah ya sassauta mana ya kuma bamu ikon cin jarabawar.
Adaidai lokacin ya iso kansu ya tsaya sai yaga sun ma gama kwashewa sauran wanda ya gaurayu da 'kasan ne suke sake kwasa.
_Comments Vote and share_
*Salmerhn ku ce*π
[10/2, 6:02 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
*Bismillahir rahmanir raheem*
_Before you go pointing your fingers at someone else, you may want to make sure your own hands are_ _clean............_
π
Ώ *62*
Da sauri yace " _ah ah Innah wannan ai 'kasa ce ta rage_ "
Bata 'dago taga me yi mata maganan ta bashi amsa da fa'din " ' _kyaleni yaro, inban kwashe duka ba 'dan waken ba isan yaran zaiyi ba hakan ma daya za'a ci ballantana kuma ya gaza haka_ "
Mahmud cikin tsananin mamaki yace
" _wai kina nufin wannan abin abinci za'ayi da shi Innah_ ?
Sai wannan karan matar ta dakata da kwasan abin da takeyi ta 'dago jin tambayar yayi matan kamar ta rainin hankali.
Tana mi'kewa taganshi tsaye kusa da ita ga wasu su biyu ma tsaye abayansa, ita tsoro ma ya bata dan yanda taganshin take tsoro ya tsarga mata azuci.
Hannun 'yarta takama tayi baya ka'dan sannan tajuya suka nufi gidansu da saurin gaske.
Wannan gidan da Mahmud yagani 'dazu nan yaga suka shiga shima sai ya biyo su abaya amma kafinma ya iso su har sun shige ciki abinsu.
Tsayawa sukayi suna 'dan dube-dube can suka hango wani matashin saurayi da bazai wuce shekara 20 ba yana kallon su daga 'dan nesa ka'dan.
Hannu Mahmud ya masa sai kuwa ya taho da sauri kamar dama jira yake su 'kira shi.
Yana iso wa ya gaida su suka amsa sannan Mahmud ya tambayi sunansa .
Matashin yace sunan sa _Rabi'u_ .
Mahmud ne yace " _yauwa Rabi'u dan Allah ko zaka mana magana da mai gidan nan_ "
Matashin mai suna Rabi'u yace " _Allah sarki ai maigidan ya kwan biyu da rasuwa, matarsa da 'ya'yansa ne ka'dai_ _suka rayuwa_ _agidan_ "
Tausayin mutanen ne ya sake shiga dukkanin azuciyoyin su har drivern taxi 'din.
Bayani Mahmud yayi wa Rabi'u akan abinda ke tafe dasu, nan take kuwa farin ciki ya baibaye ilahirin fuskar Rabi'u yafara yi musu godiya tunma be tabbatar da gaskiyar lamarin ba, shiga gidan Rabi'u yayi yai wa matar gidan bayani wanda da 'kyar ta amince da batun da Rabi'un yazo mata dashi, domin ita rayuwar yanzu tsoro yake bata, mutane sam babu tsoron Allah azu'katansu, dayawansu basa taimako saboda Allah sai dan su cuceka ko dan wani abu daban, ita kuwa da take ta fama tana lalla6a rayuwarta da 'yan yaranta guda hu'du sam bata son wata sabuwar fitina ta 6ullo musu.
Da 'kyar Rabi'u ya shawo kanta ta yadda ta amince da su Mahmud 'din sannan Rabi'u yakoma yayi musu iso.
Su Mahmud basu tsinke da al'amarin matar ba har sai da suka sanya kawunansu acikin gidan, inda suka ga komai kamar ba inda 'dan adam ke rayuwa ba, babu komai da zai birge mutun acikin gidan face tarkace da tsummokara, Mahmud sosai ya tausaya musu jikinsa yayi sanyi 'kalau.
Rabi'u ne da kansa ya je ya janyo wata ru6a66iyar tabarma ya shinfi'da musu suka zauna akai, ganin yanayin matar ne yasa Umar yayi mata bayani abayyane cewa ta saki jikinta karta ji tsoro sadaka suka kawo musu ba cutar da su zasu yi ba, amma intaga kamar bata yadda dasu ba har yanzun tana iya yi musu bayani sai sukoma inda suka fito.
Rabi'u ne yayi saurin taran maganar da fa'din " _ah ah ai baza 'ayi haka ba nariga nayi mata bayani 'dazun ai kuma ta fahimta_ "
Mahmud kam shiru yayi yana sauraransu yariga da yasawa ransa cewa ze taimaka musu cikin abinda Allah ya hore masa, so ko matar nan zata na dukansa tana koransa ne ba ze fasa ba.
Ku'di masu yawa Mahmud yaciro ya mi'kawa Umar shikuma ya bawa Rabi'u yace ya nemo masu gyara su 'dan 'kara tsayin katangar gidan saboda rufin asirin masu gidan, sannan yaciro wannan ku'din da malam ya'ki kar6a ya mi'kawa matar yace wannan sadaka ce taringa siyawa yaran abinci me kyau suna ci ba irin wannan ba, sannan kuma ta na siya musu omo da sabulu sunayin wanki akan lokaci, yace karta damu da 'karewar ku'din insha Allahu ze dawo ba da'dewa ba ya sake dubasu.
Kuka matar tasaki tare da godiya ta 'dago kudin ta ri'ke ahannunta hawayenta na sau'ka akansu yayinda yaranta duk suka matso sukayi jigum agefenta suna kallonta.
Tun bayan rasuwar maigidanta yauce rana ta biyu da wasu suka dube su da fuskar rahama, inka 'dauke masu basu zakkar abinci na kowacce shekara idan lokacin sallar azumi yayi Rabi'u ne mutun na farko daya taimakesu kuma yake kan taimaka musu aduk lokacin daya samu dama, domin har yau be ta6a fasa taimaka musu ba, aduk lokacin daya samu canji yakan kawo musu ku'di wataran har ledan taliya yakan siyo yakawo musu yace su dafa suci, randa hakan be samu ba kuwa yakan basu har naira 'dari yace su sayi wani abin dashi.
Atarihin rayuwarsu bazasu ta6a mantawa da Rabi'u ba, na biyunsa shine yau da wa'dannan bayin Allah suka zo suka taimaka musu, cikin kukan taketa jero musu addu'ah, " _Allah ubangiji ya saka muku da alkhairi ya haskaka rayuwarku, Allah yasa ku gama_ _da duniya lafiya, kamar yanda kuka ji 'kanmu kuka taimake mu_ _Allah ubangiji ya ji 'kanku kuma ya.........._
Da " _Ameen_ " kawai suke ta amsawa. Sai da suka mi'ke sazu tafi ne sannan Mahmud ya kalli yarinyar dayaji 'dazu mahaifiyarta ta 'kira ta da suna meram yace " _mamana ana zuwa makaranta kuwa?_
Sai data juya ta kalli bayanta dan ganin koda wa yake maganar ganin saitin ta yake kallo sai taga babu kowa agurin illah ita ka'dai, da kai ta amsa masa alamar " _ah'ah_ "
" _islamiya fah_ ?
Yasake tambayarta
Nanma ta'kara jijjiga masa kanta wanda manufar amsar duk ya bada ma'anah daya.
" _meyasa haka toh_ "
Yayi maganar tare da ya hannu.
Kafin meram tayi magana se mahaifiyarta tariga ta yin maganar da fa'din
" _kayyah 'dannan abincin daza'a ci ma daya aka samu, gagararmu yakeyi ballantana har_ _asamu ku'din biyan makaranta, wannan dakake gani......._
Ta nuna Rabi'u sannan tacigaba da fadin " _shi ka'dai yasan damuwarmu yasan halin damuke_ _ciki, shine akullun yake da burin yagama makaranta domin yasamu abinyi_ _nima kuma shi 'din nakewa addu'ah yasamu yagama koda baze taimaka mana agaba bama_ _bazanji haushi ba kokadan, domin wanda yayi abaya ma ka'dai ya isa, hakanma ya isa_ _yasa nayi ta masa fatan alkhairi har 'karshen rayuwarsa, domin Rabi'u mutun_ _ne yaro ne shi amma me zuciyar manya, burina inga Rabi'u yasamu abinda_ _yake so, amma inbashi ba mukan ai tamu rayuwar daban take, ba wai dan bandamu da_ _rashin karatun yaran bane ah' ah kawai dai inaga kamar mu'din haka Allah yaso ganinmu shiyasa ya yomu daban, kaga kuwa ai bazamu yi shishshigi wa lamarin ubangiji ba_ "
" _hakane kam Innah amma ai ba a yanke kauna da rahamar ubangiji domin idan yaso_ _akowani lokaci ya kan iya sauya ma rayuwa, kuma kinga zama hakan ba ilimi ai babu da'di_ , _duk da Allah ne dakansa ya halicci mutane iri daban daban amma kinga ta 6angaren_ _neman ilimi be bambanta mu ba yace ne kowa ya nemi ilimi.......... amma bakomai_ _nafahimci sosai.......yanzun muna kan hanya ne, da iznin Allah zan sake dawowa_ _kwana kusa insaka mamana amakaranta_ "
Ya dubeta yace " _ko_ _bakyaso_ ?
da murnarta ta bu'di baki tace " _inaso_ ".
" _Yauwa Mamana sai dawo ko_ "
Yafa'da tare da juyawa suka nufi hanyar fita matar nasake zuba musu ruwan albarka da godiya har suka 6acewa ganinta.
Rabi'u ne ya rakasu har gurin motarsu, wanda anan Mahmud ya ciro card 'dinsa yabashi yace ze iya nemansa idan ana da bu'katar wani abu kafin yadawo 'din ko kuma idan ku'din daya bashin suka gaza yin aikin yace ya'kirashi.
Sannan ya 'kara ciro 10 thousand yabawa Rabi'un yace wannan nashine ya ri'ke agurinsa.
Rabi'un ma godiya yayi yana 'daga musu hannu har motar tayi nisa ya daina hangosu.
Katin ya tsaya yana kallo aransa yake tunanin dama ashe har yanzu akwai irin mutanen nan ne aduniya, lallai kuwa Allah yayi gaskiya ha'kuri nada riba watarana, gashi yau ha'kurin innah yayi mata rana.
Allah ubangiji yasaka musu da gidan Aljannah ya biya musu bu'katunsu na alkhairi ya 'karashe da fa'din haka.
Mahmud tasha suka zarce suka nemi motan zuwa kano shi Umar, gidan kakansa Alhaji muhammad ya nema.
Alhaji muhammad ba 'karamin farinciki yayi da zuwan jikan nasa ba hakama matarsa, sosai suka rin'ka nan nan dashi, kamar su goyashi, Mahmud kansa yaji da'din hakan harma yakeji aransa dama tun farko agurin kakan nasa yatashi dayafi masa yanzun ma jiyake kamar karya tafi badan yabaro aikinsa da kuma matarsa ba da babu abinda zai sa shi komawa lagos.
Gidan 'yan uwan Anty kaf sai da ya zaga ya gaidasu kowa na farin ciki da ganinsa, musamman ma dashi 'din suka ga sam beyi halin 'yar uwar tasu ba hakan yasa suka 'kara sonshi fiye ma da mahaifiyar tasa.
Kwanansu biyu suka wuce 'kauye gurin danginsu na can, wato 'yan uwan mahaifinsa, nan ma haka suka ta hidima dashi kowa na tambayarsa iyalinshi da iyayensa, kafin yatafi sai da yabi yaraba musu ku'di 100k
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 67