Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dak'yar kuwa ta hak'ura bayan ta hak'uran ne yasake rokon ta akan karta yiwa Teemahn komai dan Allah ta bar shi da ita zaiyi maganinta kafin yawuche. 'Kin kulashi tayi kawai ta kauda kanta gefe hakan ne yasa Abbas yagane ba k'aramin 6aci ran mummy yayi ba da jin maganar nan. Har sai yaji yana dana sanin sanar matan da yayi ma. Hira yafar kawo mata sama kamar yadda ya saba saboda shi daman kalaman bakinsa kad'an ne. Mummy kuwa daga " uhmm ko ehh " Bata k'ara wani abu akai saboda tagama fahimtar shi so yake abin yawuce dan yaga ranta ya 6aci shi adole ya kauda zancen. Haka yayita d'an surutunsa yagama dayaga ba response mai kyau sai ya yi mata sallama ya wuce d'akinsa. Washe gari da safe............... _Vote, comment and_ _share pls_🀞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:59 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._wad'anda nasani da wanda bansani ba. 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* πŸ…Ώ *27* Washe gari da safe da ya tashi sai yayi shirinsa da wuri ya fito, har kuwa lokacin daya fito d'in Teemah bata fito ba, gashi lokaci yad'anja dayake bahaka tasaba ba duk da bai fiya yawan fitowa a irin wannan lokacin ba amma dai yasan Teemahn bata fiya makara zuwa makaranta ba. Har zai basar kuma sai ya waske kawai ya wuce d'akinnata da niyyar tada ita, sau uku yana yana buga k'ofar amma shiru ba'a kulasa ba ganin hakan yasa kawai ya tura k'ofar yashiga ko sallamar ma bai yi ba. Kwance ak'asa ya tadda ita tana ciccije baki tare da mammatse cikinta duk ta had'a gumi ga kuma robar ruwa ajiye agefenta. Da sauri ya k'arasa inda take ya tsugunna " lafiya kuwa" ya fad'a yana tatta6a jikinta daga fuskarta zuwa hannunta da niyyar jin temperaturen ta, azatonshi ma zazza6i ne amma sai yaji jikin normal sai dai d'umi babu wani abu. " meke damunki ne wai" yasake tambayarta jin bata amsa masa tambayar farkon ba. Ita kuwa Teemah dukda tana d'anjin ciwon kad'an-kad'an amma sai hakan bai hanata jin dad'in har cikin zuciyarta da jin muryar Abbas d'in cikin rahama akusa da ita duk da tana tsoron hukuncin da zai mata amma tasan tana cikin wannan halin bazai ta6a yi mata mugunta ba dan duk abinsa yana da tausayi, balle yanda taga yake tambayarta cikin kulawa da k'yar ne ma idan bai manta abinda yafaru d'in ba. Yunk'uri tayi kamar zata tashi sai yayi saurin tareta ya zaunar da ita da kyau, " ina......kwana yayah" ta fad'a idanunta na k'asa da d'an in ina saboda cikin yad'an sake murd'a mata ga kuma tsoronsa data keji. Atakaice ya amsa mata da " lafiya " sannan ya k'ara da fad'in " wai me yasame ki ne Fateemah" " cikina ne yake ciwo, amma nasha magani yafara raguwa ma ciwon yanzu"Teemahn ce tafad'i haka Shikuwa tsayawa yayi yana kallonta sanda take kan maganar sai da ta dasa aya kafin ya sake cewa " wani magani kika sha"? " ibuprofen" tabashi amsa. " tun yaushe yafara miki ciwon" " bayan an idar da sallah ne". Yariga yagane meke damunta tunda shi ma atleast yayi zaman class koba komai yasan amfanin shan ibuprofen musamman ma ita da nata period d'in baya mata da wasa amma hakan bai sa ya fasa k'udurinsa akanta ba daya d'aukarwa kansa al'kawari. Kallonta yasakeyi dakyau sai yaga tayi wata fayau da ita tamkar wacce ke jinyar satikai. " me kuke yi a makaranta yanzu." Ya tambayeta. " test " itama tabashi amsa atakaice da irin sigar da ya mata tambayar dashi. " toh yaza'ayi kenan, zaki iya zuwane?" Kai ta d'aga masa alamar " ehh" sai yace "okay hanzarta ki watsa ruwa sai in sauk'e ki inyaso inkin rubuta Test d'in sai mu dawo gida. "Toh" tace tare da fara yunk'urin mik'ewa sai ya sa hannu ya da'agota suka mik'e tare sannan yasaketa. Bayi ta nufah da niyyar yowan wankan, shikuma sai ya tsaya yabita da kallo sai yanzu ma yake ganin yanayin kayan dake jikinta ashe ma na bacci ne shi duk bai kula ba. Juyawa yayi ya fita daga d'akin nata yana mai korar shaid'an azuciyarsa. Yasamu mummy na shirin shiga d'aki itama ganin sa yasa ta dakata suka gaisa anan yake ce mata ai cikin Teemah na ciwo amma wai tasha magani........ Taran bakinsa tayi tunkan ya dasa aya tace " Allah ya sauwak'a mata, makarantar fah ko bazata ba", a yatsine tayi maganar kamar bata so shid'inma yagane tun 6acin ran jiya ne bai barta shiyasa take hakan ga dukkan alamu ranta ya 6aci sosai da Teemahn, sai kawai ya bata amsa yace mata " a'a zataje tana shiryawa ne". Tana jin hakan ta juya abinta ta wuce ciki. Dakansa yau ya had'a mata tea tun kafin ta fito daga wankan,sugar d'an dai-dai yasaka mata aciki saboda condition d'in datake ciki. Itama Teemahn dawuri tayi wankan ganin lokaci yad'an ja sai ta yi shirin nata da gaggawa tafito dayake ma tadaina jin ciwon marar sai dai kad'an-kad'an shiyasa tayi komai da kuzarinta. Bak'aramin dad'i yaji ba dayaga ta fito normal kamar ba ita ba sai kawai yace " zonan ki yi breakfast mu wuce karkiyi latti " Ahankali ta taho ga dinning d'in danji tayi banbarak'wai dayake bahaka Yah Abbas d'in yasabar mata ba, tsakaninsu sai dai kallo, kallonma sai ranar daya ga dama sannan take samu, a kullum miskilanci agurinsa shine gaba da komai, Daddy da mummy ne kad'ai bata ganin yana musu hakan. Haka yasata agaba yace tasha Tea d'in sosai, tana kur6a taji salam sai ta d'aga kai ta kalle shi had'a idanu skuayi dashike shima d'in ita yasa agaba da kallo. "Ba sugar aciki" tafad'a tana kallon gefen fuskarsa. " ahakan zaki sha ai, ke baki san illar sugar agareki ba ko? Tsoron masifarsa yasa tadinga kur6a tana kuma danna bread a bakinta kamar wasa sai gashi tasha mai yawa dan cup d'in daya had'a mata gaba d'aya ta shanye shi. Dire cup d'in tayi bayan tashanye d'in sai ya kalleta yana murmushi yace " iyehhh, irin yau anyi abin kirkin nan". Maganar tasa sai ya sata dariyah shima dayaga tana dariyar sai ya tayata suka yi tare gaba d'aya yau ya canja mata kamar ba yah Abbas d'in data sani ba, zata iya cewa yau ce rana ta farko data ta6a ganin dariyarsa tun zuwansa gidan nan, take sai tata dariyar ta tsaya sanadiyyar tunanin data shiga. Ita data ke tsammanin mummunan hukunci daga wurinsa sai kuma akasin hakan ya faru, bata ta6a zaton yah Abbas zai yafe mata laifin sata masa da wuri haka ba amma ga mamakinta sai ya sauya hakan da wani sabon salon annashuwa da farin cikin da bazata ta6a mantawa dashi ba. Idonta k'ur akansa amma sam hankalinta ba'a kansa yake ba, sau d'aya ya mata magana da yaga bata amsa ba sai kawai shima ya yi shiru ya k'ura mata nasa idanun yasan bai wuci mamakin sauyin data gani tattare dashi take yi ba wanda yasan dole ne daman tayi wannan tunanin,bama ita kad'ai ba duk wanda yasanshi idan yaganshi yanzun sai yayi mamakin sauyawarsa. Sai dai shikuma kokad'an baya so ta samu chance d'in da zata yi tunani akan hakan har sai ya bar garin tukunna dan haka sai ya d'ago hannunsa yaja kumatun ta tare da jijjigawa, ai kuwa sai ta dawo daga tunanin tare d'an firgicin tsoro bayyane a cikin k'wayar idanunta dayake daman bata gama sake jiki dashi ba har yanzu, amma ganinsa da smiling face yana kallonta sai ta saki ajiyan zuciya slowly, " kin manta zakiyi Test a school ko?, tashi kije ki gaida mummy sharp-sharp kizo muwuce". Asanyaye ta tashi tsaye tana duban fuskansa afakaice shikuma alokacin agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa yake dubawa amma duk da haka sai yace " kiyi sauri kije nace kuma kin wani tsaya anan kina kallona! Fuskarsa sake take aduk lokacin da zai kalle ta ko zai furta mata wata magana shikansa jin kansa yake wani iri daya ke bahaka ya saba ba amma wannan d'in aganinsa dolensa ne yayi mata hakan kodan ya yi maganinta saboda rashin jinta. Bata fi 3mins agun mummyn ba ta fito da d'aurarren fuska, tana fitowa kuwa shima ya mik'e tsaye ya iso gareta dan ganin dayayi bata da walwala " ya akayi ne " ya tambayeta bayan ya tsare gabanta wanda dan dolenta hakan ya dakatar da ita daga cigaba a tafiyan datakeyi. " ba mummy bace ta min masifa....... " me kika mata " Ya jeho mata tambaya tunkafin tak'arasa fad'in abinda tayi niyyar fad'a. " Nima bansani ba" Tabashi amsa ashagwa6e sai baiyi magana ba kawai ya juya yafara tafiya sannan yace "oyah hurry up muje kiyi test d'in idan mun dawo sai ki bata hak'uri. Bin bayansa tayi itama batare da ta yi wata magana ba. Shikuwa bai tsaya ko'ina ba sai wajen parking sai da ya bud'e motar ya shiga kafin ma ta k'araso itama ta shiga. Ahanya ne yayi tajan ta da hira yana tsokanarta har sai dayaga ta sake gaba d'aya kafin ya kyaleta. Koda yakaita makarantar ma dakansa yakama hannunta ya isa har office d'in shugaban makarantar yayi masa bayani tare da neman alfarma akan cewa bata jin dad'ine kuma tace zasu yi test shiyasa ya kawo ta so idan sun gama test d'in yana so ya wuce da ita clinic a dubata. Principal d'in ne ya tambayeta sunan malamin da zaiyi musu test d'in tagaya masa, sai kawai yak'ira shi awaya ya tambayeshi lokacin dazai yi test d'in sai yace masa nan da 30mins ne. Bayani yayi wa Abbas d'in daganan suka fito atare gaba d'ayansu sai Abbas yayi musu sallama akan cewa Teeman taje class ta jira lokacin yayi inyaso idan sun gama sai tasame shi amota. Daga k'arshe suka yi musabiha da principal d'in yakoma office Abbas kuma ya tafi ga motar sa yayinda Teemah ta wuce class. Tana zuwa ma bata dad'e ba akazo akayi musu test d'in alokacin kusan 11:00am tayi, ko da suka gama sai class rep d'in su (Fauzee) da wata friend d'insu suka rakota har wajen motar. Abbas kuwa hankalinsa naga wayarsa bai ga tahowarsu ba har sai da Teemah ta k'wank'wasa masa glass kafin ya ankara dasu. Ahankali ya sauk'e glass d'in yana murmushi yace " lil sis yadai ko har kun gama test d'in?" Kai kawai ta d'aga masa alamar "ehh". " Shiga mu wuce " Yace da ita. Su Fauzee kam tun da ya sauk'e glass d'in suka k'ura masa idanu suna k'are masa kallo dan sosai yatafi da imaninsu. Jin da Teemah tayi shiru bataji sun gaishe shi ba gashi har yana cewa tashiga su tafi sai ta d'an waiga ta kallo su gani tayi dukkansu suna kallonsa take sai ta ji ranta ya 6aci da hakan sai ta juya shima ta kalli 6angaren dayake taga nashi yanayin, cikin sa'a sai taga shi d'in bai masan suna yi ba dan hankalin sa ma sam baije ga inda suke ba. Sai da ta bud'e marfin motan kafin takuma kallonsu tace musu "toh Fauzee nikam na wuce sai gobenku". D'agowa fauzeen tayi ta kalli Teemahn sai ta kuma maida kallonta ga Abbas d'in tare da fad'in " ina kwana Yayah" 'Dago kai yayi ya kalle su dan shi harga Allah bai kula dasu awajen ba, sai lokacin da yaji Teemhn na musu sallama kuma ko a sannan bai zaci suna tsaye agurinba atunaninsa wucewa sukayi. "Lafiya ya school " ya amsa mata dashi. Ga mamakin Teemah sai taga ya amsa mata wasai bawani d'aure-d'auren fuska kamar yadda yasaba fitowa a asalin millitary force d'insa ba. Sai d'ayan k'awartasu mai suna Ameena itama ta gaisheshin kamar yadda Fauzee tayi abin mamaki bayan amsa gaisuwar harda tsokanar su yayi akan test d'in da suka yi wai ina de basu yi satan amsa ba" yanda ya sake musu fuska sai suma take suka sake dashi yayinda suka bashi amsa da fad'in " haba dai ai an girma anwuche wurin yanzu mun girmi satan amsa" "Ohh daa anyi kenan" yafad'i da d'an zaro idanu waje. Sai suka d'anyi dariya su Fauzeen Shikuwa cewa yayi " toh Allah yasa dai hakan ne", bari mu wuce kunga lil sis d'ina ba lafiya ina so in kaita clinic yanzu" Har karo muryoyinsu sukeyi wajen fad'in " toh Allah ya kawo sauk'i yayin da d'aya ke fad'in Allah ya sawwak'e . Jinjina kai yayi kawai tare da d'aga musu hannu daga nan yaja motar suka tafi. Sosai su Fauzee suka ji Abbas d'in ya yak'ara birgesu. Sai da ya hau titi kafin ya kallo Teemahn jin tayi shiru tun d'azun, sai yayi gyran murya ita kuwa fuskanta na saitin gabanta amma sai ta fahimci da it hakan dayake yana kallonta yayi. Sai juyo itama ta kalleshi yayin da shi kuma yariga da ya maida hankalinsa ga tuk'I. " wai dama kasansu ne yayah? Ta jefa masa tambayar tana kallonsa. " shi kuwa murmushi yayi mata dan dama abinda yake so kenan, amma sai yace mata " me kuma yafaru?,ko laifi ne dan mun gaisa dasu? " a'a" tace ahankali tare da kawar dakanta gefen hanya. Sarai ya fahimci damuwarta kishin Teemah sam baya iyah 6uya, he can recalled that lokacin daya zo gidansu batason ko gaishe shi ma tayi balle magana ya had'asu, haka ma da Mahmud yazo tai tayin rigima dan dai mahmud d'in ba irin sa bane da yasan har lokacin barinsa gidan bazasu yi wani shirin arzik'i dashi ba, kuma duk hakan yana faruwa ne sanadiyar son kanta sam bata so wani yafita ko kuma afifita wani akanta tafison a kullum ta zama tasha gaban komai akuma ko'ina ta kasance A. Bai sake kulata ba har sai da suka zo daidai wajen mai saida kayan itatuwa harma ya d'an gota shi sai kuma yadawo da baya. Fita yayi bayan yai parking sai yaje ga mai saida fruits d'in yasayo da d'an dama kuma kala-kala sannan yadawo motar aka zo aka sa masa su a boot daga nan yaja yafara tafiya yanzun ahankali yake tuk'in har suka zo gida suna yin parking yace mata "ki bud'e baya ki shigar da kayan can na ciki, "toh tace tana k'ok'arin fita ya kuma cewa " kinsan mai yasa na saya? Da kai ta amsa masa alamar "a'a". " toh tuna baya nayi ko kin manta? Murmushi kawai tayi dan tasan labarin baya d'in kaf abakin mummy, shima sai yafara gaya mata irin abinda take masa abaya d'in lokacin tana k'arama da irin muguntar datake masa da rigimar sai an saya mata fruits kullum. Dukkansu abin sai basu dariya sai ta bud'e motar tafito shima ya fito suka nufi bayan atare shi ya bud'e ita kuma tasa hannu ta d'auko ledar, tana fitarwa tayi saurin dire shi ak'asa tana nishi " miye kuma" ya tambayeta da mamaki. Karkata kai tayi gefe tare dayin k'walk'wal da idanu tana kallonsa. " gara ma ki zage ki d'auka domin ni nayi nawa tun abaya yanzu kuma lokacin kine kema" Yana rufe boot d'in yake maganan. Cikin shagwa6a tace " Allah akwai nauyi sosai yayah" " koma menene fah sai kin d'auka yau d'in nan dan na fahimci ba k'aramar raguwa bace ke d'in kina nan kullum sai surutu amma ba amfani." Baki ta tura sannan azuciye ta cicci6i ledan tayi ciki da shi, shima bayanta yabiyo hannunsa rik'e da wayarsa da kuma key d'in mota. Tafiya kad'an ce ta iso dashi inda take tafita da k'yar kamar zata fad'i, tausayi tabashi da ganin yanda take kokuwa da ledan sai alokacin kuma ya tuna da bata da jin dad'i ma ashe sai yasa hannu ya kar6i ladan ya rik'e ahannunsa " muje intayaki d'auka kafin ki fad'i wa mutane". Yaryarfe hannu ta fara bayan ya kar6a d'in ita adole wai zafi, yana tafiya tana binsa abaya har suka isa kitchen sai da ya ajiye ya juya kafin yace mata " inkin gama ki had'a min fruits salat ki kawo min" "Ayyah yayah kamanta banda lafiya ne " Tafad'a kamar zatayi kuka dan harga ita bacci takeso tayi. " kin warke ai naga." Yana kan tafiyar ya bata amsa atak'aice. Ita kuwa haushi ne ya cikata daman ba barinta zaiyi ta huta ba shine ya hana zama a school? Cewa Baabah Lami tayi ta zuba su acikin fridge ita kuma tafice daga kitchen d'in. Gurin mummy ta koma dan sanar da ita akan sun dawo amma koda taje sai bata tarar da mummyn ba hakan yasa ta wuce d'akinta ta sauya kaya kafin ta dawo kitchen d'in dan had'a masa abinda yasata. ***** Acikin kwana ukun daya rage wa Abbas ya tafi ba k'aramar sakewa da Teemah yayi ba hakan kuma shi ya kawo shak'uwa mai k'arfin gaske atsakaninsu yakan 6ata lokaci yana mata hira da labarai na ban dariya, wani lokaci ya k'ira mata Mahmud awaya suyi ta hira dashi Abbas yana jinsu sai dai yayi ta murmushi in kuma sunyi abin dariya shima sai ya dara, yawo sukanje kusan kullum dashi hakanan yakan kaita islamiyah da boko ya kuma dawo da ita gida hatta muhibbat sai da suka kai mata ziyara tare da Teemah, anan ne ta fahimci ashe ma ba budurwarsa bace wacce abokinsa zai aura ne wato Saleem. Ita kanta wani lokaci takanyi mamakin al'amarin takance ashe dama Yah Abbas ya na da fara'a da sakewa haka?, amma mai yasa bai ta6a gwada min asalin halinsa ba sai ya ari wani hali ya ya6awa kansa, kodan shi soja ne shiyasa yake mugun hali oho. Mummy kanta taji dad'in wannan sauyin domin dama can bata son wancen d'abi'ar tasu ta rashin jituwan nan, kawai dai bata da yadda zatayi ne, kuma ganin hakan ne yasa ta manta da fushin datakeyi da Teemahn akan abinda tayiwa Abbas d'in saboda sosai hakan ya 6ata ran mummy aganinta raini ne kawai ke damun Teeman tunda shi Abbas d'in ai ba abokin wasanta bane. Cikin wannan kwanakin ne kuma Fauzee ta takura Teemah akan al'amarin Abbas d'in yayinda abin yake matuk'ar k'ona ran Teemah fiye da zaton mai karatu, tun daga ranar da Abbas yakai Teemah school har suka gaisa shikenan kullum sai sun rakota in sun tshi zata koma dan kawai su ganshi, wani lokaci har 6uya take yi dan kar su ganta, hakan bazai hana washegari su kuma tambayanta abu akansa ba most especially fauzee tafi damuwa dashi sosai. Bata kula ta haka take danne ranta har sai inta dawo gida sannan ta yi ta masa mita da fitina akan hakan shikuwa da bama sanin kirki yayi musu ba yadai san sun ta6a gaisawa da k'awayenta amma yanzu koya gansu he can not even recognize them amma duk da haka dan ya k'ara bata haushi sai yace " wai har yanzu bata daina damunki ba, jiya fah da mukayi waya nace mata karta na sakoki akan maganar amma bataji, kiyi hak'uri lil sis ki barni da ita zanyi maganinta" Hakan kuma bazai hana washe gari taji sabon salo daga Fauzeen ba sai duk suka bi suka d'aure mata kai gaba d'aya tarasa waye ne mai gaskiya acikinsu. Akullum Fauzeen zancenta ita a had'ata da Abbas tana so ne dan Allah ko phone number d'insa ne Teemah ta bata yayin da shi kuma yake nunawa akan ai suna waya ma da ita kawai fooling d'in Teemah takeyi tana wasa da hankalinta. Dataga inaah so suke su caza mata kai kawai sai watsar da al'amarin gaba d'aya tama daina kulawa koda Fauzeen tamata magana. Lokacin da Abbas yafara shiryen-shiryen komawa da Teemah suke komai duk wani abu daya dangamci tafiyarsa da ita akayi shi kansa yana yabawa da k'ok'arinta akan hakan sai dai deep down yana matuk'ar jin tausayinta har aransa domin shak'uwar da sukayi ba irin shak'uwar da za'ace anyi ta ankuma manta ta bane tana mat'uk'ar tsaywa azuciya, dakansa yafahimci irin yanda take ji da nuna kishinsa wanda yanada tabbacin ita kanta bata san ma'anar hakan data keyi ba. Wani lokaci yakanyi danasanin hakan daya mata yasan zai cutar da zuciyarta ne ba kad'an ba dan yana da tabbacin da bai sake da ita har haka ba da bazata ji zafin rabuwa dashi ba kokad'an koda kuwa yabar garin, duk da yake shi ya shirya hakan a matsayin hukuncin rashin jin data tayi masa da kuma rashin kunya amma shida kansa yanzu yasan bai kyauta mata ba. Ana gobe zai tafin da k'yar ta tafi ta kwanta amma kuma sam bacci yagagara d'aukanta haka ta kwana idanunta biyu tana ta tunanin rabuwa da yayanta. Kusan sallar asubah ne ta tashi ta dauko jakar makarantar ta ta fitar paper ta yagi d'an k'arami da biro tayi rubutu akai, ajiye shi tayi bayan ta gama rubutawa, sannan ta sake yagan wani the same size da wancan takuma yin wani rubutun shima ta ajiye, wasa wasa sai da tayi kusan kala biyar duk ta tarasu agefe ta d'ora kanta akai. Har akayi sallar asuban tana kwance idanunta a rufe gaba d'aya sai takejin babu dad'i, dakyar ta tashi ta d'auro alwala tazo tayi sallar asbah d'in, sai dai tana idarwa bacci ya d'auke ta akan sallayar datayi sallan. Dayake bata yi bacci da dare ba sai wannan baccin yamata nauyi sosai har gari ya waye ma bata sani ba har kusan 7:00 tana bacci. Abbas kuwa dama fitan wuri yake so yayi shiyasa yayi shirinsa da wuri yayi zaman jiranta dan sun rabu ne akan cewa da sassafe zata zo ta tashe shi daga bacci dan kar ya makara ganin lokaci na tafiya ita kuma shiru sai ya fito ya nufi d'akin nata dan ba mamaki ma mantawa tayi da batun tafiyar tasa acewarsa. Ahankali ya tura k'ofar ya shigo bayan bugun da yayi yaji shiru yana shigowa kuwa sai idanunsa ya sauk'a akan gadon ta dayafi zaton tana kwance akai tana bacci amma kuma sai bai ganta akan gadon ba sai yaganta ak'asa akan sallaya, murmushii yayi kana yace " daga sallah sai bacci kenan" . Takardun dayagani agefen gadon ya nufi wajensu aransa yake tunani k'ilan kwanan karatu tayi shiyasa take baccin yanzu. Hannu yasa ya d'auko takardan dayaga k'ananun papers akai sai yaga anyi rubutu kamar haka........ _People are like_ _stained-glass_ _windows_ . _They sparkle and_ _shine when the sun_ _is out_ , _but when the_ _darkness sets in,_ _their true beauty is_ _revealed_ _only if there is a_ _light from within_ . Kauda wannan yayi ya je ga na k'asa shima yaga ta rubuta..... _Hold on to what you_ _must do,_ _even if it’s a long_ _way from here_ . _Hold on to your life_ , _Even if it’s easier to_ _let go_ . _Hold on to my hand,_ _even if someday_ _I’ll be gone away_ _from you. __I'm_ _going to miss u _so_ very much yayah_ Sosai jikinsa yayi sanyi dayaga papers d'in haka yadinga d'aga wa yana gani tare da k'ara maimaitawa har kusan sau uku. Daga k'arshe sai ya zare guda d'aya wanda yafi sanyaya mashi rai ya ninke yasaka abayan condom (cover) d'in wayarsa sauran kuma ya mayar mata abinta ya ajiye mata. Inda take kwancen yaje ya tsaya yana kallonta yanda take baccin ba k'aramin birgesa tayi ba " she's innocent while sleeping. Wayarsa ya ciro ya kashe hasken camera d'in sai ya d'auke ta a photo daganan yajuya ya tafi abinsa. Koda ya fito d'in sai yabiya ta kitchen dayake yasan mummy kullum dasafe in kana son ganinta toh a kitchen zaka same ta har sai taga ta sallami kowa kafin hankalinta yake kwanciya. Da sallama ya shiga kitchen d'in tana juyawa ta amsa sallamar tareda fad'in " bade harka shirya ba"? Murmushi yai mata sannan yace "nagama shiri mummy inaso inje dawuri ne dan akwai abinda nakeso nayi acikin maidugurin kafin nawuce. Jinjina kanta tayi alamar gamsuwa, sai sannan kuma suka gaisa tare dayi mata sallama gaba d'aya, itama mummyn fatan alkhairi tayi masa da kuma d'umbin godiya bisa ga karamcin daya nuna musu wata guda cif na hutun daya samu awajen aikinsa yabar mahaifansa ya taho dominsu saboda zumunci. Sai yau ne zashi Gombe kuma acan ne zasu had'u da daddyn Teemah dayake shima yanacan yaje gaida 'yan uwa da mahaifiyarsu. Amma shi Abbas d'in gobe zai wuce dayake bawani yawane da 'yan uwansu nacan d'inba kusan kowa yanufi inda zashi Daddyn ma goben zai taho watak'ila ma su fito tare da shi gaba d'aya. Dayake saturday ne sai Teemah tayi tashan baccinta tana baza mafarki ba ita tatashi ba sai ba sai kusan

Chapter 12 of 67