Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai ta daure ta ciro maman a hankali kamar tana tsoron ta6awa dan yanda yake yi mata zafi, wanda hakan shine babban dalilin daya sanya tun 'dazun take tsoron bashi. Da dabara ta gwada saita masa a baki wanda har ya kama sai kuma tayi saurin cirewa ta maida abinta ta rufe, take wani sabon hawayen ya sau'ko mata sai ta kalli Hannah tace " Allah Hannah da zafi bazan iya ba" 'Bata rai Hannah tayi tace " Haba-haba ke kuwa, ki daure ki bashi dan Allah, ke baki ganin irin kukan daya ke yi ne? Tun fa a safe baki bashi yasha ba, kina ganin kyauta kenan? Ko irin tausayin shin nan bakijji ne ke?" Teemah kam sai cewa tayi " d'auke shi Hannah please ki bashi ko zam-zan 'din ma yasha may be zai yi shiru" Ta fa'da cikin hawaye. Tsaki Hannah ta ja tare da sa hannu ta 'dauke shi a zuciye tayi waje da shi. Gani take yi kamar rashin imani Teemahn ya zarce misali ne da har bata iya tausayin 'dan jinjirin dako kwanaki bai ma fara irgawa ba a duniya. Da idanu Teemah ta bisu har suka fice, inda suna fita ta kifa jikin ta a kan gadon tana kuka da hawaye, ita da kanta haushin kanta takeji akan abinda tayi. B'angaren Hannah kuwa koda ta fita da babyn jijjiga shi taci gaba dayi tana tafiya, sai sukayi kici6us da shi a corridor, shogowar kenan yajiyo kukan baby ya cika ko'ina agidan hakan yasa ya 'karaso nan 'din da gaggawa. Da 'dan hanzarin sa ya iso kusa da Hannah. Hannah ja tayi ta tsaya sai ya sa hannu ya kar6i babyn tare da fa'din " me ya same shi ne haka yake ta faman kuka?" Amsa Hannah ta bashi da fa'din " tun safe bai sha komai ba sai zam-zam da ruwa inajin yunwa ce ke damun sa" Yana jijjiga babyn yace mata " ina Fateemahn kuma take me yasa ta barshi haka?" Hannah sai tace " tsoro takeji wai maman na mata zafi". "Where is she now?" ya tambaye ta sai ta bashi amsa da fa'din " tana dak'i na" Tafiya ya fara yi da Babyn a hannun sa ba tare da ya sake fa'din komai ba ya nufi hanyar 'dakin Hannah 'din. Hannah ma 'karasawa tayi 'bangaren Ummah ta dubo ta jin bata fito ba duk wannan uban ihun sai ta tarar ma ashe sallah take yi shiyasa. Tambayar ta Ummah tayi wai " tabashi ne?" Sai Hannah tace " ina kuwa ta bashi, har fa ta ciro kamar zata bashin kuma sai tace wai zafi yake yi mata" Ummah cewa tayi " To ai da kin taho min da shi nan d'in...." Taranta Hannah tayi da fa'din " Yayah ne ya kar6e shi ai, yanzun nan inajin isowar shi ma" " ai kuwa ba mamaki dan ko ni ma bansan da zuwan nashi ba". Ummah tayi maganar tana mai cire hijab 'din data yi sallah dashi a kanta. Teemah kam kasa zama tayi a 'dakin dan yanda take iya jiyo tashin kukan babyn gaba 'daya ya kara'de gidan nasu, ga shi maghrib tayi sam hankalin ta sai ya kasa kwanciya, dan haka sai ta yun'kura ta taso da niyyar bin bayan Hannah, tana 'ko'karin bu'de 'kofa sai kuma taji kukan babyn na sake tunkaro 'kofan daga waje. Kafin ma ta bu'de sai ya riga ta bu'de wa sai suka tsaya kallon kallo. Ita kallon mamakin ganin sa takeyi musamman da ta gansa rungume da Babyn, yayin da shi kuma yake yi mata kallon " kin kyauta ai" Amma fuskar sa wasai babu wani alamun 6acin rai akai sai ma wani 6oyayyen sihirtacce kuma 'kayataccen murmushi. *Only oneโ˜๐Ÿป page to go insha Allah.......* ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*๐Ÿ˜ [10/13, 8:01 AM] ๐ŸŒธSalmerh๐ŸŒธ: ๐Ÿ’• *CAPTAIN ABBAS* ๐Ÿ’• By *Salmerh MD* Luv story๐Ÿ˜ *Wattpad @* *Serlmerh-md* ๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* ๐Ÿ’ซ We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated 2_ *Maman Ahmad &* *Anty Maimounath o.g ( Mahnoor).* *Mungode da 'kaunar da kuke nuna mana Allah Ubangiji ya bar mana ku (Ameeen)* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _U canโ€™t change what happened in ur past, so b4 u let it destroy ur future, learn to live with it...._ ๐Ÿ…ฟ *91* Ganin kamar zata 6ata mai lokaci ne sai yayi hanzarin wucewa da kansa ya za6o mata doguwar riga da hijab. Da taimakon sa ta sanya kayan a jikin ta tare da rufawa kanta hijab 'din still tana zubda hawaye suka fita zuwa clinic dake cikin barrack 'din nasu. Daya ke ma koda wani lokaci kaje suna aiki basa yankewa so ba tare da wata damuwa ba suka isa ga babban Doctor 'din dake kan aiki a lokacin. Abbas da kansa ya yiwa Doctor bayanin abinda ya kawo su Teemah kam sai hawaye take tana faman rarraba musu idanu daga gefe. Wata nurse likitan ya 'kira yayi mata bayanin abinda zatayi sannan ya ha'da su da Teemah suka je ta 'dibi jinin ta sannan ta bata wani 'dan k'aramin abu tasa ta yin fitsari a ciki. Teemah kam duk da tana cikin wani yanayi na tsananin damuwa amma hakan bai hanata ta6e baki da " mitar wai banda 'kazanta to me ze sa ta haka, a hakan ne wai Yayah zai ce itama ta zama likita" sake kallon robar tayi tana sake jinjina rashin kunya da 'kazanta irin ta likita. Zuwa tayi ta mi'ka ma Nurse 'din tana sake kallon 'kwayar idanun ta amma sai taga bata wani nuna komai ba ta kar6a ta wuce laboratory da shi, bin bayan ta Teemah tayi da idanu har ta 6acewa ganin ta, ita kam wurin tap taje ta ringa dirzan hannun ta kamar zata sille shi sai da ta tabbatar ya wanku tas sannan ta bari ta koma office inda ta baro shi. Zaune ta same shi shika'dai yana amsa waya ga dukkan alamu Doctor 'din ma ya fita ne. A hankali ta 'karasa jikin sa ta zauna tayi luf, sai da ya kammala da wayar kafin ya tambaye ta har an gama ne kai ta 'daga masa tare da fa'din " Yayah wurin ma zafi yake min sosai" Tayi maganar tare da nuna masa gurbin da aka ja jinin. Hannu Abbas ya kai yana shafa mata a hankali yace " Vry sorry...zai daina zafin ai kinji" Cikin sakalci da marairaita ta d'age kanta sama tare da fa'din " har da fitsarina fa ta kar6a Yayah". Abbas duban fuskar ta yayi sannan ya ce mata " ba komai ai test za'a yi da shi". Sai ya kai hannu jikin ta ya ta6a yanayin zafin jikin sannan ya 'kara da fa'din " har yanzu cikin na miki motsin ne?" Teemah sai tace " Ah'ah.......ya daina amma Yayah ni tsoro nake ji" Taran ta yayi da fa'din " Nima inajin hakan Zahra.. but Doctor yace min 'kila abin alkhairi ne zai same mu, amma bari dai mu jira ganin result 'din ko sai muga ko menene?" Teemah sai ta 'daga kai alamar "to" tayi luf a jikin sa amma abin sai yana bata mamaki, kasa jurewa tayi sai 'dago tare da sake fa'din " Yayah dama akwai alkhairi a cuta ne?" Abbas sai yayi murmushi sannana yace " akwai mana Zahra komai ai da irin 'kaddarar da yake zuwa dashi wani mai kyau wani kuwa akasin haka, inajin tamkar wani gagarumin farin ciki ne zai same ni, i feeel ths in my heart kuma ina fatan hakan ya kasance ki kwanatar da hankalin ki kinji ko insha Allahu ba abin damuwa bane". Mai da kanta tayi ta kwantar a jikin san sannan a hankali tace " Allah yasa hakan ne to amma.... ni tsoro...nake ji Yayah bana son in.......". Sai tayi shiru. Abbas ne ya 'karasa mata maganar da fa'din " bakya so ki rasa ni ko?" Murmushi tayi ta 6oye kanta a 'kirjinsa tare da tukuikuye hijab d'inta. Shima Abbas murmushin yayi A saman la66an sa ya furta " silly girl". sannan ya kai hannun sa ya sau'ke shi a bayan ta a kunne ya ra'da mata " babu abinda zai raba mu kinji, sai dai mutuwa insha Allahu". Shigowan likita ne yasa Teemah ta bar jikin sa ta zauna amma still kanta na jingine da gefen hannun sa tana wasa da hannayen ta, Doctor ha'kuri ya bawa Abbas na barin sa da yayi shi ka'dai inda Abbas yace dashi ba komai kar ya damu daganan suka 'dan fara ta6a hira da Doctor 'din sama-sama. Sunyi jiran a 'kalla 30mins kafin result ya fito, a hannun Doctor aka mi'ka result 'din wanda hakan yasa Abbas zuba masa idanu danjin me ke faruwa, Doctor kuwa yana saka idanun sa kan result 'din take sai fuskar sa ta fa'da'da da fara'a Abbas kam binsa da idanu kawai yake binsa wanda fara'ar data sau'ka kan fuskar tasa yasa Abbas 'kaguwa yaji sakamakon dake ciki. Tsaye likitan ya mi'ke tare da mi'kawa Abbas hannu, Abbas ma mi'kewan yayi sannan ya bashi hannun shima Doctor yana murmushi yace "Congratulations sir" Abbas bu'de idanu yayi a kansa shima da alamar tambaya tare da fatan Allah ya tabbatar masa da zaton sa. Juyawa yayi ya kallo Teemah da ke ta binsu da nata idanun ganin kalar game 'din da suke yi akan result 'din test 'din da akayi mata. Abinda dukkan su kunnuwan su ya jiyo musu shine ".......ur madam is pregnant...." Daga bakin likitan. Ba Abbas ba hatta Teemah sai da ta bu'de idanu a kansa tana sake kallon bakin sa daya furta hakan sannan ta dawo da kallon ta kan Abbas cike da mamaki, Abbas kam ido kawai ya waro a kansa da alamar wata tambayar Doctor sai ya lumshe idanu ya kuma bu'dewa alamar tabbatar masa da gaskiyar sa sannan ya 'dago 'dayan hannun sa ya mi'kawa Abbas papern result 'din ya kar6a ya duba. *Fateema Kabir* ya fara gani a sama daga shi sai *Positive* idanun sa ya 'kara sau'ka a kai bayan sunan ta dake saman. Kan sa ya 'daga ya kalli likitan yana murmushi duk da yanzu yagama tabbatar da hakan musamman daya tuno 'dan 'dagowa da cikin nata yai ga kuma motsin da ta ji wannan kadai ma ansawer ne amma duk da haka sai ya sake tambayar likitan cewa dagaske ne Fateemahn sa ne 'dauke da ciki? Tambayar bai yita dan neman amsa ba face tsaban farin cikin daya cika zuciyar sa. Bai jira jin amsar likitan ba ya juya inda take ya ha'da da Teemahn da papern duk ya rungume su yana juyi da ita yake fa'din " Zahra ta zaki haifi baby very soon, i'm going to be a father...." Teemah kam kukan farin ciki takeyi wai yau itace da ciki itama zata goyi babyn ta wanda za'a 'kira da suna nata. Abbas cigaba yayi da godewa mahalicci kawai a zuciyar sa da wannan babban kyauta da yayi masa, a fili kuwa banda mahaukatan kisses babu abinda yake aika mata. Doctor kam tuni ya fice daga office 'din ya basu wuri ganin yanda Abbas ya 'dimauce da jin labarin. A kunne ya ra'da mata " u ar carrying my baby, my little angel, little me ....Zahra am about to become a father...." Teemah kam kuka take yi da hawaye bata iya cewa komai ba kawai sai ta 'kara rungume shi a jikin ta ganin har ya fita farin ciki da jin tana 'dauke da ciki. Abbas raba ta da jikin sa yayi ya cupping face 'din ta da hannayen sa idanun sa cikin nata ya matso da kan sa dai-dai nata sannan yace " Zahra zaki haifa mana baby ko? ashe motsin babyn mu kike ji a cikin ki....baby ne ke yi miki hello a cikin ki" Teemah ma murmushi take yi hawaye na gangara mata. Hijab 'din ta Abbas ya fara 'dagewa yana fa'din " let me say hi to my little angel". Teemah da sauri tari'ke mai hannun sa tare da jijjiga masa kai tace " plz Yayah ba anan ba". Abbas na jin haka yace " to let's go to our house " yayi maganar tare da ri'ko hannun ta. Fita sukayi hannun ta ri'ke a cikin nashi yayin da result 'din ke ri'ke a 'dayan hannun ta. A hanya suka ha'du da doctor sai ya tsaya inda yayiwa Abbas bayanin idan suna so suyi scanning cikin dan sanin sex 'din baby zasu iya zuwa ranar monday, sannan akwai Anti-natal wanda ya kamata tafara zuwa in d next 3 days. Godiya sosai Abbas ya yi masa tare da 'daukan masa al'kawarin kyautar tukuici ta mussaman dan yanzu bai fito da komai ba, doctor kam cewa yayi bakomai ai aikin sa ne, daga nan suka rabu kowa da murmushi akan fuskar sa. Kallo 'daya zaka yi masa ka gane yanayin farin cikin da suke ciki, har ya 'dauki hanyar gida ya ma manta da cewar sunzo ne da mota Teemah ce ta tuna masa sannan suka koma wurin motar suka shiga yaja su zuwa gida. Suna shiga parlour Abbas ya janyo ta zuwa jikin sa ya cire hijab 'din dake kanta tare da shafo cikin nata har zuwa 'kasan marar ta yana sake jin tudun da cikin yayi. Gajiyan data ce masa tayi ne yasa yaja ta zuwa kan kujera mai zaman mutun biyu suka zauna sannan yaci gaba da shafa cikin a hankali ba tare da ya furta komai ba. Teemah kam murmushin jin da'di take yi tana tunanin wai yau itace da ciki itama zatayi babyn kanta. Abbas duk ya gama susucewa a wurin yana ta shafa cikin nata ji yake wani zazzafan 'kaunar abin da ke cikin nata na ratsa shi jijiya har 6argo da gangar jikin sa sai ya lumshe idanu kawai yayi shiru sai yanzu ne yake ganin wautar sa ji yake tamkar ya yi ta marin kansa na wautar da yayi, ace tsawon lokaci ya kasa gane cewa ajiyar sa na jikin ta, ya kasa gane gagarumar kyautar da Allah yayi masa ne ya canja ta ya kuma canza mata rayuwa gaba 'daya, ya sanya ta zama chop-chop, sam tunanin sa bai bashi hakan ba da farko. Duk kuwa da yasan cewa ba halin ta ba ne yawan cin abinci amma ya rasa mai yasa tunanin sa bai ta6a basa cewa zata 'dau ciki a wannan 'dan 'kan'kanin lokacin ba da auren su, shi bai ta6a kawo hakan ba, bai ma ta6a saka hakan a cikin tunanin sa ba ya rasa mai dauke hankalin sa da har ya kasa gane cewa cikin sa ne ya hana ta ganin period 'din ta ma gaba 'daya duk da kuwa alamomi da suka bayyana kansu amma shi sam tunanin sa da hankalin sa sai ya karakata izuwa wani abu daban, har ya tsaya yana yi mata ihun tana damunsa da neman abin da tasan bazai samu ba, da yasan hakane da ko da wasa ba zai ta6a yi mata masifa ba akai, daya san hakane da ko a ina abin yake zai je ya nemo mata shi da kansa, ashe bai sani ba already Allah yayi masa kyauta gagaruma sanyin idaniya mai sanya farin ciki a zu'kata, haushin kansa ma yake ji yanzun musamman daya sake tuna janta da yayi har zuwa katsina inda tun acan ya kamata ya gano hakan amma ya kasa ganewa, gaba 'daya sai ya tattara laifin komai ya aza shi a kansa yanajin kansa tamkar wani mai laifi. Kan fuskar ta ya dawo da hannun sa 'daya yana shafa lallausan fuskar ta da hannun sa a hankali suna kallon juna, yayin da ya kamo hannun ta a 'daya hannun sa in a slow but romantic voice yace " ki yafe min kinji, kiyafe min duk abubuwan da nayi miki a baya, ban ta6a tunanin ciki bane ke saki wasu abubuwan, ban ta6a kawo cewar zaki iya 'daukan ciki bane a wannan lokacin shiyasa ma hankalina sam bai ta6a zuwa wajen ba, Zahra inajin kamar nafi kowa laifi a duniya na yadda na kasa gane cewa Allah ya bani kyauta ta musamman 6oye a jikin ki, bansan mai zan fa'da ki gane ba amma plz ki yafe min kinji........." Bakin sa Teemah ta rufe da nata bakin, abinda bata ta6a yi masa da kanta ba kenan iya zaman su da shi. A hankali ta ringa kissing 'din shi slowly Abbas kam mutuwar zaune yayi yama kasa mai da mata martani tsabar yanda ta tafi da imani da tunanin sa, tsawon mintina uku kafin ta saki bakin nasa ta koma kallon idanun shi lumshe ido tayi sannan ta jijjiga masa kai. Abbas rungume ta yayi sosai a jikin sa take kuma ya k'ara cire ta ya kama kafa'dun ta tare da matso da fuskar sa saitin nata hancin su na gugan na juna ya furta " i luv u, i luv u Zahra with all my heart, i luv u my baby mama" Itama a hankali ta furta " i luv u more Yayah plz don't ever leave me" Abbas jiyake tamkar ya ha'diye ta dan so, jiyake duk duniya tamkar yafi kowa sa'a da samun ta a rayuwar sa, duk da irin shirmen ta amma dai-dai da rana 'daya bai ta6a jin son ta ya ragu masa ba ko kuma wani abu makamancin hakan, bai ta6a 'kosawa ko dama sanin kasancewa da ita ba, yau gashi zata haifa masa baby, jiyake babu abinda ya kai masa hakan farin ciki. Bai bata amsa ba sai kawai ya ha'de bakin su tare da kaiwa hannu ya bu'de zif 'din doguwar rigar dake jikin ta ya sa6ule zuwa 'kasa. Sai da ya gama rikitata da mahaukatan kisses masu zafi sannan ya gangara har zuwa wuyan ta yana 'ko'karin sau'kar da bakin sa zuwa 'kirjin ta ta 'dan saki kukan shagwa6a tare da furta " Yayah plz....." "Shhiiiiii" ya ce da ita tare da 'daukan ta zuwa cikin bedroom. ***** *Bayan kwana uku* Abbas da kansa ya raka ta Anti-natal a clinic 'din, inda anan ne aka gano cewa cikin nata har yakai tsawon wata hu'du da 'yan kwanaki akai. Wannan labarin har sai da ya zame masa tamkar shine karo na farko daya ta6a jin labari mai kyau na farin ciki a rayuwar sa, musamman da ya fahimci cewa cikin ya samu ne tun a farkon satin auren su sosai hakan ya faranta ransa, lallai babu wanda ya kai mahalicci iya kyauta ta farin ciki, in bashi ba waye zai iya yi maka irin wannan kyautar ace tsawon lokaci yana tare da abin farin ciki amma bai sani ba, ina ma, ina ma, jiyake tamkar abin ya koma baya ko dan ya nuna mata kulawar da har sai taji kanta tamkar tafi kowacce mace a duniyan nan, kulan da sai taji cewa sosai tayi sa'an samun miji mai son ta da kaunar ta, 'kaunar da shi kansa bai san da yaushe ya fara shi ba, tsintan kansa kawai yayi dumu-dumu cikin soyayyar ta tun ma kafin yasan miye so 'din shikan sa balle ita da a lokacin banda shirme da tsokana babu abinda ta iya. Yanzu kam yasan cewa 'kaunar su daga Allah ne, tunda gashi Allah da kansa ya adana masa ita duk kuwa da cewa ta auri wani miji amma sai ya killace masa komai nata ya kuma bashi ita a lokacin da baya zato batare da ya 'daga hankalin sa ba, 'karshe gashi yanzu ya azurta shi da samun kyautar d'a sukutum, ha'ki'ka Allah ne ka'dai abin bauta domin bashi da tamka koda wasa. Abbas bai damu yaji sex 'din babyn ba dan cewa yayi koma menene Allah ya bashi ya gode koma menene yana son abinshi, so ba shi da matsala da wannan Teemah ma bata 'daga hankalin ta ba tabi ra'ayin sa har suka gama suka dawo gida wani lokaci ita kanta tana mamaki yanda yake yi 'din tamkar wanda ya shekara ashirin da aure bai haihu ba, irin yanda yake treating 'din ta abin har yana 'daure mata kai, yanzu ne ta gane ashe son babyn da take yi nata shirme akan nasa, kawai ya 6oye a zuciyar sa ne tsakanin sa da Allahn sa, idan ta bayyana nata kuma ko ta nuna soyayyar ta ga wasu 'ya'yan sai yace da ita ta haifi nata mana sam a lokacin bata san cewa har da kansa yake wa baran babyn ba. She is totally speechless lokacin da yazo ya sanar da ita cewa ya kar6i hutu har na tsawon 2wks kawai dan ya kula da ita da baby, sosai ta girmama wannan soyayyar dan acewar sa sai yayi har da wanda suka wuce shi a baya da be yi ba ba. Murmushi kawai tayi masa sannan ta ce "Yayah ai rayuwa baya koma wa baya abinda ya wuce ya riga ya wuce kuma ma ai a rashin sani ne yasa har ya wuce 'din ba tare da mun lura ba so ba kawai sai mu godewa Allah ba daya bayyana mana a yanzu kuma muna cikin rayayyu duk kan mu" Abbas sai yace " Na sani Zahra nasan hakan kuma nagode wa Allah ina kan yi kuma har kullum, amma idan ba ba'kin ciki zaki min dan kar na bawa family na kulawa ba plz leave me, i'm just trying naga na yi dukkan duties 'din dake kaina" Murmushi tayi ka'dan tace "me yasa zanyi ba'kin ciki Yayah, kawai dai naga ne kamar hutun da ka kar6a 'din bashi da wani amfani" "Ke kike ganin haka ai, amma ni na san akwai amfani sosai" Yayi maganar yana cire rigar dake jikin sa. Tasowa tayi ta fara taya shi rage rage kayan, sannan ta budi baki da niyyar sake yin magana ya tare ta da fa'din " ya isa plz Zahra babu ruwan ki" Sannan ya matsa daga gabanta ya ja gefe yaci gaba da rage kayan sa, tamkar wani 'karamin yaro ya 'kara sa da fa'din " ke dama ai ba'a yi miki gwanin ta" 'Kasa-kasa yayi maganar amma da yake suna kusa da juna sai taji shi, sosai ya bata dariya amma sai ta gumtse ta dafe baki with smile on her face tace " Yayah ni d'in" 'Dan karamin tsaki yaja yace " Zahra let me be plz, i'm here 4 my baby tunda ke bakya bu'katata baki son ki ringa gani na kusa da ke i know my little me want to, so leave me alone plz" Yana gama maganar ya lumshe idanu. Shiru Teemah tayi kawai tana kallon sa ganin kamar ya d'an d'au zafi kan maganar sai taji babu da'di har a ranta. Ta kowa tayi a hankali zuwa inda yake ta kai Hannun ta cikin hannun rigar dake jikinsa da yake har yanzu yana kan 6alla bottles ne bai gama ba, a hankali ta tafara bin hannun a hankali tana masa tafiyar tsutsa tare da kwantar da kanta gefen kafad'ar sa sa tace "am really sorry Yayah i didn't mean to..." Abbas kasa jure fushin yayi shima yakai hannun sa kan cikin ta ya shafo cikin yace " Little me ur Mummy is so sturbborn na kusan in zane ta a gidan nan" Sosai yanda yayin ya sata dariya domin idan ka ganshi zakayi zaton ko dagaske da mutun yake maganar, amma bata yi dariyar ba sai tayi murmushi kawai tace " Yayah ai nace sorry ko? kuma in ka zane ni nima akan babyn zan rama". Itama tayi maganar cikin tsantsar shagwa6a, sai yanzun ya kalleta sai ta turo baki baki, he just knocked her head a hankali yana murmushi yace " silly mummy...kina ta6a min baby zaki biyani abuna right there" Murmushi tayi itama tare da sunkuyar da kanta 'kasa. Rigar ta Abbas ya fara 'dagewa kawai ba tare da shima ya sake magana ba. Teemah bata hana shi ba har ya cire rigar duka ya saura mata sauran bra kawai, hannu Abbas ya kai ya shafo boobs 'din ta dake cike fam cikin bra 'din kamar zasu fashe. Sai da ya kai hannu bayan ta kafin yace " ki daina saka wannan abin plz ke bakya jin yana damunki ne?" Shiru tayi masa kawai ta lafe a jikinsa, sai ya 6alle bra 'din daga bayan ta sannan ya dawo da hannun sa ta gaba da niyyan zarewa sai ta ri'ke mai hannun " Zaki fara ko?" Ya fa'da yana kallon cikin idanun ta sai ta 'dana baki gaba ta fara k'if-'kif da idanu. Share ta

Chapter 62 of 67