Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lafiya ko hankalin kowa zai kwanta. Abbah da kanshi yasa Mahmud agaba suka je gurin wata matar abokinsa suka yi maganar kayan lefe afa'darsa tunda mata suka suka san kayan mata 'yan uwansu, transfern ku'di kawai yayi mata masu yawan gaske yace ta ha'da masa lefe nagani afa'da yace baya san algus ko ka'dan aciki saboda yarinyar ma 'yarsa ce ahaka kawai ma zai iya yi mata ballan tana kuma ace aure ne sanadi kuma auren 'dan cikinsa zata yi. Dariya sukayi masa sannan matar ta bashi tabbacin bashi da matsala da wannan ya kwantar da hankalinsa komai zai yi kamar yanda yake bu'kata, dayake daman tana sarin kaya tace wannan satin zata yi ordern su sauran kuma dole sai anan Nigeria za'a siya. Godiya yayi mata sosai ,sai abokin nasa yace " ban ta6a jin inda mahaifin ango yayi kane-kane akan kayan lefe ba............... "Akaina zaka fara gani Alhaji" Abbah ya karasa maganar yana dariya. "Asalin tuwona mai na 'din kenan Alai yusuf lallai zaka kafa tarihi a 'kasar nan". "Kwarai ma kuwa ". Abbah ya sake bashi amsa still suna dariya. Mahmud kam tunda suka zo daga gaisuwa be sakeyin wata magana ba sai kawai ya ciro wayarsa yana danne-danne dayaga sun gama maganar sun koma hira suna dariya sai kawai yatashi ya basu wuri, binsa sukayi da kallo har ya 'karasa barin 'dakin. Alhajin ne ya tambayi Abbah abinda ke damunsa shikuwa Abbah be '6oye masa ba yabashi labarin yanda batun auren ya kansance ya 'karasa da fa'din fushin Mahmud 'din na rashin son yin aure yanzu ne wai shi ba yanzu zai yi aure ba sai nan gaba , laifina anan shine nace yanzu zaiyi aure shikuma ba haka ya tsara wa rayuwarsa ba shine fushin." "Allah sarki yaro kenan, inbanda abinsa ai aure bashi da lokaci" Inji Alhajin. " rabu dashi bazai gane hakan ba ai, amma nasan wataran dakansa zai gode min idan yafahimci banyi hakan dan na ba'kanta masa face gata da nake 'ko'karin yi masa". Inji matar Alhajin "Hakane kam". Ajiyar zuciya Abbah yayi sannan yace " Allah shi kyauta" Tare da mi'kewa tsaye, Alhajin ma sai ya mike yamasa rakiya har inda sukayi parking motar su . Mahmud na hango su ya tada motar kmar daman jira yake yaga fitowarsun. Ahanya ne Mahmud yake tambayar Abbah wai kayan miye zaa siyo? Abbah ce mishi yayi "kayan auren kane!" "Toh ni Abbah ya baka siya min ba sai ita ka'dai" "Abu mai sau'ki ne ai wannan babana idan kanaso zan siya maka kwantar da hankalinka." Shiru Mahmud yayi yaci gaba da tu'kinsa har suka isa gida bai sake magana ba. Mahmud yanzu bashi da abokin hira sai 'dakinsa da kuma wayar sa, hatta Fatima (wife to be 'din nasa ma daina kulata yayi tunda akayi maganar auren su sau 'daya suka yi waya dashi daga nan be sake 'kiranta ba, haka ita ma bata 'ta6a 'daga wayarta ta 'kira sa ba, ko a chat ma babu me kula 'dan uwan sa yanzu ko wa harkan gabansa yake yi duk wannan sha'kuwan sun manta da ita. Wayewar wa ta safiyah ne wanda idan aka lissafa 13days yarage wa bikin Mahmud, sai Abbah ya'kira shi yake sanar dashi cewa ya kamata ya ziyarci Fatima ko da sau 'daya ne kafin lokaci ya iso, duk dama already sun san junansu kuma akwai fahimta atsakaninsu amma sanayyar dake tsakaninsu ada da na yanzu is totally different, yakamata su'kara fahimtar juna, bai musa wa Abbahn ba take ya amince akan zashi sai Abbahn yace toh yaje duk lokacin da ya shirya tafiya sai yayi masa magana yace ya bashi nan da 3days. " toh Abbah" yacewa Abbahn nasa kawai sannan yatashi yatafi. Bai sake bi takan maganar Abbahn ba kawai ya share yayi zamansa har akayi kwana hu'du babu wani alamar yana da niyyan tafiyar da zaiyi, rana na biyar ne da Abbah yaga shiru sai ya sake yi masa tuni akan maganar tafiyan wanda lokacin yayi dai dai da kwana tara cif yarage wa lokacin da aka saka na 'daurin aure. Mahmud 'kasa yayi da kai tare da shafa gashin kanshi sai yace da Abbahn" ai shi yamanta ma kwata kwata , amma insha Allahu kwanan nan zai shirya yaje shi", " yah kamata kam ". inji Abbahn ya fa'da lokacin yana 'ko'karin 'daukan jaridar dake gabansa yaci gaba da dubawa. Lokaci nata 'karatowa yayin da shirye shiryen biki ya kankama aduka 6angarorin guda biyu, koda yake a6angaren Mahmud Abbah ka'dai ne ke ta faman shirin sa, yayinda Anty kam ko oho bata damu ba kallonsu kawai takeyi. Mummy kuwa busy take ako da yaushe bata samun lokacin kanta 'ko'karinta taga komai yatafi yanda yakamata, duk wani abu datasan hakkin ta ne aiwatar dashi toh bata natsuwa sai taga ta sau'ke shi, sai dai har yau takasa yiwa Teemahn koda abu 'daya ne daya danganci gyara da ake yiwa amare rasa ta ina ma zata fara tayi ,daga 'karshe sai ta yanke shawaran barinta ayadda take kawai ta cire wannan a lissafinta, ta daiyi 'ko'karin tanadar mata duk wasu abu na gyaran fata da gyaran jiki kuma ta tsaya tsayin daka dan ganin komai na tafiya dai dai. Ummah (mahaifiyar Abbas) ce ma tayi mata maganan wai ko ta ha'dawa Teemahn kayan mata dan taga wasun sukan yi wa 'ya'yansu idan lokacin auren su yazo, sai mummy tace "ahh'ahh ita kam bata ba ta komai ba tsoro takeji,abinda kullum yake damunta azuci ma kenan amma dai daga bay ta yanke shawarar gara ta barta hakan kawai. Sai kuma Umman ma tace "yauwa hakan yafi ai gara abarta a yanda take saboda yiwa yara abubuwan da suka shafi wannan 6angaren kafin susan kansu yana da illoli da dama amma tunda ma ba'a matan ba shikenan ,tace dama ta so ma tun wuri suyi maganan amma sai ta sha'afa gaba 'daya abubuwa sun sha kanta itama". ***** 7days to ranar 'daurin auren Ummahn Abbas ta iso ita da Hannah suka zo dan Hanna damunta tarin'ka yi wai tafiso suje dawuri ayi komai da ita ,bata son komai yawuche ta shiyasa dolen Ummahn ta shirya suka taho, dama nufin ta sai nan da kwana biyu zasu taho, Daddyn Abuja ma yabiye wa Hannah yace ai gara su je tun yanzu duk 'daya da jibin da Ummahn tafa'di tunda bawani abu suke jira anan 'din ba ai gara sutafi ayi hidima dasu gaba 'daya, yace shi sai ranar Friday zasu ganshi ( dayake bikin ranar Saturday ne). Teemah bata ta6a ha'duwa da Hannah ba amma zuwan Hannah ya yi mata da'di sosai, saboda tasamu abokiyar hira, sosai Hannah ke 'debe mata kewa surutunta tamkar uwarsu 'daya da Mahmud itama badama gata da saurin sabo bata da ba'kunta. Washegari cikin sa'a sai ga wasu daga cikin 'kawayen Teemah na makaranta kusan su hu'du suka zo, Teemah wani ihu da ta saka ta rungumesu har ma bazaka ce tana da damuwa ba, Hannah ce tace "mata kiyi dai ahankali dan kin kusa ki zama matar gida". Bata kula da maganar Hannah ba tajasu gaba 'daya suka nufi 'dakinta kowa tasamawa kanta matsuguni, wanda kusan dukkansu akan makeken gadon Teemahn suka zuzzube Hannah ce ka'dai ta 'dan 'dosana 'duwawunta saboda sauran duk kwanciya sukayi so ba space sosai, sai kuma Teemah dake zaune akan side drawer tana facing 'dinsu, musamman ta janyo shi zuwa gaban nasu dan taringa kallon su da kyau gaba 'daya. ***** Aranar da su Ummah suka bar Abuja aranar shikuma Abbas yaje shi, dan ma irin zuwan nan na shi da ba da'dewa yakeyi 'din nan bane 'kar'karinta a yayi 'ko'kari shine yakwana 'daya shikenan zai ce zai tafi, shi akoda yaushe yafi son yaganshi a wurin aikinsa baya so yaga yayi nisa da su he so much care about his career. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh* ๐Ÿ˜ [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: ๐Ÿ’• *CAPTAIN ABBAS* ๐Ÿ’• By *Salmerh MD* Luv story๐Ÿ˜ *Wattpad @* *Serlmerh-md* ๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* ๐Ÿ’ซ We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ ๐Ÿ˜ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Donโ€™t confuse your path with your destination. Just because itโ€™s stormy now doesnโ€™t mean that you are not headed for sunshine. ๐Ÿ…ฟ *45* Daddyn Abuja ne ya sanar da Abbas 'din cewa da safiyar yau suma suka wuche Jihar Yobe, sosai Abbas yaji haushin rashin samun sun da be yi ba, har ma yace wa Daddyn nasa " me yasa toh suka tafitun yau"? Cikin jin haushi yayi maganar. " haba Abbas ka manta bikin waye za'ayi ne"? daddyn ya tambayeshi da mamaki. Kauda kansa yayi gefe sannan yace " ban manta ba Daddy kawai naga sunyi saurin zuwa ne ai dasun bari ranar Wednesday ko Thursday sai su tafi". "Yanzu kam ai shikenan tunda sun tafi komai ya wuce, in ganin su kake son yi ka bi su can 'din." Shiru yayiwa daddyn nasa bai tanka ba,kawai ya tashi ya nufi 6angarensa domin watsawa jikinsa ruwa. Daga lokacin da ya iso zuwa daren ranar tsakin da yayi yafi sau a'kirga, abubuwane suka taru suka mar yawa acunkushe ya ringa jin zuciyarsa , koda yaji yunwa ta dameshi sai ya nemi abinci anan ma Daddyn Abuja yace yajira akawo abincin ya aika asiyo. Ka'dan yarage tsakin da yayi azuciyarsa tafito fili Allah ya taimakeshi azuci yayi ta shiyasa Daddyn nasa be ji ba. Sai kawai ya tashi ya nufi harabar gida amma sam yarasa inda zai samu nutsuwa, tunani yayi ko de ya shiga cikin gari yawone?, Toh inka fitan ma ina zaka nufa? Wani 6angare daga zuciyarsa ta tambayeshi. Safa da marwa ya fara yi agurin yana tunani " wai dagaske ne za'ayi auren kenan?, Dagaske Mahmud ne zai auri Fatima bani ba". " ehh dagaske ne mana tunda gashi su Ummah ma sun tafi domin halartar 'daurin auren". Wani 6arin zuciyarsa ne ya sake bashi amsa. Tambayar kansa da kansa yayi wai " me yasa duk wani abu daya shafi 6angaren Fatima ni nake cutuwa aciki meyasa haka ?,is it because dan ba zan sameta bane ko me,? _First_ ha'duwarsu da Mahmud, lokacin ba 'karamib takaici yajiba na yanda yarinyar nan ta nuna tafison kasancewa da Mahmud fiye dashi da 'kyar ya samu ya lallashi zuciyarsa akan hakan. Then _secondly_ batun aurensu, wannan kam shiyafi komai 'kona masa zuciya saboda yanajin kamar bawai ha'din iyaye bane kamar yanda Mahmud yayi masa bayani gani yake tamkar Fatiman nason auren duk da yasan shi Mahmud 'din baso yake ba amma zuciyarsa takasa amince masa da cewa Auren na ha'di ne kamar yanda zuciyarsan akullun take bashi tabbacin cewa babu wanda zai auri Fatima akaf duniyan nan sai shi, Fateema Zahra ta Abbas ce shi ka'dai. And _now_ yayi missing kirkin Ummahn sa duk adalilin wannan banzan auren. Haushi sosai hakan yasaka shi, yace yanzu da Ummah na nan ai da ba ruwansa da neman abinci, dan ita akoda yaushe idan ka nema toh zaka samu, ya tsani cin abincin hotel shi, yafi son cin abinci agida, shiyasa akoda yaushe yake kan hanyan zuwa gida duk da nisan da gurin ke dashi hakan besa yayi ganda zuwa aduk lokacin dayaso, abu ka'dan ke sa ya kamo hanyar gida baya yin cikakken 2 weeks mai kyau batare da ya le'ko Abuja ba, koda ba zai kwana ba ma amma in ya so sai yazo, wani lokaci dan kawai yaci abincin Ummansa ma yakoma saboda na wajen da wuri suke fita akansa bakamar na mahaifiyarsa ba. Ko yanzun ma da aka kawo abincin da 'kyar yasamu ya'dan tatta6a ka'dan yabari, ba danma yanajin yunwa ba da bazai ko bu'de ba. Washe gari ma Daddynsa ne ya sake aikawa aka kawo musu breakfast, shikan 'kin ci yayi yacewa daddyn nasa shi lipton kawai zaisha, daddy ne kawai yaci abincinsa, Abbas dakansa yaje kitchen ya tafasa ruwan lipton 'din yakawo musu da daddyn dan yasan shima Daddyn gwanin shan ruwan lipton ne. Yana gamawa kuwa yayi wanka ya shirya sai yayi sallama da Daddyn ya kama hanya. Teeemah na cikin 'kawayenta suna ta zuba surutu abinku da student in an ha'du ba dama sai an yada hali, musamman na yanzu da ya kasance 'dayarsu zatayi aure dayake kusan itace ta farko ma bayan gama makarantar tasu kuma classmates 'dinta yanzune suke SS3 basu gama ba so sai suke ta marmarin ganin lokacin bikin ya iso, itace aka fara saka ranar bikinta shi yasa suke ganin kamar wani abu ne na daban, hira suke tayi abinsu, na dariyane, takaici ne, abin tausayi ne duk suna ta tunowa da school life 'dinsu lokacin suna tare da ita, ita kanta Teemah ma warewa tayi suna ta shan hirar su, ga Hannah ma acikin su kamar da ma already sun san juna. Garin yin dariya ne wata acikinsu me suna Naanah ta danne 'kafafun Teemah dayake ta mi'ke 'kafafun nata ne a abakin gadon saboda gajiya datayi da yanda ta tankwasu tun farkon zamanta agun " waashh....... Naanah kin karyan 'kafata". Ta yi maganar tana wani kwa6e fuska tare da janyo 'kafarta ta zuwa gabanta. Duk kan su sai hankalinsu ya dawo kan Teemahn suka zuba mata idanu kowa na mata sannu, sorry, da sauransu. Fauziyya (Fauzee) ce tace " ke Naanah ki riinga kulawa kar kisa ahana mu fita daga gidannan bari kiji "! Sai Hannah ta kar6e da fa'din " gaskiya kam, in ba haka ba ina ke ina jiwa amarya ciwo" "Ai kuwa de " inji Hauwa da ke 'ko'karin ja wa Teemah 'kafar tata". "Kuma dai wallahi, ku kyaleta dallah inta karye banda murakata da sabon wheel chair 'dinta agefenta, kunga ta kafa tarihi a auranta". Dariya dukkansu suka sanya har Teeman, tana cikin dariyar tace " wallahi kin iya wula'kanci yarinyar nan. " ai gaskiya ne, kya tsaya kina wani yi mana raki anan bayan ciwon bawani na kirki bane.......! Fauzee ce ta amshe maganar da fa'din " ke bata son jikin ta ya samu matsala ne ke baki ga yanda ta koma bane ta wani yi fresh da ita". " 'kwafa Teeman tayi kana tace " har ina wani abin fresh 'din anan dan Allah, ahakan ne zaki ce na wani yi fresh dani?, haba Fauzee..... dubeni fa ke baki ganin irin ramar dana yi ne,?Allah mummy da kanta ma cewa take yi wai na rame dayawa sai ta ta sani cin abinci kullum wai ko zan 'dan murmure". "Duk da haka de ke kam ki yadda kin canja, ai rama daban canjawan skin ma daban" Cewar Naanah. Fauzee kuwa tace " muma dai ya kamata mu fara haramar yin auren nan ko ya kuka gani"?Ta 'karasa maganar tana rarraba wa sauran idanu. " toh zakwa'di ai de kya bari ki 'kare secondaryn tukunna ko?" Inji Teemah Baki Fauzee ta rufe "au ashe fah da sauran mu mu 'din bamu gama ba". Dariya suka kwashe mata dashi dukkansu sai Jiddah tace " 'yar rainin sense....da 'din mantawa kika yi kenan." " Tamanta cewa ni ka'daice na girma acikinku" Teemah ce tayi maganan tana musu dariya. " ai ki bari wallahi nima da nasani da nace wa Babana zan rubuta waec alokacin nasan da bazai hana ni zai barni, kunga da ina yin candy nima sai asha biki na irin na Fatima Kb". sai Teemah tace " ke kika sani, yanzu kam ai ya wucheki sai ayi ha'kuri ajira next year " Haka suka ci gaba da hira atsakaninsu, gwanin birgewa Teemah kwata-kwata mantawa tayi ma wani batun aure, ji take kamar suyi ta zama ahaka kar su tafi. Acikin hirar ne Naanah tace da Fatima itafa gaskiya bata san waye angon ba anuna mata shi ko a pix ne, saboda taji ance wai yayanta ne 'dan gidansu, kuma yayun nata kusan mutun biyu tasani bata san kuma wanene shi daga cikin su ba so tana so taganshi. Sai duka sauran ma suka goyi bayanta dan hatta Hannah ba ta gane shi ba, ko lokacin dayaje gidansu ma basu ha'du dashi ba har yatafi shiyasa bata sanshi ba. Teemah wayarta ta tashi ta 'dauko ta nemo photon shi 'daya daga cikin wanda yake tura mata tun lokacin suna chat sosai dashi ta nuna musu kar6ar wayar sukayi suka ringa zuzuta kyanshi dan ba 'karya Mahmud ba baya bane wajen kyau da cikar kamala. Koda wayar tashiga hannun Hannah ma " wow " tafara fa'di tace gaskiya ya ha'du, ni sai na gama kamar kuna 'dan kama ka'dan dashi"? " badole ba ke kuwa abinki da jini 'daya" Cewar 'daya daga cikin su. Mahmud kyakykyawa ne shi, yana da tsayinsa daidai gwargwado, shi ba fari tas bane kuma ba ba'ki ba skin colour 'dinshi me kyau ne kuma ya kar6i yanayi da tsarin sa, gashin kansa irin na asalin fulani ne ananna'de yake kuma akwance luf luf dam ma shi yana yawan aske wa be fiya son tara gashin ba sai dai yabar 'dan daidai, kammanin sa na fulani sak yayi wata 'kila yabi jinin kakarsa ne mahaifiyar Babansa ( Innah Hansatu) sai de shi yana da 'dan kauri ka'dan kamar Antyn sa (mahaifiyarsa ) bashi da sirinta ko ka'dan, abinda kenan ya 'dauko daga wurin mahaifiyarsa." " danma baki ga 'daya yayan nata ba, shi sun ma fi kama da Kb sosai, inji Fauzee tafa'da tana me kallon Hannah Azaton su ita 'dinma wata 'kawar Fatiman ce daga wani 6angare daban duk da akwai 'dan kama na jini tsakaninsu, saboda duk wanda yaga Teemah yakuma ganin Hannah sai yaga wannan kamar da suke dashi, amma su basu ma lura da hakan ba, shirman su kawai suka sa agaba. Daga nan suka cigaba da zuzuta kyawu da tsaruwar yayun Teeman dayake sun sansu gaba 'daya ada lokacin tana zuwa school duk cikin su babu wanda be yi mata rakiyar zuwa makaranta ba daga Mahmud 'din har Abbas. Fitsari ne yadami Hannah sai ta tashi ta shiga bayi to ease her self, ko da tayi fitsarin tagama sai kuma tayanke shawarar yin wanka saboda lokacin da Teemah tayi wanka 'dazu ita daman batayi ba tana kwance tana ta chat abinta har 'kawayen Teeman suka zo. Shi yasa data shiga batin sai tace kawai bari taha'da da wanka gaba 'daya. Shiganta ke da wuya kuwa sai akazo akayi kiran Teemah wai suzo inji Ummah ita da Hannah. Tashi Teemah tayi tace wa 'kawayen nata "bari inje ina zuwa yanzu, idan Hannah tafito ku sanar da ita Ummah tana nemanta dan Allah". "Toh" sukace mata daga nan tayi waje. Koda taje d'in sai Ummah ta tambayeta ina Hannahn kuma bayan nace kuzo tare, yayanku ne yazo kuma zai wuche yanzu shine nache ya tsaya ku gaisa inajin yana 'dakinsa, kinsan shi da gaggawa wai yana da abunyi agabansa". " Ummah bayi Hannahn tashiga bari in dubota toh sai muje tare".Teemah tayi maganar tana 'ko'karin juyawa har muryarta na rawa. " ah ah kyaleta kar a6ata masa lokaci ke kije ku gaisa kawai in tafito dawuri sai ta samoki". Ummah ne tafa'di haka dai dai shigowar Mummy da try ahannunta an shishshirya abinci akai "ingo tafi masa da wannan"inji mummyn tayi maganar tana mi'kawa Teemahn try 'din dake hannunta. Kar6a Teemah tayi tafara tafiya ahankali, tunda Ummah tace _yayanku ne yazo_ take jin zuciyarta na harbawa da 'karfi, bata bu'katar wani dogon 'karin bayani domin tasan Yah Mahmud ne yazo shi tun da tasan shine future husband 'dinta dole shine yazo, dan shi ka'dai ne zai bu'kaci ganinta awannan lokacin dole tasan sai hakan yafaru. Ita duk atunaninta Mahmud ne yazo ,kuma bata san me yasa taji tsoro yashige ta ba, duk da wani tsoron Yah Mahmud 'din take ba amma sai takejin wani iri tamkar karta taje gurin shin haka taji, wai yau zata ga Yah Mahmud 'dinta, her beloved brother, amma ba'a wannan matsayin da ta sanshi akai ba, yau Yah Mahmud amatsayin wanda zai kasance miji ne agareta zata gani. Bata so tasake ganin Yah Mahmud ba, inda son ranta ne har se bayan anyi auren wata 'kila alokacin zataji son ganin shi amma yanzu kam da za'a tambayi ra'ayin ta kafin yazo da ta ce yayi zamansa basai yazo ba, bata san me zata ce da shi ba ko da ta ganshin ma yanzu. Tafiya takeyi ahankali tana tunani har ta isa 'kofar 'dakin da tasan na Mahmud 'dinne wanda iya zaman sa agidan anan yayi rayuwa, hannun ta da abu so babu daman ta tsaya yin nocking a'kofar, thank God ma 'kofar ba'a rufe gam take ba sai kawai tasa 'kafa ta tura sai 'kofar ta bu'du, ciki ciki tayi sallama bata wani jira jin amsa ba ta tura kanta ta shiga ciki. Bugun da zuciyar ta keyi ne ya 'karu fiye da na baya, sai ta kasa 'daga kanta ta kalleshi har taje ta ajiye tire 'din a kan centre table 'din dake cikin 'dakin sannan ta 'dago ta kallo bayan wanda ke tsaye agurin window tamkar andasa shi. Maganar mummy ta tuno da kusan kullum sai ta mata tuni akai inda take cewa " ayanzu baki _da wani makami Fatima face addu'arki da kuma ha'kuri, dan nasan su ka'dai ne zasu jagorance ki ga dukkan al'amuranki, dole ne kiyi ha'kuri da duk wani abu da zai faru ko zaki gani, kawai kisawa ranki daga Allah yake kuma 'kaddararki kenan, kuma shi yaso ganinki awannan matsayin, domin yawan nuna damuwa akan abu bashine zai kawo miki sau'ki ga al'amarin ba face addu'ar ki, damuwar taki bata da amfani koka'dan sai ma yasake 'daga miki hankali, tunda ke kanki kinga alamun Daddyn ki ba barin zancen auren nan zaiyi ba inajin mutuwa ce ka'dai zata sa yafasa 'daura auren nan ayana yin da naga yake ciki, ki daure ki ya'ki zuciyarki kisawa ranki san auren tun yanzu, idan ma kina jin rashin son Mahmud 'din ne to ki dole ne ki daure ki kauda wannan tunani tun yanzu, Mahmud 'din nan dai da kika sani shine zaki aura ki kuma zauna dashi, dan haka kiyi ha'kuri na tabbata Allah yana tare da dukkan bawansa me dogaro dashi, Fatima ni mahaifiyarki ce kuma mai tsananin sonki fiye da zaton ki, wallahi da'ace inada wata dama ko hanyar da zan iya hana faruwar wannan auren da zan hanashi ko dan ganin farin cikinki ka'dai ma, amma na tabbata dai dai da 'kwayar zarra ban kai ubangiji mahalicci sonki ba kuma shine yaga dama ya za6a miki shi Mahmud 'din dan haka kinga mu bamu isa mu ja da lamarin ubangiji ba, sannan mahaifinki ma basai na sanar dake son da yake miki ba Fatima ke kanki kinsani, kuma shi kanshi bazai ta6a yi miki abinda yasan cutarwa ne agareki ba har abada nasan kinsan wannan, ki daure kiyi masa biyayya kinji.... ina da ya'kinin duk daran da'dewa watarana zaki ga haske arayuwarki insha Allahu_ " Hawayen daya zubo mata tasa hannu ta goge shi tas tana yi tana sake bawa kanta 'karfin gwiwa "Mummy bazan yi kuka ba, bazan sake yin kuka dan zan auri yah Mahmud ba, na miki al'kawari insha Allahu mummy" Tana goge hawayen fuskar tata take wannan maganar. Mummy tana nufin insoka ya Mahmud in 'kaunace ka badan komai ba sai dan saboda Allah mahalicci, dama ni ban ta6a jin bana sonka ba Yah Mahmud amma wani lokaci sai inji dama ba kai Daddy ya za6a min ba sai inji dama ya barmu a yanda muke tun farko kaci gaba da zama amatsayinka na yayana nafi feeling compotable akan haka, ban San me yasa ba amma sau da dama sai inji dama Yah Abbas Daddy yace zai aura min ba kai ba". 'Daga kai tasake yi ta dube shi, tun 'dazu data shigo ahakan yake be canja tsayuwarsa ba tsaye yake hannunsa 'daya acikin aljihu ga dukkan alamu tunani yake yi wata'kila shi yasa bata samu amsar sallamar ta data masa lokacin data shigo, Yah Mahmud bai fiya yin hakan ba yakan amsa sallama koda baya cikin yanayi na walwala sannan baya ta6a kyaleta matu'kar ta kusanci inda yake koda kuwa tayi masa abin 6acin rai baya ta6a yin fushi da ita amma ji yanzu yanda ya shareta tamkar ma besan tashigo bayan tana da tabbacin yaji shigowarta tunda da sallama tashigo, gashi ma sai taga ya 'dan rame mata 'ka'dan bakamar yanda yake ada ba, kar dai shima baya son auren ne kamar ni,? kardai maganan auren ne yasaka cikin damuwa ? Ahankali ta 'dago 'kafafunta ta har sai da ta iso kusa dashi kafin ta tsaya daga bayansa " _Yah Mahmud_ "! Ta 'kira sunan shi ahankali kamar bata son yin maganan. Be amsa ba kamar yadda be juyo ya kalleta ba haka kuma babu

Chapter 22 of 67