Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
miki saboda tana_ _damunki_ " Yanzun kam kukan tafara yi masa acikin kukan kuwa tace " _bawani ni kam wallahi ban fa'di haka ba, kawai dan kaga ina bacci na sai kakama kayi_ _min sharri_ " Ta 'karashe da kukkuni 'kasa-'kasa tace " _kawai ka kama ka wani ganewa mutun jiki abanza_ " Tsayawa yayi yana kallon ta domin ayanda yasan Fateemah sarai yasan da iya gaskiyarta take wannan fitinan babu zancen wasa aciki. Ita kuwa tana cikin fa'dar hakan ta hango rigar tata daga 'kar'kashin pillown dake gefenta sai ta sa hannu ta janyo ta still bakinta ature. Tana 'ko'karin sawan ta 'dan saci kallonsa sai kuwa taga ita yake kallo. Kwa6a fuska ta'karayi tare da tura 'kafafu kamar wata karamar yarinya cikin sakalcin kuka da takaici tace " _toh Yayah ka daina kallona mana nii dan Allah_ " Shima cikin halin ko inkula yace " _Idona yana cizonki_ _ne_ ? Ya tambayeta batare da ya kauda idanun nasa akanta ba. " _Toh ka juya zan saka riga ne fah_ " Cewa yayi " _me kuma za'a 6oye min, kin manta ne nagama ganin komai_ ? Kukan shagwa6a ta fara tare da dukansa da rigar hannun nata tana 'kara 'ri'ke mayafin data kare kirjintan dashi da hannunta daya. Mahmud kam yana dariya yatashi yabar mata 'dakin ya koma parlour. 'Karfe shidan safiyar ranar Hannah ta danno mata 'kira alokacin ma ko tashi akan sallaya batayi ba jin 'karan wayan ne yasata ta tashi ta 'dauko ta. Ganin Hannah ce ke 'kiran yasa ta zauna abakin gado tare da amsawa. Gaisawa suka yi Teemah ta tambayeta Ummah da lafiyarta. Hannah kuwa tace da Teenahn " _Ai itace ma tasa na 'kiraki tun jiya ta damu akan na 'kiraki wallahi, wai bata ce idan kin dawo gida ki ha'data da Mahmud_ _bane shine taga shiru har yanzu baki 'kira ba shiyasa ta damu_ " Teemah Cewa tayi da Hannah " _ke nifa babu inda naje dama shirin 'karya nayi dan nasan idan akaji hakan za'a sanar dani abinda ke faruwa dasu Mummy, kuma baga shi ba 'karyata tayi min rana nayi waya dasu mummy harda daddy ba, amma fah dan Allah Hannah karki fa'dawa Ummah haka kawai kice mata wayata bata shiga ne kinji_ " Dariyar mugunta Hannah tayi tare fadin " _Na yaushe kuma yarinya kin makara ai Umnah kan gata nan agefena_ . " Ido Fateemah ta zaro waje tace da Hannahn " _dan Allah dagaske_ ? " _ko de inbata wayar ne 'kilan zaki fi yadda....._ 'Kit Fateema takashe 'kiran tare da kashe wayar ma gaba 'daya tana rufe baki kamar Ummahn na gefenta. Aranar ma da Mahmud zai tafi aiki binsa tayi ya sau'ke ta agidan Umar, shikansa yana 'dan jin kunya yanzun da yawan zuwan Teemahn gidan be san da me zasu fassara hakanba, kuma kar yazamana yawan zuwan Teemah gidan ya kasance yana cutar da matar Umar, shikansa bayason hakan amma be san yadda zeyi ya dakatar da ita ba. Domin koda yace zai kaita gidan Anty ma ba yadda take ba har intaji hakanma sai yaga tafi rikicewa fiye da idan yana ro'kon ta akan ta zauna agida, kuma shi aganinsa ai gidan Anty yafi tunda ko ba komai gidan mahaifinsa nan ne gadaransa . Wannan sabon salon Teemahn na 'daure masa kai matu'ka yanda fir ta tsani zama agida yanzun be san dalilin ba amma shi bayajin da'din hakan ko ka'dan. Haka ya isa office zuciyarsa cike da tunani. Yana zuwa ko zama beyi ba Umar yatare shi da wani sabon batun daya kusan juya mai 'kwa'kwalwa, jiyayi badan abakin Umar abokinsa maganar ke fitowa ba da babu abinda zai hana yayi wa wanda yafa'da 'din mugun dukan da sai yaga stars a idanunsa. Amma dayake Umar ne sai kawai yayi shiru yana sauraransa ransa kuwa gaba 'daya a6ace yake jinsa, daga 'karshen ma daina fahimtar komai yayi yade yi shiru ya zuba wa bakin Umar 'din idanu motsin da bakin yakeyi ka'dai yake iya gani. Har Umar yayi yagama maganar be tankasa ba sai da ya matso ya dafa kafa'dunsa yace " Ban fa'da maka maganar nan dan in tozarta ka ba Mahmud face dan kawo gyara wa lamarin, kai da kanka ka zauna kayi nazari akan haka inajin dakanka zaka fahimci gaskiya, ni kaina naso nayi jayayya kan maganar amma idan kaduba yarinyar nan ka kula da tsanar zama agida datakeyi ita ka'dai shika'dai ma ya isa yasa ka yadda cewa akwai wani abin a'kasa, inaso kabi ahankali harka gano asalin meke faruwa kuma suwaye ne suke shirin yi mata hakan" Umar nagama fa'din haka ya juya ya fita ya bar Mahmud zaune saroro yana tunani. Jiyayi komai ma ya tsaya masa cak, waye.....waye da wannan mugun nufi akan Fateemah,Tunaninsa yakasa bashi ko waye ne. Haka ranar ya wuni a office be tsinana abin kirki ba, koda ya biya 'daukan Teemah ma jikinsa duk da sanyi ita kanta Teemahn sai taji wani iri babu da'di sanadiyyar ganin Mahmud 'din ahaka. Zaton ta ko abinda tamasa da safe ne ya6ata masa rai shiyasa har yanzun be sau'ko ba, amma ai da zasu fita gida ba haka yake ba alokacin har tsokananta yake yi ma. Shiru tayi tana satan kallon shi lokaci zuwa lokaci shikuwa gaba 'daya hankalinsa akan tu'kin dayake yi ya mai dashi wanda hakan yasake rikita zuciyar Fateemah sam takasa samun natsuwa. Koda suka koma gida ma harkokin dake gabansa kawai yayi yayin da Teemah kuwa hankalinta duk yana wajensa sam bata jin da'din yanayin Yayan nata ayau. Har se da akayi sallar maghrib bayan ya dawo gida daga masallaci ya zauna a parlour wanda jin motsinsa yasa ta fitowa tazo gefensa ta zauna tsabar yanda hankalinta yakasa kwanciya ma ko hijabin datayi sallar bata cire ba Fuskar tausayi tace " _Yayah nayi maka wani laifine_ ? Shiru yayi beko kalleta ba. Sai tasake fa'din " _Pls Yayah kayi ha'kuri toh ka yafe min bazan sake 6ata ma rai ba_ " " _Kaji_ ! Be yi magana ba illah juyowa da yayi ya kureta da idanu, itakuwa kasa tayi da nata idanun ganin yana kallonta, kamar ba zeyi magana sai can shima yajefa mata tambaya yace " _Fateemah idan na miki tambaya kinyi al'kawarin zaki_ _sanar dani gaskiya_ ? Zuciyarta taji ya tsinke duk da bata san tambayar da ze matan ba amma gaba 'daya sai taji bata son yayi tambayar. 'Daga idanu tayi sai kuwa caraf suka ha'da ido da Mahmud shikuwa be jira jin amsarta ba yaci gaba da maganarsa. _Comment, Share and Vote @_ ~Serlmerh-md~ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _Laugh when you can, apologize when you should and let go of what you can’t change........_ πŸ…Ώ *64* "Fateemah kigaya min meyasa baki son zama agidannan idan ke ka'dai ce? Da rawar murya tabashi amsa da fa'din" banace maka tsoro nakeji ba" " Tsoron me kike ji inason yau ki gaya min" Mahmud ya fa'da da sauri. Kame kame tafara tarasa ma me zata ce dashi sai ni.......ni....tsoron....... ts Ganin batada niyyan fa'da masa sai yasake jefa mata tambayar su waye suke zuwa gidan nan idan baya nan. Da sauri tace "Bakowa " Tana rarraba idanu. Shima ce mata yayi " 'karya kikeyi Fateema nasan akwai, ki fa'da min zansa ayi maganinsu kinji, bazan ta6a bari su cutar min dake ba muddin ina numfashi, ko kinfiso kullum ki dinga zama agidan mutane yafi miki akan gidan mijinki? Shiru tayi tana sauraransa sai ya kamo hannayenta yari'ke acikin nasa da sigar lallashi yace " _Fateema nifa mijinki ne,me burin ganin farin ciki da walwalarki akowani lokaci, meyasa kika_ _za6i ki 6oyemin damuwarki bayan ni yakamata in fara sanin me_ _kike ciki amma sai de naje naji awani guri Fateema kinajin hakan kinmin adalci_ _kenan_ ? _nine fah me hakkin kula da duk wani hakkinki da_ _damuwarki ayanzun meyasa bazaki bani wannan matsayin ba_ " Fateemah kam haushin kanta take ji ayanzun dan tasan da bata nemi jin damuwarsa ba da baze tuhumeta da wannan maganar a dai-dai wannan lokacin har haka ba, ita kuwa ayanzun da jiran zuwan Daddy kawai takeyi me zesa tafa'da masa abinda ke faruwa, kalan aje akasheta kafin Daddy yazo. Shirun da Mahmud yaga tayi masa ne yasa shi bu'dan baki yana 'karfafa mata zuciya da fa'din " _kar kiji tsoro Fateemah karkiyi kokwanto ko shakka dan Allah ki gaya min kinji_ _am always here 4u_ " Kalmar nan dayafi tsana tasake maimaita, masa wato " _bakomai fah Yayah in akwai ai zan gaya maka_ .... Kallonta yayi cikin idanu domin zuwa yanzun haushi tafara bashi " _Fateemah kina ganin kamar 6oye min damuwarki shine zai kawo miki masalaha acikin_ _al'amuranki ko_ ? _Shikenan idan hakan kike ganin yafimiki so be it nima bazan damu_ _ba, bazan 'kara damuwa da irin hakan ba tunda baki san ina shiga_ _lamuranki_ !" 'Kasa tayi da idanunta da suka cicciko da hawaye tsawon mintina biyu bata 'dago tasake kallonshi ba, hakan yasa Mahmud ya fahimci cewa bazata sanar da shi 'din ba kenan. Tashi yayi da sauri ya tsaya tare da sa hannunsa 'daya ya naushi cikin 'dayan da 'karfi. Kansa yadafe zuciyarsa na masa suya sam yarasa ya zaiyi da ita, 4d first time arayuwarsa da taurin kan Fateemah ya 6ata ransa, daya san bazata sanar dashi ba da be bari Umar yatafi batare da ya sanar dashi ko suwaye suke neman lalata masa rayuwar mata ba. Damuwarsa be wuce yasan kosuye ba, domin yana mamaki, tsawon watanni biyu kenan da zuwan Fateema garin Lagos amma be ta6a jin tamasa hiran wasu da tasani anan 'din ba, kamar yadda yasan bata ta6a fita da sunan ziyartar wani gida ba haka itama bayaga Anty mahaifiyarsa babu wanda ya ta6a zuwa gidan nasu hatta abokansa tun bayan aurensa basu 'kara zuwa ba, mamakinsa shine ya akayi masu neman nata suka santa, da wani lokaci kuma a ina da har zasu nemi maida masa ita jinsin 'yan ma'digo. Toh in dagaske ne meyasa kuma bata sanar dani ba tunda har bata so wanda dalilin hakan nema yasa bata son zama agida, kenan har cikin gidanta suka sameta wannan ai rainin hankali ne. Tunowa yayi da maganar Umar inda yace wai anmata barazana da kisa ne idan har tashigo da wani cikin lamarin, kenan hakan ne dalilin daya sanya ta'ki ta sanar dani, in hakane kuwa lallai mutanen nan basu da hankali, har yaushe zaka sa yarinya 'karama irin Fateemah agaba, meyasa bazasu je su cigaba da yin sha'aninsu a iya junansu da suka saba ba har se sun shigar da innocent soul irin wannan a haukansu. Fita yayi haraban gidan ya ringa gwada 'kiran wayar Umar amma baya 'dagawa haushin haka ya 'kara sa shi jin suya acikin azuciyarsa, jiyake badan dare bane yanzun da babu abinda zai hana shi zuwa wajen Umar 'din ya tuhume shi sai ya sanar dashi kosuwaye ne, dan yanada ya'kinin Umar ze san wani abu akai tunda har labarin ya iso kunnansa, sai de ayanzun shikanshi baya so ya rin'ka garajen barinta agida saboda rashin sanin me ze iya biyo bayan hakan. Haushin kansa ma yake ji da shi da kansan be tsanantawa ransa tunanin dalilin dake hana Fateema zama agida ba, ya tabbata daya nutsu ya bincika da kansa wata'kila da tuni ya san meke faruwa, amma bakomai ko yanzun ma lokaci be 'kure masa ba, da iznin Allah zai bincika 'din kuma zai samo su dakansa koda Umar be fa'da masa ba. Wannan karan kam ba ze yi shiru ba Abbah zai samu yafa'da masa abinda ke faruwa inyaso sai yayi magana a division sukawo masa security ana yi masa gadin gidan a 6oye, kodan ayi saurin kama wa'danda ke da hannu akan lamarin cikin sau'ki. Umar kuwa ya 6oye wa Mahmud sunan dayaji ne akan lamarin badan komai ba sai dan saboda gudun kuskure, kar yaje kuma bayan yafa'a masa bincike yazo ya nuna bahakan bane yaji kunya daga baya shiyasa ya 6oye masa sunan yafi so idan ma su'din ne toh binciken sa ya nuna masa base yaji daga bakinsa ba, kuma idan ya bincika dakansa yaganecgaskiya zefi yadda da batun sa6anin idan aka sanar dashi baze yadda ba sai kaida ka fa'dan idan kayi wasa kanka fushin zai dawo. ***** *MAIDUGURI BORNO* *STATE* Rayuwa yanzu tayiwa Abbas zafi, sam baya ta6a jin da'din duk wani abu dayakeyi, wanda tun farkon auren Mahmud da Fateemah ya tsinci kansa a wannan yanayin, dalilin ma daya sanya shi neman hanya ya taho Barno kenan amma still ya kasa saita al'amuransa, wanda ada yake ganin kamar yin hakan ze 'dabe masa kaso mafi yawa daga cikin damuwarsa amma sai yaga hakan ya kasa yiwuwa agareshi, be tashi fahimtar Fateemah ce rayuwarsa ba har se da ya tabbatar da cewa yarasa ta, shikanshi be san iya adadin soyayyar da yake mata ba sai da yaji labarin za'abawa Mahmud auren ta sannan ya farga da hakan. Rayuwarsa bayan auren Fateemah ta kasance ne gaba 'daya ajuye alokacin komai yakeyi Fateemah ce kawai ke zuwa tunaninsa da idanunsa akowani lokaci, ganinta yakeyi tare da wani da sunan mijinta ne wanda shida kansa shaida ne akan haka. Ya kan 6ata lokaci yana tunaninta ko kuma yayita kallon pictures 'dinta dake cikin wayarsa wanda ita kanta ma bata san da zamansu ba, musamman yake yawan zama da wayarsa agefensa saboda yawan 'dagowa yaga hotonta daya keyi akan lokaci sam baya gajiya, wani write up data ta6a rubutawa ranar da hutunsa ya'kare a Damaturu wannan ma baya ta6a gajiya da karantashi idan yana karantawan kuwa harji yake kamar muryan ta ne ke karatun azuciyarsa tsaban yanda yasata aransa, idan kuwa yazauna yana tuno childish behaviourn ta shi ka 'dai se de kaga yana murmushi duk kuwa da 'kuncin da zuciyarsa take ciki amma baya ta6a denying murmushi akan tunaninta, yagama bawa ransa tabbacin cewa Fateema daban take agurinsa, bayaga mahaifiyarsa da Hannah arayuwarsa be ta6a bawa wata mace muhimmanci ba kamar Fateema shikansa ya yadda cewa irin soyayyar dayake matan nan ba me yankewa bace har abada domin ko bayan auren nata ma be ta6a jin soyayyar ta taragu acikin zuciyarsa ba koda da 'digo 'daya ne. Ganin kamar abin na neman illata masa future 'dinsa ne yasa yanemi hanyar zuwa Borno alokacin har angama cire list ma amma ya nemi asaka shi, wanda kusan kowa idan yaji yana mamaki domin dayawan mutane basu so koka'dan ace sunan su yafito ajerin masu zuwa borno sai gashi shikuma dakansa ma ya nemi asakaya shi, ogansa yaso ya'ki amincewa amma Abbas 'din yadage ya kwantar da kansa yace ko na 5months ne pls akaishi yagaji da zama anan 'dinne kuma shima yanaso adama dashi cikin masu karawa da 'yan ta'addan. Da hakan yasamu aka sanya sunanshi aciki. Bayan bikin Fateemah da sati uku Abbas ya gudu Maiduguri, tunda yazo kuwa abubuwa suka so shan kanshi domin har alokacin dai-dai da kwayar zarra zuciyarsa bata sarara masa daga tunanin Fateemah ba, inda yasami sau'ki ma yanzun baya waya da Mahmud saboda rashin network dan Mahmud baya kwana hu'du me kyau batare da ya 'kira sa ba, wani lokacin sai yaga kamar da gangan Mahmud 'din keyi masa hakan, domin he can't deny it, ba'karamin kishin Mahmud yakeji ba har zuciyarsa ya tsani ganin 'kiran Mahmud awayarsa amma ahakan yake daurewa wani lokacin har shima yake 'kiransa kafin yadawo Maidugurin kenan. Rashin hanyoyin sadarwan dake Jihar Borno yasa ya'danji dama dama yanzun yarage masa ne tsakaninsa da zuciyarsa kawai tunda ba zaiji labarin komai daga wurin kowa ba. Yakan yiwa wayarsa caji duk da batada anfani saboda ba 'kira yakeyi da ita ba kuma shima babu damar a'kirashi amma dan kawai ya ringa kallonta aciki yasa sam wayar bata rabo da caji, duk da idan ya farga da abinda yakeyi 'din yakan yi gaggawan bari tare da neman yafiyar ubangijinsa saboda ayanzu amatsayin matar waninsa take, amma he can't help it baya sanin lokacin da yake zurfafawa atunanin nata ko kuma duba hotunanta da har yau yakasa maye gurbinta azuciyarsa da wa ta. Yanaji tamkar yagama da al'amarin mata arayuwarsa, tun rabuwarsa da Fateemah be 'kara kallon wata mace sau biyu bama balle har yamata kallon mata. Bayaga mahaifinsa dake ta matsa masa akan aure shi kan baya jin kamar ze iya zama da wata mace amatsayin matarsa, ita ka'dai yaso ta ya 'kaunace ta ita ka'dai yabawa muhimmanci arayuwarsa, ita ka'dai take da gurbi da matsayi babba azuciyarsa kuma baya jin akwai wacce zata maye wannan gurbin har abada. Wani sa'in yakanyi mamaki domin kafin rabuwarsa da ita yasan already Fateemah nada feelings akansa, amma be san meyasa ta ta amince da auren Mahmud ba, ko dayake wasu soyayyarsu ba guda bace takan rarraba kanta zuwa wani 6angaren daban. Da yawan lokuta Fateemah yake 'daurawa laifi dan shi aganinsa da amincewarta ne komai ya wakana badan ta amince ba da yasan daddy bazai ta6a 'daura mata aure da Mahmud ba, wani lokaci sai yaga kamar da gangan ne taza6i Mahmud akansa danta muzant shi. Bayan zuwan sa Maiduguri da 'yan kwanaki ne ya 'dan fara jin dama-dama azuciyarsa game da Fateemahn badan komai ba sai dan yariga yasawa ransa cewar tabarshi kenan har abada, kuma sai yake ga dama haka 'kaddarar rayuwarsu tazo kaddara kuwa dolen kowani musulmi ne ko ya so ko ya'ki sannan aikin daya kawo shi maiduguri ma sai ya 'kara 'dauke hankalinsa gaba 'daya daga kan mafi yawan abubuwan rayuwarsa, abubuwa duk suka rinca6e masa, komai na rayuwarsa yaja baya, be fiya samun lokacin da ze zauna yayi tunanin rayuwarsa ba ko wani abu daban, abinda kawai yasa agaba shine ta'addacin dake bawa jahar borno kashi yake kuma sasu rayuwa cikin 'kunci da tashin hankali akowani lokaci. Wannan dalilin ne yasanya komai ma yabar kansa hatta Fateeman yakan wuni ya kwana bata shigo cikin tunaninsa ba, sai yake jin ma hakan yafi masa gara ya fuskanci rayuwarsa ya manta da duk wani abinda ya wuce tunda bashi da ikon canja komai, sai de dukda haka al'kawarin daya yiwa daddy kullun yana cikin ransa so yake abubuwa su 'dan tsagaita masa yasamu damar cikawa daddyn al'kwarinsa kamar yadda ya 'dauka, lokaci ne basamu ba amma be ta6a mantawa da hakan ba, yariga yasawa ransa zuwan duk da zuciyarsa bataso amma dole ne yaje Lagos saboda Daddy yafi 'karfin wasa arayuwarsa. ***** *LAGOS STATE NIGERIA* _8:21am_ Munnira ce zaune agefen a kan dinning table Anty yayinda ke siffing tea ka'dan-ka'dan at d same time kuma Anty ke bata ha'kuri tare da sake jaddada mata cewa takusan samun Mahmud a hannu domin Chiddy nasamun abinda takeso komai zai zama tarihi. Dariya Munniran tayi tace " _ai na dena damuwa Anty, tunda naje ni aka_ ' _kara duba min cewa har yanzu aikina na jikinsu hankalina yakwanta_, _dan nasan kowan nan ka'dai na dogara dashi ma makami_ _ne babba balle kuma ke da kanki kinsa min hannu_ " Anty ma murmushi tayi tace " _ke kuwa 'yar nan wani irin aiki kikayi haka_ ?. Munnira kwashe komai tayi ta sanar da Anty. Tace " _ai tun ranar dinner 'din auren su_ _nayi_ _maganinsu, kinsan yanda nake son Mahmud haka nake kishin sa, toh taya zan bari inagani ya_ _ra6i wata mace daban ni ina nan........._ Kaita ta juya ka'dan tace " _zuciyata bazata iya 'dauka ba Anty, shiyasa nasaka akayi musu_ _katanga wanda bazai ta6a bari su anfani juna ba , ita nasa akasawa_ ' _karfin sha'awa wanda idan ya 'debe ta dole sai ta nemi atallafa mata....._ _amma fah Anty da 'kyar nasamu aikin yayiwu......._ " _Mtheww wai su adole masu rotson Allah, kinsan kuwa wanda nayi mata ranar dinnern_ _ma ko kamata beyi ba, sai da na koma shine bokan yace min wai sede atura mata aljani wanda zai ri'ka sata jin_ _sha'awar ammafa bakowani lokaci ba, sai in lokacin daya samu kanta_ _tukunna sannan se sakata, shi 'dinma Anty da 'kyar yasamu yashigeta_ _inji bokan, amma jiya dana koma yace min komai_ _normal, shirina yana tafiya akan_ _tsari banda_ _matsalar komai_ ". Kallon Anty tayi wacce tabaza kunnuwa take jin tsaban shu'umanci irin na Munniran sai ma taji ta 'kara birgeta data yi maganinsu, ai ita da farko ma tunaninta beje ga hakan ba tazauna sa'ka'ka kawai tana jiran rabuwarsu ashe hauka tayi, inbadan Munniran ta yun'kura bama ai tanajin abun nasu sai yafi haka. Sai de kuma ai yiwa Fateeman haka bashine mafita ba, domin koda abun yatashi mata mijinta ze iya yin maganin matsalar ai tunda shi ba 'a yi masa komai ba. Sai de duk da haka ta wani guri batun Munniran ze iya samun kason maki mafi girma idan aka gangara 6angaren yawan bu'katuwa da kuma sashin gazawa. Ta iya yiwuwa hakan ya ta6a zaman lafiyarsu idan mijin yaga ji da yawan bu'katan Fateeman ze iya nuna gazawarsa wanda ta nan babban matsalan zai iya bayyana harma ya illata farin cikin dake cikin zamankewarsu....... lallai Munnira tayi tunani me kyau. Anty na cikin wannan tunanin se Munnira ta katse ta da fa'din " _Anty kinsan iskancin dana sa akayi musu kuwa_ ? Da kai Anty ta bata amsa alamar " _a'a_ ". Murmushi Munnira tayi sannan tace " _Mahmud bashi da daman taimakon Fateemah koda jarabarta ta tashi_ _saboda shi bashida anfani, tsakaninsa da ita sai de kallo Anty, kinga idan_ _abun ya isheta dole zata nemi mafita mafitar danasan bazai wuce tace_ _araba auren sun ba, kinga dazarar auren yarabu sai inkoma insa adawo wa_ _Mahmud da lafiyar mazantakarsa sai muyi aurenmu dashi, ko kuma ince ya aureni ni zan iya_ _zama dashi ahakan tunda ita ta'ki kinga bayan an 'daura auren sai lafiyarsa ta dawo ni_ _kuwa zama daram Anty sai ke sai jikoki"_ Ta 'karashe maganar da dariya. Anty ma murmushi tayi da farko dataji batun Munniran akan Mahmud hankalinta ba 'karamin tashi yayi ba amma 'karshen labarin sai ya wanki wancen 'din tunda taji komai zai dawo normal daga baya sai taji ranta wasai. " _lallai kanki naja 'yan mata shiyasa nake 'kara sonki ai, dan nasan ki akwai kishin kai, sai dai kuma fah karki kuskura wannan abin yata6a min lafiyar yarona dan kinsan mutuncinsa kenan_ _ako'ina_ " Wani dariyar 'keta Munniran tasaki kamar wanda Anty sa'ar ta ce, Sannan tace " _Haba Anty,ni da nake farautarsa dan anfanin kaina taya kuma zan bari gangancina ya illata sa, komai da kike gani akan tsari nake yinsa kuma kafin ayi aikin sai dana tabbatar da cewa za'a iya rabashi da hakan_ _aduk lokacin dana bu'kata kinga kuwa ai ba abin damuwa_ _anan_ ". Anty kuwa tamkar wawuya haka take binta da idanu domin gaba 'daya ta tsinke da lamarin yarinyar gani takeyi tamkar wannan tamafi uwarta shu'umanci, amma tsabar haukan Anty bata ji ko 'diris aranta cewa wannan ba kalan auren 'danta Mahmud bane sai ma taji 'karin 'kwarin gwiwa akan Munniran. Ita kuwa Munnira tana gama fa'din maganar ta mi'ke tsaye tare da gyara zaman rolling 'din dake kanta tace " _Yauma ni kinga son ganinshi nakeyi wallahi shiyasa ma kika ga na fito_ _da sassafen nan office 'dinsa zani gara tun wuri mu fara_ _fahimtar juna tunda gab muke da zama_ _abu 'daya_ " " _Aikuwa da gaskiyarki_ " Anty tabata amsa gami da fa'din, " _inkinje ki dawo dan Allah kafin ki wuce gida akwai sa'kona_ " " _Toh Anty bazan_ _ma da'de ba_ _zandawo_ " Munnira tayi maganar tana nufan 'kofar fita daga parlourn. ***** Mahmud kam lokacin daya shirya fita aiki exactly be sa6a lokaci ba yakan yawaita barin gida 7:30 dayake sai 9:00 ake bu'de kamfanin nasu so yana samun time yayi komai atsanake. Ko yau 'din ma haka yayi shirinsa cikin wata arniyar shadda gezna milk colour, Fateemah nata binsa da idanu domin ita yau 'din gaba 'daya bata jin da'di, fargaba ne yacika mata zuciya da batasan kona menene ba, hatta ga6o6inta asake take jinsu, duk abinda Mahmud yakeyi da idanu kawai take binsa. Break fast ma yau tea ka'dai taha'da masa ita kam tasha ma sam ta gagara shine dai yasha ka'dan sai ya tashi da niyyar tafiya, itama mi'kewa tayi dama already mayafinta yana ajiye agefenta sai kawai tafara warware shi. Ganin hakan yasashi tsayuwa saroro yana kallonta sai data gama warwarewan kafin yace mata " _yau fah ba inda zakije, agida zaki zauna tunda kin'ki ki sanar dani_ _dodon dake hanaki zama, kuma ma kinga yau friday ne bazan da'de ba zandawo 12:00_ _za'a rufe office ki_ _zauna

Chapter 34 of 67