Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yasan ba komai zai sata kukan ba face memories 'din Mahmud wanda shi kansa ma ji yake duk yayi laushi sosai. Suna shiga room 'din da suka sau'ka kuwa yajawo ta jikinsa ya fara share mata hawayen yace kukan ya isa hakan nan ta daina" Da 'kyar ya samu kukab nata ya tsaya sannan shima ya 'danji natsuwa ta shige shi. Wanka suka shiga a tare wanda kafin su fito daga bayin sai da ya tabbatar ta bar kukan nata gaba 'daya ta sanywa fuskar ta murmushi tukunna ya sarara mata. Tana shafa mai a 'kafarta ta 'kira sunan sa yayin da shi har ya fara saka kaya ma itan ce dai ta tsaya sai yanzu dayake ma bata 'dan jin da'di sosai duk jikinta bata jin da'din sa ga marar ta dake 'dan mata ciwo. Yana jin ta 'kira sunan shi sai ya waigo ya dube ta batare da ya amsa ba. Tambayar sa tayi cewa "Yayah ina wancen ku'din nan da aka ce wai na gado na ne" Sai yace mata "yana nan kina so kiyi amfani da shi ne? Teemah tace "ehh" Inda ta ro'ke shi akan tana so duk abinda za'a yi wa su Innah ayi musu da wannan ku'din" Abbas kai ya girgiza mata yace "ah ah wannan ai burin Mahmud ne komai za'ayi da sunan shi ne, yace shima 'din da sunan Mahmud yazo kuma duk abinda yakama ayi zai yi shi koma menene amma duk bada sunan shi ba, su 'din kamar 'yan aike ne domin wannan tafiyar ta Mahmud ce, da sunan ne akayi ta, yace in taimako zatayi tabari idan sun koma gida sai suyi planning wani abin daban yace ko makaranta ma zata iya ginawa da ku'din shima ba laifi bane kuma akwai sosai shima. Shiru tayi ta sunkuyar da kanta 'kasa bawai dan bata yadda da abinda yace 'din ba ah ah, sai dan yanda take jin yanayin da take ji ajikinta na 'kara tsananta. Abbas barin abinda yake yi yayi da sauri ya 'karaso inda take ya zauna, inda yana zama sai ta kwantar da kanta ajikinsa hawayen ta na 'kara sau'ka a hankali, sosai yaji hankalin sa ya tashi sai yafara tambayar ta mai ke faruwa meke damunta. Kamar bazatayi magana ba sai can ta 'kira sunan shi a hankali ta ce " _Yayah_ ! " _Na'am_ " Ya amsa ta dashi yana me bada dukkan hankalin sa izuwa gareta, sai ta kamo hannun sa ta kai kan marar ta tace "Yayah zafi yake min sosai ka danna min a hankali dan Allah" Kamar yanda ta bu'kata haka yayi mata sai dai instead ya danna matan sai ya rin'ka shafawa a hankali yana sake kallon cikin nata ganin ya 'dan taso ka'dan. Yana shafawan yake 'kara lallashin ta da kalamai masu sanyi tare da tambayar ta ko zasu je hospital a duba ta, girgiza masa kai tayi tace " ah ah gajiya kawai tayi shiyasa kuma zai daina ma anjima ka'dan" Shiru yayi mata kawai ya ci gaba da shafa marar har bacci ya 'dauke ta, ganin haka sai ya saki ajiyar zuciya tare da gyara mata kwanciya ya rufe ta da kyau. Kafin ta tashi har an kawo abinci da yake dama da yunwar ta tashi so bata tsaya 6ata lokaci ba ta lodi abincin ta, Abbas na ta kallon ta dan shi coffee kawai yasha tun zuwan sa sai ko kayan itatuwa, sai da ta gama kafin tayi sallah inda daga nan suka fita yawo cikin gari ganin ta warware sosai, Abbas ba haka yaso ba dan shi clinic yaso kaita amma Teemah ta'ki amincewa da hakan tace dashi ai ta riga ta warware. Washe gari da yamma Rabi'u ya tabbatar wa Abbas cewa ya gama komai na bu'de account inda ATM ne ka'dai ya rage masa. Tare dashi suka je store amma Abbas bai bari Teemah ta bisu ba yace babu inda zata, siyayya suka yo na kayan abinci masu yawan gaske inda duk suka sau'ke shi gidan Innah. Sannan Abbas yayi transfern ku'di cikin sabon account 'din Rabi'u yace ya tabbatar da cewa yaran Innah basu nemi wani abu sun rasa ba kuma duk suna zuwa makaranta, shi kansa Rabi'un ma Abbasa ya bashi daman ya rin'ka yin bu'katun makarantar sa da ku'din kar yaji tsoron ta6awa tare da yimasa al'kawarin 'daukan nawin makarantar tasa in har yana raye har inda ya ga daman tsayawa da karatun. Abbas yayi al'kawarin cewa da izinin Allah zai yi 'ko'karin ganin ya kula da hakan. Kuka da godiya ranar kam yasha su sosai kamar su goyashi, Umar kansa sai da ya ga karamcin Abbas sosai inda shima ba'a barshi abaya ba ya ciri ku'di kimanin 20k ya dam'ka a hannun Innah. Shi kuwa Abbas duk abinda yayi 'din ko 'daya bai yishi da sunan kansa ba yayishi ne da niyyar cikar burin marigayi Mahmud coz niyyar sa ce hakan shine yafaro abin tun farko dan haka duk da cewa da dukiyarsa yayi amfani amma niyyarsa daban ce. The following day suka koma Abuja inda suka bar Umar acan saboda mahaifar sa ce zai tsaya ya duba 'yan uwa da dangi kafin ya wuce Lagos. Da komawar su kuwa Abbas yaji zaman Abujan kwata-kwata ya isheshi gaba 'daya, da isarsu ko hutawa bai yi ba ya wuce ya dubo gininsa da yake yi acikin unguwar tasu, washegari kuwa gidan Ummah suka dira, suna can ma sai kuma wani abokin sa ya 'kira shi cewar suna hanya zasu kawo musu ziyara. Wannan dalilin ne yasa suka dawo gidan nasu suka tari ba'kin da suka zo, Teemah naganin Nasreen ai sai ta washe baki tana murna ta rungume ta tare da fa'din " oyoyo my baby girl", Nasreeen kam harta manta ma da ita, amma dayake asali bata 'kin mutane sai suka sake yin wani sabon kuma, yanda Teemah takeyi da yarinyar tamkar wata yarinya 'karama itama ta koma, Maman Nasreeen kam sai de tayi ta musu dariya. Da zasu har wajen mota suka yi musu Rakiya inda Teeemah tacikawa Nasreen haka da kayan ciye-ciye irin nata. Abbas yaso ya koma da matar sa Rivers su 'karasa hutun acan amma ganin Daddy nagari sai ya sashi ha'kura dan jin tsoron abinda daddyn zai ce coz sam shi bai son haniya akansa ballantana har ransa yasake 6aci karo na biyu akan zancen tafiyar. Sai ya cire batun tafiya da ita aransa ma gaba 'daya kawai ya yanke cewa gara tafara zuwa makaranta tunda babu abinda takeyi yanzun illa zaman gida wanda yake ganin kamar hakan ma zai 'kara sata ta warware in tana shiga cikin 'dalibai 'yan uwanta 'kila ko lokacin yin tunani ma bazata samu ba. S.S.C.E result 'dinta ya nemi gani dan ya san ta ina zai fara nema mata admission kafin ya wuce. Nan kuwa yasha mamaki dan Teemah kam da taji yace " Result 'dinta " Sai ta zaro idanu kamar da mamaki tace " Ni.... ni kuma nawa Yayah? Abbas yace " da 'din wa kike ganin zan tambaya anan?" Teemah da iskanci, juyawa tayi kamar dagaske ta 'dan kakkalli cikin 'dakin wai ko zata ga wani daban a ba ita ba sai kuma ta tura baki tace " Nima fa Yayah bansan inda yake ba" Waro idanu yayi akanta da mamaki yace "kamar yayah bangane ba?" Sai tace " Ni....nifa agida na barshi can damaturu kuma bansan inda yake ba yanzu sai dai a tambayi Mummy" Abbas tsaki yaja ka'dan yace " Yanzu fisabilillahi result 'din makarantar ki ne kike cemin baki san inda yake ba, to ke da kanki baki adana ba waye kike tunanin zai adana miki?" Allah zanga ranar da zakiyi wayo kekam, a hakan ne kuma kike wani son baby, salon ki ta koya musu shirmen ki ko?" Kauda kai tayi gefe ta 'kasa-'kasa tace " Ni kam inada wayo na" Muryarshi data jiyo yace mata" _meaning_ " neya sata gane cewa yajita. A'dan firgice tajiyo sai ta cikaro da shi tsaye kusa da ita da gira 'daya a'dage sama ya kama kunkumi da dukkan hannyensa kamar mai shirin fa'da da sa'an sa. 'Kasa tayi da kanta tana muzurai. Sai taji ya sake fa'din "tambayarki nakeyi ko?" Teemah 'dan matsawa baya tayi ka'dan ta kauda kai tana 'kun'kuni sai taji ya 'dalli bakinta da yatsun sa biyu. Kuka ta fara tana ri'ke bakin tana kallon shi sai ya daka mata tsawa inda yace " Shut up da Allah, dama ni sa'anki ne da zaki rin'ka yimin hakan? Kuma karki min shiru kiga abinda zan miki right now, cry-cry kawai" Hanyar barin 'dakin takama sai ya sake fa'din " kuma ki 'kira Mummyn ki tambaye ta yanzun nan ina jiranki kizo ki sanar dani feedback" Fita tayi da sauri kamar an kunnata da switch shima sai bita da idanu tare da sakin tsaki, haka kawai yau 'din ya tsinci kansa cikin 6acin rai. Koda ta koma 'dakin ma sai data sha kukan ta na shagwa6a son ranta dan ba kukan ciwo bane kawai shagwa6ar ce yau ta motsa da kuma haushin ya 'dalli bakin ta, kafin daga baya ta tashi ta koma gaban mirror ta duba fuskar ta da kyau, gani tayi ma bakin bai ko tashi ba amma duk da haka sai ta janyo stool ta zauna taci gaba da 'karewa fuskar tata kallo. Bata san meke damun sa ba yau 'din amma kallo 'daya zaka masa ka hango 6acin rai tattare da shi, ita kanta tasan bahaka ya kamata tayi masa magana ba musamman dayake neman hanyar da zata janyo mijinta ajiki takeyi yanzun take sai kuma taga rashin kyautawarta. Wani 6arin zuciyarta ne yashigar mata da tunanin "ai shima bai kamata ya 'dalli bakinta ba bata mar komai ba haka kawai dan ranshi ya 6aci kuma ai tasan ba ita bace ta 6ata masa rai 'din meyasa zai zo ya huce akanta?" Kalaman Anty ne suka bijiro ranta inda tace da ita " auren ha'di na tafe da wasu irin 'kalubale wanda sai kai da kake cikin sa ne zaka san hakan in kayi sa'a kuwa bazaka fuskanci irin wa'dan nan matsalolin ba sai kaga ka dawwama cikin farin ciki, amma dukkan su ba'a cin galaba akan su har sai in an ha'da da ha'kuri" Teemah ido ta lumshe tana tunanin abinda Yayah zai yi da result 'dinta tasan dai duk ba zai wuci batun makaranta ba ita kuwa sam bata so, wanda tayi abaya ma Allah yasa albarka amma tunda yace yanaso 'din bari ta 'kira Mummyn taji ko ta san inda yake. 'Daukan wayar ta tayi ta 'kira layin Mummy, bata 'daga ba sai da ya yanke kafin tana sake 'kokarin gwadawa sai ga 'kiran Mummyn ya shigo, gaisheta tayi cikin natsuwa tare da tambayar ta Daddy daga nan ta 'kara da tambayar result 'din sai Mummy tace da ita duk suna nan Dubai ta taho dasu tama manta ne dama taso ta taho mata da shi amma sai ta sha'a fah. Teemah aranta ta ringa godewa Allah sam bata son damuwar makaranta ita aganin ta ai ba dole bane tunda wasu ma bayi suke yi ba gaba 'daya. Sallama sukayi da Mummyn ta ajiye wayar sannan ta tashi a hankali take tafiya kamar mai jin tsoron 'kasa tafito daga 'dakin nata. A parlour ta same shi sai ta 'karasa gefen sa ta zauna tace " Yayah! Tun fitowar ta ya ji motsin ta amma bai nuna alamun ya ji ta ba sai ma ya rintse idanun sa yayi sama da kansa. Jin ta ambaci sunan shine yasa ya bu'de idanu tare da juyowa ya kalleta inda take ya hango rauni tattare da ita. Suna ha'da idanu sai ta ce " Mummy tace wai tatafi dashi Dubai" A nutse tayi maganar wanda shi kanshi sai da yaji natsuwa ta shige shi, sai yayi murmushi ka'dan wanda ya tsaya masa iya gefen baki yace " kin kyauta ai yanzu kam, it seems like kinfi so ki cigaba da zama agida fiya da zuwa makaranta ko?" Teemah kam kanta ta 'daga sama alamar " ehh" Da mamaki ya kalleta yace " wai ke dagaske kike yi ne dama? Degree 'din ne baki so ko kuma me? Baki so ki rin'ka zuwa makaranta irin na Hannah? Da kanta ta sake bashi amsa tana wasa da yatsun hannun ta. "Wonders shall never end" Yace aransa yayin da mamakinsa ya 'karu fiye dana da. Bai 'kara kulata ba kawai ya shareta aransa yake tunanin may be bata da lafiya ne coz bai fiya ganin wanda ya nuna zallar 'kiyayyar sa da karatu har haka ba, shi ada datake cewa bata so 'din nan duk ya zaci wasa ne sai yanzu ta suprising 'dinsa amma duk da haka bai fasa ba yasan idan ta tsinci kanta cikin makarantar dole ne zata waraware ai tayi abinda ke gabanta. Abbas be 'kara kulata da maganar ba har akayi kwana uku, kafin hakan kuwa zama mai kyau ma basu yi da ita ba dan saboda abubuwan da ke gabansa. Ran kwana na ukun ne shine yace da ita nextweek zata fara registration dan already an yi nisa da bada admission shima da 'kyar yasamo mata admission 'din tunda batayi jamb ba zata fara ne tun daga remedial kawai sai ta fara preparation na zamowa student. Tana jin haka sai ta yatsine fuska tace " Allah nifa banson wata makaranta Yayah" Abbas be kulata ba kawai ya 'kyale ta coz ya riga ya yanke decision cewa matu'kar bazai tafi da ita Rivers ba kuwa makaranta dole ne agareta. Kafin lokacin registration ne 'din ma shi ya koma ports bakin aikin sa, aranar ne kuma ya 'kira ta da sassafe cewa su tafi tare da Hannah ta rakata NILE, inda yace ta duba drawern 'dakin sa zata ga komai da zata bukata aciki. Ko 'kala Teemah bata ce da shi ba har ya yanke 'kiran shima bai damu ba tunda yana da tabbacin tajishi. Tana cire wayar a kunnan ta sai ta dannawa Ummah 'kira cikin siririyar muryarta da shagwa6a tace " Ummah kinga Yayah ko? Wai sai na je Nile ni kuma banaso! Cike da kulawa Ummah ta tambayeta "to wanne take so?" Teemah kuwa tace " ni fah Ummah banason ko 'daya kuma ai na gaya mishi tun ranan ma" Ta 'karashe tamkar zatayi kuka. Ummah kam lalla6a ta ta hauyi tana bata baki da ha'kuri wai ko zata amince. Amma Teemah ta kafe akan ra'ayin ta, Ummah ganin haka sai ta ha'kura ta 'kyaleta kawai tare da sanar mata cewan zata yi masa magana daga nan ta sallame ta. Take Ummah ta sake 'kiran Abbas ta sanar dashi yanda sukayi da Teemah tare da bashi ha'kurin ya 'daga mata 'kafa zuwa wani lokacin 'kila da kanta ma ra'ayin karatun zai shige ta Ummah tace yabita a hankali aga iya gudun ruwanta. Abbas kam zuwa yanzun haushi tafara bashi yarasa sam ita wace iriyar yarinya ce da komai ra'ayin ta sai ya bambamta da mutane ga shegen taurin kai, in haka ne kuwa tsab zaiyi maganin ta shima akan zuwa University 'din nan sai ya bata mamaki. 'Kin amincewa yayi da batun Ummah duk kuwa da da'da'dan kalaman da ta ringa yimasa saboda sanin halin sa amma duk da haka maganar bata wani shiga kansa ba sai ma yake ganin kamar iskancin Teeemah ne kawai yayi yawa ba komai ba, kuma ai karatun dan kanta ne zata yishi bawai shi zata yiwa ba toh ma miye abin gudu a makaranta in banda shirmen ta. Ummah data ga bazai saurare ta ba sai ta sanar da Daddyn Abuja abinda ke faruwa. Shima yayi mamakin hakan inda da kansa yasa suka zo da Hannah yaringa lalla6ata da bata baki akan ta amince da makarantar, saboda shima Abbas ya sanar da shi komai ya sanar dashi babban dalilin sa na son tashiga makarantar musamman ko dan ta rage zaman gida ita 'dayan ma da takeyi shiru kullum tunda Hannah ma ba yini take ba kwana ne kawai, Daddyn ma da kansa yayi supporting Abbas 'din 100% ya goyi bayan hakan dayake yasan shine ya hana Abbas 'din tafiya da ita. Dalilin kenan daya sanya ya ringa nuna mata muhimmanci da amfanin ilimi musamman ga 'ya'ya mata, harda manyan misalai ya ringa kawo mata amma yarinya ta 'ki canja ra'ayi duk kuwa da cewa ta fahimce shi. Amma hakan bai yi mata tasiri ba sam dan ita aganin ta tunda ba ilimin addini bane toh babu ruwanta. Daddy kam dayaga ita da Abbas 'din duk sun kafe akan ra'ayin su sai ya sanar da Daddy babbah ( mahaifin Teeemah). Daddy murmushi yayi daya ji labarin abinda ya farun sam bai yi mamaki ba coz sarai yasan halinta da kafiyar ta kuma indai akan karatu ne haka Allah yayita tun tana yarinya 'karama sam bata so har garama na islamiya ta kan bashi muhimman ci. Daddy ma awaya ya 'kirata cike da farin ciki ta gaida shi tare da tambayar sa Mummyn ta, Daddy yace tana nan lafiya sai ya 'kara da fa'din " Angel 'din Daddy sarkin rigima, ba nace ban son taurin kai ba shine kuma kike yiwa yayanki ko?" Shagwa6e murya tayi tace " banayi masa fa Daddy " "Toh ya akayi naji wai ance baki son karatu har kina 'karan Yayanki akan hakan?" Hawaye tafara inda cikin hawayen tace dashi " Allah ni Daddy ban son wani makaranta shi kuma Yayah yace sai nayi ni kam banaso Allah" Sai yace " gaya min to ni inji meyasa baki so Angel?" Tace "ni haka kawai ne Daddy" "Bakya tunanin gaba zai miki amfani ko? karfa watarana kizo kiyi regretting akan hakan?" "Insha Allahu bazanyi ba Daddy karka min fatan hakan, kuma ko nazo nayi ma bazan yi blaming kowa ba tunda nasan babu wanda ya hanani" Daddy cewa yayi "shikenan to Angel 'din Daddy amma fa banda rashin ji kinji " Da murnar ta tace "toh Daddy ai na ma daina" "Yauwa uwata Allah yayi miki albarka yasa haske cikin rayuwarki" Da "Ameen" ta amsa masa sannan sukayi sallama. Daddy yasan kowani irin mutun nada kalan nashi burin da Allah ya halicce sa da shi hakama ra'ayoyin mu suke mabambanta ne. Yasan halin Fateemah da taurin kai akan abu musamman idan batayi ra'ayi akai ba toh da wuya ka iya tan'kwarata, ha kama karatun yasan koda ansata bayi zatayi ba tunda bata yi niyya ba ba abin kirki zatayi ba kuwa ko da ta fara, shiyasa ma ya rin'ka biyeta lokacin da takeyin secondary school, makarantu sun kai hu'du ya ringa canza mata duk dan ta nutsu, duk wanda tace tana so baya gardama yake canza mata da 'kyar ta tsaya tagama aguda 'daya. Shi karatu ra'ayine kuma ba'a ta6a yiwa mutun dole, domin kuwa ko ka tilasta wa mutun ya fara to in bashi da ra'ayi bazai ta6a yin karatun ba ballantana har asamu abinda akeso. Tunda an lallasheta ta'ki ji kawai sai abarta, dayawan mutane ma ai sunyi surviving batare da sunyi karatun ba, so ba matsala bane dan ta 'kiyi rayuwa duk tacgaji haka, wani zaka yasamu amma yana 'kinyi yayin da zakaga wani yana fafutuka da 'karfin sa da komai dan kawai yaga yasamu, wani kuwa duk ma sai kaga babu damar, domin bai samucgatan ayi masan ba kuma shima sai kaga Allah bai bashi hanyar da zai nema da kansa ma ba sanadin haka dole sai kaga mutun ya ha'kura gaba 'daya, amma duk hakan ba laifi bane face salo na rayuwa kawai domin kowa da kalar tashi 'kaddarar. Balle ga ita data ke matsayin 'ya mace ai zaman auren shine gaba ayanzu, matu'kar zata zauna a hakan cikin kwanciyar hankali ta bautawa ubangijinta ta kuma yiwa mijinta biyayya to shi bashi da matsala da ita burinsa dama tayi farin ciki. Abbas Daddy ya 'kira yayi masa bayani tare da bashi ha'kuri akan maganar yace ya 'kyaleta kawai tunda bata yi ra'ayi ba, wata 'kila watan wata rana ta nemi yi dakanta lokacin da ra'ayin hakan ya shigeta. Abbas bai so hakan ba amma ya ha'kura shima ya bar zancen kawai, amma sosai ya jinjina wa kafiya irin tata, ace mutun karasa abokin gaba sai karatu.....gaskiya abin da mamaki, yasha jin labarin irin dramar da ake sha da mata akan karatu amma nata salon daban ne, maimakon tayi fitinar an hanata yi ah ah sai ma fitinar ita bataso.......ha'ki'ka duniya kowa da kalan halin sa, abinda kake ganin dai-dai ne awajen ka sa6anin hakan kuwa ga wani sai ya zama abin gudu da 'kyama na musamman, sosai yake 'kara jinjina mata a duk lokacin daya tuno duk lamarin hakan yafi matu'kar ri'ke ransa. Shima kuwa Abbas sai yace in dai hakane kuwa ba ita ba zaman Abuja dole tabishi Porthacourt, wannan karan Daddyn Abuja bai hana shi ba dan yasan shi ke da iko akan iyalinsa, ko wancan lokacin ma ya hana ne dan gudun kar ya cutar da ita, amma zuwa yanzun ya fahimci akwai 'yar fahimta a tsakanin su, kuma ma idan yacigaba da shiga tsakanin zaman nasu to bazasu ta6a sabawa da juna ba musamman idan akayi la'akari da yanayin aikinsa ba ya basu damar da zasu sake da iyalansu kamar kowa, kuma kusancin da ke tsakanin su shi yafi komai muhimmanci, abinda Ummah tayi ta 'ko'karin fahimtar da shi kenan tun a wancen lokacin amma yakasa fahimtar ta son 'yar sa da gudun kar a cutar da ita yayi wa zuciyarsa 'kawanya a lokacin ya hana shi ganin gaskiya. Teemah bata damu ba sai ma da'di da taji coz ko itama yanzun baso takeyi take yin nisa da mijinta ba ko dan ma ta cigaba da faranta masa, saboda ita ka'dai tasan halin da ta shiga wancan lokacin daya tafi ya barta. Ko ta je Rivers 'din kuwa bai nuna mata 6acin ransa ba koka'dan akan abinda yafarun duk ya fitar aransa dama dan ita ne to ita wacce za'a yi domin tan kuma tace bata so to shi miye na shi. Itace ma take 'dan jin fargaban ha'duwar su saboda tasan bata kyauta masa ba dole ransa zai 6aci da ita amma da suka ha'du ta gansa wasai sai itama ta saki ranta. Abbas rungumar matar sa yayi cikin walwala da farin ciki suka cigaba da rayuwar su. Amma Teemah kasa daurewa tayi sai data bashi ha'kuri daga baya domin guilty conscious ya kasa barin ta sai take ganin tamkar kawai yana kallon ta ne da abin aransa batare da ya furta ba, ga mamakinta kuwa sai yace mata ai bakomai karta damu komai ya wuche shi awaken sa. Sosai Teemah taji da'din hakan har cikin zuciyarta. Cikin cinye-cinyen Teemah kuwa babu abinda ya ragu aciki Abbas har ma ya saba da komai yanzu kuma ko damuwa ba yayi da canzawar ta balle yayi wani tunani akai, kawai ya bari akan lokacin cin abincin nata ne yayi shiyasa abinda kawai yasa aransa kenan duk kuwa da yasan cewa sam ba halinta bane hakan amma baya damuwa, ga wani shegen son sex daya shigeta yanzun, wannan ne ka'dai ya tsaya aransa, shi kansa yanajin da'din kasance wa da ita sosai fiye da baya har ma hakan yasa baya ta6a gajiya da kasancewar ta su be it shi ke so ko ita ta nema sam baya ta6a 'kin amincewa da hakan, sai dai wani lokaci takanyi ciwon mara, akan hakan ne yaso suje ganin likita amma tsoron kar ayi mata allura yasa ta'ki bashi ha'din kai. Abbas hankalin sa sai yakasa kwanciya da hakan sai ya shirya mata wani shiri batare da ta sani ba akan tunda bata san clinic ba anan garin da wayo zai kaita asbitin yasan in sun riga sun isa dole ne ta tsaya a dubata dan gudun kar ya cigaba da biyeta yana bin ra'ayin ta kuma abubuwa su zo su girmama su fi 'karfin tunaninsa a 'kurarren lokaci duk dama ba'a fatan faruwar wani mummunan abu amma wai akace maganin kada ayi toh fa kada asoma shi yafi. ***** Kwance take......... πŸ‘ŽπŸ» _Ina gaida mutane na makarantan wannan littafi ina kuma yi muku albishir 'din cewa just some few pages ne suka rage mana mu kammala wannan labarin sai dai alal ha'ki'ka ni kaina bansan zuwa kwana nawa hakan zai 'dauke mu ba gaskiya, fatan dai zaku cigaba da samba'do madaran comment wanda zasu rin'ka sani yi muku typing akan lokaci koda kuwa ban shiryawa hakan_ _ba......lolz_ πŸ€ͺ..... *A KAFTAH* 🀞🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* πŸ‘‡πŸΌ Assalama Alaiki warahamatullahi wa bara katuhu. Gaskiya

Chapter 58 of 67