Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
amma karka damu amince wata ba yana nufin tauye maka hakki_ _bane ni nan ina tare da kai, ya ake ciki gaya min yanzu, ra'ayinka dama na 'kira inji idan kayi na'am toh shikenan sai in kar6a maka in kuwa kaga baka so toh feel free ka sanar dani babu wanda ya isa yayi_ _maka dole matu'kar ina numfashi, karka damu da cewa Fateemah jinina ce ita bandamu ba_ _dan nima ha'din be birge ni ba, dan kaga ita ta ta6a yin aure sa6anin kai, ni sam banga dacewa_ _anan ba..........."_ Dai-dai nan Abbas ya dakatar da shi da fa'din " _Daddy_ .....!" " _Ya akayi, sanar dani karka damu_ " Daddyn ya sake fa'da masa. Be san me ze ce ba dan haka sai ya yanke 'kiran kawai yana murmushi, komawa yayi da baya bayan ya sar'ka hannayen sa biyu cikin junan su tare da maida su 'kar'kashin kansa yayi pillow dasu, idanunsa na kallon cielling 'din 'dakin kamar me karanta wani abu ajiki, daga bayane ya lumshe idanun sa maganar Ummah ce ta dawo kansa " _.....da izninsa kuwa bazaka yi kuka da Fateemah ba, zakaji da'din auranka insha Allahu_ " Wani farin ciki yakeji yana lullu6e shi, kamar a mafarki wai yau auransa da Fateemah saura 1week, jiyake kamar bashi ba, finally burin sa na gab da cika cikin sau'ki batare da ya wahal da ransa ba. ***** A can parlour kuwa har yanzu Ummah nata dramma da yaranta akan kawowa Abbas breakfast. Farko Hannah akace ta kai masa take kuwa tace " _Ummah nafa 'kone da ruwan zafi a'kafata 'dazu da muna kitchen kuma zafi yake min,_ _Teemah ta kai masa please_ " Hannah na maganar ne tana satan kallon Teemah afakaice. Juyawa Ummah tayi ta kallo Teemah ta tambayeta wai dagaske ne Hannah ta 'kona 'kafarta akitchen 'dazu? " _Dagaske ne Ummah amma ai ka'dan ne fah kawai bata son zuwa ne_ "! Ummah cewa tayi Hannah ta nuna mata gurin ta gani tukun na. Sai Hannah ta nuna wani guri daya 'danyi ja ka'dan. Ummah ma cewa tayi ai wannan ba ze hana ta tafiya ba dan haka maza ta tashi ta ha'da ta kai masa yana can har yanzu bakomai acikinsa. Rigima Hannah tafara irin na shagwa6a66u kamar gaske wai ita zafi waye-waye. Anty na murmushi ta 'dan juyo ta kalli Teemah tace " _yi ha'kuri kinji mamana daure ki kai masa ki dawo tunda yau 'din_ _'kafarta na ciwo_ " Turo baki Teemah tayi tace " _Allah Anty ruwan fah 'diga kawai yayi...."_ Tare ta Anty tayi da fa'din " _bana ce kiyi ha'kuri ba! maza tashi kije kinji_ " Tsaye Teemah ta mi'kewa tana bankawa Hannah harara da har yanzu dramar su da Ummah be kare ba, afakaice ta yiwa Teemah gwalo ganin ita zata kai. Teemahn ce ka'dai tagani takuwa 'kara sha'ka har wuyanta tare da jin matsanancin haushi . Aranta tace " _zan rama ai_ " Da Ummah taga ta ha'da masa kuwa ta ringa saka mata albarka tana 'karawa, duk da haushin da take ciki amma bakinta be kasa amsawa da _AMEEN_ ba. Tana tafiyar take tuna iskancin interview 'din da Hannah taringa yimata 'dazu a kitchen ita adole sai taji abinda yafaru jiya tsakanin ta da Yayah, tasan yanzun ma iya shege ne kawai bawani ciwo daya dameta. Abbas kam jiyake kamar idan yaci gaba da zama agarin nan toh kowa ma zai iya fahimtar yanayin farin cikin dayake ciki, dan haka take ya yanke shawaran gara ya tafi kawai tunda yanzu yanada tabbacin mallakarta inyaso sai ya dawo lokacin auren. Dama already kominsa a ha'de yake dan dama da niyyar tafiyan ya kwana,maganar daddy ne ya dakatar dashi, yanzu kuwa da ya san cewa za6in Daddyn cikar farin cikinsa ne ai shikenan, da yake dama shi ba ya yin tafiya da kayan sawa in dai tsakanin Abuja da Rivers ne sai de kayan da yasan zasu masa amfani, dangin su wayoyi, system da sauransu. Acikin wata jaka kalar Army green ya ha'da komai, Rigarsa daya cire 'dazu bayan ya dawo daga gurin Daddyn sa ita ya maida jikinsa tare da 'daukan jakan ya rataya akafa'dan sa ya nufo palour. Teemah na isa 'dakin ta tarar dashi tsaye agurin switch yana 'ko'karin kashewa, kafa'dar sa rataye da jaka sallamarta ne ya dakatar dashi sai ya juyo ya zuba mata idanu bayan ya amsa sallamar tata. Itama bata ajiye abin hannunta ba sai ta ri'ke tare da yin 'kasa da kanta tace " _ina kwana_ _Yayah_ ! Be amsa ba sai ya tako ahankali zuwa inda take tsayen ya jefa mata tambayar " _Yau kuma fushin me kike yi? Me ya sameki_ ? _Ya tambayeta tare da tsare ta_ _idanunsa masu rikitata gaba 'daya_ . Jikinta har na rawa saboda irin kallon daya ke binta dashi. 'Kasa-'kasa ta amsa da " _bakomai_ " Juyawa yayi ya koma gurin switch 'din da be kashe ba 'dazun, yana kashewa kuwa take 'dakin ya dawo duhu ba'ki'kirin. Sannan ya mi'ka hannu ya kakkashe conditioners ma gaba 'daya daga nan ya sake dawowa inda take tsaye. Yanzun kam da hasken 'dakin ya ragu har 'daga kanta tayi ka'dan ta kalleshi sannan ta kauda idanunta gefe. " _Kunyi magana da Daddy ne_ ? Jijjiga kai tayi sannan ta furta " _ah' ah_ " " _Okay ba matsala, amma make sure that baki tsallake duk wani umarninsa_ _ba koda bana nan, and ki daina fushin nan haka abincin ne bakyaso ki kawo_ _min ko kuma menene_ ? Afirgice ta 'daga idanu ta kalleshi, hakan kuwa datayi sai yasa shi saurin fahimtar ya harbo jirgin ta, zuwa inda yake ne bata so. Murmushi yayi sai yace " _Yes, ai nasan halinki baki ta6a appreciating yin wata hidima agareni ba, nima ban son abincin ki koma da abinki am ok na hutar dake_ " Cikin shagwa6a tace " _bahaka bane fa Yayah!_ Jakar dake kafa'dansa ya gyara Sannan yace " _toh menene gaya min naji_ " " _Ni....ni...nifah_ .... Kame-kame ta hauyi ta rasa takamamman abin fa'da. Murmushi Abbas yayi yace mata _"maganata gaskiya ce kenan_ ? Yana gama fa'din haka ya juya zuwa 'kofa a hankali. Teemah kam baki ta tura tabi bayansa da kallo. Har ya kusan rabin 'dakin sai kuma yajuyo ya sake kallanta yace " _ki saki ranki ki daina fushin nan kin manta yau Mummy na hanya_ _ko_ ? Da kai ta bashi amsa sai yaci gaba da fa'din " _kinga nima yau ina cikin farin ciki kema ki tayani kinji_ "? " _Uhmm_ " Tace masa Shi kuma yasake fa'din " _natafi_ " " _Allah ya tsare_ " Tace ahankali shima asaman la66ansa ya amsa da " _Ameen_ ". Daga nan yafice abinsa be sake juyowa ba. Teemah ma tsayuwa taci gaba da yi agurin tama rasa mai ke damunta, jitake kamar tafiyar tasa ne bata so amma sam tarasa dalilin hakan, yau ka'dai sai taji tamkar zatayi missing 'dinsa idan ya tafi. Komawa tayi kitchen ta ajiye kayan kafin ta wuche 'dakinsu ta kwanta agado tayi luf abinta. Hannah ma a 'dakin ta sameta wanda barinta gun su Ummah kenan bayan wuchewar Abbas. Tana barin gurin su, Ummah ta bawa Anty labarin abinda ke faruwa. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Ur comments are gating very low gaskiya kuma banajin da'din hakan harga Allah.* ~Mabiya Labarin *CAPTAIN ABBAS* kuyi min uzuri najina da kukayi shiru kwana biyu abubuwa ne sukayi yi min yawa amma yanzu kam insha Allahu nadawo da 'kafafuna, insha Allahu zaku rin'ka jina akan lokaci.~ *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated 2 my_ ❀ *Bismillahir rahmanir raheem* _Silence is the best answer of all questions nd Smile is the best reaction in all situations............ Unfortunately both never help in VIVA & INTERVIEW_ . πŸ…Ώ *74* Anty taji da'din hakan sosai tace kamar an shiga ranta anga ni, dama ita ta jima da ganin dacewar hakan, tace ai kuwa zama be kama ta ba, shiri ne gagarumi ya kusanto ta dan ma abin yazo a 'kurarren lokaci ne in ba dan haka ba ai da bikin sai ya zama bikin 'yar gata wanda aka da'de ba'ayi irinsa ba, duk da haka de tace bazatayi 'kasa agwiba dole ne tafitar da 'yarta yanda zata zama abin kwatance. Ummah ce ta dakatar mata da tunaninta ta hanyar shigo da 'korafi akan rashin sanar da Fateemah da Daddy be yi ba inda tace da Anty " Sai de ina ganin kamar fa ba'a kyautawa yarinyar ba, saboda bada yaddan ta mahaifinsu ya yanke wannan hukuncin ba, ina tsoron kar a shiga hakkinta sosai dan kinsan yanzu tana da daman da zata za6i miji da kanta ba sai an za6a mata ba musulunci ne dakansa ya bata wannan damar, duk da cewa za6a matan ma ba haramun bane amma naso da an nemi yardan ta tukunna" Murmushi Anty tayi tace " karki damu da wannan dan Allah, ni nan nasan halin Fateemah bazata ta6a yin musu ba, shima mahaifin nasu yana da tabbaci akanta ne shiyasa kika ga ya yanke hukuncinsa kai tsaye batare da wata fargaba ba saboda yasan dukkan su zasu yi masa biyayya shiyasa be damu ba, kuma yawanci idan kinga mace tayi jayayya da iyatenta akan maganar aure toh already zaki samu tana da wani me daban, Fateemah kuwa ai nasan bata da wani manemi daban ko akwai? Anty ta ta'karasa maganar tata da tambaya. Jijjiga kawai Ummah tayi tace " Bana tunanain haka gaskiya" "Toh kin gani, insha Allahu bazata damu koda ta damun ma zata sakko da yaddar ubangiji" Shiru Ummah tayi tana tunani aranta, ita aganinta duk da haka ya kamata Teemah tasan me ake ciki, kafin lokaci yazo ya 'kure yakamata aji nata ra'ayin, ita Ummah 'daukan alhaki ne take tsoro shiyasa ma ta damu sosai, wanda tunanin nan yayi mata karan tsaye a zuci ya hanata sakat dan haka sai ta yanke shawarar samun mahaifin nasu da batun. Anty kuwa baruwanta da'di taji dajin wannan labarin sai de kuma wani 6angaren tana tunawa da marigayi Mahmud, amma bata bari hakan ya nuna afili ba sai kawai ta takaita tunanin da ro'ka masa addu'ar dacewa wurin mahalicci. Sai da ta koma 'daki sannan tasha kuka har ta godewa Allahn ta, babu wanda yasani, dan haka da kanta ta ha'kura tayi shiru. Ayanda akasa ranar bikin Abbas 'din zai kasance kwana 'daya tsakaninsa da na Abban Mahmud domin shi nashi ranar Saturday ne sa6anin na Abbas daya kasance ranar Friday. Da yamman ranar Mummy ta iso su Hannah murna kamar zasu ha'diye ta baran ma Teemah da tayi matu'kar missing 'dinta sosai kuka ta sanya ta rungume ta da 'kyar Anty ta lallashe ta tayi shiru. Mummy kam dataji labarin bata wani damu ba dan ta riga da taji abakin Daddy tun a Dubai, sai de tana tunanin ko shi Abbas 'din baze amince ba tunda yanzu Teemah matsayin ta daban, bazawara ce ayanzu. Abinda kenan ya tsayawa Mummy ama'koshi ya kuma hanata jin da'di. Amma ganin yanda kowa ke farin ciki da al'amarin musamman Anty dan kane-kane tayi ta hana Fateemah zuwa ko'ina bayan ta nemo matar da zata ringa yimata komai, hakan ne yasa Mummy ta saki jiki tabi ayari aka cigaba da hidima da ita. Ummah tasamu Daddy da abinda ya dameta amma shima nuna mata yayi ba komai shikansa yanaso yayi mata maganan amma yafi son idan Yah Kabiru ya iso, dan shi ka'dai bazai iya ba yarinyar na matukar bashi tausayi ganin bataje ko'ina ba amma rayuwa ya gwara kanta, kuma yana tsoron kar jin labarin ya dawo mata da past 'dinta baya. Babu wanda ya sanar da Fateemah cewa auranta za'ayi kowa kawai harkar gabansa yakeyi, su Mummy tunanin su wai kar atuna mata da baya kuma ta 'daga hankalin. Ummah cema ke yawan yawan damun Daddy akan asanar da ita saboda kar garin neman gira kuma a rasa ido, ita kullun damuwarta gudun shiga hakkin yarinyar, ganin ba'a bata daman daya kamata abata ba aka hau shirin 'daura mata aure. Daddyn kansa abin na damunsa amma jiran Yayah Kabiru yakeyi idan yazo sayi maganar tare, yanada tabbacin cewa Fateema bazata ta6a gujewa umarninsa ba, dama Abbas ne matsalan dan kuwa har yanzu be san inda al'kiblarsa take ba akan auren, duba da yanda ya tattara yayi tafiyarsa duk da kuwa yasan cewa auren ya iso, hakan kuwa dayayi sai Daddy ya bari akan rashin son auren ne yasa, shi kuwa bayajin akwai abinda zai hana auren nan yiyuwa koda ma Fateemahn tace bata so toh dole sai tayi ha'kuri tunda ita da Abbas 'din 'yan uwan junane, saje can su 'karata. Idan yaga akwai cutarwa ne sannan zai 'dau matakin daya dace akan Abbas 'din. Tuntuni su Teemah sun can cewa Yayansu zaiyi aure amma kuma hakan ba dalili bane da zai sa har a tsare ta a'daki da gyaran jiki ,wata rana kuma harda Hannah akeyi musu, hakan da aka mata kuwa sai ya dinga tuna mata da lokacin aurenta da Mahmud wancan ma kusan hakane yafaru. Bata san dalilin daya sa za'a ringa yi mata gyaran jiki ba, dan wani zaiyi aure amma dayake gwanar son kwalliya ce ita sai kawai ta basar da zancen ta saki jiki aka cigaba da gyara ta. Duk kuwa da yanda aka kai da yimusu abubuwa tare amma cikin lokaci 'kan'kani Teemah ta yiwa Hannah zarra ta fita haskawa, wani lokaci dukkan su suna mamaki wai duk akan auren Yah Abbas ne ake musu wannan shirin? Lallai Anty na bala'in sonmu sosai. Hannah ce ma me 'dan 'ko'karin tambayar Mummy wai a ina Yayah ya samo matar auren da ake wani uban shiri haka? Gaba 'daya gida ya 'dau 'dumi, ga ba'ki sai zuwa suke tako ina, duk da maganar bata fito da wuri ba amma fah yadda dangi ke 'ko'karin zuwa abin na basu mamaki sosai. Tace " gaskiya ni Mummy abin na bani mamaki sosai, kamar wani 'yar gidan minista ko shugaban 'kasa zai auro? Murmushi Mummy tayi tace mata " _Za6in Daddyn ku ne shine ya za6a masa matar_ " Zaro idanu Hannah tayi cikin mamaki tace " Mummy kuma Yayah ya yarda? Mummy amsa ta bata da fa'din "Abinda nima bansani ba kenan har yanzu" Ta6e baki Hannah tayi tace " _ta6 gaskiya ina jin tausayin yarinyar nan, kinsan fa halin Yayah sai a_ _hankali, da wuya ake fahimtar sa_ " Teemah kam banda bugu babu abinda zuciyarta keyi alokacin dan kuwa fargaba ne taji ya kamata na fitan hankali da batasan dalili ba, bata sani ba ko itama tausayin amaryar Yayan takeji. Bata sa musu baki a maganar ba amma tsuru-tsuru tayi kamar wata marar gaskiya. Kanta na 'kara kullewa ne aduk lokacin da ta ga yanda Anty ke sata a gaba da abubuwa , shafa wannan, sha wannan, yi kaza, abin sai ya fara bata tsoro mafi yawa ita da Hannah ake yiwa amma idan abin sha ne ita ka'dai ake bawa tasha, idan kuwa ta tambayi Anty dalili sai tace shima 'din na gyaran jikin ne ko bata ganin cewa Hannah tafita haske, Anty sai ta dulmiyar da ita da fa'din haske kawai zai 'kara mata itama, tace ai kinga Hannah tafiki haske ka'dan shiyasa ita ba'a bata. Hannah kam kullun jimanta wa wannan amaryar Yayan takeyi, tasan shi bashi da yawan fa'da amma tasan halinsa shi bau'da'd'den mutun ne, da gane al'kiblarsa nada matu'kar wahala, magana wannan sai yaga dama yake yinta koda kuwa babu abinda ya damesa, idan ransa na 6ace kuwa wannan 'kasaita da miskilancin na musamman ne, ita kuwa a tsarin ta bata son mutun haka, tana ganin kamar ita bazata iya auren mutun irin sa ba, dan wani lokaci magana da baki ma na sanyaya al'amura akan mutun ya 'kyale ka, shi kuwa wannan yazama jinin jikinsa, tana ganin miskilancin Yayah ya shahara sosai da ita kanta abin na damunta balle matar da zai aura su rayu tare. Idan fannin kyau ne, ita kanta tasan Yayah 'karshe ne a wannan fagen dan ko ita ma bazata nuna masa komai ba duk kuwa da tana matsayin mace amma Yayah ya mata fintinkau, yana da kyau da kwarjini na musamman wanda ba kowa ke dacen samun irin sa ba. Sannan ya nada sanyi hali aduk lokacin da dayaga dama baka gane hakan har sai rayuwa ta ha'daka wauri guda dashi. Ranar da Hannah taji cewa Teemah Yayanta zai aura........ 🀞🏻 *Karku raina please kunsan wannan kyauta ce kawai nayi muku, sai mun ha'du gobe idan* *Allah ya kaimu kuma* . πŸ‘ŽπŸ» ~Muna gaiyatar ku zuwa bikin mu fah, mun tanadar da masauki me girma sai kun zo....~ 🀠🀠 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~Dedicated to my fans.~ *Bismillahir rahmanir raheem* _If you treat her the same way you treat others, how is she supposed to know that she is special to you....?_ πŸ…Ώ *75* Ranar da Hannah taji labarin cewa Teemah ne Yayah Abbas zai aura ba 'karamin farin ciki tayi ba, sai de kuma tana jin tausayin Teemah ka'dan saboda halinsa, amma damuwar ta be yi yawa ba danta fahimci cewa tsakanin Teemah da Yayahn akwai wani 6oyayyen sirri da har yau takasa gane ko menene shi. ***** Sai da bikin ya rage saura kwana biyu kafin Daddy yazo, hakan ma Mummy ce ta matsa masa akan yayi saurin zuwa saboda Teemah, amma da shi niyyan sa sai ranan Thursday zai taho inyaso friday sai a'daura aure aranar kuma sai ya wuce lagos saboda auren Abbahn Mahmud da za'a 'daura ranar saturday. Amma da Mummy ta matsa kawai sai ya taho, ganin sa kuwa har sai da ya sanya Teemah kuka taje da gudu tafa'da jikinsa tana ta rungume shi tana kuka, Daddy kam murmushi yayi ya dinga bubbuga bayanta ahankali yana bata ha'kuri harta yi shiru sannan sukayi gaisuwa me kyau da ita ha kama Hannah da suka zo gaida Daddyn tare. Hannah kam mamaki ba 'karamin cika ta yayi ba na ganin shagwa6ar da Teemah ke yiwa Daddy dan ko ita da take auta ma wani abin idan Teemah tayi sai dai ta tsaya kalonta dan ita bayi take ba duk kuwa da take autar gida ce ita, kuma Yayah Abbas ne ya hanata, dan baya barinta aduk lokacin daya ga tana yiwa Ummah shagwa6a taka mata birki yake yi 'karfi dayaji sai da ya hanata. Tun shigowan su ta kama guri ta zauna tayi shiru tana jiran Teemah ta gama kukan dan gani da tayi hankalin Daddy gaba 'daya ya koma kanta da rarrashin ta kamar wata yarinya 'karama. Dasuka gaida shi kuwa suka fito ahanyar koma wan su Hannah ke tsokanan Teemah cewa " _taji kunya ai da shagwa6a kamar wanda Daddyn goya ta zai nayi dan ta da'de bata ganshi ba shine harda irin wannan kukan?_ " Tayi maganar tana ta6e baki. Amsa Teemah ta bata da fa'din " _Anyi 'din ina ruwanki_ " Kai Hannah ta ka'da taci gaba da tafiya take fa'din " _hmm, kiyi dai a hankali dan ina jiyake miki watarana, wannan_ _irin shagwa6an sai kace wata 'yar shekar uku? ke da_ _aure ke gabanki_ " Azafafe Teemah tace " _ai kema auren ne ke a gabanki tunda kema macece_ " " _Nasani ai shiyasa ma nake gaya miki, shi aure ai duk sunansa aure, amma kuma mazan kala-kala_ _ne_ !" fa'din Hannah Teemah kuwa cewa tayi " _shiyasa ai naga kina wa Bilal shagwa6an kuma yana kar6a miki tun_ _ma kafin yazama mijin naki_ " Dariya Hannah ta saka sannan ta juyo ta kalli Teemah tace tace " _aini nawa daban ne dan indai Bilal ne ze kar6a min fiye da haka ma shiyasa ma ai nace miki mazan_ _kala-kala ne_ " Tafiya Teemah ta fara tare da fa'din " _nima indai mijin irin Yah Mahmud ne toh bana fargaba koka'dan_ " Da gudu Hannah tasha gabanta tace " _Waye ya gaya miki irin marigayin mijinki ne_ ? _naki tamkar dodo yake inkin ce zakiyi ta masa haka wahala zaki sha_ " Haushi ne yacika Teemah sai ta ja ta tsaya tayi kwafah sannan tace " _Hannah bana son wula'kanci da mugunta_ "! Gaba tayi tana mita, Hannah ma sai ta bita abaya tana murmushin mugunta, ita kam tana son 'yar uwarta kuma tausayin Teemahn takeji sosai. Teemah kam sai mita takeyi 'kasa-'kasa take fa'din. " _akan me zaki rin'ka yimin mugun fata ? angaya miki dodo zan aura ne da har zansha_ _wahala a wurinsa? Wama yace miki zan sake yin auren ?_ _Ni babu wani aure da zanyi bari kiji yanzu, ko da zanyi ma ba yanzu zan_ _sake auren ba kuma ma sai na za6a na tace wanda nasan bazai kawo_ _min matsala ba sannan zan yadda na aure shi_ " Dariya sosai ne ya kama Hannah dan duk taji abinda Teemahn ta fa'da amma sai ta mazge ta maida shi murmushi tace " _kice kafin nan ma har na haifi 'yata ko 'dana sannan muzo musha biki mu kwashi shoki a bikin babbar uwa mama Fatee!"_ Teemah kam ko kulata bata yi ba ta wuce hanyar bayi direct tana tsaki asaman la66a tace " _ke kika sani ai mara kunya kawai_ " Hannah zubewa tayi akan gado tana murmushi aranta tace " wai yaushe za'a sanar da Teemah cewa auren ta ne ya kusanto? ya kamata asanar da ita gaskiya hakanan, ai lokaci na tafiya ni sam banga anfanin 6oyewan ba, ni kam idan bazasu fa'da ba wallahi anjima zan gaya mata meke faruwa inyaso sai ince karta fa'di cewa abaki na taji" " _Yes!, hakan ma za'ayi_ ! Ta karashe da murna ita ka'dai kamar me ta6in hankali. Da daren ranar kuwa sai Daddy ya 'kira Teemah yafara da bata ha'kuri akan tafiyarsu Dubai batare da ta sani ba, da kuma lokacin rasuwar Mahmud da be tsaya ya tausheta ba be wani ke6e da ita a matsayin sa na uba ya bata baki ba wanda shi kanshi yasan be kyauta ba, sai de alokacin tsananin tausayin ta da yakeji ne yasa hakan, ya kara da fa'din mata batun gadon ta wanda aka bata cewa komai a hannun Abbas sai yanda sukayi, yana cikin maganar ya shigar da batun auren da ake kai ayanzu, inda yaringa 'ko'karin fahimtar da ita cewa bawai rashin gata ko so bane yasa duk hakan ke faruwa face tsananin son da ake mata. yace " _duk abinda zanyi ina yi ne Fateemah saboda ke da farin cikin ki, abaya ni na za6a miki mijin aure wanda Alhamdulillah kin cika 'ya ta gari Fateemah da_ _kika yi min biyayya wanda har shi Marigayin_ _ya koma ga mahallici banji wata sa6ani a tsakanin ku ba, naji da'din haka_ _sosai da kika amince da za6ina Fateemah yau ga ni na sake dawowa da_ _wani 'ko'kon barata, kuma mai girman gaske ban sani_ _ba ko zaki iya tayani cika shi!, a karo na biyu Fateemah na sake za6a miki mijin aure wanda na yadda da nagartar sa, nasan yanzu 'yancin kine ke keda wannan damar kuma addini ne yabaki, amma na shiga gabanki_ _na tauye ki, kiyi ha'kuri Fateemah ki ya femin sannan_ _kimin uzuri ki kar6i za6ina, duk abinda zanyi ina 'ko'karine inga na baki abinda nasan ya dace_ _dake domin na tabbata ba zakiyi kuka dashi ba ba zakiyi dana sanin amincewa da za6ina ba insha Allahu_ " Fateemah kuka takeyi sosai amma na zallan hawaye, hawayen ta ya kasa tsayuwa, kuma ta kasa bu'dan baki tayi magana aranta take fa'din " _na amince Daddy na amince da za6inka, ni 'yarka ce kaine ka haifeni kabani dukkan gata insha Allahu bazan ta6a_ _baka kunya ba, bazan ta6a bijirewa umarnin ka ba, bazan ta6a cewa_ _me yasa ka aikata hakan agareni ba_ " Hakan takeso ta furta amma bakinta yayi mata nauyi ga kuka daya ci 'karfinta sosai har sai da Daddyn Abuja ya sanya baki shima yayi ta rarrashinta kafin tayi shiru ta tsagaita kukan amma dayake daga zuciyarta kukan ke tasowa sai hawayen ta ya kasa tsayuwa gaba 'daya, dole cikin kukan ta tabbatar wa Daddy amincewar ta. A tare suka ha'da baki wajen sanya mata albarka da kuma haske mai 'dorewa har 'karshen rayuwarta sannan suka sallameta. Tana jin 'kunci, takaici da ba'kin ciki ga memories 'din Mahmud da ya dawo mata sabo yabi ya cika

Chapter 42 of 67