An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ο»Ώ[10/2, 5:43 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
Luv storyπ
By
*Salmerh MD*
π« *DA BAZAR MU* *WRITER'S ASS* π«
We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all....... *DA BAZAR* *MU MUKE* *TUN'KAHO.*
Dedicated to
*Safiyya Aliyu wakili*
(Masoyiyar asali)... marubuciyar
*MASAUQIN SO* da
*SHI NAKE JIRAH* ....on point.......
Allah ubangiji ya saka miki da mafificin alkhairi
(AMEEN SUMMA AMEEN)ππ»
*Bismillahir* *rahmanir raheem*
Littafin Captain Abbas ba na ku'di bane, kuma ni.ban ce asiyar ko asiya ba duk kuwanda yayi kuskuran aikata hakan toh yaci da gumina kuma na bar ahi da fitowar rana da fa'duwansa.
π
Ώ1
'Yan makaranta naga suke ta wucewa da alamar tashin su kenan daga makarantar,
daya ke yara qanana ne shiyasa mafi yawancinsu kafin ma su tashi ake zuwa zaman jiran daukan su,
wanda inka duba zaka ga motoci ne awurin suka fi yawa sai da tsirarun 'yan adaidaita,
wasu kuwa daba nisa ne dasu ba sae suke qarasawa da qafafunsu da alamar sun riga sun gane hanyar gidan dakansu basai anmusu jagora ba,
kadan daga cikinsu kuwa musamman ake xuwa dan aqarasa dasu gida koda qafan ne
,hakan yana nuni dacewa ba'a so ne suka mo hanyar
gidan su kadai......
Wata yarinya ce nagani atsaye bazata wuce shekara takwas ba,tsaye take da lunching box din ta kalar pink mai kyau ahannu.....
Atsayenta ta ke bata da alamar motsawa ko ina ga dukkan alamu itama jira take azo atafi da ita gida,
Har yara sun fara watsewa sae kuwa naga wani kyakykyawan yaro matashi ne wanda bazai haura 15 yrs ba yazo tabayanta ahankali ya lalla6o karab yarufe mata idanu,
Kokadan banga alamar razana atattare da ita ba sai ma dan dariya data yi irin nasu na yara.
sannan tadago hannun daman ta ta saita hannun daya rufe mata idon dashi ta sa ke mar mintsini mai shiga jiki
take ya bude mata idanun sannan yafara yarfe hannu
Kai ,
kai,
kai
"Haba ke kuwa dan Allah yafada kamar zaiyi kuka.
Dariya tafara yi masa tana qara kallonshi.
"Gaskiya yarinyar nan muguntarki ta shahara
Wama ya koya miki irin wannan abin ne dan Allah."
Ya fada yana qara kallon cikin idanunta
Da alamar mintsinin yashige shi sosai
Kamo hannunta yayi daniyar su fara tafiya,zuwa gida don yasan daman bayaga dariyan toh ba magana zata sake yimar ba
Al'adarta kenan ita inde tamar mugunta toh sae de tayita dariya amma ko me zai fada bata ta6a bashi amsar maganrsa
Mu wuce gida toh"
yace da ita
Na kusan yin maganinki ae badae ni kike rainawa ba.
ah ah yayah
Bakai ne karufe min ido ba"
sai yanzun ta budi baki tayi magana tana me turo bakin gaba
Toh dan na rufe miki ido sae akace kuma ki gutsure min fatata?
Kalli fah yanda kika yimin!
fuskar tausayi tayi dan ganin gurin yayi jaa sosai
Sorry yayah
bazan sa ke ba!!
Kima sake kiga wanda zai ringa dawo da ke gida.
Yitayi kamar zatayi kuka,ta tsaya da tafiyar
Miye kuma ya faru?
Bakai bane?
Toh yi haquri taho abinki daddy's angel kinga yau akwai rana,muyi sauri muje gida kar rana ya dafa mu.
Tafiya tafara ahankali
ganin hakan yasa shi yah qara kamo hannunta tare da kar6ar lunchbox din dake hannunta
Nace kiyi sauri wannan ranar fah tafara damuna.
Wae ma ni kekam da ba ke kadai kike dawowa bane?
Wato dan nazo sau daya na rakaki gida kuma shikenan kema kika daena tahowa dakanki ko?
Zanyi maganinki ae yarinyah kwanan nan.......
Bata kula maganar daya ke yi mata ba.
Sai ji yayi tafara cewa yauwa yayah yau apple xaka siyamin tana fada tana tsalle irin na farin cikinnan tana kuma nuna mai teburin fruit din dayake junction din shiga unguwar tasu.
Ke nifah yau banfitoh da kudi ba......
Take kuwa tafara kuka tana mar ihun ita kam dole sai ya siya mata bai kulata ba suka cigaba da tafiyah.
Aikuwa suna zuwa daidai gurin mai kayan fruits din ta kwace hannaunta daga cikin nasa ta qi wuce wa takafe awurin tana kwa6a fuska.....
Yasan ko mai zai ce da ita ba yadda zatayi ta bishi batare da ta ga abinda takeso din ahannunta ba.
"Maiyah"
yace qasa qasa sannan yawuce wurin mai fruits din ya kar6o mata aleda sunkai guda biyar akan anjima zai kawo masa kudin.
Dayake sun saba da mai fruits dinma sosai so bashida matsala da yaran yasan kudinsa zasu zo cas ba ragi shiyasa bai damu ba
daman kullum idan akazo daidai mai fruits din zakaga ta fara tsalle tana fadin abinda takeso asiya mata
Wataran tace pineapple,wataran watermelon,wataran kuma tace babana,ko kuma apple kamar yanda tayi nayau kenan.
Lemu ne kadae bata sha ita kwata kwata bata sonshi ma kokadan.
Kuma kullum Indai suka zo wucewa sai ya siya mata abinda yake ao din inkuwa bae siyaba toh kuwa zai sha rigima
sosai aranar
Sallama yayi apalourn kafin yatura qofar yashiga,ganin bakowa apalourn yasashi zama akan two seatern dake cikin palourn.
Ita kuwa ciki ta wuce dagudunta uniform kawai tacire ko kaya bata saka ba tasake fitowa da sauri ta nufi ledar da apple dinnata ke ciki.
Bai lura da ita ba harse data dau ledar tanufi kitchen kafin ya hango ta
"Teemah"
Yace da qarfi
Na'am ta amsa mai
Yayah wankewa zanyi neh a kitchen"
Ta tafada mar dan ita azatonta akai ne yake qiran nata.
Dawo nan
Yafada tare da miqewa xaune"
Dawowa tayi da ledar ahannunta tazo gabanshi ta tsaya
Hannu yasa ya kar6i ledar ya ajiyeh agefensa sannan yadaga hannu yakamo kunnanta daya
"Stubborn girl kike so ki zama ko"
Kuka zata fara
Ya daka mata tsawa
" oyah jeki sa kaya my friend"
yafada sannan ya sake mata kunnan nata.
Ban hanaki zama da pant ba ne acikin gida?
Wuche kije kisa kaya ni inbahaka ba zanga mai baki apple din ai.
Yarinya sai rashin jin tsiyah"
Dakuka tajuya dakin nata, taje tasako wata riga mara kauri iya gwiwanta tafito
Duk ta qagu taganta tanashan apple dinta .
Tana shigowa sae kuma ga fanni (house maid) dinsu ce itama tashigo.Kusan sa'ar sa ce itama amma zata dan girme masa kadan
"Fanni kunna min AC pls."
Yafada da dan guntun tsuka da alama zafi Ya ishesa sosai.
Ha 'ah kun iso kenan?
Matar dake shigowa ta wata qofah daban ta ke fadi
Ehh mundawo mummy tun dazu ma"
Matashin yaron ne yabata amsar maganar tata
Murmushi tayi
Sannan tace
ai kuwa najiyo hayaniyar ku dazu ina shirin tada sallah ne shiyasa ban fito ba
ehh nida wannan mara jin ne ai yafada yana kallonta.
ita kuwa ko ajikinta sai faman kokuwa ta ke yi da apple din dake gabanta.
Toh yau din kuma za aji kanku kenan"
ceawr mummyn nasu sannan taqara da cewa
"Yanaga hannunka kamar ciwo yayi ja.
Kallon Teemar yayi yaga ko ajikinta kamar bada ita ake maganar bama.
Bugewa nayi mummy
Ayyah sannu Abbas"
Shiga dakina akan mirror inaga akwai man zafi Kasamu kashafa awurin da wuri.
Toh mummy.
Yace da ita....
Sannan yamiqe daniyar zuwa dauko maganin
Bayan fitarsa ne mummy tadawo da kallonta ga Teeman
tace da ita
"yau Teemah ko kulani ma bazakiyi bako kinsamu apple ya dauke miki hankali"
Dagudu ta taso tazo ga mummyn tana da dariya dan zuwa yanzu taci iya wanda zata iya ci daga ciki kuma ya isheta,daya da rabi ta cinye rabin kuwa sanda mummy ta mata magana ne ta ajiyeshi ta taho gareta
Qoqarin hawa jikin mummyn ta ke yi
mummyn ta dakatar da ita da fadin
"a' a dakata daganan mamana bakiga hannunki bane"
Maza jeki fanni ta watsa miki ruwa sae ki zo ina jiranki
kinji "
Da gudunta tafita ta nufi wurin fannin"
Dai dai nan shima ya dawo dakin yana me qarasa shafa maganin ahannunsa
Zama yayi a inda yatashi dazu
Yarinyan nan akwai rigima mummy......
Wani abin tamaka ko?
Mummyn tafada tana me tattaro hankalinta garesa
Nan yabata labarin
abinda Ya faru dazu awajen me kayan fruits
suka danyi dariya dukkansu.
Shiyasa ai naga ta nutsu ta bata hankalinta akai Ashe rigima tayi akai sosai.
Inka ci abinci sai ka zo ka miqa masa kudin nasa.
Uhmm barin ci abinci tukunna.
Abbas din yafda sannan ya miqe ya nufi daining side ya dibi abincin dai dai yanda xai iya ci,ko takanta bai bi
Dan yasan tunda tasha wannan abin toh ba qara waiwayan abinci zatayi ba.
*Wannan kenan*
ππ»
*Interested* ?π€
*Pls keep following* *me* .........
Akwai cakwakiyah fah agabaπ
*Salmerh md* π
[10/2, 5:48 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
π« *DA BAZARMU* *WRITER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DAZARMU* *MUKE TUN 'KAHO*
Luv storyπ
By
*Salmerh md*
*Alhamdulillah* !,
masoya. *CAPTAIN* *ABBAS* haqiqa naji dadin yanda kuka nuna soyayyar ku ga wannan littafin.hakan yasani matuqar farin ciki marar misaltuwa........kusani in sha Allahu *ana tare* π€
*HAPPY JUMMA'AT* *2 ALL MUSLIMS* ππ»
*Bismillahirah manir* *raheem*
π
Ώ *2*
Mintina goma ya dauka agurin cin abincin,cak ya miqe tsaye
Dakinsa ya shiga ya watso ruwa yayi sallah Sannan yayi zaman shirya jikinsa da kyau.
Abbas yaro ne shi amma sam bashi da wauta ko hayaniya irinta yarintan nan anatse yake komansa kamar wani babba.
Haka idan yayi gayu har mamaki zai baka don irin yadda ya iyah zama ya gyara jikinsa tsab kamar bashi ba.
Fitowa yayi da niyar zuwa gurin mummy,sai kuma yaganta a parlour tana kallon wani hausa movie.
Mummy dake zaune acikin parlourn
kallon inda taji motsin tafiya tayi,sarai tasan Abbas ne dan jiyo irin qanshin turaren dayake amfani dashi da tayi.
murmushi ne ya su6ce mata sanda ya bayyan aidanunta
Aranta ta ke jinjina irin tsabta da kula da kai da Abbas din
yake dashi.
Qaraso wa yayicikin parlourn amma tunkafin yayi magana sai mummyn tariga shi dacewa
"harka shirya kenan"
Murmushi yayi mata batare dayayi magana ba.
'Karaso wa yayi ya zauna agefenta
Sannan yace
"barka da hutawa mummy"
Amsa masa tayi da "yauwa dan albarka"
Sannan tajeho masa tambaya tana qara kallon inda yake zaunen daga gefenta.
"Yanzu zaka miqa kudin mai fruits dinne?"
Kai Abbas din yadaga mata alamar
"ehh"
cewa tayi
"Bari toh na dauko maka kudin "
tana fada ta miqe ta nufi bedroom dinta
2k takawo ta miqa masa.tare da zama a inda ta tashi dazu
Abbas. Bai kar6i kudin ba illah dariyah yayi kadan sannan yace
"Mummy inaga fah bazai wuce 1k ba kudin, dakyar ma inzai kai.
Cewa tayi kar6i de nikam Abbas ka kaimasa,idan kuma kaje da 1k din shikuma yace bai isa bafah, cewa yayi da ita "zai ma isa mummy "
Sa ke miqa masa kudin tayi tana fadin
"ungo kaje Abbas bana son musu"
Kar6a yayi sannan ya juya ya fita yana fadin
"sai na dawo mummy"
"Uhm"
kawai tace dashi sa nnan ta maida idonta taci gaba da kallon data keyi a television.
Teemah kuwa nacan bacci ne ma yadauke ta bayan fanni tamata wanka,kafin ta ahafa mata mai sai bacci ya dauke ta,ganin hakan fanni tasa ka mata pant kawai tabarta,adakin tafito taci gaba da ayyukanta.
,3:00 dot tatashi abaccin, dayake ranar alhamis ce, ba islamiyah,
shiyasa babu wanda ya damu da baccin datayin.
Tana tashi kuwa dakin mummy ta fara zuwa da kwa6a66an fuskarta irin na yarinta da kuma yanayin bacci.
Tura qofar tayi tashiga,gani tayi bakowa adakin,amma jin motsin ruwa abayin yasata gane cewa mummyn nata bayi ta shiga,hakan yasa ta nufi bakin gadon mummyn ta dora kanta akai,amma 'kafafunta suna a qasa.
Tsawon minti biyar mummyn ta qara sannan ta fito daga bayin,ganin Teemahr ahaka yasa ta taho gareta
Mummy
Zama tayi abakin gadon itama sannan ta ce
"ya akayi ne 'yan mata"
Ta fadi tare da dago kan teemar ta tsayar da ita.
lumshashshun idanunta ta sau'ke akan na mummyn batare da tayi magana ba.
Ganin hakan yasa mummyn ta kama hannunta ta koma da ita bayin ta sake watsa mata ruwa dan ta warware daga baccin da tayin.
Tare suka fito da mummyn
Amma sai ita mummyn tawuce gaban madubi ta zauna akan dressing stool da niyyan yin shafa.
Gani tayi Teemar still tana tsaye,
"Ke baki da kunya ne kam da kika tsaya ahakan din"
mummyn tace da ita da dan tsawa kadan
"Maza jeki fanni tasa miki kayanki sai kidawo"mummyn tasake fada mata amma wannan karon idonta naga shafa man data keyi ne.
Pant din data cire shita dauka ta mayar jikinta sannan ta nufo inda mummyn ta ke ahankali,
Jikin mummy taje ta dora kanta a bayanta,
mummyn bata kulata ba itama ta ci gaba da abinda takeyi,sai bayan tagama ne zata miqe sannan ta sa hannu ta jawo ta gabanta
Kallon fuskar ta mummyn tayi da kyau sannan tace "wai ni yau me ke damunki mamana"?
Bude baki teeman ta yi tace
"Daddy! "
Mummyn kallonta tasakeyi tare da fadin
"me kuma daddyn yayi"?
Kwa6ah fuska Teema tayi tare da turo baki kamar anmata wani abin ne
Ganin hakan da mummyn tayi yasa ta fadin
"tsaya toh bari idan na shirya sai in qira miki shi.
Kai Teeman tadaga alamar toh
"Maza kema jeki wajen Fanni kice tasaka miki kayanki, Inyaso sai ki dawo inqira miki shidin kinji mamana"
mummy ne yi wannan maganar alokacin data duba kayan dazata dauko.
Teema yi tayi kamar bataji abinda mummyn tace da ita ba.
Wata super exclusive atampa mummyn tadauko mai kalar ganye da zanen yellow yellow ajiki,baqaramar kar6arta kayan suka yi ba,tana gama shiri takamo hannun Teema tare daukan wayarta suka fito parlour, ahanyan zuwan ta ke cewa "bakijin magana ko Teemah?
So kike Abbas yayi fishi yadaina rakaki school ko?
sai yanzu Teemah ta 6udi baki tace
"a'a mummy zanfara jin magana",
"Karki fada mishi kinji mummy"
Murmushi kawai mummyn tamata,
tunkan su qaraso mummy tafara kwalla qiran fanni,bakinta biyu ana ukun fanni ta amsa tare da nufowa parlourn da hanzarinta.
Atare suka iso cikin parlourn da fanni
"Gani hajiya"
Fannin ta fada tana mai risinar da kanta
Mummyn na shirin zama tace da fannin
"Don allah taimakeni da kayan yarinyar nan,yau rigima ta ke ji dashi"
"Toh hajiya"
Fannin tace tare da juyawa dan dauko
abinda hajiyar ta umarce ta
Mummyn ne taqara fadin
"kinga fanni harda man shafar ta ki dauko min pls"
"Uhm"
fannin tace sannan taci gaba da tafiyah
Mummy wayarta tadago tayi dialling number din Daddy
Sallama tayi bayan yadauki qiran
Shima daddyn ya masa mata
"Yah akayi ne uwar gida?
Lpy lau"
Cewar mummyn sannan ta ciga ba dafadin
"Wannan qiran bana wa bane alhaji na angel dinka neh."
Cewa daddyn yayi "ahh toh bata mana "
"Ina take "?
Yasake Fada !
Teemah da tun da taji muryar daddynta ta matso da sauri kamar ba wacce ta ke ta kwa6a fuska dazu ba.
Kallonta mummy tayi taga yanda ta warware daga sakalcin data ke yimata dazu.
"Ungo mummyn ta ce da ita"
Dawuri ta kar6a sannan taja gefe ta zauna akan wata kujerar daban dan nesa da mummyn,sannan ta dago wayar ta qara akunnenta.
"Daddy" tace da farin ciki afuskarta
cewa yayi "na'am mamana"!
" yah school?
"tace lafiya daddy "
"Yauwa mamana kina karatu ko?
Kai ta daga alamar ehh
Daddy yaushe zaka dawo ?
Cemata yayi "very soon angel zan dawo"
"kin ci abinci ko? Ya tambayeta
Cemasa tayi " a'a daddy apple naci!
Yayah ne ya siyamin ahanyar school dinmu.
yace
"Gaskiya yayah ya kyauta.
Abincin fah ?
"Shima zanci"
cewa yayi
"Toh je kici abincin sai muyi awayar ajima ko "
Toh "tace masa
Sannan ta tashi ta kawo wa mummy wayar
Akunne mummyn tasa ka
Anan daddyn yake tambayarta ina Abbas dinfah.
Dan dariyah tayi sannan ta bashi labarin abinda ya faru briefly,taqarashe da cewa Abbas yakai kudin mai
fruits dinne.
Cewa daddyn yayi idan "Abbas din yazo ta qirashi anjima.
Daga nan sukayi sallama kowa ya ajiye wayar.
Mummy kallon Teema tayi sannan tace iya fitinar dama kenan.?
Dariya kadan teemah tayi sannan tace
"mummy ina yayah yake "
"Ya kai kudin bashin da kika sa yaci....!
Amsar kenan da mummy ta bata.
Toh dayake bawani fahimta tayi ba hakan yasa tayi shiru bata qara magana ba.
mummy Kallon kayan dake ajiye agefenta tayi sannan ta ce
"Oyah zoki saka kayanki"
Tun dazu takawo lokacin kina waya"
Matsowa teema tayi kusa da mummyn.
Mai mummy tafara shafa mata sannan tasa mata kayanta pink din riga da wandon jeans mai kyaun gaske,sosai kayan ya kar6i jikinta.
Mummy tana gama shiryata ta miqe tace bari taje tayi sallar la'asar.
Tafiya tayi tabar Teemah tan game da wayarta awurin,koda mummyn ta idar ma bata sauqo dawuri ba can tayi zamanta adakinta.
Abbas ma sai da yayi sallah a masallaci kafin ya shigo gidan,aparlour ya taddata tana ta game abinta,koda yayi sallama ma batasan yayi saboda hankalinta yadauku a game din datakeyi din.
Zuwa yayi ta bayanta ahankali ya kwace wayar
Sai sannan tadaga kanta da sauri ta juya bayanta
Tana gani. Shi ne kuwa ta taso da gudu tazagayo inda yake,kafin ta iso shikuma yafara jada baya- baya ,itama sai ta biyo shi,guje guje suka farayi yanata mata dariya,ita kuma kamar zatayi kuka tanata binshi akan sai ya bata wayar wai,dayagaji da gudun sai ya zauna akan kujera yana dariyah,zuwa tayi itama inda yake din tana cewa
" yayah ni kabani "
ta ke masa qafa tayi
Dayaji zafi yace "wash"
Ke tsaya ni kin karyan yatsu"
Baya ta matsa kadan tana qare masa kallo
"Ungo "ya ce tare da miqa mata wayar "
Bata kar6a ba itama sai tsugunan datayi awurin qafar tasa inda hannunsa yake yana shafa qafar,nan itama takai hannunta ta daura akan hannun nasa,
"Sorry yayah"
Tafada kamar zatayi kuka,
shikenan ai yahuche ,ya daina zafin"
Haka yace da ita,
Don yadda yaga tayi yau din yabasa mamaki,bahaka tasaba yi masa ba musamman idan tasan ta mai mugunta,dariyah take qara binsa dashi,amma yau harda cewa "sorry"
datayi hakan sai yaji tabasa tausayi.
Abbas akwai sa haquri sosai,bai fiya yin fushi ba akan abu.yakan bi komai ne da murmushi koda na 6acin rai ne,gashi akwai tausayi.
Ita kuwa Teema "sorry" data fada mar, tafada ne dan tsorotan datayi ganin yanayin fuskarsa,dukda wayo bai isheta ba amma tafahimci cewa yaji zafi sosai,kuma gashi bada niyyan mugunta ta takasanba.......arashin sani ne.shiyasa ta ce sorry.
Shikuma abbas ganin tayi hakan yasa shi daure wa yace mata yadaina jin zafinma,duk da azahiri bawai yadaina ji din bane.
Jin yace yadaina yasata danji dadi.
"Kinci abinci kuwa?
abbas ya tambayeta
Jijjiga kai tayi
Alamar a'a
"Oyah muje kici abinci"
Yana fada ya miqe tsaye
Teema kuwa niqe kai tayi gefe.
Ganin hakan datayi yasan bata da niyyan ci dinne.
Shiyasa yace
"Tashi kinji haba angel din daddy"
Still batah kula shiba.
"Tashi muje inbaki abaki"
Yafada tareda riqo hannunta,
Tashi tayi tabiyo shi suka nufi dinning din.
Haka yadinga bata abaki ita kuma tana bashi labarin cewa wai tayi waya da daddy dazu"
"Cewa yayi tayi shiru tukunna bakyau surutu in ana cin abinci, insun gama sai ta bashi labarin.
Shirun tayi kuwa ,shikuma yaci gaba da bata abaki.
Suna zaune awurin mummy tasauqo itama,dayake dama tasan sun saba hakan shiyasa bata kulasu ba.illah tambayar teema datayi wayarta.Don mafi yawancin lokuta teemah bata yadda taci abinci dakanta,musamman in rigimarta ta tashi,sai dai abbas yabata abaki,inkuwa bahaka ba toh sai de tayi zamanta batare da taci abincin ba,randa taga dama kuma dakanta take cin abinta.
Abbas ne ya miqawa mummy wayar dayake ahannunsa ta ke.
Sannan yace "mummy kinga abinda nafada miki ko?
Yafada yana dan darawa,
"Meyafaru?
Tatambayesa.
#800 kawai yakar6a mai fruts din"
Yafada yana qoqarin ciro ragowar canjin daga aljihunsa,
Juywa tayi tafar tafiya.
Cewa yayi" mummy ga canjin"
Ka ajiye akwai gobe ai.mummyn tafada batare data juyoba.
Murmushi yayi sannan yakoma yazauna.daman yasan sarai mummy ba kar6ar kudin zatayi ba.
Ahankali yace "dauko hijab dinki muje mu sayo choculate."
Ai tanajin haka ta miqe da gudu ta nufi dakinta.
Parlour ya koma dan ya jirata.
Bata da de ba tafito da half hijab dinta ahannu
Kar6a yayi sannan ya tsuguna dan yasamata.
Ahankli yace mata "mummy taganki?
Ah ah tace dashi hadi da jijjiga kai.
Toh muyi sauri muje mu dawo,kinsan tahan shan za'ki.....
*Salmerhmd* π
[10/2, 5:48 PM] Ummiyo: π *CAPTAIN ABBAS* π
By
*Salmerh md*
Luv storyπ
π« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
π«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
Dedicated to.....daukacin masoyan CAPTAIN ABBASπ........ina tare daku masoyana.π
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
π
Ώ *3*
fita suka yi daga 'kofar palour cikin sauri don ma kar mummy tagansu,
cikin sa'a kuwa bata gansu dinba har suka je suka siyo choculate din suka dawo gida,
tarkace dayawa Abbas ya siya mata,sai dai bai hallaka kudin duka wajen siyan choculate din ba dan yana tunanin gobe idan Allah ya kaimu karta qara mar rigima irin na jiya a hanyar,shikuma be so ya sa ke dauko abu batare da kudi awurinsa ba
don gaskiya ya na kunyar sa ke tambayar mummy kudi,
Hakan yasa ya rago kusan #500 yabari a aljihunsa.
Duk kayan za'ki Abbas ya siya mata bai ma siyah wa kansa komai ba sai wani sweet guda biyu da basufi #50 ba.
Adakin Abbas din suka yada zango,anan yasata agaba tana ta cinye cinyen ta,daga 'karshe suka fito suka dawo parlour,suka bar ragowan kayan adakin Abbas din.
lokacin ma daf maghrib ta yi,hakan yasa Abbas yace shi kam zai tafi masallaci.Yace itama ta je maza tayi sallah.
Toh"
tace tare da miqewa ta nufi dakin mummy.
Waya ta samu mummyn tanayi,sai kawai ta qaraso wurinta ta zagaya ta bayanta sannan ta kwantar da kanta a kafadun mummyn.
Mummyn bata kulata ba har sai da ta kammala da wayar kafin tace
"Angel din daddy daga ina haka?
Teemar cewa tayi
"Yawo mukaje da yayah"
"hmmm"
Mummyn tace sannan ta qara da fadin
"Lalle teemah,
wato kin samu Abbas kin mnta da ni ko?
Tafada da dan murmushi akan fuskarta
"har zaki je yawo ko ki fadamin?
Teeman
Cewa tayi
"sorry mummy munje siyan cho........
Awwwn.......tace da wuri tare da kama bakinta ita adole kuskuren fa'da tayi.
Murmushi mummyn tayi sannan ta zagayo da ita ta gabanta
"in qarasa miki?
Tafa'di tana kallon idon teemah
Jijjiga kai Teemahr tayi alamun "a'a"
Meyasa ?
Mummyn ta tambaya.
"Yayah yace kar infada miki"
teema tafada da dan fuskar tsoro kadan.
kamo hannunta mummyn tayi ta matso da ita daf da ita,
sannan tace
Kun fi qarfi na ni kam Teemah ,keda Abbas bakwa jin maganata yanzu,shan za'kin nan ban sonshi kokadan amma keda Abbas baku ji ko.?
jijjiga mata kai tayi teemar tare dacewa
" mummy sorry baza mu sake ba"
Bata kula ta ba mummyn kawai ta miqe tsaye dan ji da tayi anfara qiraye qirayen sallah.
Bayan anyi sallahr isha suka hadu a dinning dan cin abinci.
Abbas yana bawa teemah abakinta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 67