Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
duk da laifinta ma tunda take biyeshi gashi sai 6ata musu lokaci yake abanza. Ba ita ta 'kare wayar ba sai 11:28am wanda tana cire wayar akunnanta Teemah taja tsaki tare da banka mata harara. Hannah murmushi tayi tace mata " _ya haka ne 'yan mata, let me be please ko dan ke baki san so ba ko? yes na_ _tabbata hakane, shiyasa ma naga kike wani banka_ _min harara..._ " Dakatar da ita Teemah tayi cikin jin haushi da fa'din " _ban san so ba kika_ _ce_ ? _Karki manta fah har aure nayi kinga kuwa 'karshen sanin so kenan ko_ " Dariya ka'dan Hannah tayi idanunta akan wayarta tace " _wancan ai is different, aure kikayi amma ba soyayya ba, na tabbata duk ranar da soyayya ta kamaki zaki gane cewa nawa wasa ne, wancen auren kin ai bashi da bambanci da babu,_ _ehh toh kuma, bansani ba kam ko kafin ya rasu ya koya miki soyayyar shi, kuma fah ba mamaki dan yanda naga kika_ _rin'ka kuka kina damuwa da rashin san nan ze yiwu son mijin naki ke damunki......._ Mi'kewa tsaye Teemah tayi tace " _Ya isa dan Allah Hannah kitashi mutafi ni surutun ya ishe ni haka_ " Tayi maganar tana 'ko'karin 'daukar mayafinta. Ganin ko motsi Hannah batayi ba yasa Teemah taja tsaki ka'dan tace " _Haba dan Allah kina gani ko Hannah lokaci na tafiya salan Yayah ya sake hanamu fita ko me_ ? Tana gama fadin haka ta nufi gaban mirror tasake duba jikinta ganin batada matsala yasa ta dauki turare kawai tasake feshe jikinta dashi. Sai lokacin Hannah kuma ta ajiye wayar tata ta sau'ka a agadon tana dariya tare da fa'din " _da kin barni na fa'di gaskiya ai yarinya_ " Juyawa Teemah tayi tace " _Ni dai muje dan_ _Allah, inkin gama ki sameni wajen Ummah._ " Teemah ta fa'di tare da barin 'dakin gaba daya. Hannah kam Teemah na fita ta janyo wayarta tacigaba da chat 'din da takeyi da Bilal. Tana isa parloun ta hango Ummah zaune akan kujera nesa ka'dan da kujerar dake gefenta kuma Yayah Abbas ne zaune suna 'dan hira. Kallo 'daya Teemah tayi masa sai ta 'dauke kanta, sanye yake cikin black trouser da wata longslip ash colour me zanen ba'ki layi-layi ajiki, sosai kayan sukayi masa kyau suka kar6eshi. Kirjinta taji yana bugawa wanda hakan yayi sanadin rage mata speed 'din tafiyarta, ahankali ta 'karaso har inda suke 'din ta zauna gefen Ummah, sai da ta iso ma sannan taji mahaukacin 'kamshin turarensa mai da'di ya bigi hancinta, daya ha'du da nata 'kamshin kuwa sai ya riki'de ya bada wani 'kamshi me 'kayatarwa, Ummah ce ka'dai zatayi iya bayyana hakan saboda ita ce atsakaninsu. Abbas kam yi yayi kamar be ganta ba, amma Allah ne ka'dai yasan yanda zuciyarsa ta yaba da yarinyar, sosai yaga zallan kyaun ta ayau 'din dan purple atamfar data saka ba 'karamin fito da ita yayi ba. " _Har kun gama_ _shiryawa ne_ ? Ummah ta tambayeta bayan ta maida dukkan hankalinta zuwa ga Teemah. Kai Teemah ta 'daga mata alamar " _ehh_ " Kasancewar sun gaisa da Ummahn dasafe Abbas ne kawai basu gaisa ba dan shi ba'a zuwa 'dakinsa haka kawai dan gaisuwa idan ba shine yanemi mutun ba toh sai de inya fito ka gaisheshi, hakan yasa ta 'dan 'dago kanta ka'dan tace " _ina kwana Yayah_ ! Be amsa ba sai da ya 'dago shima ya kalleta kafin ya amsa da fa'din " _lafiya 'kalau_ ." Bata 'kara wata gaisuwar ba dan tasan ko tayi ma ba sake amsata zaiyi ba. Abbas kam yanzu kasa 'dauke idanunsa yayi akanta Allah ma sai ya taimakeshi Ummah ba shi take kallo ba hankalinta nakan Teemah ne, Teemahn kuwa kanta na kasa shiyasa ma yasamu chance 'din kare mata kallo hankalinsa kwance. " _Dan Allah Fateemah inkun je_ _karki biyewa Hannah kinji, nasanta iyayi gareta gashi inta fita shopping tana da'dewa kafin ta dawo kamar zata na'do komai pls_ _karki biyeta Fateemah ku dawo_ _da wuri kinji Antynki ma tana hanya yau zata zo_ ? Ummah ce tayi maganar cikin sigar lallami. Kai Teemah ta 'daga mata alamar " _toh_ " Tana murmushi dajin cewa Anty na hanya sai de gaba 'daya jitake ta takura da zaman, hakan yasata lafewa ajikin Ummah kamar wata 'yar yarinya 'karama. Muryar Abbas suka jiyo yana fa'din " _wai Ummah ina zasu ne ba fah na son yawon nan ni_ " 'Dagowa Teemah tayi da mamaki ta kalleshi suna ha'da idanu kuwa sai ta kauda kanta gefe tare da turo baki aranta tace _lallai ma Yayan nan, bacin shine jiya ya hanamu fita yace sai yau kuma da_ _yau 'din tayi sai_ _yawani ce be san da_ _zancen ba_ . Ummah tariga tasan halinsa na nuna ko'in kula akan abubuwa shiyasa ma bata meda zancen baya ba duk da tasan yasan da batun fitan amma sai kawai tace masa " _Shopping zasu je ko_ _zaka kaimin_ _su_ " " _Ni kuma Ummah? Inada inda zani fah_ " " _Nasani ai Abbas naga akn hanya shiyasa_ " ummah ce ta fa'di hakan tana kallonsa. Yana so yace ina driver amma sai yaji bakinsa yayi masa nawi, kawai sai ya koma baya ya ha'da jikinsa da jikin kujera yayi wa Ummahn shiru, minti 'daya be cika ba sai ga Hannah ta fito cikin 'dan sauri-sauri ta nufo su. Sai da ta gaida Yayan kafin tace da Teemah su tafi. Dayake alraedy Ummah ta sallame su inda ta tura ma Hannah ku'din shopping 'din a account bata basu cash ba. Tashi Teemah tayi suka yiwa Ummah sallama , Ummah nata yi musu addu'ar Allah ya bada sa'a suka amsa da (Ameen) kafin suka nufi 'kofar fita. Abbas ma tashi yayi ya bi bayansu yana wannan 'kasaitacciyar tafiyar nan tasa me birgewa. Ahanya yazo ya wuche su Teemah nayi mata gulmar wai shi ai zai kaisu. Haushin ha'da su da Ummah tayi Hannah taji dan tasan ba barinsu zaiyi su sake ba. Koda suka isa jikin motar ma Hannah 'kin shiga gaba tayi dan har yanzu basu gama da Bilal ba chat sukeyi dashi shiyasa ma bata son shiga gaban don tsoro takeji kar Abbas ya kamata. Muhawara suka tsaya yi dan Teemah ma 'kin shiga gaba tayi sai da ya daka musu tsawa kafin kowa tayi saurin bu'dewa tashiga. Koda ya kai sun kuwa 'kin barin su yayi sai da yaga sun gama yabiya ku'din kafin yasako su agaba suka dawo gida. Shopping sosai sukayi dan suna da ishashshen ku'di a account 'din Hannah shiyasa ma suka saki ransu suka jidi tarkace harda na banza, cikin sa'a kuwa sai Abbas ma ya biya bill 'din. Koda suka isa gida kowa 'diban kayan yayi, Hannah ce tafara 'diba ta wuche ciki, koda Teemah ta 'diba ta fara tafiya kuwa kasawa tayi sai da ta ajiye dan wanda Hannah ta bar mata sunfi yawa. Numfashi take sau'kewa ahankali tana watsa hannu ga dukkan alamu zafi suke mata. Tana 'ko'karin sake 'dauka ta tsinkayo muryarsa yana fa'din " _idan bazaki iya ba dole sai kin 'dauka duka lokaci 'daya ne_ ? Sai lokacin ma tunanin hakan yazo mata dan haka sai ta raba kayan ta 'dauki ka'dan ta nufi ciki inda ta bar sauran awurin akan inta dawo ta 'karasa 'dauka. Tana cikin tafiya taga yazo ya wuche ta hannunsa da ragowar kayan, bin bayansa tayi sai ya kasance kusan tare tafiyar tasu take. Yana shiga parloun kuwa itama ta 6ullo sai ya kasance atare suka shigo. Anty na saitin 'kofa ne dan haka ita tafara ganinsu take kuwa taga dacewar kasancewarsu a inuwa 'daya, zata so Fateemahn tasamu jajirtaccen namiji irin Abbas wanda zai kula da rayuwarta ba kamar yanda ta so cin zarafinta abaya ba. Teemah na shigowa idanunta kan Anty ya sau'ka ai bata san lokacin data sake kayan ta nufe ta da gudu ba ta fa'da jikinta. Abbas bin ta yayi da kallo yana mamakin hakan kuma, wanda sai alokacin shi kuma ya hango abinda yasa Teemahn gudu. Ahankali ya 'karaso bayan yayi 'ko'karin danne ba'kin cikinsa ya yi mata barka da zuwa sannan ya ajiye kayan su Teemah ya shige ciki. Anty bakinta kamar gonar auduga ganin Fateemah ta warware. " _Anty dagaske dama ashe zaki zo_ ? Ta tambaya tana dariya. Antyn ma dariyar tayi tace " _zanzo mana Fateemah bani na fa'da miki ba_ " " _Mummy ma tace zata zo ai itama_ " Cewar Teemah Washe baki Anty tayi tace " _Allah ya kawota lafiya ashe shiyasa naga bakinki ya'ki rufuwa duk murnar za'a ga Mummy ne?_ " Dariya dukkansu suka sanya har Ummah Teemah ce ta 'karasa da fa'din " _harda kema ai Anty_ " Bayan sun gama dariyar ne Ummah tayi mata bayanin cewa ai Mummyn ba yau zata taso ba sai zuwa gobe in Allah ya kaimu. Hannah kam tuntuni ta shige ciki tunda ta gaida Antyn tayi shigewar ta dayake dama ita bason matar takeyi ba. Ranar kam Fateemah murna kamar ta tashi sama dan taga Antyn ta. Awurinta ta wuni tabi tacika ta surutu har yamma suna tare da 'kyar Ummah ta korata dan Antyn ta samu ta 'dan huta. Da daren ranar Daddyn Abuja ya dawo, Abbas kam beji da'din haka ba danshi tsoron ha'duwa dashi yakeyi dama kafin yazo ma sai da ya tabbatar baya gari kafin ya zo ashe ma yakusan dawowa. Daya san haka kuwa da ya koma abinsa tun da safe. Ai kuwa da daren ya gama shirinsa da sassafe ya fito yaje ya gaida daddyn yayi masa sallama. Daddy yariga ya fahimce shi ayanzu be 6oye ba kuwa yace masa " _wato kana guduna ne ko Abbas_ ? 'kasa yayi da kansa yace " _ah ah Daddy bahaka bane dama yau 'din na shirya komawa_ " Daddyn ma ce masa yayi " _Toh ba komai, Allah ya bada sa'a amma karka manta kadawo da wuri domin nextweek za'a 'daura auren ka nariga nagama shirya komai ranar kawai ake jira tazo, sai ka fara shiri_ ". _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~Dedicated to my~ ❀ *Bismillahir rahmanir raheem* _Do not think about the past..... Accept the Present..... Think for the Future....nd face tomorrow with a sweet and beautiful smile._ πŸ…Ώ *73* Abbas a firgice ya 'dago idanunsa ya sau'ke su akan Daddy, Daddy kam ko ajikinsa dan yana gama fa'din abinda ze fa'da ya shige ciki. Motsi me kyau Abbas kasawa yayi sai de yabi bayan Daddy da kallo da idanunsa da suka gama riki'de wa zuwa ja, har ya shige cikin kuwa Abbas be daina kallon 'kofar ba tsawon mintina biyar kafin ya tashi ahankali 'kafafunsa ma nauyi suka masa da 'kyar yake 'daga su ya nufi 6angaren Ummah. Zuciyarsa ce kawai ke beating da 'karfi ajikinsa bayaga haka kuwa gaba 'daya jikinsa yayi sanyi 'kalau. Fasa zuwa wurin Ummah dan yi mata sallamar yayi kawai sai ya wuce 'dakin sa ya zauna a kujera tare da dafe kansa. Tsawon mintina yana a haka shi ka'dai yasan me yake ji azuciyarsa baya fatan abinda Daddy ya fa'da ya kasance gaskiya, aure!......aure kuma da waye haka toh? Yana jin wannan karan kam ba ze sake yin saken da zata ta kubce masa ba, ba ze 'ki yiwa Daddy biyayya ba amma shima zai auri za6insa koda daga baya ne. Su Teemah ne yau a kitchen suna aikin breakfast ita da Hannah, sunayi suna 'dan ta6a hira inda duk hirar tasu Hannah ce 'kwa'kulo ta wani lokaci har fa'da sukeyi in maganar Hannah ya bawa Teemah haushi garin haka ruwan zafin jikin marfin tukunya ya zuba wa Hannah a 'kafarta. Tare da su Ummah da Anty suka ci breakfast 'din, bayan gamawar su ne Ummah ta 'dauki na Daddy tace zata kai masa, Anty ne tace da su Hannah sukai na Yayansu ma tun da be fito an karya dashi ba, take Ummah ta hana tace abarshi yanzu akaran banza zai koro min yara na tace abari sai yazo dakan sa dan baya son ana damunsa idan yana 'dakinsa, dayake bata san da batun tafiyar sa ba. Koda takai na Daddyn kuwa ta same shi ne yana amsa waya hakan yasa ta gama harha'da masa kafin ya kare wayar ta kawo center table ta ajiye masa agabansa, dan tasan shi be fiya cin brekfast akan dinning ba. Yana sau'ke wayar kuwa yace mata " ' _danki ya wuche ko?_ Da mamaki tace masa " _wani 'dan kuma Alhaji?_ Tea cup 'din dake gaban sa ya 'dauka ya 'dan kur6a ka'dan sannan ya cire daga bakin sa ya kalle ta da kyau ya ce " _Abbas nake nufi!"_ Mamakinta kasa 6oyuwa yayi har sai da ta bu'di baki ta tambaye shi dalili dan kuwa daya zo be cemata zai koma so soon haka ba, bayaga haka ma ko sallama be je yayi mata ba haka kawai sai take jin bata yarda ya tafin ba. Anan daddy yayi mata bayanin komai dake faruwa yace " ' _kilan haushi na da yake ji ne ya shafeki kema shiyasa har ya wuche be sanar da ke ba, amma ni kam yazo yayi min sallama da sunan zai koma bakin aikinsa ni kuwa ban dakatar dashi ba"_ Ummah kam gaba 'daya kanta sai ya kulle da maganar Daddyn bata fahimci komai ba dan haka sai tace " _Alhaji haushin ka na me Abbas zaiji kuma, ko de akwai wani 6oyayyan_ _abinda yafaru ne da_ _bansani ba_ " Juya kai Daddy yayi tare da fa'din " _Ehh toh kusan zance hakane gaskiya, sai de wannan al'amarin daban ne, kinsan dama ina shan yawan yi masa batun aure while shi kuma baya so, toh ina ganin dalilin kenan da ya sa ko ha'duwa dani be son yi shiyasa daya ga na dawo jiya sai shi kuma ya shirya komawa ayau, lokacin daya zo min sallama ni kuma nasanar dashi hukuncin dana riga na yanke, wanda dama ko da be zo Abuja ba ni zansa shi yazo saboda dole ana bu'katarsa_ _domin auren sa za'a 'daura a sati me zuwa in Allah ya kaimu_ " Ummah kam wani banbara'kwai taji maganar tamkar amafarki cewa tayi " _haba, haba Alhaji aure kuma da gaggawa haka ba wani shiri kamar_ _wani abin sirri, gaskiya be kamata ba, meyasa baza kayi hakuri ka 'kara masa lokaci ba_ ? " _Nagaji da jiran lokacin nasa ne shiyasa nayi haka, ke kanki kin san mun dad'e muna fama dashi a kan maganar nan, ba sai na gaya miki ba, amma yaron nan baya ma saka zance na acikin al'amuransa ballantana ya bata muhimmanci, sanadin haka ma kina gani wasan 6uya ya fara dani, duba fa kigani jiya-jiya na zo gidan ga_ _amma dan ya nuna min halinsa yau da sassafe sai ya zo min da batun komawa, duk nasan manufar sa ai tunda ni ne na haife shi, har yaushe zan ta maimaita masa abu iri 'daya kullum?_ Kwantar da murya Ummah tayi ta ringa bashi ha'kuri dan taga kamar beji da'din abinda Abbas 'din ya masa ba amma sai Daddy ya dakatar da ita da fa'din " _ni ai banda matsala dashi yanzu, na riga na yanke decision 'din dana ga yayi min and bazan fasa ba, munyi magana da Yah Kabiru akan haka kuma Alhamdulillah nasamu ya amince amma fah da 'kyar dan kin san shima 'dan partyn Abbas ne, wai taya zance ya auri bazarawa bayan shi be ta6a zama da mace ba"_ Zaro idanu Ummah tayi akansa tace " _Yah subhanallah, me kakae shirin fa'da ne Alhaji? dan Allah Alhaji ka daina wannan maganar ai ko ni nan ba yadda zanyi ba inde har bazawara kake nufin zai fara aura, wallahi bazan ta6a goyon bayan hakan ba, kayiwa Allah Alhaji ka dakatar da wannan zancen, zanyi magana dashi insha Allahu cikin 'kan'kanin lokaci zai zo maka da_ _magana mai kyau_ ............" Kafa'da Daddy ya 'dage alamar wannan ba damuwar sa bace shi, sannan yace " _ai da zaiyi hakan da ya da'de dayi tun ma ba azo wannan_ _matakin ba daya da'de dayi tun abaya, kuma da_ _kike cewa wai bazawara menene....ki gaya min auren bazawaran haramun ne_ ? Dolenta ta jijjiga kanta domin tasan bata da hujjan haramtashi tunda annabin mu haka yayi. Duk da haka sai tace " _Amma dai Alhaji ka duba lamarin kaima dan Allah, dududu nawa Muhammad 'din yake ne har ayanzun fa be gama cika shekara talatin ba, amma kake ta faman damun kanka da batun yayi aure har yanzu fa yana da sauran lokaci......._ Taran ta yayi da fa'din " _Bazaki gane bane ke, nifa da kike gani zaman sa hakan nan 'din ne sam banso, musamman da ya kasance aikinsa na yawo ne, sosai na yadda da tarbiyar yarona kuma na bana zarginsa ,dalili ma kenan da ya sanya na ke so naga yana da iyalin kansa dan gudun_ _kar wata 6araka ta 6ullo daga baya shiyasa nake son taran ta da wuri_ , _dan Adam duk 'dan Adam ne, hankali na zaifi kwanciya sosai idan ya_ _kasance yana_ _da iyali_ " Kauda kai Ummah tayi gefe dan ta lura Daddyn ba canja ra'ayi zaiyi ba sai tace " _Toh Alhaji in kuma iyalin ne dole sai ya kasance bazawara_ ? 'Dan 6ata rai Daddy yayi ka'dan yace mata " _Kinsan banason musu ko_ ? Sai tace " _Kayi hakuri Alhaji_ " " _bana so na sake jin kin fa'di haka, inada iko akan yarana shiyasa na yanke hukunci, kuma nasan dukkansu zasu min biyayya, kuma babu fashi auren nan da iznin Allah sai anyishi, iin kuwa_ _har kikaga ba'a 'daura auren yaron nan da Fateemah ba to ikon Allah ne ka'dai_ _ya hana hakan faruwa_ " Shiru Ummah tayi tana juya zancen a 'kwa'kwalwarta dake cushe tab da tashin hankali, bata sake furta masa komai ganin kamar maganganun nata basu da wani amfani dan ga dukkan alamu wannan mutumin bashi da niyyan sauya ra'ayi, tsawon da'kiku tana ahaka yayin da da Daddy ke ta shan tea 'dinsa cikin kwanciyar hankali, can Ummah ta mi'ke tsaye jikinta sanyi 'kalau ta nufi hanyar barin 'dakin tare da fa'din " _Allah ya kyauta_ " Daf da zata fita ta tsinkayo muryarsa yana fa'din " _baki tambayi wacece yarinyar ba kike shirin tafiya kuma_ ? Juyowa tayi ta kalleshi sannan tace " _babu amfani ai tunda ba saninta nayi ba, sunan ta danaji ma ka'dai ya_ _isheni_ ........" Da sauri ya tare ta da fa'din " _who told u that jin sunan ta ka'dai ya ishe ki?, Fateemah ce fah , Fateemahn gidan_ _nan_ !" Ummah najin haka ta washe baki tace " _haba dan Allah Alhaji , gaskiya baka kyauta min ba Fateemah ce shine_ _kuma ka barni nake ta 6ata bakina abanza_ ? Murmushi Daddy ya mata yace " _yanzu kam ai kinji sai kuje ku fara shirye-shirye dan nasan ba'a rabaku da shi_ " Yana gama fa'din haka yaci gaba da cin abincin sa. Ummah ce ma ta 'kara fa'din " _Shirye- shirye sosai ma_ _kuwa_ " tare da barin 'dakin. Daga wurin Daddy Ummah direct 6angaren Abbas ta wuce, bata same shi a palournsa ba dan haka sai ta nufi ciki da sallamar ta inda tasame shi zaune abakin gado sanye da dogon wandon jeans da farin singlet , bazaka ta6a gane yanayin da yake ciki ba in ba kasani ba, sa6anin Ummah da suna ha'da idanu dashi ta fahimci ba dai-dai yake ba. Da sauri ta 'karasa kusa dashi ta 'kira sunanshi. Jin yanda tayi maganar ne ya sashi 'ka'kalo murmushin dole ya sanyawa fuskar sa tare da 'dagowa ya kalleta amma be tsawaita ba ya kauda kansa gefe dan ba ya son ta fahimci halin dayake ciki. Da 'kyar ya bu'di baki yace " _ina kwana Ummah_ ? Da " _lafiya 'kalau_ " ta amsa masa, kafin ta sake yin wata magana kuwa ya tareta da fa'din " _Ummah baki bari naje ba sai kika zo da kanki kuma_ ? Cewa tayi " _bakomai ai duk 'dayane_" sannan ta 'kara da fa'din " _u look tensed Abbas meke faruwa ne_ ? Abbas kansa ya shafa yace " _ba komai fah Ummah kawai na tashi da ciwon kai ne yau_ _'din_ " Tace " _Ahakan kuma da kace zaka hau hanya_ ? Shiru yayi mata beyi magana ba. Ummahn ma sai ta zauna a gefen sa tare da fa'din " _look Abbas, mahaifinka yagaya min cewa nextweek za'a 'daura aurenka, hakane ko_ ? Cemata yayi " _Haka nima haka yagaya min 'dazu_ " Tace " _good, kasan me nake so da kai_ ? 'Dagowa yayi kawai ya kalleta sai taci gaba da fa'din " _banson ka sanyawa raka damuwa da wannan batun balle har yayi affecting al'amuranka dan Allah, ni nan inada_ _tabbacin auren ka alkhairi ne Abbas kuma ha'din Allah ne, da izninsa kuwa bazaka ta6a yin kuka da Fateemah ba, zakaji da'din auranka insha Allahu domin na yadda da tarbiyar Fateemah 'dari bisa 'dari kuma kaima kanka shaida ne akan haka......."_ Tun anan kan Abbas ya fara yi masa nauyi be san wace Fateemah bace amma yanaji ajikinsa kamar ya santa. Har Ummah tagama surutunta ma be jiba hankalinsa duk ya 'dauku ga tunanin ko wacece yarinyar sai ya ji Ummah na sake fa'din "......... _please ka cire damuwar nan aranka kaji_ ? Ahankali bakinsa ya furta " _insha Allahu_ " Dan be san me ze ce da Ummah ba bayaga haka. Ummah kam tashi tayi tsaye tana fa'din " _yauwa babana Allah ubangiji ya albarkakaci rayuwarku gaba 'daya ya sanya haske cikin al'amuranku"_ Da " _Ameen-Ameen_ " ya amsa mata. Daga nan tayi hanyar fita tana fa'din " _yaran nan zasu kawo maka breakfast 'dinka yanzu sai ka samu ka 'dan ta6a please ko ka'danne_ " Shikam yanzu ba breakfast bane damuwar sa maganganun Ummah ne ke masa yawo a 'kwa'kwalwa, so yake yasan wacce Fateemah ce haka da har mahaifiyarsa ma da kanta ta yadda da ita har kuma take ikirarin shima shaida ne akan halinta haka?. Wani sanyi yaji ya lullu6eshi tare da ratsawa har cikin zuciyarsa wanda hakan ya sashi lumshe idanu. Be san wacce yarinya bace amma ji yayi zuciyar sa tayi na'am da batun auren nata, azahiri kuwa sam bahaka bane domin 'kwakwalwar sa bata daidaita ba har yanzu yakasa tantance yanayin da ya shiga, yafi so ya san yarinyar kafin komai yabiyo baya, Ummah yakamata ya tambaya amma yakasa aikata hakan yana gani harta tayi tafiyarta. Tunda Ummah tafa'di sunan yarinyar ya 'danji dai-dai damuwar sa kaso hamsin duk ya kau, natsuwa yaji ya 'dan shige shi ka'dan da be san dalili ba, shi kansa yana so yaji da'din auransa kamar yadda Ummah tayi masa fata sai de kafin hakan ya kamata yasan yarinyar tukunna. ***** ' Bangaren Mummy kuwa yau ta gama duk wani shirin ta na shigowa Naija, dama tun jiya taso ta taho amma wani sabon al'amari data ji daga bakin Daddyn Teemah sai yasa ta fasawa a jiyan kawai ta shiga kasuwa ta bugo siyayya na fitan hankali sai yau ne take shirin tahowa da 6oyayyen farin cikinta azuci da Daddy ne ka'dai yasan tana ciki. Sun rabu da Daddy akan shima yana bayanta nan da 'yan kwanaki, da kansa shine ma ya rakata airport har se dayaga tashin su kafin ya koma gida. Abbas na zaune har yanzu abakin gadon motsin kirki ma bayayi kamar an dasashi, ringing 'din wayarsa da yajiyo a parlour ne ya fargar dashi amma be ko motsa ba balle ya je ga wayar tasa. Sai da yasake jin ringing karo na biyu kafin ya tashi tare da yin tsaki ka'dan dan shi ayanzu besan damuwa wanda yake ciki ma ka'dai yana jin ya isheshi. Ganin sunan B-Daddy da yayi akan fuskar wayar ne yasashi 'dagawa da sauri amma kafin yayi receive har 'kiran ya yanke dan haka sai yabi bayan 'kiran tare da zama akan 'daya daga cikin kujerun 'dakin, ringing 'daya na biyu Daddy ya 'dauka Abbas ne yayi saurin yi masa sallama. Daddy ma amsawa yayi daga 'dayan 6angaren tare da fa'din " _na 'kira baka 'daga ba_ ? " _Afuwan Daddy bana kusa ne wallahi_ " Ya 'kara da fa'din " _Daddy kana can ana shirin yimin aure ba shiri_ ? Murmushi Daddy yayi jin ya maida abin kamar wasa bayan acikin muryarsa ma zaka fahimci 'kuncin dake tattare da shi. Yace masa " _Nima haka sama ta ka labarin yazo min, Hassan ne ya 'ka'kabo mana_ , _nayi 'ko'karin hana dan ban goyi bayan al'amarin ba amma Hassan ya dage 'karshe dole sai da na amince,

Chapter 41 of 67