Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yayan nata dan indai haka ne zai wuya zumunci ya yanke atsakaninsu. Sai da sukayo sallar isha'i kafin suka 'kara komawa cikin gida, suna zuwa yawuce wurin mummy yace 6angaren sa yake so akai musu abincin su acan zasu ci. Da " toh " ta amsa masa shikuma daganan ya juya yakoma 6angaren nasa ya samu Abbah. Teemah aka saka ta kawo abincin gaba 'daya, kuma sai alokacin ne ta samu tagaida Abbahn saboda 'dazu batasamu hankalin gaidashi ba ganin mummynta na kuka. Muryarta da sanyi sanyi tace "ina yini" Yana cewa" lafiya" kan ya 'kara wata magana harta ma'ke tsaye bata 'kara yin wata magana ba, saboda ita sam ji tayi mutumin be kwanta mata arai ba musamman data fahimci adalilinsa mummynta ke kuka 'dazu kuma tun fitar su take ta tambayar mummy akan abinda yasa metan ta'ki gaya mata haka ma data ce mata mutunin 'kin kulata tayi, tana ganin kamar tasan mutumin awuni wuri amma takasa tuno a inda tasan shi 'din hakan yasa tayi fishi ta 'kyale mummyn tayi tafiyarta 'dakinta bata sake dawo wa ba sai yanzun da mummy tasa ta kawo musu abinci. Tana cikin tunanin taji yo muryar Abbah yace mata " angama makaranta lafiya ko Fateema?" " ehh lafiya 'kalau". " Toh Allah yabada sa'a yasa me amfani ne" Ciki-ciki ta amsa da " Ameen ". Shi kuma daddynta da yaga yanda tayi maganar kamar ranta be so cikin sanyi sai ya 'kirata zuwa inda yake zaune yace mata " yah na ganki haka Angel 'din daddy, meke faruwa ne? " bakomai daddy"! Yace " kin gane wannan 'din kuwa "? Ya 'kara sa maganar da nuno Abbah da hannunsa. Jijjiga kanta tayi tare da kallon Abban atake sai ta gano kamar da yake da Mahmud da tunda bata lura ba sai yanzun . Bud'an baki tayi tace. " Lah daddy kamar yana kama Yah Mahmud". Dariya suka sanya dukkansu har Abban Teemah kam sai ta tsaya tana kallon su, hatta da dariyar su ma iri 'daya ce da yah Mahmud ta fa'di aranta. " Allah me iko" . Sai taji daddynta na fa'din " mamanki bata fa'da miki waye shi ba? ". Kai ta 'kara jijjiga wa alamar " ehh". Abbah da daddy duk sunyi mamaki kowa yajinjina al'amarin Khadeejan acikin ransa wanda hakan 'karara ya nuna azahirance cewa ranta ya 6aci da Yayan nata ne duk da 'dazu ta 'dan sau'ko kafin tafiyarsu masallaci. Abbah beyi mamaki ba domin aganinsa sam koma me tayi bata da laifi ta cancanci tayi fiye ma da hakan saboda ita akawa ba dai dai ba. Yayinda Daddy yake tunanin irin 'kunci da damuwan da ta rin'ka shiga abaya duk asanadin rashin 'dan uwanta amma ace yanzu taganshi yana cikin gidanta amma kuma sai ta tsiri shariya! Kai abin da mamaki gaskiya, amma yazama dole Fateemah tasan matsayinsa awurin ta da maman nata gaba 'daya, koma miye yafaru ai be kamata ta'ki sanar da 'yarta koshi waye ba." Azahiri kuma sai ya fuskanci Teemah yace " Kinga wannan dakike gani azaune anan toh yayan mummyn kine, Uncle 'dinki ne, kuma mahaifin yayanki ne wato Mahmud. Ido ta zaro waje tana kallon daddyn alamar mamaki. Sai ya yayi murmushi tare da jinjina nata kai sannan yacigaba da fa'din " musamman fah yazo tun daga Lagos dan ya gaishe mu yakuma tayaki murnar kammala makarantar dakika yi" Yana kawo wa dai dai nan yakamo hannunta yace " Jeki gaida shi da kyau kinji ". Duk abin nan dake faruwa Abbah kallonsu kawai yakeyi, ba 'karamin birgeshi sukeyi ba sai azuciyarsa yake 'kara jin son faruwar wancen al'amarin musamman ma daya lura da cewa Fateemahn akwai nutsuwa, zai so 'dan shi ya aureta su rayu dashi, in har Mahmud ya aureta koba komai yasan shi bazai yi rashin dacen iyali irin nasa ba. Ahankali cikin natsuwa ta mi'ke ta nufi Abban taje ta tsugunna gefe dashi daga 'kasa ta gaida shi ya amsa fuskarsa kamar gonan auduga. Tambayarsa tayi yasu Mahmud fah da An..Anty " Ta tambaya harda Antyn ne saboda sanin sunan Anty datayi a bakin Mummy da kuma Yah Mahmud lokacin data Antyn ke yawan damunsa akan ya koma gida sa'ilin da yana service anan balle data ta6a daka mata wta uwar tsawa wata rana akan ta 'dauki wayar Mahmud toh tun lokacin bata ta6a mantawa da ita ba. Abbah kuwa da 'din hakan yaji sai ya amsa fa'din " suna nan lafiya tare sanba'da mata ruwan albarkatai. Bata tashi akusa da Abban ba mummy ta shigo da sallamarta ,suka amsa gaba 'dayanau har Teemahn Abin mamaki fuskar mummy wasai tana murmushi tacewa Teemahn " ke kuma kin wani nutsu kamar me hankali ya baki zuba musu abincin ba haryanzu ?" Dawo da kallonta tayi gurin Daddy tace " hala bakwa jin yunwa ne shiyasa." " Yah yusuf hu'du ban me kake mata haka har kuka manta da cikin ku." Dariyah suka sanya dukkansu cikin jin da'di, Teemah ce ka'dai tayi murmushi ,kowannensu yaji dad'in sakewan da Mummy tayi musamman daya kasance ita da kanta tazo harma tasa su dariya, ta kuma 'kara da fa'din " dan ku tashi kuci abinci dare na 'karayi ". Da kanta ta zuzzuba musu abincin tace bismillah Teemah kuwa hanyar wahe ta nufah sai Abbah ya hangota sanda take daf da barin 'dakin " tafiya zakiyi ko Fateemah" Tsayawa tayi caka ta juyo tace " ehh Abbah inajin bacci ne sai da safe" " toh Allah ya bamu alkhairi" Abban ya fa'di tare da fara cin abincinsa. Harta kusan fita a'dakin sai mummy tace " ki jirani a'dakina ina zuwa yanzu". " Toh mummy" Tace tare da barin 'dakin. _Comment_ , _Share &_ _Vote_ _Pls_🀞🏻 *Readers adinga* *min uzuri dan Allah kamar yanda nasan ku dashi, nasan ba kullum nake samun* *daman yi muku* *typing ba* *abubuwane suke* *min yawa , ni kaina bajin da'din hakan nake ba amma* *insha Allahu komai* *yakusan* *daidaita* . *Bear with me pls* Ina masoyan Mahmud ku toh duk ku marmatso kuji😜........ *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Control your _Anger_ , it is one letter away from _Danger_ . πŸ…Ώ *39* *BORNO STATE* Motar su Abbas na fita daga wurin graduation 'din hanyan Maiduguri suka 'dauka basu tsaya ko'ina ba sai a wani gidan mai, koda suka sha man kuwa hanya straight suka kama batare da ya sake komawa gida ba. Hakimce yake a seat 'din baya inka ganshi zaka zaci wani basareka ne musamman inkayi duba da yanayin zaman dayayi, yawani hakimce baya fa'din komai sai in lokacin da zai yi magana da driver ne kafin zakaji muryarsa, balle ma ba wata maganar kirki sukayi tsakaninsu ba inya wuci aikin bada umarni. Da ikon Allah kuwa lafiya lau suka isa, Abbas saka drivern yayi ya yi tu'ki a high speed shiyasa suka isa dawuri, kuma cikin kariyar ubangiji babu wani abin da suka ha'du dashi ahanya wanda yake ba daidai bane. Da shigarsu cikin garin Maiduguri sai suka wuche gidan ogansa me suna Oga philip, suna yin horn me gadi ya bu'de musu 'kofa. Ko zama Abbas beyiba ya fara shirin tafiya inda ya fito oga Philip bai so hakan ba amma Abbas yace ana nemansa ne shiyasa, dolen oga Philip ya barshi yagama kintsawa yafito, lokacin 'karfe hu'du kusan da rabi na yamma 4:28pm , sallama yayi musu tare da godiyah sosai saboda Oga philip mutun ne daya cancanci ayi masa godiya, tun farko Allah ya ha'da jininsu da Abbas tun farkon ha'duwarsu awurin wani course dasuka je bada jimawa ba, yana shiyake kula daduk wani abu dayashafi Abbas 'din ko kuma zai taso ta 6angarensa yakan yi 'ko'kari sosai wajen ganin ba'a samu wata matsala ba. Duk sau'kan da Abbas zaiyi a maiduguri toh Oga philip ne ke bashi masau''ki ko a agidansa ko kuma wani gidan daban, shiyasa ko wannan zuwan ma da yayi sai ya sau'ka agidansa, bashi da matsala komai,inkuwa yaji an'kira sallah baya 6ata lokaci yake isa masallacin dayake akwai akusa dasu, kuma daya sanar dashi cewa yana so yaje damaturu amma yace bazai kwana ba aranar zai dawo sai Oga philip 'din yace " toh ba matsala daganan ya ha'dashi da driver suka kama hanya suka zo damaturun atare, yakuma ce da drivern yakula da tu'ki da kyau dan kawai saboda Abbas 'din. Yanzun ma sawa yayi aka 'kara kai Abbas 'din airport yakuma binshi da fatan alkhairi. Bai 'kira kowa ba aranar sai mummy ya mata sallama awaya dayake itan basu ha'du ba lokacin da zai tafi shiyasa ya 'kirata yace mata ya wuche Porthacourt. Sai dai kuma tun lokacin da yatafi ya bar Teemah a tsaye yakejin be kyauta mata ba harma dashi kansa, sai yake jin dama ya tsaya ya kar6i leave awurin aiki kafin ya taho 'din da yasan komin yaya de zai 'dan yi kwana biyu, da zaiyi irin wannan tafiyar ba. Amma yazaiyi hakan ma ba laifi tunda yagama abinda yakawo shi dama burinsa yaganta kuma yagantan, wannan ma satan hanya yayi shiyasa and baya son tun ba'aje ko'ina da fara aikin ba ya fara samun problem dasu shiyasa yatafi aranar batare da ya ko tsaya sun yi gaisuwar kirki da su daddyn ba dan ma kar ya shiga cikin lokacinsa. *DAMATURU, YOBE* *STATE* Koda fitan Teemah a'dakin direct 6angaren mummyn ta nufa dan cika umarninta, mummy kuwa bata bi bayanta ba sai ma kujera dataja tayi zamanta, su Abbah nagama cin dinner suka sha hirar yaushe gamo da kuma tuna baya da yayan nata wannan karon faran-faran batare da wani damuwa ba. Daddy ne yace maza ta tashi ta tafi dan kamar yaji tace Teemah ta jirata a'daki yace tayi sauri taje kar ta hana masa yarinya bacci. " su yarinya manya" Inji mummyn Tana dariya tabar 'dakin tare da yi musu sai da safe. Koda ta isa 'dakin nata kuwa barci tasamu Teemahn nayi abakin gadonta kamar ma zata zame ta fa'do, aranta tace " Allah sarki harta gaji da jira tayi bacci. Taso ta tasheta amma ganin yanda tasake take bacvcn sai ta 'kyaleta kawai anan 'din sai dai ta 'dan bigeta ahankali tace " ta gyara kwanciyar tata da kyau. Daddy har yayi shirin bacci sai kuma yaji kamar akwai kukan sauro ka'dan a'dakin kuma gashi yanada ba'ko sai yace bari ya 'dauko magani dayake shi dama ba so yakeyi ba be fiya anfami dashi ba dama mummy ce dayake ita ko kukan sauro na hanata bacci shiyasa sam bata rabuwa da insecticide a'dakinta. Mummy nagama shiri kenan saura ta kwanciya, sai kuma tajiyo kamar motsi a parlour da farko harta 'dan tsorata sai ta tsaya cak a inda take tsayen, tana cigaba sauraron motsin yayinda yake 'kara tunkaro ta sai kuma tajiyo muryar daddy yana sallama ahankali saboda dare. Sai da ta amsa kafin tace " ai har kaban tsoro ma" " very sorry, maganin sauro za'a bamu naji kamar akwai 'dan kukan sauro a'dakin". " ah ah kaida kece bakaso?". " ehh albarkacin ba'ko za'a bani " "Hmm kai de fa'di gaskiya " Tayi maganar tare da juyawa dan zuwa inda maganin yake ajiye, sai kuma asannan daddy ya lura da Teemah dake kwance, "sai da kika samin yarinya bacci anan ko?" Sai tayi saurin fa'din " kafin nazo ma harta yi baccinta". " badole ba ina zata iya jiranki kinje kin samu Yayanki kina ta'di kin manata da ita, badole tayi baccinta ba itama, aini banga laifinta ba". Batayi magana ba bayaga " hmm" kawai sai mi'ka masa Insecticide 'din shi kuma maimakon ya kar6a a'a, sai ya mi'ka hannunsa ya cafko nata hannun yajata zuwa parlour binsa tayi kamat ra'kuma itama. Zama yaje yayi akan kujera ita kuwa sai takalleshi da mamaki tana daga tsayen tace " yalla6ai ya haka naga ka zauna?". " magana zamuyi Khadija " Ido ta zaro waje tare da fa'din yanzun kuma?, da daren nan." " ahakan tazo Khadeeja, kuma ahakan za'ayi" Ya fa'da in a serious tune ,ganin hakan yasa mummy taje ta zaunan itama ta fuskance shi. " yauwa ki saurareni da kyau kiji, kinsan Yusuf 'din nan abokina ne shi tunma kafin na ha'du da ke right? Sai tace " ehh". " toh amatsayinsa na abokina misali idan akace ya nemi alafarma agurina kina ganin ya kamata na'ki saurarensa"? tace " a'a " " saboda me"? " saboda zumunchi ,kuma ya kamata ka karramashi amatsayinsa na aboki agareka." " idan kuma ya 'kara da zamowa sirki ( in-law) agareni fah "? "Fiye da hakan ma zakayi masa inda hali". "good". Yace da jin da'di sannan yaci gaba da fa'din " Yataso ne musamman all d way from Lagos ya zonan dan kawai yasada zumunci dake tsakani, wanda nake tunanin cewa ada sam babu shi, nasan kinsan da haka ko"? " ehh" Tace asanyaye dan tafara jin tsinkewan zuciya akan wannan irin maganganun daddyn. " Lokacin da zaizo be zo da niyyar neman aure ba face abin da nafa'da miki abaya, saboda ya sanar dani da jimawa akan zezo mana nan amma bai sa rana ba saboda kar ya saka rana yazo tafiyar bata yiwu ba, shiyasa yabari ahaka nima kuma dalilin dayasa na'ki fa'da miki kenan, amma Alhamdulillah sai gashi yazo mana batare da munsan ma yataso ba, sai kawai muka ganshi. "Hakane"? Mummy kai kawai ta 'daga masa domin jikinta yafara yin sanyi da wa'dannan irin maganganun, kardai Yah yusuf ku'di yake bu'kata awurin Daddy, haba no waonder taga ya rame ba kamar da dayake da 'dan 'kibarsa ba, ashe ya'dan shiga damuwa ne shiyasa............... Firgigi tayi tana kallon daddyn domin tana cikin tunanin tajishi yace " kina jina" da 'dan 'karfi, bata sani ba ashe bakinsa na biyu kenan domin na farkon kamma batasan yayi ba. Ran'kwafowa yayi yana dubanta da kyau sannan yace " tunanin me kuma kike yi Khadeeja"? Bakinta har karo yakeyi wajen fa'din " ba komai". Owk Yace sannan yaci gaba " Allah cikin ikonsa tun da yaga Fateemah sai ya yaba da hankalinta harma yace yanason aurenta ma 'danshi Mahmud" Ido mummy tazaro waje tare da mi'kewa tsaye akan daddyn. " Mahmud de" Tafa'di tare da nuni da wani 6angare tamkar Mahmud 'din yana wajen. " shi de bawani ba, be yi bane ko me" Shiru tayi still tana tsayen. Hannu ya mi'ka yakamo nata hannun "Zauna mana sai ki yimin bayani da kyau wala Allah zanfi fahimtarki". Zaman tayi kamar yadda ya bu'kata amma bata iya yin wata magana ba. Daddy kuwa sai yaci gaba da fa'din " Khadija mun kusan kammalawa da maganar ahalin da ake ciki yanzu 'karshen furuci na kawai yake jira yaji". "Toh kace masa baka amince ba kawai" " awani dalili" yaddyn ya tambayeta. " Habah, haba dan Allah Mahmud fah naji kace? " ehh mana, ko kina da wani wanda kike ganin yafi Mahmud 'din" Karka'da kai tayi cikin takaici "Amma inajin ka manta wacece mahaifiy.......... " hold it pls, lets go straight to d point, ok!". Yatari maganan da tayi niyyan fa'din cikin gaggawa harma da 'daga hannunsa 'daya sama , wanda hakan 'karara yake nuni da cewa baya bu'katan jin komai daga gareta. Shiru mummy tayi tare da binsa da idanu, mamaki ma yake bata daman ta da'de da fahimtarsa aganin ta shi sam baya so yaji anfa'di karkatacciyar magana akan Yah yusuf 'din sai yayi 'ko'karin gyarata, shiyasa da datake yawan complain akan sharetan da yakeyi shi daddyn shine me tausarta akullum sai ya nuna kamar wai abubuwa ne suka masa yawa, sai da abin yayi yawane kafin shima ya saduda ya goyi bayanta amma duk da be ta6a nuna mata cewa Yah yusuf 'din badai dai yakeba, sai de yace suci gaba da addua kawai, kuma duk wannan abubuwan dasuke faruwa ita aganinta bakomai kesa daddy yin hakan ba face akan goya masa baya da Yah yusuf 'din yayi lokacin da daddyn ya nemi auranta. Jinsa yayinda shi kuma yaci gaba da fa'din " munyi magana dashi kuma na fahimce shi, ayanzu kuma gab nake da nuna amincewa ta 100% saboda girma dayake dashi a idanuna, bazan iya 'kin nuna amincewata ba kuma ina fatan kema zaki goya min baya with all your support". Ya 'karashe maganan yana kallonta. Itama kallon nasa ta tsayayi daga baya baya kuma ta kauda kanta gefe. " taya za'ayi na goyi bayanka alhali ina da tabbacin Anty bazata ta6a son zuri'armu ba, balle ma har ace 'yar da ni na haifa, 'danta ya aura!" Gashi kai kuma ka kasa fahimta ta" Nasiha sosai daddy ya mata wanda ya matu'kar kashe mata jiki tare da kawo ayoyi da hadisai wanda suke nuni akan halayyar 'dan Adam da kuma bata misalai akan yadda ikon Allah ya buwayi ko'ina yace mutun ba komai ba bane shi compares to mahallici dan haka komai zatayi ta yadda da Allah da kuma 'karfin ikonsa kafin tasa tsoron wani abin halitta. Ya 'karasa da cewa " ina fatan kin fahimceni kuma zaki bani ha'din kai" ahanakali tace" insha Allahu". "Yauwa, sai da safe". Yana mi'kewa ya fa'di hakan yayinda mummy takasa amsa sai da safen dayake mata, ta dai tsaya atsaye duk tunani ya cikata, " ha'ki'ka gaskiya Daddy ya fa'da kuma tasani cewa Allah ne mafi rinjaye akan komai, toh amma abinda takasa ganewa shine kar dai ace wannan dalilin ne ya kawo Yah yusuf inda take?" Sosai abin nan ya dameta, washe gari kuwa bata nuna komai ba suka yi gaisuwa cikin sakin fuska har suka gama karyawa sannan ne da suka ke6e da Abbah ta sake jefah mishi tambayar da ke damunta azuci inda tace " kar dai abin nan daka fa'da jiya shi ya kawo Yah Yusuf garin nan?". " ah, ah, ah, khadeeja, kin manta me na gaya miki ne jiya hala? Ido ta tsura masa tana kallonsa ga dukkan alamu cikakken bayani take bu'kata daga wurinsa. Ganin hakan sai ya ci gaba da fa'din " ba abinda yakawo shi kenan ba, kamar yanda na sanar dake ,yazo ne ya sada zumunchi sai kuma yayi katari da Fateemah sai yaga dacewa da sha'awar aurawa 'dansa ita shine yamin maganan nima kuma na amince, kinga gara namiki gwari-gwari yanda zakifi fahimta." Ya 'karasa da murmushi " amma kai kana ganin bawata matsala ko? nifah gaskiya ina tsoron abinda zaije yadawo, kafa san halin Anty ba 'kaunar mu take ba gaba 'daya". " Kin manta wannan 'dinma kenan ko?" Kauda kai tayi gefe tare da fad'in " ban manta ba" " toh karki damu kanki dan Allah, ita 'din ba Allah bane ya halicceta?, ki ringa sawa ranki yadda da 'kaddara kowacce iri ce, na tabbata 'kaddaran wannan al'amarin ne yakawo shi akwannan, toh kinga kuwa idan har Allah yace za'ayi toh fitinan wani ko wata be isa yasa afasa ba,dan haka ki saki ranki kinji". "Da kai ta amsa masa, dan kasa bu'dan baki tayi ta ce komai. Ko bayan barin sa 'dakin ma bata motsa ayanda ya bartan ba, tun yanzun tausayin 'yarta yafara shiganta. Daddy kuwa da komawarsa wurin Abbah sai suka kammala magana inda daddy sai alokacin ne ya nuna amince warsa akan lamarin, 'karyar da yiwa mummy kuwa akan tunruni ma ya amince yayi hakane saboda ta daina sawa ranta kamar maganar zata fasu. Yayin da Abbah ya nuna tsantsan farin ciki da amincewar daddyn harma ya 'kara da fa'din " bada wani jimawa ba zasu ji daga garesu domin baya so a'dauki dogon lokaci akan lamarin". " bakomai ai, Allah ya nuna mana " inji Daddyn Teemah Zama suka yi suna 'dan ta6a hira tsakaninsu anan mummy ta tadda su, aka cigaba da hiran da ita, ranta ajagule take jinsa ,amma bata so Yah yusuf ya zargi wani abu daga 6angarenta shiyasa ma ta taho inda suke 'din, kuma ma dan kar daddy yace ta'ki jin maganarsa. Da lokacin tafiyar Abbah yayi sosai ya musu alkhairi daga mummyn har Teemah, ya bawa kowa kyautan ku'di daidai yanda yayi ra'ayi saboda acewarsa be taho musu da komai ba wai suyi ha'kuri da wannan sai in ya 'kara dawowa. Teemah da bata san abinda ke faruwa ba taringa bashi 'sakon gaida Yah Mahmud kusan sau hu'du tana maimaitawa jitake kamar tabishi su tafi, shikiwa Abbah sai amsa mata yakeyi yana murmushi da jin da'di, sai da mummy ta banka mata harara kafin tayi shiru ta daina magana. Da daddy suka tafi domin shima akwai abinda zai kashi can arean Lagos 'din harkan kasuwancinsa. *LAGOS* Koda Abbah ya isa gida Mahmud ne ka'dai ya nuna farin ciki da dawowar tashi, dan tun da yaje 'dauko shi a airport yake washe ha'kora, wannan na 'daya daga cikin burikansa dayake son ganin faruwarsu, sai kuma gashi hakan yafaru, ba 'karamin da'di yaji ba da Abbah yace zaije Yobe , da farko ma yace zai bishi suje tare amma da Anty ta azalzale shi a'daki tayi masa masifah tare da fa'din matu'kar ya 'dauki 'kafa yabi Abban nasa toh yasani _babu ita_ _babu shi_ " Dajin hakan sai ya ha'kura da tafiyar saboda duk yanda yakai da rashin ji sam baya son mummunan kalma daga mahaifansa, ha'ki'ka iyaye iyayena kuma duk girmanka da ikonka yazame maka dole kabisu kodan samun rabauta awurin mahallici, amma be sanar da Abbansa abinda yafaru ba sai kawai ya nuna masa cewa akwai abinda yataso masa ne shiyasa ya fasa zuwa, amma insha Allahu zaizo yaje ko daga bayane. Abbah be wani damu ba yace " toh shikenan ba matsala, kai ai daman 'dan can ne ko bakaje yanzun ba matsala, da'ace baka ta6a zuwa ba ne toh da 'kafata 'kafarka amma yanzu kam ka fansheku, Allah ya nuna mana lokacin dazaka sake zuwa 'din " "Ameen" Mahmud ya amsa wa Abbahn dashi, be damu da _yah_ _fanshe sun_ da Abbah yake nufi ba sam ma abin be zo kansa ba, Abbah kuwa nufinsa shi Mahmud 'din da Antyn sa. Sai kawai ya 'kyale Mahmud 'din yayi tafiyarsa shi ka'dai, domin koshima bazai so bakin uwa yakama 'dan sa 'daya tilo da Allah ya mallakawa ba. Abinda Mahmud be sani ba shine duk abinda Anty ta fa'da kaf yaji ta, kuma wannan dalilin ne yasa ya 'kara saka himma wa tafiyar tasa. Koda yatafin kuwa basuyi waya ba har yaje ya dawo gida ko fatan sau'ka lafiya bata yi masa ba ballantana taji yanda ya sauka shine ma ya gwada kiranta sau 'daya dayaga bata 'dauka ba sai be sake 'kiraba yace inhar ba da gangan ta'ki 'dauka ba toh intaga missed call zata kirasa, ilai kuwa yaji shiru, bata 'kirashin ba kamar yadda shima be sake 'kiranta ba har ya dawo sai dai suyi wayarsu shi da Mahmud. Ko yau 'din ma da zai dawo Mahmud kawai ya 'kira ya sanar dashi ,shi kuwa be sanar da Anty ba kawai yaje ya 'dauko shi. Anty bata ma gida lokacin da Abbah ya dawo tatafi yawace-yawacen ta acikin gari ita da 'kawarta Anty chideh. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Remember the 5 (five) simple rules to be happy, Free your heart from hatred.....Free your mind from worries...... Live simply.......Give more and Expect less. πŸ…Ώ *40* Koda ta dawo ta ganshi agida kuwa 'dauke kai tayi tamkar ma bata ganshi ba, shima Abbah sai ya'ki yi mata magana yasan da kanta ma zata kulashi idan nata ya 'debo ta. Kwana biyar bayan dawowarsa sannan ya 'kira Mahmud tare da Anty, yayi musu bayanin abinda ke faruwa, yayin da hankalin Mahmud yakai 'kololuwa wurin tashi rasa yadda zaiyi ma yayi hakama Anty. Ita kam tsaye ta mi'ke da gama jin abinda Abban yagama fa'di tace "banji abinda kake fa'da da kyau ba, 'dan sake maimaita pls". Murmusawa Abbah yayi, yana kallonta har kamanninta sun soma sauyawa atake, be damu ba ya sake mai maita mata akaro na biyu duk da yasan ta ji shi da kyau, kawai sha'kiyanci ne ke damunta shikuwa yana daidai da ita awannan karon. Kwankwaso ta kama da hannunta 'daya jikinta har rawa yakeyi tsabar masifah. "Amma kai ko kunyar fa'da ma bakaji? Kallon ta Abbah yayi wannan karon sai ya koma baya jikin kujera ya zauna ya jinginu yana binta da kallo yana murmushi dama yasan sai ta masa rashin hankali shi kuwa me sashi barin maganan nan se ikon Allah kawai sai yace mata. " abin kunya nayi ne da har zanji kunyar fa'di"? "Dakata

Chapter 19 of 67