yaranta maza biyu, bayan rasuwar sa kuwa dangin sa sai suka kar6i yaran a hannun ta suka ri'ke agurin su.
Sam bata da matsala koka'dan, tana da hankali da nutsuwa, uwa uba ilimi ingantacce ya wadace ta boko da arabi, ga ta da son mutane da kuma yawan kyautata musu, wanda wannan dalilin ne yasa Abbah da kansa yayi sha'awan auren ta domin ya sa6unta rayuwar gidan shi da ya kafu shekaru da dama da suka shu'de.
Ahalin yanzu kuwa burin Abbah yariga yacika domin an 'daura auren da Haleeman sa, bawai dan baya son Anty ba ah'ah sai dan kawai yana so shima rayuwar gidan shi ta canja.
*****
'Kayataccen Dinner aka shirya wanda tsirarun mutane ne suka halatta saboda ba gaiya sosai akayi ba, shima 'din Abbas be wani 6ata lokacin sa ya gaiyaci abokansa ba wa'dan da suke kusa dashi ne suka sani su 'din ma yawanci friends 'din sa na secondary school ne.
Daga wurin dinnern aka wuce da amarya zuwa sabon gidanta da ke.......
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce* π
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated to my fans all over media_ π
*Bismillahir rahmanir raheem*
_Failure is neccessary 4 any learning curve......_
_Failure makes u stronger, bolder and_ _less scared of taking risks......._
π
Ώ *78*
Daga wurin dinner sai aka wuce da Teemah zuwa sabon gidan ta dake Maitama.
Duk kushen mai kushe be isa ya kushe gidan Teemah ba, dolen sa sai ya bawa wannan gidan yabo ta musamman domin kuwa ko acikin ayari ba ze baka wahalar warewa ba, iya ha'duwa gidan ya ha'du matu'ka da duk wani abu da 'dan Adam yasani na more rayuwa, Ba stairs bane gidan plat house ne dan'karere, sai dai 'dakuna uku ne kacal agidan da kuma babban parlour 'daya dake tsakiya, sai babban kitchen dake daga can hanyar wani corridor da zai fitar da mutun har bayan gidan inda wani 'kayataccen lambu yake gwanin birgewa....
I can't even describ ths house 4u clearly, but u urself should imagine it, koma yaya tunanin ku ya baku just take it as if daku aka shirya komai na gidan.
Abbas da kansa ya rakata har 'dakin ta lokacin 'karfe 7:30pm ne, ko tsayawa be ba ya barta ya fito ya shiga nashi 'dakin dake nesa ka'dan da ita.
Itama binsa tayi da idanu har ya shige ciki.
Teemah kam Abbas na shigewa sai ta tura 'kofar ta ta fara cire 'kayatacciyar shigan da akayi mata na fitan dinner party 'dazu.
Sosai irin wannan dressing 'din auren suka isheta, dan kayan na takurata da nauyi, sai da ta cire gaba 'daya kayan kafin ta nutsu kuma sai alokacin ne hankalin ta yadawo jikin ta, kawai sai ta saki baki tana 'karewa ha'duwa, kyau da tsaruwan 'dakin da Yayah Abbas ya ambace shi da suna nata ne.
Tashi tayi tana juyi tare da murmushi " _wow_ " tace tare da daka tsalle dan ganin dream bed design 'din ta a'dakin kamar an shiga zuciyarta an gani, most especially colour 'din bed 'din fari ne tas sai akayi masa kwalliya da orange colour daya 'kara haska shi, colourn paint 'din entrance door dana bayi ma duk farare ne, hakama tiles 'din dake 'kasan 'dakin shima fari tas, wani shegen ha'da'd'den labile aka sanya a'dakin orange colour mai matu'kar birgewa.
Sosai 'dakin ya tafi da imanin ta haka tayi tsalle ta fa'da kan gadon tana murmushin farin ciki, ta zubawa farin ceiling fan 'din dake saman 'dakin idanu.
Mummy da Daddyn ta ne ka'dai suka san best colour 'dinta akaf fa'din duniya sai ko Yayah Abbas dan ta ta6a fa'da masa da jimawa tun suna damaturu lokacin daya je hutun aikinsa acan, bayaga su ukun nan kuwa babu wanda yasan favourite colour 'din ta har yau, hatta Hannah ma bata sani ba, amma acikin su ukun bata san waye ya yi mata wannan kyautar ba koma waye ita kam yasata farin ciki mara iyaka.
Shab tama manta da cewa ba kaya ajikin ta duk ta cire su, tana kwancen tana ci gaba da 'karewa 'dakin kallo kawai sai ta ji 'karan sau'kan ruwan sama lokaci guda tamkar da bakin 'kwarya.
Afirgice ta tashi ta zauna tana rarraba idanu sam bata san da akwai hadari har haka agarin m bama ita, sai sau'kan ruwan kawai taji.
Tashi tayi tafara duba abinda zata saka ajikin ta amma ta kasa samu sai masu nauyi ita kuma basu take so ba, da 'kyar hannun ta ya jawo wata figigiyar riga ja mai sharara bata ma ko wuce mata gwiwa ba amma ahaka cikin hanzari ta saka shi ajikinta.
Tana gamawa saka wa sai ta fara duba wani 'dan viel da zata rufe kanta dashi sai kawai taji 'karan thunder mai 'karfin gaske irin mai razanar wan nan ha'de da wal'kiya mai haske.
A 360 ta fito a'dakin tana toshe kunne ta nufi 'dakin da taga ya shiga 'dazu, duk taku 'daya da takeyi tsoro ne yake sake kamata da haka har ta isa 'dakin.
Tana zuwa kuwa dai-dai shima ya bu'de 'kofan nasa sai sukaci karo dashi, jikin shi ta shige tana kakkarwan tsoro shima dayaga haka sai yasa hannun sa ya rungume ta ajikinsa sosai.
Tsawon mintina 8 tana faman sau'ke ajiyan zuciya sannan ya 'dago ta ganin kamar ta 'dan nutsu.
" _Me yafaru ne wai? Me yasa meki_ ?
Tambayar daya jefe mata kenan tare da jijjiga ta.
Cikin in in ta bashi amsa da fa'din " _Yayah ni tsoro nake ji sosai_! "
" _Tsoron miye kuma? ke bazaki bar shirme ki girma ba ko_ ? _Ba gani nan agidan ba babu wani abin tsoro agidan nan da ze kamaki, ko kinga_ _wani abu ne_ ?
Kai ta jijjiga masa sai tace " _thunder nake tsoro_ !
" _Toh ai baya kama mutun shi, oyah jeki 'dakinki ki kwanta ki huta ko zaki ci abinci?_
" _Ah ah_ "
Tace dashi
sai yace " _toh jeki ki huta kinga yau akwai sanyi kar ya shiga jikin ki!_ .
Teemah kam kuka ta sanya mishi tana bubbuga 'kafafu a'kasa tace
" _ni wallahi tsoro nake ji ni ka'dai!_
" _Wai ya kike so in miki ne toh, umm_ ?
Ya fa'da yana kallon ta.
Shiru tayi bata ce komai ba, ganin haka yasa ya juya ya koma ciki dama dubota zeje yi dayaji 'karan yasan sai ta tsorata sai kuma suka ha'du ashe be yi 'karya ba.
Binshi itama tayi abaya tana tafiya tana waiwaye kamar irin wani abu na binta abaya 'din nan.
Duk da tana cikin firgici amma hakan be hana ta ganin kyaun 'dakin sa ba, compared to nata ma ai nata bakomai bane, hakama bed size 'dinsa ba irin nata bane, ya zarce nata da girma, nashi komai fari tas aka sanya mishi, curtain ne ka'dai mint green da zanen fulawowi su kuma dark green ajiki.
Abbas yana zuwa ya wuce bathroom ya 'dauro alwala, koda ya fito ma kallo 'daya yayi mata ya kauda kansa ya wuce ga dadduma, sallah ya gabatar kusan raka'ah shida sannan ya 'daga hannunsa ya dinga jero addu'o'i wa'dan da bata san iyakar su ba.
Teemah tun tana kallon sa har ta gaji ta lalla6a ahankali zuwa bakin gadon ta kwantar da kanta amma 'kafafun ta na a'kasa ahaka bacci yayi awon gaba sa ita.
Abbas ne daya idar da sallahn yazo inda take ya tsaya akanta sai yanzu yaga tsantsan kyau da tayi cikin rigar dake jikinta, ahankali yakai hannu ya shafi gashin kanta har ya fara yawo da hannun nasa akan nata sai kuma wani abu ya 'dar su aransa, da sauri ya cire hannun yana kallon hannunsa kamar wani sabon abu ne.
Tashi yayi ya tsaya akanta ya 'kura mata idanu yana so ya kauda sa'kar haukan da zuciyarsa ke haska mishi amma ya kasa, ahankali ya gyara mata kwanciyan da kyau ya lullu6e ta sannan ya koma 'dayan gefen ya kwanta shima.
Bacci kasa 'daukan sa yayi ya zubawa fuskar ta ido yana ta sa'kar zuci, sam baya son hakan ya dinga zuwa ransa amma bazai iya ba, gashi yakasa kauda tunanin nan aransa.
Kishi ne ko shai'dan koma miye ke sarrafa zuciyarsa yakasa ganewa.
Ranar Abbas har makara yayi na zuwa masallaci, lokacin da ya tashin kuwa Teemah na jikinsa kamar de jiya haka yau ma tayi, sai ya 'dan bata glance ka'dan dai-dai kuma itama ta bu'de idanun ta caraf sai sukayi 4eyes dashi, wanda motsin da yayi ne ya farkar da ita daga baccin da take yi.
Take ta diririce ta fara kalle-kalle ganin yanayin kusancin dake tsakanin su dashi yasa da sauri ta tashi zaune tana sussunkuyar da idanun ta 'kasa dan ta fahimci itace, laifinta ne.
" _Mage ce ke ko_ ?
Taji ya ce da ita
Yayi maganar bayan ya tsareta da kallo.
Kai ta jijjiga masa tana 'kif-'kif da idanu, maganar tasa it's clear that ita mai son jiki ce, haka yake nufi kuma ta fahimta amma sai ta'ki bawa kanta laifin ita ka'dai, asace take duba 6angaren daya kwanta itama ko zata ga space 'din daya bari abaya ya matso amma sai bata ga komai ba.
Abbas be sake kulata ba dayake ma be fahimci me take yi ba gudun kar ya makara yasa ya mi'ke ya nufi bayi yana tunanin irin shegen son jikin datake da shi ga uban birgima kamar wata yarinya 'karama.
Har ya shiga bayin ya gamo abinda zai yi ya fito tana nan zaune awurin kamar yanda ya barta 'dazu.
I'kama ya tayar ya gabatar da Sallar sa cikin nutsuwa tare da yin addu'o'in azkar 'din sa cikakke.
Al-qur'ani ya mi'ka hannu ya 'dauko saman drwaer ya bu'de suratul A'araf ya fara karatun sa cikin sauti mai da'din sauraro tamkar bashi ne Abbas ba mai jin kai da rashin son maganan nan ba, qur'ani kenan, zancen Allah mai abin mamaki, duk wani girman kan ka ,miskilanci da 'kafafan ka duk rashin iya hausan ka da 'karfin da harshen ka keda shi akan yaren ka but when it's comes to it (QUR'ANIL KAREEM) dole harshen mu ya dawo iri 'daya.
Karatun nasa ba 'karamin shigan ta yake yi ba, hakan yasa ta koma ta maida kanta akan pillow tana sauaraon sa tare da zuba masa idanu, wani 'ka'k'karfan ala'ka take jin zuciyarta na 'kulla mata game da Abbas 'din sai take jin tamkar he is the only man in d entire universe take wani sabon babin 'kaunar Yayan nata ya shige ta take jin shi 'din na daban ne, kamar kar ya 'kare karatun haka take ji.
Ko da ya 'kare karatun kuwa sai ya sake bu'de wani page daga cikin 'karshen Al'qur'anin yafara karanto addu'ar da ke rubuce a ciki wanda akeyi bayan an gama karanta Al'qur'ani mai girma ( Du'ah 'u Khatmil Qur'an).
Yana shirin ajiye wa bayan ya kammala karatun sai suka ha'da idanu dashi kauda kanta tayi da sauri yayin da shi kuma ya kasa 'dauke nasa idanun daga kanta, fuskar ta yake 'karewa kallo har zuwa la66an ta, wani sabon salon 'kaunar ta ke 'kara nin kuwa masa a zuci, wanda har be san lokacin da ya mi'ke ya isa gaban gadon ahankali ba, ita kuwa tuni ta rintse idanun ta ganin ya nufo ta dan bata san me yake shirin aikata wa ba.
Abbas kam shai'dan mai masa muguwar sa'kan nan be zo masa ayanzun wata'kila sanadin karatun da yayi ne shiyasa, wannan karan shai'dan 'din be yi masa mummunan sa'kar daya saba yi masa akanta ba, jiyayi kamar ana fizgansa zuwa gareta idanun sa na 'kara haska masa asalin kyaun surar datake dashi......da 'kyar ya dawo da tunanin sa dai-dai tare da jijjiga kansa ahankali.
Wani 6ari na zuciyarsa ne ya wurga masa tambayar " _me kake shirin yi ne Abbas_?
Lumshe ido yayi yakuma bu'de su atake sai ya sau'ke su akan fuskarta dake 'dauke da rintsetsten idanu har yanzun bata bu'de ba, 'karfin gaske yake jin zuciyarsa na fizgarsa zuwa gare ta.
Dakewa yayi a tsayen sai dage ya harha'do wasu 'kabilun kalaman da sam basu ne acikin ransa a wannan lokacin ba " _yau ma bazaki... yi sallar ba...ne?_ "
Yayi maganar yana wani gyara tsayuwa.
Jin yanda yayi tambayar yasa Teema ta bu'de idanunta ta 'dan waigo a karkace ta kalleshi dayake dama ta bayan ta yazo ya tsaya, goshi ta ha'da dan ji tayi tarasa me ma zata ce dashi, aranta tace " _ina ruwansa toh da sallan ta_ ?
Jitayi yasake jefa mata wata tambayar inda yace
" _Ko har kinyine bansani ba_ ?
Kai ta jijjiga masa amamar ah ah tare da sau'ke idanun ta zuwa 'kasa.
Abbas taran ta yayi da fa'din " _amsani da baki i thought mun gama da wannan 6angaren tun ba yau ba_ ?
Ahankali ta bu'di baki tace
" _a'a banyi ba_ "
" _Sai yaushe kenan_ ?Ya sake tambayarta.
Cewa tayi
" _May be gobe_ "!
Tayi maganar kaman an matsi bakin ta ne an sata dole.
" _Okay_ "
Kawai yace da ita tare da
juyawa ya koma parlour dan kallon news 'din safiya.
Teemah kam da idanu ta bishi har ya bar 'dakin gaba 'daya, sai kuma taji ta kasa ko da motsin kirki ma, haushin ta 'daya yanda ya wani tsare ta da tambaya shi sam be san yaji kunyar abu ba, hakama ranar yawani cire mata kaya dan bata da lafiya ko kunya bayaji shi bayan yasan ita baso take ba, jiya ma haka yasa ta wai ta 'dauke pant 'din ta a bayin sa bayan ko be fa'da bama idan ta tuna zata 'dauke abin ta da kanta, toh period 'din da takeyi ma sai yaji dalili ne ko kuma ranar gamawar ta ?
Duk cikin ranta take wannan tunanin.
'Dan karamin tsaki ta ja bayan ta 'mare tunanin tace " _mutum sai sa idon tsiya gashi kamar mumini amma san bahaka bane_"
Tare da juyawa ta gyara kwanciyar ta da kyau.
Caraf idanun ta suka sau'ka akan photo enlargement 'din sa dake manne a bangon 'dakin saitin ta, tun shigowan ta 'dakin bata lura dashi ba sai yanzun sai taga kamar ita yake kallo shima.
Sanye yake da full dress na Uniform Karky 'dinsa na sojoji, kansa babu hula ya ri'ke ta a hannun sa wanda ya 'dago hannun sa dake ri'ke da hulan ya 'dora akan 'kirjinsa yana murmushi aka haska pix 'din ba 'karamin kyau yai ba ita kanta ya birgeta, daga dungun 'kasan photon kuma wani 'dan 'karamine shima aka ha'da su, shima nasa ne kuma still da karky ajikinsa, ya 'dan 'daga hular dake kansa ka'dan kamar me shirin sarawa wani, bambamcin kawai wannan 'din ya 'dan sunkuyar da kai ne sa6anin sarawa da shi kai asama ake yinsa, wannan ma sai yafi yi mata kyau fiye da waccen babban dan shi 'din yafi sake fuska aciki kuma yayi salo me birge duk wanda yagani yakuma fa'da'da fara'ar sa afili har ana ganin hasken hakoran sa.
Daga 'kasa taga an rubuta *Cpt. M A AL-HASSAN* .
Sunan ta sake maimaitawa abakin ta sosai taji da'din fa'darsa abaki.
Ahankali ta sau'ka daga gadon ta koma gaban pix 'din ta rin'ka shafawa tana kallon sa, ta6e baki tayi aranta tace a photo ka'dai ake ganin fara'a da murmushinsa shi, shiyasa ma yafi kyau anan 'din fiye da ganin sa zahiri"
Tayi maganar tana wani shashshafa photon ahankali.
Ta shashance tana kallon sa har bata san cewa ta 'dau tsawon lokaci ahakan ba.
Har Abbas ya shigo ma bata sani ba gyaran muryarsa kawai taji daga bayan ta sai kuwa tajiya da sauri.
Suna hada idanu yace da ita
" _Bana son rigima fah, idan kika kuskira kika yi min 6arna ni da ke ne_!"
Yana gama fa'din haka ya wuche bayi.
Ita ma binsa tayi da kallo tare da hararan bayan sa batare da tace uffan ba har ya shige cikin bathroom 'din.
Teemah bata wani 'kara 'daukan dogon lokaci awurin ba ba ta wuce 'dakin ta da rabon ta dashi tun jiya da dare.
Wanka tayi tafito ta sami wata atampa cikin jerin kayan data gani jere a ma'ajiyar kayan dake 'dakin nata.
Riga ne da skirt kayan 'din kin zamani, ko da tasa kuwa sai taga kamar kayan daga cikin kayan ta ne aka 'dauko shi, domin ganin yanda ya zauna mata ajiki.
'Bata lokaci tayi ta kashe 'dauri bayan ta zizaro kwalliyar ta ta yayi gwanin birgewa sai dai bata cika fiskar ta da tarkace ba light make-up tayi kawai yau 'din.
Maman Amal Teemah ta tuna da kalaman ta na baya da kuma Anty da nata maganganun basu da'de ba da ta fade su, wa'dan nan bayin Allahn sun bada 'kyakykyawar gudum mawa arayuwarta ita kanta tasan hakan, sune suke cewa da ita taringa yin kwalliya sosai agidan mijin ta, Allah sarki Maman Amal 'yar uwa mai 'kauna saboda Allah kenan, lokacin auren ta na baya da Mahmud ba 'karamin 'ko'kari tayi ba na ganin ta gyara zaman takewar su, amma bai nifi tsawon rayuwa tsakanin ta da Yah Mahmud ba, Teemah da kanta tasan Maman Amal mai son tsakani da Allah ce kuma har yanzu darussan ta na nan bata manta ba, sosai Teemah tayi missing wannan baiwar Allahn.
Tana kammalawa da 'daurin ta tashi tana 'karewa jikinta kallo acikin dressing mirror, 'karan door bell ne ya dakatar da ita sai ta tsaya shiru tana tunanin ko Yayan ta zai je ya bi'de , amma sai taji 'karan ya kasa karewa kusan mintina uku ba'a daina ba hakan yasa ta fahimci cewa babu wanda ya bu'de 'kofar, sai tayi tunanin ko har yanzu yana bathroom ne.
Saurin fita daga 'dakin tayi ta nufi palour da niyyar bu'dewa sai kuma taci karo da shi wanda suka bu'de kofa atare suka fito, shima 'din door bell 'din ne yafito shi.
Sau 'daya ya kalle ta sai ya 'dauke kansa yaci gaba da tafiyar sa, Teemah daga inda ta ganshi bata 'kara motsawa ba ganin ya fito kawai sai taja ta tsaya.
Hannah ce ta shigo hannun ta ri'ke da wasu ha'da'd'dun warmers guda biyu.
Tana ganin Teemah tasaki murmushi amma bata kula ta ba, sai da ta rissina cikin natsuwa ta gaida Abbas tukunna wanda yana amsawan yakoma ciki dan be gama shiryawa ba yafi to.
Yana shigewa Hannah ta danno da gudu ta rungume ta tana dariya ta ce " _mrs Dodo kinyi kyau fah irin wanna show haka gaskiya kin yi wuta amarya, banzo da waya ba Allah da na miki photon mrs Yayah first day in her husband's house_ "!
Ahankali take maganar dan kar Abbas ya jiyo ta.
Duka ta kai mata sai ta goce tana dariya.
Dariya sukayi dukkan su, hannun ta Teemah ta kamo tace " _zo mu shiga ciki kiga wani abu_ "
Hannah da sauri ta 'kwaci hannun ta tare da fact din ke barni ba yau ba, zan dawo watakila gobe yau din nana Ummah da babban warning ta ha'dani tace kar na yarda na wuce time din data bani wai in koma da wuri"
" _Ke de Hannah Allah ya shiryeki, idan baki son zama ai bazan tilastaki ba amma miye na buga wa Ummah_ _sharri har haka_ ?.
Teemah ta fa'da fuska ba yabo ba fallasa.
Tuni kuwa Hannah ta fahimci bata ji da'din hakan ba domin ta tabbatar mata sai tace
" _wai ke kina tunanin sharri ne" "ehh mana toh da menene? "Allah Teemah ba sharri nayi mata ba, can't u see hannu na ko waya fah babu!_
Ta dago hannayen ta tare da waresu sannan taci gaba
" _Tasan i'm addicted 2 my phone shiyasa ma ta 'karbe bayan ta ha'da ni da warning, dan tana tunanin ko dan wayar ma dole zan koma gida da wuri, ban gama kawo abincin bama fah bari in 'dauko sauran_ ".
Hannah tana maganar tana nufan 'kofa, Teemah ma sai ta bita abaya suka fita tare.
Sai da suka fitan ne Hannah tana murmushi tace da sigar tsokana
" _kin san yanzu ke amarya ce Ummah bata so a dame ku ne shiyasa...._
'Kasa-kasa tayi da murya tace " _ke inaga fa Ummah jika take so da wuri....._ "
Duka Teemah ta kai mata tana dariya itama da sauri Hannah ta goce itama tana dariyar da haka suka isa wurin motan batare da ta 'karasa fa'dan abinda tayi niyyan fa'di ba.
Kar6an coolern Teemah tayi a hannun ta itama sai tace da Hannah
" _Bani zan tafi dashi ki je abin ki karki 6ata ran Ummah tun da bata so a dame mata ya'yah gara kiyi sauri ki_ _tafi_ "
Dariya sosai Teemah ta bawa Hannah takuwa dara tare da fa'din
" _yarinya kenan!_ "
matsowa tayi daf da kunnan Teemah tace " _Darasin ki na gaba mrs dodo zaki gane kuren ki ai_ "!
Hannah na gama maganar ta shige cikin mota tana dariya, sai alokacin kuma Teemah ta gaida driver tare da 'dagawa Hannah hannu.
Ashe har da driver Ummah ta ha'do ta ya kuwa jirata dan ma kar ta zauna 'din dagaske.
Sai da taga sun bar gidan sannan takoma ciki, tana shiga sai ga Abbas ma ya sake fitowa cikin shigar suits ash colour, yana ganin ta yaja ya tsaya turus, take ya wani ha'de goshi tare da 'kan'kance idanu yace " _what nonsense!.... daga ina kike.._ ?
ππ»
_Comment_
_Vote_
_Share_
*_Salmerhn ku ce_* π
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_My 'kungiya on top_ π€π»
_This page is specially goes to u *DBWA* i heart u mutane na._ π₯°
*Bismillahir rahmanir raheem*
_Whenever you ar *STRESSED* , eat chocolates, sweets nd everything.... because when_ _stressed is spelled backwards it becomes β_ _*DESSERTS* β_ ππ»
π
Ώ *79*
Hankalin ta kwance ta bashi amsa da fa'din " _wannan na kar6o "_
Tayi maganar tare da 'dago coolern ta nuna masa dan bata zaci laifi ta aikata ba.
Tsawa Abbas ya daka mata har sai da ta tsorata, yace
" _Shut up da Allah ni, ke aka aika ki kawo ne_ ?
_ko ita wacce aka aikon bata da hannu shigowa da shi sai ke? Wama yace miki ki rin'ka fita a haka da irin wannan shigan?_
Har yanayin fuskar ta ya canja zuwa yanayin kuka kamar yanda na shi ma canja ya koma yanayin 6acin rai, cewa tafara yi.
" _Yayah ni...._
Dakatar da ita yayi da fa'din
" _Yaya what_ ?
_did i send u_ ?
Shiru tayi ta sunkuyar da kanta 'kasa ita masifar tasa mamaki yake bata ma.
Shi kuwa tsawa ya sake daka mata inda da 'karfi yace " _tamabayar ki nake_ _yi na aike kine_ ?
Sosai ta tsorata da tsawan nasa dan ita har ga Allah bata san irin hakan sam.
Kai ta jijjiga masa da sauri alamar " _ah ah_ "
Kwafah yayi yana kallon ta yace " _so_ ...!
tare da 'dage gira 'daya.
Baki tura gaba ta juya kai gefe a ranta tace " _kai ka sani ai masifaffe mai hali biyu kawai_ "
Afili kuwa 'kun'kuni tafara tana wani ha'de rai itama.
Gani tayi ya fara tahowa inda take ai da sauri ta ajiye coolern ta yi 'dakin ta da gudu, tana shiga kuwa ta datse 'kofan ta tsaya maida nunmfashi.
Abbas kam binta yayi da kallo har ta shige 'din sai ya saki guntun tsaki, har zuciyarsa yaji haushin fitan da tayi ahakan bayan yasan akwai maza a harabara gidan, batyan mai gadi yasan dole Hannah da driver zata zo amma shine an ta rai,a shi sai ta fita ahaka tana juya musu jiki, wama yasan irin yanda shigar tan ya birge su.
Wani tsakin ya 'kara ja ya koma 'dakin sa ya 'dauko keyn mota ko ta kan abincin bai bi ba ya yi waje abinsa.
Teemah kam jikin 'kofan ta mannu ta ringa sau'ke ajiyan zuciya, shab ta manta ma akan cewa ya tsani 'kun'kuni shiyasa tayi, da badan haka ba da ba za tayi masa ba acikin irin yanayin da ta ganshi 'dazun......
Afili ta ce " _kai_ _wannan_ _mutumin ba dai mugun hali ba"_
Bata fito ba sai da ta 'dau kusan 40 mins a'dakin sannan ta bu'de 'kofan ahankali ta le'ko, sam bataga alamun mutum ba kamar yadda bata ji motsin kowa ba dan haka sai ta fito gaba 'daya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 46 Chapter of 67