Hannah dake tsayen abayan Teemah.
Teemah kam fita tayi ko waiwayowa batayi ba ta fice daga 'dakin
tana jan 'kafa kamar bazata ba, tariga tasan halinsa sarai bawani abincin da ze sake ci tunda baya cin abinci sau biyu lokaci 'daya 'kilan kawai wani abin ne yasa shi cewa takawo masa.
Da sallamarta ta shiga 'dakin nasa taje ta ajiye abincin akan 'dan 'karamin dinning 'din dake 'dakin nasa me kujeru biyu kacal.
Tana shirin juyawa ta tsinkayi muryarsa yana fa'din " _kawo min_ _nan_ "
Komawa tayi ta 'dauko sannan ta kawo masa tana ajiyewa shikuma yana mi'kewa yake fa'din " _zauna kici ina zuwa yanzun_ _nan_ "
Hawaye kawai taji ya gangaro mata, kamar tasa hannu aka tayi ihu dan takaici, dama tasan bacin abincin zaiyi ba, da ta san cewa ita ze sa taci ma da bazata zo ba.
Kusan mintina biyu tana zaune da abincin agabanta, tana share hawaye, dataga ba yanda zatayi kawai sai ta bu'de tafara ci ahankali sanin halinsa datayi akan hakan, dan tunda yace taci toh matu'kar bataci ba baze ta6a barinta ta tafi ba, dan haka sai ta ringa ci ahankali take turawa bakinta harta jita dam, daga nan ta tsaya da cokalin ahannunta, tana jiran fitowarsa.
Ashe watsa ruwa yaje yayi sai da ya shirya kafin ya dawo parlourn cikin kayan baccinsa me birgewa jikinsa na tashin sayayyan 'kamshi.
Zuwa yayi ya zauna tare da ha'de hannayensa wuri guda yasata agaba yace mata " _ya dai_ ?
" _Na'koshi ne Yayah_ "
Muryarta na rawa tayi maganar.
Baya yayi ya jinginu da jikin kujera dan yaga ba laifi ta 'danci ka'dan sai yace " _U can leave, amma fah ki kiyaye kina cin abinci akan lokaci dan duk ranar dana_ _dawo na ga baki canja ba wallahi zan sa6a miki ne, bana son yawan_ _kukan nan da damuwa kuma, ko shi Mahmud 'din ce miki yayi ki dinga yi_ _masa kuka idan_ _ya rasu_ ?
Da kai ta bashi amsa alamar " _ah'ah_ "
Sai kawai yaci gaba da da fa'din
" _Ya kamata kisani Mahmud is now no more, baze ta6a dawowa ba, is better ki nutsu ki san_ _abinda ya dace ba ki ringa damun mutane da kuka da damuwa_ _ba, zan bawa Abbah_ _ha'kuri akan tahowarki dan nasan beji da'din hakan ba, sannan_ _idan nadawo naga kin saki jiki ni da kaina zan kaiki Lagos 'din ki dubo_ _su har wurin Mummy ma duk zan kaiki amma sai naga kina jin_ _magana tukunna......_ _clear_ "
Ta gya'da kanta tare da furta " _yes_" ahankali.
" _Toh gudnight_ "
Daga nan be sake kallon inda take ba ya maida idanunsa kan television.
Tashi tayi ta fita zuciyarta fal farin ciki, musamman dataji yace zai kaita gurin Mummyn ta, ai gaba 'daya sai ta manta da komai.
Hannah ma sai da ta fahimci farin cikin dake kan fuskar Teemahn data tambayeta kuwa take ta sanar da ita yanda sukayi da Abbas 'din.
Murmushi kawai Hannah tayi tare da jinjina masa aranta tasan yana yin duk hakan ne dan yaga 'kuncin Teemahn yaragu.
Wani lokaci takan ga kamar Teemahn na da sa'ansa domin Yayah yakanyi mata abinda bakowa ke samun hakan daga gareshi ba, bata san dalilin sa ba amma tana jinjinawa dangatar dake tsakaninsu.
*****
Washegari 'karfe bakwai ya bar gidan yayi tafiyarsa ya koma Rivers state, Umman ce ka'dai tasan da fitarshi itan ma atsatstsaye yazo yayi mata sallama yafice.
Tasan halinsa sarai yanzun yana hakan ne dan kar tasake yi masa magana akan Fateemah shiyasa yayi hakan ita kuwa yanzu ta riga ta saduda barinsa zatayi taga iya gudun ruwansa tunda kam yace Fateemahn amanar sa ce ita, toh nata kallo ne.
*Masoya Abin alfahari ina yin ku sosai da sosai wallahi nima, bazance muku komai ba dan bani da bakin gode muku all i know is that kuna sani farin ciki...... addu'o'in ku nasani walwala, Allah ubangiji ya bar minku ya sada ku da dukkan alkhairinsa.*
~WANNAN SALMERHN NAYI MUKU FATAN ALKHAIRI~
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce*π
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated to my sister Khadeeja Usman Allah ya bar min ke._
*Bismillahir rahmanir raheem*
_A good heart and a good nature are two different issues, A good heart can win many relationships, But a good nature can win many good hearts._
π
Ώ *70*
Kwanan Fateemah biyu agidan sannan ta 'dan saki jikinta, Daddyn Abuja ma daya dawo sosai yayi farin ciki da zuwanta dan ko shima bawani da'di yaji da barinta da akayi acan ba kawai de yayi shiru ne saboda al'amarin ahannun matan yake, yanzu kuwa da ya ganta ya kuma ji labarin cewa Abbas ne ya kawo ta ai shikenan gaba 'daya sai ya manta ma da haushin Abbas 'din daya keji ya ringa sa masa albarka.
'Ko'kari sosai Hannah keyi wajen ganin ta mantar da Teemahn damuwar da take ciki, saboda bata barinta zama shiru sai de in tatafi makaranta wanda makarantar ma dan ya zama dole ne shiyasa lokuta takance da ita badan tana zaman 'dakin rasuwar mijinta bama da se ta ringa rakata makarantar ai.
Teemah kam baki take ta6ewa ta yi shiru, dama yanzu gaba 'daya ta canja wannan rashin jin duk babu shi ta dawo wata salihar 'karfi da yaji, wani lokaci idan tana abu se kaga kamar ba ita ba.
Haka abinci ma yanzu bata ci da wasa 3square meal 'din nan duk basa wuceta takanyi 'ko'kari taci a'kalla kamar spoon goma koma fi akowani lokacin cin abinci, Ummah sosai take jin da'din canjawar tata musamman data ga yanzu tasaki jiki har tana cin abinci batare da an takurata ba.
Damuwar ma duk ta rage shi yanzu ta barwa zuciyarta, addu'ah kawai take masa akowani lokaci musamman idan tayi sallah toh sosai take 6ata lokaci waken yi masa addu'ah wanda a lokacin ne tafiya yin kuka sai de ko Hannah bata bari ta fahimci yanayin data ke shiga.
Tana waya dasu mummy da Anty akai-akai, inda mummy kanta da taji cewar Teemah ta dawo Abuja sai da ta sau'ke ajiyan zuciya da can 'din ma kawai ta daure ranta ne tare da yiwa Anty kawaici, amma tunda ta koma Dubai sai taji zuciyarta ya kasa nutsuwa sai take ganin kamar Antyn zata iya sake cutar da Fateemah tunda tana gabanta.
Anty kuwa bayan tafiyar Teemah da kwana biyu sai taji damuwarta ta dawo mata sabo fil, tunaninta ya yawaita akoda yaushe bata da aiki sai zubda 'kwalla, gashi babu wanda ke zuwa gurinta ayanzun, Abbah ma 'kara nisanta kansa yayi da ita, dan tun tafiyar Teemah sau 'daya kawai ta ganshi, wannan 'dinma ta window ne lokacin shigowar sa gida kenan jin dirin mota yasa ta le'ka sai taganshi.
Ganin sa 'din kuma sai ya 'kara kashe mata zuciyar dan gaba 'daya Abbah ya lalace wani rama taga yayi na masifa, tausayinsa har se da ya sata sakin hawaye, tasan koma menene yafaru laifinta ne, mutuwa ba a hannunta yake ba, amma tasan son zuciyarta shine sanadin komai.
Komawa tayi ta jinginu da jikin window ta lumshe idanu yayinda hawaye suka ci gaba da gangarowa ta 'kasan idanun suna sau'ka saman kuncinta, samata 'daga kanta tace
" _Allah na tuba ka yafe min, ka yafe min kura kuraina, ya ubangiji Allah ka sanyaya zu'katan duk wa'danda na_ ' _kuntatawa, Ya Allah kaji'kan Mahmud ka haskaka masa 'kabarin sa_ "
Washe gari da sassafe tayiwa 'dakin Abbah tsinke, sallamrta ka'dai ya amsa saboda darajar da sallama ke da shi ga dukkan wani musulmi, daga nan yaci gaba da shirinsa be ko kalli inda take ba, kallo 'daya Anty tayi masa ta fahimci cewa shirin tafiya yakeyi dan haka sai ta zauna agefen gado ahankali tace " barka da warhaka Alhaji fatan antshi lafiya"
Da " lafiya 'kalau"
Kawai ya amsa ta atakaice.
Anty ma sai tayi shiru bata 'kara magana ba kawai ta rin'ka binsa da idanu.
Ganin kamar bashi da niyyar sake kulata sai tace dashi
" _Alhaji dan Allah kayi ha'kuri ka yafemin laifukana, ka daina fushi dani,_ _wallahi nayi dana sanin duk abubuwan dana aikata abaya, ni kaina inajin tsanar kaina akan haka_ , _bansan ya zanyi in goge laifina awurin mahallicina ba amma nasan idan kun yafeni wata'kila_ _Allah zaiji tausayina ya min afuwa_ "
_Nasan ban yi mana adalci ba koka'dan, ban kyauta wa rayuwar mu ba gaba 'daya tunda_ _gashi son kaina yasa har nayi sanadin da 'dana yarasa_ _rayuwarsa......_
Kuka ne ya kubce mata tayi na kusan mintina biyu sannan taci gaba da fa'din
" _Mahmud yace kayafe masa Alhaji, yace in ro'ka masa yafiya awurinka akan duk laifukan_ _daya maka arayuwarsa......_
Sai ta sake sakin kuka gwanin tausayi.
Abbah ma dakansa sai da ya share hawaye da jin abinda Anty take fa'di tunanin yaronsa da tausayin kansa ya 'kara kamashi, 'dansa 'kwaya tal da Allah ya bashi gashi be samu damar bashi farin cikin daya dace ba har ya bar duniya, yau gashi babu shi, Mahmud ya tafi, sai de yasan Allahn daya kar6e shi yafishi son shine, yasan kuma Allah baya ta6a barin wani dan wani yaji da'di, sai fatan Allah yayiwa Mahmud Ubangiji ya sada shi da dukkan rahamarsa.
Yana goge hawayen fuskarsa ya 'dauki 'yar 'karamar jakar kayansa daya gama shiryawa tare da 'daukan wayoyinsa ya nufi hanyar fita.
Ganin Abbah na shirin fita batare da taji kalma 'daya me kyau daga bakinsa ba yasata ta mi'ke da hanzari tace
" _Alhaji ko bazaka min magana ba dan Allah kayi min izini in tafi kano_ "
" _Allah ya kiyaye_ _hanya_ "
ya fa'da tare da ficewa abinsa daga 'dakin.
Anty kam kuka tasanya har tana 'dan bubbuga kanta da hannunta, nadama da takaici ne duk suka ha'du sukayi mata yawa, duk da tana farin ciki da barinta da Abbah yayi amma kuma halin dayake cikin ya matu'kar tsaya mata arai, tasan dama ba ze ta6a hanata zuwa kano ba, baze ta6a shiga tsakaninta da ahalinta ba, shi akullum ma burinsa taringa ziyartar su tare da mutunta familynta sa6anin nata halin.
Zata je ta nemi gafarar iyayenta ta gyara dukkan kurakuranta na baya, ta faranta musu a matsayinta na 'ya agare su.
Ko zata samu su yafe mata laifukanta garesu.
*****
Daddy musamman ya baro Dubai yataho domin ya amsa gayyatar Abbas inda suka je shi da Daddyn Abuja suka halacci taron 'karin girmansa inda daga ranar ya amsa matsayinsa na *CAPTAIN* .
Tun acan Daddynsa yafara wa Yayan sa magana akan Abbas 'din, complain ya shigar akan cewa wai yayi-yayi dashi ya yi aure amma ya'ki, shi kuma duk wannan abubuwan ba farin ciki suke saka shi ba, dan ko wani irin matsayi mutun yakai aduniya matu'kar bashi da iyali toh darajarsa ragaggiya ce, gara tun wuri kayi wa 'danka magana yafito da mata inbahaka ba wallahi da kaina zan za6a masa mata idan nagaji da magana.
Murmushi Daddy yayi sannan yace
"Haba Hassan kabarshi mana yasamu nutsuwa, yaushe ma yasamu ya zauna da har za'a fara yi masa maganar aure, shi auren de lokacine idan lokacin yayi kuwa ba se ka tsaya 6ata bakinka ba, da kansa zakaga ya furta, dan Allah ka sarara masa Al-Hassan ka raba masa hankali"
Kauda kai Daddyn Abuja yayi wanda Daddy yafahimci cewa maganar tasa bata wani shiga ransa ba amma de yasan Hassan 'din ba ze taka maganar sa ba tunda ya furta, dan Hassan na matu'kar bashi girmansa sosai.
Daddy daga can ya wuche ko Abuja be dawo ba, saboda baya son ha'duwa da Teemah a dai-dai wannan lokacin dan uasan rigimarta yawa ne da ita.
Abbas kam tare suka dawo gida shida Daddynsa, dan har yanzu acikin hutunsa yake be gama ba.
Sai da yazo gida kafin su Ummah suka shirya wata 'kwarya-'kwaryar walimah acikin gida na tayashi murna, yaji da'di sosai da hakan barin ma daya ga Fateemah ta 'dan saki ranta yanzun bakamar da ba, gashi ta 'dan yi kyan gani duk da hijab ta zun6ula har 'kasa amma hakan be hanashi fahimtar canjawarta ba.
Ahankali ya 'kara fahimtar rungumar 'kaddara da tayi saboda ko a dinning yaga yanzu tana ' dan sake wa taci abinci harma ayi hira da ita, duk da murmusho yafi yawa anata fuskar amma sometimes takan jefa nata ka'dan.
Idan Hannah na makaranta kuwa sau tari da Ummah zaka same ta tmsuna ta'di abinsu, ko kuma ta yi kwanciyarta akan cinyar Ummahn tana shagwa6arta wani lokaci har bacci takeyi agurinta.
*Bayan sati 'daya......*
Teemah ha'kurin ta yafara gazawa ganin har yanzu Yayah Abbas be sake mata maganar tafiyan ba, kuma xe mata yayi idan yadawo zai kata, tayi 'ko'karin kiyaye duk wani abu da tasan ze sa shi canja ra'ayi amma shiru bata ji yace komai ba.
Bata san me zata ce dashi ba dan haka sai ta fara bawa Ummah labari ka'dan-ka'dan, sai tace da Ummahn " _Yayah fah uace zamu je wurin Mummy da Anty in gaishesu amma kuma naji be sake_ _maganan ba_ "
" _Antyn naki ba kince tana kano ba_ ?
Ummah ta tambaya tana kallonta.
Sai tace
" _Ehh tatafi kano, ai shi ne yace zamu_ _wajenta_ "
"Toh inaga be shirya tafiyan bane tukunna, amma nasan tunda har ya fa'da toh babu shakka zai kaiki 'din, zai fison idan kin warawre gaba 'daya"
Cikin shagwa6a tace "Ummah nafa riga warware gaba 'daya"
" _Toh ni Fateemah ni miye nawa, ba fa dani kukayi_ _shawaran ku ba_ "
Kwa6a fuska tayi kamar zata yi kuka gani hakan yasa Ummah ta janyo ta zuwa jikinta ta kwanatar.
" _Haba Fateemah, kiyi ha'kuri mana ki 'dan 'kara bashi lokaci kinji_ "
Ummah ma biye ta ringayi da lallami har zancen ya kau.
Ita kam ma ai jinta take yi kawai, dan ko Abbas ya 'dago zancen tafiyar toh ita ba yadda zatayi ba.
Yawon ai ya isa hakan gara ta zauna wuri 'daya ta iddasa zaman takabarta inyaso daga ko ina ne ma taje.
Teemah kam ha'kurinta 'karewa yayi, kwana biyar bayan maganar da sukayi da Ummah sai taje dakanta tasame shi.
Duk yanda take ganin ta canja Abbas cewa yayi be ga hakan ba shi har yanzu dan haka tafiya ba yanzu ba.
Ranar kam kuka tasha da dare dan haushi, tana cikin kukan ne Anty ta 'kirata awayarta tana 'dauka kuwa tasake mata kuka, take Anty ta rikice ta fara tambayarta abinda ya faru, me aka mata?
cikin kukan tayi mata bayanin komai, Anty kam murmushi tayi dan take ta fahimci wayo kawai Abbas yamata dan ta saki ranta ta sake da kowa, amma duk da haka sai tace da ita
" _har kin sa na ji wani iri ma, ai inajin Abbas 'din yama fiki gaskiya, amma de kiyi ha'kuri kinji, ki bari idan na koma Lagos 'din nasan zai kawo ki tunda shi yafa'di haka, ai yawo banaki bane yanzu Fateemah, akwai sauran lokaci kinji inna samu lokaci ma zanzo na duba ki a Abujan kinji_ ?
Baki ta tura gaba ciki muryar shagwa6arta tace
" _Dan Allah Anty kizo toh, ni nagaji da zaman ne Anty, bafah na zuwa ko'ina ko shopping Hannah ce_ _ka'dai take zuwa, ni Ummah bata_ _barina in bita kuma idan ta dawo sai ta ta min dariya_ "
Murmushi Anty tayi daga 6angarenta, tana mamakin yarintar Teemah ita kam, ashe yarinya ce ' karama sosai har yanzu, tasan koda tace zata mata bayani ma 'kila ba gane manufarta zatayi ba, dan haka sai ta bar wancan tunanin kawai tace
" _Ayyah very sorry kinji, soon kema zaki fita ai yanzun be kamata kina yawo bane shiyasa amma in lokaci yayi nasan babu me hanaki fita_ "
Sosai Anty tayi ta rarrashinta har ta ha'kura tayi shiru.
Ganin ta nutsu yasa har Anty ta bata labarin kaf yanda suka yi da mahaifanta bata 6oye mata komai ba, yanda tasha gwagwarmaya kafin ya amince da ita, da 'kyar ya furta mata kalmar yafiya dan shi tsakaninsa da Allah ya tsani ganinta arayuwarsa ma.
Teemah ta tausaya mata da jin labarin, inda tasake bata 'kwarin gwiwa sosai kamar ba ita bace me zuba shagwa6a ba 'dazu.
Anty najin da'din kasancewa da ita dan ko ba komai takan 'de be mata kewa, gashi tana 'ko'karin bata shawarwari masu kyau duk da take yarinya 'karama amma akwai ta da ilimi, bayan sata ahanya data tayi lokacin suna Lagos, Anty tamkar sa'arta ta maida ita dan duk shawaranta da ita takeyi yanzu, in abune ma ya dameta Teemah take sanarwa su jajanta tare sosai take janta ajiki tana jinta tamkar 6arin zuciyarta ce.
Sau tari Anty na addu'ar Allah yasa Fateemah nada cikin Mahmud saboda zata so ace tasamu jika daga ita, amma lokaci guda take kauda wannan tunanin idan ta tuno kato6arar da Munnira ta aikata, musu sai dai akullun bata cire rai idan son jikan yacika mata zuciya sai kuma taji kamar batun Munniran 'karyane babu wani barrier da ta yi atsakaninsu ,alokacinn ne take 'karyata Munnira da kuma aikin bokayen sai taji kamar tunanin ta gaskiya ne, Fateemah nada cikin Mahmud ajikinta.
Har kwatanta ranar da za'a ce maganar ta tabbata takeyi tana misalta irin farin cikin da zataji, takance da kuwa anga zallar so dazata nunawa jikan nata, bata jin akwai abinda zata so fiye dashi aduk fa'din rayuwarta kuwa.
Lokacin da sukayi sallama da Anty Fateemah ma shiru tayi tana tunani, abin na damun ta sosai, yanda akabi aka tsare ta agida kamar munafuka, turare wannan Ummah hanata amfani tayi da shi, duk kuwa da yanda Teemah ke da jarabar turare amma hanata akayi amfani da masu 'karfi, sai da taga Teemah na shirin yi mata kuka kafin da 'kyar ta barta take amfani da wani me sanyin 'kamshi sam bashida 'karfi, wani lokaci idan tasaka shi ajikinta mintina biyar bayayi ajikinta sai taji babu 'kamshin duk ya gushe, sannan bata kwalliya kullum tana nan sai fama da waya a'daki.
Islamiya wannan idan suka ce zasuje tare da Hannah Ummah hanata takeyi, akwai ranar dama ta san'di jiki suka fita ta 'kofar kitchen har suna murna amma cikin rashin sa'a sai ga Yayah agabansu take kuwa ya maida ta gida yace maza ta koma babu inda zata je.
Ranar kam tasha kuka, wani lokaci gani take kamar ita ka'dai aka tsana agidan shiyasa akeyi mata haka, yayinda kuma taga ake riritata tare da girmama bu'katunta fiye da Hannah sai kuma ta 'karyata zancenta na farko, sam tarasa dalilin hakan gaba 'daya ta gaji.
Dai-dai lokacin da tacika sati uku cif da zuwa gidan adai-dai lokacin Yayah Abbas ya koma bakin aikinsa wanda yayi dai-dai da wata biyu da kwana uku da rasuwar Mahmud.
Zuwa lokacin kam Teemah ta saduda ta daina damuwa, ri'ke 'kuncinta kawai tayi azuciya.
Abbas 'din ma dayake bazama sosai yayi agidan ba, ita dai tasan yaje Gombe inda daganan taji labari abakin Ummah cewa ya wuche Dubai daga can.
So rashin zaman nasa yasa bata fiya ganinsa ba, amma duk da haka 'ko'kari sosai ko da bayanan amma yana kula dasu yana yawan turawa Hannah ku'di yace suyi amfani dashi, wai shi duk a'ko'karinsa naganain ya kula da amanar marigayi da ya kar6a, Hannah kam murna ta ke yi aduk lokacin da taga alert awayan ta takance " _albarkacin ki fah nake ci Teemah, da Yayah baya son bani ku'di ko na tambaya baya bani sai yaji 'kwa'kwkwaran dalili kafin nan yabani, kuma Daddy ma baya bani idan na tambaya sai ya wani ce in tambayi_ _Yayah na yabani kuma fah yasan dramar da muke sha dashi, amma duk da haka gurinsa yake turani, shi wai adole_ _be so_ _insaba da kashemanyan ku'da'de sai kuma_ _yanzu naga ba'a tambaya bama bayarwa yake yi_ "
Ta6e baki Teemah kwaia tayi dan ita bata da matsala da wannan.
Abinda ke damunta ma ya isheta, dan haushi ranar kam har kuka tayi musamman da ta tuno da Mummy, da ance aure toh yanzu kuma fah tunda babu auren memiye kuma dalilin tsareta,
bata ja tsawon lokaci ba ta bawa kanta ha'kuri, wani lokaci harda laifin mummy take gani, tasan ai itace ta shareta da bata manta da ita ba da duk haka be faru ba.
Daddy kam ba'a ma maganarsa dan shi samun layinsa bata fiye yi ba dayake yana yawan tafiye tafiye shiyasa bashi da takamammiyar number da zata sameshi akai
.
Ko bayan tafiyar Abbas ma bata damu ba dan zuwa yanzun babu ba'konta cikin duk rayuwarta komai tasaba dashi, zaman gida da sauransu, ita kanta ma yanzu tana jin da'din rayuwarta mafi yawan damuwarta ya kau, Anty ma har yanzu tana kano bata koma Lagos ba kuma cikin sabo da sha 'kuwarsu babu abinda ya ragu sai ma 'karuwa.
Ahaka da da'di ba da'di har Mahmud yacika wata hu'du da rasuwa, inda duk mutanen zuwa yanzu alhinin rashin sa ya ragu azu'katansu addu'a kawai suke binsa dashi.
Alhaji Muhammad kuma sosai yagaji da zaman Anty agida koda yayi mata magana kuwa sai tace Abbah ne yace tazo gida, tafa'di hakane kuma dan bata so mahaifin nata yaringa damunta da batun komawa.
Shikuwa da be san manufarta ba suna rabuwa da ita sai ya tuntu6i Abbah awaya yace masa " _Yusuf wai meke faruwane, naga tsawon wata biyu kenan harda_ _kwanaki Maryam nagida, bamu ta6a tattauna dalilin zaman ba, naga_ _kuma ko ka 'kirani baka kawo maganar ince dai lafiya ko?_
Abbah cewa
" _Lafiya 'kalau Alhaji ina nan ma zuwa kwanan nan insha Allahu nima_ "
" _Toh Allah ya kawoka lafiya, gara de ayi abinda ya dace ina ganin zai fi_ _ko_ "
Cewar Alhaji Muhammad yana me shafa gemunsa.
Abbah sai ya tabbatar masa da cewa
" _insha Allah komai zai tafi dai dai bisa dacewa_ "
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce* π
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh MD*
Luv storyπ
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
*Bismillahir rahmanir raheem*
_Crushes are more beautiful than affairs because there is no_ _responsibility, no worry_ , _no commitment. Just look at your crush and smile like an_ _idiot_.
π
Ώ *71*
Abbas kam yanzu girma ya 'karu, ta'kama da izzah sai abinda yayi gaba, Daddynsa ne ka'dai yake 'dan kashe masa gwiwa aduk lokacin da yayi masa zancen aure walau awaya ne ko kuma azahiri, sam bayason maganar auren nan amma yarasa yanda ze 6ullo masa, babban damuwarsa kenan ayanzu shiyasa ya tsani maganar ma kwata-kwata.
*****
Kamar yanda Abbah ya yiwa Alhaji Muhammad al'kawari hakan ne ya faru domin acikin satin ranar wata laraba ya sau'ka garin Kano, Alhaji Muhammad yaji da'din zuwansa dan kuwa ko ba komai yana ganin yanzu ne ze san matsayin da 'yarsa ta take awurin Abbah, dan haka bayan gaishe-gaishe har Abbahn ya huta ma sannan Alhaji Muhammad ya nemi jin salin abinda ke faruwa daga bakin sa, Abbah kam be sanar da shi komai ba yace masa kawai tace ne zata zo ta duba iyayenta shi kuma yace ta bashi lokaci in yayi settling sai suzo tare, ganin kamar lokacin tmya'ki samuwa ne shi yasa ta taho, batun kuma cewa shine yace ta zo 'din bahaka bane, yace wata'kila bata ahirya komawa yanzu bane shiyasa ta fa'di.
Alhaji Muhammad kam shiru yayi masa amma bawai dan ya gamsu ba, duba da yayi da cewar tun tsawon shekarun auren su da ita hakan be ta6a faruwa ba, toh me yasa sai yanzun kuma, yana kyautata zaton matsala suka samu amma Abbah yake 6oye masa, Alhaji be tsawaita tunani ba shima ya basar da zancen dan yasan basu ta6a samun matsala har abin yazo gabansa ba sai de lokacin auren marigayi Mahmud da ya kawo 'karar ta, wannan ma Abbah ya kawo 'karan ne dan kawo gyara wa lamarin, kafin da bayan hakan kuwa be ta6a sanin ya yanayin zamansu ba, yanzu kuwa da babu ran Mahmud be san takamam man menene matsalar su ba kuma ya san de baza'a rasa ba dole akwai wani abu, kawai de Yusuf na 6oye masa ne shikuwa ba haka yaso ba, yaso yaji abinda ke faruwa domin ya 'dan gyara al'amarin idan Allah ya bashi dama, dan shi da kanshi wani lokacin Maryam na bashi tsoro duk kuwa dayake 'yar cikin sa ne amma tun lokacin dayaji asalin 6oyayyen halinta gaba 'daya ya tsinke da lamarinta.
Alhaji aikawa yayi akayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 67