tana ci,duk dama kafin ta kar6a sai yayi kusan spoon uku kafin ta kar6i daya.
Mummy bata kulasu ba,har sai da suka 'kare cin abincin kafin tafara wa Abbas fada akan shan za'kin nan dasu keyi.
mamaki Abbas yayi akan tayaya akayi mummy tasani.
kallon idon teemah yayi sai yaga ta sunkuyar da idonta 'kasa hakan ya tabbatar masa da cewa ita ta fada wa mummyn.
Aransa yace "zanyi maganinki ai yarinya"
Afili kuwa ha'kuri yabawa mummyn tare da cewa insha Allahu bazasu sakeba.
Jinsa kawai mummy tayi don tasan abu mai wahalar kenan shi ne su daina din.
Musamman ma shi Abbas din.
matu'kar Teemah zata nuna masa tana son abu toh kuwa dole na fa sai yaga ya nema mata abun ko ma miye ne shi.
"Allah yasa" ta ce sannan ta miqe ta wuce parlour tazauna a akan cough.
Abbas kuwa mummy na tashi shima ya ajiye spoon din dake hannunsa kamar dama jiran tashin nata yakeyi,sannan ya kamo kunnen Teemah da 'karfi.
Sosai taji zafin wajen
"Yayah"
Teemah tafada cikin azaba. Kamar zatayi
"Ganin dayayi tana shirin yi mai kuka ne yasashi tsare ta da idanu,tare dora dan yatsansa akan bakinsa yaqara da fadin.
"shiiiiii.......Don't let that tears out"
'Kasa 'kasa yayi da muryarshi saitin kunnanta sannan yace
"Baki jin magana ko"?
Dawuri ta jijjiga kai alamar
"a'a
'Kayi ha'kuri yayah bazan sake ba"
Ta fada tana mai kai wan hannu akan Hannunsa inda ya riqe mata
kunnan.
Tausayi ta bashi saiya sake ta da wuri.
Amma ahankali yace mata
"Wlh inbaki daina yawan gulman kinnan ba ko,zanga mai 'kara rakaki makaranta ai."
Turo baki tayi gaba don in akwai abinda ta tsana aduniya toh bai wuce Abbas ya ce bazai 'kara rakata makaranta ba.
"Nifa yayah ban fada mata ba fah,dakanta ne tasani,"da kuka ta 'karashe maganar.
Ganin haka yasa yace "toh naji ni,ya isah haka".
"Abincin ya iSheki ne?
Ya tambayeta yana mai kallon fuskarta dayake ta sa hannunta akan fuskar so baya ganin idanunta,itama bata kulashi ba.
"Ina tambayar kiii?
Ya 'kara fada cikin dan dagun murya kadan.
Tashi tayi da gudu tayi wajen mummyn tana kuka.
"Mummy kinga yayah ba"Tafada tana me dora kanta akan cinyar mummyn.
"Kun fi kusa ai mamana"
Mummyn tafada batare da damuwa da kukan da teeman keyi ba.
Don sarai tasan bai wuce akan case din shan choculate dinnan bane.
Shine har Sukayi fada akai.
'Kara powern kuka teema tayi tare bubbuga 'kafan ta akan tiles din dakin.
"Haba *TEEMAH* so kike kijiwa kanki ciwo ne ?
'Dagowa teeman tayi sannan ta ce
" mummy bashi bane?
Me yayi ne wai 'dan nawa."
Mummyn ta tambayeta tana mai kallon fuskarta.
"Wai ma bazai rakani school gobe ba.
Cewa mummyn tayi
"Kiyi shiru wasa yake miki "
Daganan mummyn takamo ta ta kwantar da ita akan cinyarta sannan tacigaba da lalla6a ta,anan kuwa bacci ya dauke ta.
Abbas kuwa tun sanda ta gudo wajen mummy shima ya tashi ya wuce dakin sa.
Harya watsa ruwa yayi shirin bacci,sai kuma yaji dai inah, hankalinsa bai kwanta ba.
sai ya fito ya dawo parlourn da sallamarsa yashigo.anan ya samesu da mummyn teema harta yi bacci.
Mummyn ne tace "yauwa abbas 'kira min fanni man tazo takaita dakinta.
kaga hartamin bacci anan tana kan rigima."
Cewa yayi "mummy bari kawai na kaita "
Owk .
"Matso wa yai ya dago ta amma sai da yayi nishi,don ba laifi teemah akwai nawi.
Da 'kyar ya 'karasa da ita dakin nata,ya kwantar da ita akan gadon yana haki.
Kafin ma ya fito sai ga fanni tashigo itama.
Cewa yayi "
yauwa saka ma ta kayan baccinta.
Sanan ya juya yatafi ko amsar fannin ma bai jira yaji ba.
Washe gari da zai kaita makarantar suna fita ya tare mai adai daita Ya 'karasa dasu makarantar.
koda aka tashi ma haka ya sa ke tare musu wani adaidaitan suka sake hawa.
Teema bata ankara ba har se data gansu a 'kofar gida kafin nan ta lura.
Aikuwa kuka tasaka tunkan ma sufito daga cikin adaidaitan.
'Dan adidaitan ne ya juyo tare da fadin
"yadai 'yan mata"
Abbas kuwa
Bai kulata ba illah ciro kudi da yayi ya miqawa 'dan adidaitan,sannan ya fito,itama fitan tayi tana qara kwa6a fuska.
"Wuce muje"
Yafada a tsare.
Yarda abin da ke hannunta tayi ta wuce ciki
da gudu,da qarfi bu'de get 'dinta ta shiga,don duk abinta tana tsoronsa wani lokacin,don inya tsare toh baya wasa .
Dagudunta tashiga gidan baba maigadi ma yana mata magana amma kota juyo.
Dayaga haka sai ya tashi ya leqa wajen shima don zatonshi ko wani abin ne yafaru.
Abbas ya hango yana tahowa hannunsa riqe da lunch box dinta data yar awajen.
"Aww ashe tare kuke ma"
Inji baba maigadi
Murmushi kawai abbas din yamasa
Sannan yawuce abinsa ciki.
Kodaya shigo bai ganta ba,sai yayi zaton ko tana wajen mummy neh.
Ai kuwa mummy tasha rigima aranar,
data gaji da rigimar ne sai ta aika aka 'kira mata Abbas.
Koda yazo tambayarsa mummyn tayi
"wai meke faruwa ne?
"Cewa yayi mummy yau ba'a siyo fruits ba ! Ya 'karashe da dariyah
Tambayarsa mummyn tasake yi
" akan me yasa toh be siya mata ba."
Cigaba tayi da cewa
"mantawa nayi ne ma ,harfa naciro kudi akan zan baka lokacin dazaka tafi dauko tan saboda rigimarta
,amma ban tuna nabaka ba har sai da ka tafi nagani,
yanama ajiye akan mirror.
Dauko ka bawa habibu (drivern gidan)yaje ya siyo mata .
Dariya ya sakeyi kadan sannan cike da mugunta yace
"Rabu da ita mummy it's her purnishment".
Cewa mummyn tayi
"kamata toh kuje can ku
'Karasa ni ta dameni da kuka.
Hannu yasa ya 'dagota sama ya fice da ita,bai ajiyeta ko ina ba sai dakinsa.
Yana ajiyeta yana fadin yarinya 'karama sai uban nawi.
Aikuwa ranar yasha rigima da 'kyar yasamu yaje ya sallaci juma'ah,saboda hayaniyar kukan da ta keyi.
Ana sallamewa kuwa ya dawo gidan da sauri,don gaba daya hankalinsa na awajenta neh.
zuwa yanzu yafara regreting din 'kin siya matan dayayi.
Yayi yayi taci abinci kuma ta'ki.
Har kusan la'asar ta 'ki nutsuwa.
Daga 'karshe tausayi tabashi sosai,haka yasa ya fita yaje gurin habibu ya bashi kudin sannan ya sanar dashi abinda zai siyo din kafin yadawo ciki.
Da 'kyar ta yadda fanni ta mata wanka kafin habibun yadawo.
Daya ke ma wurin banisa ne dashiba a 'karshen layinsu ne wajen mai fruits din,so habibun bai dade ba yadawo
lokacinma ko wankan ba'a gama mata ba.
Da fanni tagama shiryata saita kawota wurin Abbas din,Mummy kuwa duk wannan abin bata san anayi ba,alokacin mummy baccin ta ta ke yi.
Shima daya gata dawo din, tashi yayi yaje ya dauko mata ledar gaba daya ya dan'ka mata,kar6a tayi tare da fitowa parlour ta zauna akan kujera cikin sanyin jiki,kuma har alokacin bata daina ajiyan zuciyan kukan datasha ba.
Bata dade da zama agun ba bacci ya dauke ta rungume da ledar ahannunta,batare dataci komai daga ciki ba........
Koda Abbas yafito zashi masallaci sallar la'asar ne yagan ta anan tana bacci.
Yaso yatashe ta saboda baccin la'asar babu kyau,amma ganin yanayin yanda take baccin sai yaji tabashi tausayi.
Hakan yasa ya'kyaleta kawai ya yi tafiyarsa masallacin.amma kafin yatafi sai da yadawo da ita ya kwantar da itaA tsakiyan 'dakin.
Sannan yafice ya tafi.
Lokacin data tashi abaccin kuwa kamar ba ita ba,tsab ta warware,tamanta rigimar datayi.
Washe gari Saturday wuni sukayi suna buga game a 'yar 'karamar laptop dinsa.anan ma zokuga drama awurinsu kamar TOM nd JERRY.......
Sai da lokacin islamiya yayi kafin suka tashi.....amma kafinma ace sun gama shiri,sUnyi sallah,sunci abinci har sun dan shiga lokaci.
Haka ahanzarce suka fito,dole yau sai habibu yah kaisu saboda kartayi latti,don inyace yauma da kafar zasu toh kuwa ba 'karamin latti zatayi ba.
Koda suka sau'keta gida suka dawo abinsu shida habibun batare da ko sau'ka yayi a motar ba.bye bye kawai yamata tashiga ciki.
'Karfe biyar daidai yakama hanya ya koma islamiyar don ya dawo da ita gida yanda suka saba abinsu.Dayake sai 5:30 ake tashinsu.
*****
Abbas ba'ko ne agidansu teemah watansa daya kenan da zuwa gidan yanzu.
Amma idan aka lissafa a duka duka wannan shine zuwansa gidan na uku kenan akaf din rayuwarsa.
kuma tunda yazo Habibu bai sa ke kaiwan Teema makaranta ba,haka ma dauko ta,dan acewar Abbas din ahakan ne zai ga gari da kyau,amma in amota ne wai bazai gani dakyau ba.
Teemah kuwa tun ranar farko dasuka zo daidai wajen mai kayan fruits daya siya mata babana,
shikenan tasamu abinka da yarinta wai kullum
Sai an siyah mata,kullum da kalan data ke za6a,in kuwa aka 'kii siyah toh fah ranar antaro *match*............
*****
The following day kuma takama ranar sunday ne,kuma aranar daddy yayi musu zuwan bazata.
Sosai sukayi farin ciki da zuwan nashi ,musamman ma daya cika su da tsarabobi ai sai suka sake rikicewa da farin ciki......haka suka yi ta murna da annashuwa.......
Awurin cin abinci ne bayan sun kammala da abincin Daddy yasake yimusu wata bazatar kuma...,,....
Don cewa yayi zuwa ranar laraba Abbas zai tafi makaranta.
Dama hutun J.S.C.E. yakeyi,so yanzu shima zai koma SS1,already ma daddy yace an kammala masa komai ,shi kawai yarage ya tafi.............
*Yah ne readers,* *kuma nasan daddy* *ya muku* *bazata ko?*
( *Hhhh* ๐)
*don't worry just* *keep following* *ME* ........
*YANZU FAH MUKA* *FARA* .
*Ur comments is needed* ๐๐ป
nd
*Share pls*
*Salmerh md* ๐
[10/2, 5:49 PM] Ummiyo: ๐ *CAPTAIN ABBAS* ๐
By
*Salmerh MD*
Luv story๐
_Wattpad@_
_Serlmerh-md_
๐ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
๐ซ
~We are here to~ ~make you~ ~happy,smile,educate~ ~and to~ ~realized~ ~that we are the best~ ~among all~ .....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
๐
ฟ *4*
Shirye-shirye aka farayi na tafiyar abbas 'din makaranta,dayake hankali bai gama isan Teemah ba shiyasa bata wani damu da batun tafiyar ba har se ranar da ze tafin kafinnan, wato ranar laraba.
Dawuri yagama shirinsa don shima irin yaran nanne masu jarabar son makaranta.Baya wasa da harkar karatun shi tun asali,wannan halayyarsa ne tun yana yaro qarami.
Ballantana Yanzu da ya 'kara wayo sai ya fi jin yin karatun sosai.
11:00am ne flight dinsu,ba sassafe zasu tafi ba,hakan yasa yau 'din ma yace shi ne zai kaita makaranta.
Ahanya neh yake sanar da ita cewa shima fah zai tafi makarantarsu anjima,ko ajikinta bata damu ba illah cewa datayi "ai nima zan dinga raka ka kullum inzaka je"
Dariya ma tabashi shikam,dan shirman nata abin dariyah ne, wannan shi ne ana ce miki ga gabas kina 'kara tambayar ina al'kibla.
Sai da yayi dariyar kuwa sannan yace mata
" ke bafa anan bane makarantar,tafiyata zanyi nima,yanzu sai de Habibu ya rin'ka kawoki a mota kullum."
Kanta ta lan'kwasa gefe 'dayan kafa'darta tare da fadin
"hum um-hum um"
harda bubbuga kafafunta a'kasa irin na shagwa6a66un yaran,sannan tace ni banaso.
Kallonta yayi sosai dan so yake ta fahimci maganar tasa sosai amma yarinta bazai barta ba sai kawai yace mata
"dolenki ai yarinya,inkuma bahaka ba sai de ki rin'ka zuwa ke ka'dai."Kinga habibu ma huta da zirga- zirga.
Kuka tafara masa na rashin dalili,ehh mana rashin dalili,daga cewa habibu ne zaina kawota makaranta kuma sai kuka,toh danma bataga yatafi yabarta ba kenan daya zatayi. abin dariyah wai
cewa tayi .
"sai na fa'da ka da Daddy"
Batasan cewa daddyn shi ne jagoran tafiyan ba.kiyi ha'kuri karki fada ni da daddy ya fa'da da sigar yanda itama tayi magananta,ta ke kuwa yabata dariyah."me zan siyo miki idan naje makarantar ya tambayeta."ai nima binka zanyi inzaka tafin,irin yanda kake rakani,a'a nawa nikai zanje bawanda zai rakani kuma idan natafi zandade bandaqo ba.amma wannan karon bata kulashi ba don yafara bata haushi.sai kuma ta tuna fruits 'dinta
Kai ta 'daga ta kalleshi,hannunta na ri'ke cikin hannunsa suna tafiyar.sai tace toh yayah idan katafi wazai dinga siyamin Apple da pineapple harda babana ma?
Habibu zaina siyamiki kinji? Yabata amsar tambayarta ta cikin sauri. Kuka tafara masa wai ita bata son na habibun nashi take so.
suna tafiyah tana kuka,tausayinta yakeji dan yasan dolene daman taji ba da'di,shikansa ma bada'din yakeji ba don sosai sukayi sabo fiye da zaton mai karatu.
Da 'kyar ya lalla6eta tayi shiru sai da yace mata dawasa yake mata babu inda zaije.Kuma shine zai na siyamata apple 'dinta kullum.
tana jin haka kiwa kuka ya 'dauke cak.
Haka ya rakata makarantar dai dai zata shiga ya miqa mata lunchingbox 'dinta yace ta shiga class dinsu banda wasa,harta fara tafiyah sai ya 'dan 'daga 'kafa ka'dan ya iso gareta,dayake bata wani yi nisa da inda yake tsayen ba,hannunta yakamo sannan ya tsuguna dai dai tsayinta.
Sake daidaita mata 'dan Hijab 'din uniform 'din dake kanta yayi,wanda dudu-dudu bai wuce iyah kafa'dunta ba.
Kallon cikin idonsa tasa keyi itama,sai yayi murmushi ya kamo kumatunta duka biyu ya 'dan jijjiga mata fuskar
"Smile mana kin wani 6ata rai kamar an dokeki"
Dariyan kuwa tayi masa.Tana sa ke kallonsa.
"Silly girl"
Yace ahankali
yana murmushi
Hannunta ta 'dago ta danna saitin dimple 'dinsa.
Bawani zafi amma dan kawai ya 'dauke mata hankali yasa shi cewa
" kai kai,Allah yarinyan nan kin iyah mugunta"
Sai yayi kamar zaiyi kuka tare da kama gurin data danna 'din.
"Sorry yayah"
Tafada tana turo baki gaba
Sake 6ata rai yayi sannan ya ce.
"Zan ha'kura amma sai naje anmin allura idan ya daina zafi toh shikenan zan han'kura amma idan bai daina ba toh shikenan bazanma dawo ki ganni ba.
Kin yadda?
Ya tambayeta.
Kai ta 'daga masa alamar ehh tayadda.
Tashi yayi tsaye sannan yace toh ki je class,"
"barinje amin allauran ko?
Sa ke 'daga masa kai tayi
"ko zaki rakani?ya sake tambayarta
yanzunma kai ta kuma jijjigawa alamar a'a.
"To kije class anjima habibu zaizo ya 'dauke ki kinji.
Duk da kai take bashi amsa.
Sannan tajuya tanufi cikin makarantar shima bai tafiba tsaya wa yayi yana kallon bayanta harta isa bakin class din su sai ta juyo kamar tasan bai tafinba.
Hannu ta 'dago ta mai bye-bye.
Shima 'daga mata hannun yayi.
sai da yaga ta shiga class kafin shima yajuya ya kamo hanyar gida.awurin mai kayan fruits ya tsaya,alokacin ma mai kayan bai gama kintsa wurinba,haka Abbas yajirashi tsaye agefe har ya kammala gyara wurin ya kik-kintsa fruits 'din kowanne a muhallinsu kafin abbas ya matso yasiyah matah,wanda tafi ra'ayinsu daganan ya isa gidan.
Yana shiga yasamu mummy zaune aparlour tana kallon wani series,binsa tayi da kallo dan ganinsan datayi ri'ke da leda a hannu.
Dariya yayi yana kallon mummyn shima saboda irin kallon tuhumar datake binsa dashi.
"Mummy kayan Teemah ne na siyo mata don zata dawo yau bana nan"
Murmushi mummyn tayi tare da fa'din "lalle Abbas da 'ko'karinka.Kai da zak tafi har se ka biyeta kasiya mata bayan ma kawi agida.a'a mummy cewa tayi nawan tafiso." Ku kuka sani ai mummyn ta qarasa zancen nata tare da komawa ta jinginu da kujerar da take zaune akai.
"Toh kaiwa fanni tasaka mata a fridge kafin tadawo
karsu lalace dan yauma naga garin adafe yake,ragowar mafa inaga yawa ne dasu a fridge din"
Ce mata yayi
" a'a mummy wannan yafi da'di.haka yafadawa mummyn yana qoqarin barin parlourn .
"Zan gani ai idan ka tafi wa zai rin'ka siya mata mai da'din tunda namun ba da'di.
Dariya kawai yayi sannan ya 'karasa
Fita daga 'dakin,wurin Fannin ya nufa a inda yasan zai fi samunta cikin sau'ki, daga nan yawuce 'dakin Teemahn,bayan yabata ledar.
Guri yasamu ya zauna abakin gadonta ya yi tagumi.
Ha'ki'ka sabo ba da'di don yanda Abbas yakeji,jiyake kamar kar yatafi yabarta,amma bazai yiwu ba.
Sosai ya 6ata lokaci a'dakin nata amma shikanshi baisan dalili ba,illah kawai kewarta dayake ji tun kan ya tafin.
10:30 suka fita shi da daddy da mummy,Habibu ne ya kaisu airport 'din daganan ya dawo da mummy gida su kuma suka wuche Abuja.
Koda lokacin tashin su Teema yayi Habibun ne yaje ya 'dauko ta yadawo da ita gida.
Sai data gansu a 'kofar get 'din gidan habibu na danna horn kafin ta turo baki Sannan tace
"Nifah bahaka yayah yake min ba"
Juyowa yayi ya kalleta daidai anbu'de get 'din gidan.
Cewa yayi Bayan yaja motar ciki
" me yayan yakeyi wanda ni banyi ba,?
ni dama na kawoki a mota"
"shi ai yayan kullum se ya siya min fruits ahanya"
Kai kuma baka siyamin ba,ai inya dawo daga alluran sai na fa'da masa"
kuma 'dazu yace wai zaka dinga siyamin kafin yadawo"
Tafa'da masa da turarren baki irin ita adole tayi fishi 'dinnan.
"Fishi yana gaba yarinya "
habibu yafa'da azuciyarsa don yagane cewa wayo Abbas 'din yamata da sunan allura zashi.
Afili kuwa yace mata yayi " ii ha'kuri 'yar Daddy yanzu zanje insiyo miki."
"a a ni banaso na yayah nakeso ni,idan ya dawo zai siyo min ai. tafa'di hakanne bayan sun fiffito daga motan.
Aransa yace "ashe zaki jima yarinya" afili kuma ya ce mata"kinga ai kin hutar dani"
Ciki tashiga da sallamarta 'yar siririyah,bataga kowa a parlourn ba hakan yasa ta wuce 'dakin mummy.
Zuwa tayi da gudu ta rungume mummyn nata tabaya dayake atsaye take agaban ma'ajiyan kayan sawanta wata 'kila wani abun zata 'dauka ko ajiyewa dan ba kaya ta ke nema ba.
"Oyoyo mummy"
Teeman tafa'da
Itama mummyn cewa tayi "oyoyo yarinyar mummy"
Sannan ta kama hannunta tazauna akan side drawer daga gefen gado tace mata"wato yau yayah bayanan harda oyoyo na samu ko?
"Ai mummy allura yaje zai dawo yace min "
Hmm " kawai
mummyn ta ce
Rage mata kayan jikinta tayi sannan tace mata taje fanni ta watsa mata ruwa,sai ta dawo.
Fita tayi hannunta ri'ke da kayannata tashiga 'dakin ta watsa su akan gado tayi wajen fannin akitchen tasameta tana wanke wanken kayanda aka gama anfani dasu yanzu.
'Dakin suka koma fanni tamata wanka kafin su gama kuwa tasha surutu kuma duk hirar yayah ake tayi mata.
Itama fannin ta biyeta,suka tayi tare.
'Dakin mummyn suka dawo bayan fanni ta shiryata.
Mummy naganin sun dawo ta mi'ke tace suje suci lunch dan tana so ne ta'dan fita.
Harsun zauna anfara zuba abinci teemah tace ita kam a'a bazataci abinci ba pineapple ta keso.
Jin haka yasa mummyn ta fara mata masifa da 'dagun murya akan rashin son cin abincin data koya.fanni ce ta tuna da fruits 'din da Abbas ya kawo 'dazu kafin ya tafi.
Bata yiwa mummyn magana ba illah zuwa datayi ta duba,cikin sa'a kuwa tasamu pine apple 'din aciki.shikadai tadauka ta feresa mai kyau sannan ta dauko takawo wa Teemahn.
Sai da taka wo sannan mummy ta tuno dashi,Ashe fah Abbas yasiya mata kafin yatafi kamar yasan ma zata musu rigima akai.
Haka ta wuni tana shan abinta taqi cin abinci.
Da lokacin islamiya yayi habibu ne yakaita ya dawo da ita kuma.
Har washe gari bata wani damu da rashin Abbas 'dinba,don ita duk atunaninta alluran yatafi dagaske kamar yanda ya sanar da ita.kuma ai yace mata sai ya warke sannan zai dawo..........
Dataga lokaci yafara jah ne sai tafara takurawa mummyn akan ina yayan yaje?,mai yasa ya'ki dawowa?
Tun mummy na ce mata yatafi alluran itama kamar yanda Teemahn ta 'dauka harta gaji ta tafara ce mata ya tafi makaranta ne bazai dawo yanzu ba.
*Serlmerh-md*
@ *wattpad*
Vote nd share pls ๐๐ป
[10/2, 5:49 PM] Ummiyo: [3/14, 10:26 AM] ๐ธSalmerh๐ธ: ๐ *CAPTAIN ABBAS* ๐
By
*Salmerh MD*
Luv story๐
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
๐ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
๐ซ
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
Dedicated to sister Safiyyah๐Allah yabar zumunchi.๐ค
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
๐
ฟ *5*
Tun lokacin da Abbas ya tafi kuwa Teemah bata ta6a mantawa dashi ba,don mafi yawancin lokuta idan ka ta6a ta ko kamata wani abin takance "sai nagaya ka/ki da yayah,koda kuwa amakaranta ne ko gida,harta mummy da Daddy basu tsira ba,suma abu kad'an sai tace sai ta fad'awa yayah dan ita azatonta har yanzu watarana zai dawo.
Mummy bata ta6a kuskuren had'a su awaya ba don acewarta daga ta gwada k'ira mata shi sau d'aya tasan Teemah ta ringa damunta kenan kullum,shiyasa bata ma fara ba,duk da basu fasa waya da ummahn Abbas d'in ba suna wayarsu kusan kullum, haka sometimes mummy kan bata labarin irin rigimar da Teemahn keyi akan rashin ji daga Abbas d'in da batayi ba har yanzu,dariyah kawai kowaccen su keyi daga haka su shashantar da zancen.
Akwai ranar da ta ta6a saka mummy agaba da kuka wai dole suje gurin yayanta,mummy tarasa yazatayi da ita ta ce mata ai alluran nasa bai k'are ba"kuma in yak'are zai dawo da kansa,amma sam ta'ki yadda.ita wai dan dole suje su kawo shi gida,
Haka data dage sai da mummy tayi wayar k'arya ta tambaya awayar ta ce "abbas nake nema?
"Aw baya kusa?
Alluran haryanxu?
Owk toh shikenan inya dawo ace masa Teemahn shi ce ta ke nemansa.
Da mummyn tacire wayar akunnenta sai tace mata
" ai wai bayanan amma alluran ma yakusa ya k'are kuma idan ya k'are zai dawo.
Ai Teemah najin haka tafara dariyah ta fad'a kan cinyar mummyn.
Salati mummy tafara kamar gaske ,
Kai abbas d'in nan bayajin magana ,ashe yawo yatafi abinsa ya kyale angel d'ina agida.
D'ago kai Teemah tayi ta kalli mummyn
"Mummy ke ba yayanki bane?
"A'a Teemah" mummyn tafad'a sannan ta sa hannu ta d'ago Teemah ta tsayar da ita agabanta.
"Mummy yah abbas fah sunansa ke kuma kina ce mishi "Abbas"
Kumatunta mummyn takama duka 6angare biyun tana mata murmushi.
Teemah "Abbas d'ana ne ba yaya na ba.ke kuma kinga ai ke k'arama ce.K'anwarshi ko?
Kai TEEMAH tad'aga wa mummyn tana d'an smiling itama.
"Yauwa my angel
"maza jekiyi home work d'inki ko"
mummy is sleepy"
Da haka mummy tasamu ta kora ta daga wurinta dan tasan inba hakan tayi ba to hirar bazai ta6a k'arewa ba.
Teemah da fara'arta ta fita daga d'akin mummyn ta nufi nata.Yau farin ciki ta keji har aranta don yayah yace zai dawo in allurarsa suka k'are.
Ai kuwa daga ranar tafara lissafin ranar da abbas d'in zai dawo.ita kadai tayi ta ware rana amma kullum shiru ba labarinsa.
"Mummy gobe yayah zai dawo ko"?
Kullun sai tambayi mummyn,amsar mummyn kuwa baya wuce "bansani ba nima Teemah"dan bata so tafiye yi mata k'arya.
Inkuwa daddyn ta ne zai fita ce mas take yi idan yaje yadawo mata da yayah!
Shima cemata yake toh,inya dawo ta kuma tambayarsa kuma sai yace ai basu had'u bama da Abbas d'in.
Itama Teemah tun tana damuwa harta zo tadaina damun kanta akansa,takance "ai ba ruwana da yayah yanzu tunda ya manta dani yah daina sona" haka ahankali harta ha'kura ta manta dashi ma gaba 'daya,abinku da yarinta.
Hakan da yafaru kuwa ya matu'kar samawa mummy lafiya,dan acewarta itama ta huta da fitina.
Har ta gama primary tashiga Js class amma Abbas bai 'kara dawowa gidan su ba itama kuma ba'a ta'ba zuwa abuja da ita ba.Kuma zuwa wannan lokacin kwata kwata ta manta da tarihin rayuwarta tare Abbas d'in,tadai san tana da 'dan uwa amma ko da a photo taganshi bagane shi zatayi ba.
Tana Ss1 wata ranar jumma'ah tadawo gida dayake dawuri ake tashinsu. In ranar Friday neh,motar su na shigowa ta hango wata sabuwar mota a wajen parking bata san me motar ba,dan haka ta shiga parlourn da sallamarta,Daddyn Abuja tagani azaune shi kad'ai a parlourn yana waya.da fara'arta ta k'arasa inda yake zaunen ta zauna kusa da shi,daga inda ta ke zaunan tana iyah jiyo muryar wanda suke magana da daddyn,tana jin irin yanda yake yiwa daddyn nata.
Kauda kai tayi tare da ta6e baki.
Daya gama da wayar ne ya kalleta ya ce "uwata kin dawo ne"
Dariyah tayi kad'an tace "nadawo daddy ya hanya yah 'yan Abuja?
"'Y'an abuja gaba d'aya "dadyn ya tambayeta.sannan yacigaba da fad'in mamana fah ashe an girma"
Kunya taji da sai tad'an rufe fuskarta da hannunta.
Daidai nan kuma daddynta ya fito cikin shirin sa na fararan kaya.
Sai da ya iso ya zauna akujerar da take fuskantarsu kafin yace mata "ya akayi ne baga kin dawo da wuri?"
"Daddy yau fa friday kamanta ne,"
Ohh sorry haka ne fah,ashe dawuei kuke tashi,"
Na zaci ai ganin daddynki kika dawo kiyi dan kinji yazo" ya fad'a mata da sigar zolaya.
Toh aini bansan ma yadawo ba daddy waye zai fad'amin nida nake makaranta.
Nasani ne angel "
Ko daddyn naki ne yasanar da ke.
Dariya sukayi gaba d'aya daga nan ta tashi ta d'auki jakarta "daddy ina zuwa "
Tafad'a tare da barin d'akin.
Parlourn mummy tafara zuwa tana yin sallama taga ummah azaune au da mummy,yada jakar tayi ta tafi da gudu tafad'a kan cinyar ummahn tana dariyah,
"ummah na ashe harda ke akazo shine daddy bai gayamin ba?
Ai gani kinganni"
Ummahn tafad'a tana maijin dad'I har cikin ranta yanda Teemahr take sonta.
Gaida ummahn tayi tare da yimata ya hanya amma still bata bar jikinta ba.
Mummy ce tace mata
"Ai se ki d'aga ko tunda hankalinki ua kwanta,da wanne zataji da gajiyar hanya ko kuma da nauyinki"
"Katuwa da ke sai son jikin tsiyah"
Ai tana jin haka ta turo baki gaba
[3/14, 10:28 AM] ๐ธSalmerh๐ธ: "Ummah wai ni k'atuwa ce inji mummy"!
"Kyaleta mamana bawani k'atuwar da kike"Kawai dai tana fad'a ne.
"Hakama fah d'azu
naji wani ma babba dashi yana yiwa daddyn Abuja shagwa6a awaya"amma ni sai mummy tahana ni tace min wai ni k'atuwa?
Tak'arashe da turo baki gaba.Dariya ne yaso kama ummah dan tasan wannan sai aikin Abbas.
Amma afili bata cewa Teemahn komai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 67