Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mata zuciya tab amma ko dan irin yadda taga farin ciki kan fuskar iyayen nata ma dole zatayi musu biyayya dan kawai ta faranta rayukansu kuma taci gaba da ganin hakan har abada hakan ma ka'dai ya isheta. Kwance take akan gado amma hawayen ta duk yabi ya ji'ka pillown jagab kamar wanda ruwa ne ya zuba akai, ita kanta tana so ta daina kukan amma hawayen ta yakasa tsayuwa. A wannan halin Hannah ta shigo ta same ta tana kan kukan, tana jin motsin Hannah kuwa ta taso ta taho gurinta ta rungume ta sai yanzu ne sheshshe'kan ta ya bayyana, Hannah ma duk jikinta yayi sanyi sai de bata raba 'dayan biyu cewa maganar aurenta taji shiyasa take kuka, dan haka sai ta bata chance sai da tayi kukan ta isheshshe sannan ta fara bata ha'kuri wanda da 'kyar tayi shiru har sai da Hannah tace zata je ta sanar da su Mummy cewa tana kuka kafin ta 'dan sarara ta sanar a Hannah meke faruwa. Hannan bata yi mamaki ba danta riga ta sani dan haka sai ta ringa lallashinta tana bata ha'kuri har ta samu tayi shiru. Abakin Hannah taji labarin cewa Yayah Abbas shine mijin da za'a aura mata nan da kwana biyu, zuwa lokacin kuwa zuciyarta da idanunta sun riga sun bushe ta fawwalawa Allah komai, ta fahimci cewa duniya dama kowa da kalar 'kaddarar sa da Allah yake jarabtarsa dashi wata'kila nata kalan 'kaddarar kenan na fannin aure, shine *auren za6in iyaye* , hakan ma ta gode Allah tunda nata iyayen na raye kuma tasan son da suke yi mata ne duk yasa haka, tasan dayawan mutane na son su kasance tare da iyayensu ko dan su ri'ka yi musu biyayya ma amma babu su basu samu wannan damar ba kuma sunyi ha'kuri, balle ita da nata iyayen na raye toh me ze hana ta yin biyayya agare su ko dan gudun dana sani agaba ma dole zata basu farin ciki koda kuwa wani iri ne indai har tana da daman yin hakan zatayi shi koda menene kuwa. Yanzu ne ta fahimci manufar komai, yanzu ne tagane cewa gyaran amare akeyi mata wanda wasu lokuta ake ha'da ta da Hannah ayi mata a fahimtar ta dan kar tunaninta ya yi tsayi ne shiyasa ake yin hakan. Ke nan kowa ma na farin ciki da wannan auren, kowa murna yake yi akan zatayi aure shiyasa tun ranar da taga aka fara yi mata gyaran farin ciki ya sa'k'ko cikin gidan nasu, zuwan Mummy ne ma ta 'dan ga canji daga gareta dan ita Mummy bakace ga damuwar ta amma tana yawaita tunani wanda ita kanta Teemah abin na damunta. Yanzu ne ta fahimci manufar maganan Hannah da tace *nata mijin dodone* ! Tare da tunowa da kalaman Yayan ranar da zai tafi inda yake cewa ta tabbatar tayiwa maganar Daddy biyayya koda baya nan. Tarasa ina tunaninta ya tafi tun farko da batayi noticing komai akan lamarin ba. Aranar kasa bacci tayi tunanain Mahmud duk ya dameta gaba 'daya baccin da ya kamata tayi ma kasawa tayi, har kusan 2:00 am idanunta biyu. Tunowa tayi da wayarsa dake cikin kayanta tayi sai kuwa ta tashi da sauri taje ta lalu6o wayar. Tayi 'ko'karin kunnawa amma wayar akashe dan haka sai ta jona a charge ta zauna tayi tagumi agabanta. Shawara ta yanke dan haka sai ta mi'ke ta nufi bayi ta 'dauro alwala tazo ta tada sallar nafilfili bayan ta idar ta ringa jero addu'o'i sannan ta shafa. Tana idarwa kuwa sai ta fara jin bacci dan haka akan sallayar bacci yayi awon gaba da ita. Ba ita ta farka ba kuwa sai da Hannah ta tasheta cewa ta tashi tayi sallah lokaci ya 'dan ja. Hannah na idar da sallah ta tafi gurin Mummy ta sanar da ita abinda ya faru na cewa Teemah tasan da batun auren ta yanzu, Mummy cewa tayi " _dama mahaifinku yace idan yazo shi zai sanar a ita da kansa ai_ " Mummy taji da'din haka dama ita tafison asanar da ita barinta cikin duhun bashi da amfani sam. Teemah kuwa Tunda ta idar da sallah ta gama addu'o'in ta shafa sai ta 'dauko wayar Mahmud ta kunna tare da kwanciya akan gado, Gallery ta shiga ta dinga bi 'daya bayan 'daya tana kallon pictures kala-kala nashi dana wasu da bata sansu ba, sai nasu da suka 'daka tare ita da shi tare wani suna dariya wani kuma ma ba'a gida sukayi ba. Sosai pictures 'din suka tuna mata da baya ta ringa gani tana 'kara maimaitawa, sabo fil Mahmud ya dawo mata, haka mutuwar sa ma sai ta ke jin tamkar yau ne suka rabu..... Takai 1hr da wayar a hannnunta sosai ta shagala da kallon pictures 'din dama tun rasuwar sa bata 'kara bi takan wayar ba sai yanzun shiyasa duk hankalin ta ya 'dauku ga kallon hotunan kawai sai taji wayar ta 'dauki 'kara. Firgita tayi har sai da ta tashi ta zauna tarasa yanda zatayi har 'kiran ya yanke bata 'daga ba wanda atake wani 'kiran ya sake shigowa a karo na biyu duk numbern 'daya ne da na farkon kuma babu suna yafito. Daurewa tayi ta 'dauka da niyar sanar da me 'kiran cewa me wayar ya rasu 'kilan bashi da masaniya ne shiyasa. Receive ta danna tare da bu'de speaker, bata 'kai wayar kunnan ba sai ta ri'ke ahannu. Tanajin yanda me 'kiran ya furta _Alhamdulillah_ daga 'daya 6angaren ga dukkan alamu 'daukan da akayi ne yasa shi jin da'di. " Assalamu alaikum, Yalla6ai Rabi'u ne daga Katsina, kullun munata neman layinka bama samu sai yau 'dinnan, wallahi duk na damu akan baka zo kaga aikin da aka yi agidan ba, gashi da sauran ku'din ma har na sa Meram a makaranta tafara zuwa ga..... Ko sallamar be bari ta amsa ba yaci gaba da koro bayani. Cikin rawar murya Teemah ta tare shi da fa'din " _bashi bane, shi 'din ya rasu tun wata hu'du da suka wuce_ ...... Kuka ne ya kubce mata tana jin yanda me 'kiran yafara jero salati sai tayi saurin kashe 'kiran tare da kashe wayar ma gaba 'daya. Sai yanzu tunanin waye Rabi'u yazo kanta, yanzu ne ta tuna da labarinsu. Ranar 'karshe ranar da Mahmud zai rasu ma sunyi magana da shi akan komawa katsina kamar yanda yayi al'kawari. 'Kiran da Rabi'u yayi mata ne yasa kukan ta ya kasa tsayuwa ta ringa zubda hawaye tana tuna baya, dama tana tunanin Maman Amal (matar Umar) kullum, yanzu da abubuwa sukayi mata yawa kuwa jitake bau wanda tafi bu'katan ha'duwa dashi sama da ita gashi bata da contact 'din ta batada na Umar ma, cikin haka Hannah tazo tayi 'kiran ta akan cewa wai Anty ne 'kiran ta, dayake yanzu kullum da safe ne ake yi mata wankan turaren sauran duk abinda za'a mata already an gama shi tun jiya sai de abin da Anty ke bata kullun tana sha ne har yanzu bata daina bata ba. Tashi Teemah tayi tana wani kauda kanta wai dan kar Hannah ta ga hawayenta, amma tuntuni Hannah tasan kuka takeyi amma bata kulata ba, dan ita kanta tana jin tausayin ta ahalin yanzu. ***** Ana gobe 'daurin auren ne Abbas ya iso da 'karfe bakwai na dare, sai da yayi alwala ya sallaci sallar maghrib kafin ya shiga cikin gida domin gaida iyayensa da burin ganin ta azuciyarsa. Ummah kuwa sai da ta ganshi hankalinta ya kwanta saboda kafin yanzun hatta layukansa ma basa shiga, hankalinta duk ya bi ya tashi da rashin zuwan nasa tsoronta 'daya kar Abbas ya 'ki zuwa ne tasan mahaifinsa bazai ji da'din hakan ba, kuma idan har hakan ya faru kenan 'kiyayyar sa ga auren ya nuna 'karara wanda ita sam bahaka take bu'kata daga gareshi ba. Gaida su yayi gaba 'daya fuskar sa normal ba yabo ba fallasa yana yi yana rarraba idanu afakaice ko zai ganta amma be ganta ba ko Hannah ma be gani ba. Ko da ya tashi zai tafi sai Ummah ta tashi tabi bayansa awani corridor suka tsaya ta tambaye shi dalilin daya sa be taso da wuri ba tace " _harka 'daga min hankali wallahi_ _sosai na 'dauka bazaka zoba, bansan har sau nawa na gwada 'kiranka ba ayau amma duk ban same ka ba_ " Murmushi Abbas yayi mata yace " _haba Ummah zanzo mana ai Daddy ne da kansa yace in dawo_ . " _Yauwa Babana kayi ha'kuri dan Allah ka kar6i_ _auren nan da hannu bibbiyu, dama ai kace Fateemah amanarka ce, kai kace an baka amanarta tun abaya so kaga sai kaci gaba da kulawa da_ _amanarka cikin sau'ki tunda ta dawo 'kar'kashin ikon ka, dan Allah Muhammad karka bani kunya, karka_ _cutar min da yarinya kaji_ ? Tabbaci ya bata da fa'din " _Insha Allahu Ummah karki damu_ "! Albarka tasa masa tare da yi masa zancen abinci yace akwo masa coffee ma ka'dai ya isa. Ummah da kanta ta ha'da masa sannan aka fara cigiyar Hannah akan tazo ta kai masa coffee 'din da 'kyar aka samo ta a 6angaren Daddy yasa ta gyaran wasu kaya daga. Hakan yasa dole sai de Teemah ce za ta kai masa tunda kam Hannah na aiki. Tana kwance akan gado rufe ruf da blanket kanta ciwo yakeyi mata ga jikinta zafi rau amma ahakan ta aure ta mi'ke lokacin da sa'kon ana 'kiran ta ya risketa. Hijab ta zun6ula har 'kasa kan shararar rigar da ke jikinta sai ya kasance fuskar ta ne ka'dai ake gani. Ahaka ta kar6i coffee 'din ta taho zuwa 'dakin nasa. Tunani takeyi na yadda Yah Abbas zai kar6e ta amatsayin mata, sannan ga Zazza6i ciwon kai da mara da yasa ta agaba tun 'dazu tarasa yadda zatayi, Hannah taso sanar mawa ko zata samo mata magani amma tun lokacin data fara jin ciwon marar bata sanya Hannah a idanunta ba. Ahankali take tafiyar kamar bazata yi ba har ta isa 'kofar 'dakin inda tun kan ta shiga zuciyarta ya fara harbawa, ahankali ta tura 'kofar tare da yin sallama ta shiga. Abbas kam be amsa ba sai ma ya lumshe idanu aransa yace " _Alhamdulillah_ " Da ganinta, dama idanunsa da zuciyarsa ba 'karamin son ganinta suke ba. Teemah kam rashin amsawan nasa sai ya sa ta shiga ru'dani tunda tasan sarai yaji ta duk kuwa da cewa ahankali tayi sallamar amma ta tabbar yajita sai de ko in beyi niyyan amsawan bane kawai. Shi kuwa Abbas tsayawa yayi kallonta duk da ba wani wadataccen haske bane a'dakin amma kallo 'daya yayi mata yaga canjawar da tayi afili tayi wani kyau na musamman ga haske data 'kara na gyaran data sha ya kuma sake ha'duwa dana menstrual period, daya ke idan tanayi haske yake 'kara sata ka'dan. Gaban sa tazo ta ajiye 'karamin tray 'din bata mi'ke ba sai da ta gaida shi tukun na. Abbas amsawa yayi yana kallonta dan tuni ya shagala da sha'kan da'd'da'dan kamshin dake tashi ajikin ta, 'dakin bawani haske sosai illah hasken television da ke aiki kawai a palourn shi 'din ma be wani wadaci 'dakin ba dan wani guri idan aka nuno yakan yi duhu ne gaba 'daya hakan kuwa sai ya sa 'dakin ya kasance ba shida maraba da wanda babu hasken ma gaba 'daya. Lokuta da dama tana mamakin sa yanda yake son kasance wa a cikin duhu shi, kamar wani marar gaskiya. Tana 'ko'karin mi'kewa sai kamar an matsi bakinsa yace " _tafiya zakiyi kuma_ ? Fasa mi'kewan tayi sai ta koma kamar yadda take tsugunne da farko. Zazza6i takeji sosai ga ciwon kai sanadin haka kuwa har yanasa idanun ta tara ruwa. Data rasa me zatayi sai kawai ta 'dauki cup ta tsiyaya masa coffee 'din tare da mi'ka masa. Hannu ya sa ya kar6a tare da fa'din " _I thought kin manta ne ai_ " Maganar tasa bata bu'katar amsarta dan haka sai ta yi shiru. " _Wai meke damunki ne_ ? Yasake tambayar ta yana kallon ta. Tambayar kuwa sai ya sa ta sakin hawaye, da sauri ta kai hannu ta share hawayen wai dan kar ya gani amma ina yariga yagani. Zaro idanu yayi yace " _me aka miki_ ? _Ko yau 'din ma ba'a son ranki kika zo ba, nifa bance dole sai ke zaki kawo_ _min abu ba!_ _Ko wani abu na miki yanzun_ ? Girgiza masa kai tayi alamar " _ah ah_ " Hawayenta naci gaba da zuba. " _So kukan fah na_ _menene_ ? yasake tambayarta. Cikin in i nan kuka tace " _Kai...kaina ke min.. ciwo_ " Abbas be yi mamaki ba dan lokacin data mi'ka masa coffe 'din yaji 'dumin da jikinta ya 'dauka dama yasan za'a rina. Ajiye coffee 'din yayi yakai hannu ya ta6o fuskarta sai yaji zafi gau take yace " _Sabhanallah tun yaushe yafara miki?_ " _D'azu_ " tabashi amsa atakaice. " _Kinsha magani ne_ ? Ya sake tambayarta. " _ah 'ah_ " tabashi amsa tare da jijjiga kanta. Mi'kewa yayi yace mata " _tashi muje_ " Yayi maganar yana fita daga 'dakin, itama Teemah sai ta bishi abaya a hankali dan har jiri takeji yana 'dibanta, hatta haske bata son gani dan sai taji idanunta na mata zogi sosai. Wurin driver ya wuce ya kar6o key sannan ya nufi gurin motar har ya bu'de zai shiga kuma sai ya tuna wani abu. Jiranta yayi sai data iso sannan yace mata " _zonan wato dana tafi bakya cin abinci sosai ko_ ? Shiru tayi masa tana rarraba idanu. Tsaki ka'dan yaja sannan ya juya ya shiga motar tare da tada ta. Teemah ma shiga tayi yaja suka fita daga gidan. Sai da yabi da ita wani eatry yasata dole sai da ta 'dan ta6a abinci tukunna kafin suka wuce inda zasu. Wani 'karamin private clinic dake kusa dasu ka'dan ya kaita. Suna zuwa kuwa suka samu wata nurse ce a duty dan haka itace ta duba Teemah. Abbas kam kamewa yayi akan kujera yace Teemah tafa'di abinda ke damunta wa nurse 'din. Nurse 'din itama murmushi tayi tace " _meke damunki ne_ _'yan mata_ ? Ahankali Teemah ta bu'di baki tace " _Zazza6i nakeji da ciwon kai da....da kuma...._ Kasa 'karasawa tayi sai ta 'dan saci kallon Abbas sai taga shikan idanunsa nakan wayar sa ne. Muryar Nurse 'din tasake ji tana fa'din " _inajinki, da me kuma?_ Sai da sake kallonsa kafin ta fisgi maganar tace ".... _da...Menstrual_ _pain_ " Tana gama fa'di sai ta wani rintse idanu da 'karfi. Abbas kam murmushi yayi ganin akan wannan abin take wani jan magana. Nurse 'din ma murmushi tayi mata tace " _kina jin kunyar_ _Yayah ko_ ? Bata kulata ba sai ta kauda kanta gefe. Tashi Nurse tayi taha'da mata magungunan da suka dace, taso tayi mata allura amma Teemah tace bata so, harta fara lalla6ata sai Abbas yace abar alluran kawai tunda bata so. Koda suka koma gida kuwa be barta ba sai da ya tabbatar tasha maganin ta tukunna , tana shiga 'dakin su kuwa ta tarar da Hannah tsaye da waya a hannunta Anty ma na zaune a gefen gado ta zubawa Hannah idanu. Sallamar ta ce ta dawo da hankulansu gareta Hannah harda ajiyan zuciya Anty kuwa da sauri ta zo ta tareta. Hannah ce ta jefa tambaya tace " _Teemah ina kika shiga dan Allah duk kinbi kin 'daga mana hankali_ _gashi mun ta 'kiran wayarki bakya 'dagawa har 'dakin_ _Yayah naje fah ban same ki ba?_ Teemah da dafe kai tace. " _Wayar na nan 'ka'kashin pillow ne kuma tana silent_ " Anty ne ta taho da sauri ta ri'ke ta tare da fa'din " _Fateemah meya faru kuma naji jikinki da zafi_ _sosai_ ? Ledan magungunan ta 'dago ta bawa Anty a hannunta tare da fa'din " _Anty clinic mukaje_ _da Yayah_ " daga nan ta basu labarin zazza6in daya dameta 'dazu. Anty kar6a tayi da mamaki tace " _Ya akayi baki sanar da_ _kowa ba toh_ ? Tana shirin yin magana Anty ta dakatar da ita da fa'da akan shirun da tayi bata sanar musu halin da take ciki ba, tace karta sake yin irin haka yanzu ba dan shi Abbas 'din ya lura ya tari abin ba da tasan meze faru ne? Su suna can suna shirin biki while ita wacce akeyi domin tan kuma tana nan tana fama da jinya ina anfanin haka? Ha'kuri Teemah tayita bawa Anty tace bazata sake maimaita irin haka ba. Anty bata bar 'dakin nasu ba sai da ta tabbatar da sassaucin zazza6in kafin nan taje ta kwanta itama. Abbas kam da kansa yazo ya duba ta lokacin 'karfe 11:48pm su suna ma bacci basu san yazo ba, ganin tana bacci yasashi jan 'kofar ya rufe ahankali tare da hamdala dan yasan zazza6in ya sau'ka kenan tunda har tasamu tayi bacci, yaso ya shiga ya ta6a yaji lafiyar jikin amma saboda kasancewar Hannah na 'dakin yasa kawai ya juya batare da ya shigan ba. ***** Washegari yakama ranar Friday wanda ya kasance aranar jama'ah da dama suka shaida 'daurin auren Muhammad Abbas Al'hassan tare da amaryar sa Fateema Kabeer inda yasamu hallatar alummar musulmai da dama dayake a masallaci aka 'daura auren bayan an idar da sallah juma'ah. Abbas kam farin cikinsa ba ze ta6a misaltuwa ba domin shi ka'dai ne zai iya fassara irin yanayin daya shiga alokacin daya ji an sar'ke sunansu waje guda, godiya kawai ya ringa zubawa mahalicci dan bashi da abin da zai iya furtawa bayan haka. *Wash Allah na nagaji sosai............Dan Allah readers ku taimaka inga ruwan comments in ba haka ba ni daku sai jibi ko ma monday wallahi.* _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _No man succeeds without a good woman behind him......either Wife or mother, if it is both, he is twice blessed indeed_🀞🏻 πŸ…Ώ *76* Haka a gida ma da yawan mutane na farin ciki da wannan aure sai faman sanya albarka akeyi. An shirya Teemah cikin wata doguwar riga mai kyan gaske kalar touqoise blue da ratsin golden, rigar ta kama ta sosai daga 'kirji 'kasan rigar kuwa abu'de yake ba 'karamin fito da kyaunta rigar tayi ba. Hannah kam yau ba ta jin gari, tunda aka 'daura auren ta fara 'kiran Teemah da suna _amaryar_ _Yayah_ , Teemah tun tana mitar bata so har ta ha'kura tayi shiru balle da taji kanta yafara sara mata ai tuni sai ta nemi 'dakin da aka sau'kar da Mummy ta shiga da niyyan hutawa. Mummy kam korota tayi tace maza taje cikin 'yan uwanta ta zauna bata son zama shirun nan. Fuskar shagwa6a tayi tace " _Allah Mummy kaina ke ciwo ne shi yasa_ " Mummy tace taje yanzu ta 'dau maganinta tasha ba jiya an siya miki magunguna ba, hayaniya ne ke saki ciwon kan ba komai ba. Fita tayi taje 'dakin su nan ta samu Hannah da 'kawayenta sai ihu sukeyi, haka ta zauna agefensu tayi shiru bata kula su amma duk yadda Hannah tasan zata takalo ta tasata magana sai tayi. 'Karfe uku nayi duk suka wuce gidajensu da sunan zasu je kowa ta yo shirin walima su dawo. Hannah ma kasuwa ta shiga aka bar Teemah ita ka'dai. Taji da'din raguwar hayaniyan amma kuma sai ta ringa jin zazza6i na son taso mata. Zama tayi a'dakin nasu ta'ki zuwa ko'ina kuma ta'ki shan maganin ma . Kafin yamma kuwa zazza6in Teemah sabo fil ya dawo ga jiri dake faman 'diban ta har bata iya tsayuwa da kanta sai ta kama abu, gaba 'daya ta fita a hayyacinta. Anty ne tazo neman ta dan afara shirin yi mata kwalliyar yamma ta zuwa walima, gagarumin walima ne da Daddy da kansa ya shirya shi. Sosai Anty ma tayi 'ko'kari dan kuwa duk wasu kaya da Fateemah tayi anfani dasu da ma wa'dan da zata sa agaba duk Anty ne ta 'dau nauyin yinsu tare da 'dauko wata shahararriyar mata wacce ta 'kware a fannin kwalliya na zamani domin ta ringa yiwa Teemah make'up har biki ya 'kare. Ko yanzun ma da kanta ta shiga duba Teemah sai ta tarar da ita kwance ta du'kun'kunu a cikin blanket. Da sauri ta 'karaso tazo gareta tana tambayar ta "me ya faru? Tayi saurin fahimtar abinda ke faruwa ne sanadin zafin da taji jikinta yayi ga kuma ha'duwan da ha'koranta keyi. Fita tayi da sauri da niyyan 'kiran Mummy sai kuma tariga ha'duwa da Ummah tun kafin ta kai ga Mummyn. Ummah kam ganin hankalin Anty atashe yasa tayi saurin barin maganar da takeyi ta taho ta tareta da tambayar meke faruwa ne? Bayani Anty tayi mata atakaice tun kafin tadasa aya kuwa Ummah ta furta " _subhanallah_ " sai tayi gaba, tare suka 'dunguma zuwa 'dakin su Teemahn da Anty da wasu mata guda biyu. Ganin yanayin Teemah yasa Ummah fa'din " Fateemah sannu ko, sannu Allah ya sauwa 'ka! Juyawa tayi ta kalli 'dakin tace "wai ni har yanzu Hannah bata dawo bane? Wata Antyn su da suka zo daga Gombe ce ta bata amsa da fa'din " inaga de bata dawon bane 'kila" Ummah dialling no. tayi ta 'kira shiru tsawon seconds bakwai sannan ta furta "Ameen wa alaikassalam" "Jama'ah Alhamdulillah" "Fateemah ba ta jin da'di ne nace ko zaka aiko doctor adubata " "Ok, toh shikenan" tafa'da tare da yanke wayar. Iya abinda kowa yaji kenan kuma babu wanda yasan da waye tayi magana. Sai da ta cire wayar a kunnanta kafin tayi musu bayanin cewa " Abbas zaizo yanzu 'kila ya taho da likita ko kuma ya kaita asibiti ban san wanne zaiyi ba" Fita tayi tace "bari tana zuwa yanzu kafin ya iso" 15mins be cika ba sai gashi ya bayyana a'dakin cikin wata arniyar shadda sky blue mai kyan gaske wanda ya dace da yanayin jikinsa. Da sallamar sa ya shigo tare da gaida wa'danda yagani a'dakin. Sake tambayar Anty yayi abinda ke damun Teemah Antyn sai tace dashi " _inajin zazza6in ne ya dawo dan jikinta ya dau zafi gaskiya sosai_ " Tayi maganar tare da kaiwa hannunta zuwa jikin Teemah. Abbas kam tana gama bayani sai ya kallo inda yaga maganin ta jiya, aikuwa sai yagansa still agurin, zuwa yayi a hankali ya isa inda yake ajiyen ya duba sai ya ga tun wanda ya 6alla mata jiya ne bata 'kara shan wani ba. Sai yanzun yakai dubansa kan Fateemah da tun safiyar yau yake mararin ganinta amma be ganta ba sai yanzun. Jikinta arufe ruf illah kanta ne yake iya kallo dan fuskarta yana 'daya bangaren ne ta juya musu baya. Tuni 'daurin da aka mata ya zame ya koma gefe ya bar iya gashinta dake kwance gwanin sha'awah awaje yana ta she'ki. Takawa yayi a hankali zuwa bakin gadon yasa hannu ya ta6o fuskar tata sai yaji zafi gau be 'dauke hannun ba sai da ya shafi gashin kanta da ya 'dau hankalinsa yanda babu wanda zai lura cewa dagan gan yayi. Juyawa yayi ya fara tafiya yace da su akaita motansa zai same su acan, yace gara muje hospital adubata yafi" Yana gama fa'din haka ya bar 'dakin. Wasu su biyu ne suka kama kafa 'dunta zuwa inda ya fa'da 'din Anty na binsu abaya. Anan ya same su ri'ke da ita an lullu6a mata mayafi akanta wanda yarufe jikinta da kyau, hakan kuwa ba 'karamin da'di yaji aransa ba, sai daya iso ya bu'de motan kafin ta shiga da taimakon Anty sannan shima yashiga tare da furta _bismillah_ don zatonsa ko da 'dayansu za'a. "Sai kun dawo, Allah ya tsare ya bada lafiya in gantacciya" Anty ne tafa'di haka kafin ya amsa kuwa har sun juya masa baya. Ganin sun juya kuwa yasashi sakin hamdala azuciyarsa dama shi ba son rakiyar yake ba dan sai ya cire babbar rigar dake jikinsa ya wulla ta baya dama duk ta takurasa ha'kuri kawai yakeyi da ita na yau ka'dai. Jan motar yayi suka bar haraban gidan, sai da ya hau titi kafin ya juya ya kalleta sai yaga ta kwantar da kanta ajikin cinyoyinta ta takura guri guda ga dukkan alamu sanyi takeji sosai. Be yi mata magana ba hannu yasa kawai ya kashe AC gaba 'daya sannan yaci gaba da tu'kinsa. Koda aka gwada ta ma ba komai ke damunta ba zazza6in ne kawai sai stress daya mata yawa amma bakomai, kuma ciwon na 'kara 'karfi ne sanadin rashin cin ishshen abinci da batayi. Yau kam cewa yayi ayi mata allura dan bata son shan magani ma yace ko najiya ma 'kin sha tayi. Kuka tafara tare da ro'konsa akan dan Allah yayi ha'kuri bazata sake 'kin shan magani ba. Kau da kai yayi yace da nurse 'din ta ha'da injections 'din yace kuma bata son cin abinci ma doctor. " _Yayah plz

Chapter 43 of 67