Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kace ta bari Allah zan rin'ka shan magani kullun_ "! Yi yayi kamar beji ta ba sai ma yace da doctor ta hanzarta please. " _Wallahi ni bana son alluran nan, kuma sai na gayawa Ummah da Anty da Daddy ma_ ". Murmushi doctor tayi aranta take mamakin irin dramar wa'dannan Yayah da 'kan wan suna matu'kar birgeta ita kam. Dakansa ya ri'ke ta tana fiffisgewa amma sai da aka mata har biyu sannan ya saketa. Zamewa tayi ta 'dora kanta ajikin 'kafafunsa taci gaba da kukanta daya ga haka sai yace ta koma kan sofa 'din dake office 'din ta kwanta, itama sai tayi kamar bata jishi ba, murmushi yayi ka'dan yasan haushinsa takeji yanzu dagangan sai yace da nurse 'din " _doctor inajin fah alluran be isheta_ _ba_ " Tana jin haka ta mi'ke ta koma inda ya fa'din ta kwanta shiru tana sau'ke ajiyan zuciya, dayaga kamar zatayi bacci ne sai yace su tafi gara taje ta huta gaba 'daya a gida. ***** Can gida kuwa already shirye-shiryen walima ya kankama kowa nata faman shiri, lokacin da suka iso gidan ma 'dakinsu yayi niyyan kaita amma jin hayaniyar Hannah da 'kawayenta a 'dakin dole sai ya maida ta 6angarensa dan so ya ke ta huta sosai zuwa lokacin kuwa bacci yariga yaci 'karfinta gaba daya. Suna isa tazame ta ta 'dora jikinta akan gadonsa sai kuwa bacci ya 'dauke ta ahakan sai sakin ajiyar zuciya take yi na kukan da tayi 'dazu. Abbas kam tsayuwa yayi akanta yana 'kare mata kallo ba 'karamin kyau ta masa ayadda take 'din ba, ahankali yadawo da idanunsa saman la66anta da suka 'karayin ja sosai. Da sauri ya kawar da mugun tunanin da yazo ransa tare da fa'din " a _uzubillah_ " Gani yayi kamar kayan da ke jikinta sun mata nauyi dan haka sai ya 'dauki wayarsa yakoma parlour, layin Hannah ya'kira amma bata 'daga ba, daya sake 'kira kuwa sai ta 'daga amma bata jin sa tsaban hayaniyan daya yi yawa agurin da take. Take yayi tsaki ka'dan tare da yanke 'kiran. Dama so yake ya sanar da ita ta kawo wa Fateema kaya marasa nauyi amma hakan be samu ba ganin bajinsa zatayi ba, sai kawai yafara tunanin wata mafitar daban. Baifi 5mins a parlour ba sai ya tashi ya koma bedroom 'din tare da 'daukan stool yakoma gaban gadon ya zauna ya zuba mata idanu. Ahankali yakai hannunsa zuwa bayanta ya zuge zip 'din doguwar rigan da ke jikinta wanda yakamata 'dam ya zauna sosai. Ahankali ya zare rigar zuwa 'kasa har ya cire ta gaba 'daya. Abbas kam suman zaune ne yaso kama shi dan be ta6a tsintan kansa acikin irin wannan yanayin ba, be ta6a kallon surar mace azahiri irin hakan ba, macen ma kuma Fateema, idanunsa be ta6a cin karo da abu makamancin hakan ba, 'kirjin ta ya kura wa idanu dake sanye cikin jan bra mai kyan gaske, ajiyan zuciya ya sauke tare da kawar da idanunsa gefe itama Teemah adai -dai lokacin sai ta motsa ka'dan dan sosai taji alamun sauyi atattare da jikinta iska taji na hura ta amma saboda 'karfin alluran dake yawo ajininta yasa bata wani yi motsin na kirki ba ta cigaba da baccinta. Tashi yayi yaje cikin kayan sa ya 'dauko rigar polo ba'ka na aikinsa ya dawo inda take, yanzun kam hawowa gadon yayi gaba 'daya yafara 'ko'karin saka mata rigar, a hankali, idan yaga kamar zata motsa sai ya dakata da abinda yakeyi sai ta kuma yin luf sannan yake cigaba da sawa kamar me dressing wa jinjirin da ba'a so ya tashi a bacci da haka har yagama mata, shi kansa mamakin kansa yakeyi yanda har ya iya tsayawa ya 6ata lokacinsa wurin sanya mata kaya duk kuwa da cewa hakan ba'kon lamari ne agurinsa amma a hakan sai da ya sa mata. Shida kansa ya san Fateemah dabance a rayuwarsa, bata da me kama koka'dan azuciyarsa. Yana gamawa kuwa aransa ya furta " _tubarkallah-masha_ _Allah_ " tare da shafa gashin kanta ahankali, Dan yadda rigar ta matu'kar amsan jikinta ya kuma 'kara fito mata da asalin kyaunta da haskenta kamar ace nata ne, baran ma da ya ha'du da ba'kin skinny trouser 'din dake jikinta ai ba magana, sosai Abbas yaga 'karin hasken ta ya zarce na baya. Abbas kam shashancewa da kallon ta yayi ya mori wanda suka wuce shi ma abaya, shi kansa yasan Fateemah mace ce, mace ce da kowa ni 'da namiji zaiyi sha'awar kasance wa da ita. Ya godewa Allah aransa yafi sau a 'kirga saboda kawai mallaka masa ita da yayi amatsayin mata. Abbas 'dinku kam kasa jurewa yayi lokacin da idanunsa suka sau'ka akan bakinta, sai ji yayi kamar an fizgeshi ya ran'kwafo da kansa zuwa dai-dai fuskarta, bakinsa ya ha'da da nata ya bata light kiss asaman la66an ta. Yana cire bakinsa kuwa yaga ta turo bakinta gaba tare da juyi zuwa 'dayan 6angaren. Sai da ya lullu6eta kafin ya tashi yana murmushi ya koma kan stool 'dinsa ya zauna. Tsawon mintina talatin yana zaune wurin agabanta kamar mai gadin ta, sannan ya koma parlour anan ya tarar da tarin missed calls awayarsa har da na Daddy, Ummah da sauran abokansa. Abokansa kam dama yasan dole zasu neme shi dan be yi sallama da su ba ya taho abinsa, amma be bi ta kansu ba, sai yabi bayan 'kiran Daddy, shima na Daddyn be shiga ba wanda hakan yasa ya gane cewa tafiyar su zuwa Lagos tayi nisa kenan. Sai da ya 'kira Ummah yace da ita yana bu'katar ruwan tea ta amsa masa da toh sannan ta tambaye shi jikin Fateemah yace da sau'ki yasanar da ita cewa sun dawo ma already suna gida. Godiya wa Allah Ummah tayi tare da fa'din tana zuwa anjima toh tadibo ta. A silent ya saka wayar bayan sun gama magana da Ummah tare da ajiyeta agefensa, sam be yi niyyan zuwa ko'ina ba dan haka yayi zamansa a parlourn yana gadin farkawar ta. Daga shi Abbas har ita babu wanda ya halacci taron walimar, inda kuwa babu laifi walima ta 'kayatar fiye da zaton mai karatu, gurin ma ka'dai abin kallo ne dan idan kaga yanda aka tsara gurin dole sai ya birgeka komai fari akayi decoration 'din wajen gwanin birgewa, ga wasu shahararrun malaman musulunci da aka gayyato maza da mata inda suka ja hankalin mutane akan ha'kuri da zaman takewar aure, ga 'dumbin jama'ar al'ummar musulmai da suka halatta suma ba 'a cewa komai, Ga Hannah ma da tawagar ta agefe guda suma ba laifi yawa ne da su, zakayi mamaki idan ka kalli ayarin 'yan CAPTAIN ABBAS FANS 1&2 suma agurin suna ta rawar kai abin su afa'dar su wai bikin nasu ne,'dai-'dai kun cikin su ne ke zaune aguri 'daya, wasu ko fuskar nan babu walwala, musamman ma masoyan CAPATIN na ha'ki'ka da suke jin cewa za'a musu kishiya, su kam har banson ganin fuskar su dan ko ka'dan babu walwala, sunzo ne da niyyar ganin kalar amaryar Abbas 'din amma basu samu dama ba dan Cpt. abbas ya 6oye amaryarsa ya hana su ganinta, basu sami ganinta ba kuwa har taro ya watse gaba 'daya. Ummah da kanta ta kawo masa Tea 'din inda tasame shi zaune a parlour, taso ganin Teemah amma Abbas yace bacci takeyi dan haka sai kawai ta tambayi yanayin jikin ya sanar da ita cewa ba laifi jikin da sauki, tace "toh Allah ya sauwa'ka" daga nan ta tafi da zummar sake dawowa ta dubata idan ta tashi. Mummy naso taga 'yarta taga halin datake ciki dan rabon su da ganin juna tun da rana data hanata 6uya a'daki, zazzabin nata ma labarin sa tazo taji bayan sun wuce asibiti ta kira layin Teemahn kuma ba'a 'daga ba, tana so taganta amma nauyin ganinta tare da Abbas 'din sai ya rinjayi 'kudurinta dole ta sanyawa ranta ha'kuri zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Bayan sallar maghrib Hannah tazo da sallamar ta ta gaida shi tare da fa'din " 'dazu ka kirani Yayah? Yana kishingi'de cikin kujera be ko kalleta ba yace " meyasa toh sai yanzu zaki zo? "Ayyah Yayah muna wajen walima ne fah alokacin shiyasa" Sarai yasan 'karyane dan haka sai ya jijjiga kansa ya kauda kan daga barin kallon ta yace ki 'dauko wa yarinyar nan kayan baccinta inajin zata bu'kace su" Taso ta tambaye shi wacce yarinyar amma tsoron yanayin dayake ciki ya sanya ta ta ja bakinta kawai tayi shiru ta fita. ***** Teemah kam bata tashi ba sai 'karfe tara kusan da quarter ma sannan ta farka, ahankali ta bu'de idanunta sai kuwa taga duhu, bata tashi ba sai ta fara lalu6en Hannah a gadon hannu da 'kafa amma bata jita ba, " Hannah! " Hannah!! ta kira sunan ta har sau biyu, jin shiru yasata ta janye bargon dake jikinta ta sau'ko daga gadon tamkar zatayi kuka, tana shirin barin 'dakin sai taga haske ya gauraye ilahirin 'dakin gaba 'daya. Juyawa tayi sai caraf suka ha'da idanu dashi, zaro ido tayi waje tare da rufe bakinta da hannayenta duka biyu wanda sai alokacin kuma ta fahimci a inda take. Be kulata ba sai ya kawar da kansa gefe duk kuwa da cewa yaji da'din yanda yaga ta tashi garau da ita, amma be nuna hakan afili ba, sai ya wuce ta ya nufi bayi ya dan watso ruwa sai alokacin ne yaji nutsuwar yin wankan ya shige shi, tun 'dazu yake so yayi amma ya kasa sallah ka'dai ke sashi barin inda take yana idarwa kuwa baya 6ata lokaci ako'ina yake dawowa yaci gaba da gadinta, dama burinsa be wuce ya ganta ta warware ba. Yana shiga bathroom 'din kuwa sai itama ta wuce parlour da hanzarin ta da niyyar barin 'dakin, amma sai ta tarar da 'kofan arufe da lock, mamakinta kuwa be wuce na yanda akayi tazo nan 'din ba ga kuma wata riga ajikin ta dabata san daga ina ta sameta ba. Kan stool 'din dake wajen dressing mirror ta koma.ta zauna tana jiran fitowarsa domin ya bu'de mata 'kofa ta tafi. Abbas ma yaso ya 6ata lokaci a gurin wankan amma daya tuna cewa bataci komai ba sai kawai ya hanzarta ya fito in less than 15mins. Shima yana fitowa direct gaban dressing mirror ya nufa dan ganin yanayin jikinsa yi yayi tamkar be ganta ba sai ma murmushin mugunta daya sake yi tare da kwar da kansa. Dama yasan zata nemi hanyar fita shiyasa ya sakawa 'kofan lock kafin ya baro parlourn tun da wuri. Towel 'dinsa 'daure a 'kugun sa ya fito, da farko Teemah rintse idanu tayi data ga ya nufo inda take ahaka, amma daga baya data gaji da rufe idanun sai ta bu'de su ahankali ta sau'ke su akansa. Abbas duk yana lura da ita amma be tanka ta ba. Ita kuwa akan cikinsa ta sau'ke idanun ta, ta kuwa 'kurawa jikin nasa idanu ta na kallo har zuwa 'kirjin sa. Tasaba ganin Yaya Mahmud ahaka amma yau da taga Abbas sai ta ga tsarin halittarsa ba iri daya 'daya data Mahmud ba, sosai yanayin jikinsa ya birgeta yanda jikin ya wani mummur'de ga wasu parks da ya ajiye sai take jin sha'awar ta6awa, amma bazata iya ba dan tasan halinsa idan ta ta6a shi 6a66allata zai yi wannan Yayan kam, kan ta 'daga zuwa fusakarsa, suna hada idanu sai ya 'dage mata gira tare da fa'din " _ya dai_? Kau da kai tayi gefe da sauri tace " _ni ina so in tafi ne"_ " _Zuwa ina kenan_ ? Ya tambaya batare da ya kalle ta ba. Amsa ta bashi da fa'din " _D'akin mu, gurin Hannah..._ " Taranta yayi da fa'din " _can 'din yafi nan ne_ ? Bata bashi amsa ba sai kawai ta tura baki gaba tayi fuskar kuka. Ko kallan inda take Abbas bai sake yi ba yaci gaba da sha'anin gabansa. Teemah kan kukan shagwa6a tafara yimasa ka'dan-ka'dan, Abbas still 'kin kulata yayi sai daya ga kukan na shirin yin yawa ne sannan ya waigo azafafe ya dubeta yace " _for god sake ni na hana ki tafiya ne? Kije abinki mana ko na 'daure ki ne.._ ? Da turarren baki cikin shagwa6a ta furta " ' _kofan fa arufe da lock ai na duba 'dazu_ " Goshi ya dafe kamar ehh dagaske ya manta ne sai yace " _muje in bu'de miki_ " Gaba yayi aransa ya furta " _zanyi maganinki ai_ " Itama sai ta bishi abaya har zuwa parlourn, yana budewa kuwa ko magana bata sake yi ba ta fice abinta. Tura 'kofan kawai yayi da gangan ya barta abu'de dan ya san zata dawo. Ai kuwa ko bedroom 'din be gama shiga ba yaji ta dawo da saurin ta har tana shirin wuce shi. Murmushin gefen baki yayi yana tafiya yace " _ya kin dawo kuma_ ? Tana ha'ki ta bashi amsa da fa'din " _Ni...ni tsoro nakeji, Yayah gidan fah shiru kamar ba kowa ga shi_ _hasken...ma ya ragu sosai bazan iya tafiya a...haka ba_ " Cigaba da tafiyar sa yayi, itama take tabi bayansa tana fa'din " _please Yayah toh ka rakani mana!!_ Bai waigo ba yace da ita. " _Saboda me kenan_ ? " _Ayyah plz Yayah, wanka.... nake so naje nayi kuma inajin....tsoro_ " Ta sake ro'konsa cikin jan magana sanadin ha'kin da ke damunta har yanzu. Sai cewa yayi da ita" _toh ni ina ruwana da wankan ki_ " Abayan sa ta tsaya lokacin yana cuming kansa, sai tayi fuskar tausayi tare da ran 'kwafar da kai gefe gashi dama 'dan gudun datayi yafara sata jin jiri daya ke ya ha'du da yunwa ga rashin 'karfin jiki ga maganan da takeyi yanzun sai yasa zuciyarta ya riga harbawa faster than d normal duk gaba 'daya sai suka ha'du suka canja reaction 'din ta atake sai ta fara ganin dishi-dishi, tuni hawaye ya gangaro mata asaman kuncin ta. Abbas sam be lura da yanayin da ta shiga ba dan ya riga ya juya mata baya, har ya isa wurin mirror ya 'dauko man dayake shafawa a'kafar sa ya zauna akan stool tare da fa'din " _zo nan inkina son in rakaki zo kimin wani aiki_ " Duk da yanayin da ta shiga amma tana jin ya fa'di haka ta taho a hankali zuwa inda yaken kamar yanda ya bu'kata. Shi kuwa 'kafar sa 'daya ya 'dago mata sannan ya mi'ka mata mai 'din tare da furta " _take this_ "! Teemah bata yi wani musu ba kanta a 'kasa tasa hannu ta kar6a dan ta riga ta fahimci manufarsa dan haka sai ta tsugunna tafara shafawa a hankali. Aranta take fa'din dole zatayi masa a yanzun kodan ya rakata ma, dan bata da wani bu'katan da ya wuce ta fita daga 'dakin nasa abubuwa dayawa take so taje tayi . Abbas kam yanda take shafawan slowly ba 'karamin birgeshi yayi ba, hakan kuwa yasa shi 'kura mata idanu yana kallon fuskarta, anan ya hango hawayen datake fitarwa, take kuwa ya janye 'kafar sa da sauri. Faruwar hakan kuwa ke da wuya sai ta 'daga kanta ta kalleshi, ha'da ido sukayi dashi kafin ta 'dauke nata idanun sai ya jefa mata tambayar " _me ya faru kuma ? Ba nace zan raka ki ba_ ?. Bata bashi amsa ba sai ta kauda kanta gefe tare da yun'kurin mi'kewa tsaye. Jiri ne ya 'debeta tana 'ko'karin fa'duwa sai yayi saurin tarota ta dawo jikinsa. Kan gado ya maida ita ya kwantar inda hawayen ta yaci gaba da gangara ta gefen idanuwan ta. Abbas be yi mamakin hakan ba dan yasan jirin nata harda yunwa ma musamman daya san cewa da kansa yasa an mata alluarar cin abinci. Dan haka da hanzari yafara 'ko'karin rabata da kayan dake jikinta da nufin idan ta watsa ruwa sai ya bata abinci zatafi jin ta normal sosai. Amma sai Teemah ta ri'ke masa hannu tana hanashi aiwatar da abinda yayi niyya tana mai 'kara sautin kukan ta. Hannun yabi da kallo ba tare da ya kulata ba sai ya cire hannunsa daga cikin nata ahankali tare da kamo hannayen nata duka biyu ya ri'ke cikin hannunsa guda 'daya, yasan idan yabiyeta zata ta 6ata masa lokaci ne abanza shiyasa gara yayi mata hakan. Skinny 'din dake jikinta ya janye shi gaba 'daya zuwa 'kasa tana mutsu-mutsu amma be 'kyale ta ba sai daya ga ya raba sa da jikinta sannan ya sake mata hannuwan ta. Take kuwa tafara 'ko'karin kare jikin ta dasu wanda hakan sai ya bashi dama ya cire rigar ma cikin sau'ki. Tana ganin haka kuwa ta juya ta kifu da cikinta a 'ko'karinta na ganin takare jikinta tana gunjin wani wahalallan kuka. Abbas ko 'kala be ce da ita ba sai da yaga ta kifun sai ya 'kara samun daman kai wa hannu yayi unhooking bra 'din dake jikinta sannan ya mi'ke tsaye. Wani 'dan 'karamin sabon towel ya 'dauko mata ya lallu6a mata daga bayanta. Tana jin haka kuwa ta kai hannu takama shi tare da 'ko'karin cusa shi a'kar'kashin ta sai da taga tarufe jikinta sannan ta tashi ta zauna tana 'ku'k'kuni. Abbas kam ko kula 'kala be ce da ita ba sai ma ya wuce bathroom ya ha'da mata ruwan wanka da kansa, wanda itama Teemah sai alokacin ta zare bra 'din ganin baya 'dakin sai tayi saurin cusa shi a 'kar'kashin pillow ta 6oyeshi. Tana ganin ya fito kuwa sai tayi saurin mi'kewa tsaye tana rarraba idanu tamkar mara gaskiya, wani sabon jiri taji na 'diban ta sanadin tashi da tayi a fizge sai ta kai hannu ta dafe goshin ta dashi tare da komawa ta zauna abakin gadon. Abbas ma da sauri ya 'karaso gabanta ya sa hannu da niyyan 'daukan ta amma sai tafara yi masa rigima, hakan kuwa yasa ya barta yace toh maza taje tayi wanka tafito yanzun nan. Teemah kamar gaske ta tashi tafara tafiya dan ji take data bar shi ya 'daga ta gara taje da kanta koma a yaya ne, taku biyar mai kyau batayi ba sai taji idanuwanta sunyi luuu, take taga duhu ya cika mata idanun. 'Kasa tayi da sauri ta zauna dirshan akan tiles tana maida numfashin wahala har yun'kurin amai tafara ji sai kuwa ta saki kuka tare da 'kiran sunan Mummy.. Da hanzari Abbas ya taho gareta shikan sa a'kage yake yaga tasa wani abu acikinta dan haka haka be yi wata-wata ba kawai ya cicci6e ta, take kuwa tafara yi mai rigiman bataso ya kaita gurin Antyn ta amma shi ko bi ta kanta ma bai yi ba, be direta ako ina ba sai cikin bathroom. Yana shirin sata a bathtub tayi saurin 'kan'kame shi da 'karfi sai ya kalleta ganin ta'kiyin magana yasa dole sai da ya sau'ke ta batare da ya saka ta acikin ba. Sai daya ajiyeta kafin ya tambayeta " _me ya faru_ ? " _Ni...da kaina zanyi_ " Ta bashi amsa da fa'din haka cikin wata shagwa6a66iyar muryarta. Da 'dan tsawa yace " _ba fah nason taurin kai ni, Allah sassa6a miki zanyi idan kika dameni_ ! Tana so ta bubbuga 'kafafu amma motsin kirki ma yanzu tsoron yinsa take yi saboda tsoron jiri ko ha'ki dan ha ka sai ta juya masa baya tana 'ku'k'kuni. 'Kwafa Abbas yayi yana kallon ta tsawon da'ki'ku, kawai sai ya juya ya fita daga bayin bata sani ba sai ji tayi ya rufo mata 'kofan da 'karfi. Sanadin haka kuwa yasa ta juyowa sai taga baya nan, gurin 'kofan ta isa tasaka lock sannan tazo tayi wankan ta anatse, sosai kuwa taji da'din ruwan daya ha'da mata data gama wankan nata sai ta sake ha'da wani me 'dumin tayi tsarkin ta dashi mai kyau sannan tayi niyyan fitowa tare da 'daura towel 'dinta. Rarraba idanu ta hau yi a bayin ko zata samu abinda zata rufa wa jikinta amma bata ga komai ba, tsaki taja ka'dan sannan ta 'dan le'ko da kanta tare da fa'din "Yayah! Yana bedroom 'din lokacin data 'kira shin yana 'ko'karin saka pyjamas. Hankali kwance kuwa ya amsa ta da fa'din " _uhmm_ " haka kawai yace da ita Sai ta kuma fa'din _Yayah na gama wankan_ " Yace " _toh me kike jira da ba zaki fito ba?_ Cewa tayi " _Ayyah Yayah towel ne fah kawai ajikina dashi zan fito ahaka_ ? Tsayawa yayi da abinda yakeyi yace " _da 'din aya ya kika shiga bathroom 'din_ ? Rage murya tayi 'kasa-'kasa tace " _ni gaskiya kunya nakeji_ !" Sai ji tayi yace " _kunyar wa kenan_ ? Shiru tayi ta'kiyin magana sai hararo hanyar 'dakin da tayi tana tura baki. Abbas kam jin tayi shiru yasa shi fa'din " _Look, Allah 30seconds kika 'kara abayin nan ni da ke ne yau agidan nan zakiga abinda zan miki, ba 'dazu an miki allura biyu ba, toh yanzu hu'du zan sa a miki try me kiga abin_ _mamaki_ "! Zaro idanu tayi waje tare da rufe bakinta kamar wacce tayi 'karya jin abinda ya ce 'din. Sarai ta tuna muguntar da yayi mata 'dazu har yanzu ma zafin allurar be daina ba ballan tana har guda kam ai mutuwa zata yi. Tunowa tayi da 30 seconds 'din da ya ce mata, wuf ta bu'de bathrum 'din ta fito tana wani sunkuyar da kai 'kasa. Abbas ma yi yayi tamkar be ganta ba kawai ya wuce parlour yabarta a'dakin. Kayan ta ta gani na bacci riga da wando da kuma packet 'din pad akan gado sai dai babu pant ita kuma ta wanke na jikinta. Bata tsaya mamaki ba kawai ta 'diba kayan ta koma bayi ta saka su ajikinta, dama yau bata da bu'katan pad sai de ko gobe dan period 'din ta yana bata hutun kwana da wuni 'daya akowani wata, so ko yanzun ma rashin pant 'din be dame ta sosai ba tun da kam tasamu kaya. Kayan kuwa light pink ne mai laushi , gaban rigar kuma bottles dark pink ne ajere da wani 'dan 'karamin flower daga gefen 'kirjin rigar, wandon kuwa yana da 'dan fa'di ka'dan, kayan basu da nawi, dama tana son kayan sosai musamman ma saboda laushinsu. Harta fito sai kuma taga rigar na fidda mata shape 'din 'kirjin ta sosai, haka ta saba sawa amma yanzun sai taga bazata iya fita gurinsa ahaka ba tunda ko mayafi bata da shi. Bra 'din ta ta 'dauko ta sake komawa bayin ta saka. Rashin kaurin kayan ma yaso ya hana ta sakewa, amma bata wani 6ata lokaci ba dan cikin ta har 'kugi yake yi mata saboda yunwa, tunanin ta ma inda zata samo abincin dazata ci a wannan daren. Yanke shawara tayi akan zata ro'ki Yayah ya rakata kitchen tasamu abinda zataci in yaso ko daga nan ma ya barta zata iya komawa 'dakinsu ita ka'dai. Tana fitowa kuwa sai ta ganshi tsaye ransa duk a6ace, a hankali ta 'karasa ta 'karasa bakin gado zata zauna, kafin ma ta zauna sai taji ya kama hannun ta kafin ta yun'kura kuwa taji yaja hannun dole tabi bayansa. A parlour kan dinning 'dinsa na marowatan nan in jita ya ajiyeta, ganin warmers da plates harma da spoons akan table 'din sai ta 'daga kanta ta ta dube shi , " Oyah eat" yayi maganan tare da nuna mata warmers. Abinci ne kala biyu tagani harda pepper soup 'din kayan ciki, ita kuwa duk basu mata ba sai ta bu'de ledan data gani a ajiye shima, fruits ne a ledan tana ganin haka kuwa ta kauda warmers 'din ta janyo fruits 'din ta tafara sha, dama bata jin da'din bakin ta sosai hakan yasa abu me mai ' ko sam bata sha'awar sa. Fruits 'din taringa ci tana za6an masu 'dan tsami tana sha, haka duk ta bi ta lalata kusan rabinsu dan in dai ta ta6a taji ba tsami toh ajiyewa take yi ta 'dauki wani. Tana cikin hakan sai ta ganshi tsaye akantsa hannun sa ri'ke da tea cup. Sosai ta tsorata dan ta zaci ze yi mata masifan 6arnar da tayi ne amma ga mamakin ta sai ta ga ya mi'ka mata 'daya hannunsa, kar6a tayi sai taga magunguna ya 6allo mata kafin tayi wani yun'kuri sai ya mi'ka mata tea cup 'din. 'Kamshin da tea 'din keyi ne yasa ta sha'awar shan sa, aikuwa taringa sha a hankali tare da maganin da 'da'd'aya har ta shanye su. Abbas kam beyi mamaki ba dan yasan halin ta dama da jarabar son fruits shiyasa ma ya sa aka kawo, yazaci ma zata 'danyi sha'awar peper soup 'din amma sai yaga bata ko kula shi ba. Yana ganin ta gama da maganin ya juya ya abinsa koma bedroom. Data ga ya juya ne sai tayi saurin dakatar dashi da fa'din " _Yayah toh tsaya ka rakani mana, na gama fah_ ! Ko kulata

Chapter 44 of 67