tana san'da ahankali.
Jin shiru a ko'ina ne yasa ta 'dan saki jikin ta ganin kamar baya gidan.
Coolern data bari a hanya 'dazu taje ta 'dauke sannan tafara bubbu'de su tana ganin abincin.
Wainar shinkafan data gani ce ka'dai ya birge ta dan haka sai ta 'diba tafara ci a hankali.
Sai da ta gama sannan ta koma 'dakinsa ta gyara shi da kyau babu wani datti amma sanda ta share shi tas ta kunna burner sai ta ja 'kofan ta rufe tare da komawa nata 'dakin duk sai data bisu ta kintsa su inda cikin 'kan'kanin lokaci 'kamshin gidan ya canja, lungu da sa'ko sassanyan 'kamshin turaren wuta ne kawai ke fitarwa.
Sai da ta gama da wannan sannan taji ta shiru, saboda babu wayar ta tare da ita, gashi kuma tana so tayi 'kira amma bata san yadda zatayi ba, ta manta 'dazu kuma bata ce da Hannah ta kawo mata ba.
Yana fita ko 1hr be kai ba yadawo sai gani tayi ana shigowa da drinks da snacks kala-kala ana ajiyewa.
Abinda kawai ya ha'da su cewa da yayi ta saka drnks 'din a fridge da yawa, ya kuma tsaya sai da yaga ta sa 'din ragowar kuma ta adana su kafin ya sake fita batare da yace da ita komai ba.
Zuwa 11am sai ba'ki suka rin'ka zuwa daga gida, 'yan uwa da dangi kaca-kaca sun kuwa matu'kar 'debe mata kewa dan kuwa hira auka rin'ka yi da su Hannah gashi da isheshshen abincin su suka taho wanda suka ci ya ishe su har da saura ma.
Abbas ma da yake yasan da zuwan ba'kin so bai ko le'ko gidan ba har sai bayan sallar maghrib, a lokacin kuwa dukkan ba'kin sun tafi saura ita 'daya.
Gudun hayaniyar su nema yasa be zo dawuri ba sai da ya tabbatar duk sun tafi dan yasan mata duk inda suka ha'du akwai surutu.
Yana shigowa gidan 'kamshi ya yi masa maraba, sosai da'din 'kamshin ya ratsa masa zuciya, a parlour ya zauna ya wani lumshe idanu yana sha'kan dadda'dan 'kamshin da ke tashi a parlourn.
Tsawon mintina goma sha yana zaune a parlourn, sai daga baya ne ya tashi ya kama hanyar 'dakin sa, yaso ya duba ta kafin ya wuce amma kawai sai ya barta ya shige dan agajiye yake gaba 'daya.
Teemah kam bata ma san ya dawo ba tana can kwance tayi zuru-zuru tsoro duk yabi ya cika mata zuciya, motsin kirki bata iya yi banda 'dan 'karan da fanka keyi babu abinda ke tashi a'dakin.
Tsoronta sake ninkuwa yakeyi aduk lokacin da idanunta ya kai ga kan agogon dake manne a bangon 'dakin, ganin lokaci na 'kara tafiya amma har yanzu shiru, tunanin inda Yayan ya tafi wannan lokacin ka'dai takeyi taso da ace wayarta na hannun ta da ta 'kira shi ko kuma ta 'kira Hannah ta sake ro'kon ta ko zata tausaya mata ta dawo dan taya ta zama.
Abbas kam yana shiga 'dakin sa yatar da shi tsab a gyare ga wani sassanyan 'kamshi na musamman daya ke fitarwa shima, duk dama ba'a birkice ya bar 'dakin ba amma yanayin daya samo shi a yanzun ya matu'kar birgeshi.
Wanka yashiga inda ya kwashi kimanin mintina 20 kafin ya fito, shiryawa yayi cikin kayan baccinsa masu birgewa sannan yafito yaje ba'kin 'kofar ta yayi mata knock, Teemah naji ta 'dan firgita amma dataji an sake bugawa sai ta taso a 'darare, da rawar murya tace " _waye ne_ ?
Da 'dan hanzari yace da ita
" _Open up pls, wa kike tunanin zaizo_ ?
Tana jin muryarsa ta yi saurin sa hannu ta bu'de 'kofan, shima Abbas juyawa yayi ya koma parlour, itama Teemah sai ta fito ta biyo shi abaya tare da fa'din " _sannu da zuwa Yayah_ "
" _Yauwa matsoraciya_ "
Yace da ita batare da ya waigo ba.
Dai-dai lokacin da ze zauna yace " _me kike yi a 'dakin dama_ "
Da " *bakomai* " tabashi amsa atakaice.
" _Tsoro ko_ ?
Yasake tambayar ta bayan ya daidai ta zamansa da kyau akan kujerar.
Tana tsaye bata zauna ba tace dashi " _Ni ka'dai ce fah agidan tun 'dazu, kuma nace Hannah ta zauna kar ta tafi amma_ _ta'ki yarda sai tayi tafiyarta kuma ni kuma tsoro nakeji_ "
" _Kin fiya tsoro daya ne ke, bagashi na dawo ba idan ta zauna ma me zata kare miki_ "
Yayi maganar yana 'ko'karin canja chanja channel 'din T.V dake faman aiki.
" _Ai zamuyi hira da ita_ "
" _Hmm_ "
Kawai yace batare da ya sake furta komai ba.
Shiru suka yi dukkan su na 'dan wani lokaci banda 'karan T.V babu komai.
Abbas ne ya yanke shirun da fa'din " _bani ruwa plz_ "
Tashi Teemah tayi a hankali ta nufi hanyar kitchen cikin cikin tafiyar ta me 'daukan hankali wanda ita kanta bata ma san tana yi ba, Abbas binta da idanu yayi yana 'kare mata kallo rigar dake jikinta roba ce, amma tabi duk jikinta ta kamata ta ko'ina, ilahirin shape 'din jikinta babu wanda be bayyana ba, harta shige ya daina kallon ta amma be 'dauke idanun sa daga wurin ba sai daya ga ta fito daga kitchen 'din ne yayi saurin juyar da 'kwayan 'idanun sa ka'dai batare da ya motsa kansa ba, gudun karta kama shi yana kallon ta.
Ruwan ta zuba masa cikin wani farin glass cup ta mi'ka masa, Abbas kar6a yayi yana kallon fuskar ta ita kuwa idanunta nakan cup 'din ne so bata san ma yana kallon ta ba, yana kar6a sai ya kai baki ya shanye ya sake mi'ka mata cup 'din.
Tana zubawa yasake shayewa sai ya dire cup 'din.
Teemah kai ta 'daga ganin irin yawan ruwan da ya sha suna ha'de idanu sai ya 'dage mata gira 'daya.
Ita kam kauda kanta tayi gefe tare da 'daukan cup 'din ta mi'ke tsaye domin mai dasu muhallin su, Abbas kam harda kishin gi'da ya sake bin ta da wani sabon kallon har taje ta dawo.
Sai data dawo sannan ya sake maida ta 'dakinsa ta 'dauko magungunan ta, data kawo ya sake sata ta dauko ruwa, zuwa yanzun kam tafara gajiya da aikan nasa, meyasa dama ya barata ta maida ruwan bayan yasan ze ce tasha magani, sai ta fara ha'de ranta tana kwa6a fuska.
Abbas da ya lura da ita sai yayi murmushin gefen baki kawai ya jijjiga kansa, ri'ke take da ruwan ahannun ta, yayin da shi kuma yake 6allan maganin amma ya tsareta da idanu har se da ta maida nata idanun 'kasa sannan shima ya kalli maganin dake hannunsa yace " _Ni kam ina fatan Allah ya nuna min ranar da matata zatayi farin ciki da kasancewar mu, ranar da zan ce tayi min abu ta aikata min batare da ta 6ata ranta ba_ "
Kanta ta 'dago ta kalleshi dan bata san inda kalaman nashi suka dosa ba sai kuwa suka ha'da idanu dashi, ko a fuskar sa da cikin idanunsa Teemah bata fahimci yanayin sa ba dan shi kullun ahakan yake da wuya ka fassara ainahin yanayin da ka ganshi aciki.
Jitayi ya cigaba da magana inda yace
" _Ban sani ba ko sai ranar dana mallaki Zahra ta, may be ita zatafi faranta min bazata dinga gajiya_ _da min hidima ba_ "
Shiru tayi tana tunanin _wacece kuma Zahra dayake magana akai haka_ ?
Maganin Abbas ya mika mata tare da fadin " _Kar6i kisha_ !"
Ita tunanin Zahra ne ya tsaye mata arai koda ya mika mata maganin ma kar6a tayi kawai ta rike a hannu ta zuba ma hannun idanu, sai daya sake cewa da ita tasha sannan ahankali taringa sha da 'dad'daya har ta shanye lokaci-lokaci takan 'daga ido ta kalleshi zuciyarta cike taf da tambaya amma takasa furtawa.
Koma wa yayi jikin kujera ya jingina sannan yace da ita " _ki ringa shan maganin ko bana gida kinga yau ma tun safe baki sha_ _ba_ "
Ahankali tace da shi
" _ai na riga na warke yanzu ni lafiyata 'kalau_ "!
" _Ban yarda ba, ban yarda da half treatment 'din nan ba ki rin'ka sha_ _akan lokaci kinji_ ?
Kai ta 'daga masa alamar taji, daga nan ta mike ta maida cup 'din ruwan inda ta dauko.
Abbas lumshe idanu yayi yanajin zuciyarsa na harbawa sosai yake jin wani sabon yanayi yana ratsa shi.
Koda ta dawo kuwa sai bata zauna ba ta wuce 'dakin ta inda ta watsa ruwa tare da canja shiga zuwa kayan bacci.
Zama tayi a bakin gadon ta tana tunanin wayarta sosai tayi missing wayarta a kwana biyun nan dan zama shirun yafara isan ta sosai, gashi ita ba gwanar zama ta kalli T.V ba da kuwa tasan zai 'debe mata kewa.
Hisnul Muslim ta 'dauka cikin takardun data gani a drawern 'dakin tafara karanta azkar 'din safiya da maraice bayan shi sai ta 'kara dana kwanciya bacci kafin ta kammala ma sai bacci yaso yaci 'karfin ta, a hankali ta mi'ke agadon ta kwanta take kuwa bacci ya dauke ta.
Lokacin da Abbas ya tashi ze daga parlourn har ya le'kata sai yaga baccin ta takeyi, hasken 'dakin ya kashe mata ya bar dim light kawai tare da ja mata 'kofar ya wuce nasa 'dakin.
*10:30pm*
Ta farka daga baccin kamar an tsikare ta ta tashi ta zauna tabi ilahirin 'dakin da idanu, tana gama fahimtar inda take wato a'dakinta kuma ita ka'dai ai sai ta tashi tafice da sauri ta bar da'kin, Allah sai ya taimake ta hasken parlour na nan be kashe ba.
Amma Teemah bata tsaya nan ba ta wuce 'dakinsa, 'kofan abu'de yake dan haka kawai sai ta tura ta shiga da 'yar siriryar sallamar ta.
Zaune yake a bakin gado farar singlet ce ka'dai ajikinsa da dogon wando, system 'dinsa na agabansa inda ya bada dukkan hankalin sa akai yana dubawa, 'kafarsa 'daya na tsaye yayin da 'dayar kuma take tankwashe ya zauna akai.
Sallamarta ce ta sa shi 'dagowa ya kalle ta da mamaki dan kuwa yasan tayi bacci tun tuni kawai sai ya ganta yanzun kamar an koro ta.
ππ»
*Duk wacce taji aranta kamar cewa wannan SALMERHn* *bata kyautawa... pls badan niba tayi min afuwa saboda Allah, ni kaina nasan bana kyautawa amma* *abubuwa ne dayawa suka sha kaina, koda banyi typing* *ba amma wallahi kullum kuna raina ba'a son raina kuma nake muku jinkiri ba* , *ba yadda zanyi ne kawai* .........
~FATAN ZAKU CIGABA DA MIN UZURI DA HA'KURI HAR MU KAI GA CI.~
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce* π
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_My 'kungiya on top_ π€π»
_This page goes to u *DBWA* i heart u mutane na._ π₯°
*Bismillahir rahmanir raheem*
_Anyone can make u happy by doing something special, but only someone special can make u happy without doing anything._
π
Ώ *80*
Hankalinsa da idanunsa ya mayar kanta ya tsaya 'kare mata kallo, yau riga da wando ta sanya ajikin ta, yariga yasan zancen daya kawota amma duk da haka sai ya jefa mata tambayar
" _ya akayi_ ?
" _Babu komai_ " itama tace masa atakaice.
Cewa yayi
" _Toh me ya hana ki bacci har yanzu? ko rigimar da saura ne bata 'kare ba_ ?
Yasake jefa mata wata tambayar.
Goshi ta ha'de tawani yi kicin-kicin da fuska tace dashi
" Ni bana wani yin rigima.....kuma ma ai baccin nake ji ne yanzun shiyasa nazo dan inajin tsoron 'dakin can 'din"
Ido ya zaro waje akanta yace
" _Kullun ne wai ke kike jin tsoron_ ?
_Come on... go back to ur room kiyi addu'ah ki kwanta_ "
'Kafa ta fara bubbuga masa cikin shagwa6a take cewa " _ni wlh tsoro nake ji ni ka'dai_ ....
Yatsan sa 'daya ya 'dago ya nuna ta dashi yace " _bafa na son iskanci ...da 'din da wa kk kwana da zaki tsiro min da wannan iyayin yanzu_ ?
Kuka ta sanya mishi yanzun tana 'kara maimaita " _ni wallahi tsoro nake ji kuma ai ko da ma bani ka'dai nake kwana ba_ _da Hannah ne_ !
Kwafa yayi yana kallon ta kamar an matsi bakin sa sai ya sake fa'din " _kafin itan kuma fah_ ?
Shi adole tsare ta zaiyi da fa'din hakan.
Teemah kuwa cikin kwanciyar hankali ta bashi amsa da fa'din
" _ni da Yayah Mahmud_ "!
Take Abbas yaji wani mugun bugu azuciyarsa, ransa gaba 'daya yaji ya 6aci atake sai ya rintse idanun sa, wani mugun kishine yataso masa a zuciyarsa ga wani tunani na daban daya 'dar su aransa, sai ma yake ganin kamar da gangan ta ambaci sunan Mahmud 'din dan ta 6ata ransa.
Sam shi beyi tunanin zata ambaci Mahmud alamarin ba, he thought da can baya zata yi magana akai dan shima tunanin sa yatafi ne a lokacin datake gida a Damaturu, wancan lokacin kam yasan ita 'dayan ta take kwana kuma dashi yaso kama ta.
Be iya jura ba sai da ya dafe kansa tsabar yanda yake sara masa, 'kasa yayi da kansa ya sauke idanun sa akan system 'din dake gaban sa, tamkar wanda yaga abin tsoro aciki ko kuma system 'din ne yayi masa laifin sai ya rufe ta da 'karfi.
Kamar an tsikare shi kuma sai ya mi'ke tsaye bai ko sake kallon inda Teemah take tsaye ba ya shige bathroom.
Teemah kam binsa tayi da idanu domin bata san me yasa shi canjin mood cikin 'kan'kanin lokaci haka ba, amma ganin har ya shige be kula ta yasa ta tafi a hankali tayi kwanciyar ta.
Abbas haka da kayan jikin nasa bai ko rage ba yaje ya kunna shower akansa, zuciyarsa, nutsuwarsa da tunaninsa duk suka caku'de suka dagula masa lissafin sa gaba 'daya.
Banda emergining rayuwarta da Mahmud babu abinda ke zuwa ransa alokacin, rayuwarta na baya agidan Mahmud yake tariyo wa har sai da ya kasance shine babban damuwar sa alokacin, shi kansa yasan ba dai-dai yake aikata wa ba amma zuciyarsa ta kasa yadda da cewa 'kaddarar su kenan bayan yariga yasan hakan ne nd he can't change it, he cant even erase d fact that ta ta6a zama gidan wani da sunan aure, kishin hakan ne ya hana zuciyarsa sakewa, shai'dan yariga ya yi masa mugun hu'dubar da ba za ta amfane shi da komai ba.
Shi kansa Abbas yasan kuskure ne hakan saboda babu amfani tuna irin wannan passed 'din musamman ma daya kasance yanzu Mahmud is no more but ya kasa goge hakan azuciyar sa, muguwar sa'kan nan ta ri'ke mashi zuciya sosai tana kuma sake haifar masa da zazzafan kishin Fateemah aduk lokacin da hakan yazo ransa.
Shi kansa ya'ki yake da zuciyarsa akan hakan mafi yawancin lokuta yana burin ganin ya dai-dai ya tunanin sa, rayuwar auren su ta 'dau hanya, amma kafin faruwar hakan sai gashi da bakin ta ta sake tuna mishi cewa wani ya mallake ta kafin shi, kenan wannan passed 'din ba zai ta6a barin rayuwar su cikin sau'ki ba, rayuwar ta da Mahmud yasan azuciyar ta ne ba zai ta6a iya kankare mata ba amma me yasa sai ta furta masa da bakin ta?
Haka ya bar shower nata zuba akansa kusan 1hr yana tsaye guri guda batare da ya motsa ko da 'dan yatsan sa ba, da 'kyar ya samu ya saita tunanin sa da taimakon kalmar innalillahi wa innah ilaihi raji'un dayake maimaitawa ya samu har ya watso ruwa tare da 'dauro alwala ya fito.
Lokacin da ya fito ma har tayi baccin ta Teemah kam cikin natsuwa batare da damuwar komai ba.
Kallo 'daya yayi mata ya 'dauke kansa, sai daya sa kaya kafin ya shimfi'da dadduma ya tada sallar nafila kamar yanda ya sabayi kullun, shafa'i da wuturi ya 'kara a kai sannan yayi zaman ro'kon mahallici haka ya dinga jero addu'o'i akan Allah ya kawo masa sauki cikin al'amuransa ya daidai ta tsakanin zaman sa da iyalinsa in har hakan shine alkahirin dake cikin rayuwarsu gaba 'daya, kuma ya jikan Mahmud yasa mutuwa hutunsa ce.
Bayan da ya idar ma be tashi akan dadduman da wuri ba, sai da yaji ya dan nutsu kafin ya tashi a awurin.
Ji yayi kamar yakoma parlour yayi baccinsa a acan, amma sai yaga rashin dacewar hakan kuma daga yanzun baya son yadinga bawa shai'dan 'kofar da zai ringa gina musu katanga tsakaninsu dan haka sai ya tako zuwa gaban gadon ya tsaye nesa ka'dan da ita yana me sake koran shai'dan azuciyarsa.
Su hajiya Teemah sarkin birgima har ta juya tafara bararraje wa, jiyayi yana son ganinta sosai be yiwa idanunsa rowa ba kuwa ya 'karaso 'bangaren da taken tare da zama agefen ta yana me kusan ta kansa izuwa gareta, gashin ta dake tsefe ne duk ya baje mata afuska saboda fitan da ribbom 'din dake kan wanda ta 'daure dashi yayi.
Tunawa yayi da rigimar ta tun tana 'yar karamar ta bata son kitso sam, yasan hakan ne sanadiyyan zuwa hutu daya keyi acan Damaturu, wasu lokutan idan yana can shine zai zauna ya tsefe mata kan da lallami wataran kuma har sai ya siyo mata tarin choculates kafin take zama, tun be iya tsifan ba har ya zo ya koya da kyau yana mata a weekend.
Idan za'a yi kitson ma sai an kai ruwa rana kafin asamu ayi, bayan haka kuwa idan taga kitson akanta sai tafi kowa iyayi da yanga dashi.
Har ta girma bata son kitso, kullum kanta atsefe, Mummy kanta tayi tagaji 'karshen ta haka ta ha'kura ta 'kyale ta har abin yabi jikinta. Hakan kuwa be sa gashin ya lalace ba, domin yana nan ne kamar mara zuciya tana dai yin saloon akan lokaci amma babu kitso, gashi ba'ki kullum yana shai'ki ban sani ba ko dan kasancewar ta tsakiyan fulani ne ko kuma nata halittan ne haka oho.
Hannu yasa a hankali ya tattara mata gashin gaba 'daya zuwa tsakiyar kanta kusa da goshin ta anan yasa ribbom 'din ya 'daure mata gashin, dan yasan anan kam kowani irin bacci zatayi bazai ta6a takura ta ba.
Idanunsa ya tsayar akan fuskar ta ya tsaya 'kare mata kallo musamman 'dan 'karamin bakinta na rashin kunyan nan.
Da yatsan sa ya shafo bakin a hankali sannan ya maida hannun nasa gaban goshin ta yana 'dan shafa 'kananun gashin dake gaban goshin a hankali ta yadda bazama tasan ana ta6a jikin ta.
Abbas ya kai kusan 15mins agaban ta sannan ya tashi ya koma 'dayan gefen ya kwanta shima yasata agaba yana kallon ta a haka bacci yayi awon gaba dashi.
Washe gari da asubah daya tashi yau kam dabaibaye shi tayi, yajima da farkawa sai yajita ajikin sa amma beyi ko motsin kirki ba gudun karya tashe ta, 'kiraye-'kirayen sallah ne yasa shi motsawa tare da yun'kurin tashi wanda hakan yasa ta bu'de idanu.
Jin kamar tana jikin mutun yasa ta 'dago idanu da sauri ta kalleshi sai ta kuma komar da kanta 'kasa saboda ta 'dan ji nauyin hakan dayafaru, shikuwa ganin alamar kamar bata da niyyan barin jikinsa sai ya ce da ita
" _Madam 'dagani zanyi sallah ne, ko tashin ma sai na 'daga ki kafin ki tashi dan na_ _ga alama naki son jikin na musamman ne_ "
Jan jikin ta tayi ahankali ta bar jikinsa tare da juya masa baya tana 'ku'kk'uni.
Sarai yajita amma be kulata ba saboda hanzarin karya makara yin sallah ,sai da ya mi'ke kafin yace " _shine azhkar 'dinki na tashi daga shimfi'da ko?_
Shiru tayi masa aranta tayi tsuka sai ayyana irin yanda ya takurata takeyi, kullum baya barinta tayi bacci mai kyau in badan ma tana jin tsoro ba da ina zai ganta ma balle ya dame ta.
'Dan 'karamin tsaki tasake ja tare da gyara kwanciyar ta da kyau dan taji da'din yin wani baccin.
Ita kanta tasan tana da birgima dan ko Hannah nayi mata complaint akan hakan watarana wasu lokuta idan suka tashi daga bacci amma ita baya damun ta kamar yadda bata kula Hannah koda tayi mata mitan dan kuwa ita bata san ta yadda zata daina ba.
Ko da datake gida ma gadon ta babban size daddy ya sai mata da mummy tagaya masa cewa tana da birgima, bata son taji ta takura idan zata kwanta shiyasa ma take birgimar ta son ranta, duk kuwa wanda yace zai kwanta gado daya da ita sai ya dasawa zuciyar sa ha'kuri sa6anin hakan kuwa sai de kai kayi ta annabawa ka bar mata gadon.
Tunanin ta tsayawa yayi cak lokacin data jiyo muryar sa yana rero karatun littafi mai tsarki cikin dadda'dan sautin sa me sa nutsuwa ga fidda dukkan 'kal'kala da dokokin karatu, tana jin fitsari amma ta'ki tashi taje tayi dan kawai kar ta yanke jin karatun.
Har ya 'kare karatun tana nan kwance, tana ji har ya gama gaba 'daya ya mi'ke tsaye.
Tana ganin ya mi'ke agurin itama sai tayi hanzarin mi'kewa da saurin gaske ta shige bayi ko tura 'kofan ma batayi ba dan yanda fitsarin ya matsata ta ke saurin sau'ke shi.
Abbas da idanu ya rakata har ta shige bayin sannan ya jijjiga kansa afili yace " _Allah ya shirya_ " sannan ya dawo da hankalin sa ga abinda ke gaban sa.
Yau 'din bacci yakeji saboda baccin sa na daren jiya ka'dan ya samu yayi dan haka yau ko news 'din safe ma be tsaya gani ba kishingi'da.
Teemah brush kawai tayo tafito dan tafi son tayi wanka a'dakin ta saboda zatafi sakewa acan kuma ma ko dan saboda kayan dazata saka ma.
Inda yake tazo ta tsaya har bacci ma ya 'dan fara 'daukan sa, sai yaji alamun ta akusa dashi, share ta yayi ya cigaba da baccin sa sama-sama sai ya jiyo ta tana 'kiran sunan shi a hankali.
Idanun sa ya 'dan bu'de sai ya sau'ke su akanta, suna ha'da idanu sai tayi saurin fa'din " _ina_ _kwana Yayah_ "
" _Lafiya lau_ "
Yace da ita sai ya sake maida idanun sa ya rufe zaton sa ko dama gaisuwar ce.
Ganin haka sai tayi saurin sake furta " _Yayah_ !
" _wai me zan miki ne_ ? Yayi maganr a'dan tsawace.
Teemah sai ta nutsar da muryarta cikin natsuwa tace " _Yayah wayar ka zaka 'dan ban aro in 'kira su Mummy tun fa dana zo nan gidan ban 'kara_ _waya dasu ba_ "!
idanun sa still arufe yace
" _Ina taki wayar_ ?
Ya sake tambayarta sai tace " _ni bangani ba bansan ko tana gida ba_ "
Baya son dogon surutu dan haka sai ya nuna mata wayar tasa inda take.
Teemah 'dauka tayi ta koma parlour ta 'kira layin Mummy kamar yanda taga an rubuta awayar, bayan sun gaisa da ita sai ta ha'da ta da su Anty har ma da Ummah.
Inda duk suke 'kara yi mata tuni akan biyayyar aure da bin dokar sa, Ummah ce ka'dai data kar6i wayar taringa ce da ita tayi ha'kurin zama da mijin ta.
Cikin farin ciki suka 'kare wayar, bata maida masa wayar ba sai ma zaman ta data gyara zuwa kwanciya tayi pillow da hannun kujera.
Galleryn sa ta shige ta ringa bi tana kallon pictures 'dinsa dama wa'danda ba nasa ba.
Cikin haka taci karo da pic 'din wata mai kama da ita tana bacci, ganin kamar su da ita ne yasa ta tsaya 'karewa pic 'din kallo sai kuma tafara ganin kamar ita ce bawata daban ba, amma ta kasa tantance asalin gaskiyan waye ce a photon dan haka sai ta tashi tanufi wurinsa tana me 'kara kallon fuskan wayar domin tabbatar wa.
Data kasa fahimta sai kawai ta bari akan wata daban 'din ce ba ita ba, domin kuwa ita bata san lokacin da akayi pic 'din ba, amma bari ta tambaye shi.
Tun kan ta 'karasa cikin 'dakin tafara 'kiran sunan shi dolen sa ya yanke baccin ya sake bu'de idanun sa tare da fa'din " _ya akayi_ ?
Kamar an korota tace dashi
" _Yayah kalli pic 'din wata awayar ka me kama dani_ ?
Tayi maganar tana me sake kallon cikin wayar.
Beyi mamaki ba dan yasan yana da pix 'dinta daya dauka da hannun sa wanda ita kanta bata ma san da zaman su ba.
Amma duk da haka
Abbas sai yace da ita
" _ingani_ "!
Dayake yana kusan tsakiyan gadon ne shiyasa sai da ta hau saman gadon ta zauna kafin ta nuna masa.
Abbas be kar6i wayar ba sai ya 'dago kansa ya maida kan cinyar ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 47 Chapter of 67