dan Allah Alhaji, inaga kamar ka manta da maganar da akayi kwanaki agidannan ko, inace kai da bakinka kace zakayi bincike bayan yaro yasanar dakai ga abinda yakeso shine zakaje ku wani 'kulla 'kulle-'kullenku daga zuwanka, ka zo kace ga abinda za'ayi, kai aganinka kayi adalci kenan,? Toh ya kuma kake so ayi da ita waccen da take s.....da Mahmud 'din yake sonta?
Da wuri ta daidaita harshenta dan kar ta kwafsa.
" kinje kin tambayo auren ne"?
Abban ya tambayeta hankalisa akwance domin shi baya jin yana da damuwa koka'dan saima wani farin ciki dayakeji, yayin da masifar da Antyn keyi yake 'kara masa kwarin gwiwa dan ganin yacika Burinsa.
" haushi tambayar tasa ta bata, take kuwa ranta ya 'kara 6aci tafara masifa kamar ta ari baki
" taya za'ayi kace ko na tambayo aure dama mace tana tambayar aure ne?
"Ni na sani ne ko akanki za'a fara"!
yasake fa'da cikin kwanciyar hankali .
" Wallahi Alhaji karka ga nayi shiru akan wannan maganar ka zaci ko maganar ta fasu ne, dama na fahimci take-takenka tun farko so kake ka'ki sa baki amaganar shiyasa ka tsiro da wani batun bincike, toh wallahi bari kaji ba rantse da Allah ko zan tafi tsirara ne sai naga Mahmud ya auri Munira, kuma bari in tabbatar maka wani abu da baka sani ni 'dana bazai auri wata 'kazama wai Fatima ba ko da kuwa mata sun 'kare a duniya toh sai sai ya zauna ba mace amma bazai ta6a auranta ba ,akai kasuwa".
Tana gama fa'din hakan tayi waje tana ta sababi.
Binta da kallo dukkan su sukayi har Mahmud 'din wanda yake zaune akan 'kafafunsa tamkar gunki tun lokacin dauaji bayanan Abban nasa na farko be 'kara jin komai ba, masifan da Anty tafara na 'karshe shine ya dawo shi cikin hayyacinsa saboda da 'karfi tayi maganan.
Sai data 6acewa ganin su kafin suka dawo da kallon su ga juna suna ha'da idanu kuwa Mahmud yayi 'kasa da idanunsa.
Bayyanan niyar murmushi Abban yayi sai yace " Mahmud kaima baka so ko"?
Shiru Mahmud 'din yayi yana rarraba idanu , baya jin ya yiwa Abbah adalci idan yace " ehh bayaso" inkuwa yace yanaso toh tamkar ya siyawa gidan nan tashin hankali ne, tunda yasanAnty bazata ta6a goyon bayan Abbah akan maganar ba, bayaga haka ma shifa kwatata bayaso yayi aure yanzu, bayanzu ya shirya yin aure ba kuma ko zaiyi auren ma ba dai Fatima ba, sai dai kuma ai da yarinyar da Anty ta keso ya aura 'dinnan gara Fatima sau dubu akanta, kai bama ha'di, duk itama Fatiman be ta6a yi mata kallon so ba , be ta6a ko kwatanta wai shi ze so ta ba, shi bai ma da plan 'din yin aure akwana kusa amma be san dalilin Abbah na nema masa auren Fatima ba.
Yace da ace Abbah zai bashi za6i da ita Muniran ze za6a saboda wani dalili.
Yana cikin tunanin ya tsinkayo muryar
Abbah yana sake maimaita tambayar daya yi masa da farko ha'di da cewa " kar ka damu Mahmud ka bu'de zuciyarki kasanar dani abinda ke ranka ,ni mahaifinka ne, bazan ta6a 'kin kar6ar kowacce irin uzuri daga gareka ba, matu'kar kaga za6in dana ma ka be maka ba ka sanar dani"
Numfasawa Abban yai jin har yanzu Mahmud be ce komai ba sai ya'kara cewa " sai dai inason kasan wani abu Mahmud har abada ni mahaifinkane, me 'kaunarka ne, bazan ta6a yima za6in da nasan zai cutar da kai ba, idan waccen yarinyar ne da mahaifiyar ka ke magana akai i thought na maka bayani, bincekena be nuna min komai na alkahiri tattare da su ba shiyasa bazan ita barinka ka auri yarinyar ba, amma bansani ba ko kana son abinka ahaka, feel free ka sanar dani ra'ayinka kaji Mahmud"!
Da 'kyar Mahmud ya bu'di baki yace.
" Abbah.......sai kuma yayi shiru.
" Inajinka "
"Abbah ban'ki za6in da kayimin ba, na amince kuma nagode sosai, Allah ya 'kara girma".
Albarka Abban nasa yata saka masa saboda farin cikin be watsa masa 'kasa a idanu ba, ha'ki'ka wannan ranar ta farin ciki ce agareshi ,daga nan ya sallami Mahmud ya tafi.
Koda ya koma 'dakinsa kuwa zama yayi kawai abakin gado ya dafe kansa dake masa sara ba 'ka'kkautawa, kasa aiwatar da komai yayi alokacin jin abin yake kamar amafarki, " _wai shi_ _aure, auren ma_ _kuma_ _Teemah_ " .
Yana a zaunen wayarsa tafara ringing se ya 'kyaleta danji yayi ma ta 'kara masa takaici, kusan 'kiran zai tsinke sannan yasa hannu ya 'dauko ha'di da jan tsaki domin da farko beyi niyyar 'dauka ba amma da 'karan yayi yawa ne yasashi bashiri ya janyo ko duba sunan me 'kiran beyiba yayi picking kawai ya kai kunnensa.
Shiru yayi ko daya 'dauki 'kiran amma daya jiyo muryar Abbas ne sai ya 'dan saki ransa ka'dan.
Bayan sun gaisa sai Abbas 'din ya sanar dashi cewa yana Abuja yau 'din nan ya sau'ka,
Take sai shima ya bashi amsa da fa'din nima ina hanya insha Allahu"
"Toh se ka iso"
Daganan suka yi sallama kowa ya ajiye wayar.
Mahmud be fito daga 'dakin nasa ba sai da shirin tafiya Abuja, a harabar gida yasamu Abbah ya sanar dashi cewa zashi Abuja.
" ina fatan lafiya"
Abban ya tambaye shi
Sai Mahmud ya bashi amsa da "ehh lafiya 'lau kawai zashi ne yana da appointment da wani acan"
Fatan Allah ya kiyaye Abbah yayi masa sannan yace ko akwai wani problem "?
Mahmud yace "a'a
Jinjina kai Abbah yayi.
Daganan Mahmud yayi tafiyarsa yakama hanyan Abuja.
*ABUJA*
Abbas bacci yakeyi lokacin da Mahmud ya isa gidan, wanda baccin ya 'dauke shi sa'ilin yana kwance akan kujera a parloun dake 6angarensa, yana tsaka da tunanin Fatimansa baccin yayi awon gaba dashi.
Mahmud na shigowa 6angaren nasa sai kuwa shima ya farka daga baccin da yakeyi 'din, dama shi Abbas haka yake sam baya bacci me nauyi, da salati ya farga daga baccin sai idanunsa ya sau'ka akan Mahmud dake tsaye yana kallonsa yana ayyana dama shine a irin wannan yanayin narshin damuwa amma shi kam be san ranar da farin ciki zata 'dore agareshi ba.
Da sauri Abbas ya mi'ke zaune yana masa murmushi, " harka iso ne" Abbas 'din ya fa'di.
Sai dai ga mamakinsa fuskar Mahmud a 'daure take tamau babu fara'a balle yayi tunanin samun amasar shi, damuwa ce 'karara tattare da fuska da kuma yanayin Mahmud 'din, dama yasan za'a rina domin tun lokacin dasukayi waya da Mahmud ya fahimci ba daidai yake ba sai kuma gashi yanzu daya ganshi da idanunsa sai yafi gasgata zuciyarsa fiye da 'dazun dayaji muryarsa acikin wayan.
Be ce da Mahmud 'din komai ba kawai sai ya tashi ya wuce cikin bedroom 'dinsa, bathroom ya fa'da bayan ya cire kayan dake jikinsa ya watso ruwa tare da canja kayan dake jikin sa zuwa dogon wandon jeans da rigarsa fara sa6anin da dayake sanye da 3quatern wando baki da kuma singlet.
Kayan daya saka 'din sun matu'kar amsan jikinsa sai suka 'kara fito da ainahin kyaunsa da kwarjininsa afili.
Sake fitowa yayi cikin takunsa na 'kasaita ya nufo palourn nasa inda yabar Mahmud, turus shima ya tsaya mamaki ne ya 'kara cikashi ganin ayanda ya bar Mahmud 'din ahaka yadawo yasame shi tsaye hannayensa duka zube acikin aljihun wandonsa.
Abbas aransa yajinjina wannan lamari " lalle Mahmud na cikin damuwa sosai" shi kanshi abinda ke damun Mahmud 'din sai ya fara damunsa tun ma kafin yaji menene.
Sosai ya tsorata da yanayin Mahmud 'din kasancewarsa mutun me surutu da haba haba da jama'a, da wuya kaganshi a irin wannan yanayin da yake ciki ayanzun in dai bada wani kwakkwaran dalili ba.
Hakanne ma fa yasa koda yaje yin shirin sa be 'dau dogon lokaci ba ya kamalla dawuri ya wuri ya fito dan ya yaji me ke faruwa.
Abotarsu daga Allah ne, tun lokacin dasuka ha'du a damaturu sai Allah ya sanya musu 'kaunar junansu sannan suna mutunta juna tare da damuwa da damuwar junansu tamkar 'yan uwa na jini.
Abbas na kammala tunanin nasa sai ya wuceh wurin fridge ya 'dauko fresh milk tare da glass cup guda biyu ahannunsa.
" why are you still standing Mahmud ka zauna mana zaifi ai ko"
Yafa'da bayan ya iso ya tsaya daga bayan Mahmud 'din.
Ahankali Mahmud ya taka yaje ya zauna akujera me zaman mutun biyu yayin da Abbas yabishi abaya ya joining 'dinsa suka zauna atare.
Yana zama sai ya fara tsiyaya fresh milk 'din a ' daya daga cikin kofunan daya kawo 'din bayan ya ajiye su akan centre table dake gabansu.
Abbas mi'kawa Mahmud cup 'din yayi batare da yayi magana ba, sai alokacin kuma Mahmud yayi ajiyar zuciya tare da huro zazzafan iska da 'karfi daga bakinsa sannan ya 'daga lumsassun idanunsa ya kalli Abbas da su.
Shikuwa Abbas sai ya 'dage masa gira 'daya tare da nuni da abinda ke ri'ke ahannunsa da idanunsa alamar " anshi mana" .
Hakan da Abbas yayi ne yasa Mahmud shima ya kallo hannun Abbas 'din sannan a hankali ya cira hannunsa ya kar6i cup 'din daga hannun Abbas.
" hmm "
Abbas yace tare da jijjiga kansa bayan Mahmud ya kar6i abinda yake bashi 'din ,sake jinjinawa wannan al'amarin yakeyi dahar ya iya meda Mahmud haka a 'dan 'kan'kanin lokaci,because it's hardly kaga Mahmud na fishi arayuwarsa.
Shima Abbas tsiyayan fresh milk 'din yayi yasha sannan ya ajiye cup 'din ahankali, sar'kafe hannanyensa yayi cikin junansu bayan ya gyara zamansa da kyau ya fuskanci Mahmud 'din sai yace masa " naganka wani iri, hope all is well with u"?
Comment
Vote
Share
*Salmerh* π
[10/2, 6:00 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* π
*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
ππ»
*HAPPY JUMMA'AT* *2 ALL* *MUSLIMS* .
π
Ώ *41*
" hmm"
kawai Mahmud yace daganan ya kuma yin shiru.
Shirun da Abbas yaji ne yasa ya 'dago kansa ya kalli Mahmud da kyau,
aransa yake tunanin
" wai yau Mahmud ne haka?
Abin na bashi mamaki sosae musamman da yaga yanda idanunsa suka koma ja alamar yana tattare da 6acin rai sosai.
Sake 'daukan cup 'din dake gabansa yayi ya 'kara kur6an freshmilk 'din, kafin ya cire kofin abakin sa yajiyo muryar Mahmud yana furta " Fatima"
irin amamakance 'dinnan, Abbas bewani damu ba koda yaji ya ambaci sunan domin shi ayanzu bashi da burin da ya wuce yaji meke tafe da Mahmud 'din dan haka sai yaci gaba da shan abinsa ahankali batare da ya tankawa Mahmud ba.
Kallon Mahmud yaci gaba dayi daya zurawa centre table 'din dake gabansu idanu tambayr Mahmud ya yanke shawaran yi inda yace " wacce Fatima kuma Mahmud" yana gama fa'di ya'kara kaiwan cup a bakinsa.
Mahmud kuwa kamar an tsikare shi ya mi'ke tsaye yaci gaba da fa'din
" _Teemah fah_ Abbas, _wai_ _Abbah na Teemah zai_ _aura min "_.
Abbas be san lokacin da ya furzo freshmilk 'din da ya kur6a ba, wanda ke bakinsa dai dai yasha kenan yaji maganar Mahmud 'din tamkar atsakar kansa yayi ta, hakan yasa ya furzo shi da 'karfin da bai shirya ba sai ya zarce da tari.
Sosai tarin ya sar'ke shi tamkar wani me ciwon TB dan har Mahmud dake tsaye cikin 6acin rai ma saida ya taho da sauri kusa da shi yana masa sannu, fridge Mahmud yakoma ya 'dauko masa ordinary ruwa ya bu'de marfin sannan ya mi'ka masa, ka'dan Abbas yasha sai ya ajiye goran kana yaci gaba da kallon Mahmud tamkar wani sabon halitta ya gani.
Shiru suka yi dukkan su, na 'dan wani lokaci yayin da Abbas yake ta addu'a aransa cewa " Allah yasa kunnuwansa ba dai dai suka jiyo masa ba, inma dai dai ne Allah yasa ba tashi Fatiman Mahmud yake nufi ba ".
Murmushi Mahmud yayi wanda ni kaina bansan ma'anar ta ba domin bata farin ciki bace, sannan yaci gaba da fa'din " kamar de ni, Abbas kaima kayi mamaki ko?
Shiru Abbas yayi yana kallon sa bashi da buri ayanzu illah yaji 'karshen zancen Mahmud 'din.
Tunawa da maganar Mahmud yayi wanda yayita bada jimawa ba inda yace " wai Abbah _Teemah_ _zai aura_ _min_ .
Kauda kansa gefe Abbas yayi da sauri daya tino maganar acikin zuciyarsa in banda innalillahi babu abinda yake iya fa'da.
Yana juyowa sai suka ha'da idanu da Mahmud sai yace. " kaima kana tayani mamaki ko Abbas, ni bansan me yasa Abbah na ya yanke wannan hukuncin ba batare da ko yin shawara da ni ba, juyowa yayi da sauri kamar zautacce yayi facing Abbas sannan yaci gaba da maganarsa.
"Kasan wani abu Abbas?
Ni ban ta6a kawo faruwar hakan ba ko da a wasa, hasashe na be ta6a kawo min yiwuwar aure tsakanina da Fatima ba not even in my dreams".
" Fatima fah Abbas, my lovely sis, my lil sis how can I...........
Dafe kansa yayi da sauri ya kasa 'karasa maganar da yayi niyyan fad'i.
Abbas ma rintse idanunsa yayi da 'karfi yayi baya ya jinginu da jikin kujerar daya ke zaune.
Mahmud kansa ya ri'ke da 'karfin gaske dayake mugun sara masa, yanajin da zai iyayin hawaye ayanzu da babu abinda zai hanashi yayi saboda yasan shine ka'dai zaisa ya samu 'dan sassauci amma ina......
Da 'kyar Abbas ya daure ya tashi yakoma kusa dashi ya sa hannunsa ya dafa kafa'dar Mahmud 'din
duk da yanajin wani 'kuna azuciyarsa da be ta6a experiancing akwai irinta ba, amma yah ya iya akan son zuciyar shi bazai iya ya bar Mahmud ya bijire wa maganar mahaifinsa ba, duk da ba wani sanin Abbahn yayi sosai ba amma yasan Abbah bazai ta6a yanke hukuncin da yasan akwai cutarwa aciki ba musamman ga 'dansa na cikinsa, kuma ma idan yayi la'akari da yanayin da suke zumunci must especially labarin da Mahmud yabashi farkon ha'duwarsu a Damaturu ya tabbata Abbah ba zai rasa dalilin da ya sa ya za6i hakan ba.
" Laifina ne, nasani laifina ne da ban bayyana kudurina akanta tun farko ba, na ri'ke abuna acikin raina, ina can ina tunanin yaushe ya kamata na mallaketa!, yaushe zata zamo tawa!!, bansani ba ashe BURINAH da mafarkina bazasu ta6a tabbata ba.
" Amma duk da haka bazan iya barin ka acikin wannan yanayin ba, Mahmud ko ba komai kai abokina ne.
Duk acikin zuciyarsa yake wannan tunanin.
Dan a yanayin da yaga Mahmud 'din sosai ya tausaya masa alamu sunnuna 'karara shi be yi na'am da wannan ha'din ba.
Da 'kyar yasamu ya bud'i bakinsa yafara magana
" kayi hakuri Mahmud kasan Abbah yana sonka bazai ta6a ha'da ka da abinda ba dai dai bane agareka, ka daure ka ya'ki zuciyarka kayi masa biyayya na tabbata zaka ga ribarsa wata rana, ko ba komai iyaye abin girmamawa ne nasan kasan wannan, kuma shi aure ba yana nufin tashin hankali bane, Mahmud aure rahama ne, sannan ibada ne, cikon addini ne. Ni agani na Abbah gata yayi maka tunda har yayi maka za6in matar aure da kansa, kuma ma ai kaga Fatima yarinya ce, kasanta, kasan kalar tarbiyyarta ,kasan damuwarta farin cikinta da ba'kin cikinta kaga baka da matsala da wannan kamar yadda nasan bazaka samu problem da ita ba. Idaan kuma batun *so* ne, na tabbata ahankali zaka so ta basai an 'dauki wani dogon lokaci ba,insha Allahu baza 'a samu matsala ba musamman inkayi la'akari da sanayya da kuma shakuwar dake tsakaninku, inkuma kana tunanin ba ita kake so ba wacce kake so daban, Mahmud ai kai namiji ne kana da damar dazaka auri mata daga 'daya zuwa hu'du inkaga zaka iya"
Muryar Abbas har rawa takeyi da 'kyar yasamu yah dasa ayar maganar tasa tare da numfasawa duk a'ko'karinsa naganin ya taushi Mahmud 'din.
Da 'kyar yasamu Mahmud ya sau'ko ya 'dan kwantar da hankalinsa daga 'karshe bedroom 'din Abbas ya shige shima ya watsa ruwa sannan yazo ya kwanta, cikin sa'a kuwa yana kwanciya bacci ya 'dauke sa.
Se bayan shigan Mahmud ciki kafin Abbas yasamu ya mi'ke akan 3seatern shi fuskan shi na kallon ceilling yayin da ya tsurawa ceilling fan 'din dake juyawa asaman idanunsa, hannun sa yasa ya dafe saitin zuciyarsa dayake jin yana harbawa da 'karfin gaske, daga 'karshe lumshe idanunsa yayi ahankali, wani abu yakeji ya tokare masa 'kirji wani abu da besan mene ba ke damunsa ba, ehh mana be sani ba shin nauyin da yake ji azuciyar san na son Fatima ne ko kuma na ba'kin cikin rabuwa da ita neh.
Be ta6a tunanin irin wannan abin zai iya zuwa ya yanke masa kyakkyawar ala'kar da zuciyarsa ta 'kulla tsakaninsa da Fatima ba.
Jijjiga kansa yayi ahankali kamar da wani yake hira akwancen acikin zuciyarsa yace " ina son...ki..Fati....amma ga dukkan alamu yanzun kinmin nisa".
Bu'de idanunsa yayi sanadiyyar sallama da kuma 'karan 'kofa dayaji alamun anbu'de anshigo.
Hannah ce yagani tsaye ajikin 'kofan tamkar tana tsoron shigowa, daya ga haka sai ya maida idanunsa ya kuma rufesu kamar yanda suke da farko batare da ya kula. Ko kuma amsa sallamar tata ba.
Itan ma data ga haka sai tace masa
" Ummah ce tace in zo in duba ka wai tajika shiru".
Baifi tsayuwar second biyar tayi ba bayan tayi maganan sai ta juya takoma inda ta fito, domin tasan Yayan nata ba magana zai yi mata ba shiyasa ma ta juya batare da ta jira amsa daga gareshi ba.
Kamar be ji me tace dashi ba ,sai can sai ya yun'kura ya tashi tare da saka takalmansa yafita a'dakin.
Parlourn Ummah ya nufah inda ya sameta zaune akan kujera me zaman mutum uku Hannah ma na zaune agefenta.
Ciki-ciki yayi sallama sai suka amsa dukkansu atare suna masu maida hankulansu gareshi saboda yanayinsa daya canju.
Agefe dasu ya zauna sai ya gaida Ummahn nasa tare dayi mata barka da yamma, ita kuwa a gaggauce ta amsa domin damuwa data gani 'karara a fuskan Abbas 'din harma da muryarsa ga idanunsa da suka yi jajir suma.
Hannah ce ta tashi ta bar 'dakin Ummah ma bata lura da ita ba sanda ta fitan domin hankalinta nakan Abbas alokacin.
" me yafaru ne Abbas ko de kana bacci Hannah ta taso da kai,"
Be yi magana ba sai ita ce tacigaba da cewa "ka ganka kuwa, meke damunka ne pls?"
Lumshe idanunsa yayi ahankali koda ya bu'de kuwa sai ya sau'ke su akan fuskan Ummah.
Tasowa yayi ya dawo kujeran da take zaunen inda Hannah ta tashi, koda ya zauna 'din kuwa sai ya zamo ya kwanta tare dayin matashi da cinyar Ummahn, ita kuwa sai binshi takeyi da kallo tana mamakin sa.
"Abbas meke damunka ne wai "
Tasake maimaita tambayar tata akaro na biyu tare da 'dora hannunta akan sa.
Ahankali yace
" Ummah Abbahn Mahmud yace wai aure zaiyi masa!".
'Kwafah tayi tana kallonsa kana tace
" haba Abbas shine kuma kabi ka 'daga hankalin ka dan Mahmud zaiyi aure"?
" Mahmud baya son auren fah Ummah, kuma ma wai kwanan nan za'a yi auren gashi can duk ya bi ya 'daga hankalinsa akan maganar da kyar nasamu ya sau'ko Ummah".
Daga nan yayi shiru domin daman da 'kyar yake maganar daurewa kawai yayi, in baka sani ba zaka zaton damuwar da Mahmud yake ciki ce shima ta dame shi amma ga wanda yasani kuma sai de yace.......π€( me za'ace)? _Ni de nace_ _Allah sarki bawan_ _Allah_ .
Comment
Vote
Share
*Salmerh* π
[10/2, 6:00 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* π
*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
ππ»
π
Ώ *42*
*ABUJA*
Fa'da Ummah tafara yiwa Abbas atsanake inda take cewa " wato na fahimci dukkanku ra'ayi 'daya gareku ko Abbas?
Gaba 'daya sai kuka ha'du kuka 'daga hankulanku akan batun aure kawai,! saboda Allah me hakan ke nufi kenan? abin mamaki ma se kace wasu yara 'kanana, dube ka fah yanda ka koma kaima kenan inaga shi uban gayyar kuma? kaida ya kamata ace ka bashi baki ya amince sai kuma ka tayashi shiga damuwa wannan ai shirme ne Abbas, daga kai har Mahmud 'dinma ni bansan lokacin dazaku girma ba wallahi, ace dan abokinka zaiyi aure kazama haka toh in kaine kuma ai Allah ne ka'dai yasan ya zakayi........ hakan da kuke yi fah bakomai yake 'karawa ba illah 'kara fito da zallar 'kiyayyar da kuke yiwa aure"
Baki ta kama tace "anya ma lafiyarku qalau kuwa Babana".
Shiru yayi mata be bata amsa ba.
aransa yake cewa " lafiyar mu 'kalau Ummah ,bazaki gane bane!
kowa na tashi damuwar daga ni har Mahmud 'din, ni ita nakeso ina sonta sosai Ummah fiyeh da kaina, amma yanzu kam dole na ha'kura da ita domin tayi min nisan da bazan iya kamota ba har abada, da ace ba Mahmud bane da wallahi babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da Fatima ko ma waye shi sai inda 'karfina ya 'kare, amma Mahmud kam dole na ha'kura inba zuciyata ha'kuri domin shi mutun ne, mutum ne da kowa zaiyi alfaharin kasancewar sa atare dashi, bazanso akan mace ala'kata dashi ta rushe ba, da irin wannan tunanin bacci yayi awon gaba dashi akan cinyar Ummahn daman aikin sa kenan idan yadawo gida sai de yayi ta bacci wani lokaci sallah ce ka'dai ke tada shi yana idarwa kuwa zai koma, amma idan yana bakin aikinsa kuwa kusan mantawa ma yakeyi da batun bacci arayuwarsa koda yake yanzun ma zuwan Mahmud ne ya tada shi abaccin kuma badan zuwan Mahmud 'din ba da zai 'dan 'dauki lokaci yana bacci abinsa.
Ita kuwa Ummansa idanu ta zuba mishi kawai tana 'kara mamakin hali irin na sa, shi baya son ace yayi aure sannan kuma ance abokin sa zaiyi nan ma kuma sai duk sauka ha'du suka 'daga hankulansu, " kai yarannan kuna da abin mamaki, Allah dai yakawo muku abokan zama nagari".(Ameen).
Washegari Abbas da Mahmud tare suka fita daga gida bayan Ummah ta ha'da su tayi musu nasiha sosai daganan ta sallame su suka tafi kowa ya nufi inda zashi, bayan Abbas ya sake 'karfafa wa Mahmud gwiwa akan maganar daya zo da itan tare da jaddada masa muhimmancin bin maganar iyaye kamar yadda Ummah tayi musu.
Haka suka rabu Mahmud na yiwa Abbas 'din godiya da kuma fatan alkhairi domin zuwa yanzun Alhamdulillah ya ji dama-dama a zuciyar sa, he is now ready to face his reality.
*DAMATURU*
Daddyn Teemah be bari mummy ta sanar da ita ba shine dakansa ya zaunar da ita yayi mata bayani yanda yasan zata fi fahimta, itanma da farko ta 'dan ji tashin hankali amma aranta, dayake bawani zama takeyi ta fahimci me zuciyarta take ciki ba shiyasa takasa gane inda nutsuwarta ta dosa akan maganar daddyn.
Ji takeyi tamkar tayi na'am da maganar amma deep down tana jin kamar kuma bata aikata daidai ba.
Daddy kuwa kafin su rabu sai da ya tabbatar da cewa ta amince da maganar 100% kafin hankalinsa ya kwanta, daman damuwarsa kenan shine kar Fatiman ta'ki amincewa duk da yana ganin kamar wayo be gama isanta ba kuma hakan bazai barta ta kasa amincewa da maganarsa ba, amma 'dan adam sai Allah, kowa nada nashi kalan burin arayuwarsa.
Har Daddy suka gama maganar su da Teemah mummy bata saka musu baki ba, ita abubuwa ne suka taru suka yi mata yawa azuci, tunda ranar da akayi maganar auren nan mummy bata sake yin baccin kirki ba, tausayin 'yarta ta yawa yake yi mata ta fuskoki da dama.
Babban damuwarta shine yanda Anty zata kar6i batun nan, tasan da wahala ta yadda da auren, idan ma ta yadda 'din toh wani irin zama zatayi da Fatiman.
Sannan secondly alamu da yawa sunnuna cewa tun ba yau ba Teemah ta fara son Abbas, she can proof that Zuciyar Fatima Abbas takeso, amma rashin wayo irin nata yasa takasa bambance abinda takeso harma gashi ta amsawa mahaifinta cewa ta amince da auren Mahmud.
Yanzu kam mummy ta saduda ta barwa Allah komai " bani da abin cewa nikam ayanzu sai de nayi ta miki addu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi aryuwarki".
Teemah sai da ta koma 'daki sannan ta fara fahimtar yanayinta, jin ta tayi wata iri, kaf sai ta nemi nutsuwa azuciyarta ta rasa sai asannan taji tamkar bata yiwa kanta adalci ba.
Fa'dawa tayi rigingine akan gadonta abun duniya duk sun taru sun mata yawa, Abbas ne ya fa'do ranta karo guda sai taji zuciyarta ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 67