Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tsinke da 'karfin gaske, har sai da ta rintse idanunta ta kuma dafe 'kirjinta da hannunta. Daga nan abubuwan da suka faru atsakanin su suka rin'ka dawo mata 'daya bayan 'daya...... Yah Abbas.....Rashin fara'arsa......Muguntarsa....Masifarsa.... Komai ma nashi yaringa dawo mata azuciya, juyi tayi zuwa 'dayan 6angaren yayin da ta tuno lokacin da Mahmud ya zo gidan su, basu wani 'dau lokaci ba suka saba da juna sa6anin Abbas da alokacin ma kullum sai sunyi fa'da dashi. Tashi tayi ta zauna abakin gadon ta cigaba da tunani haka kawai batare da tasan dalili ba taji zuciyarta tana mata comparing halayyar Abbas da Mahmud amma kwata-kwata ta kasa samun laifin Mahmud aranta ko 'daya sai de duk da haka zuciyarta takasa nutsuwa da maganar da suka gama da mahaifinta lokuta 'kalilan da suka gabata, sai take jin ma dama ba Yah Mahmud daddy ya za6a mata da sunan ta aura ba. Tashi tayi da gaggawa kamar wacce aka bawa umarni ta nufi wurin ajiyan kayanta sanadiyyar tuno wani abu da tayi, bincike tafarayi acikin kayan inda ta ringa ciro kayan da 'da'dd'aya tana zubo dasu 'kasa sai da ta ciro kusan rabi daga cikin kayan nata kafin ta samu abinda take nema 'din. Da sauri ta tattara ta dawo 'kasa akan tiles ta zubasu itama ta zauna dirshan agabansu. 'Ko'karin ha'da papers 'din takeyi amma har yanzu ta kasa ha'dasu, haushi hakan ya bata dan ayanzu damuwarta be wuce tasan miye acikin takardan ba da tun ranar daya batan takardan ta lalace da gumi, tun ranar taji ba'kin cikin rashin ganin abinda ta kardan ta 'kunsa ga dai alamun rubutun da akayi da biro tana gani amma gane ko menene sam ya gagare ta. Ko ta 'dan harha'da sai taga beyi yadda take so 'din ba ga dukkan alamu guri me muhimmancin ne ya fi ji'kuwa tun awancen ranar. Haushin bazata ta6a ganewan ba yasata ta dun'kula su tayi jifa dashi kamar zatayi kuka. Tana watsarwan kuwa sai tajiyo muryar mummy ta 'kira sunanta tare da 'karasowa cikin 'dakin nata ahankali. Tana ganin mummyn sai taji hawaye ya gangaro mata da bata san dalilinsa ba, tahowa tayi da sauri ta rungumo mummyn suka zauna abakin gado. Fatima bata sani ba ashe tun fara binciko kayan da Teeman tayi mummy ke tsaye tana kallon ta dama so take taji asalin ra'ayin ta akan maganar, koda tazo tasameta awancan halin kuwa sai ta tsaya karantar yanayinta tayi zaton ko wani abin ne daban yake faruwa , and now she's crying. Sai da ta yi kukanta kusan na mintina biyu kafin nan mummy ta 'dagota daga jikinta, atsare tasa ta tayi shiru kana tace tasanar da ita meke damunta, menene yasata kuka. Ido mummy ta zuba mata tana karantar yanayinta da kyau, yayin da Teemah ta maida kanta 'kasa kamar me jin kunyar ha'da idanu da mummyn sai kawai taci gaba da tsiyayar da hawaye, hawayen ma da sauri suke 6ul6ulowa dan koda mummy tayi 'ko'karin goge mata ma kasa tsayuwa suka yi dolenta ta barta . Sai da tasake maimaita tambayar tata kafin ahankali Teemah ta 'dago tace da ita " kirjina zafi yake min mummy" "Miye dalili" mummyn ta tambayeta. Hannu ta 'dago ta 'dora akan kirjin nata sannan taci gaba da fa'din " mummy dagaske daddy yakeyi wai aure zai min?" " miye saki zafin 'kirjin " mummyn tasake tambayarta maimakon ta bata amsar tambayar da Teemahn tayi mata. Sai tace itama bata sani ba, kawai de tana jin kamar bata son auren ne. " bakya son auren ko kuma Mahmud 'din ne bakyaso"? Mummyn tasake tambayarta idanunta kafe akan Teemah. " Nima fah bansani ba mummy nide kawai zafin nakeji a 'kirjina". Shiru sukayi dukkansu na 'dan wasu da'kiku sai mummyn tace mata ta share hawayenta kukan ya isa haka. Tambayarta mummy tasakeyi wai "meyasa ta amince wa mahaifinnata bayan tasan bataso. Goge hawayen tayi kamar yadda mummy ta bu'kata, amma kuma game da tambayar sai ta rasa amsar dazata bawa mummyn dan haka kawai sai tayi shiru. Ganin hakan da Teemah tayi tasan zaiyi wahala tasamu jin amsarta dan haka sai ta juya ta kallo cikin 'dakin inda Teemah ta zauna 'dazu. " wa'dancan 'kananun papers 'din fah na menene su kuma"? Juyawa Teema tayi ta kallo inda suke itama batare data yi niyyan fa'din komai game dasu ba. Fahimtar da mummy tayi cewa Teemahn bata da niyyan sanar da ita sai kawai ta mi'ke tsaye tace " inkin gama kisame ni apalour ina jiranki." Da kai Teemah ta amsa mata daga nan takama hanyar waje. Binta da idanu Teemah tayi harta 6acewa ganinta, daganan ta tashi sai ta nufi gurin data watsar da pieces 'din takaddun, ta tattare su gaba 'daya ta maida su can 'kar'kashin jerin kayan da suka rage bata wargaza ba. Tana 'kokarin fara gyara kayan sai ga Baabah Lami ta shigo da sallamarta tace "Hajiyarki tace kayanki sun zubo " Kai ta 'daga alamar "ehh" sannan ta matsa daga gurin kayan ta nufi hanyar bayi domin ta watsa ruwa dayake daman bata yi wanka ba lokacin da daddy yakirata. Daga ita sai towel tafito abayin, yayin da tabaro kayan data cire abayin domin wanki suke bu'kata. Fitowarta kuwa keda wuya Baabah Lami ta jefa mata tambayar wai yau kuwa lafiyarta ? "Uum lafiya ta 'kalau me kika gani"? tayi maganar tana 'ko'karin goge fuskarta da wani 'dan 'karamin wiper dake ri'ke ahannunta na dama . Baabah Lami shiru tayi taci gaba da gyaran kayan da takeyi, Teemah kuma sai ta wuce gaban madubi ta sake duba yananyin fuskarta daganan ta dawo inda kayan tan suke zube aciki tasamu wanda zata sanya sai ta koma 'daya 6angaren da tuntuni arufe yake ta bu'de shi ,bakomai aciki illah tarkacen inners 'dinta dasuke kala kala. Zura doguwar rigarta tayi bayan tasaka ta saka bra da pant ko kunyar Baabah Lami ma bata ji ba tayi shirinta abinta, tana gamawa kuwa ta zari mayafi ta fice a'dakin tare da cewa Baabah Lami " ina zuwa" ta nufi gurin mummy. Tana isa gurin mummyn ko gama daidai ta zamanta bata yi ba mummyn tace " yanzun muka gama waya da Abbas yace wai agaisheki" Murmushi ne ya kubce mata har sanda ha'kwaranta suka 'dan bayyana afili. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh*😍 [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all _cApTaIn_ _AbbAs Fans_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* To know that you do not know is the best. To pretend to know when you do not know is a disease. πŸ…Ώ *43* Har bata san lokacin da tace "Kuma mummy dakansa yace agai sheni? kai mummy ta 'daga mata, sai ta sake cewa " lallai Yah Abbas sai yau yaga dama ya tuna dani kenan" "Da in cemiki akayi ya manta dake ne? " ya manta dani mana mummy "! Teemah ta bawa mummy amsar tambayarta. Mummy bata 'kara kulata ba sai de afakaice take 'kara kula da yanayin ta saboda murmushin da tayi tun 'dazun yakasa barin kan fuskarta harma sai ya 6oye damuwar da take ciki 'dan lokuta ka'dan da suka gabata. Tausayi Teemahn take bawa mummy sosai zuwan yanzu ta gama harbo jirgin 'yartata sai de ga dukkan alamu ita kanta bata san me take ciki ba har yanzu, shiyasa kawai zataci gaba ro'kon Allah akan ya takaita mata yabar abin a lullu6e kamar yadda Teemahn bata gane ba Allah yasa yatafi a hakan har abada, domin matu'kar Teemah ta fara gane bambancin soyayyar 'yan uwan taka da kuma soyayyah me zaman kanta (ta aure) tasan za'a samu matsala ne,fatan ta de Allah yasa har ayi agama lafiya kar asamu problem 'din komai, tunda aure ma zatayi ai shikenan. Domin indai Abbas ne tana ganin da kamar wuya, ko yanzun ma babu wani gaida ta da yace yanayi, ita ce mummyn dakanta tabashi labarin abin da ke faruwa a gidannasu kuma ko da ta fa'da masan ma bata wani ji alamun canji atattare dashi ba ko daga muryarsa har yanayinsa, da suka gama wayanne suna sallama sai yace" agaida mutan gidan " shine ita kuma mummy tace da ita Abbas na gaidata kuma tafa'di hakanne saboda mitan da Teeman keyi wasu lokuta akan cewa Yah Abbas ya manta da ita. Acikin satin aka gama maganar auren Teemah harma aka sa rana sati hu'du masu zuwa. Daddyn Teemah dakansa ya yanke wannan lokacin domin yana ganin adaidai wannan lokacin zai fi dacewa ayi bikin batare da kowa ya takura ba. Mummy bata so hakan ba domin ita aganinta lokacin yayi kusa bata so aka yanke lokacin kwana kusa haka ba, koda ta yiwa Daddy maganar ma sai yace mata "kar ta damu ai komai lokaci ne, ba gaggawa sukayi ba wata 'kila haka Allah ya riga ya tsara lokacin bikin Fatiman yace kinga kuwa mu bamu isa muja da ikon Allah ba". Dolen mummy taja baki tayi shiru, 6angare guda kuwa hankalinta yakasa kwanciya sam da wannan auren.Yayin da daddy shikam ba ruwansa, kusan kullum idan ya zauna sai dai kaji yana waya ya sanar da cewa lokaci kaza ne bikin Fatima 'yar wajensa, acikin lokaci 'kalilan kusan mafi yawa daga 6angarensa sun san da labarin auren kama daga kan abokansa har 'yan uwa da dangi ma duk ya sanar dasu. 'Bangaren Anty kusan hauka taso tayi akan wannan maganar gaba 'daya ta hana kowa sukuni agidan, gajiya Abbah yayi da halintan datakeyi musu akan auren, wani lokaci ya tanka mata ai kuwa kamar jira ta keyi, shi dama mahaukaci yafi so idan yana abinsa yasamu mataimaki, daga nan haukar Anty ya 'karu daddy ma ranshi ya 6aci sosai musamman yanda take ha'da ilahirin zuri'arsa ta zagesu kaf abin na masa ciwo sosai, amma sai ya lallashi zuciyar sa ya samu ya 'dan sassauto domin ji yake a ranar kamar yayiwa Antyn dukan tsiya, amma yasan haka bazai ta6a kawo gyara ba, zagi kuwa har sai da yaji kamar ya toshe kunnuwansa, munafukai takirasu yafi sau a'kirga, shikuwa yariga yayi alwashin ganin faruwar wannan auren yace ko ma miye zai faru sai dai ya faru amma shi kan be ga me hana shi 'daurawa Mahmud aure ba , mahmud dama ba ya gida tun dawowarsa daga wurin Abbas be fiya zama agida ba, wani lokaci arana sau 'daya Abbah ke kallonsa amma hakan ba damunsa yakeba, tunda dai be musa masa cewa bayaso ba ai toh "Alhamdulillah zai sau'ko ne idan ma fushi yayi. Da abin Anty yayi yawa ne sai Abbah ya yanke shawarar sanar da mahaifinta halin da ake ciki, beyi 'kasa agwi wa ba ya shirya yatafi kano musamman ya je domin yakai 'karanta agurin mahaifinta Alhaji Muhammad, abinda be ta6a faruwa ba kenan tun farkon auren su sai awannan lokacin. Yanzun ma yaga abin nata yayi yawa ne shiyasa, dan ko kunya bataji ballantana tsoron Allah take furta maganganu marasa kan gado ciki harda alwashin kisa akan wai inhar suka yadda auren nan yayiwu. Ran Alhaji Muhammad ba 'karamin 6aci yayi ba da yaji abinda Abbahn yagama zayyano masa, tun ma kafin Abbah yabar wurin yafara masifah yana nunawa mahaifiyarta illar rashin hankali da kuma 6ata rayuwa da halayyan yaro tun bai je ko'ina ba, yace wannan rashin hankali har ina, maimakon Abbah da za'a bawa ha'kuri sai ya zamana shine ke bawa Alhaji ha'kuri gashi girma ya kamashi yanzun sosai harma baya fita harkan kasuwancinsa sai de a jagoranceshi,maganar ma da 'kyar yake fizgota yakeyi tsabar ranshi daya 6aci da Antyn. Da 'kyar suka samu ya sau'ko daga dokin fushin da ya hau, mahaifiyar Anty har sai da hawayen ta ya 'diga tsabar yanda taji hankalinta ya tashi domin fa'dan Alhajin kakaf kanta ya tattara ya dawo afa'darsa wai ai duk laifin tane. Koda Alhajin ya sau'ko sai ya bawa Abbah ha'kuri sosai tare da cemishi idan yakoma yaturota tazo yace mata yana nemanta inda hali ma su dawo tare. "Abbah yace bakomai za'ayi kamar yadda ya keso" Alhaji Mahammad yayi yayi da Abbah akan ya 'dan kwana musu biyu amma Abbah ya'ki amincewa yace yana so ne yaje yaga 'yan uwan mahaifinsu" Alhaji Muhammad dayaji haka sai ya washe baki yace " ai babu komai hakanma yayi, yace daman ma yanaso ya tambayeshi ko yajeshi 'din ashe ma abin nacikin ransa, Sai Alhajin ya 'kara jan hankalin Abbah akan kyautata mu'amala da kuma ri'ke zumunchi yace zumunchi ba'abin yarwa bane akula da ita sosai.. Fatan alkhairi yayi masa shi Alhajin daga nan Abbah ma yayi musu sallama yafita agidan yana me 'kara yiwa Alhajin godiya tare da yi musu alkhairi sannan yayi tafiyarsa. A waya sanar da Anty sa'kon mahaifin nata inda ya 'kara da fa'din " nan da kwana biyu tasamu ta je domin yace karta 6ata lokaci" Batayi magana ba illah wani dogon tsaki da ta ja sannan ta kashe wayan, Abbah kuwa be damu da yanda tayin ba dan shi fiye da hakan ma yasan zata aikata, transfern ku'di yayi mata a account 'din ta kafin ya maida wayar cikin aljihunsa wanda yasan zai isheta duk wani shige da ficenta har taje ta dawo. Koda Abbah ya isa gurin 'yan uwan mahaifinsa sun yi farin ciki da zuwansa sosai, 'dai 'dai ku daga cikin su ma sun rasu yayinda ma'danda suke rayen ma duk 'karfin su yakasa ayanzun, wasun da suka rasu Abbah yanada labari wasu kuwa be sani ba sam dan ba wani communication sosai ne atsakaninsu ba, tausayinsu yakeji sosai duk 'kinsu dasukayi abaya be damu ba yasan ko ada 'din ma ba laifinsu bane giyar talauci ce tasa su sukayi yadda suyi rayuwa dasu. Sai ya ha'da yayi musu ta'aziya gaba 'daya yakuma yi wa iyalansu kyaututtuka sosai wanda zata anfane su tareda wa'dan da suka rage arayen daga yayu da 'kannen mahaifin nasa dukka ya ha'da yayi musu alkhairi. Da ya sanar dasu ma batun auren Mahmud ne yatashi sunnuna farin cikin su sosai harma da dama daga cikin su suka rin'ka zubda hawaye suna masu neman yafiya daga gurin Abbah akan abinda suka aikata musu abaya. Shima kusan kukan suka saka shi domin idan yagansu akowani lokaci tunowa yakeyi da mahaifinsa amma dole ya daure ya hana nashi kukan tasiri ya ta basu baki yana nuna musu cewa ai tuntuni komai yawuce shi agurinsa be ri'ke su a zuciya ba komai yafaru ai mu'kaddari ne kuma rubutacce ne awajen mahallici. Kwanan sa uku tare da dangin mahaifin nasu kafin Anty ta iso wai a hakan ma sai da Abbah yayi mata 'karyan a kwana biyu mahaifinnata ke nemanta amma duk da haka sai da ta 'kara akan yanda ya sanar da itan. Be tafi aranar ba sai washe gari sannan yayi sallama da kowa yakama hanya. Alhaji fa'da yayi wa Anty sosai harma ya jajjada mata cewa matu'kar tace bazata kwantar da hankalinta ta zauna lafiya agidan aurenta ba toh kar tayi tunanin tana da mahaifi aduniyan nan. Yace kuma datake wani borin hana auren bata tunanin cewa shi Mahmud 'din da ita 'yar gidan Khadijan sun fi kusa akan wata daban da takeso 'dan tan ya aura, yace wata daban 'din ma girman cikin garin lagos. Shi aure mu'kaddari ne kuma lokaci ne, idan Allah ya riga ya tsara abu toh babu wanda ya isa ya canja shi, sannan ba'a jayayya da qaddarar ubangiji koma ayaya tazo maka u must have to accept it, karta bari shai'dan yayi galaba akanta akan abun da ba ita keda ikon sawa ko hana yiwuwarshi ba, yace da ace son ran mutun ne dashi dakansa bazai barta ta auri Yusuf alokutan baya ba saboda yasan halinsu da bambamci , amma miye dayake Allah yariga ya rubuta sai sunyi auren yace bagashi ba , ni ban isa na hana ba, kamar yadda kema kika yi ka'dan ki hana dan haka tun wuri ki maida hanakalinki ki san me kike ciki, idan har kika kuskura na 'kara jin kinyi irin abu makamanciyar wanda naji ayanzu toh wallahi Maryam kisani zamu raba ala'ka dake ,saboda ni kinga ban aurar dake ga wannan bawan Allahn dan ki ta 'daga masa hankali ba, yace wallahi da yasan abinda zata aikata kenan ma da tun farko ba zai amince da batun auran ba, amma bakomai wannan duk cikin 'kaddara ne kuma babu wanda ya isa ya gujewa tasa 'kaddarar matu'kar tazo. Da nasiha ya kammala maganar tasa ga dukkansu tare da 'kara bawa Abbah ha'kuri yace ya 'kara akan wanda yayi tayi abaya. Godiya Abbah yayi masa daga nan suna idar da sallahr azahar ya kama hanya ya koma lagos. Anty kuwa kusan Satin ta 'daya a kano bayan komawan Abbah, duk da bawani da'din zaman takeji ba amma wani lokaci takanji cewa zama agidan yafi mata wai ko zata hita da taahin hankali, gashi tana ji tana gani abu na nema yafi 'karfinta abanza kuma takasa 'daukan mataki. Kuma ako wacce wayewar gari sai mahaifinta yayi mata nasiha sosai cikin natsuwa akan rayuwar duniya iya yanda yasan zata fahimceshi, ita kanta mahaifiyar tanma yanzu ba kamar da ba, dayake girma yakama ta itama kuma sai tayi sa'a yazo mata da shiriya, wani lokaci takanji tamkar tayi kuka dan ba'kin cikin halin da akace 'yarta nayi, domin tasan komai akace maryam 'din tayi laifinta ne komai da aka 'kirga awurinta ta koya sai dai yanzu tanaji tamkar maryam 'din tafi 'karfinta tama kusan nunka mugun halin data koya agurin mahaifiyarta 'din. Itama sosai take zaunar da Antyn duk dama bata fiya sauraranta ba domin ba 'karamin raina mahaifiyartan tayi ba, gara ma shi Alhaji tana 'dan jin shakkan shi hakan yasa dole take zama ta saurare shi ko bata so ko da ba zata 'dauki abinda yake fa'da 'din ba amma dai zata zauna dolenta, tsawon lokaci tana sauraran karatun nasa batare da ta 'dauki koda abu guda daga ciki ba. Abinda basu sani ba ayanzun shine, Anty bata da burin daya wuche taji ance babu wannan maganar auren. Tsana mafi girma take ji azuciyarta game da auren, tana jin koda me nene ze faru sai ta ga ta hana wannan auran faruwa. Duk da yawan nasihar da Alhaji muhammad ke mata amma dai dai da rana 'daya tak sam 'Kudurin Anty be canja ba daga cikin 'kudurorinta na baya sai ma abinda ya 'karu domin 'karan tan da Abbah ya kawo bai gyara komai ba sai ma lalata wa dayayi. *sharhi nake bu'kata ga duk wanda yakaranta* 🀞🏻 *Salmerh* 😍 [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: πŸ’• *CAPTAIN ABBAS* πŸ’• By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* πŸ’« We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* There is no any slave of Allahwho commits a sin, then he perfects his ablution, stand b4 Allahu subhanahu wata'ala to pray 2raka'ah of prayer, then seeks Allah's 4giveness, expect that Allah will 4give him. Abu Dawud,2/86, At-tirmizi 2/257. πŸ…Ώ *44* Abu 'daya ke cin zuciyar Anty akoda yaushe in ta tuna shi kuma shine yafi sata damuwa fiye ma da batun auren Mahmud 'din haushin hakan kuma shike 'kara sata takae jin haushin kowa,dan tasan batun aure me sau'ki ne matu'kar tasamu ta ziyarchi gidan _'dan_ _Oga_ (boka) tasan matu'kar ta samu ta ha'du da shi to bata da sauran damuwa. Amma prolem 'dine taya zata ha'du dashi? Mtsalar ka'dai dake cinta kenan har azuciyarta, ita aganinta maganar auren nan dasuke ta wani 6ata bakinsu akai arana 'daya zata iya warware shi kaf kuma waru kenan, da ace ta 'dau mataki toh da dolen kowa ya ha'kura da maganar auren amma kuma sai tayi rashin sa'a 'kawarta Anty Chideh ta'ki sam ta taimaka mata akan lamarin, sai ma wasu banzayen sharu'd'da datake faman gindaya akai kafin wai tayi mata jagora zuwa wajen _'dan Ogahn_ itakuwa sam bazata iya abinda Anty chiden take 'ko'karin taga ta aikata ba, akullum tunaninta yanda zata samo mafita ne amma taras,shi 'din nan dai tafi yadda da aikinsa sai dai ta rasa yadda zatayi tunda 'kawarta ta'ki kaita , tambaya kuwa babu irin wanda batayi ba amma tarasa wanda yasan shima balle 'kauyen dayake rayuwa. Idan ta matsa sai akwatanta mata wani wuri daban , da zumu'din ta take zuwa amma kamar ha'din baki kalaman su iri 'daya ne. Akwai wani guri da suka je da wata 'kawarta, bokan ce musu yayi wannan auren babu fashi sai anyi, the same abinda wata matsafiya ta gaya musu da suka je da mahaifiyar Munira harma da ita kanta Muniran. Anty kamar zatayi hauka dataji abinda suke ta faman sanar dasu. Inta matsa wai ko za'a samu wata hanya da za'a awarware maganar takance ita ko nawa ne she is ready to pay it indai auran zai fasu. Akwai wani bokan dayace mata ehh akwai dama za'a iya warware maganar amma ba ku'di zata biya ba zata tattaro ta dawo gurin na tsawon wata guda akwai aikin daza'a yi. Sam sai taji zuciyarta be yi na'am da wannan batun ba, auren da ake 'ko'arin yinsa nanda sati uku masu zuwa taya ya itakuma za'a ce tayi 1month tare dasu da yaushe kenan za'a warware maganar, bayan an 'daura kokuwa? Bata manta labarin da Chide 'kawarta ta bata ba na wani daya ta6a yi mata aiki tace satin ta guda agurinshi yana faman sex da ita ba 'ka'k'kautawa sai cewa yayi wai suna 'diban abinda zasu ha'da jinin tane da mijin nata alokacin, itakuwa dayake ta 'kagu taga ta malleka shi sai bata damu ba ta daure tayi ta jure wahalhalun da bokan ke bata, tace har tacika satin ana abu 'daya, tace data koma gida sai da tayi jinya kusan na. 11days kafin nan ta warware, atlast ma kuma bata ga komai ya canja ba babi wani abinda ya faru sai da ta je gurin wani daban kafin nan tayi sa'a aikin ta yaci. Tace ballantana ita da ba mallaka ko juyo da hankalin wani take bu'kata ba ayanzun burinta ta warware maganar ne toh dan me zata tattaro ta dawo gurin boka har na tsawon wata guda, yana nufin ita ma so yake yayi mata irin na 'kawarta kenan Allah ya kiyaye tace afili, _angudu ba'a_ _tsira ba kenan_ . 'Kin amincewa tayi kawai tayi tafiyarta. Dama agurin Anty chiden take da hope 'din samun ingantaccen wurin da tasan za'a share mata hawaye domin itace tasan gurare da dama acikin garin na lagos, amma kuma shara'din Anty Chidehn tazo mata dashi sai ya girmi tunanin ta, sam bazata iya aikata abinda 'kawartan ta ke son ta aikata ba, how on earth ace tayi irin wannan abin.... Koda ta koma gida (Lagos) ma cigaba tayi da neman mafita amma tarasa ta ina zata fara, kullum hankalinta atashe yake, gaba 'dayan su agidan ma sai suka rasa gane kanta, Abbah kuwa ko kallo ma bata ishe shi ba, kamar yadda itanma bai isheta kallo ba , zaman gidan tamkar wasu abokan gaba aka tara aciki haka suke yinta kowa harkar dake gabansa kawai yakeyi, Anty ta 'debi abin ne da zafi 'karfi dayaji take so taga ta hana abinda Allah bai haramta ba, duk kuwa abinda take yi shiga da fitan ta da wasu abubuwan Abbah kallon ta kawai yakeyi yana mamakin taurin kanta, zai yanzu yake 'kara jaddada wa kansa rashin sa'ar mata yayi, ha'ki'ka shi kan baiyi sa'a ta wannan 6angaren ba, bayaga haka kan be sa me zai ce ba, Alhaji Muhammad mutumin kirki ne dashi kanshi zai iya bada shaida akan haka, sannan yana da tabbacin Alhaji yaja wa Maryam (Anty) kunne akan haka harma ya ha'da da tabbatar mata cewa matu'kar bata kar6i wannan auren ba toh babu ita babu shi, lokacin da Alhaji Muhammad yayi wannan maganar shikanshi Abbah bai ji da'di domin bazai so ace iyalinsa ta samu matsala da mahaifinta ta dalilinsa ba, yaso yayi magana tun awancan lokacin amma sai yayi tunanin wai ko zata yiwa kanta fa'da da wannan kalmar ta saduda ta barwa Allah ikonsa amma sam sa6anin haka yagani wanda be sani bama sai yace acan ta 'karo taurin kan da taje, ha'kika duk wanda yayi nisa da wuya yake jin 'kira koda me 'kiran ya hau kan babban tsauni ne,sai dai kawai Allah ya shiryamu gaba 'daya.(yasa mu gane gaskiya gaskiyace kuma yabamu ikon yin aikin da ita). Shima Abbah babu abinda yasa agaba ayanzu illah yaga anyi auren nan angama shi

Chapter 21 of 67