Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
toh haka akeyineh ke,? "Gaye ya dage yaga 'yan mata sai kuma kika kwafsa bai san dama da 'yar k'auye ya had'u ba." Turo baki Teemah tayi gaba tace " nice y'ar k'auyen ko yayah" . Shiru yayi yana gumtse dariya batare daya kalle ta ba. Kasa hak'uri tayi sai da ta k'ara cewa " abinda ma naa fishi kyau" Dariya ne sosai yakama Mahmud Teemah kuwa sai ta kauda kanta gefe kamar zatayi kuka ta tsani wannan dariyar har ranta sai da yagama dariyar sannan yace " sorry lil sis wasa nake miki ai shine babban d'an k'auyen ma ". Ko kulashi k'inyi tak'ara yi har suka koma gida sai da mummy tasa baki kafin suka shirya. _Comment, vote and_ _share pls_ 🀞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:59 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ⚠ *NOT EDITED* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Just because you have experienced pain doesn’t mean you won’t feel happiness again. πŸ…Ώ *32* Shak'uwa ce sosai tsakanin Mahmud da Teemah fiyeh da zaton me karatu, sai dai compared to shak'uwar dake tsakaninsu ayanzu toh wancen nabayan ba komai bane. Tun da Mahmud ya tattaro yadawo gida shikenan Teemah tasamu d'an uwa, aboki kuma yayah, batada da matsala ta kowani fanni, sosai Mahmud yayi k'ok'ari wajen ganin ya gina zumunchi mai k'arfi a tsakaninsu and he win. Yakan 6ata lokacinsa sosai wajen ganin yah koya mata karatu musamman dayaji labarin zata zana weac ashekaran, sosai shima yaji dad'in wannan labarin dan Teemahn kam masha Allah akwaita da saurin girma. Haka idan suka fita yawo sukan 6ata lokaci sosai suna zaga gari, dan Mahmud ma ba de son yawo ba sai akayi sa'a kuma itama Teemahn gwanar son yawo ce shiyasa bakinsu yake yawan zama d'aya dashi. Ko sabon saurayi Teemah tayi ko kuma irin wani ya nemi yin magana da ita d'innan toh tare suke raina musu hankali da Mahmud d'in. Wani lokaci idan ya tsare ya 6atarai yana masifah har zakayi rantsuwa akan ehh lallai akan gaskiyarsa yake masifahn nan kuwa duk yanayin hakan ne saboda Teemah tu,da ya lura batason hakan shima sai ya biyeta. Axuk lokacin saza'a mata magana toh nuna sukeyi kamar wai ai they are already married, ma'ana matarsa ce, wani idan yaji hakan sai yabshi hak'uri yawuche abinsa, wani ko k'in yadda yakeyi da hakan sai ya k'aryatasu tare da k'ara dagewa akan shifah lallai sonta yakeyi kuma da aure. Idan kaga Mahmud na masifah wa saurayi akan Teemah toh baya rasa nasaba da k'in yadda da saurayin yayi akan cewa Teemahn matarsa ce. Haka zai dage yayi ta bud'e ido yana masifah Teemah kuwa sometimes dariyah ma yake bata amma bazatayi dariyar ba dan kar agano su. Sai idan su, ke6e ko kuma su shiga mota sannan sai tafara dariyah tana kwatanta masa yadda yayi alokacin dayake masifan, shima tayata dariyar yakeyi suyi tayi dayake suda kansu sunsan abin dariyar sukeyi. Akwai ranar da wani yabiyo bayansu har k'ofar shiga gida, da Mahmud yaga kamar binsu akeyi sai yayi parking shima atare suka fito da me binsu d'in sai kowa ya tunkari d'an uwansa da mabanbantan manufah. Mahmud shi damuwarsa yaji dalilin binsun dayakeyi yayin da d'ayan kuma yake burin son magantuwa da yarinyar daya gani d'azu tashiga motar. Fitowan da Teemah tayi ne ya d'auke hankalin mutumin daga kallon Mahmud ya mayar dashi kan Teemahn, ya wani k'ura mata idanu kamar zai cinyeta d'anyah. Lura da inda mutumin ya kai duba da hankalinsan da Mahmud yayi ne yasashi fahimtar manufan binsun dayatayi har zuwa gida. Sun had'u da mutumin amma sam hankalinsa yatafi wani wuri be ma san sun had'un ba may be shi de ya tsaya da tafiyar daya keyi. Ahankali Mahmud yajuya ya kalli inda mutumin yasa hankalinsa sai suka yi four eyes da ita. Da saurinta ta k'araso inda uake ta rink'e masa hannu da dukka hannayenta biyu yayinda take k'ok'arin 6oye fuskarta da rigar dake jikinsa. Dukkansu sai suka tsaya kallonta ganin tana k'ok'arin 6oye fuska ne yasa Mahmud d'ago idanu ya kalli mutumin dai dai shima ya kallo Mahmud d'in suna had'a ido dai Mahmud ya d'age masa gira alamar tambaya. Sannan yah furta " hakalinka ya kwanta ko? " Kana ganin yanda ka tsoratar min da 'yar uwa, meke faruwa ne? In ina mutumin yafara yanaso yayi magana amma yanda Mahmud d'i. Yayi masa magana sai yasa shi fargaban abinda yakeso ya furta d'in. " Dakatar dashi Mahmud yayi tare da d'agamasa hannu " go straight to the point mr. man don't waste my time here". Haka de mutumin ya daure ua furta abinda ke cikin ransa nan kuwa Mahmud yafara masa bori kamar zai ari baki. " can't you see that she is married?, how dare you said you love her? Karkata kai yayi tare da rik'e kunkuminsa sanna, yace " owhh wato kune irin mutanen nan masu lalata tarbiyar al'ummah ko? Mutumin najin hakan ya rik'e baki tare da saurin bawa Mahmud hak'uri, yace shi bahaka bane manufarsa, kuma be masan da aurenta da bazai ma fara binsu ba balle har yayi musu magana, hak'uri sosai yayita bawa Mahmud kafin yajuya yakoma cikin motarsa yaja yayi gaba. Har yaja moitar tasa Mahmud natsaye ayanda yake yana binsa da idanu sai da ya daina hango motar kafin ya juya kad'an ya kalli gefensa inda Teemah ta k'ank'ameshi yace "ke sakeni" Ahankali tad'ago kanta dataga mutumin bayanan kafin ta sakeshi gaba d'aya. Cemata yayi " miye hakan wai kikeyi naga harda su 6uya? " wallaho yayah tsoro yabani ni yafiyeh kallo dayawa" " Daga kallon kuma fah? tace " shikenan" "Hmm,Toh ke nakasa ganewa haka zaki tazama ba saurayi ne? naji fah daddy na cewa aurar dake zaiyi daga kin k'are secondary school ke kuma sai sani kike ina ta kore in- laws d'in nawa." Dariya kad'an tayi tace" kai yayah harda wani in-laws? " ehh mana,musammam ma wannan duk yafi birgeni wallahi da alama zai so ki da gaskiyah gashi ba laifi harya d'an fiki ma kyau ya k'arasa da zolaya. " haba yayah ahakan nidai wallahi be fini kyau ba..... , " toh naji yah isa wasa nake miki ai daman ki, fishi kyau waneshi ya kamo lil d'ina kyau." " amma ai de shid'in yah miki ko" Dawuri ta jijjiga kanta tare da 6ata rai tana tura baki. " mekenan" ya tambayeta " nidai banaso..... "Sauran fah toh ? Yasake tambayarta amsa shi tayi da fad'in " dukkansu"! Ido yah zaro waje yace " babu wanda ya miki? kai ta d'aga alamar "ehh" " ta6 lalle kam". Haka kawai yace tare da jajjiga kansa alamar mamaki sannan yasake kallonta "ki shiga gida barin shigo da motar sai mu k'arasa maganar agida ko? " uhm tace tare da juyawa ta tura k'aramar 'kafar dake jikin gate d'in gidan tashiga ciki. Shima sai yaje ga motar ya tayar tare da danna horn take kua axka bud'e gate d'in yatura motar yashiga yanayin parking yafito yasameta a inda take tsayuwan jiransa. " muje " Yace mata atak'aice tare da nufar k'ofar dazata sada su da babban parlourn gidan. Baifi taku uku yayi ba yaji yo muryarta ta k'ira sunashi a hankali. Tsayawa yayi tare da waiwayowa ya kallota " ya akayi" ya jefa mata tambayar agajarce " fishi kayi danine yayah? yanajin abinda ta fad'a ya juya yafara tafiyarsa sannan yace " ba dole nayi fushi ba, lil sis k'arfi da yaji kin maida ni babban mak'aryaci a gidannan." Daga yadda yayi magana ta fahimci babu wani fushin dayakeyi da ita kawai dai ......... Garin saurin ta taroshi sai k'afanta d'aya yad'an karkace aciki. High hill d'in dake k'afar tata bata ji ciwo, komai ba amma sai tace wash tare da rage tsawo ta kama k'afar kaman dagaske ciwon taji. Aikuwa dawuri Mahmud yadawo yana tambayarta " menene ya faru? " yar k'auye kawai yanzu dan wannan takalmin ne shine harda fad'uwa? Abinda yace kenan bayan ya fahimci dalilin wash da kuma durkuson nata . Hannunta yakama ya mik'ar da it tsaye,sannan yace cire takalman ki rik'e ahannunki tunda mun iso gida, bazanma k'ara siya miki irinsu ba tunda kin kasa iyah koyan tafiya dasu har yanzu." Gaba tayi tafara tafiya tabarshi agun sannan tace " ni ba abinda yasameni dama so nake ka jirani". " kut lalle Yarinyar nan" yace tare da mik'a hannu kamar zai kamota ita kuwa sai ta kwasa da gudu tayi ciki shima sai ya bi ta abaya. Mummy na zane kawai taga mutun tazo kanta da gudu ta ruk'unk'umeta kafin tana k'ok'ari, yin magana kawai sai ga Mahmud ma yashigo kamar yanda Teemahn ta shigo. Salati mummy tasake tare da fad'in " wai meke damunku ne wai? Haka ne sallamar ? " kyaleta mummy Allah yarinyar nan tarena ni sosai." tana daga jikin mummyn tafara fad'in " bawani mummy niban raina shiba kawai dan na........ Kafin taka'arasa mummy ta buge mata baki " kubb" yimiin shiru ni". Sosai taji zafin hakan aikuwa take idanta yai jah kamar zatayi kuka Mahmud kwa mezeyi inba dariyah ba, haka yatashi yafice ad'akin da sauri yana kwasar dariyah. Teemah kuwa gefe tayi tayi zugum tarsa meke mata dad'i. Sai da ta daina jin zafin kafin ta tashi ta wuche d'akinta. Tana shiga tamik'e agadonta tana shan iska bayan ta rarrage kayan jikinta. Waya taji na vibrating ad'akin nata gaba d'aya sai tarasa takamamman inda k'arar ke fitowa har k'iran ya yanke bata samu inda wayar take, vibration d'in ne yasake tashi akaro na biyu kuma sai asannan ta tuna wayar Mahmud dake cikin jakar ta wanda tafita dashi d'azun. Ai da gudu ta tashi taje ga jakar taciro wayar "AUNTY" tagani arubuce akan fuskar wayar, k'iran na gab da yankewa tayi recieving " hello" tace ahankali. Dan tunda ta fahimci me k'iran sai taji gabanta ya fad'i shiyasa ma ta amsa asanyayeh. " shiru taji ta d'ayan 6angaren hakan yasa ta k'ara furta "hello.....d'in akaro biyu tana shirin yin na uku ne taji an amsa mata da " keh dan ubanki kyaleni ni!" " ina mai wayar" " asanyayeh ta amsa mata da " kiyi hak'uri Anty bari in kai masa." " 'duut" Taji wayar ya yanke sai ta dafe k'irji da hannunta d'aya saboda yanda taji bugun zuciyarta na k'aruwa komawa tayi ta kwanta rigingine tana ayyah na hali irin na wannan matar data rasa dalilin tsanar datake yimusu wanda tun ba yau ba ta fahimci hakan. Ahankali tatashi dan ta kaiwa Mahmud wayar sa, cikin sa'a kuwa sai suka had'u da Mahmud d'in yazo ansan wayartasa. Mik'a masa tayi kawai tajuya ciki shikuwa sam be damu ba saboda azatonsa tun fushin d'azu nake bata sauk'o ba. Haka yajuya yayi tafiyarsa zuwa d'akinsa,yana shiga d'akin kuwa yana shirin ajiye wayar sai yaga Anty ta k'irasa. D'auka yayi tare da zama akan side drawer yayi receiving called d'in. " Assalamu Alai..... .... Kafin yak'arasa sallamar sai yaji tace " wacce 'yar iska kabawa wayarka Mahmud? " kai Anty 'yar iska kuma?, " Teemah ce fah,yarinyar Anty....?? " shine ne me? Shiru yayi be sake yin wata magana ba sai itace tacigaba da fad'in " yaushe zaka dawo gida? " ni kam babu rana gaskiya " yafad'i akufule. Itama dataji haushi sai ta fara yi masa masifah akan babu ranar dayace. Wai saboda me ze ce haka, tsabar ya raina ta har tana tambayarsa ranar dawowarsa ko kunya wai baya ji zaice mata barana dan yaje ya tare agurin waccan munafukar, umarni tabashi akan cewa nan da 1week take buk'atan ganinsa a lagos koma ya zeyi ya neni hanya yazo tana buk'atan ganinsa. Cire wayar yayi daga kunnansa kafin yakashe ta gaba d'aya ma ak'asan mak'oshi yake fad'in "baza'a zo bad'in". Mahmud be sanar da kowa yanda sukayi da mahaifiyarsa ba daga mummy har daddy babu wanda yake da labarin domin yadda ya yanke aransan cewa bazashi ba toh sam bai da niytar zuwan ne shiyasa yak'i sanar da kowa dan yasan mummy najin labarin zatayi convincing d'insa akan lalle sai yaje. Hatta Teemah ma bata sani ba. Amma yadda Antyn ke yawan tuntu6arsa awaya akan tafiyar kad'ai yasa mummy fahimtar wani abu game da shi. Dan ayanda ta lura duk sanda zai d'aga wayar indai na mahaifiyarsace tana lura da canjin fuska atattare da shi matuk'ar akusa da ita yake. Kuma ko minti nawa zai kai da wayar akunnansa bazaka ta6a jin yayi magana ba shiru kawai yakeyi yana sauraronta. Hkana kad'ai dayakeyi babbar alama ce dake nuni da wata matsalar azahiri. A kwana na biyar ne ta zaunara dashi ta tambayeshi abinda ke faruwa domin walwalarsa gaba d'aya tayi low. Aranar kama be 6oye mata ba haka ya zayyano mata duk yadda sukayi da Antyn tasa a tunaninsa ko Mummyn zata bashi shawaran da zata taimake sa. Ai kuwa mummyn fad'a tayi masa sosai itama har kamar zata yi kuka, take fad'in me yasa zai yi haka, ai koma me Antyn ta buk'aci ya mata kamata yayi ya mata batare da musu ba kodan darajar ta na uwa agare shi. Tace akan me zai 6oye yak'i yin bayani bayan yasan koma miye zai faru ko yafaru toh kanta abin zai koma tunda ahalin yanzun tare yake da ita. Koma badan hakan ba tace " mahmud mahaifiyar ka ce fah ai tafi k'arfin hakan, tafi k'arfin tace kayi abu kuma kak'i yinsa matuk'ar bai bar kan hanya ba toh dole ne kayishi koda kuwa ranka bayaso." Hak'uri sosai yabawa mummy tare da fad'in shi abinda Antyn keyi ne yafara isansa shi yasa yak'i zuwa amma insha Allahu zai shirya yaje shi d'in kamar yadda ta buk'ata." " Murmushi ne ya kwace wa mummyn take kuwa tasanya masa albarka tare da yi masa addu'a da fata mai kyau daga indallahi kana ta sallameshi dan yaje yafara shirin tafiya acewar ta gobe take so yawuche. Haka Mahmud wannan karon ma ya shirya yatafi bada son ransa ba wani lokaci ji yake kamar yakai k'aranta wurin Abbansa dan yadda take takurawa rayuwarsa amma idan ya tuna cewa aikin banza zaiyi sai kawai yafasa dan ko da yafad'a d'in toh kamar yakai kukansa ne inda bazai samu biyan buk'ata ba koda kuwa kad'an, .ai san dalili ba amma shi wani lokaci ji yake kamar yana jin haushin iyayen nasa musamman Abbansa da sam baya fighting masa komai sai dai ya zuba masa idanu ko ya k'yale sa sai de inshi yana so ya yunk'ura, shi yasa yafi son zama awurin Antynsa Khadija shi aganinsa acan yafi walwala idan yana can sam baya jin cewa yana da matsalar komai. ***** Lafiya lau ya sauk'a ,koda ya sauk'an kuwa be k'ira kowa yasanar da sauk'an tasa ba aidansu, wani friend d'insa yak'ira yazo ya d'auke shi yakawo shi gida, be ma shiga ba yajuya yakoma saboda akwai uzuri agabansa godiya kawai Mahmud yamasa sannan shima ya shiga gida. Ahankali yake tafiyar tamkar bazaiyi ba hannunsa babu komai sai agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, gefen kafad'arsa kuma 'yar jakar da yake saka kayansan da zai bukata inzaiyi tafiyane. Haka ahankali har yak'araso k'ofar parlournsa, key hondern dake tare dashi yaciro ya lalu6i makullin da zai bud'e masa d'akin yasaka ya bud'e yashiga ciki. Sake tura k'ofan yayi ya rufe abinsa tankar ma ba'a bud'e ba. D'akin ma ashare tsab bawani datti dayake duk bayan kwana biyu Anty take sawa a share masa koda ma bayanan so bashi da matsala da wannan, kawai sai ya ajiye jakar kayansa tare da rage kayan dake jikinsa. Bayi ya shiga ya watso ruwa tare da d'auro alwala yazo ya tada sallah ya rama wanda yawuche shi tare da sallatar wanda tagabato adai dai lokacin. Yana idarwa ya d'auki wayarsa ya k'ira mummy ya sanar da ita isowanshin lafiya harma suka d'anyi hira da Teemah kad'an basu wani d'au lokaci ba yace mata bacci yakeji he need to rest, sallama tayi masa tace idan yatashi yak'ira zata bashi wani labari, " toh kawai yace mata atakaice dan yasan babu wani larin da zata bashi k'aryace kawai da kuma son yak'iratan datakeyi. daganan ya kwantaa bayan ya maida wayar a silent da niyyar kishingid'a, kamar wasa kuwa sai bacci ya d'auke shi suka tafi.😜 Antynsa bata san ya iso ba, kuma duk k'iran data ta yi masa aranar ko guda d'aya bai d'auka ba hakan kuwa bak'aramin 6ata ranta yayi ba amma sai ta kyaleshi da niyyar duk lokacin data sameshi awaya sai taji dalilin hakan inma zigashi ake yi yamata rashin kunya toh duk zataji. Bashi ya tashi ba sai da aka k'ira sallar maghrib,koda yatashi alokacinma sai yaji gaba d'aya kansa yamasa nauyi,hakan ya sa yad'an 6ata lokaci abayi yana cikin ruwa da kyar yasamu yafitoh. Sallar maghrib d'in yagabatar tare da zaman jiran lokacin isha'i yacika itama ya gabatar da ita, baya son yaje masallaci su had'u da Abbansa ne shiyasa baije ba amma da farko harya yi niyyan zuwa sai fasa. K'arfe takwas da rabi daidai tayi masa ne ak'ofar babban parlourn Anty. Hannu yasa yatura ahankali tare da yin sallama ciki ciki. Suna can wajen cin abinci dan haka basu ji sallamar tasa ba amma sunji k'arar k'ofan. Jin k'arar dasukayi yin ne yasa suka maida hankulansu wajen k'ofar shiru sukaji babualamun mutun kuma domin daya shigo tsayuwansa yayi awuri d'aya shiyasa basu kuma jin motsinsa ba. "Waye ne? Abbah ya tambaya batare da ya mik'e ba. Ahankali yah amsa da " nii neh" kamar dole aka saka shi. Suna jin muryarsa suka mi'ke atare suka nufo shi tare da ambatar "MAHMUD" alokaci guda. " Mahmud kani da daren nan? Abbansa ya tambaya cikin mamaki. Kai ya d'agawa Abban alamar ehh Hannunsa yakamo suka koma gurin cin abincin dukkansu nan take Anty ta had'a nasa nasa plate d'in ta tura masa shima. Dayake daman yunwa yakeji sai be wani yi yanga ko gardama ba ya bud'e ciki ya kwashi abincinsa sai da suka gama kafin Abbansa ya tambayeshi meyasa yayi tafiyar dare? " bayanzu na zo ba Abbah" Yabawa Abban nashi amsa . Ido Abban ya ware "bayanzu babana tun yaushe kazo? " Tun da rana". Salati Anty tasaka takama baki sanna tace " yanzu Mahmud tun da rana ka iso amma kak'i zuwa inda muke sai yanzu". Abbane ya d'aga mata hannu yana murmushi yace " pls barshi Maryam may be yagaji ne shiyasa...... " amma me yasa bazai ko sanar akan yana hanya ba..... Anty ne tasake fad'in hakan. Abbah kuwa cewa yayi wannan tsakaninku amma dai kibarshi kwa gama dasafe idan Allah yah tashemu lafiya". Juyawa yayi ya kalli Mahmud yace " abana jeka huta sai da safe koh". Mahmud da tun d'azu yake zaune kamar mutum mutumi kallon Abban sa yakeyi da mamaki, domin yajima baiga Abbansa na irin hakan acikin gidansa ba, sai yau yaga Abbansa na dakatar da Anty akan abu kuma tayishi, sosai hakan yasashi mamaki matuk'a, shiyasa be ma ji abinda Abban ya fad'a da farko ba sai da Abban yasake maimaitawa kafin ya yi firgigi. be san cewa addu'ar da mummy keyi akullum bane yafara tasiri akan Abban. " meke faruwa ne ? Aban ya tambayeshi. "Ahh bakomai Abbah " " toh maza jeka kwanta sai da safe" Tashi yayi tare da sake yi musu sallama ya wuche abinsa. Anty kuwa abin ne yafara yimata yawa domin ga matsalar Mahmud daya d'an d'au lokaci aranta tana tunani ta yadda zai yadda da batun auran Munirat, sai rana tsaka kuma matsalar Abbah ta kunno kanta kusan sati kenan tarasa gane kansa, gashi duk tarasa dalilin hakan. Koda tayiwa Anty chideh magana kuma sai ta rink'a yi mata yanga kamar ma bata son zuwa. Itakuma vagane gurin zatayi ba yanzu kuma bata son canja wa tagi son wancan wurin d'in dasuka yi mata aikin tun farko dan sosai ta yadda da aikin nasu. Washe gari daya zo gaida iyayen nasa sai yace wa Antyn yanso me yakoma dawuri domin akwai aikin dake jiransa acan idan wani abu take so ya mata tafad'a dawuri sai yagama mata shi ayau dan yanaso yakaoma" Antyn kamar bazata fad'a ba dan tsoron abinda zai biyo baya kar kuma tak'i fad'a yace yau yake son komawa tunda babu abinda zai mata, sam bahaka taso ba , taso su ka6e su biyu sannan suyi maganan musamman ma dayanzu yadda yakasance Abbansa na yawan yi mata katsalandan a abu shiyasa take tsoron fad'in abinda ke ranta a gaban idanunsa. Tunanin hakan yasata ta bud'i baki badan ranta yaso ba anan ta yada manufarta nasawa datayi yazo d'in. Haushi Mahmud yaji sosai bayan yaji bayanan Antyn. Dayake cewa tayi yakamata ya tsaida matar da sai aura kodan gudun lalacewar da duniya take ciki dan hakneta mtsa akan yazo gida domin su tsaida magana wuri d'aya. Haushinsa d'aya ne dayaji wai duk wannan masifan data tayi masa d'in wai akan batun aure ne toh ni wama zan aura ? Ya tambayi zuciyarsa. Azahiri kuma murmushi yamata kana yace " kwantar da hankalinki Anty, nibama yanzu na shirya yin aure ba gaskiya, shiyasa ma har yanzu banda kowa da muka yi batun aure da ita kinga kuwa ai da sauran lokaci" Abbah ido kawai ya zubawa wayarsa tamkar baya jinsu amma kuma gaba d'ayan hankalinsu da kunnuwansa na gare su ne. Anty ne h tasake fad'in cewa " ai karka damu Akwai wata 'yar k'awata.......... sai tadakata ta kallo Abban Mahmud d'in.... " mahmud aransa yace dama nasani ai" yayinda afili kuwa kallonta yakeyi kamar wanda tana fad'an maganar zai amince. Gani tayi Abban Mahmud d'in sam hankalinsa baya tare da su sai tayi hamdala azuciyarta. Daganan taci gaba da fad'in...... " yarinyar nada hankali Mahmud shiyasa nayi sha'awan kai ka aureta nasan baza'a samu matsala daga gareta ba bansan dai kai ba" Takarashe maganan da yanayin tausayi. Shi kanshi sai yaji tausayinta amatsayinta na uwa mahaifiya agareshi, idan har tana ganin bata da matsala da yarinyar toh why not shi data haifa kuma? Batare da wani 6ata lokaci ba take yace mata gobe yake so ya koma amma insha Allahu kafin ya tafin zaije yaga yarinyar inyaso sai yabar komai ahannunsu. Farin cikin da Anty taji tamkar ta goya shi haka taji kawai sai fara yi masa godiyah kamar wanda yamata kyautan wani abu. Sai asannan kuma Abbah yayi magana inda yace " ga dukkan alamu yarinyar tatafi da hanakalinki gaba d'aya ko? Murmushi tayi amma bata yi wata magana ba dan karta 6ata plan d'inta tunda tasamu ya amince ai shikenan. Da yamman ranan Anty ta had'a Mahmud da drivernta dayake ahi yasan gidan sai ta masa bayanin abinda zai kaisu gidan atsanake. Fita yayi bayan sun isa ya bar Mahmud d'in zaune acikin mota shikuma yaje yayiwa Mai gadin gidan bayani take kuwa yawuce ciki yah isar da sak'on da aka bashi. Minti goma mai kyau bata cika sai ga Munira tafito cikin shirinta na k'asaitacciya awurin iyayenta. Riga tasa iya gwiwanta yakuwa yi mata kyau sai dai rigarasosai yakama mata jiki dayake roba ce da dogon wando daga ciki kanta kuma wani d'an k'aramin veil me tayane kanata dashi, tana tafiya tana karairaya dayakr dama tasan da zuwansa mahaifiyarsa tariga ta sanara tun kafin ma ya iso shiyada tayi masa shiri na musamman. Tun daga nesa Mahmud ke k'are mata kallo yana karantar yanayinta. Murmushin takaoci yayi lokacin daya fajimci yarinyar ya kuma tuno inda yafara ganinta,sam ba irin matan dayake ao ya aura ba kenan asali ma shi baiga wani abinso tattare da yarinyar ba tun farko dahar Abty take ganin dacewansu dashi. Tsaki ne ya subce masa lokacin daya tsinkayo muryarta tana fad'in " Hi " Bai kulata ba sai ma kauda kai da yayi gefe kome yatuna kuma oho sai ya fito yazo tagabanta ta tsaya tare da folding hannayensa a k'irjinsa. Gaishe shi Munirah takuma yi tare da yi masa iso zuwa cikin gida. Bai amsa mata ba sai ma tambaya daya jefah mata nacewa " wacece ita? Murmushi tayi tare da fad'in " ohh sorry" Sunana Munirah kuma nice wacce Mahaifiyarka ta za6a maka atsayin mata. " oh really " Yafad'a da sigar rainin hankali yana kuma murmushi. Kallonsa ta tsaya yi domin afili zaka fahimci manufarsa koda baka da wayo balle ita. " kinsan wani abu? Idonsa acikin nata yayi maganar sai kawai ta jijjiga kanta dan sosai jikinta yafara yin sanyi. " ko kad'an bakiyi min ba! Sake matsowa yayi kusa da fuskarta yakuma fad'in " kinsan dalili? Da kai ta bashi amsa alamar " a'a". Sai yace mata " saboda ko kad'an baki dace dani ba". " Ki gayawa zuciyarki cewa Mahmud d'innan banaki bane, dan nasan wannan duk munafurcinki neh,ni kuma insha Allahu bazan ta6a auranki ba, mark my word." Yana fad'in haka yajuya ya shiga mota da gudu driver yazo ya shiga shima yatada motar suka fita agidan. Har suka bar haraban gidan Munirah bata iya motsawa ba, mintina yakai uku ta k'ara bayan fitan motar tasu daga gidan kafin ta dawo hayyacinta, gefe da gefenta ta kallah taga babu kowa da

Chapter 15 of 67