Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
juyawa fuskar sa da murmushi yace "...... _ya kuma baki baby mai kama da waye ma.......?_ Ya ritsa ta da idanu. Murmushi maganar tasa ta tasa ta sai ta tarasa mai ma zata ce dashi kuma sai kawai ta ya mutsa fuska tare da rike cikin ta alamar yunwa takeji. Abbas ma murmushin yayi mai sauti sai ya bata cup 'din a hannun ta ta ringa sha a hankali bata shanye ba ta mi'ka masa cup 'din tace ya isheta dan bata jin da'din bakin ta sosai. Abbas be matsa mata ba sai ya kar6a ya ajiye tare da tambayar ta zafin ciwon muryarta ciki ciki ta bashi da fa'din yana mata zafi ka'dan-ka'dan amma idan ta motsa 'kafarta sosai takejin zafin. Abbas cewa yayi da ita " _sorry... zai daina very soon da iznin Allah kinji_ " Shiru tayi masa tafara 'ko'karin kwanciya, Abbas sai ya gyara mata kwanciyar tare da lullu6e ta da kyau yace bari yana zuwa daga nan yafita a'dakin. Yana komawa 'dakin sa ya'kira layin nurse sukayi magana inda ya roketa cewa kar ta 6ata lokaci bayan haka sai ya tura mata address 'din gidan nasu sannan ya ajiye wayar. Bayi ya koma ya wanke bedsheet 'din daya cire a gadon harda kayanta da suka jike 'dazun gaba 'daya ya hada ya wanke ya fita corridon baya ya shanya su. Yana kammalawa ya shiga bathroom yayi wanka na biyu sannan yafito ya shirya cikin wani ba'kin long trouser da jan T-shirt kamar bashi ba, yana shirin fitowa sai yaji 'karan door bell, yasan Anty nurse ce ko kuma driver cikin su 'dayane ya iso. *Toh ga al'kawarina na sauke read more biyu ne bayawa nayi muku, amma nima sai a daure a faranta min dan naji da'di* .๐Ÿฅฐ _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerhn ku ce* ๐Ÿ˜ [10/13, 1:58 AM] ๐ŸŒธSalmerh๐ŸŒธ: ๐Ÿ’• *CAPTAIN ABBAS* ๐Ÿ’• By *Salmerh MD* Luv story๐Ÿ˜ *Wattpad @* *Serlmerh-md* ๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* ๐Ÿ’ซ We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* I _dedicated this page to my fellow *Wattpadians* , Ha'ki'ka *SALMERH*_ _najin da'din kasancewa daku ,wannan page 'din kyautar kune_ .๐Ÿฅฐ *Bismillahir rahmanir raheem* _A mistake is only a mistake when u don't learn from it. Otherwise it is a *LESSON* ._ ๐Ÿ…ฟ *83* Zuwa yayi ya bu'de 'kofan sai yaci arba da driver a tsaye kar6an abincin yayi bayan sun gaisa harma drivern na bashi ha'kurin jinkirin da aka samu yace ruwane yasa ba'a kawo dawuri ba. Abbas kuwa yace masa bakomai ai sannan ya wuce dinning. A gate motar driver da Anty nurse suka yi clash yana fita itama ta shigo, Abbas na ajiye abin hannunsa sai ya kama hanyar 'dakin ta domin duba yanayin datake ciki kafin ya isa sai yasake jin door bell karo na biyu, be 'karasa 'dakin ba sai ya juya izuwa 'kofan dan a 'kage yake Nurse ta iso dan ta duba masa ita. Anty nurse ce tsaye tana murmushi shima murmushin yayi tare da matsawa yabata daman shigowa yana fa'din " _har ina shirin sake 'kiranki ai_ " Nurse tace " _na hutar da kai ai tunda gani na iso"_ ! Zama take 'ko'karin yi a kujera Abbas ya dakatar da ita da fa'din " _muje dai tana ciki ai ba batun zama kuma_ "! Dariya nurse tayi itama tace " _toh bakomai yalla6ai ai dama ba zaman nazo yi ba_ " Gaba yayi ta bishi abaya har zuwa 'dakin Teemah inda suka same ta har tafara bacci, motsin shigowar su ne ya farkar da ita sai ta sau'ke idanu a kansu. Tana ganin nurse sai ta maida kallon ta kan Abbas tana kwa6a fuska. Nurse 'din ne tana dariya tace mata " _Ashe 'yar shagwa6an Yayah me tsoron allura ce ma! Ya jikin naki_ ? Ahankali tace " _na warke tun 'dazu!, ina kwana Anty_ " " _Lafiya lau Alhamdulillah_ " Anty nurse tace tare da zama agefen ta, Abbas kuma yana tsaye ya kama kunkumi da duka hannayensa biyu yana kallon ta. " _Meke damunki_ ? Anty nurse 'din ta sake tambayar Teemah tare da ta6a wuyanta. Take idanun ta suka tara ruwa sai ta 'daga kai ta kalli Abbas 'din suna ha'da idanu ya taho kusa da ita ya zauna tare da tallafan ta zuwa jikinsa sai ta 6oye fuskanta a'kirjinsa a hankali tace " _Ni bana son allura Yayah_ " Jinjina kai yayi tare da fa'din " _Alright ki nutsu bazata miki ba magani kawai zata baki idan ta dubaki, kinji"_ Dayake yariga yayiwa nurse 'din bayani tun a waya so bawani sabon bayani datake bu'kata daga wurin su illah ha'din kan Teemah. Hanglove take sawa a hannun ta take fa'din " _ina jin guri zaka bamu fah yalla6ai dan naga alama in kana kusa ba zamuyi abinda ya dace ba da wannan shagwa6a66iyar_ ". Raba ta da jikinsa yayi yari'ke kafa'dun ta yace " _ki nutsu ta duba ki kinji in har kika yi mata rashin ji_ _kinsan tana da allura ko, ni kuwa bazan hanata yimiki ba, zan dawo yanzu bari in 'dauko_ _wayata_ ". Fita yayi ya bar su inda Anty nurse 'din tace mata ta gyara da kyau ta dubata, hawaye tafara yi ka'dan-ka'dan tare da fa'din " _Anty dan Allah kar kimin allura in kika yimin mutuwa zanyi, Yayah ma mugunta yamin 'dazu........._ " " _Shiii...! yi shiru bazan miki allura ba karki damu kinji_ " Kai ta 'daga mata sannan ta bata chance ta duba ta. Bama wani ciwo taji ba kawai dai 'kan'kanta da rashin 'karfi da jikintan ke dashi ne ha'di da rashin sabo yasa take jin bada'di, ga kuma shigan 'karfin da akayi mata shiyasa take jin zafi sosai. Da farko nurse 'din tayi tunanin ko ciwo sosai Teemahn taji amma sai kuma taga abin da sau'ki musamman dayake ta yi anfani da ruwan zafi so ba wata matsala sosai. Data ga haka sai tace da Teemahn " _Dama shi mijin kine_ ? Da " _Ummm_ " Teemah ta bata amsa tana mai jin kunyar ta ga jikinta. Nurse na cire hanglove 'din hannun take fadin shine kike cewa yayi miki mugunta ko? Waye ya gaya miki ana fa'din haka?ko bakya son shine akayi muku auren ? Teemah kam shiru tayi tana tunanin me zata ce da Anty nurse 'din, ita kuwa nurse tana har ha'da magunguna taci gaba da fa'din " _kar kinayin taurin kai in bahaka ba kullum ciwo zaki rin'ka ji kinji_ ? Kai ta 'daga mata alamar " _toh_ " " _Yauwa Fateemah, ko kinfi son mijinki yana neman wasu matan awaje_ ? Yanzun ma da kai ta bata amsa daidai Abbas ya turo 'kofan ya shigo dan hankalin sa yakasa kwanciya. Dukkan su sai hankalinsu yakoma kansa. Gefen Teemah yazo ya zauna sai nurse tayi masa bayanin babu ma matsala sosai idan taci gaba da amfani da ruwan 'dumi ma komai zai dai-dai ta. Sai ta bashi wasu magunguna kala biyu tace ta sha wannan zazza6in nata zai sau'ka kuma zai 'kara taimakawa wajen healing ciwon da wuri. Godiya Abbas yayi mata inda a take yabawa Teemah maganin ta sha sai suka fita tare da nurse suka bar Teemah ita ka'dai inda ta koma ta sake kwantawa. Suna fita parlourn nurse tace dashi " _yalla6ai kafa so kayi 6arna gaskiya_ " Kai Abbas ya sosa yace " _Allah ya takaita ai na kuma gode masa_ "! Sai tace " _hakane amma dai a kiyaye gaba saboda gudun matsala duk dama farkon shine_ _me wahala amma gaskiya a'dan sarara mata na kwana biyu_ " " _Bakomai wannan ba matsala bane dr. nagode sosai_ " Daga nan sukayi sallama ta tafi. Teemah kam fitsari ne ya matsata ta tashi ta shiga bayi, tana tsugun nawa sai ta mi'ke dan azaba zafi take ji sosai amma sai ta daure ta sake tsugunnawan sama-sama tayi fitsarin idanun ta harna hawaye amma haka ta daure dan bata so Yayah yasan da ciwon balle yayi mata batun allura. Abbas ma 'dakin nata ya koma sai ya be ganta ba motsin ruwa da yajiyo a bayi ne yasa ya fahimci tana ciki, tsayuwa Abbas yayi yana jiran fitowar ta. Teemah na share hawaye ta fito, tana ganinsa sai tayi turus ta sunkuyar da kanta ahankali ta isa gefen sa kanta a'kasa. Hannunta ya kamo yajawo ta zuwa jikinsa yace " _me yasame ki kike kuka, what's wrong kuma ba kince kin warke ba_ " Kai ta 'daga masa. Abbas shiru yayi yana kallon ta ya san tana jin zafin kawai de tace ta warke ne dan kar yace allura. A hankali ya sake fa'din " _Toh meyafaru_ ? Tace _"ni ka kaini wurin Mummy_ !" " _Ba yau ba sai kin warke zan kaiki owk!_ Shiru tayi bata masa magana ba sai shine ya sake fa'din " _Baki gaji da zama da towel 'din bane har yanzu_ ? " _Yanzun ma kaya zan saka_ " tace da shi a hankali. Sakin ta yayi taje ta dubo kayan sai kuma ta tsaya ta rungume su a'kirjin ta tana kallon shi. " _Ya akayi in zo insa miki ne_ ? Da sauri ta jijjiga kanta " _ko sai na fita_ ? Yayi maganar tare da 'dage gira. " _Umm_ " tace dashi. Sai yayi murmushi tare da barin 'dakin yace " _ina jiranki a parlour yanzu kar ki sake kwanciya fah kinji._ " Kayan tasaka cikin natsuwa sannan ta fita ta same shi akan dinning yana break fast, wurin sa ta isa ta zauna tayi shiru daya nemi taci dai tace ahh sai anjima zata ci,sai daya gama sannan suka koma 'dakin sa dukkan su Teemah bacci take ji dan haka sai da ta kwanta Abbas kuwa system 'dinsa yasa a gaba yana operating zaune kusa da ita seconds-seconds yake juyawa ya ganta. Ranar haka ya wuni agida babu inda yaje illah masallaci, da azahar Teemah ta tashi ta koma 'dakin ta sallah itama, dayake data yi baccin sai taji jikinta yayi mata wani iri zazza6in babu yanzu amma kuma still bata koma normal gaba 'daya ba, ruwa ta watsa ajikin ta ta reda sake zama cikin ruwan 'dumi dan ta fahimci shine ya 'dan sanyaya mata zafin 'dazu dasafe. Wata ba'kar doguwar riga ta sanya ajikin ta me adon golden colour stones manya, sai data idar da sallah sannan ta 'dauki veil shima golden ta yane kanta dashi, parlour ta dawo dan yanzun kam ba laifi ta 'dan ji dama-dama, anan Abbas yazo yasame ta ya kuwa ji da'din hakan shima cikin shigar 'kananun kaya yake bai so fitan ba amma daya tuna cewa gobe ne tafiyar su Mummy sai yaga dacewar kaita dan suyi sallama ma kuma ko dan ya faranta mata tunda dakan ta ma ta nemi zuwa 'dazun, shaf ya manta da batun tafiyar sai yanzu daya fita Daddy ya 'kira shi dan ya isar masa da wani sa'ko shiyasa ma ya tuna sai kawai ya ce da ita tatashi ya kaita gurin Mummy. Yana tafiya zuwa 'dakin sa domin 'dauko key yayi maganar so be kula da yanayin da ta shiga ba abinda ka'dai yasani shine zataji da'din hakan. Teemah kam farin ciki ne yacika sosai har da tashi da 'karfinta dan murna alokacin ne ta tuna da taji zafi a'kasanta amma ahakan ta daure dan kar yace yafasa. Abbas sam hankalin sa be je kan yanayin tafiyar ta ba saboda yaga ta warware shiyasa ma be damu ba be sani ba ashe idan an kula sosai za'a ga chanji tattare da ita. Suna shiga parlourn suka tarar da su Ummah ga6a 'dayan su zaune a cikin parlourn, Teemah taso ta isa da gudu amma sai taji tsoron kar taji zafi sai ta 'karasa a hankali, hakan ma dan tana daure wa ne shiyasa sosai take 'karfin hali wurin ganin ta 6oye ciwon ko dan gudun allura ma. Tana isa ta fa'da jikin Mummy sai kuma ta saki kuka, wanda ya jawo hankalin dukkan su zuwa gare ta, Abbas kam mamaki ne yacika shi ganin lafiya 'kalau suka taho toh menene kuma na kuka yanzu anan. Anty murmushi take yi dan tana ganin Teemah ta fahimci yanayin ta data ke ciki, Ummah kuma mamaki ne ya ziyarce ta yayin da tausayin Teemah ya cika zuciyar Mummy nan take. Abbas zama yayi daga 'dan nesa da su ya zuba mata idanu. Mummy bata tam baye ta me yafaru ba illah kawai rungumar ta da ta yi itama tana babbuga bayan ta alamar rarrashi. Ummah kam Abbas take kallo ganin duk ya zama kamar a birkice da ganin kukan Fateemahn. Anty ne tace da ita " _zo nan Fateema wai me ya sameki kike kuka haka nan ko duk missing 'din namu ne_ ? Taso wa tayi a nutse ta dawo wurin Antyn tana me cigaba da zubda hawaye. Anty mi'kewa tayi tare da kama hannunta suka shige ciki inda sika bar parlourn batare da ko gaisuwa sunyi da Abbas ba. Fitan sun ne yabawa Abbas daman gaida su Ummah, gama gaisuwar keda wuya kuwa Mummy ma ta bar 'dakin dan sosai yau 'din taji nauyin sirikin nata ya kamata. Ummah kuwa ganin anbar su su biyu take sai ta 6ata rai ta kalle shi tace dashi " _Muhammad wace mugun ta kake yiwa yarinyar nan da har_ _take irin wannan kukan_ ? Ido Abbas ya 'dan zaro waje yace " _mugunta dai Ummah ni 'din_ ? _Ai kinsan halin yaron ki ba mugu bane, Allah shagwa6a ce ke kawai damun_ _ta wai dan kanta na ciwo_ " Ya 'karashe maganar da sosa kansa. Ummah cewa tayi " _Ni dai kasan banason zalinci koka'dan ballantana rashin imani da tausayi, komai zakayi ka rin'ka tuna cewa shekarun ku ba 'daya da ita ba da kuma raunin ta na 'ya mace_ "! " _Toh Ummah insha Allahu zan kiyaye_ " Yasan halin Ummahn sa adun'kule yanzun tayi masa fa'dan, yasan ba mamaki tagano matsalar su ne shiyasa tafa'di hakan dan ta gama gano abinda yafaru. Yanzune ma yake jin dama be kawo ta ba yazo abinsa shi ka'dai, bayan yasan su Ummah sun girmi tunanin sa, sai dai kuma a wannan yanayin ba ze iya fita yabar ta ita ka'dai ba hankalinsa ba zai kwanta ba sam, dama beyi niyyan zuwa ko'ina ba sai kuma Daddy ya aike shi. " _Tasha maganin ciwon kan ne_ ? Ummah ta tambaye shi. Da " _ehh Ummah tasha magani tun 'dazu ma_ " yabata amsar tambayar tata. " _Allah ya sauwa'ka toh"_ Toh Ummahn ta sake fa'di atakaice. Anty kam suna shiga ciki ta zaunar da Teemah a bakin gado tare da tsare ta da tambayar me yafaru. Da in-inah Teemah tafara magana cewa " _Ya....yah ne...!_ Da sauri Anty ta tare ta da fa'din " _dukan ki yayi_ ? Sai ta jijjiga kanta alamar " _ah ah_ " Anty kuwa bata sake tambayar ta sai tace " _Toh shikenan kiyi shiru ki daina kuka, jikinki na ciwo sosai ne?_ Cikin shagwa6a Teemah ta bata amsa da fa'din " _K'afata na min ciwo idan...zauna da tafiya... ma_ " " _Toh yi ha'kuri a hankali zai daina kinji, ina kinyi amfani da ruwan zafi_ ? Kai Teemah ta 'daga mata. Anty ma sai ta jinjina kai kawai batare da furta wata kalma ba. Wani abu ta ha'da mata a cup da madara tabata ta ce ta shanye zafin zai daina da iznin Allah. Teemah da bata san ko menene ba kar6a kawai tayi ta shanye abinta dan so takeyi zafin datake ji ya daina gaba 'daya ko dan tana yin fitsari ba fargaba ma. Yanzune Anty ta fahimci cewa barrier 'din da Munnira tayiwa Mahmud da Fateemah yayi tasiri akan su, yanzu ne ta sake tabbatar da gaskiya cewa Mahmud be 'dorawa Fateemah iddar komai ba har yakoma ga mahallicin sa. Ha'kika ta cutar da rayuwar 'danta ta fuskoki da dama, addu'ah tayi masa cikin ranta tare da nema masa gafarar mahalicci. Lallai da gudummuwar ta rayuwar gidan 'dan ta na cikinta ya ta6ar6are, ha'ki'ka bata kasance uwa tagari ba, bata fatan irin hakan yasake faruwa ga rayuwar wanin ta har abada. 'Ko'kari tayi ta maida hawayen ta tace yah Allahu kayafemin, ka kai haske cikin 'kabarin Mahmud. *2:20pm* Hannah ta dawo da mugun gajiyar ta inda tasami Ummah da Abbas zaune a parlour suna 'dan ta6a hira, zama tayi a kusa da Ummah tare da fa'din " _wash Allah na, Ummah na gaji sosai yau 'din nan,_ _Allah gudowa ma nayi_ ". Abbas kallon ta yayi da mamaki yace " _saboda me kenan_ ? Hannah juya idanu tayi sai suka ha'da ido da Ummah afakaice, sai tace " _Yayah lecture 'daya ne yarage mana kuma ance lecturer 'din baya gari shiyasa na taho_ " Abbas shiru yayi ya dai ji tane kawai ba wai dan ya yarda ba, amma be kulata dan shi yanzu damuwar da ta dami ransa dabance, so yake yasan halin da matar sa ke ciki kafin ya wuce. Hannah gaishe shi tayi sai ta tambaye shi " _Yayah ya Teemah fah_ ? Kafin yayi magana sai Ummah ta bata amsa da fa'din " _tana ciki tare suka zo, ba mamaki tana wajen Antyn ta_ " Hannah najin haka ta tashi da sauri jakar ta ma anan tabari ta nufi ciki. Teemah har yanzu tana wurin Anty inda take 'kara jan hankalin ta akan ri'ke mutuncin aurenta sanin girma da kuma darajan da mijin ta ke dashi tare da ri'ke sirrin dake tsakanin su. Da sallama Hannah ta shiga 'dakin ta samu Anty na 'daure wa Teemah gashin kanta. Da gudu taje ta rungume ta tana fa'din " _i so much miss u matar Yayah!tun yaushe kuka zo_ ? " _Zaki karyani Hannah dan Allah_ ! Inji teemah Hannah kuwa sai tace " _Ba laifi ai kona karyakin be wuci ace 'kiyayyar dangin miji ba_ " Murmushi Anty tayi tace musu maza su koma 'dakin su suje su huta wannan hayaniyar ta isa haka. Suna shiga 'dakin Hannah ta sake tambayar ta wai tun yaushe suka zo? Da " _Bamu da'de ba_ " Teemah ta bata amsa tana yatsina fuska. Abbas har zai tafi sai yace da Ummah bari yaga Mummy kafin ya wuce. Yana shiga 6angaren da zai kaishi 'dakin da Mummyn take sai yajiyo hayaniyar Hannah yasan may be suna tare ne tunda yaji hayani ya har haka. Canja hanya yayi ya isa 'dakin Hannah be tsaya bugawa ba kawai ya tura 'kofar sai ya tsaya batare da ya shigo ba. Shiru sukayi da ganin san dama ita Teemah ba wani dogon magana takeyi ba Hannah ce me surutun. Shi kanshi be san me yakawo shi ba, zuciyar sa ke bu'katan hakan, dama ganin ta yaso yi kuma daya gantan sai ya rasa abin fa'da kawai sai ya 'karaso cikin 'dakin a hankali, yazo gabanta ya tsaya yana kallon ta a hankali ya furta " _ya jikin naki_ ? Da sauri tace dashi " _da sau'ki_ " Yace " _toh zan tafi amma anjima zan dawo mu koma gida kinji_ " Teemah shiru tayi masa shima sai kawai ya juya ga Hannah yace " _Hannah plz ki tabbatar taci abinci_ " Yana gama fa'din haka ya fice a 'dakin cikin takunsa na 'kasaita, shi kansa yana mamakin kansa a yau 'din yanda yake ji game da matar tasa, Hannah na wurin ne ma shiyasa be son jan magana sosai. Yana fita Hannah ta tashi da sauri ta le'ka bayan sa ganin yatafin yasa ta sake dawowa wurin Teemah ta dafa kafa'dar ta da mamaki tace " _matar Yayah nifa bangane ba, me ya sameki naji Yayah yana tamabayar jikinki harma da bani kwangilar saki cin abinci_ ? " _banda lafiya ne_ " Teemah ta bata amsa a takaice. Karkata kai Hannah tayi da zararran ido take kallon Teemah da sigar tsokana tace " _Ciwon amarci ko?_ " _Wata'kila_ "! Teemah tace tare da gyara zamanta. " _Kede fa'di gaskiya matar captain ai nima naganki badai ba_ " Da 'dan 'karfi Teemah tace " _Bansani ba Hannah plz ki 'kyaleni ke dama ba mutun ya ha'du dake ba duk_ _yadda yakai ga kewar ki sai kin 6ata ran mutun kike jinda'di_ " Dariya Hannah tayi tace " _Come down mana amarya! 6ata ran me kuma nayi miki amaryar Yayah fisabilillahi? ke de kice bakya so in san cewa Yayah ya fa'da_ _ne, amma ai tun 'dazu ma bangane kanki ba duk kin canja Allah kinyi wata iri_ _ashe ashe yarinya taji da bambanci ne_ !" Saukar da murya Teemah tayi tace " _Hannah Allah banaso bambancin me kuma naji?_ Da murmushi Hannah tace " _Kin fini sani ai yarinya keda kika san komai kuma ni zaki tambaya, jifa yanda yazo shima 'daya ko kunya_ _bai ji wai ya jikin naki.? Bayan yana gani na wurin ko kunyata fa be ji ba"_ Baki ta kama tace " _kai Allah ya shiryi Yayah wallahi_ ". " _Kema Allah ya shirye ki ai kema ba kunyar ne dake ba da kike waya da Bilal a inda nake kina jin kunyata ne? kuma kamar a kunnan sa hakan da kika ce"_ " _Bazan yi mamaki ba ai nasan yanzu amarya kike kuma ba kya laifi, so ko kin kareshi ma nasan ba laifin ki bane, ballantana_ _yanzu da kika san da'din miji nasan fiye da haka ma zakiyi, sai dai plz kiji 'kaina karki fa'dawa Yayah_ _abinda nace nayi al'kawarin indai da raina zan tayaki zaman jego da rainon baby_ " Duka Teemah ta kai mata tare da fa'din "' _yar rainin sense_ _kawai_ " sai ta goce tana dariya tace " _Toh ina laifi da zan miki zaman jego tunda wannan 'din ba a gayya ceni ba wancen kam_ _ai kinga ko babu gayyata sai naje may be ma sanadin haka na samu namesake_ " " Allah ya kiyaye 'yata tazama takwararki" Hannah kwafa tayi tace " _Harma_ ....."? Da " _ehh_ " " _aw ashe ma zaki haihun kinga kuwa zuwana tabbas_ " Teemah ta amsa mata tayi da fa'din " _bismillah sai ki je ai mugani_ " " _Dai na gagagwa kamar yau ne insha Allahu matar Yayah ai anyi me wuyan.... kai amma fa nasan kin ji jiki da ganin_ _yanda kika koma har kina bani tausayi wallahi_ " Juya wa Teemah tayi ta kwanta kawai tana mita wai Hannah ta tattare surutun duk 'yan gidan nan akanta, she is so talkative ita bazata iya da surutun Hannah ba. Hannah ma tashi tayi tana rage kayan jikin ta take sake fa'din " _dan Allah matar Yayah in zaki haihu ki haifo min baby girl me kama dani_ _kinji_ ? Teemah 'kin kulata tayi da Hannah taga haka sai tace bari ta je ta kawo musu abinci......tana fitan tasake fa'din " _ko baki kulani bama de sai kin haifa_ " Abbas daga wurin Mummy ya wuce bai sake dawowa ba. Ko gurin cin abincin Hannah bata bar Teemah da tsokana ba har suka 'kare. Sai daga baya suka koma wajen su Mummy anan ta sake suka ta hira abinsu kamar ba ita ba. Sai bayan sallar isha'i Abbas ya dawo gidan dan su tafi, lokacin kuwa hajiya Fateemah an saki jiki a gida kawai sai taji labarin wai yazo. Ummah ce tace ko za'a barta agida kawai zuwa gobe sai ta koma saboda ganin kamar Teemah batason tafiyar. Teemah kam da murnar ta ta amsa da " _ehh Ummah...._ " Da sauri Mummy da Anty suka ce " _ah ah tafiya zatayi, zaman me zatayi musu kuma anan, gara ta koma gidan_ _mijinta yafi_ " Dole Ummah tayi shiru dan bakin su yafi nata. Da fushi kuwa ta tafi suka bar su Hannah da kewa. Bayan tafiyar su ne Anty tayi wa su Ummah bayanin cewa dama ba iddar Mahmud akan Fateemah, Mahmud be 'dora mata iddah ba, tabasu labarin duk abinda ya faru game da hakan da yake a baya lokacin rasuwar Mahmud bata bayyana wannan 'din ga kowa ba saboda aganin ta sirri ne. Dukkan su sunyi mamaki sosai sai abin yaso ya dawo musu sabo aransu kowa na tunanin ashe har haka Teemah tayi zaman 'kunci tare da Mahmud lalle duniya abin tsorone, tunda gashi wanda akayi domin san ma babu shi yatafi ya bar kowa da tarin nadama. *Allah Ubangiji ya sa mufi 'karfin zu'katan mu ya kyautata mana 'karshen mu.* ( ~Ameen~ ) Mummy ce ke wannan addu'ar acikin ranta, Anty kam hawaye take sharewa a hankali dan ta tuna da 'danta marigayi, Ummah kuwa har taje bacci tana tunanin wannan abin aranta. Suna komawa gida direct 'dakin Abbas suka wuce amma bai bari ta kwanta ba sai da ya bata magani tasha sannan ya bari ta kwanta yaraka 'dakin ta canjo kaya ma 'ki yayi dole sai da ta saka wata t-shirt 'dinsa mai 'dan girma sai kuwa rigar ta rufe mata jiki ka'dan domin ya'dan sau'ko mata, shi kanshi Abbas rigar tana bashi balance bai fiya sakata ba sai in yanada bu'katar shan iska., wanka

Chapter 50 of 67