Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tunda yasan ba halinta bane wannan tsirfe-tsirfen, sam bai san inda ta aro hakan ya ya6a shi cikin rayuwar ta ba. Teemah kuwa data ga yayi shiru ya shareta bayan abinda ya gama furtawan sai kawai ta sanya masa kuka tana fa'din "Allah Yayah ni fa yunwa nake ji kuma pepper soup 'din Ummah nake son ci......" Tana mai cigaba da sheshshe'ka tayi maganar cike da sakalci da shagwa6a. Kallon "kin isheni" yayi mata tare da ha'de ransa amma hakan bai wani yi tasiri ba dan tana ganin hakan ma sai ta 'kara sautin kukan ta fiye da na baya kuma still kanta na jikinsa. Abbas system 'din ya rufe da 'karfi dan takaici sannan ya kalle ta, sosai ya tsani kukan nata baya so ko ka'dan amma bai san meyasa rigimar Fateeemah ya kasa barin ta ba har yanzu sam ita bata sanin girman ta. Wani lokaci idan tayi masa wani abin ji yake as if tafi kowa wayo a duniya amma kar kaso kaga wurin rigimar ta har sai ta hana shi natsuwa da sukuni idan ta fara domin kuwa 'daga masa hankali take yi ta kuma hana kanta samun natsuwa itama. Ganin bata da niyyan sararawa sai ya kai hannu da niyyan kamo hannun ta dan ya lallashe ta, Teemah kam sai ta fisge hannun nata da 'karfi ta kawar gefe tana jin in dai ba cewa zai yi zai kawo mata ba to ita babu ruwan ta. Yanda tayin sai ya bawa Abbas haushi take sai yaji wani iri a ransa, gashi har yanzu bata daina kukan ba sai ma 'kara volume ta keyi duk ta cukuikuye shi sai ya rasa yanda zaiyi da itama gaba 'daya he had no choice than ya bu'de mata idanu dan haka da 'dan 'karfi yace " Wai ni kam ni na saki jin yunwan kika dameni haka? ba fa na son iyayi ina gaya miki" Itama Teemah kamar an fizge ta sai tace "kaine mana kaine kasani jin yunwa.....kuma sai nacgaya ka da Daddy tunda kullum masifa kake min" Shiru yayai yana kallon ta tana ci gaba da kukan ta wanda maimakon ya ragu "ah ah sai ma 'karuwa da yake yi akan nada. Wata uwar tsawa ya daka mata wanda har sai da ta firgita in da yace " Shut up da Allah! Haba ths is too much, abincin da ba yau akayi ba not even yesterday shine zaki wani ce shi kike son ci? A ina zan samo miki bacin kinsan Ummahn ma kanta ba nan take ba? For God sake Zahra ki barni na huta ki sarara min dan Allah......in ba haka ba zaneki zanyi idan kika isheni.......baga can kitchen ba kije kiyi duk abinda kike so mana ko tsabar kin raina ni ne yasa kike yi min hakan.......?" Teemah kam cak kukan ta ya tsaya tun lokacin daya fara masifar, sanadiyyan wani motsi da taji a cikin ta na ban mamaki da bata ta6a jin irin sa ba tun da tasan rayuwar ta. Taso ta share amma da taji wani motsin na biyu tamkar an harbe ta a cikin ai bata san lokacin data tashi ta zauna ba dafe da cikin nata ta furta " Yah ilahi...Yayah cikina motsi yake yi...., na shiga uku mutuwa zanyi inaga ni kam" Sai ta 'kara sanya wani sabon kukan. Wannan dalilin ne ya sanya shi yanke masifar da yakeyi shima ya dawo da hankalin sa gareta da mamaki ya 'dage gira 'daya sama take kuwa salon maganar tasa ta canza da tambayar " Motsi kuma kamar yaya? Yana 'ko'karin dafo cikin ta nata shima yayi maganar. Cikin kukan tace dashi "Allah ni...ma bansani ba Yayah.... ji naimyi cikin na harbi na ni kam mutuwa zanyi Yayah pkease ka taimake ni" Abbas take jikin sa yayi sanyi dajin irin kalaman nata wanda daga ji ma kasan iya gaskiyar ta take fa'di ba'a baki bane kawai, domin yanayin 'karyar ta ma daban ne. Dan duk wanda yasan Teemah toh yasan cewa bata fiya 'karya ba ita balle wannan da yasan cewa babu mamaki in dai cikin Teemah ne abinda yafi haka ma zai yi ko dan abubuwan data ke yawan 'dirka masa. Tsaban yanda ta tsorata da abin kallo 'daya zaka yi mata ka fahimci a firgice take motsin kirki ma 'kinyi tayi hannun ta dafe da cikin ta har yanzun tana kuma sau'kar da hawaye. Tashi yayi ya tsaya yana kallon ta ita kuwa kanta a 'kasa. Yana gwada kaiwan hannu jikin ta sai tayi saurin fa'dawa jikin sa ya rungume ta, itama ma kuma haka. Chance ya bata ta sha kukan ta shi kuma ya sa hannu acikin yana shafawa a hankali take wani tunani yazo ransa jin taurin dake marar ta ya 'karu fiye sa wanda ya taba ji kwanaki. Yin tunanin keda wuya sai ya cire ta a jikinsa ya ri'ke gefe da gefen kafa'dun ta yace "let's go to d hospital Zahra we need to see........" "Yayah.... Zatayi magana ya tare ta fa'din " shiiii.... Sai tayi shiru dan dole "Oyah hurry up canza dressing ina jiran ki now" *~_UR COMMENT IS GETTING LOW KO HUTU KUKE SO_~* ❓ _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/13, 8:01 AM] 🌸Salmerh🌸: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Allah ya raya mana Princess Fatima, Allah ubangiji ya haskaka rayuwar ta da hasken sa yasa cikon addini ce.(Ameeen)πŸ‘πŸ» @ Dr. khausar* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _A *true friend* sees d 1st tear, catches d 2nd one nd stops d 3rd.....they ar not d ones who ar there when it’s convenient only...... *True friends* ar also there when it’s not...Hold a true friend nd don't ever let them go coz *True friend* comes just once in a lifetime._ 🀞🏻 πŸ…Ώ *92* Abbas ma bai fiya barin ta tana shan za'ki ba saboda an gaya masa cewa hakan nada illah musamman ga mai ciki irin ta. Koda ya koma office kuwa baya yin cikakken 1hr ba tare da ya 'kira yaji lafiyar ta ba. Matan blocks 'din su ma na nan-nan da ita musamman saboda karamcin Abbas a wurin su. Bata aikin komai sai yi masa girki, duk kuwa da cewa tana son yi 'din amma Abbas hana ta yin komai yake yi sai dai wani lokacin ta saci jiki tayi idan taga baya nan. Amma da kansa yake yin komai a gidan. Matan block 'din su ma da yake yawancin su manyan mata ne so sai suke tausayin ta da ganin 'kan'kantar ta, su kansu duk ranar da sukayi katari da ita ta 'dauki tsintsiya hana ta suke yi. Cikin ta na da wata bakwai sannan ta sanar da Hannah a chat dan sosai zuciyar ta ta kasa daure rashin sanar da Hannah labarin cikin, duk iya 'ko'karin da ya kamata tayi amma ranta yakasa sakewa, inda suna cikin chat tace da ita " Hajiya ki fara shirin raino fa dan Matar Yayah nada ciki har na tsawon wata bakwai" Hannah kam wasa ta 'dauki abin dan haka sai itama tace " wacce matar Yayahn kenan kike magana? Kinsan ai ni bansan ya 'kara yin aure ba". Teemah bata ba ta amsa ba sai kawai ta 'kirata video call tana murmushi ta nuna mata cikin. Hannah mamaki, murna da farin ciki gaba 'daya sai suka hanata magana ta bu'de baki kawai tana kallon ta. Teemah ma kallon t take yi sai dai ita murmushi ne akan fuskar ta mai sanyi. Hannah nuna ta tayi tace wai dagaske ciki ne a jikin ki?" Teemah cikin ta k'ara nuna mata tace " ga zahiri kuwa kina gani Hajiya" Hannah ihun murna ta sanya tare da tashi ta nufi wurin Ummah tana 'kwala mata 'kira. Da sauri Teemah ta yanke 'kiran tare da kashe wayar ma gaba 'daya tana dariya. Taso ta 'kyale Hannah kawai sai dai taga suprise 'din baby kamar yanda take ganin take-taken Yayah, amma sai ta kasa jurewa saboda sam bata ga dacewan ace har tana da cikin daya kai ciki amma Hannah bata da labari ba. B'angaren Hannah kuwa tana isa wurin Ummah ta dago wayar tana fa'din " Ummah kalla kiga abin mamaki, Fateemah na da babban ciki tace min har ya kai 7months....." Gani tayi Teemah bata kan layi sai ta sake gwadawa amma baya tafiya, ta kira voice call shima akace mata switch up. Ummah kuwa gaba 'daya hankalin ta ta tattara ta mayar kan Hannah jin ta kusan samun jika, ganin Hannah na jan tsaki ne yasa ta tambayar ta " meya faru?" Sai Hannah tace " Wallahi Ummah kinga tayi disconnecting call 'din kuma na 'kira baya tafiya" Ranta duk a jagule tayi maganar ga dukkan alamu bataji da'din hakan ba. Ummah cewa tayi " amma kin tabbatar cewa cikin na ajikin ta?" Sai tace " Allah dagaske ciki ne Ummah ai ta nuna min kuma tace har 7month......" Taranta Ummah tayi da fa'din shikenan naji 'kira min mijin nata, tunda isheshshe ne shi wato har yayi wayon 6oye min abu irin wannan ko? 'Kira min shi da sauri zai zo yasame ni ne" Hannah ba tayi magana ba sai ta hau 'kiran nashi wayar amma cikin rashin sa'a sai na shin ma bai tafi ba. 'Dago wa tayita kalli Ummahn sannan tace " ba fa na samun sa Ummah shima 'din" "K'yale shi zuwa anjima may be za'a same shi" Hannah kam kasa hak'ura tayi ta ringa gwadawa nashi da na Teemah amma gaba d'aya ya 'ki shiga, abin ya 'kona ran Hannah sosai jitake tamkar tayi tsuntsuwa ta taho Ports a lokacin kawai dan taga Teemah. Teemah kuwa bata sani ba ashe da gangan Abbas ya'ki sanar mawa Ummah gudun kar ta uzzura masa akan ya maida ita gida dan yasan Ummah najin wannan labarin ba barin sa zata yi ya runtsa cikin kwanciyar hankali ba. Shikuwa yanzun sam baya so yaga yayi nisa da iyalin sa ba ma ya 'kaunar abinda zai kawo rabuwar koda kuwa menene shi. Sosai yake so ya cika rayuwar ta da zallan 'kauna da soyayya. Hatta hakkin sa da ke kanta daya zama dole ma daina kar6a yayi dan gani yake tamkar abin zai yi mata yawa ne, musamman ma da yake ya san kansa yanda yake galabaitar da ita a duk lokacin daya kusanceta shiyasa ma ya sau'ke mata wannan nauyin, sosai yayi 'ko'kari wajen ganin ya danne nashi bu'katan, in dai ba ita ta nema ba da kansa kam baya ta6a kusantar ta kuma itama Teemah yanzu da sau'ki ba sosai abin ke motsa mata ba sai tayi sati biyu zuwa uku ma bataji wani abu ya dame ta ba game da hakan, itama kuma bata sanyawa ranta damuwa ba musammn data ga cewa shima baya ra'ayin hakan sai itama take 'ko'karin binsa akan yadda yake so 'din duk da bai fito fili ya gaya mata dalilin daya sashi yin hakan ba amma tasan dai ba zai ta6a yin abu dan ya cutar da ita ba. Har kusan 2hrs Hannah bata gaji da 'kiran layin sa ba dan yanda ta 'kagu ta tabbatar da labarin, ga Ummah ma da nata masifan a gefe, da 'kyar suka same shi a nashi wayan har sai data sau'ke ajiyan zuciya data ji ya shiga, da murnar ta ta mi'kawa Ummah wayan tare da fa'din "yesss ya shiga Ummah". Ummah kar6a tayi da sauri ta sada wayar da kunnan ta da fatan Allah yasa abinda taji daga bakin Hannah ya kasance gaskiya ne. Abbas na office yaga 'kiran Hannah, bai san dalili ba amma haka kawai sai yaji zuciyar sa ta tsinke bawai dan basa waya ko bata 'kiran sa ba ah'ah, dan ko jiya ma sun gaisa da ita a waya amma haka kawai yau 'din ya tsinci kansa da fa'duwan gaba ganin 'kiran ta. 'Dauka yayi sannan ya kai kunnan sa, ba halin sa bane fara yin magana idan zaiyi waya matu'kar bada iyayen sa bane amma yau 'din sai yaji bakin sa ya furta sallama. Muryar Ummah yaji ta amsa sallamar tare da fa'din " Muhammad kaji kunya kai kam" Kai Abbas ya sosa duk da bai san laifin sa wurin Ummahn ba da har ta fa'di hakan amma sai yaji shi wani iri sai yace. " Afuwan Ummah, barka da war haka" Ummah bata bi ta kan gaisuwar tasa ba sai cewa tayi "Ina 'yata take?" Amsa ya bata da fa'din " tana gida Ummah ni na fita aiki ne". Ummah sake cewa tayi "Ina fatan dai lafiya take?" Sai yace "Ehh Ummah lafiyar ta 'kalau" " to masha Allah, yaushe zaka dawo min da ita gida dan gaskiya banaso ta haihu cikin inyamuran nan?" Cike da mamaki ya zaro idanu tare fa'din " haihuwa kuma Ummah? waye ya sanar da ke ciki gare ta?" D'an 6ata rai Ummah tayi tace da shi " Ni bana son shashanci Abbas tambayar ka nayi answer me kawai". Abbas sai ya lumshe idanu tare da shafo kansa sannan yace " Ummah ki bari watan haihuwar yayi mana sai in kawo ta...". Tun ma kafin ya idasa rufe bakin sa Ummah ta tareshi da fa'din " ban amince sam kama canza shawara" Shiru yayi yana jin wani iri a zuciyar sa tare sa tunanin yadda zai 6ullo mata, Ummah kam ganin yayi shirun ne yasa ta fa'din " ni dai ina jira nan da 2weeks in ga 'yata a gefe na, in ba haka ba kuwa zaka sha mamaki na Muhammad, domin da kaina zanzo har Rivers 'din in 'dauko ta". Ummah na gama fa'din haka ta yanke wayar ba tare da ta jira jin na bakin sa ba, dan ma abin ya ha'du mata da farin cikin jin labarin cikin shiyasa ma masifar batayi tsayi ba. Abbas kam da kallo ya bi wayar tare da mamakin inda Ummah tajiyo wannan labarin, yasan in ba Teemah ba babu wanda zai sanar da ita tunda kam shi babu wanda ya fa'din mawa. Lokacin daya koma gida sai ya tarar da ita har tayi masa abinci mai 'dan sau'ki, tuwon semo tayi da miyar egussi, sosai yake ya bawa 'ko'karin ta ta wannan fannin, domin shi ka'dai yasan yanda yake ji a duk lokacin daya tarar ta tanadar masa abinci koda kuwa wani iri ne sosai yake appreciating, dan ya fahimci bata wasa da abincin sa musamman data san cewa ba ya cin komai a waje so bata ta6a barin sa ya nemi abinci ya rasa ba, ko da kuwa mai sau'ki tana matu'kar 'ko'karin yi masa kuma yana yabawa da hakan. Haka idan ya dawo a kullum tana 'ko'karin ganin ta tayashi rage kayan jikin sa, a yana hana ta ma amma dole kullum bata barin sa, hatta wanka da wasu abubuwan idan ya kama duk tana taya shi, shima kuma ba laifi lokaci-lokaci ya kan yi mata massaging 'kafafuwan ta dan wani sa'in yana 'dan yin kumburi ka'dan. Sai da ya kammala da cin abincin kafin ya dube ta yace da ita " Ummah ta 'kirani". Teemah na jin haka sai ta zaro idanu waje tana kallansa, take sai ya gane rashin gaskiyar ta sai kuma tace " me tace maka kuma?" Shiru yayi shima ya zuba mata idanu. Duk da bawai yau ne karo na farko da Ummah ke 'kiran sa ba, kusan kullum sai sunyi waya da Ummah hatta ita Fateemah ma suna waya dukkan su da ita amma yanzun kallo 'daya zakayi mata ka fahimci ta shiga wani yanayi da jin 'kiran Ummah. Maimakon ya bata amsar tambayar ta ah ah sai yace da ita " mara kunya....ai na lura tunda kika samu cikin nan kika zama mara kunya kuma shine har da sanar da Ummah cewa kinyi ciki ko?" Kai ta kawar gefe tace " Ni fa bance mata ina da ciki ba". Sai yace " To a ina ta samu labari?" Shiru tayi masa tana 'kara ha'de goshin ta. Sai shine yaci gaba da fa'din " Ni dai let me tell u...idan kika kuskura kika haifamin baby mara kunya ko kuma mara son makaranta ni da kene". Hawaye ta fara tare da mi'kewa ta shige cikin bedroom taje ta zauna dirshan a 'kasan tiles tana zubda hawaye, ji take ranta babu da'di a duk lokacin da Yayah ya ambaci makaranta ko kuma yayi mata gugar zana da hakan, ta so ta yi 'din kamar yanda ya bu'kata amma sam takasa shigar da shi cikin ranta domin koka'dan babu niyyan a zuciyar ta, shiyasa ma ta ha'kura, amma a kullun addu'ah takeyi Allah ubangiji ya cire masa abin a ransa shima ko zata huta da mitar sa akan hakan. Abbas ma tashi yayi biyo bayan ta a 'dakin yazo ya zauna daga gaban ta ya fuskance ta, bai bi ta kan kukan nata ba illah tambaya da ya jefa mata inda ya sake fa'din " waye ya sanar da Ummah cewa da ciki a jikinki ai nasan kece kika fa'din mata". Ya 'karasa maganar tare da 'dage gira 'daya sama. Teemah kam da muryar kuka tace dashi " Ni dai bani bace sai ko in Hannah". Sai yace " ita Hannah a ina taji labarin ?" Teemah shiru tayi kawai tayi 'kasa da kanta wani hawayen na gangarowa, sai shine yaci gaba da fa'din " ai kema kin san tsakanin Hannah da Ummah dole ne idan taji sai ta gaya mata, gashi yanzu tace wai dole sai dai in maida ki Abuja wai bata son ki haihu a nan" Yanayin da ya 'karasa maganar ma kanaji kasan ransa baya son tafiyar koka'dan, amma sai tayi 'ko'kari wajen ganin ta ri'ke kukan da take yi tace dashi " duk 'daya ne ai Yayah da can da nan 'din ba wata matsala". Muryar sa da sanyi yace " kenan kema kinfi son can 'din ko?" Itama a hankali tace " ah'ah fa Yayah ba haka bane....". Sai ya tare ta da fadin " .......haka ne mana, kin fi son ki tafi ki barni ko tausayina bakiji ko?, yanzu fa idan ba kyanan komai ma ni zan rin'ka yi hatta abinci ma babu wanda zai na dafamin......". Bai ma 'karasa maganar ba ta sanya kuka inda cikin kukan tace " Yayah to ya zanyi ni kam, Allah inajin tausayin ka amma ai kaga Ummah ce da kanta ta nemi hakan ba yadda zamu yi ne shiyasa". Hannun ta ya kamo cikin nasa hannun yana murza 'yan yatsun ta cikin natsuwa yace " kawai kice mata ke ba yanzu zaki koma ba in taji daga bakin ki i'm sure zata ha'kura". Kai Teemah ta jijjiga masa tare da fa'din " Allah ni kam bazan iya ba Yayah, Ummah ce fa". Shiru yayi yana kallon ta ko da wasa bai son abin da zai raba su, sam baya son tayi nesa da shi amma kwatsam rana tsaka Ummah ke 'ko'karin shiga tsakanin su, bai san yadda zai yi ba amma gaskiya yana jin tamkar hakkinsa za'a shiga akana hakan, gashi ma tun kafin ranar tazo ya fara shiga wani hali na damuwa. Janyo ta yayi jikin sa ya share mata hawayen tare da rungumar ta a jikinsa sannan yace " kukan fa na menene haka Zahra?, ba kince ba kya son barina ba?". Da kai ta bashi amsa akamar "ehh" sai yaci gaba da fa'din " Kar ki damu kinji, ni duk abinda kike so shi zan miki, so ki kwantar da hankalin ki bana son kukan nan, ko kina son baby yayi miki dariya yace Momcyn shi cry-cry ce?" Kai ta jijjiga tana murmushi sai yace " to oyah wipe all da tears ur husby ll always be by ur side ok..." Da haka ya rarrashe ta har tayi shiru maganar ta wuce batare da sun tsayar da magana 'daya ba. ***** *Bayan sati 'daya* Zaune yake akan dadduma yana karatun al'qur'ani mai girma cikin sautin sa mai dad'i inda yake karanto suratul Anbiya'i. Abbas kenan da hakan ya riga ya zama jinin jikinsa a duk bayan kowacce sallar asubah ya kan zauna yayi karatun sa cikin natsuwa in da watarana suke yi da Fateema wataran kuwa shikad'ai yake abin sa musamman ma yanzu da baccin asubah ke yawan damun ta sanadin cikin. Wajaje 5:30am ne na safe, yayin da Teemah ta tashi ta shiga bathroom dan watso ruwa a jikin ta, domin wani yanayi da take jin kanta tunanin ta ko ruwan sanyin zai 'dan sanyaya mata, da 'dan 'karamin towel 'dinta ta fito 'daure a jikin ta bayan ta watso ruwan ta fito, a hankali take tafiya, da 'dan madaidaicin cikin ta a gaba ya 'dan 'dago daga cikin towel 'din, sai hips 'din ta da ya 'dan 'kara bu'duwa shima da mazaunan ta ta yadda bata isa tayi tafiya ba sai sun motsa. Duk kuwa da ta watsa ruwan amma koka'dan bata nasaran jin wani sauyi tattare da ita ba na daga cikin yanayin ta data keji sai ma abinda ya k'aru, ta rasa mai yasa hakan yanzun bata sani ba ko dan shi baya neman ta ne yake sata itan oho. Zuwa tayi ta zauna a gaban mirror tayi shiru tana kallon sa ta cikin madubin. Abbas dake faman karatun sa tamkar ance ya 'dago sai kuwa suka ha'da idanu ta cikin mirror 'din, Teemah sai ta lumshe ido ta yi 'kasa da kanta a hankali. Abbas kam tuni ya fahimci yanayin da take ciki da suka ha'de idanu, don tuni ya gama karantar ta zuwa yanzun ba sai ta bu'di baki ta sanar da shi yanayin da take ciki ba da kansa ma yake fahimta. Takaita karatun yayi tare da rufe Qur'anin ya dawo inda take ya tsugunna daga gabanta tare da kamo hannun ta ya ri'ke cikin nashi yana wasa da shi. Da idanu tabi hannun nasu sannan ta 'dago da kanta ta kalli fuskar shi. " Akwai matsala ne?". Ya tambayeta idanun su cikin na juna. Sai tayi saurin kawar da nata idanun tare da jijjiga mai kai alamar "ah ah" nufin ta ta 6oye masa damuwar da take ciki. Abbas kam murmushi yayi mata tare da maida hannun sa kan cikin ta ya dora sannan yace " Baby na na son gaidani fa naga yana ta waving min hands". Yanzun kam itama murmushin tayi jin shirgin 'karyan daya shirga wa abinda ke cikin cikin ta da be san mecece rayuwa ba balle ya nemi mahaifin sa. Abbas kam cikin towel 'din ya maida hannun sa wanda har sai da ya sata lumshe idanu dan yanda taji wani irin abu ya ziyar ce ta sakamakon hannun sa da taji kan cikin nata. A hankali ya ringa shafa cikin yayin da Teemah ma tabi kan hannun san da nata hannun suka cigaba da shafa cikin tare suna zuba murmushi, shi kam har 'kasan marar ta yayi da hannun sa a hankali yana mai cigaba da shafawa yana fa'din " Baby na Boss ne da alama tun da har yana yana da wayon son gaidani da sassafen nan" Teenah kam zuwa yanzun shiru tayi tana jin yadda yakeyi matan tasan ba wai dan baby bane kawai. Da haka a hankali ya dawo da hannun sa saman 'kirjin ta sai ma ya janye towel 'din tare da ha'de musu baki, sosai ya warware mata jiki da salon sa kafin ya d'auke ta zuwa kan bed. Abbas sai daya tabbatar ta gama satisfying sannan ya raba jikin sa da nata ya 'kyale ta dan be damu da kansa ba a yanzun, domin yasan ada ba 'karamin 'ko'kari tayi ba wajen 'daukan nashi bu'katun duk kuwa da cewa 'karama ce amma bata ta6a nuna gajiyawa da bu'katar sa ba, dan haka shima yanzun a cewar sa turn 'din sa ne dole zai 'daga mata 'kafa ba zai takurata ba har zuwa lokacin da zata sau'ke nauyin dake jikin ta. Kwance yake a gefenta yana 'ko'karin dai-dai ta nutsuwar sa wanda da 'kyar yake samun hakan domin matu'kar ya kusance ta hankalin sa sosai yake tashi, Teemah kanta tasan hakan har ma ta ta6a yi masa magana sai yayi mata musu ita kuwa ta san ba gaskiya yake fa'da mata ba dan ko be fa'da ba tasan me yake ciki, shiyasa ma cikin kwana

Chapter 60 of 67