sa tace " Maman ka matsoraciya ce sosai gaskiya"
Tana murmushi ta 'dago ta kalli Abbas tace " da ba ka zo ba da bansan yanda zanyi da ita ba yau 'din nan"
Ta 'karashe maganar tare da 'dan sakin dariya.
Abbas sai yayi murmushin shima yace " Ummah ai ke kika 'kyale ta da zane ta kika yi tun farko da baza ma akai wannan matakin ba"
Murmushi sukayi dukkan su har Teemah da jin abinda ya fa'da 'din wai Ummah ta zane ta.
Daga lokacin kuwa bata sake jin fargaban bashi ba duk da zafin bai daina ba amma da sau'ki yana 'dan raguwa mata musamman idan ya sha.
Washe gari Anty ta iso, ba'ki dayawa daga 6angaren Ummah ma sunzo, kama daga kan 'kawayen ta da matan abokan Daddy har ma dana Abbas da wasu 'kawayen Hannah duk sun sukayi ta sam barka wa yaron, duk dacTeemah bata san kowa agarin ba in ya wuci Maman Nasreen amma duk da haka gidan baya ta6a rabo da jama'ah kullum, Mummy ce dai sai ana jibi suna kafin ta iso.
Jinjirin ma sai tayi sa'a bai fiya yin kuka ba sai dai idan yaji yunwa sannan shiyasa baya ma wuni a tare da ita.
Sau tari dan shayar dashi kawai ake kawo shi wurin ta inda tana gama bashi kuwa za'a kuma tafiya dashi.
Wani sa'in har ji take yi tamkar ta ri'ke abinta ta rungume shi a 'kirjin ta amma kunyar jama'ah yasa take basarwa, bata ma hakan aka ba kuma saboda tasan na'dan lokaci ne watarana ma su ka'dan su zasu yini batare da kowa ba.
Abbas kansa idan ya zauna yasa su a gaba banda godewa Allah babu abinda yakeyi musamman idan ya gansu wai ace iyalan sa ne su 'din familyn sa ne na kansa abin na matu'kar ratsa shi kalar yanayin farin cikin dayake tsintan kanshi aciki kuwa abin ba'a cewa komai.
Matan abokansa duk sunzo da mazajen su suka gaida Teemah wasun su tasan su yayin da wasun kuwa bata ta6a ganin su ba sanadin haihuwar ne ha'duwar su.
Maman Amal ma ta zo tun daga Lagos inda Teemah tayi matu'kar farin ciki, musamman da taga yanda baby Amal 'dinta ta 'kara girma tayi wayo tana gudun ta ko'ina.
Leesah ma babu ranar da gari zai waye bata zo gidan ba, wani zobe na gold ta siyo ta sawa yaron a hannu mai kyau da tsada itama kullum son Babyn na 'kara ratsa ta barin ma da taga ya na kama da baban sa ai shikenan idan tazo kuwa bata barin kowa ya ri'ke shi sai ita ka'dai.
Tun kafin ayi suna
ma Leesah tafara 'kiran sa da Annoor ta kuma ce sunan da za'a 'kirashi dashi kenan kenan.
Hannah kam bataso hakan ba dan ita da niyyar ta a k'irashi Irfan sai kuma Haleesah ta riga ta sanya masa suna dole badan taso ba ta ha'kura da nata sunan tana jin badan wani abu ba da Leesah bata isa ce zata saka wa jinjirin suna ba amma sai Hannah tayi mata kara ta bari saboda darajar abu 'daya.
Ranar suna yaro yaci sunan *Mahmud*, babu wanda bai mamakin sunan da Abbas ya sanyawa jinjirin ba, inda jama'ah da dama suka yaba masa tare da yaba irin karamcin daya yi, especially wa'danda suka ji abin a sama cewa kawai sunan marigayi mijin matar sa na baya ne, sai suke ganin kamar shi 'din halin sa daban ne dan bakowa zai iya irin hakan ba.
Wa'dan da kuwa suka san asalin zumuncin dake tsakani sai sam barka kawai suke yi, wannan dalilin kuwa ba 'karamin farin jini ya jawo wa babyn ba.
Anty kuwa har kuka tayi dan farin ciki take ta 'kira Abbah tayi masa albishir cewa an yiwa marigayi takwara, ta 'kira mahaifin ta ma ta gaya masa tana hawaye, shima Alhaji Muhammad albarka ya ta sanyawa Babyn masu yawa tare da yiwa mahaifin little Mahmud 'din fatan alkhairi mai d'orewa.
Irin 6arnar ku'din da Abbas yayi a wannan ranar abin ba'a cewa komai, dan wurin event 'din da akayi sunan idan kagani zaka saci ko wani 'kayataccen biki za'ayi a wurin, jakunkuna aka rin'ka rabawa mai 'dauke da turmin atampa mai kyan gaske, sannan ga wani jakan kuma shima mai photon baby shima ciki kayan ciye-ciye ne fal duk akayi ta rabawa mutane.
Duk wanda ya halacci taron sunan da farin ciki akan fuskarsa ya tafi domin kuwa ko ka'dan ba'a yi wani abu da zai sosa ran wani ko wata ba a wurin har taro ya watse.
Kyaututtuka kuwa da Teemah ta samu suma ba'a magana, cikin masu bada kyautar kuwa hadda Anty inda ta yiwa Baby da maman sa kaya masu yawan gaske kowa da nashi akwatin, Daddy ma ya aiko nashi kyautan da yake bai samu yazo ganin baby ba.
Ana kammala suna Abbas ya koma Rivers, haka ma su maman Amal da wasu mutanen na nesa duk kowa ya kama gaban sa suna masu farin cikin samun 'karuwar da Abbas 'din ya samu, inda aka bar Ummah da Anty har ma da Mummy suka cigaba da kulawa da mai jego har tsawon sati biyu sannan Anty ta koma Lagos da yake itama a halin yanzun abokiyar zaman ta nada tsohon ciki ne haihuwa yau ko gobe.
Mummy kam sai da ta kai 1month cif kafin ta koma Dubai, bayan tafiyar ta ne kuma Abbas yazo ya duba iyalan sa inda ya same su cikin 'koshin lafiya da kwanciyar hankali baby yayi 6ul-6ul a binshi, dan ma kullum sai sun tura masa photon shi a duk wankan da aka mishi su Hannah sai sunyi masa photo sun turawa Abbas wataran dukkan su sukeyi wataran kuwa Baby da mamar sa wataran kuma shi ka'dai.
Haka ma yana yawan 'kiran su video call a haska mishi babyn wataran ya ganshi yana bacci, wataran kuwa zai ganshi idanun sa biyu yana wasa da hannun sa abaki.
Abbas idan yaga hakan kuwa sai yace mata wato har yanzu tana masa rowan ko?"
Teemah sai tace " ah ah"
"Toh meyasa yake kai hannu baki?"
Ha'de goshi takeyi tace " Wasan shi fah kawai yake yi Yayah, kai dan baka ga yanda yake tsotseni bane shiyasa ai zaka ce wani ina masa rowa"
Sai cewa yayi " rama min yake yi ai kema kin tsotseni"
Teemah da sauri tace
" wallahi ba wani nan, to in dai haka ne ma bazan 'kara nuna maka shi ba"
Abbas ha'kuri ya bata yana dariya yace " to shikenan ya wuce, ni wasa nake miki maman Baby"
Lokacin da Abbas yazo ya gansu ba 'karamin farin ciki yayi ba har ji yake duk fa'din duniyan nan babu abinda ya kai masa farin ciki sama da su.
Wani kyau yaga Teemahn tayi masa da yake already Anty ta aiko an fara yi mata gyara ga haske datayi kamar ba mai jego ba, ko irin 'karnin nan da wasu masu jegon keyi sam bai ji a wurin ta ba illah 'kamshi daga ita har lil Mahmud 'din, da yake ma dama Teemah gwanar son 'kamshi ce kuma Anty tasa an kawo mata wasu ha'din su humra da sauran su masu bala'in 'kamshi shiyasa bata wasa da amfani dasu,
dayake kuwa bata wasa da kayan 'kamshi ciki da waje tana 'ko'karin kulawa sosai.
Aranar da yazo 'din kuwa Teemah da kayar ta sha, duk da tana yi masa tuni da cewa gidan Ummah ne ya bari fah kar tazo amma Abbas bai saurare ta ba yaci gaba da abinda yakeyi har sai daya gama rikita mata lissafi da salon wasannin sa cuz he really missed her a lot ji yake kamar ba zai sake iya 'daukan lokaci ba tare da ita ba, Teemah kuwa duk da ranta ba'a sake ba amma yanda yake sarrafatan yasa har ta fara 'daukan layi itama.
Kukan da Annur ya saka lokaci guda ne ya ceceta domin kuwa da sauri ta 'kwaci jikin ta tafi ta 'dauki 'danta ta rungume tana jijjiga shi.
Abbas kam tana barin jikin sa yayi baya ya kwanta tare da lumshe idanu a fili ya furta " Uwa! Uwa kenan!"
Wannan shine step na farko dake raba soyayyar mace ga mijinta domin matu'kar ta samu Baby to dole ne soyayyan babyn sai ya rinjayi na kowa ciki kuwa har da mijinta duk da dai baza'a ta bar son shi ta komawa danta ba amma na 'dan sai yayi rinjaye fiye da komai.
Abbas tashi yayi ya zauna yana kallon yanda take faman jijjiga shi da dukkan kulawa sai yaui mirmushi a hankali yace da ita " ki kaishi wurin Ummah mana please sai ki dawo "
Sai cewa tayi " ah ah Yayah barshi kawai ai zai yi shiru, Ummah ta gaji dayawa yau 'din duk a wurin ta ya wuni tun da rana"
"Hmm" kawai yace tare da 'ko'karin sau'kowa daga gadon, sai daya sau'ko da 'kafar sa 'kasa sannan yace " wato dai kince Annur ya fini ko?"
Da sauri ta furta " ah ah fa Yayah ai kaga d'azun kuka yake yi ne shiyasa"
Tana maganar tana tahowa inda yake ta zauna daga gefen sa tare da raba Annur 'din daga kafa'dar ta sai ta ri'ke shi a cinyar ta, Abbas ne ya 'dauke sa ya 'dagashi sama yana jijjiga shi yana murmushi, yaron ma kallon fuskarsa yake yi kamar an ce masa mahaifin sa ne.
Abbas yana murmushi yace " Ai dama na gaya miki, idan kin haihu nasan guduna zakiyi ki tattare duk ki komawa 'dan ki, kika 'ki yadda, ni kuwa nasan hakan dama sai ya faru gashi tun ba'aje ko'ina ba zance na ya tabbata gaskiya"
Murmushi tayi ta koma daga bayan sa ta rungume shi tare da fa'din " afuwan Yayah ba haka bane fa, banaso yayi kuka sosai ne har Ummah taji kuma tazo kaga da kunya sosai hakan ai"
Yana kallon babyn yace " to ni sai yaushe kenan za'a kulani... kin san fa gobe zan koma akwai aiki a gaba na, ko zamu je can 'daki na mu kwana?"
Kanta ta kawo gefen fuskar shi tace " da sauran lokaci fa Yayah,kuma ma ni gaskiya ina jin kunya ace daga zuwan ka har na bika 'dakin ka?"
'Dan b'ata rai Abbas yayi yace " bana son fi'ili ni, yau kika fara kwana acan 'din ne ko kuma yau ne kawai kunyar tazo miki?, ke 'din nan naga alama kin gama gaji dani ko? shikenan bakomai i know what to do kar ki damu"
Ya 'karashe maganar cikin basarwa kamar wani da gaske.
Ita kuwa jin yanayin da yayi maganar ne yasa ta sanyaya murya dan sai taji ba da'di cikin sanyin jiki tace " me zakayi Yayah?"
A tsare yace " amarya zanyi wacce bazata gaji dani ba"
Cike da firgici ta saki wuyan sa tare da juyawa ta koma ta jingina bayan ta da nashi tana kuka tace " an gaya maka ni 'din gajiya nayi da kai ne?"
Sai yace "ah to nima na sani ne? In kina son in yarda baki gaji dani ba then tashi mu tafi "
Kuka ta sanya mishi tana hahharba 'kafa tace " Ni dai kagaya min in kaine ka gaji dani...ai ni ban fa'da ba.
"Ban yi tunani akan hakan ba tukunna"
Ya fa'da cikin halin ko in kula.
Shiru tayi mata yi magana ba, sai ta cigaba da kukan ta, shi kam tashi yayi ya nufi 'kofa da babyn a hannun sa ba tare da ya sake kallon inda take ba.
Bai damu ba yasan ko badan bayn bama dole zata biyo shin idan ya tafi ko dan rigimar ta ma dan haka hankalinsa kwance ya fice a 'dakin.
Dan haushi ma ita yana fita sai ta ta shi kamar an tsikare ta ta shige bayi, bata san me ya kawo ta bayin ba dan haka sai ta watsa ruwa kawai ta fito, tana fitowa sai suka ci karo da Hannah da shigowan ta 'dakin kenan itama.
Kau da kai Teemah tayi tamkar Hannah ce tayi mata laifin sai ta nufi gaban mirror tana goge jikinta dake ji'ke da ruwa.
Hannah ta6e baki ganin bata ko kula ta ba itama bata damu ba dan tasan bazai wuci fushin Yayah bane take yi da har itama ta samu rabon ta.
Duba gadon Annur tayi bata ganshi ba haka ma nasu gadon ma baya kai wannan dalilin ne yasa ta juya ta kalli Teemah tace da ita " ina yaro na yake in mai gudnyt rabo na da shi tun da maghrib gashi bacci nake ji yanzun"
Teemah bata juyo ba ta bata amsa da fa'din " ki je ki kar6o shi a wurin Yayah"
Hannah sai cewa tayi
"Ta6'di ke de shirya ki kar6o shi ina jiranki kun fi kusa ai".
Shiru Teemah tayi ta cigaba da goge jikinta, bata shafa mai ba sai kawai ta 'dauki turaren humrar ta tabi jikinta da shi sannan ta nemi kayan bacci riga da dogon wando ta sanya dan ita tafi son irin su dama.
Tana gama shirin ta 'dauki hijab 'din ta babba ta sanya da silifas ta bar 'dakin ba tare da ko kallon inda Hannah take ta sake yi ba.
Zuwa lokacin kuwa tuni hankalin Hannah ya riga ya 'dauku ga wayar data keyi bama tasan lokacin da Teemah ta bar 'dakin ba.
A hankali ta tura 'kofar tare da yin sallama 'kasa-'kasa sai amsa mata shima ba tare da ya 'dago ya kalle ta ba fuskar sa na kan ta Annur yana yi mai wasa.
Shigowa tayi tare da tura 'kofan sai ta ja ta tsaya ta na kallon su, ita haushin ta 'daya warning 'din da Anty tayi mata akan sa, sam bata son ya wargaza mata gyaran da aka soma yi mata tun ba aje ko'ina ba dan ko itama tana so ta tsumu ba yanzu ta so ha'duwar su ba, amma ga dukkan alamu ba fahimtar ta zaiyi ba har da cewa wani amarya zaiyi.
Tsaki taja a ranta ta dan ta tsani wannan kalmar sam..
A hankali ta 'karasa inda yake ta tsaye nesa ka'dan dashi sannan tace " Yayah kawo shi mu tafi kaga dare na 'kara yi kuma Hannah ma na so ta ganshi "
Sai yace
"Ni kuma so nake mu kwana da shi ya za'ayi?"
Shiru tayi ta tura baki gaba tare da 'kura masa idanu, bata san yaushe Yayah ya koyi irin hakan ba bata san me ya canza shi ba dan Yayan ta data sani ada ha'kurarre ne akan komai, kallon kallo suka tsaya yi kiwa abinda ke ransa daban, shikam ransa fes babu komai illah so da 'kaunar ta bayaga haka babu komai, shine ya yanke shirun nasu da fa'din " Zo ki zauna ki bashi abincin sa naga yana shan yatsu"
Zaman tayi kamar yanda ya fa'da 'din ta mi'ka masa hannu akan ya bata babyn sai bai bata ba sai yayi mata nuni da hijab 'din dake kanta.
Ja tayi ta cire shi ta ajiye a gefe.
Abbas sai ya mi'ka mata Annur 'din sannan ya taya ta 6alla botiran saman rigar guda uku yace to ta bashi.
Shi kam zuba musu ido yayi yana kallon yanda babyn ke sha cikin nutsuwa, babban abinda yafi tafiya da imanin sa ajikin ta bai wuce boobs 'din ta ba, yanzun kuwa ganin yanda suka sake cika suka tsaya sai yake jinsa cikin wani yanayi, dan basuyi komai ba illah da 'da cika da sukayi sosai yake kewar su yake kuma jin son sarrafa su.
Har Annur yayi bacci Abbas na gefe yana kallon su, Teemah sai ta cire shi tana rufe bottles 'din ta Abbas ya 'dauke babyn cak ya kwantar da shi sannan ya rungumo ta ta baya tare da ri'ke hannun ta a hankali yace " saura ni ko".
Shiru tayi sai ya juyo da ita ta fuskance shi ya sake fa'din " aji dani nima"
Tana 'ko'karin yin magana ya 'dora yatsan shi saman la66an ta alamun tayi shiru dan yasan bai wuci complain zata yi ba, matso da fuskar sa yayi kusa da nata ya ha'de musu hanci suna jin 'dumin numfashin juna tare da sau'ke hannun san dake saman bakin nata ya jone bakin nasu wuri guda ya fara shan harshen ta, tsawon da'ki'ku kuma sai ya tsaya tamkar ya manta me yakeyi yayi jim, Teemah kuwa da ta ga haka sai ta cigaba da kissing 'din nashi kamar dama can ita ta fara.
Ita kanta tasan tayi kewar shi kawai dai bata son ta watsar da maganar Anty ne shiyasa take 'dan denying 'dinsa, kuma gashi tana jin nauyin Ummah bazata iya sakewa da shi a gidan ba.
Tana cikin tunanin sai taji hannun sa a cikin rigar ta yana mata tafiyar tsutsa har zuwa saman 'kirjin ta. Ajiyan zuciya kawai ta sau'ke duk dama bai fito fili ba amma yanda yaga yake samun response 'din ta ma sai bai yi tunanin kusantar ta ba ya tsaya a iya romance ne kawai ba komai da ya mata.
Inda ya 'dau tsawon lokaci yana juya ta son ran shi haka kuma itama dan sai da ta tabbatar tayi easing abinda ke damun sa kafin sukayi bacci manne da juna tuni ta manta da fushin amarya.
Hannah kam har ta gama waya tayi zaman jiran Teemah amma shiru har kusan 11pm kawai sai itama ta kwanta tayi baccin ta ganin basu da niyyan dawowa.
Da asussuba Teemah ko ta gudo daga 'dakin sa wai dan kar Ummah tazo ta ga basa nan.
Sallah ta samu Hannah nayi dan haka sai ta kwantar da Annur ta tafi bayi itama sai da tayi wanka kafin ta 'dauro alwala ta fito.
Da ta idar da sallar ne Hannah ta jefa mata tambayar
" Yayah ne ya ri'ke ku ko"
Da'din tambayar Teemah taji dama bata so Hannah taga kamar itace ta 'ki dawowa dan haka da wuri ta bata amsa da fa'din " ai wallahi kamar kinsani...Yayah cewa yayi wai shi sai da 'dan sa zai kwana, ni kuma wallahi kunyan Ummah nake ji kar ta gane a wurin sa muka kwana shiayasa ma kika ganni sassafen nan"
Hannah kuwa sai tace
" Hmm, kin makara ai Ummah da dare tazo duba Annur wai ko yau ma ya'ki yin bacci irin na jiya? sai nace mata ai kun tafi wurin Yayah"
Zaro idanu Teemah tayi tace " dan Allah Hannah dagaske?, na shiga uku ni kam yanzu ya zanyi duk fa laifin Yayah ne Allah"
Hannah murmushi tayi tace " Firgici haka sai kace dagaske bayan kinje kin 'din kuma miye abin damuwa?"
Teemah sai tace
"Ba zaki gane bane Hannah ke kam, ai da kunya irin wannan abin, ni dan Allah ki gaya min ya zanyi?"
Murmushi Hannah tayi yanzun ganin yanda duk Teemah tabi ta rikice sai tace da ita
"Wasa ni nake miki dan Allah ki nutsu, bata zo ba kuma yanzu kam ai bazata sani ba tunda kun dawo, amma shine kuma kuka barni na raba dare ina zaman jiran ku bayan kin san bazaku dawo ba...Allah naji haushi?"
Ajiyan zuciya Teemah ta sau'ke tare da fa'din
"Very sorry lil sis baza'a sake ba"
Ai ma baki san wani abu ba? Yaron nan in gaya miki yau ko damuna baiyi ba yayi ta baccin sa...."
Hannah sai tace
"Ah to yaga innar sa taje neman lada ba dole ya risina ba"
Fa'din Hannah tana murmushi.
Teemah sai tayi murmushi kawai batare da tayi magana ba.
Aranar kuwa Abbas ya koma kamar yanda ya fa'da mata, ita kam da fatan alkhairi ta bisa dan bazata iya ce ga takamamman yanayin data ke ji game da shi ba, fama take da zuciyar ta tana ta 'ko'karin 'karya ta kewar shin data ke ji 'karfi da yaji ta sanyawa ranta 'karfin hali da nuna halin ko in kula game da tafiyar sa tasa.
Teemah tun bayan sati da haihuwar ta tafara yin sallah, gyaran da ake yi matan kuwa ba 'karamin fitar da ita yayi ba, idan ka ganta tashin farko bazaka ta6a cewa itace ta haifi Annur ba, dan yanda tayi 'das abinta abin ba'a cewa komai.
Kullum matar take zuwa daga 10:00am zuwa 12:00pm tayi mata duk abinda zata yi ta tafi so gyaran bai wani takura ta ko shiga lokutan wasu al'amuran ta ba.
Shi da Abbas a nufin sa wai suna gama 40days 'din nasu zasu koma amma Ummah ta tayi babakere tace sam bata ji zancen ta haka ba sai sun 'kara hutawa.
Abbas har ransa ya 'dan 6aci da hakan amma sai ya 6oye bai nunawa Ummah ba, sai dai Teemah da suka ke6e da ita ya bayyana mata halin daya ke ciki inda ta matu'kar tausaya masa tana jin ba dan Ummah mahaifiya ba ce da babu abinda zai hana ta bin mijinta, domin ita kanta tasan yayi ha'kuri sosai sai dai bazata iya ja da batun Ummah ba dan haka kawai sai tai ta bashi baki har ya ha'kura ya koma Ports.
Wasa-wasa har sai da suka haura 2months da 'yan kwanaki kafin Ummah ta bashi matar sa, hakan ma sai data ga ya shiga wani yanayi kafin nan ta sallame su domin a wani zuwa da yayi ya ri'kewa Teemah wuta Annur nata faman ihu amma bai ko kula da hakan ba, Teemah ce ma hankalin ta ya kasu biyu amma shikam yayi nisa cikin son kasancewa da ita, k'aran bugun 'kofa ne yasa shi 'kyaleta ba wai dan yaso ba yayi saurin kintsawa tare da zuwa ya bu'de 'kofan, ganin Ummah yasa shi jin kunya take yayi 'kasa da kansa yabi ta gefen ta ya fice daga 'dakin batare da ya ha'da ido da ita ba, Ummah kam da kallo ta bishi cikin ranta tace " kaji kunya ai fitinanne kawai".
Duban ta ta mayar kan Teemah dake faman jijjiga Annur tana sussunne kai itama Ummah sai tace " ki bashi ko ruwa ma yasha zaiyi shiru"
Da kai Teemah ta amsa mata batare da ta 'dago kai ta kalli Ummahn ba.
"Hmm"
Kawai Ummah tace a zuciyar ta kana tayi waje da tunanin yanda Fateemahn zata iya kulawa da iyalan ta Annur dacwannan fitinannen ita ka'dai, ita Ummah tausayin tane yasa ta kasa barin ta koma masa har yanzu, dan gani take Teemahn bazata iya kulawa da babyn ita ka'dai ba, a hakan ma cikin kwanakin nan tana barin ta tana yiwa Babyn abubuwa da kanta wai dan ta koya ta saba kama daga kan wanka, shirya shi, goyo rarrashin sa idan yana kuka harma da canza masa pampers duk ita ke yi da kanta, Alhamdulillah kuwa ba laifi tana 'ko'kari sosai dan haka washe gari Ummah ta sallame su suka koma gidan su, da yake ma already ya kammala ginin sa dan haka babu 6ata lokaci suka dira a can.
Sosai tsarin gidan ya bambanta da gidansu na farko dan wannan mansion ne guda ga kyau ga girma, kallo 'daya zaka yi masa ka tabbatar yaci ku'di na gaban kwatance.
Sosai gidan ya birge Teemah, ga 'dakuna wadatattu wanda mutane kusan goma ko ma sama da haka zasu iya rayuwa aciki batare da wani ya takura 'dan uwan sa ba.
A ranar kuwa Teemah har sai data gane ashe dama shayi da zallar ruwa ake yinsa, sosai ta daku a wurin sa ta sha uwar wuya dan kac-kaca yayi mata, 'dinkin da akayi mata ne ha'de da gyaran da tasha sai ya suka ha'du suka matse ta.
Shi kam Abbas baya jin gari sai yi yake yana 'karawa har da bashin sa na baya sai da yayi, shikan sa yayi mamakin yanayin daya same ta domin bai yi zaton haka ba duba da haihuwa da tayi amma sai ya same ta ba yanda ya zata ba hakan ne kuwa ya kusan zautar dashi.
Sai da komai ya lafa bayan har sunyi wanka ma sun koma sun kwanta dayake abin na ransa sai bai yi 'kauron baki ba hannun sa cikin gashin ta a hankali yace da ita " ban fa gane ba wai dama haka ake sake canzawa idan an haihu, gaskiya in dai haka ne next year ma zaki 'kara haifa min little princess 'di ta, kinji yanda kika koma kuwa har nayi zaton ma ai ko da amarya ta nake tare fa?"
Ya 'karashe maganar da murmushin tsokana.
Teemah kam bata 'dago ba sai hannu da ta kai ta kamo kunnan sa taja da 'karfi sai ya ce " awshhh zaki ciremin kunnn fa?"
'Dan sassautawa tayi tare da fa'din "can't u see yanda ka ci zalina ko ?"
Abbas sai yace
" Sorry babe ba laifina bane ai duk laifin kine da kika rikitani...ban ma gaji ba fa na barki ne ki 'dan huta kawai kafin nan".
Cikin shagwa6a tace " ni
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 64 Chapter of 67